Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafito, sannan Mahmud pilot shima yafito yaje yamik'awa Billy hannu itama tafito tare da yimasa kallo d'aya ta noce kai k'asa,

Bilal, Bassam da junior na hango cikin suit riga da wando iri d'aya milk colour sai rigar can ciki popul da necktie shima milk, takalminsu halfcover sun fito tare da nufo wajen, suna zuwa suka shiga gaba tare da gyara tsayuwarsu, sauti DJ yasaki dake nuna alamun cewa tabbas ga amare da angwayensu nan sun iso nan take kowa ya zubawa k'ofa ido yana jiran shigowarsu.

Ahankali su Bassam suka fara shigowa sannan yaya mahmud da faraaha nabiye dasu Batool da dr.Ahmad suma suka biyo baya sannan su Billy da yaya Mahmud pilot suka shigo, wow mutanen wajen suka fad'a saboda ganin yanda tsarin nasu yayi kyau, gashi sai taku sukeyi d'ai bayan d'aya tamkar suna bin sautin kad'an, Basmah kuwa suka shigo tare da sadeeq abokin yaya Mahmud da sai faman manne mata yakeyi ita kuma tana basarwa kamar bata fahimta ba, ga kuma Khalid abokin dr. Ahmad da shima sai shisshige ma Zainab yakeyi ita kuma tana jin haushin sa, bayan duk sun zauna akujerun da aka tanadar masu kowa da matarsa mc yashiga kwararo dad'a d'an kalamai da zasu sanyaya zuciyar angwaye da amare cikin raha da nishad'i yayin da duk lokacin da ya d'auko kalmah ya ajiye sai hall d'in and'auki dariya, saida mc ya tabbatar ya gama saka kowa nisha d'i sannan akaci gaba da gudanar da shagalgulan bukin yanda ya kamata, mc ne yafara magana cikin barkwanci irin nasu yace

"So iyaye, yanne, k'anne so dama sauran mutanen dake wurinnan irinsu k'awayee, abokanai kai harma da 'yan uwa da abokanan arzik'i muna so gaba d'aya amik'e tare da tafawa don karrama angwaye da amare saboda nuna tsantsar farin cikinmu agaresu, but kafin nan zanso d'aya daga cikin wud'an da ke wajennan yafito don bada tak'aitaccen tarihin wud'annan ma'auratan" kasancewar babu wanda yasan ta inda zai fara bada tarihin ma'auratan yasa har aka kwashe fiye da minti biyar mc namagana amma babu wanda yafito, sai murya dake tashi k'asa k'asa mutane cike da mamakin taya hakan zai faru"

"To angwaye idan harfa aka kasa samu dolene zaku bamu amarenku don subamu tarihin kansu da kanku, ko kuma tarar dubu hamsin ga kowane ango, so DJ let have a count to five" kowacensu kallon angwonta tayi kamar zatayi kuka saboda bazasu iya tsayuwa agaban iyaye su wani bada tarihinsu da nasu ba, can mc yafara k'irga tare da taimakon DJ na tamashi "5.4..3...2...." Kafin su ida five sai ga Basmah tafito tsakiyar wajen cike da kunya ta duk'ar da kanta k'asa, nan waje ya d'au ihu tare da mik'ewa tsaye harda angwaye da amare ana tafi, kallon juna sukayi tare da sauke ajiyar zuciya kafin can suji muryar mc natashi

"Hello" duk aka amsa da hy, hall d'in yayi tsit kallon Basmah yayi had'e da cewa "what is ur name" ya karamata microphone abaki cikin lallausar muryarta tace "Basmah" had'e da folding hannayenta akan k'irji.

"Basmah ko zamu san meye alak'arki da wud'annan amaren har ma da angwaye" yasake karamata microphone din abaki, juyowa tayi takallesu had'e da yin murmushi sannan tace

"They are my relatives"

"Da hausa kenan 'yan mata?" takarb'i lasifikar tana dariya tace

"'YAN UWANA NE!" tare da duk'ar da kai k'asa tana kallon yanda hasken wajen ke jijjuyawa ajikin tays d'in dake k'asan wajen

"'Yan uwanane!, nice relation, shin ko zaki iya bamu tak'aitaccen tarihinsu.

"Yes comfirm" nan tafara bada tarihin yaya Mahmud dasu Batool tana d'an had'awa da barkwanci ana dariya daga k'arshe tace

"Both dr Ahmad and sister faraaha are very kind and very nice person dt have a good moral behavior of helping people in our society, so i think no need for their history because is always upon to the most of our people in the society, thank you all" tana gama fad'ar haka tabar wajen don gudun kada mc yak'ureta saboda batada wani tarihi da zata iya bayarwa akan dr. da kuma faraaha, sosai mc yayi appreciating d'inta, gaba d'aya wajen aka d'au tafi don ba k'aramin burge mutane Basmah tayi ba, nan aka sakarwa amare sauti suka fito suka d'an tattaka masoyansu da masoyan dady sukayita fitowa suna yimasu lik'i da ruwan kud'i can na hango maku sis 'yartulluwa andija anyi ture kaga tsiya sai faman lik'i takeyi da rafar naira goma goma hankalinta kwance batare da tadamu da 'yan dubu dubu da taga sunata yawo awajen kamar ruwa ba, tsabar gudun kar arena mata wayau tasake turo d'an kwalinta gaba tana taunar cingum fuskarta d'auke da wani makeken glass da ake kira no respect, murmushi nayi tare da d'aga mata baban d'an yatsan hannuna alamar jinjina mata da k'ok'arin da tayi na samun damar shigowa wajen batare da an hanataba,

Nan mc ya gabatar dasu teburin yanka kek wanda nan ma abun gwanin ban sha'awa akayi komai sannan aka wuce wajen jerin abintayyen da aka tanada kala kala da ake kira serve ur self, angwayene agaba sai sauran mutane suka biyo layi abayansu, sai da kowa ya kammala d'ibar abunda yakeso saiga 'yan home of novel da 'yan Asy khalil novels suma sun biyo layi sai d'ibar ganima sukeyi sukuwa 'yan group din hajjace novel da zauren sainah tuni na hangosu can gefen amare kowace na ruguguwar kashe salfie dasu hatatta 'yan group d'in khairat up suma sun samu damar halartar wannan dinner don bak'aramin mamaki nashaba lokacin dana gansu,sara2zamfara ce ta ahedamun ai wajen Ummi sukaje tanemi masu izini aka basu damar shiga, maganar gaskiya anci an chashe sosai awajen bukinnan dady kuwa banda wasar baki babu abunda yakeyi tebur tebur yabi yana yiwa mutanen dake cikin hall d'in sannu da kuma godiya, juyowar da zanyi nahango 'yan rano online auna lek'e ta window suda 'yan Billy s fari novels, aunty fareeda ce nafara ganewa tana yafitoni da hannu, juyawa nayi ina kallon mutanen hall d'in kowa na harkar gabansa sannan nak'arasa wajenta, dariya nayi tare da cewa

Aunty fareeda ya haka? Ina kika baro Ummie da oum imaan dasu Hijjah yaks ga naman kaji dana raguna nan na yawo ta ko ina"

Kibarni kawai wud'an can tsinannun securities d'inne suka hanamu shigowa kinganmu nan haddasu zee kitchen's da oum aslam dasu baby leemah duk anhanamu shiga, pls ungo ledata don Allah zubomun naman kaji, ji nayi an wafce ledar ahannun aunty fareeda kafin inkarb'a ashe meamah ce tace

"Tab wlh baza'a zubobah haka kurum kusa gp d'inmu yayi down" tana watsawa aunty fareeda harara, kamar zatayi kuka tace

"Meamah ni zakiyiwa haka, ashe dama bakida m"

"Eh naji amma baza'ayi wannan abun kunyar ba" nan taja hannuna muka wuce aunty fareeda nafad'in "meamah..meamah.."

Muna barin wajen mukaci karo da haifa ita da Zainab pinki sunrik'o Bilal da Bassam, kallonsu meamah tayi tundaga sama har k'asa tace

"Oh iyayen shisshigi wato ku har iyayinku ya kaiku nan" basu ce mata k'ala ba suka nufi wajen mom dasu, kallonsu Basmah tayi had'e da yin murmushi tace

"Sannun ku sisters" ai kamar jira sukeyi da sauri suka amsa da yawwa had'e da mik'a mata hannu auna rige rigen fad'in sunansu Zainab pinki tace

"Sannu Yayya Basmah agaskiya mu masoyankine muna matuk'ar sonki saboda yanda kike son 'yan uwanki da kuma irin role d'in da kike takawa wajen nuna jajircewa akan hak'uri" haifa taci gaba da cewa "hakane gaskiya yayya saidai ni inaso ki k'ara koyamun yanda kika had'a ferfesun kifinnan naki da ranar wajen breakfast da yaya mahmud yasaki" tak'arasa maganar cikin sigar zolaya da dariya,

Dariya Basmah tayi had'e da cewa "it's pass sweetheart, let take a pics" tafiddo wayarta tare da shiga tsakiyarsu suka d'au hoto, nan suma suka cicciro nasu wayoyin da yake ba k'arya suka d'auka tare da yimata godiya, duk k'wak'war meamah akan sai tayi hoto da dr.Ahmad hakan ya faskara don Batool takasa ta tsare ko nan da can bata bari yaje ganin haka yasa tamik'o mani wayarta had'e da cewa zataje wajensu tayi kamar zata d'auki gorar ruwa don Allah in d'aukesu hoto, aikuwa ashe Batool na kalle da duk wani motsi nata tana zuwa wajen tasa mata k'afa sai ga meamah ak'asa tafad'i daidai lokacin nikuma na d'auki hoton, ganin Batool ta wurgomin idanuwanta yasa nab'oye wayar had'e da juyawa nabar wajen don kada nima tasamu k'etar da zata yimun, can na hango maku meamah ansa mayafi had'e da rufe gefen fuskarta wanda da alama ya kumbure tayo inda nake, ashe duk abunda kefaruwa aunty fareeda tahango ta taga nan ta azamata dariyar k'eta harda hawaye had'e da cewa

"Ala gui meamah, dama duk wanda yahana tukunyar wani tafasa to tasa ko zafi bazatayi ba".

Nan dai aka kammala dinner cikin farinciki da walwala Ummi tasa aka kwaso souveneirs masu uban yawa tace abawa su aunty fareeda tare da naman kaji ak'aton tray anyi raping dinsa da takardar nan mai k'yalk'yali sunata murna tare da cewa Allah yabar masu Umminsu agidan dady....

_oum imaan k'orafinki yakarb'u asha karatu lafiya_



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____83πŸ’Ž


Dady baibar wajenba saida ya tabbata angama kwashe kowa wud'anda suka samu hallara wajen bukin sannan shima yashiga motarsa ya wuce gida, yana isa tuni Ummi tahad'a masa ruwan zafi masu zafin gaske saboda kaida kawon da taga yasha, kallonta yayi had'e da cewa

"Sannu rabba'atul bait, ngd Allah yayi maki albarka, amma ataimaka a ida ladar mana ko kuwa?" saboda ta fahimci meyake nufi yasa har zata fita tadawo tacire hijab d'inta ta ajiye akan gado sannan ta rakasa har cikin bayin ta taimaka masa ya watso ruwan sannan suka fito atare, kasan cewar yariga yayi sallar sa ta isha'i da kuma shafa'i da wuturi yasa yana gama tsane jikinsa yajawo Ummi had'e da hayewa kan gado yaja masu blanket, ahankali ummi tafurta masa akunne "Dadyn yara akwaifa gajiya, kuma gashi Bilkisu kad'ai nabaro a part d'in sai 'yan buki, Bilal kuma na wajen Bassam can zai kwana saboda d'akinsa na saukar da bak'i, kaga da kunya subud'e idanuwansu suga bana nan" cikin wata kasa lalliyar murya dady yace

"To mehakan zai canza rabba'atul bait, ai sunsandai wajen mijinki kika tafi, ko bakyason nasama maki wata abokiyar fira tunda Bilkisu guduwa zatayi tabarki?" Lumshe idanuwa Ummi tayi tana karb'ar sak'onnin da yake aika mata dasu kafin can taji yamik'a hannu ya d'auko wayarsa, lambar Bilkisu yakira lokacin tana gyarawa Ummi d'akinta saboda yanda 'yan buki suka b'ata mata shi duk da bawata taruwa akayiba sai zuwa gobe atashi safiyar d'aurin auren, tana d'agawa dady yace

"Bilkisu ki kulle part d'in naku idan kowa ya kwanta kuma kitabbatar kinyi addu'a kafin kirufe kinji ko?"

"Eh dady saida safe" tafad'a, yana kashe wayar ya kalli Ummi had'e da cewa

"Ina shikenan ko?, kinji 'yar taki ko nemanki batayi ba don tasan dadynta nabuk'atar kulawarki" murmushi tayi tare da rufe idanuwanta shikuma ya kashe masu wutar d'akin dake gefen bedside wardrobe, nan take suka tsunduma duniyar masoya tamkar wasu sababbin ma'aurata.

Billy kuwa tana gama waya da dady taci gaba da gyaran gadon da takeyi, acan gefen gado tana shara saiga tissue tasharo mai uban yawa da jini ajikinta wanda hakan ba k'aramin tsoratata yayiba, mamaki tashigayi son tasan ummi ba ad'akin ta kwana jiya ba yayya Basmah ce takwana ciki to idan hakane kenan ita tatara wud'annan abubuwan kuma da alama mantawa tayi bata zubar ba, shin to inhar hakane wannan jinin meye ajikin tissue d'in?

Ganin batada wanda zai bata amsar wud'annan tambayoyin nata yasa taci gaba da shararta, bayan ta kammala tafeshe ko ina da room freshener sannan tajawo d'akin ta koma nata, ganin ita kad'aice kwance aciki don Zainab daga wajen dinner tabi baba k'arami akan cewa zata jene ta d'auko kayanta sai tadawo gobe yasa Billy ta tashi had'e da d'aukar hijab d'inta ta saka, wajen wata cousin d'in Ummi taje tace "momy jidda don allah kitaso kirufe k'ofarnan ni wajen 'yan uwana zanje inkwanta"

"Ke Billy sai kibarmu nan mukad'ai kitafi can to mezai k'araki dashi idan kika kwana can da nan d'in bazai k'araki dashi ba?"

'Bata rai Billy tayi had'e da cewa "Momy jiddah nifa bana son haka, kamarya mezai k'arani dashi? 'YAN UWANA NE fa, gaskiya kada kikoma yimun hakan banaso" tana gama fad'ar hakan tajuya tabar falon tare da cewa

"Saida safe kuma kiyi addu'a idan zaki rufe"

"Hain shashasha wacce batasan abunda takeyi ba, mace bata sonku kuda uwarku amma sai shsshige mata kikeyi ita da 'ya'yanta samnar banza samnar wofi" mom Jidda tafad'a cikin jin haushin Billyn

"Eh koma meye naji d'in" Billy tafad'a itama lokacin data ida ficewa daga cikin falon tanufi part d'in mom

Ab'angaren mom kuwa tunda suka dawo bayan ta watso ruwa takoma d'akinsu Batool dake zaune ita da yayya Basmah suna fira, zaunawa itama tayi cikinsu sukaci gaba da firar abun gwanin ban sha'awa uwa tare da 'ya'yanta, wayar Basmah ce dake cikin jikka tayi k'ara Batool tajawo jikkar had'e da ciro wayar tamik'a mata, karb'a tayi tanabin special no d'in data gani arubuce ankirata da ita da ido kafin can ta d'aga,

"Hello, assalamu alaikum" taji anfad'a

"Wa'alaikassalam" itama tamayar masa da amsa ta b'angarenta,

"Kina magana da sadeeq ne abokin yayanki"

"Oh Allah sarki yaya sadeeq, bakaji gajiya ba?"

"No..indai akanki ne babu wata gajiya da zata iya hanani kira don inji muryarki" murmushi basmah tayi duk da dai harga Allah bataji tana sonsa ko kad'an ba, amma zatayi accepting d'insa tagani kozai iya cire mata tunanin da k'aunar Mahmud pilot kuma yamaye mata gurbinsa, muryarshi ta tsinkayo akunnenta yana fad'in

"Kinyi Shiru Basmah kona takurakine?" Mik'ewa tayi tabar d'akin takoma falo takwanta akan kujera tree seater sannan tace

"No!.ko kad'an just dat ina jin baccine"

"Ayya ina tuba, dama zuciyatace ta tirsasani kiranki akan sai taji zazzak'ar muryarnan taki zata samu natsuwar da zata bani damar yin bacci kuma.." Ai kafin yarufe baki Basmah taji wani irin ciwo da bazata iya kwatantasaba ya taso mata,

"innalillahi wa inna ilaihirraji'un" tafad'a da k'arfi had'e da mik'ewa tsaye tanufi d'aki har suna neman karawa da mom dake k'ok'arin fitowa daga cikin d'akin zata shiga nata

"Ke lafiya?" Mom tafad'a tana kallonta, k'ok'arin danne yanayin da takejin kanta ciki tayi tare da d'an sosa k'eyar kanta sannan tace

"Fitsarine ya matseni mom"

"Mts..Basmah yaushe kika tsiri wannan d'abi'a kuma?, maza kije kiye mana kintsareni da wud'annan idanuwa naki, ai wannan d'abi'a ba mai kyau ceba ko kad'an inma zaki dena kidena" sannan tawuce bedroom d'inta tanaci gaba da fad'an,

Hayewa tayi kan gado had'e da lumshe idanuwa tana fitar da lumfashi ahankali, kiran sadeeq ne yasake shigowa awayarta, saida takusa tsinkewa sannan tad'aga har lokacin idanuwanta na arufe

"Hello" tafad'a batare da tasan cewa shine yasake kira ba, wata ajiyar zuciya yasauke jin muryarta da yayi had'e da cewa

"Basmah are you ok"

"Yeah! Yaya sadeeq am ok tafad'a had'e da cewa sorry kaji natsinke maka waya ko?"

"Ayya badamuwa, tunda dai lafiya kike"

Yanayin da take jin kanta aciki daurewa kawai takeyi tana wayar dashi don kada yaga tayi masa walak'anci bawai don tana buk'atar hakan ba, haka taci gaba da amsa wayarsa har saida ya gaji don kansa yayi mata sai da safe, saboda tund'azu shikad'ai ke surutunsa, batayi minti biyar da gama waya dashiba kawai taji wani irin azababben ciwon kai yataso mata, rik'e kan tayi tana k'ok'arin yiwa Batool dake zaune kan gadon tana tofa addu'ar bacci zata kwanta magana kawai taji kamar an cinna mata wuta acikin zuciya, nan take ta tuna da cewa gaba d'aya yau Batasha maganin taba saboda baau wuni agida ba gashi kuma hankalinta ya d'auki da suka dawo balle tasha sai yanzu da taji ciwon yataso mata, ai kafin tasake yunk'urin yin wani abu saiga jini nafita ta hancinta, hannunta tad'a ya sauka saman kafad'ar Batool yasata juyowa,

Arud'e take kallonta cikin tashin hankali ganin jinin dake fitowa ta hancin ta, don tunda Basmah tafara bleading tahanci daidai da rana d'aya bata tab'a bari wani yagani ba, afirgice batool tace

"Yayya, meyake faruwa, jinifa kefitowa daga hancinki?" Cikin k'arfin hali tasa hannu tagoge jinin dake neman gangarowa cikin bakinta had'e da cewa

"Batool bud'e wardrobe maganina na nan saman kaya kid'aukomun, gaba d'aya yau namanta bansha ba"

Batool da gaba d'aya tagama rud'ewa saukowa tayi kan gadon batare da tabi takan maganin da tace ta d'auko mata ba tafice d'akin aguje, wannan karon d'akin mom tafara shiga tasanar da ita halin da 'yar uwarta keciki sannan tanufi d'akin yaya Mahmud shima tafad'o masa, tsabar firgicewa yaya dagashi sai boxer da bes yafito har suna rice rigen isowa d'akin shida Batool dat fashe da kuka, yana zuwa ya tadda mom rik'e da ita itama tana kukan, kallonta yayi tana k'ok'arin goge jinin da tissue d'in da mom tad'auko tare da cewa

"Is over Basmah, wlh wannan karon duk abunda zai faru saidai ya faru, amma dole kowa yasan halin da kike ciki, taya za'ayi muzuba ido kirasa rayuwarki saboda farincikin 'yar uwarki, to koda za'a fasa d'aura auren mune gaba d'aya banda gobe saidai afasa, amma sai nafad'i dalilin wannan ciwon nakai, haba Basmah dubi yanda k'arfin halinki kenema ya salwantar maki da rayuwa to bazan juri hakan ba ko kad'an nayi iya abunda zan iya amatsayina na d'an uwanku dake sonku gaba d'aya" kallon mom yayi sannan yace "mom kidena kuka dole yau kisan abunda muka dad'e muna b'oyewa akan wanna ciwon da Basmah keciki"

"Pls yaya don girman Allah kada kafad'a, kada kafad'i abunda zai rusa farincikinmu don Allah, mom karki tab'a yarda da yaya" Basmah tafad'a daidai lokacin da Billy ta kawo bakin k'ofar d'akin, har zata shiga sai taji Batool namagana cikin kuka kamar haka

"Yayya dolenefa mom tasan komai don ita mahaifiyar muce sannan yanda muke son Billy kema haka muke sonki, natabbata itama Billy bazata so ganinki acikin wannan yanayin ba don itama tana sonki, har sau nawa zaki hak'ura da farincikinki, har zuwa wane lokaci zakuci gaba da sadaukar da rayuwarki akan soyayyar 'yar uwarki, duk da bamuda yak'ini akan yaya Mahmud zai soki irin soyayyar da kike yimasa tun baki mallaki hankalinki ba yakamata ace ansan da wannan matsalar taki in akwai yanda za'ayi a maganceta sai ayi amma dole kidena azabtuwa haka dole kidena shanwahala akan soyayyar d'an uwanki da zaki iya mallakarsa amatsayin mijinki, mom yayya tadad'e tana son yaya Mahmud d'in borno kuma koda sukazo garinnan ashirye take data nuna masa haka, amma duk yadda tayita k'ok'arin nuna masa soyayyar da take yimasa yakasa fahimtar hakan daga k'arshe ma saita fahimci cewa gaba d'aya hankalinsa baya kanta yana wajen 'yar uwarta, tundaga lokacin da taji yafurtawa Billy soyayya kuma tafahimci itama tana sonsa tad'auki d'a marar yak'i da zuciyarta akan tahak'ura dashi wanda gaba d'ayanmu nida yaya muka goya mata baya akan haka saboda soyayyar da muke yiwa 'yar uwarmu bayan munsan cewa tana k'aunarsa fiye da tunani" share hawaye Batool tayi cikin kuka tace nagaji da ganinki kina shan wahala haka bayan gaba d'aya keda Billy duka 'YAN UWANA NE kuma ina sonku,

"Haba Batool yanzu mekikayi haka, ashe alk'awarin kenan da kika d'aukarmun? Ashe akwai ranar da zaki iya bud'e baki kitona wannan sirri da muka riga muka binne tsakanina daku, shin atafi ina son yaya mahmud to ai itama Billy atana sonsa fiyema da yanda ni nake sonsa kuma shi ai ita yace yana so bani ba, kada kuzamo masu aon kai yaya, wlh natabbata son da suke yiwa junansu zai iya jefasu mummunan halin da yafi nawa idan akayi yunk'urin raba tsakaninsu, shin yanzu meye amfanin yasan da soyayyar dani nake yimashi, shin kunyarda cewa kurasa 'yan uwa biyu aduniya akan kurasa 'yar uwa d'aya? a gaskiya baku kyautamun ba ko kad'an idan kuka yimun haka kuma kun karya zuciyata akan yardar da nake da ita akanku" wani irin tarine ya sark'eta tad'ago kai tana kallon mom dake faman sa tissue tana tare jinin dake fitowa cikin hancinta sannan da k'yar taci gaba da cewa

"Mom nasan ke uwace da zata iya rufewa 'yarta asiri, don Allah kada kibari maganarnan tafita, koda hakan na nufin zan rasa rayuwata, kada kitab'a basu damar aikata wannan kuskuren har sai farincikin 'yan uwana da burinsu ya cika " kallon mahmud mom tayi dake tsaye hawaye naziraro mata a idanuwa tace

"Son jeka kafiddo mota muje asibiti da ita tukun" da sauri Basmah ta k'ank'ameta tare da fashewa da kuka tana fad'in

"Pls mom don Allah kada kukaini asibiti, narok'eku daku barni agida akwai maganin da likitana yabani ina sha," kallon Batool tayi tace "Batool d'auko maganin dana cemaki in sha, zansa mu sauk'i sosai, zan samu relief kafin gobe, mom nayi maki alk'awari gobe da kaina zanje inga likitan dake dubani kafin afara walima dama dalilin tashin ciwon saboda mantawa danayi yau bansha maganin ba gaba d'aya shiyasa" jin cewa akwai maganin da zai taimaka mata da gaggawa yasa mom tace Batool ta d'auka abata tasha amma idan ciwon bai kwantaba dole suje asibiti komai dare,

Wani irin kukane ya kuccewa Billy dake lab'e tana saurarensu tayi saurin sa hannu ta toshe bakinta had'e da ficewa part d'in aguje...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

UπŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Bless upon you people who says bad word to me, thank you so much, amma ina so kusani babu abunda zai canza gayanda nad'auko labarin nan insha Allah, I feel so bad ga yanda kuke k'orafi da nuna anajan littafi ko ana jamaku rai after all am here trying all my possibilities wajen ganin nakammala littafinnan dis week, Basmah zata mutu ko bazata mutuba, zata auri Mahmud ko bazata auraba is all about of her destiny, ciwon Basmah is so worst or not, duka fiyema da hakan nafaruwa kuma azahiri ana samun hakan acikin rayuwar al'ummarmu, ni akoda yaushe fatana asamu darasin da za'ayi koyi dashi daga ciki, bawai inbi ra'ayin kaina kona fan's ba, wlh mutum d'aya idan yak'aru da wannan littafin Alhamdulillah kwalliya tabiya kud'in sabulu, so for those who says anything they want on me, pls keeps it up, am always free heart bazan tab'a rik'eku araina ba_😍
πŸ’ŽPage_____84πŸ’Ž


Dagudu ta isa part d'insu lokacin mom Jidda nashirin rufe k'ofa don bayan tafiyarta ba rufe ba saboda saida suka gama fira ta watso ruwa sannan tazo zata rufe k'ofar saiga Billy tagani tataho aguje tana kuka da kad'an tabingijeta, da sauri mom Jidda tajaye had'e da bin bayanta da kallo har tashige d'akinta, mere baki mom Jidda tayi had'e da cewa

"Ikon Allah" sannan tarufe k'ofar had'e dayin bisimillah don neman tsari daga shed'anun aljanu, bayan tarufe kuma ta tottofa addu''o'i ajikin k'ofar sannan tawuce d'akin Billy, ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita yasa tak'arasa daga cikin d'akin had'e da zaunawa gefen gadon da take kwance takifa kanta akan pillow, dafata tayi sannan tace

"Ke Billy lafiyarki kuwa? Mekuma yadawo dake bayan kince wajen 'yan uwanki zaki kwana?" Shiru tayi mata batare data tankataba taci gaba da kukanta kamar ranta zaifita,

"Au shine kikayi kunnen uwar shegu dani sai kace nina b'ata maki rai, ina ai saida nace kiyi kwancinki nan amma kikak'iji waike mai 'yan uwa harda wani cemun 'YAN UWANA NE, yanzu kuma da kikaje aka shuko maki rashin mutunci aka yimaki walak'anci shine zakizo ki ishemu da kuka har ina yimaki magana kina k'yaleni, to ai shikenan ke kika sani" tamik'e tare da ficewa abunta tana fad'in "yarinya can gasu gada....waya aikeki?"

Ita kuwa Basmah bayan tasha magani, mom takalleta had'e da cewa "duk da nakasance mai matuk'ar son kanta, da goyawa 'ya'yanah baya akan abunda sukaso to wannan karon dolene in kauda kaina domin duka abunda yafaru akanku nice sila tunda nakasa kula daku lokacin daya kamata sai yanzu da lokaci yak'ure, Basmah kinyi kuskure sosai wajen tirsasa zuciyarki dena son abunda kika sancewa bazata tab'a iya hak'ura dashi ba, don haka dolene kiyi hak'uri har Allah yayi maki wani zab'in mafi k'ololuwar alkhairi akanki, matuk'ar kinsamu sauk'i nayi alk'awarin bazan tab'a bayyana sittin zuciyarki ba da kuma halin da

Please Login or Register in order to submit comment