Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shanye wannan abun ba!"

"Banza kya fad'i haka mana, yo ai naga kezai amfana bani ba, idan ma baki shaba ai don kanki, ni bari ma natambayeki ina kika kai d'ayan na ruwa? Yafi wannan gumbar fa aiki kuma kinsan yau kike da tabbacin zaiyi maki amfani don nasan dole alhaji ya kwashi amarci, kinga daga nan karagar tadawo hannunki sai yanda kikace agidan"

"Hmmm bari kawai k'awata yana nan har namatsu isha'i tayi wlh, ki nake kamar ma nasakashi yanzu don zaifi aiki ko?"

"Aa ban fad'a ba, inkikayi bansaki ba, wannan irin gaggawa har ina, kiyi amfani da wannan lokacin kafin dare kije anyi maki qunshi da kitso mana, in kuma ba haka ba kyaji da rawar kanki ke kad'ai"

Allah sarki mom indama kin raba kanki da wahalar wannan shaye shaye da ture ture don kam dady yariga daya d'an d'ashi amarcinsa da tsohuwar zumarsa kuma rabba'atul baiti d'insa.


















*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_ALHMDLLH I feel so bless to have u my fans, u made me so happy for ur sweet and amazing comment in my previous page, ubangiji Allah ya albarkaci kowannenku tare da ahalinsa, MOM luv's u 🀣🀣🀣🀣 tana mik'o gaisuwa da babbar murya, STAY ALWAYS BLESS MY FANSπŸ˜˜πŸ’‹πŸ˜˜_


πŸ’ŽPage_____32πŸ’Ž


Mom dai ba haka tasoba atunaninta idan tasaka maganin yanzu zaifi mata aikin don haka da taji abunda kilishi tafad'a sai takaici yasa tabar wajen cike da jin haushi, ita kuma hajia kilishi ta shareta ba tare data kula taba taci gaba da ida har had'a 'yan kayanta,

Ummi kam ya mahmud tabawa kud'in da dady yabata tace idan yafita yabiya ta banki ya kaimatasu, tunda akayi maganar mom zata dawo yau cikin Billy ya murd'a tare da fad'uwar gaba amma saboda kada tanuna yanayin da take ciki 'yan uwanta suji ba dad'i yasa tadanne dukkanin damuwarta tana tayasu murnar dawowar mom d'insu, shikenan ta tabbata daga yau farincikin da suke ciki ita da umminta da d'an uwanta zai tawaya, gefen da takoma tayi shiru tana wannan tunanin yasa yaya Mahmud fahimtar halin da take ciki, matsowa yayi akusa da ita tare da kallon fuskarta yana had'a girarsa tasama.

"Meyake damun 'yar qanwa tane?" Yafad'a cikin yanayin da yasa Billy sakin murmushi, lumsa idanuwanta tayi sannan tabud'e tana kallonsa tace

"Me kuwa zai dami qanwar nan taka matuk'ar tana tare da kai?"

"Hmm! to idan hakane tunanin me takeyine? Kodai tasamu wani saurayinne daya d'auke mata tunani"

"Tab...hakan ba abu bane mai yuyuwa ba, domin babu wani saurayin da zai iya fara tunkarata matuk'ar bata hannun yayana ya biyo ba" dafe goshi mahmud yayi had'e da game hannuwansa waje d'aya yana begging d'inta.

"Narok'eki kisanar dani damuwarki my sis kada kisa nayi tunanin ko k'anwata aure takeso" duk da yasan dalilin shiga wannan damuwar tata yafad'i hakan ne don yasan yanzunnan zata saki damuwar saboda bata son zancen, ai kuwa yana rufe baki tab'ata fuska had'e da turo baki, dariya yayi yana nunata da d'an yatsa kafin yace "Bilal, Bassam kuzo kuga fuskar auntyn nan taku, kufad'amun da metayi kama" da gudu Bilal ya rugo yana turo idanuwansa awaje kafin yace

"Lahh yaya kamar fuskar baby Japanese d'innan da muka kalla yau da safe...kai kuma k'aryane da chaki chan tayi kama" muryar Bassam daya k'araso wajen sukaji yana fad'ar haka,

Rufe idanuwa tayi ta rumk'e hannuwanta tasaki wata k'arar da tasa Bassam da Bilal guduwa suka b'uya a bayan yaya Mahmud dake kwasar dariya har da tuntsirawa yana rik'e ciki, ganin haka yasa suma suka biye masa sunata faman yimata dariya, cikin jin haushi da takaici tajawo throw pillow d'in dake kan kujera ta nad'awa ya Mahmud shi agefen kafad'a, mik'ewa yayi tare dasu Bassam suna zagayen kujerun ita kuma tana biye dasu tana neman duka masu pillown har lokacin basu dena yimata dariyar ba, ganin bazata k'yalesu ba yasa suka shige kitchen wajensu ummi dake tsane plates d'in dasu Basmah ke wankewa, kallon fuskokinsu yayi yaga suma dariyar sukeyi don duk suna sauraren abunda kefaruwa tund'azu, Billy na shigowa taga gaba d'ayansu suna dariya har da Ummi aikuwa a fusace tayo kansu Bilal, Ummi dake k'ok'arin b'oye tata dariyar tayi saurin dakatar da ita, kunnuwan Bassam da Bilal takamo mata takawo agabanta tana fad'in

"Maganar gaskiya yaya baka kyautaba, yanzu har Bilal nada bakin kiran Bilkisu da baby Japanese, shi bakaga tashi fuskar bane?, shi kuma wannan hadda wani cewa chaki chan don tsabar rashin ji"

Maburkakin dake gefenta tad'auko tamik'a mata tana dariya

"Allah ungo wannan kizazzane su" ai kuwa kamar jira Billy takeyi, tana karb'a tafara tsalawa Bilal shi a d'uwawu da sauri ummi ta sakesa ya fice aguje haka shima Bassam so biyu ta tsulamasashi ajiki zatayi na ukku ummi tasakesa shima yafice yana fad'in,


"D'aya na fuskar chaki chan dana fad'a shi kuma d'ayan dukan na fuskar jet-li ne daban fad'a ba"

Ai kuwa gaba d'aya suka sa dariya, girgiza kai ummi tayi tace "Bassam, Bassam Allah dai ya shirya" kan yaya Mahmud tayo dake gefe rik'e da maburkakin shima zata doka masa yayi saurin tsayawa da dariyar had'e da rik'e kunnuwansa yana fad'in "wayyo aunty Billy am sorry natuba" jump frog yafarayi yana cigaba da fad'in sorry aunty Billy, yanda yakeyi sai yabata dariya ai kuwa da wayo da wayo yasamu yafice daga kitchen d'in.

Kallonta Batool tayi kafin tace "To jet-li ai seki zubar da makaman fad'an tunda yayi maki wayau ya gudu" tana dariya takarb'i aikin da Yayya Basmah keyi tana fad'in "kinjita ko ummi?"

"Tsakanin kune ai kunfi kusa" ummi tafad'a, kallon Basmah tayi alamun takawo mata k'ara itama tabud'e hannuwanta alamar baruwana,

Cike da nishad'i suka kammala aikin, bayan sun gyara ko ina tsaf sannan gaba d'ayansu suka nufi part d'in mom don su gyara kamar yanda dady ya umurta. Kallon Billy Batool tayi tace

"Twiny kishiga bedroom d'in mom kigyara tunda kinsan bawani gyaran gado na iyaba, muje in d'auko maki sabon bedsheet d'in da zaki shimfid'a akai, ke kuma yayya Basmah sai ki shiga kitchen kigyara ni kuma sai ingyara d'akunanmu da palour ko kuwa?" kasan cewar Basmah bata fiye son surutu ba yasa ta gyad'a mata kai kawai batare data tanka taba.

Cikin gwanewa Billy tagyarawa mom d'akinta gwanin ban sha'awa, bayan ta wanke toilet d'in dake cikin d'akin shima, fitowa tayi tasamu itama Batool ta kammala gyaran d'akunansu tana gyaran palour, sannu my twiny har kin fito, "Eh bari naje nataya yayya Basmah tunda naga kema kin kusa idawa"

"Ok babu matsala" da haka Billy tawuce kitchen ta rik'awa yayya Basmah suka k'arasa goge goge, suna fitowa ko ina ya gyaru tsaf yanda ake buk'ata suka nufi hanyar ficewa zuwa part d'in ummi, kallonsu Billy tayi tace

"Yayya Basmah banga an gyara store ba, kuma baku canza cuttings ba" rausayar dakai tayi kafin tace "Billy am totally tired, kawai abarshi gobe magyara" kallon Batool tayi itama dai hakan d'in tafad'a tana k'ok'arin zaunawa.

"To kuzo kujirani ni bari ingyara don gaskiya bai kamata abar wajen ahaka ba." Da sauri da sauri tashiga store d'in suna biye da ita ta dinga jaye kwalayen abinci da buhu huwan tana sharewa, ganin haka yasa suma adole suka taimaka mata aka gyara wajen sannan suka rufe part d'in, suna koma wa part d'in ummi kowacensu tayo wanka, bayan sun kimtsa yaya Mahmud shima yafito cikin shirinsa da yayi mugun kyau kai kache shuwa arabne, wata bugaggiyar shaddace sanye ajikinsa kalar ruwan kwai sai shining da d'aukar ido takeyi, tasha design d'in d'unki brown colour, sai takalmi suma brown colour k'irar Italy da hularsa itama Brown colour cikinta anyi masa design da zare shima kalar ruwan k'wai, yayi matuk'ar kyau sosai.

Da sauri da sauri ya shigo, yana gyara zaman agogonsa a tsintsiyar hannunsa,

"Kuma inane? Basmah, Batool, my sis kufito mutafi sauri nakeyi, so nake idan nakaiku inbiya wajen mom inkaimata sak'on dady, wai kuna inane? Wlh zantafi abina" yak'arasa fad'ar haka lokacin da yagama daidaita zaman agogon a hannunsa. Yana rufe baki suna fitowa kowaccensu masha Allah, Ummi ce tafito biye da su Bilal data gama gyara su cikin wasu k'ananan kaya masu d'an karen kyau, wani irin farincikine ya rufeta data kallesu gaba d'ayansu sunsha kyau bata san lokacin da bakinta yafara fad'in,

"Masha Allah yaran dady, _i'izukuma bikalimatillahi tammat, minkulli shayd'anin wa hammah, wamin kulli ainin lammah_" tadinga rik'o fuskokin kinsu d'aya bayan d'aya tana shafa masu, sannan suka fice suna yimata byebye, azuciyarta sai fad'in take Allah ya tsare manaku yasa kudawo lpy.

Misalin k'arfe tara da rabi hajia dake zaune afalo tare da wasu 'yan mata su biyu zaune agefenta ta k'walawa mom kira, da dawowarta kenan daga wajen rakiyar k'awarta kuma aminiyarta hajia kilishi bayan tasake d'orata akan salon makirce makirce da kissar da zata b'ullo da ita idan takoma, wajen ta iso hannunta rik'e da wayarta tana lallatsawa, harararta hajia kaka tayi kafin tace

"Hayn..aikinfa kenan, wannan shashanci naki narok'i Allah ya rabaki dashi, yanzu wane shireshiren kika yiwa kanki kafin maigidan naki yazo?" Batare da mom tad'ago ba tace nikad'ai nasani hajia tanaci gaba da latsar wayar" cike da takaici hajia kaka ta wafce wayar ahannunta tana fad'a.

"Samnar Banza da wofi ke kad'ai kika sanme bayan kin kasa gyara kanki, dubeki kamar wata ballagaza babu kitso ba k'unshi, wlh Allah kigyara halinki kafin duniya magyara makishi, zaki zauna ne yaran nan su taimaka maki ko sai nakira papinki yaci mutuncinki tukuna" cikin jin haushin fad'an da hajia kaka keyimata agaban yara yasa tab'ata fuska ta kumbura tana hararar 'yan matan tanaji kamar ta dokesu.

Ganin hajia tamik'e tsaye yasata zaunawa ak'asa, sukuma 'yan matan sukayo kanta d'aya tacirewa mom d'an kwali tahau tsefe mata kai, d'aya kuma tafara yimata zanen siffa (lallen hydrogen) a k'afafuwa da hannuwa, nan take itama wacce ke saman kanta tana kammala tsifar tafara yayyafa mata kitso, cikin mintunan da basu wuce hamsin ba sai ga mom ankoma tamkar amarya har wani k'yalli takeyi.


















*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Thanks for being my shadow. That i really don't wan'na leave me, because somewhere in my life i know that you ure shining a light on it, *AUNTY FARIDA MOHAMMED* thanks for incouraging me with ur warmest comments, jxkillahu khair_πŸ‘πŸ»


πŸ’ŽPage_____33πŸ’Ž


A bakin wata katafariyar super market yaya Mahmud yayi parking d'in motarsa adai dai inda aka tanada don ajiye motocin, sai da yagama daidai ta zaman motar sannan suka fito, su Bassam ne agaba sai su Billy da suka biyo bayansu, shi kuwa Mahmud babban yaya biye dasu abaya ya wani matse fuska kamar bashi ba, duk wani motsi da 'yan uwan nasa zasuyi yana akan idonsa, cikin natsuwa suka dinga kwasar abubuwan da suke so wanda mafi yawancin abunda 'yan matan suka kwasa kayan kwalliyane su kuma yaran kayan wasa suka dinga jida suna sakawa cikin basket d'in dake jaye a hannunsa, shidai kallonsu kawai yakeyi batare daya d'auki komai ba kuma har lokacin yana biye dasu abaya, wani gefe sukabi dake Jere da underwear's kala kala amma ga mamakin sa babu wacce ta kalli wajen balle tasa ran d'auka, ganin haka yasa ya tsaidasu yana fad'in "Anan fa? Babu abunda kuke buk'atane naga zaku wuce?" Cike da jin kunya kowaccensu ta duk'ar da kai k'asa sannan sukaci gaba da tafiya, da sauri ya sake dakatar dasu yana merar baki, hannuwansa dake cikin aljihu ya fiddo d'aya ya dinga d'auko unders d'in yana jefa masu cikin basket saida ya kwatanta yad'ibi kowanne adadin saiti ukku kaloli daban daban sannan yawuce abunsa gaba batare da yakallesu ba yana sake matse fuskar nan alamun ba reni.

Kallon kallo aka shigayi tsakanin Basmah dasu Billy kafin suba juna hannu sukashe suna dariya, jin dariyar da sukeyi yasashi tsayawa had'e da juyowa lokaci guda yana watsa masu wani irin kallon da yasa cikannansu murd'awa, da sauri suka rufe baki tare da wucewa ta gabansa suna sake danne dariyar dake neman fito masu, sai daya kalli gefensa sannan ya sakebi bayansu yana murmushi,


Room fresheners masu k'amshi Billy takwasa kusan kala goma kuma kowane k'waya biyu biyu su Basmah suka bita da idanuwa suna kallo,

"Ke duk ina zakije da wud'an nan turarukkan haka sai kace ke kikafi kowa son k'amshi?" Yaya Mahmud yafad'a yana waro ido, sai data shagwab'e fuska sannan tace

"Kai yaya aishi k'amshi rahamana, babu wata kyauta aduniya mafi tsadantuwa kamar k'amshi" turo idanuwansa yasakeyi yace

"Injiwa yafad'a maki, lalle son k'amshinki yayi yawa, to yanzu wud'an nan duk ina zaki kaisu?"

"Su ummi da mom na d'aukarmawa" Mahmud bai sake cewa komai ba, suna gamawa suka nufi wajen payment akayi masu total kud'in da zasu biya almost 40thousand naira, kuma kusan duk turarukkan ne sukafi yawan kud'i, gashi kud'in dake hannunsa gaba d'aya 50thiusand ne har gami da nasa, dole yaciri 10thousand acikin kud'insa yak'ara akan nasu 30thousand da dady yabasu yabiya aka saka masu kayan cikin jikkuna suka wuce, bayan sun fito ya d'auki hanyar da zata sadashi da titin da GT bank yayiwa ummi depositing d'in kud'in data bashi ya kaimata, yana fitowa bankin yatayar da motarsa aguje ya mai dasu gida, yana ajiyesu batare da yashiga ba ya tayar da motar yanufi gidan papi cike da d'okin ganin mom d'insa.

Papi ne yasamu zaune bisa wasu kujeru shida amininsa daya kawo masa ziyara a harabar gidan suna fira, duk'awa yayi har k'asa ya gaishesu cikin natsuwa har yana tsokanar papi da cewa "sannu da hutawa gayen baby hajia kaka" dariya papi yai kafin yace

"Ja'irin yaro injin dai zuwa kayi katafi da mom d'in taka dake neman ta sanyawa babyn tawa ciwon kai"

"Aa papi ai wannan aikin dadyne ni sak'o nazo kawo mata daya bani" Mahmud yafad'a tare da mik'ewa yabar wajen, murmushi abokin papi yayi yana fad'in

"Ikon Allah yaran zamani kajifa abunda yake cewa, Allah dai ya shirya manasu" papi ya amsa da amin.

"Yawwa alhaji niko nace kaddai kacemun wannan d'an wajen 'yatace Hussaina!"

"Sosai kuwa shine, domma yaranta nafarko da na biyun basu tsaya ba, ai wannan shine yaronta na ukku "

"Masha Allah gashi tubarkallah duk inda saurayi ke kaiwa yakai, gashi da natsuwa har naji ina yiwa jikanyar wajena sha'awar had'ata dashi" murmushi papi yayi kafin yace

"Allah sarki ko 'yar wajen Ibrahim da Allah yayiwa rasuwa shida matarsa"

"Eh ita nake nufi, kasan har ta kammala karatunta nagaba da secondary a b'angaren kiwon lafiya (nurse) har tafara aiki awata asibitin kud'i dake nan garin"

"Kai madallah abu yayi, Allah yataimaka kuma yajik'an iyayenta, zan yiwa shi Mahmud d'in magana, idan ya amince sai yaje su daidaita da ita" wani irin farincikine ya bayyana a fuskar alhaji hamza wato aminin papi wanda koba'a fad'a makaba kasan yaji dad'in fitowar wud'annan dad'ad'an kalamai daga bakin aminin nasa, haka dai sukaci gaba da tattaunawa cike da fatar Allah yasanya qudurinsu yazamo alkhairi kuma yasa yaran su amince da juna.

Lokacin da Mahmud ya shigo paloun kasa gane mom d'insa yayi saboda yanda yaga tagyru k'asa da sama, gaisheda ita yayi yana fad'in

"Momynmu kingaki kuwa? Masha Allah gaskiya kinyi kyau sosai, nikam ina zanga maik'unshin nan kitso inyi masu kyauta" yak'arso wajen hajia dake marar baki tana fad'in

"Hmm andaiji kunya tsabar rashin gyaran jiki har d'an cikinki kinsaka shi cikin mamaki, adai san angirma adena shashanci" b'ata fuska Mahmud yayi yana gaisheda hajia kaka, bata tankashi ba saida tagama yiwa mom fad'a sannan tajuyo fuskarta d'auke da murmushi,

"Ahh..mommodu yanzu kake tafe? Ina k'annen naka suke da umminku, inace dai duk lafiya kuke ko?"

"Lafiya klw suke, yanzun nan na ajiyesu gida mundawo daga wajen sayayya"

"Kai malan mommodu!, shine kak'i kazo dasu, ko gudu sukeyi ink'wace masu kayayyakin da suka sawo inyiwa papi kwalliya dasu, don nasan sayayyar tasu bata wuce ta kayan kwalliya"

"Aikuwa kamar kinsani babyn papi suka d'ai suka kwaso" kunnensa tarik'e

"Dama aini babyn sace ba takaba, tukuna barima intambayeka kai sai yaushe zaka kawomun taka babyn ko so kakeyi saina mutu sannan?"

"Awwshh...fara cikamun kunne tukuna sai infad'a maki ko!" Yafad'a yana rik'e da hannunta data rik'e masa kunne, Sakin kunnen nasa tayi ai kuwa kafin tayi wani k'wak'k'waran motsi har yabar wajen yana fad'in,

"Kunjimun tsohuwa da neman magana, tunda nashigo kinbi kin nanik'eni wuri d'aya ko bari bazakiyi naje wurin momynah naji d'imin jikinta ba" kitchen yanufa wajen mom dake faman sarrafa abunda za'aci da rana, rungumota yayi tabaya yana fad'in

"Momynah sannu da aiki, mekike dafawa tsofaffin nan dake neman su wahalshemuna dake?" Juyowa tayi had'e da dungura masa ludayi akai, "kaima nan kad'an iyayenka za'a kirasu da tsofaffi haddai dadynka" dariya yai tare da fiddo kud'in dake aljihunsa ya mik'a mata, "Allah sarki dadynah yayi matuk'ar kewarki sosai, ga wannan yace akawo maki ko akwai abunda zaki siya kafin yazo"

Karb'ar kud'in tayi tad'an juyasu sannan tad'ora akan fridge d'in dake cikin kitchen d'in, "kace masa ngd" tafad'a sannan taci gaba da abunda takeyi. Wani irin ba dad'i Mahmud yaji ganin yanda mom tayi da kud'in sai yatuna yanda Ummi takarb'i kud'in cikin girmamawa tanata kwararowa dady godiya da dad'ad'an addu'o'i tabbas ko anan kad'ai aka tsaya akwai banbanci tsakanin Ummi da mom d'insa ssai, kallonsa tayi taga yanda ya canza fuska sai itama taji ba dad'i aranta, murmushi tak'ak'aro don tafaranta ransa tace

"Wato dadynka kad'ai yayi missing d'ina kaida k'annenka da kuma umminku bakuyi missing d'ina ba ko?"

Hakan da tafad'a sai yaji wani irin sanyi aransa haddai da tace da umminku, arayuwarsa bait tab'a jin mom takira ummi amatsayin wacce zasu iya zama mallakinta ba sai yau, ko yaushe in abu yashafi Ummi saidai takirata da sunanta wato Aisha amma sai gashi yau da bakinta take kiranta da umminsu, addu'a yayi azuciyarsa akan ubangiji Allah yasa mafarkinsa yazamo gaskiya, yana fatan Allah yasa ummi ta zubar da duka makaman yak'inta kenan, azahiri kuwa cewa yayi

"Munyi missing d'inki sosai, haka itama ummi da kullum take k'ok'arin kulawa damu tare da yimuna addu'a" Runtse idanuwa mom tayi saboda yanda kalaman suka daki zuciyarta, da ace Mahmud zai gane halin da take shiga aduk lokacin dataji yakira sunan ummi ko yayi mata zancenta to da baiyiba, don rad'ad'in hakan zai iya tsaida numfashinta. K'arfin hali tayi zuciyarta nayi mata zugi tace

"Ayya 'yar uwata Allah yabiyata, gaba d'aya kulawar da kuke samu tasaka baku ba har abbanku ya canza sosai, a gaskiya sai yanzu nakejin rashin da cewar abubuwan da sukata faruwa tsakaninmu" tsabar farincikin da yaji yasa yasake rungumeta "Momynah ba komai ai wannan abun duk yawuce, indai ummice natabbata babu komai aranta" ji mom takeyi kamar takamasa ta mammake saboda yanda taji yana siding d'in ummin, haka dai sukaci gaba da firarsu ta d'a da uwa bayan taci nasarar canza firar, Mahmud baibar gidan ba sai bayan la'asar ranar tare da papi, hajia kaka, mom d'insa sukayi lunch cikin soyayya da k'aunar juna a tsakanin d'a da iyaye.

Bayan Mahmud yawuce papi ya zaunar da mom yayi mata nasiha sosai sannan itama hajia ta d'ora da tata akai, sosai mom tayita kuka kai kace zata sauya daga mugun halinta.

Ummi kuwa bayan fitarsu saiga kiran dady awaya, kasan cewar tak'are duk wasu aikace aikace daya kamata tayi tare da taimakon yaran nata yasa tasamu d'aya daga cikin kujerunta ta zauna tare da d'aga wayar, cikin wata iriyar zazzak'ar murya tace

"Hello abu Bilal!" Murmushin da saida taji fitar sautinsa dady yayi har hak'oransa nabayyana saboda dad'in sunan da tayi masa dabata tab'a kiransa dashiba, shiru yayi yakasa amsa mata saboda yanda yaji wata irin kasala ta saukar masa, jin baice komai ba yasa tasake cewa

"Hello, assalamu alaika abu Mahmud" akasalance ya amsa da

"Wa'alaikissalam rabba'atul bait oum bilqees"

"Ya aiki dadyn yara, hop dai ka isa lpy"

"Lpy klw, alhmdllh tsantsar kewarkice kawai ta uzzurawa zuciyata shiyasa nakiraki, ina fatar kina kula mani da kanki yanda yakamata ko"

"Matuqar kana kula mani da kanka to tabbas nasamu kula ta musamman domin kai d'in ne ni"

"Oum Bilqees kenan, in dai a fannin dad'ad'an kalaman dake kwantar da zuciyane kullum d'an koyo nake komawa agabanki, ke gwanace domin kinkai mak'ura wajen iya sarrafa zuciyata dani kaina wajen dad'ad'an kalamai"

"Hmm abu mahmud kenan, nikuwa gani nake ai kaine malamin kuma koyarwar takace, gwanewarka ita tahaifarwa da d'alibarka fahimtar karatun cikin sauk'i har tasamu kwarin guiwar iya karatun fiye da yanda ka koyar da ita, shiyasa har kake kallon kanka amatsayin d'an koyo akanta" dariya dady yayi kafin yace

"Idan kuwa hakane yazama dole nayiwa wannan d'aliba tawa kyauta, domin na tabbata duk inda nashiga da ita zata sakani farinciki da alfahari"


"To shikenan ina maraba da wannan kyauta taka ko yaushene domin itace zata k'aramun k'aimi da kwarin guiwa naganin cewa nasaka farincikinka da alfaharinka lillinkuwa akowane lokaci"

"Nabaki dukkanin zuciyata amatsayin kyautarki, domin na tabbatar da kalamanki" muskutawa ummi tayi daga zaunen da takoma akwance tana fad'in

"Madallah da wannan kyakkyawar kyauta maigirma data sanyani fita zakaran gwajin dabi acikin 'yan uwana mata, nayarda da cewa nafi kowacce macce sa'ar samun adali kuma nagartaccen miji, dukkanin maza da kake gani aduniya ina yimasu kallon matane, kai kad'aine namiji awurina dake haskamun duniyata da kuma lahirata..."

"Kibarni haka oum Bilqees kada kisa nakasa attaka komai" wata irin ajiyar zuciya sukayi atare har suna rigegeniyar fad'awa juna "I LOVE YOU" dukkaninsu dariya sukayi cikin jin dad'i sannan dady ya yimata bayanin cewa yaturo yaronsa akawo masu kayan abinci ita da mom, nan take sanar masa da cewa sai dai akaisu gaba d'aya part d'in mom saboda tana dasu sosai har yanzu basu k'are ba, godiya tatayi masa da addu'a yana amsawa da amin sannan ya kashe wayarsa cike da alfaharin samunta a amatsayin matarsa. Ummi nagama waya da dady saiga su Bassam sun dawo, gaba d'aya suka wuce d'aki suka ajiye jikkunan kayan da suka sawo, jikkar turarukkan kad'ai Billy ta d'auko tana nunawa Ummi,

"Ummi dubi turarukkan dasu yayya Basmah da Batool suka d'ebo maku keda mom" kasancewar Ummi ma'abociyar son k'amshice yasa tad'ago tana kallon Basmah da Batool da sukayi galala suna kallon Billy tace

"Wow....Basmah, Batool da kanku kuka zab'o mana wud'annan? Kai gaskiya sunyi kyau sosai, kuzonan yarana Allah dai yayi maku albarka" tak'arasa cike da murna tana bud'e masu hannuwanta suzo, rungumesu tayi sosai tanaci gaba dayi masu addu'a

"Nida momynku muna godiya kunji ko?" Billy dake gefe tsaye tahard'e hannuwanta akan k'irji sai kallonsu takeyi tana murmushi, azuciyarta tana fad'in "Allah sarki 'yan uwana, abun gwanin ban sha'awa, inama ace duka umminah tahaifeku!"

Koda dady ya kammala waya da ummi mom yakira, itama fira suka d'an tab'a da ita, ba laifi yasamu had'in kanta saboda qudurin da tasawa aranta sun d'an tab'a soyayya, duk da rabin soyayyar k'orafice akan yarage sonta, bata samun kulawarsa nan yayita bata hak'uri tare da tabbatar mata da cewa bahaka bane har yanzu yana matuk'ar sonta kuma yau zai tabbatar mata da hakan. Nan dai yafad'a mata cewa tagyara da anyi sallar isha'i zaizo ya d'auketa.

Ana gama sallar isha'i mom ta d'auko abunda hajia kilishi tabata jikinta har rawa yakeyi tayi inserting kamar yanda tace, murmushi tayi tana kallon madubi, cikin isa da gadara da kuma yak'ini akan maganin tace

"Rest in peace Aisha dake da 'ya'yanki" sannan tabushe da dariya, tana cikin dariyar ne hajia kaka takirata tab'akkata wata dalleliyar atamfa super exculusive wax da tasha d'unki sosai tare da wasu sababbin kaya data d'unka mata kala hud'u, ga takalmi, jikka, 'yankunne da sark'a, mayafi duka sababbi ta siyomata, Allah sarki uwa rahamace, fad'a tasake yimata sosai sannan tace taje tagyara kafin alhajin yazo,

Dady na isowa aka bashi izinin shigowa ya gaida papi da hajia cikin girmamawa sannan aka kirawo mom papi yasake yimasu nasiha, godiya dady yayi masu sosai sannan ya d'auki matarsa kuma amaryarsa mom suka nufi gida...







































*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

🀣🀣 _Bana kyautar page ni Billy s fari saboda already nariga da nabada

Please Login or Register in order to submit comment