Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da alama taji duk abunda Ummi ke fad'a, wani irin jirine yasoma d'ibarta da kad'an tafad'i.

Da sauri Ummi tak'arasa wajen tarik'ota tazaunar abakin gado tana jefawasu Billy harara da duk sun mik'e tsaye suna k'ok'arin kaiwa 'yar uwarsu d'auki dake neman fad'uwa,

"Me kukeyi haka da yasa bazaku iya jira tafitoba, to ynzo daban isoba tafad'i taji ciwo fa? wannan ai sakarcine" sosai take yimasu fad'a Basmah nabinta da kallo, azuciyarta tana cewa

"Allah sarki yanzu dama soyayyar da Ummi keyi mani har takai haka, muguwar hud'uba tasa nakasa fahimta, dubi yanda nab'ata mata jiki d'azu amma gaba d'aya bata samu ba saima tausaya mani da takeyi" tunanin tane yakatse lokacin da taji Ummi najero mata sannu ita da yaya Mahmud, dak'yar tabud'e baki tana goge hawayen da suka zubo mata da hannu tace

"Hinm" tana kallon yaya Mahmud da tund'azu ita yake kallo.

Taimaka mata Ummi tayi tasaka rigar da suka fiddo mata sannan takarb'i cup d'in dake hannun yaya mahmud ta kai mata abaki, ko kad'an bata yimata masu ba don ita kanta ta tabbatar da tanajin yunwa sosai, kafin kace me har tashanye tea d'in gaba d'aya, jaye cup d'in tayi daga bakinta sannan tace su Billy suje sukawo mata abinci, nanma Basmah batayi musu ba taci abincin sosai don tacinye fiye da rabin plate sannan tace tak'oshi, kwashe kayan su Batool sukayi suka kai kitchen daga can suka shige d'akin su Bassam don yimasu addu'o'in bacci yayin da Ummi da Mahmud suka shiga bincikar Basmah abunda yafaru.

Saida tayi kukanta mai isarta sannan tashiga labarta masu gaskiyar abunda yafaru bayin fitarta gida. Sosai sukayi mata fad'a tare da nuna mata illar hakan da tayi da kuma cutarwar da zai yimata, Basmah na kuka tarungume Ummi tana rok'onta tayafe mata abubuwan da tayi mata.

Ba Ummi kad'aiba hatta ya mahmud yayi mama kin sauyawar Basmah lokaci guda tare da godewa Allah daya ganar da ita gaske, lallashinta Ummi tayi tayi fuskarta d'auke da farinciki tace

"Bakomai dama ni band'auki abun komai ba, duk abunda kike yimun ina kallonsa amatsayin kurciya wanda indai zan iya hak'uri da k'urciyar Bilkisu dole kema sai nayi hak'ur da taki don duk abu d'aya kuke gareni, fatana akoda yaushe Allah yayi maku albarka kuma ya shirya munaku"

Sosai Basmah taji dad'in kalaman Ummi, tanajin kanta awata sabuwar rayuwa tajin dad'i Marat misaltuwa.

Yaya Mahmud kuwa ya qudurta aransa idonsa idon mugayen abokanan Basmah da suka so ruguza mata rayuwa wlh sai yayi qasa qasa dasu. Hannunta yarik'o yana fad'in don Allah Basmah kirik'e wannan gaskiya da Allah ya nuna maki kada kibari shed'an yakoma ribantuwa dake na tabbatar inkikayi haka bazaki tab'a nadama ba har abada kinji ko?, Ummi da kike gani itama wata ni'imace da Allah yabamu ita agurbin da zamu rik'eta amatsayin uwa, matuk'ar mukabita to zamu samu ingantacciyar rayuwa har agidajen aurenmu" jinjina masa kai tayi alamar tabbatar masa da zatayi abunda ya fad'amata. Alokacin suma su Batool suka shigo da niyar kwantawa don bacci ya soma d'ibarsu,

"Yayya Basmah sannu" suka yimata had'e da cewa

"Ummi saida safe"

"Aw. babu arwalar zaku kwanta?" Ya Mahmud ne yafad'i haka tare da mik'ewa zaifita shima yana yiwa Ummi saida safen.

"A'a yaya ai zamuyi, Yayya Basmah kin rama sallolin dake kanki kuwa?" Batool tafad'a tare da shigewarta toilet , dafa kafad'un Basmah Ummi dake gefenta zaune abakin gado tayi tace

"Yawwa tunda kinsamu sauk'i kitashi Bilkisu ta taimaka maki kiyo arwala kirama sallolin dake kanki" ta k'arasa maganar tana kallon Billy.

"To Ummi" dukkaninsu suka fad'a sannan itama tafice tana jaddada masu karwacce ta sake takwanta batare da tayi addu'aba.


Mom kuwa tunda tasamu dady ya lallab'a su papi suka amince akan zata koma gobe tasaki wata irin ajiyar zuciya da tasa kowanensu juyowa suna kallonta, ficewa tayi daga gurin papi ya girgiza kai yana fad'in "Allah ya shirya mana zuri'a" su kuma suka amsa da amin.

Sallama su dady sukayiwa papi bayan sun ajiye masa kud'i masu yawa suna godiya, k'in karb'ar kud'in papi yayi yace Allah dai yayi masu albarka amma Sam bazai karb'a ba. Dole tasa abokin dadyn yad'auki kud'in cike da yaba dattako irin na surukin aminin nasa.

Bayan sun fito fuskar dady cike da fara'a yace

"Alhmdllh Alhaji kaga yanda hajia Hussaina ta canza ko?"

"Eh wlh masha Allah, idan kam haka yad'ore zaka samu natsuwa sosai acikin gidanka, babban abunda yafi burgeni shine yanda mahaifanta suke da dattako gaskiya kayi sa'ar sarakanan k'warai"

Murmushi dady yayi ba tare da yace komai ba na tsawon mintuna kafin suci gaba da tattaunawa akan wasu harkokinsu na yau da kullum.

Mom nashiga d'akinsu ta cillar da hijab d'inta gefe had'e da sakin wani shu'umin murmushi tana kallon hajia kilishi, hararar ta tayi kafin tace

"Shifa wannan murmushin tawajena?"

"Hmm kibari kawai, Kinga yanda alhajina ya koma, sai kace irin 'yan 30yers d'in nan yayi wani irin fresh kaman bashi ba, hmmm har zan yadda ace shearing d'ina nakeyi da wata! Wlh yanzu yak'in zai soma don sai na tabbatar da cewa koda kissa koda munafurci alhajinah yazama mallakina nikad'ai, ashirye nake dana sadaukar da komai nawa akansa don nikaina nahango tsantsar soyayya da kaunar da yake yimun, kawai shiga tsakanin mune akayi, kinga yanda yake nunamun irin missing d'ina da yayi?"

Wata irin dariya hajia kilishi tayi da tasa papi da hajia kaka dake palou zaune juyowa suna kallon b'angaren da sutin kefitowa girgiza kai papi yayi kafin yace "Baby bari nashiga daga ciki kafin wud'annan shashashun sufasa mani dodon kunne" mik'ewa itama tayi tana fad'in

"Ai saidai mutafi tare don idan naci gaba da zama anan zan iya shiga d'akin nacicci masu mutunci, yaran wofi kawai da basusan sun girma ba"

Hannunta tamik'awa papi yarik'e sannan ta tashi suka nufi d'akin baccinsu tanaci gaba da mitar irin abubuwan da sukeyi kamar wud'anda basa da 'ya'ya agabansu....














*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____30💎


Yanzu ke har kina tunanin cewa Aisha zata iya saken da zaki mallaki alhaji ke kad'ai ranki? Kar kimantafa itace first wife d'insa, idan har ke da kika shiga gidan amatsayin matarsa ta biyu kina jin haushin shearing d'insa da wata mekike tunani ga wacce ita yafara sani arayuwarsa kuma ita tafara saninsa, gaskiya son kanki yayiwa qawata ina laifin kema kinemi aza taki kujerar acikin zuciyarsa ta yanda zaki samu matsayin da bazai iya musawa duk wani muradinki ba,

'Bata fuska mom tayi kamar maishirin yin kuka "Haba taya zakice nacika son kai don nanu maki ina buk'atar alhaji yazama mallakina nikad'ai?, A gaskiya naji zafin kalamanki sosai don sun b'ata raina matuk'a" tak'arasa maganar cikin jin haushin hajia kilishi, mere baki itama tayi kafin tace "ikon Allah naga ai gaskiyace nafad'a ko?, nifa duk tugguna da makirci basa hanani fad'in abunda ke raina don haka inzaki iya to ki had'iyi bomb saiki fashe da alama bakyada buk'atata yanzu, dama donki na iso garinnan kuma gobe tunda sassafe zan tafi abina" tana gama fad'ar haka itama tamik'e cikin fushi tana k'ok'arin har had'a kayanta, ganin da gaske takeyi yasa mom ta sauka daga nata fushin sanin da tayi akan wannan maganar aminiyar tata zata iya fushi da ita natsawon lokaci, kuma bata buk'atar haka ayanzu, kamo hannunta tayi tana fad'in.


"Kai aminiya! Nifa ba haka nake nufi ba, taya za'ayi alamurrana su iya tafiya dai dai bisa tsari idan babuki, to shikenan kiyi hak'uri" dakatawa da had'a kayan tayi tana harararta da wutsiyar ido, mom tayi dariya

"Nadaiji kuma nagode, yanzu zauna sai muyi magana ko?" Zaunawa tayi tana kallonta kafin nan su tuntsire da dariya had'e da tafa hannuwa,


"Ja'ira ai nazata tunda nafad'a maki gaskiya fushi zakiyi dani" kilishi tafad'a tanaci gaba da tuntsirar dariya"

"Kome ma zakice naji, ai mai so gawani yaga takansa, yanzu dai so nake kid'orani a hanyar da zata taimakona, wlh nidai natsani Aisha da 'ya'yanta har ga Allah nidai bana son ganinsu" shiru hajia kilishi tayi tana kallon mom sannan tamatso kusa da ita tana rad'a mata wasu maganganun a kunne na tsawon lokaci kafin tad'ago tace

"Don haka kiyi k'ok'arin aiwatar da plans d'in da muka tsaro cikin lokaci sannan wannan dana fad'a maki su biyo baya" tsabar jin dad'in abunda kilishi tafad'a mata yasa tarungumeta tana yimata godiya kamar wacce akayiwa abun arzik'i daga bisani kuma suka shiga kimtsa kayansu kafin gobe kuma kowace tayi gidan mijinta.

Cike da fara'a dady yadawo gidan, a lokacin gaba d'aya yaran sunyi bacci Ummi kad'aice zaune a d'akinta bayan tagama shafa'i da wutiri tana tilawar qur'ani, saida ya lek'a duka d'akunan yaran sannan ya shigo d'akin Ummi, da sallama abakinsa ya k'araso cikin d'akin tare da zaunawa gefen gado yana sauraren daddad'ar k'ira'ar Ummi dake k'ok'arin ganin takai k'arshen aya saboda shigowarsa.

Bayan takammala karatun tarufe Qur'anin had'e da juyowa tana kallonsa fuskarta d'auke da murmushi tace

"Sannu da dawowa dadyn yara"

"Yawwa rabba'atul bait, meyasa kika katsiye karatun, sai nakejin salon k'ira'arki tamkar ta sheik Abdul-basid Abdus-samad dake su'udiya, gaskiya nakan k'ara jin k'aunarki araina saboda yanda kike rik'o da addininki, ya Allah kada kabani damar sake rayuwa aduniya matuk'ar babu rabba'atul bait atare dani..."

Cikin hanzari Ummi tayi k'ok'arin rufe masa baki saboda gudun kar ya k'arasa maganar dake fitowa daga cikin bakinsa, amma ina!. har ya k'arasa yana dariya had'e da d'an ciza tafin hannunta dake rufe da bakinsa, shagwab'e fuska Ummi tayi kamar wata yarinya tana yarfi da hannun, kyakkyawar runguma dady ya kaimata har lokacin yana dariya, k'amshin jikinta da yake shak'a ya sashi lumshe idanuwa yana fad'in "dadyn bb is sorry" shima wani marairaice muryar tasa yayi alamun ban hak'uri, hakan yasa ta tintsirewa da dariya tare da tighting d'insa sosai tana fad'in "kai ko!"


Sunjima ahaka suna warming d'in jikin junansu kafin Ummi ta tashi tana cewa

"Yaa salaam kagani ko dadyn yara gaba d'aya kasa na shagaltu batare da nabaka dinner kaciba, am so sorry plz made mistake" ta k'arasa maganar tare da barin d'akin.

Tunda tafara magana ya kwantar da jininsa akan gadon k'afafuwansa ak'asa yana binta da kallo har tafice, a hankali ya rufe idanuwansa yana tunano karamci, halacci da hak'urin da Ummi take dashi, tabbas idan har yardarsa zatasa Allah yabata aljannah to baya tantama da cewa ita 'yar aljannah ce d'ari bisa d'ari domin ya yarda da ita fiye da kansa aduniya, ahaka Ummi tadawo ta samesa, murmushi tayi kafin ta k'arasa wajen, gadon tahau cikin natsuwa tare da hura masa iskan bakinta ahankali afuska, batare daya bud'e idanuwansa ba yasa hannuwansa gaba d'aya ya rungumota ajikinsa, k'ok'arin zillewa tayi cikin wata irin kasalalliyar murya yace

"Relax rabba'atul bait!, so nake kifad'amun, wace irin baiwace dake wacce tasa zuciyata bata gajiya da soyayyarki haka kuma gangar jikina kullum take mararinki?" Wani irin farincikine ya mamaye ilahirin zuciyar ummi dajin wud'annan dad'ad'an kalamai dake fitowa daga bakin maigidanta, sassanyar ajiyar zuciya tayi kafin tace

"Ai wannan baiwar kaine sirrinta domin akanka kad'ine take tasirantuwa" tana gama fad'ar haka tayi sauri mik'ewa daga jikinsa cike da jin kunya.

"Ka taimaka kataso kaci abinci kada yunwa takama mani kai"

"Ai idan dai har ina tare dake babu wata yunwa data isa taziyarci rayuwata"

"Gaskiya fa dadyn yara?"

"Sosai kuwa rabba'atul bait" yafad'a yana dariya tare da biyo bayanta zuwa parlour,

Saida Ummi ta tabbatar tacikawa dady tumbinsa sannan takwashe kwanonin takai kitchen, dawowa tayi tana kallonsa tace

"To yallab'ai sai da safe ko?, nafara jin bacci naziyar toni" a hankali yamik'e tare da rik'o hannunta suka nufi bedroom d'inta, kallonsa tayi ya wani matse fuska,

"Dadyn yara ya haka?"

"Anan yau zan kwana"

"Amma kasan...."

"Shiiiiiii" yayi saurin rufe bakinta da d'an yatsansa, turo bakin tayi tayi tare da had'e girarta ta sama, murmushi yayi batare da yace mata komai ba don yafahimci kome take nufi, shikam ak'ida irinta Ummi nabashi mamaki, duk da yasan don gyara tarbiyar yaransu takeyi amma ai shima yaci ace tabarsa yanayin yanda yake so a part d'in ta.










*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Where are u my Tee-tee *{Teemah gabs}* here are my greeting goe's to u, u're such a wanderful, kindness and a lady with classy💁🏻 dt i will never ever forget in my entirely life. Thanks for been by my side, with u i will be always being bless in my writing, sincerely u're so nice and am proud of you. JAZAKILLAHU KHAIR👏🏻_


💎Page_____31💎


Yau kam Ummi tasha mamaki sosai da yanda dady ya sarrafa dukkanin soyayyar da yake yimata don ganin ya isar da sak'on acikin k'undin zuciyarta, kuma alhmdllh sak'o ya isa don yanda Ummi tasha soyayya da tarairaya awajen dady yak'arawa mas kima da daraja sosai acikin zuciyarta ta yanda take jin duk duniya babu wani namiji dake iyayin tasirin da yayi acikin zuciyarta idan bashi ba, wata irin sabuwar duniya take jin kanta aciki wacce ta sakata cikin farinciki marar misaltuwa adaren jiya. Da asuba dady ya tashi shima cikin yanayin farincikin da bazai iya misiltashi ko fassarawa ba, murmushin da baisan lokacin daya kucce masa ba ya saki tare da mik'ewa yafad'a toilet, wanka yayi tare da d'auro arwala akai, yana fitowa ya tasheta itama, saida yaga tashiga toilet sannan ya fito yatada yaransa suma sukayi arwala, hannun Bilal da Bassam yarik'o suka nufi sashen yaya mahmud dake k'ok'arin rufo k'ofar d'akinsa da zimmar zuwa masallaci, gaba d'ayansu suka wuce cikin sauri kasancewar har liman ya tayar da sallah.


Itama Ummi koda tafito d'akin su Bilkisu tafara lek'awa ta tarar suma sun tashi har sun tada sallah sannan itama takoma d'akinta, bayan tagama sallah tadinga kwararo wa kanta da maigidansu da 'ya'yansu addu'o'in neman tsari da samun nasara da zaman lafiya acikin zamansu da rayuwarsu.

Koda dady suka dawo masallaci kai tsaye ya wuce part d'insa yayin dasu kuma su Bassam sukabi yaya mahmud d'akinsa yanayi masu tilawar azkar d'in safiya da marece.

Bilkisu kuwa tana ganin safiya tafara wayewa ta tashi don yin aikace aikacen da suka sabayi, juyowa tayi tana kallon Basmah da sallame sallarta kenan tad'ora kanta agefen gado tace

"Yayya Basmah morning, ya k'arfin jiki?"

"Alhamdulillah Billy" tafad'a tana murmushi, itama Batool gaisheta tayi tayi mata yajiki sannan suka soma da gyaran d'akin, duk aikin da sukeyi Basmah nakalle dasu gwanin ban sha'awa yanda suke taimakekeniyar junansu wajen aikin, suna kammalawa suka nufi hanyar fita d'akin don cigaba da aikace aikacensu, muryar Basmah suka tsinkayo tana fad'in,

"Ina kuma zaku tafi kubarni 'YAN UWANA?" Cike da mamaki duk suka juyo suna kallon fuskarta dake d'auke da wani d'ankarqmin murmushi dake nuna nadamarta bisa abubuwan dake faruwa,

"Kada kiyi mamakin jin wannan kalma abakina matuk'ar ba wariya kuke son yimun ba, nayi nadamar dukkanin abubuwan da nakeyi kuma nagane cewa ku 'YAN UWANA NE na hak'ik'a, especially ke Billy danake d'auka kamar babu alak'a atsakaninmu, ina rok'onki daki manta da duk abunda yafaru kirik'eni a amatsayin 'yar uwarki dake matuk'ar sonki" tak'arasa maganar had'e da bud'e mata hannuwanta.

Lumshe idanuwa Billy tayi suna kallon kallo ita Batool tanajin wata irin sabuwar soyayyar 'yar uwarta kwance fal azuciyarta, da gudu Billy tak'arasa wajenta tare da shigewa cikin jikinta, wasu zafafan hawaye suka zubo mata ahankali tamaida hannayenta tarungume Billy tana jin sanyi azuciyarta, "kiyi hakuri kiyafemun duk.." take fad'a hawayen naci gaba da zubo mata afuska, da sauri Billy takatseta ta hanyar cewa "Ya isa haka Yayya Basmah, ni bantab'a jin cewa kunyimun laifin daya kai kinemi yafiyata ba, akullum ina kallon ku ''YAN UWANA NE da kuka isa gareni da kuma d'an uwana, komai yawuce yayya abunda ya kamacemu shine mufuskanci gaba"

Cikin jin dad'in kyawawan kalaman Billy Batool tayi tafi tace

"Gaskiya kun matuk'ar burgeni, to nikuma da kuka bari agefe waye zai rik'emun hannuna" Basmah na murmushi tayi mata alama da idanuwa tazo tana mai mik'o mata d'ayan hannunta, da sauri itama tak'arasa wajen tarungume su tana fad'in

"Ku 'YAN UWANA NE da banida kamarku, kuma ina matuk'ar sonku sosai"

Ummi da taji har yanzu bataji motsin yaran taba tafito don jin ko lafiya suke, sai gashi tatarar dasu cikin yanayin da yasa lunkuwar farin cikin da take aciki, gyaran murya tayi kafin gaba d'ayansu sujuyo suna kallonta tace

"Agaisheku yaran dady Allah dai yayi maku albarka, shine kuka zo kuka tasa auntynku agaba kuma neman karyamun ita baccin kunsan batajin dad'i, murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta cike da jin kunyar ummi kafin tace

"Ai alhmdllh naji sauki sosai Ummi"

"K'arasowa daga ciki Ummi tayi ta zauna gefen gadon kusa da inda Basmah ke zaune ak'asa sukuma su Batool sun koma acan gefenta suna gaisheda Ummi, Dafa kanta tayi lokacin da itama tabud'e baki tana gaisheta, cike da fara'a ta amsa masu gaisuwar sannan takalli Basmah.

"Basmah kin tabbatar kinsamu sauk'i babu abunda ke damunki yanzu?"

"Eh ummi naji sauk'i sosai sosai"

"Masha Allah" tafad'a tare da juyowa tana kallon su Billy

"Maza kuje ad'ora breakfast ganinan zuwa yanzunnan, Basmah ke kuma ki kwanta kid'an huts kafin anjima kinji ko, Allah yak'ara sauk'i?" Tana gama fad'ar haka bata jira amsarsu ba tafi ce su kuma suka nufi kitchen don cika umurninta, ganin haka yasa itama Basmah tabi bayansu bayan tacire hijabin dake jikinta batare da takoma baccin kamar yanda Ummi taceba, har ga Allah Basmah bata iya girkiba don haka batasan mezata fara dashi ba, batare dama tashiga kitchen d'in ba tawuce store ta d'auko tsintsiya da moper tafara gyaran falon duk da shima d'in bawani iyawa tayi ba tunda mom basasu takeyi ba.

Kai tsaye Ummi nafitowa tawuce part d'in dady, zaune ta iskoshi gaban computer dake can gefen gado yana wasu 'yan cike cike ta e-mail, sallama tayi ya d'ago kansa had'e da amsa sallamar yana mai jifarta da wani irin murmushi dake tabbatar mata da yalwatuwar farinciki atare dashi, murmushin itama tamayar masa tana mai k'arasowa inda yake tare da zaunawa agefen gado.

"Barka da safiya dadyn yara, antashi lpy?" Tafad'a cikin wata iriyar muryar dake d'auke hankalin duk wanda ke sauraro, a hankali dady ya juyo da kujerar da yake zaune akai ya matso kusa da ita da yake irin kujerar nance mai taya da ake amfani da ita amafi yawancin offisosa, hannuwanta biyu yarik'o da hannayensa yace "yawwa rabba'atul bait, tashin safiyata kuwa alhmdllh, ya jikin 'yarki Basmah gaba d'aya jiya nashafa'a da intambaya, injin tasamu sauk'i"

Sai da ummi kad'an b'ata rai kafin tace "tasamu sauk'i sosai, amma dady yayi laifi tunda bai tambaya ba sai yau kuma dole yakarb'i hukunci ahannun umminta" turo idanuwa yayi kafin ya kama kunnuwansa duka biyun yana fad'in

"Dady is sorry, ayimai afuwa don bazai iya jurewa hukuncin da rabba'atul baiti d'insa zata yimasa ba" wani irin far ummi tayi da idanu sannan tace "za'a duba idan k'orafi zai karb'u" anan take sanar dashi addu'ar da yakeyi tare da burinsa akan yaransa to Allah yakarb'a masa, ayanzu tana tabbatar masa da 'ya'yansu sun zama abu d'aya, wato tsintsiya mad'aurinki guda, no more problems or crasis a tsakaninsu, ta labarta masa yanayin da tariskesu aciki da wasu maganganun da tad'anji sunayi dake nuni da sulhun da suka samu.

Tsabar farinciki yasa dady ciro mak'uddan ku d'in da baisan ko nawa bane agefen aljihunsa ya damk'awa Ummi ahannu "ungo wannan tukuicin albishir da kika bani, idan hakan ya tabbata ko ayanzu Allah yakarb'i rayuwata alhmdllh, nasan banbar matsala abayana ba, kuma inada yak'inin nabar ingantacciyar zuri'ar da zata sakani alfahari" ya k'arasa maganar yana goge hawayen dake fita tare da dariya lokaci guda afuskarsa, hannunsa itama tarik'o tana jinjina kanta alamun tabbatar masa da abunda tafad'a, sannan ta mayar masa da ku d'in acikin tafin hannuna, "Aa dadyn yara kabarsu iya farincikin da naga kasamu ya wadatar dani agurbin tukuicin da zakayimun, sunjima suna tattaunawa akan maganar nan yake damar da ita barin dawowar mom yau, murna da fatan alkhairi tayi masa kafin nan su sake shagala cikin duniyar soyayya ta ma'aurata, ummi kam matuk'ar mamaki tashashi da irin wannan salo da dady ya b'ullo dashi tsakanin jiya da yau,

Ummi nadawowa har sun kammala gyara ko ina tare da had'a breakfast ko waccensu tayo wanka suna jiran fitowarsu, Ab'angaren mahmud ma haka akayi saida ya tadasu Bilal daga baccin da suka koma yayi masu wanka sannan shima ya shiga yayo wankan, yana kammala gyarawa ya rik'o hannuwansu suka nufi part d'in Ummi, suna shiga suka hango kowa akan dining table suka d'ai ake jira sai dady, gida ummi sukayi sannan suma suka samu wuri suka zauna akan dining table d'in ana d'an tab'a fira kafin dady yafito, shigowarsa yasa kowanensu yayi shiru har ya k'araso wajen shima yajawo kujera yana kallonsu d'aya bayan d'aya, cikin natsuwa suka shiga gaishesa yana amsawa had'e da mik'awa 'yan mazan hannu, plate Ummi tad'auka tafara sieving d'insa, pancake ne da yasha zuma a samansa, sai had'in ruwan coffee data yimasa a cup sannan ta d'auko wani d'an k'aramin bowl tazuba masa ferfesun Neman kaza da yasha kayan yaji sai k'amshi ke tashi ta ajiye masa agabansa, kallonta yayi had'e da cewa "thank you rabba'atul bait, Allah ya saka maki da alkhairi" Amin ta amsa masa dashi tana k'ok'arin cigaba da zuzzuba masu abincin Billy tayi saurin mik'ewa had'e da karb'ar sarving spoon d'in dake hannunta tana fad'in,

"Ummimu kizauna kihuta kema bari nak'arasa" sai da Billy ta tabbatar da tazubawa kowa nasa yanda zai ishesa ta ajiye masa sannan takoma tazauna, dadyne ya d'ago kai yana kallonta cikin yabawa da natsuwar da Allah yayi mata yace "Agaisheki Allah yayi maku albarka amma ke ina naki banga kinzuba ba?" Gaba d'ayansu suka amsa da amin Billy ta amsa masa da cewa "Dady nida my twiny zamuci" tana mai saka cokalinta a plate d'in Batool dake kusa da ita, tunda aka fara cin abincin babu wanda yakoma cewa uffan har aka kammala, nan take Billy da Batool suka kwashe kayayyakin da akayi amfani dasu suka kai kitchen bayan sun dawo, dady yayi gyaran murya alamun yana son yin magana dasu mai muhimmanci, nan take kowanensu yanatsu had'e da tattaro hankalinsu agaresa, cikin jin nauyin abunda keson fitowa daga bakinsa yayi masu bayanin dawowar mom yau tare da nasiha mai ratsa zukatansu akan suji tsoron Allah suso 'yan uwansu kuma suhad'e kawunansu hakan zaisa hankalinshi ya kanta kuma asirinshi yarufu duniya da lahira, sosai kalamansa sukasa ummi jin tausayinsa kuma yaran suka yimasa alk'awarin cewa zasuyi yanda ya umurcesu da yardar Allah wanda hakan ya matuk'ar k'ara masa natsuwa sosai.

Dubu d'ari ya fiddo ya mik'awa ummi dubu hamsin yace tayi 'yan wasu saye saye da gyare gyare da take da buk'ata, karb'a tayi tana mai godiya da yimasa addu'a sannan ya mik'awa mahmud dubu hamsin yace yaje ya kaiwa mom d'insa itama idan akwai abunda take buk'atar saye. Makullan part d'in mom ya mik'awa mom yace tabawa Basmah suje su gyaggyarawa mom part d'inta tare da sake ciro wasu dubu hamsin yaba mahmud yace ya d'auki dubu ishirin dubu talatin kuma yaje da Basmah da k'annenta su siyo duk abunda suke buk'ata. Godiya sukayi masa sosai tare da addu'o'i sannan yamik'e don wucewa office, har mota Ummi tarakasa yayi mata bye bye kiss sannan ya shige cikin motar tana yimasa Allah ya kiyaye, Allah sarki uwa da d'a sai Allah wani irin farincikine yabayyana a fuskokin yaran mom wanda yakasa b'oyuwa saboda jin dad'in mahaifiyarsu zata dawo.

Mom kuwa safiya na wayewa ko sallah batayi ba ta d'auko gumbar da hajia kilishi takawo mata da tazo ta sirrin mallaka ta dameta tsaf tashanye tana faman nishi saboda yanda cikinta yacika da ita har yana neman d'ad'ewa.

Dariya hajia kilishi tashiga yimata tana yimata kirari "kaga amaryar alhaji da kanta, yau sai gidan alhaji akwan kwad'i amarci, wayyo alhaji daga yau kazama na Hussaina basa kanka asare aduk inda kashiga..."

Murmushin k'arfin hali mom da ko motsi mai k'arfi bataso tayi saboda yanda cikinta ya babbak'e mata.

"Kai wlh Allah ji nake da bansha abunnan ba, kinji yanda zuciyata ke tashi kuwa? gashi ko shed'ar kirki bana iyayi Allah sa dai bazata sakani zawo ba wannan sheri har ina, wlh Allah badon alhaji ba da kud'i bazan iya

Please Login or Register in order to submit comment