Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fahimci komai ba akan yanayin da tashiga jiya hakan yabata damar sakin jikinta dashi sukasha fira sosai sannan yabar falon zuciyarsa cike da tambayoyi akan abubuwan da suka faru da ita tsakanin jiya da yau, yana fita takoma d'aki ta d'auko wayarta takira hajia kilishi, bayan sun gaisa ta dinga kora mata bayanan abubun da suka faru da ita da kuma rashin cimma nasarar da basu samu ba, dariya hajia kilishi tayi sosai har tana fad'owa akan gado wanda hakan ya hasalar da mom takashe wa yarta, hajia kilishi na hawaye takira har sau biyu amma tak'i d'agawa saida takirata akaro na ukku sannan ta d'aga, gimtse dariyar tayi tare da cewa

"Sorry k'awata ai dole inyi dariya, cewafa kikayi kinyita birgima da alhaji a tsakar parlour wai izuwan aljanu duk don kirage zafi ai kinga dole inyi dariya, a gaskiya yaran nan basu kyauta makiba amma ai ba matsala tunda akwai sauran a ajiye ko?" Cikin wata irin murya mom tabugi gaba tace "sai inyi maki u....me dashi ai wlh ba alhaji ba ko duniya zan mallaka nabashi baya, tun jiya na yanke shawarar jefashi acikin masai na manta amma yanzu kin tunamun"

"Ke.ke..ke qawata wlh ajiyemun abunda inaso, da tsada nakarb'osa yanada kyau sosai wlh kawai kema don baku had'u bane, duk wannan yanayin da kika jiki wlh da alhajinki yazo hannu to shi zai tsinci kansa ahaka, tayanda kullum yana tare dake kuma bazai so b'acin rankiba don karki yimasa k'walele.."

"Mts..yo anfad'a maki ni jakace da zanjuri haka?, wlh ba tsinanniyar da zan ajiyewashi tayi amfani dashi, banza wai tukuna ma u..meye kika had'ani dashi?" Dariya hajia kilishi tasakeyi kafin tace

"Hmmm... Desire fluid ne da kuma sperm d'in ayu, ke banza na manta da sauran, kawai kibarshi tunda kinyi missing ushe mai aljanu"

"Mtsss..kidena wannan sakarcin kinemomun mafita, can da yawarki dake da maganin kuma wlh bazan ajiye maki Shiva"

"Shikenan naji tunda plan A and B kin ruguje mana su bari muje Plan C, kice alhajinki bai fahimci komai ba yagama yarda cewa aljanune ko?"

"Eh mana haka nake tunani"

"Good, da kanki kinsamo mana mafita, kuma natabbata zaiyi working, da wannan damar zakiyi amfani ki dinga sak'a mata makirci kala kala, ince dai tasan da wannan zancen?"

"Eh, don har tazo dubani"

"Wow, kinga saiki san tuggun da zakiyi mata awurinsa ta yanda alhaji zai tsaneta"

"Kamar ya?"

"Hmmm kiyi tunani, natabbata da kanki zaki shirya hakan, sai anjima zankiraki daga baya" sai da mom tayi wata irin dariyar shak'iyanci sannan tace

"Ai har nagama gano shirin da zanyi, kihuta qawata sai nakiraki" suka ajiye wayoyin atare mom najin wani irin nishad'i atare da ita.

Allah sarki Ummi da bata san me ake k'ullawa akan taba, ganin sauyin datayi a fuskar mom yasa tayi tunanin sake zuwa ta dubota anjima, ita kuwa gaba d'aya tagama shirya plan d'inta akan yadda zata soma had'ata da dady akan maganar da tayi d'azu cewa tabata mom d'in ce ba lafiya da taji dady nafad'i.

A hankali tafito d'aki hannunta sargafe da hand bag d'inta cikin fararen kayanta na aiki, tsohon dake zaune akan kujera tsakar gida yana karanta jarida takalla tana murmushi taje ta rungumesa,

"Ina kwana Jaddi, ni zantafi nasoma yin latti"

"Oh nikuwa gashi ina son muyi wata magana maimahimmanci dake faraaha, amma shikenan idan kindawo mayi"

"To jaddi shikenan natafi"

"Adawo lafiya" cikin natsuwa take tafiyarta har ta isa bakin titi, mai adaidaita sahu tatara tafad'a masa inda zai kaita

A jidda specialist hospital yaya Mahmud yanufa, yana kaiwa yayi parking motarsa daga ciki, yabud'e masu suka rirrik'o Batool suka shiga da ita ciki tana takawa ahankali.






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


๐Ÿ’ŽPage_____39๐Ÿ’Ž


Suna shiga suka nemi wuri suka zauna, yaya Mahmud ya shiga lallatsa wayarsa don ganin family Dr. d'insu wato Dr. jamil, kusan ringing uku tanayi bai d'aga ba, da alama wani abun mai muhimmanci yakeyi, ganin haka yasa yadena kira yashiga waige waigen ta inda zaifara, dr.kamal ya hango wanda ya kula da case d'in Billy lokacin da batada lpy, da sauri yaci gabansa yana murmushi tare da mik'a masa hannu.

"Assalamu alaikum, morning dr." Cike da fara'a dr kamal yacire glass d'in dake idonsa shima yana mayar masa da murmushin da yake yi masa "wa'alaikassalam malam Mahmud yau kaine a asibitin namu"

"Wlh kuwa dr. Sister nace ba lafiya" tak'are maganar yana nuna masa inda suke zaune da hannu,

"Ayya kaddai ace 'yar gidan dady ce, don nalura k'anwar nan taka shagwab'abb'iyace shiyasa take yawan jima kanta."

"No bahaka bane, wannan karon Auntyn tace Batool, kuma nayita kiran dr. Jamil but not answer"

"Eh to! Dayake gaskiya muna gudanar da wani muhimmin tarone anan ciki nak'arawa juna sani, nima yanzunnan nafito daga ciki zand'oko wasu takaddu da ake buk'ata awurin, but bari na had'aku da nurse faraaha idan ba serious case bane, idan kuma zaku iya jira nan da 1hr in sha Allah mun k'are kaga ni ko dr jamil we should handle the case" hannu yaya Mahmud ya mik'a masa had'e da cewa "noo..thank you very much, ko sister faraaha d'in muka samu gani is OK, am sorry na tsayar dakai" shima mik'a masa hannun yayi tare da cewa

"Habaa!..nothing much, u're welcome" sannan ya wuce, agurguje ya d'auko takardun a office d'insa sannan ya shiga wani office sai gashi sun fito tare da ita abayansa yana fad'a mata magana had'e da nuna mata inda su Mahmud suke zaune, murmushin ta mai k'ayatarwa tasake tana comperming d'insa cewa babu wata matsala, wucewa yayi ita kuma ta doso wajen cikin tafiyar dake tabbatarwa duk wanda ke kallonta irin natsuwar da take da ita, mutuwar tsaye Mahmud yayi wajen kallonta har ta iso wajen ba tare da ya ankara ba, da gefen ido ta kallesa kafin ta d'auke kanta tana cigaba da murmushi, sallama tayi tana kallon Billy data ware idanuwa had'e da rufe baki

"Laah aunty faraaha" ta taso da sauri ta rungumeta,

"Lil sis kece kika k'ara zama 'yar lukuta haka, masha Allah, inasu ummi da Bilal lpy suke?"

"Lafiya klw aunty faraaha ya aiki kwana biyu kin b'uya, gaskiya nayi missing d'inki sosai" Billy ta fad'a tare da d'ago kai tana kallonta, harararta tayi tana fad'in

"Ni cikani kafin raina ya b'aci, keda gaba d'aya tunda kuka bar asibiti nan kika manta dani, tukunama dai waye ba lafiya acikinku?" Tak'are maganar tana kallon gefen da mahmud ke tsaye ya shagala da kalonnta, Sai alokacin yadawo hayyacinsa, d'an sosa k'eyarsa kansa yayi kafin yace

"Am..sannu sister faraaha!, dama sister nace muka kawo tasamu 'yar matsala a k'afarta" yana mai nuna mata Batool dake zaune ta jingina kanta a kafad'ar Basmah, kallonsa tayi cike da yaba kyawon da yayi mata kafin tad'an basar tana fad'in.

"Sannu yaya Mahmud" tare da duk'awa tarik'o k'afar Batool

"Ayya sorry sister, me yasamekine?" Kamar jira Mahmud keyi yayi carab da maganar gudun kar Batool tafad'i cewa mom d'insu ce ta taushe mata k'afa yace

"Ammm..dama garin sauyawa fridge wajen zamane a kitchen ita da Basmah to ashe ita Basmah d'in bata rik'a dakyau ba sai tasakar matashi ak'afa" tun daga yanda Mahmud ke bayani faraaha ta tabbatar da bahaka bane d'ago kai tayi ta kallesa alamar ka tabbatar kuwa, batare da yace mata komai ba yabar wajen yana d'an murza saitin zuciyarsa, don har ga Allah d'ago kan da tayi tana kallonsa ba kad'an yaji wani abu ya dirar masa azuciya ba, mik'ewa tayi tacewa Billy sujirata yanzu zata dawo, orthopedic clinic d'in dake cikin asibitin tanufa,
bayan kamar minti biyar sai gata tadawo tare da wata messenger ta turo irin kujeran nan da ake gungura marar lpy, rik'o Batool tayi da taimakon Basmah suka d'orata messenger d'in tajata tare da bin bayan sister faraaha, ganin haka yasa suma su Billy suka rufa mata baya, kasancewar asibitin kud'ice nan take ake ciro folder Batool k'wararren likitan dake on duty ya dubata da yake dama faraaha tariga tayi magana dashi, sosai ya duba k'afar had'e da d'an messaging d'inta, ihu sosai Batool keyi tana kiran "wayyo yaya Mahmud kataimakeni zanmutu, twiny kizo kusa dani don Allah wlh mutumennan ba yada imani, yayya Basmah don Allah ina kike kuzo kutai makeni" cikin kwanciyar hankali matashin dr. Dake sanye da glass ke aiwatar da jikinsa batare daya damu da ihun da takeyi ba, "wayyo yay..." da sauri ya katseta tare da d'ago kansa yana fad'in

"If you shout again i will cut ur leg" sannan yaci gaba da murza k'afar, kuka take rerawa tamkar wacce akayiwa mutuwa shi abun ma sai yabashi dariya. Aransa kuwa cewa yake lallai wannan yarinya duk wanda ya kwasheta zaisha fama da rakin tsiya, shi alokacin da yaga an gungurota cikin keken mararsa lafiya ya d'auka wani serious injury ne da ita, ashe waima d'an targad'ene tayi shine ake wani gungurota akeke, to inata ace kariyace tayi ko gwabcewa, wai! Yafad'a afili batare da yasan maganar tafitoba, wani haushine ya kama Batool jin abunda yafad'a, wato ita da ciwo shida fad'in wai!, tattakewa tayi ta rafka wani uban ihu tare da kiran Ummiii, tsabar yanda ihun ya firgita dr. Saida ya tashi fad'uwa da sauri ya rik'e gefen gadon wanda har saida yabuge goshinsa da gefen wata drower da ake ajiye takaddu aciki, faraaha ce tabud'o gambun office d'in da k'arfi tashigo don ganin ko lafiya Batool ke zabga wannan uban ihu da yawuce ace na treatment ne. Tsaye ta iskosa yana k'ok'arin daidaita zaman curt d'insa tasama had'e da necktight d'insa yab'ata fuska sosai, akan kujerarsa yakoma ya zauna sannan yajawo wata takarda dake saman table d'in dake gabansa ya d'anyi rubuce rubuce akai sannan ya kalli Batool da har lokacin tana kwance tana sharb'ar hawaye ak'asan zuciyarta kuwa dariyace take sosai tare da jin dad'in yanda ta rama cutar da yake yimata. Ad'an tsorace faraaha takallesa tace

"Dr injin dai lafiya naji patient d'in taka nata ihu" da yake suna d'an wasa tsakanin su shiyasa tasamu damar yimasa wannan tambayar.

Cike da jin haushin ta da tazamo solar had'ashi da wannan muguwar patient yace

"Ai sai kije kitambayeta, ungo takardar maganinku, insha Allah babu wata matsala d'an targad'ene taji" tare da mik'a mata takardar ta karb'a sannan tanufi inda Batool d'in ke kwance, haushin sane yak'ara rufeta lokacin dataji yace wai d'an targad'ene taji, wato don baisan irin zafin da takeji ba shiyasa yake kiransa da wai d'an, k'wafa tayi tana k'ok'arin saukowa daga kan gadon suka had'a ido dashi ta zabga masa wata irin harara dake nuna kaima Allah ya had'aka da irin wannan targad'en da kake kira wai d'an, kallo yabita dashi ganin yanda faraaha tarik'ota tana faman tsilga k'afa sai kace wata gurguwa, juyowa faraaha tayi tace "Thank you dr. Ahmad" murmushi kawai yayi mata kafin ya cije baki had'e da girgiza kai "yarinya Allah ya sake maidoki anan kuma muhad'u wlh sai kin yabawa aya zak'i" yafad'a acikin zuciyarsa yana k'ok'arin ajiye folder d'inta gefe, har ya ajiye sai kuma ya sake d'auko wa yana karanta sunan da aka rubuta ajiki, _FATIMA BASHAR MAI FURNITURES_ sunan ya sake maimatawa afili sannan ya maida folder d'in ya aje.

Suna fita Batool takalli faraaha tace

"Sister don Allah ko ciwo zai kasheni kada ki k'ara had'ani da wannan dr.wa naji kince masa? Wlh he's very wicked, kinji yanda yake murzammun kafarnan kamar yasamu busashshiyar gyad'a? Wlh Allah zai isarmun mugu kawai!" Dariya faraaha tayi had'e da sakinta tace

"Ok, tunda zaginsa ma zakiyi duk wannan taimako da yayi maki ni bazan rik'a kiba, sai kiyi tafiyarki da kanki" turo baki tayi tana d'an k'ok'arin takawa da kanta, aikuwa kamar wasa taji tana iya tafiya da kanta duk da tana d'an jin zafi kad'an ak'afar, juyowa tayi tace da ita

"Laa..sister duba kiga ina iya tafiya da kaina"

"Eh mana ai duk waccan muguntar da kike cewa yayi maki itace silar iya tafiyarki, kinga dr. Ahmad mutumne mai kirki da sauk'in hali sosai, kawai shidai bai fiye son tsiwa da rashin kunya bane, ko nice shi zanyi maki fiye da yanda yai maki, irin wannan ihu da kike yimasa ai sai kisa masu k'aramar fahimta su zargesa" turo baki Batool tasakeyi sannan tace "yo ai da zafi yakemun kuma hadda cewa wai zai yankamun k'afa idan ban rufe masa baki ba" saida faraaha tayi dariya sosai sannan tace

"Baki sanshi bane, ai haka yake da son zolaya, kawai yafad'ane don kiyi shiru amma ba yana nufin haka ba" k'ok'arin wata maganar tayi takatseta "kinga muje kada kisa kafara nemana awurin aiki, Mahmud kam yau kasa b'oye abunda keransa yayi har saida ya furtawa faraaha yana k'aunarta, duk da yakasa samun kyakkyawar kulawa da amsa daga wajenta saboda yanayin aiki da take ciki saida ya nace mata sosai yabarsu Batool can acikin mota, dak'yar yasamu ta bashi lambarta koshi don taga yana son takura mata awajen aikine.













*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


๐Ÿ’ŽPage_____40๐Ÿ’Ž


Sosai faraaha kebin farinciki aranta saboda cimma burin soyayyarta datayi wajen yaya Mahmud, tun lokacin da aka sallamesu asibiti take d'awainiya da soyayyarsa azuciya kuma dai dai da second d'aya bata tab'a fitaba, taso taja masa aji sosai lokacin daya furta Kalmar so agareta amma tsoron kada ajin ya tsinke takasa samun tudun dafawa ya sata bada kai bori yahau, a natse take aikinta fuskarta d'auke da murmushi tana tunano kyakkyawar fuskar her first luv d'inta, haka tab'an garen Mahmud shima bakinsa kasa rufuwa yayi tsabar farincikin samun soyayyar da yake tunanin ta kucce masa ada duk da cewa ko yanzu bayada tabbaci akan amsa tayin soyayyar sa, cike da farinciki ya saki stearing motar had'e da murza tafin hannunsa yana fad'in " Thank you ya rabh for making us together again" Murmushi Basmah dake gefensa tayi don tagama fahimtar hak'ar faraaha ta cimma ruwa, gefe ta maida kanta tana kallon yanda motoci kewucewa kan titin, yayinda ita kuma Billy tamatso inda suke ta tsakanin kujerar ya Mahmud da kujerar Bassam tadafa kamar yanda yara keyi sannan tace

"My broth wai mekake yiwa wannan sabbatun haka, pls don Allah karik'e motarnan kada kasa mubuga" dafe stearing d'in yayi yana dariyar da saida gaba d'aya fararen hak'oransa suka bayyana kafin yace "Bari kawai my sister abun sirrine, zamu magantu anjima, yawwa bari natambayeki wai tunda aka sallamoki asibiti kinyiwa sister faraaha godiya kuwa?, kinsanfa ta taimaka maki sosai lokacin" Billy tace "a'a ni kwata kwatama na manta da ummi nada nombert balle inkirata nayi godiya" juyowa yayi tare da d'aga hannunsa kamar zai doketa yace "ke ko!, kinfiye mantawa da alkhairi dole yau d'innan kikirata kiyi mata godiya" wata irin dariyace ta kuccewa Basmah har tana rik'e cikinta, juyowa tayi tana kallon Billy tace "Gaskiya sister yayankin nan ya fola (Teemah gabs word๐Ÿคฃ) da yawa, irin wannan zance haka ai zai iya shek'eni wajen dariya" gaba d'ayansu suka kwashe da dariya suna fad'in "Gaskiya ne" rank'washi yakai mata akai daidai lokacin da yake k'ok'arin parking abakin wata had'ad'd'iyar restaurant "gulmammiya! wato tun yanzu zaki fara yimana putting eyes ko?" raurau tayi da idanuwanta da suka cika da hawaye don ita abu kad'an kesakata kuka kafin tace "Kai yaya da zafi fa" sorry yafad'a tare da bud'e gambun motar yana fad'in "kufito muyi breakfast yau yajin aiki zamuyiwa girkinsu Ummi" turo baki Basmah tayi tana d'an goge hawayen da suka zubo mata, ahankali tayi k'asa da muryarta tace "Bawani can kai dai kawai kace 'yar k'aramar liyafa zaka had'a mana, tamurnar samun soyayyar faraaha" yana jinta ya saki murmushi kawai ya wuce abunsa batare da yace komai ba sannan suma suka fito suka rufa masa baya, kowace abunda takeso tafad'a aka kawo masu, sunci sun sha sunyi nak sannan yaje dasu shop d'in dake gefe a cikin restaurant d'in, chaoculate ya kwasar masu sosai da biscuit biscuit sannan yaje ya biya kud'in suka kamo hanyar gida, Batool kam Alhamdulillah tasamu sauki a k'afarta sosai duk da har yanzu tana d'an d'ingishi da ita, suna isa suka fito motar da gudu suka nufi part d'in Ummi suna dariyar yanda yayan nasu duk yabi yarud'e akan faraaha yanata zuba masu kyauta, dariyar shima yayi tare da rik'o Batool dake tafiya ahankali don bazata iya guduba "sannu Batool d'in mom" yafad'a sunaci gaba da tafiya ahankali hannunsa rik'e da ita har suka iso part d'in Ummi tana bashi labarin yanda faraaha ta taimaka mata d'azu, wani irin farinciki yak'ara tsintar kansa aciki yanaji a wannan karon bazai tab'a yadda nauyin bakinsa yakaisa ga rasataba.

A parlour suka tadda ummi zaune tana yanke wa su Bassam akaifa (qumba), Basmah tazo tabayanta ta sagalo hannuwanta a wuyan Ummi tana fad'in "Ummi sannu da aiki" had'e da bugo k'eyar Bassam dake zaune ana yanke masa yatsan k'arshe nak'afarsa "kai d'an lukuti tashi kabamu waje tsogumi zanyiwa Ummi" d'ago kai yayi zaiyi kuka Billy dake zaune kan kujera gefen da Ummi kezaune k'asa tajawo hannunsa ta d'orasa akan cinyarta tace "k'yale yayya Basmah nafahimci 'yar k'ibar nan tamu ta tsole mata ido, magani yakan farcen da Ummi tayi maka gayuuu" da haka ta badalar dashi daga kukan da yake shirinyi, ita kuwa Ummi dariya tayi tace

"A'a..nifa dad'ine dake kenan Basmah bakya girma, yanzu da kinsa na yanke masa farce da kika fad'omun haka, cikamun wuya tunda kina neman samun yaro kuka" sakinta Basmah tayi tana dariya had'e da cewa

"Kai Ummi sorry irin wannan gwatsilewa haka ai sai kisa yaya yimun dariya idan yana wajen" "ai kuwa baki tsiraba tunda gani awajen ko yanzu" taji muryarsa da shigowarsa kenan yana dariya shida Batool, juyowa tayi takalli Ummi "Kin gani ko Ummi dama nafad'a maki" hannu ummi tasa tashafo fuskarta sannan tace "K'yaleshi fad'amun wane labarin kika kawomun yarinyar momy" da sauri ya k'araso wajen yatureta gefe "pls Ummi kada kisaurareta, wannan alk'awarinane ko meye da kaina zan sanar dake in lokaci yayi"

"Wlh kada kiyarda Ummi wayau zaiyi maki, kawai kabari infad'a idan kai kunya kakeji, Ummi wlh yaya ya.." Filo ya d'auka throw pillow yad'auka ya jefeta dashi takasa k'arasa maganar,

"A'a babanah wai meye haka kake b'oyewa 'yar taka ko ba'a sone inji" ummi tafad'a tana murmushi

"Ummi zakiji amma ba yanzuba" saida Basmah takai bakin k'ofar fita parlour tace "Ummi yaya Mahmud da nurse d'innan faraaha sun fola" tana gama fad'a taruga aguje tayi wajen mom tana dariya, sosai ummi kedariyar itama tana tambayar Basmah data dad'e da barin wajen wai meye fola. "Babana wannan yaren fola a ina Basmah ta samoshi, wai sun fola" tafad'a cike da mamaki, Billy ce tayi saurin cewa "waifa sun fad'a soyayyar juna take nufi ummi"

"Allah sarki, da gaskene babana?
Mahmud da gaba d'aya kunya tarufeshi ya sosa kansa yana kallon Batool dake can gefe zaune itama tana yiwa su Bilal wasa abunsu tayi kamar bata san suna firar ba.

Murmushi Ummi tayi "ah to madallah, aiki yarinyar nada hankali sosai Allah yasa matarkace idan alkhairi ce agareka, nikam naji dad'in wannan folawar, shin haka ake fad'a ko Bilkisu?" tak'arasa zancen tana kallon billy dake faman dariya,

"Kai ummi haddake ke fad'in haka kuma?, nifa kalmarma dariya take bani, Basmah bataji wlh awajen wata qawarta Teemah gabs ta d'auko wannan yaren"

"Aw.. ashe kema Billy fad'a kawai kikayi bakisan meye ma'anar saba" ummi tace haka tana dariya, anan dai suka zauna suna cigaba da yin firarsu hankali kwance abun gwanin ban Sha'awa kai kace Ummi ce tahaifesu gaba d'aya.

Duk wani shiri da mom zatayi ga Ummi idan dady yadawo part d'in taga abunta, ai kuwa yana dawowa ko sannu da zuwa mom bata yi masa ba lokacin da yashiga part d'inta, tanajin sallamarsa zai shigowa d'akin tafashe da kukan munafucci, da sauri ya ida shigowa d'akin yana tambayarta kome kefaruwa da ita amma tak'i tankasa sai kukanta take rabka, tagumi yabuga yana kallon ikon Allah kafin can yasake cewa "Momyn yara don Allah kidena wannan kukan, kifad'amun menene yafaru idan kuma laifi nayi makine ai saiki fad'a mani ko?" Cikin kukan tace

"Haba alhaji kaduba kagani tunjiya dana sanyo k'afata cikin gidannan nakasa samun kwanciyar hankali da natsuwa, yarana duk sungujeni saboda tsorata da sukayi da yanayin da suka ganni jiya aciki wanda nikaina ban tab'a tsintar kaina acikiba sai jiya, yau kuma ina tunanin babu wanda yasan da haka daga mijina sai 'ya'yana ashe kaje kafad'awa aunty Aisha, har nan part d'in tazo tana yimani sannu wai tunjiya daka fad'a mata banida lpy taso tazo dubani amma kace tayi zamanta muggan aljannune dani, haba alhaji ashe kai bamai rufe asirina bane, har take cewa Allah yasa ba nagadone nakwaso ba, kenan so take tayi mun anan maganganu ga iyayena don taga nadawo daga wajensu" wani irin kuka mom tasake fashewa dashi wanda dole dady yayarda da cewa bak'in ciki da munin kalaman da Aisha tayi matane yasata cikin wannan k'uncin da yakaita ga zubar da hawaye shiru yayi yana nazarin kalaman da shi kad'ai yasan zuciyarsa ta raya masa cewa mom aljanu sun shafeta sai kuma Mahmud daya fad'ama, kuma ya tabbata mahmud bazai fad'awa Ummi halin da mom d'inshi tashiga ciki ba saboda yasan irin hankali da tunanin da yake dashi, dole sai in fitowa Ummi tayi taji yana fad'a masa shine tayi amfani da wannan damar don ta muzguna mata, wani b'angaren zuciyarsa tace ko kad'an wannan ba halin rabba'atul bait d'inka bane ba zatayi hakan ba, yayin da wani b'an garen kuma yabashi cewa ai ajizancin d'an Adam na iyasa tayi haka tabbas in hakane Aisha bata kyau taba don tasani baitab'a zuwa yafad'a mata sirrin dake tsakaninsa da matarsa ba kamar yanda itama baitab'a fad'in nataba awurin mom, to don me zatayi masa haka bayan tasan yana kamanta yimasu adalci, wato so takeyi ta sakashi cikin damuwa kenan" mom kuwa dake lek'ensa tana ganin yanda fuskarsa ta sauya zuwa alamun b'acin rai tak'ara volume d'in kukanta hadda wata sheshshekar kuka takeyi tanajan numfashinta, gudun kar tashiga yanayin data shiga jiya yasa dady yafara lallashinta yana bata hak'uri tare da tabbatar mata da zaid'auki k'wak'k'waran mataki, da haka yafito part d'in cikin b'acin rai zai shiga wajen ummi sai gashi yaga mota tashigo tayi parking cikin harabar gidan, da guda yaga junior d'an wajen k'anwarsa hajia hafsat dake aure borno yafito yayo wajensa yana fad'in "unclee..", cike da fara'a ya taromasa hannu ya chab'esa sama yana fad'in "oyoyo my son"

Wani kyakkyawan saurayi dako zai girmi yaya Mahmud bazai wuce da shekara uku ba naga yafito daga cikin motar tare da zagayawa tacan gefe yabud'e murfin motar, hajia hafsat ce tafito tana murmushi da farincikin ganin yayan nata, takowa takeyi zuwa wajensa shi kuma saurayin ya take mata baya yana sissinne kai k'asa, Mahmud kenan! yaro d'an kwalisa mai cikar zati da kuma kamala, farine sosai yanada dogon hanci sai dai bayada idanuwa sosai, bakinsa kuwa zaka d'auka jambakine aka shafa masa saboda yanda yake d'auke da k'ananun lab'b'a da ake kira pink lips, yanada matsakaicin tsawo kuma d'an kakkabrane saidai ba sosai ba. Yanada matuk'ar jinkunya ga magabatansa yayinda yake zama miskili cikin tsararrakinsa, awurin 'yan mata kuwa zaka d'auka shi kurmane, suna matuk'ar kama da Billy tayanda zaka d'auka shi yayantane, tunda yataso yake matuk'ar son Bilkisu saboda yanda ummansa kefad'in kamarsa da ita. Ko kad'an baya wasa da yaran gidan duk da zamowarsu taubasansa (cousins) amma indai Billy na awuri babu wanda yarena da zolaya kamarta, ita kuma hakan yasa bata fiye son suzo ba saboda d'aukar abun amatsayin takuratane yake, Mahmud shine first born d'in hajia Hafsat tana matuk'ar sonsa sosai saboda sunan mahaifin sane ya gada wato sunan mijinta kuma abbansa, sun tsaya masa sosai wajen karatunsa wanda saboda k'wazonsa yasa shima yake shallake duk wani matakin karatun da suka d'orasa akai cike da nasara, yanzu yanada shekara 30 cicciccif arayuwarsa, kuma yayi nasarar had'a degree ukku a wannan lokaci tafanni daban daban, yahad'a degree d'insa tafarko ne afannin computer science ta biyu kuma a fannin marketing ta ukku kuma a fannin koyon tuk'in jirgin sama wato pilot wanda yanzu haka ya samu

Please Login or Register in order to submit comment