Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya jiyo muryar mom d'insa dake tsaye abakin k'ofar part d'inta tana kallonsu tana fad'in

"Dama ya za'ayi yayi abunyi bacin an maidashi susutacce sai yanda akayi dashi, toni bazan lamunci wannan akan yarona ba, shikenan tsabar mugunta an mayar mani da yaro bayajin maganata sannan baya son 'yan uwansa, mutum ko tsoron hakkin haihuwa bayayi akansa ai wannan mugun tace wlh"

Baki bud'e Ummi ke kallon mom batare da tace mata komai ba Don babu kalamin datayi mamakin jin fitowarsa daga bakinta, sai dai takai aya sannan ta kalleta sama da k'asa tace

"Allah ya sawak'e"

Cikin k'ufuwa mom tafara masifa

"Allah a fuska fir'auna azuci kin raba mani kan yara kuma nayi magana waike ustaziya kina fad'in Allah ya sawak'e, to ai yasawake abunda yafi haka tunda duk qulle-qullenki bai rabani da mijinta ba"

mahmud baice mata uffan ba yaja hannun 'yan uwansa da niyar barin wajen mom ta fincike hannunsa

"Lallai yaron nan asiri yayi tasiri kanka, yanzu kana gani tana neman cimani mutunci zaka rab'ani ka wuce? " kawai sai tafashe da kuka tana cewa

"To wlh bari alhaji yadawo sai yayi maka tsakani da matannan tunda ba ita tahaifeka ba, shikenan k'irik'iri ana neman rabani da yarona"

Tsoron Allah ne yakama bilal jin wai mom ke fad'in yana kallon za'a cimata mutunci bacin ita kecin mutunci wasu

Basmah ce tafito tana kiran mom uban waye yasaki kuka

Bud'e bakin da Mahmud zaiyi yabata amsa yaji tarasss.. saukar mari afuskar Billy Basmah tayi mata Tana fad'in


"Wato ke 'yar iska tunda yaya ya d'aure maki shine zakiyiwa mom rashin kunya har kisata zubar da hawaye? Idan ita uwar ki...."

Kafin tarufe ida itama taji tass-tass saukar marora afuskarta har sau biyu, wuyanta ya shak'o yana neman illatata Ummi tayi saurin b'anb'are hannunsa

"Enough babana ai batasan meke faruwa ba, dirar mikiya tayiwa abun shiyasa tayi haka, k'yaleta kaji ko?"

Wani irin jiri ne ya d'ebi mahmud nan take yafad'i k'asa dafe da kansa , Ummi ce tayi saurin rik'osa tana fad'in

"Subhanallahi babana lafiya?"

Tureta mom tayi had'e da cewa

"Shikenan kin sabatta mun yaro, wayyo nashiga uku shima so kikeyi ki kasheshi kamar yanda kika kashemun sauran yarana.........
































Mr's huss@in✍🏻

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NANE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____5πŸ’Ž


Baya Ummi taja had'e da rik'o hannuwan Bilkisu da Bilal ta nufi part d'inta idanuwanta na zubar da hawayen tausayin Mahmud, ko shakka babu tasan tana matuk'ar k'aunarsa aranta shi yasa bata iya jurewa idan ta gansa cikin damuwa, gashi yanzu tanaji tana ganinsa awani hali amma an haramta mata taimakonsa. Har ta kusa shiga part d'inta sai kuma ta juyo,

Kallon inda su mom suke tayi har lokacin suna kan mahmud sun kasa bashi taimakon daya kamata. Goge hawayen idanuwanta tayi had'e da cewa.

"Bilkisu maza shiga ciki keda Bilal ina zuwa"

"Ummi ina zakije?"

"Kuje nace ina zuwa bakwa ganin d'an uwanku ba lafiya"

Wurin gate ta nufa ta yiwa maigadi knocking da saurinsa ya fito ya russana agabanta yana fad'in.

"Allah yatsareki hajia ina gaisuwa, me kike buk'ata ne yanzu nayi maki"

"Am malam habu ina saleh driver yake?"

"Bai jima da fita ba ya raka abokinsa da yazo wurinsa d'azu..." kafin ya rufe baki sai ga saleh driver ya iso yana rera 'yan wak'ok'insa, yana hango Ummi ya rugo aguje yana gaisheta.

"Yawwa saleh maza ka fiddo da mota ga Babana can ba lafiya kukai sa asibiti pls kayi sauri"

"Angama hajia" saleh ya fad'a tare da nufar wajen da motoci suke ajiye ita kuma ummi ta wuce part d'inta da nufin gyarawa tabi bayansu.

Saleh na fitowa da mota sai ga batool, cikin gadara tace,

"Kai saleh ina zakaje ne? to kajira zamu kai yaya Mahmud asibiti inji mom"

Tana gama fad'a masa tabar wajen. A wani private hospital _Jiddah specialist hospital_ suka nufa kasancewar acan family doctor d'insu yake kuma a can duk 'yan gidan suke da folder, suna isa ba tare da b'ata lokaci ba aka shiga duba Mahmud, nan likita ya tabbatarwa da mom ba kome ke damun saba illah damuwa daya sa a ransa itace ke haifar masa da tsananin ciwon kai a duk lokacin da wani abun ya b'ata masa rai, don haka akula adena barinsa cikin damuwa domin hakan na iya tasiri ga zuciyarsa har yasa zuciyar ta fara yi masa ciwo.

Jikin mom ne yayi sanyi jin abunda likitan ya fad'a, kallonsa tayi kafin nan tace.

"Dr. toh ya jikin nasa yanzu?"

"Ki kwantar da hankalinki babu wata matsala yanzu haka anyi masa allurai tare da sanya masa drip bacci ya d'aukesa yana farkowa zaku iya wucewa gida, Amma dai ku kula sosai!"

"Insha Allah dr mun gode"

Rufe bakin mom keda wuya saiga Ummi ta shigo asibitin cikin damuwa ta nufi inda mom take,

"Momyn yara ya jikin baban nawa ina fatan da sauk'i ko?" ko kallon inda Ummi take mom ba tayi ba balle ta samu damar amsa mata. Hakan yasa Ummi ta samu kujerar dake gefe ta zauna, bata jima zaune ba sai ga family dr d'in su ya shigo,

"Ah...Hajia sannunku ina wuni,"

"Lpy klw dr"

"Ya na ganku anan, waye ba lafiya?"

"Babana ne Mahmud ba lafiya"

"Ayya why not da ba'a kirani nazo har gida ba? me ya samesa?"

"To nima dai ban sani ba, amma muna tsaye kawai mukaga ya fad'i k'asa had'e da dafe kansa..."

Kafin Ummi ta rufe baki mom ta Katseta da masifa,

"Ta yama za'ayi kisani kina nema ki kashe mun yaro to wallah....."

"Hajia hussaina!, hajia hussaina!! me nake shirin ji a bakin ki?, wannan sakarcin ne har cikin bainar jama'a?" muryar daddy ce suka jiyo da dirowarsa kenan ya samu labarin suna asibiti shine ya biyo baya, cike da b'acin ran abunda yaji mom na fad'a yake kallonta tare da narka mata harar mai tsanin nuna b'acin rai. Da sauri dr ya mik'a masa hannu yana fad'in

"U're welcm sir"

"Thank you dr jamil ya aiki?"

"Alhamdulillah how was the journey"

"Fine and good wallahi Dr isowata kenan yara ke fad'a mun my son is at hospital"

"Eh yanzu na keji ga hajia har nake tambayar don me ba'a kirani nazo gida ba, saboda tun d'azu ina gida yanzun nan na shigo urgently duba wata patient tawa"

"Nima da aka fad'amun haka nace why not daba akiraka ba"

Kallon mom dady yayi ta wani d'aure fuska had'e da kauda Kai gefe kafin ya maida kallonsa ga Ummi, Murmushi tayi tare da cewa,

"Sannu da hanya, an iso lafiya?"

"Lafiya lau hajia Aisha ya gidan?"

Wani murmushin ta sake sakar masa kafin tace.

"Gida kam yanzu ba dad'i tunda babana ba lafiya Amma kasan cewarka a nan yanzu nasan insha Allah komai zai dai-daita"

Wani mugun tsaki mom taja tabar wajen a hasale, Girgiza kai dady yayi sannan ya shiga room d'in da aka kwantar da Mahmud wanda ganin mom ta shiga ciki ya tabbatar masa da hakan, ita Ummi da dr sukabi bayansa.

Bayan an sallami Mahmud sun koma gida, da safe yana zaune ya jingina da jikin gadonsa cike da farin cikin dawowar mahaifinsa yace,

"Mom dama jiya daddy zai dawo shine baki fad'a mun ba" tab'e baki tayi had'e da mik'a masa cup d'in tea data gama had'a masa tana cewa,

"Ya za'a yi na sani bacin munafurci ya hana a sanar mani nima, tsabar rainin hankali ma dadyn naka kama wayoyinsa yayi yasa rufe tun shekaran jiya nake trying nasa ban samu bs ashe yasan me ya shirya tunda a wancan part d'in zai sauka..."


"Haba mom!, haba mom!!...yanzu dadyn ne kike cewa ya munafucceki bacin kinsan duk abunda zai yi agidansa baya nuna ban-banci, to wlh ni kaina saida na tambayi Ummi yaushe zai dawo, the same thing itama haka ta fad'a mani cewa bata sani ba don bata samun wayoyinsa idan ta kira, mom to meye ribar dady da Ummi idan sun b'oye maki wani abun? pls mom don Allah kidena irin wannan abun bai dace ba"

"Oho dai suma suka san dalilinsu ni idan ma ancuceni nida yarana wlh Allah ba zan yafe ba"

Shiru mahmud yayi yana kallon mom idanunsa cike da k'walla ya kasa ce mata komai, tunowa da kalaman likita ya sata sakin Murmushi tare da cewa.


"Sorry yayan B3 nadena dama da wasa nake yi maka"

Turo k'ofar d'akinsa da sukaji anyi yasa Mahmud ya kasa bawa mom amsa, Bilkisu ce ta shigo bakinta d'auke da sallama hannunta da k'aton tire da abinci ummi ta aikota ta kawowa mahmud d'in.

"Mom ina kwana, ya Mahmud ina kwana, sannu ya jiki, gashi ummi tace akawo maka tana gaisheka"

Billy ta fad'a tana kallonsa, Dariya Mahmud yayi sannan ya ce

"Washhh...billy jepanis wannan surutu Mai had'e da tambayoyi to wace kike son na fara amsawa daga ciki?" saida ta turo baki jin sunan da yayi mata amfani wajan yi mata magana sannan ta duk'a da niyar ajiye tiren abincin mom da tund'azu ta cika tayi fam tasa hannu ya buge tiren duk abincin ya watse a k'asa ita kuma Billy ya b'ata mata jiki.

"Uban waye ya kawoki d'akin nan, anfad'a mata cewa bana iya kula da d'ana ne da har zata wani dafo wannan k'azamin girkin nata ta kawowa d'ana? maza kibar d'akin nan kafin nab'ata maki rai da wasu shegun idanuwanki kamar k'wayar gero!"

Da sauri mahmud ya taso ya rik'e hannun Bilkisu tare da cire rigar jikinsa yana goge mata kayanta inda abinci ya zubar mata bayan ya gama ya duk'a ya tattaro abincin daya zube a plate sannan ya koma kan gado yasa hannu ya fara ci, sai da yayi kusan loma uku sannan ya d'ago kai yana Murmushi ya cewa billy.

"Sister kicewa Ummi na gode kuma abincin yayi dad'i sosai"

Kad'a masa kai tayi sannan ta duk'a da nufin gyara wajen yace

"Sister jeki zansa a gyara wajen"

Jiki ba k'wari tabar d'akin yanzu kam inda sabo tafara sabawa da abubuwan da mom keyi mata, tana fita taci karo da Bilal zai shiga d'akin da sauri ta rik'o hannunsa,

"Bilal karka shiga mom na ciki" duk'owa tayi tana gwada masa yanda jikinta ya b'aci "kagani daga shiga in kaiwa yaya abinci shine ta kifar da abincin k'..."

Rufemata baki yayi tare da cewa

"Aunty Billy kidena fad'a Ummi tace mudinga hak'uri idan anyi mana wani abun tunda 'yan uwan mune"

"Shikenan Bilal yanzu duk abunda aka yi mana hak'uri zamu yi tayi babu wanda zamu fad'awa? Ai wannan basu suka yi ba mom ce tayi"

"Aunty ai itama mom 'yar uwar muce tunda mom tace k'anwar tace"

Rungumesa tayi "Bilal kai yaro ne k'arami amma kana da fahimtar da nikaina bani da ita" bata ankara ba taji ya hura mata iska a kunne ya ruga aguje yana dariya, binsa itama tayi aguje tana dariya don izuwa yanzu ta fahimci ko meyasa yake yi mata haka,

A b'angaren mahmud kuwa Billy na fita ya kirawo wayar Basmah.

"Hello yaya mahmud ya jiki?" ba tare da ya amsa mata ba yace.

"Kizo d'akina yanzu" sannan ya kashe wayarsa, kallon mom yayi yace


"Mom for Godness sake me yasa kika zubar da abincin da Ummi ta aiko min dashi?"

"Saboda bana so kaci kuma ka watsan kasa a ido, waya san ko meta saka maka a ciki don ta kashe ka tunda bata son ganin 'ya'yana a raye"

"Kamar ya kenan mom?, kinsan adadin ko sau nawa inacin abincinta? Idan Ummi na son kashe maki 'ya'ya da tun-tuni muna yara zata kashemu, ko kin manta lokacin da kukaje egypt da daddy kika barta mu a hannunta har na tsawon shekara d'aya, meyasa lokacin bata kashemu ba sai yanzu da muka girma, duk da bawani wayo ne dani ba, bana manta wahalar da tayi da basmah lokacin ko shekara biyu bata yi ba a duniya, ko kad'an bata barin Ummi bacci da tsohon cikin Billy haka Ummi ke goyon Basmah abayanta idan tana rigima har sai tayi bacci me yasa bata kashe mu ba sai yanzu....? pls mom ko ba zaki so Ummi ba Atleast ya kamata kiso yaranta kamar yanda take son mu"

Wata muguwar harara mom tayi masa had'e da maka masa pillow ajiki..

"Rufemin baki shanyayye ai gashinan garin kwad'ayinka an shanyeka zaka dameni da wani tsohon labari, bari in fad'a maka over my died body bana son Aisha da yaranta Don haka kaima tun wuri kasama ranka haka, dole ne karabu dasu don bana son tarayyarka dasu ko kad'an" sannan ta fice daga d'akin tana cigaba da masifa, dariya Mahmud yayi

"Mom kenan ikon Allah!, kinsan gaskiya Amma bakyaso a fad'a, to nidai bansan ya za'a yi na rabu dasu ba don su d'in 'YAN UWANA NE na jini!"

Mom nafita taci karo da Basmah ko kallonta bata tsaya yiba saboda masifar da take yi ta wuce abinta, binta da kallo Basmah tayi had'e da tura k'ofar d'akin ba tare da tayi sallama ba

"yaya me aka yiwa mom naga ta fita tana masifa kamar irin rikitaccin tsofaffin nan?"

"Stupid koma kiyo sallama kafin na tashi na b'abb'allaki a gurin nan"

"Oh! yaya Allah ya baka hak'uri daga tambaya"

Komawa tayi tayo sallama ya amsa sannan yace ta shigo

"Yawwa Basmah maza ki harhad'a kayan nan dake k'asa kishare abincin kiyi moping wurin sannan kishiga toilet d'ina ki wanko kwanonin Ina jiranki"

"To yaya amma waye yayi b'arin abincin?"

"Basmahhhh...! nifa shine yake had'ani dake wato yawan tambayar da kuma Shan batu, to mommy ce ta zubar da abincin shikenan?"

Had'e rai Basmah tayi don Ita bata son fad'a arayuwarta balle gwasalewa, aikin ta farayi tana qunquni har ta kammala.

"Yaya Nagama ga kwanonin"

"OK thank you Basmah ajiye munsu akan bedside zuwa anjima na kaisu"

"Yaya Mahmud kwanonin waye?"

"Na ummi ne" wani irin takaicin wanke su taji yataso mata aria, murmushin mugunta tayi kafin tace.

"Bari na kai mata tunda ba kada lafiya"

"Ok sister say a big thanks to her"

Jiki na rawa Basmah ta nufi part d'in Ummi tana qiyasta rashin mutunci da zata yi idan taje ciki....


_SORRY FOR THE LATE UPDATE, AM TOO BUSYπŸ‘ yanzu ma nayi manage ne don d'ai naga cewa na faranta maku saboda zab'en da ake yi😍_





Mr's huss@in✍🏻

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NANE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____6πŸ’Ž


'Tana isowa part d'in Ummi ta tadda Bilkisu da Bilal suna wasan 'yar b'uya Billy ta d'aure masa idanunsa, garin ya lalabota saiga Basmah takawo kai ai kuwa ya rik'eta hannu biyu-biyu yana ihu yana fad'in.

"Yeeeeee...Aunty Billy na kamoki wallahi, no cheating bud'emun idona"

Speechless Basmah tazama tana kallon Bilal dake kulle da idanuwa duk yabi ya cukurkud'e mata doguwar rigar dake jikinta, muryarsa ta jiyo yana kuma cewa.

"Please Aunty Billy karki ce ba hakan bane Allah na kamaki kicire mun k'yallennan a fuskata"

Cikin jin haushi ta ajiye trey d'in kayan dake hannunta ta cire masa k'yallen, d'ago kan da zai yi ta d'aukesa da mari had'e da turesa ya fad'i k'asa,

Wata irin muguwar k'ara yayi da tasa Billy fitowa daga inda ta b'uya da gudu ta k'araso wajen ta d'aga Bilal tana kallon basmah.

"Haba yayya Basmah wannan wane irin d'aukar alhaki ne?, meye ribarki cikin cutar da d'an uwanki kuma jikinki?, Allah fa bazai barki ba idan kina hakan!"

"OK Billy nuna mun d'an uwan kine kinji, kinga saiki rama masa ko?"

Kuka Bilal keyi jikinsa na rawa yace,

"Sorry yayya Basmah bansan ke bace, na zata aunty Billy ce shi yasa nayi maki haka"

"Rufemun baki munafukin yaro kawai Billyn ce ta kai girmana in ba iskanci irin naka ba" ta sake d'aga hannu zata kai masa duka da sauri Billy ta rik'e hannunta,

"A'a yayya Basmah gaskiya ba zaki sake dukan saba ai wannan cin zali ne, yaro bai yi maki komai ba kin maresa, ba tare da kinji tausayin saba kika hankad'esa ya fad'i, amatsayinki na 'yar uwarsa ko tsoro bakya yi ya ji ciwo, shine duk bai isheki ba kike nema ki k'ara dukansa, a gaskiya bazai yuyuba is enough."

Sake d'ago d'ayan hannunta tayi da nufin marin Billy tana fad'in,

"To bari na nuna maki koke baki wuce in duke kiba da mari ba balle kuma shi"

"Kul..karki kuskura kifara...!"

Muryar Ummi ce suka jiyo dake tsaye abakin k'ofar shiga Parlourn tun lokacin da taji kukan Bilal ta fito tana kallon abunda kefaruwa, a hankali ta k'araso wajen ta cire hannun Billy data rik'e hannun Basmah sannan tace

"Bilkisu me yasa zaki yiwa auntynki rashin kunya? Oyah say srry to her"

"Ummi ita fa..."

"Kibata hak'uri nace"

"Yayya Basmah kiyi hak'uri"

"Good maza kushiga daga ciki Ummi ta fad'a"

Bayan sun wuce Ummi ta kalli Basmah da sai faman kumburar baki take yi ta rik'o hannunta.

"Basmah don Allah kidena biyewa yarannan kuna sa'insa dasu, kece babba akansu kamata yayi ace kina behaving very matured ba wai ace komai kid'aga hannu kice zaki yi duka ba, kinsan yau da gobe sai Allah shaid'an zai iya sa watarana surama duk da bana fatan hakan ya faru tsakaninki da k'annanki!"

Da k'arfi Basmah ta k'wace hannunta daga rikon da Ummi tayi mata tabi takan trey d'in kayan abincin da tazo dasu aguje tana kuka suka tarwatse treyn ya fashe.

Murmushin k'arfin hali Ummi tayi cike da mamakin Basmah had'e da cewa.

"Allah ya sawak'e miki!"

Aguje Basmah ta shiga wajen mom tana kuka, nan take shirya k'arya da gaskiya ta fad'a mata, ana haka sai ga daddy ya shigo, ko gaisuwa babu mom ta fara zuba masifa tana sheda masa abunda Basmah tazo ta fad'a mata.

"To wallahi alhaji nagaji da wannan nuna banbanci da ake yimun cikin gidan nan, yanzu kenan babu dama Basmah ta hukunta yaran nan idan suka yi mata laifi sai Aisha tasa baki don tanuna cewa 'ya'yan tane, wai har da cewa idan Basmah ta dokesu surama suma!"

Shiru dady yayi yana nazarin maganganun ta kafin yace.

"Zanyi bincike, amma ke Basmah kin tabbatar da haka aka yi? don idan naji ba haka bane to saina sab'a maki saboda bazan lamunci shashanci agidana ba"

Nan Basmah ta fara fik'i-fik'i da idanuwa saboda tasan kwanan zancen, ko kad'an dady baya lamuncewa ayi masa shashanci, dady naganin haka yayi tsaki had'e da cewa mom

"Kin gani ko, bansan me yasa kike d'aukar k'ananan maganganun yaran nan ba kina bari suna tasiri azuciyarki ba, tazo ta shirya maki k'arya kin kama kin haye, to yanzu meye amfanin wannan? daga yau karki sake zomani da irin wud'an nan maganganun idanko ba haka ba saina mugun sab'a maki"

Haba!, mom najin haka masifar tak'aru kamar an zubawa wuta fetur tana cewa,

"Dole kafad'i haka mana tunda Aisha da 'ya'yanta sune 'yan gata, to tunda kace haka ka raba d'aya biyu ka nuna kafi sonta akanmu to wlh saina tabbatar maka d'auki matakin da sai dai ran kowa yab'aci a gidan nan, Acuci yarinya sannan kazo kabud'e mata ido don karka b'atawa 'yan gwal rai"

mtssss dady yayi tsaki sannan yafice daga d'akin ya barta tana cigaba da surfa masifar ta.


_Dukkanin k'orafinku ya iso a kunnuwana AKAN rashin samun update d'ina har na tsawon kwana biyu ina mai baku hak'uri akan haka, Amma ina so kusani banyi alkawarin yin update kullum ba saboda inada abubuwan yi agabana, just dt ina iya k'ok'arinane naga nayi abunda zai faranta raina da kuma naku, saboda haka masoyana kuyimun uzuri a duk lokacin da kukaji shiru nagode πŸ‘LUV YOU ALL❀_






Mr's huss@in✍🏻

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____7πŸ’Ž


Part d'in Ummi dady ya nufa ransa duk ab'ace, ya rasa wace irin rayuwace mom take son ake yi a cikin gidan sa, ita ko kad'an bata fahimtar me ake cewa kishi da kishiya ta yiwa kalmomin mummunar fahimta ta yanda ba zata tab'a barin a zauna lafiya ba a cikin gidan. Har ya iso cikin falon Ummi yana wannan tunanin, Bilal ne ya rugo da gudu yana fad'in,

"Oyoyo dady" Cabesa dady yayi tare da kissing forehead d'insa shima yana cewa,

"Oyoyo my Bilal kana lpy?"

Kai ya d'aga masa yana wasa da buttle d'in jallabiyarsa. Ummi kuwa dake cikin bedroom fitowarta wanka kenan ta jiyo muryar dady, agurguje ta shirya sannan ta bud'e bedside fridge d'inta ta d'auko gorar ruwan faro mai sanyi tare da cup ta nufo parlon fuskarta d'auke da murmushi, Bilal na ganin Ummi ta shigo ya sauka daga jikin dady tare da barin parlon aguje yana k'walawa Billy kira.

"Aunty Billy, aunty Billy kizo ga daddy"

Wani irin lafiyayyen murmushi dady yayi ganin Ummi ta nufo inda yake fuskarta d'auke da murmushin da ako yaushe ke haskaka masa zuciya,

A hankali ya bud'e mata hannayensa ta yiwa kanta mazauni bisa ki'rjinsa shi kuma ya zagaye hannayensa abayanta, a lokaci guda suka lumshe idanuwansu suna jin wani sanyi da natsuwa na saukar masu acikin zuciya, sun jima a haka kafin can suyi breaking hugging d'in da suka yiwa juna, ruwan Ummi ta tsiyaya masa a cup sannan ta mik'a masa cike da girmamawa, karb'a yayi tare da had'owa da hannunta ya kai ruwan abakinsa yana sha yana kallonta a hankali har ruwan ya k'are. Ajiye cup d'in tayi tare da cewa.

"Barka da rana dadyn su B, ya gajiyar hanya?"

"Yawwa Rabba'atul baiti, gajiya takau tunda gani ga iyalina, Abu mafi burgewa na same su cikin k'oshin lafiya sai dai kash...da alama ko tunanina basa yi tunda kowacensu hankalinsu kwance yake kunyi wani fresh daku..!"

Da sauri Ummi d'ora yatsansa akan lips d'inta tace,

"Babu bukatar canzawar zuciyar dake samun kyakkyawar kulawa ga wanda ya ajiyeta, jarumtar da kake da ita wajen bamu kula da cire mana kewar rashinka atare damu bazata tab'a barin tunani yayi tasiri akan mu ba balle har yasa mucanza daga yanayin da kake k'ok'arin son ganin mu akoda yaushe, Idan kuwa hakan tafaru to tabbas rashin adalci da godewa jaruminmu ya tabbata akan mu"

"Rabba'atul baiti kenan! Bakya gajiya da kiran jarumtaka ga jaruminnan da ya kasa daidaita gidansa, Shin bakya tsoron ace wata rana ya samu rauni agabanki!?"

"Ko kad'an bata haufi akan haka idan kuma har ta faru zanyiwa jarumin nan nawa uzuri, in d'auka cewa Allah ya jarabce sane ko kuwa nice nakasa wajen iya wasashi shi yasa hakan ta faru bawai don ya gaza ba"

Murmushin jin dad'i dady yayi tare da yiwa Allah godiya daya mallaka masa Aisha a matsayin matarsa

"Tsarki ya tabbata ga ubangijin daya mallaka mani ma'abocin fitar da kyakkyawan murmushi a fuskarsa, dukkanin murmushin da zaka yi yakan k'ara mini k'warin guiwa da kuma dalilan da zasu k'ara mani sonka da k'aunar ka tare da zama a cikin gidan ka cikin ko wane irin yanayi"

Yayi murmushi tare da cewa "Idan ko haka ne zan kasance mai k'ara yalwar murmushi na don intabbatar kin soni fiye da adadin numfashinki da nawa"

Sosai dady ya samu natsuwa da farin cikin da suka nemi kwace masa a part d'in mom, fira take yi masa wacce kesa idan har zai iya mantawa da kansa saboda tsananin dad'inta to tabbas zai manta dashi,

Billy ce ta shigo bayan ta biye da Bilal aguje yana dariya ya yi saurin b'uya bayan dady, Billy naganin dady tayi tsaye cak had'e da duk'ar da kai k'asa,

"Dady ina wuni"

"Lpy klw Bilkisu ya aka yi naga kin biyo k'anin naki ko laifi yayi ne?"

"Eh dady wai cemun yayi..." Bilal na dariya ya katseta yana fad'in.

"Dady wai don d'ai nace mata Billy Japanese yanda yaya mahmud kecewa shinefa take son dukana"

Gaba d'aya dady da Ummi sukasa dariya,

"Haba Bilkisu d'an wannan abun shine ya kai ayi duka akansa...Bilal yama ake cewa.. Billy Japanese ko?" kukan shagwab'a ta fara yi tana bubbuga k'afa, A hankali ummi ta zagayo bayan dady ta damk'o hannun Bilal tana cewa.

"Zo gashi Bilkisu narik'e makishi tunda dadynku yayi siding d'insa"

"Wayyo ammi ki cikani da zafi zata yimun"

"Ban fad'a maka kadena cemata haka ba? Yau saika gane kuskurenka tunda bakaji"

"Ummi da wasa fa nake yi mata ko aunty Billy na?"

Saida ta hararesa sannan tace

"Eh Ummi, amma kice kar ya sake"

"Aww ni zaki bawa kunya? Shikenan zaki sameni ne"

Dariya suka yi harda daddy dake kallon su, abinda sam yaran Mom basa yi wato wasa da dariya ga junansu sai dai son girma kamar su suka yi kansu....


*Assalamu alaikum 'yan

Please Login or Register in order to submit comment