Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a matsayinka na k'anena kakira matata awaya ka zazzageta bisa wani dalili da baka da tabbas akansa, meyasa zaka aikata haka, ai kamata yayi ace koba komai taci albarkacin ina yayanka awajena, amma duk da haka karuntse idanuwa kaci mutuncinta, hak'ik'a da wani mutumne awaje ya aikatawa iyalina haka to tabbas sai nayi shari'a dashi, yanzu kuwa dole inyi hak'uri kasancewar kai d'an uwana ne, amma kafinn nan Ina shawartarka da kada kasake aikata haka domin cin zarafine da cutarwa ga bayin Allah, kumashi Allah kasan baya yafe hakk'in wani tun aduniya balle lahira, Aisha da kake gani macece mai matuk'ar hak'uri da juriya, kullum batada burin da yafi ta sakani cikin farinciki tare da kwantarmun da hankali, duk abunda nake so shi takeyi, wanda kuma bana so baza tab'a yin shiba taya kake tunanin irin wannan mace zanso a muzantata ko awalak'antata agabana kuma inyarda, shin ashe irin wannan mace bata cancanci ace angujewa damuwar taba? Ina son matata kamar yanda nake sonku sosai shiyasa bana tunanin zan iya rabuwa da ita komai rintsi komai wuya, nadad'a maku gaskiyar kowaye ita don Allah kucire tunanin cewa ta asirceni domin yin hakan kuskurene" alhaji bukar ne yadafa kafad'arsa alamun ban hak'uri kafin baba k'arami yace

"Don Allah yaya kayi hak'uri, kema hajia Aisha kiyi hak'uri, tabbas bai kyutaba abunda na aikata wanda nadamar haka takawoni wajenki don innemi yafiyarki, koma meye yariga yafaru kuma nayarda nayi kuskure don Allah muyafi juna" kanta na duk'e ak'asa tace

"Babu komai kuma komi yawuce, koba komai kuma tamkar 'YAN UWANA NE tunda na auri d'an uwanku don haka nayafemaku kuma kuyafemun, Allah yabamu ikon hak'uri da junanmu" gaba d'aya suka amsa da amin cike da kunyarta, dady kuwa jiyayi k'aunarta na sake lillinkuwa acikin zuciyarsa yana jin kansa amatsayin wanda yafi kowa sa'ar mata aduniya, lumahe idanuwansa yayi Yana kallonta tare da sauke wata irin ajiyar zuciya kafin yace

"Nagode maki sosai da kika d'auki 'yan uwana amatsayin auma 'yan uwanki kuma kika yafe masu, ubangiji Allah yayi maki albarka" amsawa tayi ciki ciki had'e da mik'ewa tabar wajen tana murmushi, part d'inta tanufa tanaji gaba d'aya zuciyarta tayi fresh batada wata sauran damuwa aranta tunda Allah ya daidaita tsakaninta da mijinta, abokiyar zamanta, dangin mijinta, 'ya'yan mijinta yanzu batada wata matsala.

Abangaren dady ma tana fita suka yanke shawarar za'a maye gurbin da Basmah tasamu nakaratu da sunan Bilkisu dama tuni itama zainab 'yar gidan alhaji bukar dady yasa itama ansamo mata admission zasu fara zuwa tare next week, Billy kam gaba d'aya yanzu tazama 'yar gatan kowa mafi yawancin lokutama apart d'in mom take kwana shi kuma Bassam da Bilal awajen Ummi har mom nayimata sherida tazama uwar maza,

Hakama Basmah duk da mahmud nayawan jin soyayyar Billy na motsa masa azuciya hakan bai hana yabata kula sosai ba, tasamu sauk'i k'warai da gaske gashi koda yaushe sai k'ara murmurewa takeyi tana fresh saboda yanda tasaki jiki sosai, hakan yasa yau yaya Mahmud ya quduri aniyar karb'ar hakkinsa amatsayin matarsa, Yana dawowa daga gidansu yabiya ya sawo kazar amarcinsa guda biyu tare da madarar hollandian yabiyo dasu, kwance ya iskota tana kallon wani tsohon season film my lover my wife, tanajin shigowarsa tamik'e tare da tarbosa tana fad'in

"Sannu da dawowa yaya"

"Yawwa 'yar gidan Ummatah" turo baki tayi had'e da cewa "Ummanka dai ko Ummatah"

"Ummanki Ummatah, shikenan?"

Ledojin ya mik'a mata tare da wucewa kitchen ya d'auko tray da cups yazube masu aciki, hannunta ya rik'o bayan ya zauna k'asa tare da d'orata akan cinyarsa, duk da yasaba yimata irin wud'annan abubuwan sai taji yau abun yasha banban dana kullum, ahankali yadinga yagar naman Yana bata abaki har saida taci tak'oshi sannan shima yaci, ita dai gaba d'aya hankalinta na akan film d'in da take kallo batasa komai aranta ba, kwashe kayan yayi yakai kitchen sannan yadawo ya zauna kusa gareta tare da jawota ajikinsa yana fad'in

"'yar gidan Ummah meye sunan wannan film d'in da naga tunjiya kike faman kallonsa" ahankali ta motsa bakinta har lokacin idanuwanta na akan tv tace

"My lover, my wife" shiru yayi Yana tunanin kalmar wai my lover, my wife, ya maimaita azuciyarsa sai yaji tamkar don shi akayi kalmar. Murmushi yayi tare da cewa

"K'adarallahu wama sha'a fa'ala"

Ganin gaba d'aya hankalinta na akan tv yasa ya tashi yaje yakashe tvn sannanya kashe wutar palourn, bubbuga k'afa tafarayi tana kukan shagwab'a had'e da cewa

"Kai yaya, kai yaya! Pls don Allah ka kunna mun abuna in kallah" cikin wata irin kasalalliyar murya yace

"Basmah darefa nayi kizo muje mukwanta gobekya iyar kinjiko" k'yalesa tayi tana turo baki duk da cikin duhune amma hakan bai hana yagani ba saboda d'an hasken wutar bedroom d'in daya zo nan"

Ta gefenta yabi zai wuce tasake bubbuga k'afafuwanta kamar zatayi kuka, dawowa yayi tabaya yana kallonta sannan ya d'auketa chak ya shige da ita ciki yana bata hak'uri, tare suka shiga toilet sukayo brush sannan suka dawo suka kwanta abunsu bayan ya kashe masu wuta had'e daja masu bargo, ahankali yafara matsowa kusa gareta yana shasshafa jikinta, ai nan take jikin Basmah yad'au rawa saboda sai yanzu tafahimci cewa suk wanda yaci ladar kuturu to dole zaiyi masa aski, tsorone yakamata sosai inda take tunanin kamar bazata iya bashi kan taba amma awani gefen zuciyarta bataso tayi masa haka don iya adalci yayi matashi, kimanin wata d'aya kenan da aurensu suna kwana agida d'aya, d'aki d'aya, kuma a gado d'aya amma saboda yanayin da take ciki bai tab'a neman hakkin saba awajenta sai yau don me zata hanasa, runtse idanuwa tayi tanajin yanda yake aika mata da sak'wanninsa masu wahalar karb'a awajenta, ai batasan lokacin data tafashe masa da kukaba, duk da yayi nisa bayajin kira hakan bai hana yasaurara mata ba yana tambayarta idan bata buk'atar hakan zaiyi hak'uri, jin tayi shiru yasa yaci gaba da abubuwansa cikin natsuwa da kwanciyar hankali saboda tunawa da abunda likita yace tare da lallab'ata, Ina ganin haka nikam nace

_Sai da safe k'awata Basmah Allah ya sanya alkhairi, yasa pilot yayi sa'ar jefa k'wallo aragartayanda yakamata😃🙈_



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Gaisuwa tare da fatar alkhairi agareki MY NOURI *UMMU MEENAL* 💋❤, bak'ina bazai iya fad'ar iya adadin alfahari da kuma farincikin da nakeyi ba, saboda samunki acikin rayuwata, mutane kance soyayya had'uwar jini ce amma tamu ta shallake haka saidai nace had'uwar ruhikan muce, domin kulawarki da soyayyarki agareni is always beyond my expectation, ba abunda zance dake illa Allah ya saukeki lafiya kuma yabamu healthy babies rayayyu masu albarka, haka kuma ina yimaki fatan Allah yasoki soyayya mai tsanani fiye da lullunkawar wacce kike yimun kuma yabaki aljannah da rahamarsa👏🏻 *HAPPY JUM@T TO U, LUV U SO MUCH*_


💎Page_____94💎


Cike wani irin salo mai rikitarwa da wuyar d'auka Mahmud ya dinga sarrafa Basmah cikin kulawa da kuma tausayawa har yasamu cimma burinsa, duk da yatsinci kansa awani yanayi na daban dabai tab'a tsintar kansa acikiba hakan bai hanasa yin komai cikin natsuwa ba, har ya samu gamsuwa batare daya cutar da itaba,

Basmah kam taci kuka kamar ba gobe wanda yasa har saida zazzab'i yasoma rufeta, tashi yayi had'e da shiga toilet ya tsarkake jikinsa sannan yadawo ya jawota ajikinsa yana rarrashi, addua yayi mata sosai cikin ransa tare da tawassali da albarkacin darajarta data kawo masa har gida, Allah yabata lafiya kuma ya yaye mata wannan ciwo dake damunta, Sosai yaji wata irin kima da darajarta sun k'aru azuciyarsa, duk da ko har yanzu baya jin soyayyarta acikin zuciyarsa amma yabata wani matsayi namusamman aciki.

Koda aka kira sallar asuba tashi yayi yasake tsarkakikke jikinsa sannan ya sauya kayansa, yana k'ok'arin tayar da ita yaji antada sallah a masallaci don dama sun makara, hakan yasa yaga bari yabarta har sai yadawo masallaci sai ya taimaka mata tagyaro jikinta tayi sallah

Yana fita ta tashi tana faman cije baki saboda yanayi da rad'ad'in zafi da take jinta aciki, samu tayi ta mik'e ta lallab'a tashiga bayi, ruwa masu zafin gaske dake cikin flaks ta surka a bahon wanka sannan tashiga ciki, duk da tanajin yanda suke d'an qunarta haka ta daure tajima sosai aciki tana gasa jikinta, cikin mintuna da basu wuce biyar ba bacci ya sake d'auketa tana cikin bahon wankan saboda dad'in ruwan da takeji suna ratsata ajikinta,

Shi kuma ana sallame sallah ko addua'a bai tsaya yiba saboda hankalinsa nawajenta yabaro masallacin, yana shigowa yaga bata bisa gadon da sauri ya bud'e toilet d'in ya hangota cikin bahon wankan, hakan yasa ya rufo mata k'ofar yadawo yacire bedsheet d'in ya aza wani sannan yaciro mata wata doguwar riga marar nauyi da hijab ya d'ora mata akan gadon, zaman jiran fitowarta yayi har nakusan minti biyar amma yaji shiru, hakan yasa yakoma tashi yatura gambun k'ofar toilet d'in, hangota yayi cikin bahon wankan bacci ya d'auketa wanda sai alokacin ne yalura da haka, tsaye yayi yana k'are mata kallo kafin ya cire jalabiyar jikinsa ya ajiye gefe sannan yasa hannu ya danna inda ruwan zasu zuk'e sufita tacan k'asa don har sun soma hucewa, hakan da yayi yasa tafarka daga daddad'an baccin daya d'auketa tana ganinsa a a gabanta cikin sauri da jin kunya tashiga kakkare jikinta idanuwanta na k'ok'arin kawo k'walla, basar da ita yayi yasake had'a mata wasu ruwan masu d'umi sannan ya taimaka mata tayi wankan tare da tsarkake jikinta sannan yaciro mata towel d'in dake sagale ya d'aura mata,

Rik'ota yayi tana takowa ahankali har suka fito ya zaunar da ita bakin gado sannan ya shimfid'a mata abun sallah, rigar yafara samata sannan yasa mata hijab had'e da cewa

"Basmah kidaure kiyi sallah saiki koma ki kwanta kinji" d'aga masa kanta dake k'asa tayi sannan yarik'ata ta tashi tsaye yana fad'in "ko azaune zakiyi bazaki iyaba atsaye" tare da k'ok'arin zaunar da ita, girgiza masa kai tayi ta tada sallar sannan shi kuma ya wuce kitchen ya kunna gas ya d'ora ruwan zafi akai, cikin minti uku sukayi daidai zafin da yake buk'ata ya sauke tare da juyewa cikin cup bayan ya kashe gas d'in ya had'a mata tea mai kabrin gaske, koda ya shiga har ta dad'e da gama sallar ta kwantar da kanta abakin gado, lallab'ata yayi yasamu tashanye ruwan tea n tsaf sannan yad'ibo PCM dake cikin bedside wardrobe yabata tasha saboda yanda yaji jikinta nata yayi zafi, rik'ota yayi takoma saman gadon takwanta sanan shima ya zagayo tabayanta ya kwanta tare da rungumeta sosai ajikinsa yaja masu bargo,

Billy kam tuni sun fara wuce makaranta A.B.U zaria ita da Zainab yayinda take karatunta fannin medicine ita kuma Zainab faculty of science, sosai take samun kulawar 'yan uwa takowa ne gefe saboda yanda ta zame masu zakaran gwajin dabi, kowa na son Billy saboda hakurinta da kaifin hankalinta, hakama kafin tawuce makaranta saida tarok'i dady daya barta taje borno wajen Umma daga nan kuma tagano 'yar uwarta, ganin idan ya hanata bazata ji dad'i ba yasa ranar Saturday yace da ita dasu mom duk su shirya aje borno kwana d'aya adubo Basmah da jiki wanda hakan ba k'aramin dad'i yayi masu ba, nan suka hau shiri mom ko kunya babu tana shire shire zataje dubo 'yar gaban goshinta Ummi nata yimata tsiya har sukaje lafiya kuma suka dawo lafiya, fad'ar irin dad'in da Basmah taji naganin iyayenta da 'yan uwanta ba'a magana, hakama Mahmud ganin Billynsa bakad'an ya tado masa da cutar soyayyarta da akoda yaushe ke mak'ale azuciyar saba, wanda hakan yasa tunda suka had'u so guda bai koma bari suka sake had'uwa ba har suka tafi, Basmah tafahimci hakan amma tabasar saboda tasan illar so kuma tasan dole haka zata faru,

Ummi kuwa tunda Billy tawuce makaranta zazzab'i ya soma rufeta, gaba d'aya bata iya aikin komai ga yawan bacci da rashin kuzari duk sunbi sun adda beta, da farko dai dady yayi tsammani kewar rashin Bilkisu atare da itace ta tab'ata, lura da ko sau d'aya bata tab'a rabuwa da itaba kamar irin wannan lokacin, ganin abun yak'i ci yak'i canyewa yau kimanin sati uku kenan yasa mom tarakata sukaje asibiti, tashin farko likita ya tabbatar ummi na d'auke da juna biyu na tsawon sati uku da kwana biyar, iya kunya ranar Ummi tajita duk da dai tana sha'awar haihuwar amma sai take ganin kamar yanzu tayi tsufa da yinta, sosai mom ta taya dady farinciki da murnar jin wannan labari har tana fad'in "Allah ya kawowa uwar maza 'yammace kota huta da tsokanar da nake yimata" dariya dady yayi had'e da rungume mom yace "Amin momyn yara tare dake" k'wace jikinta tayi taje inda Ummi ke kwance cike tarufe fuskarta tace

"Yaya Allah ya inganta kuma ya tsayar gareki da alkhairi, ai nikam daga Bassam d'an autana babu k'ari in sha Allah, haihuwa fa shidda alhaji! Ina laifi aiko ahaka Allah yatsayarmun alhamdulillah"

Bayan sun dawo gida kuwa haka Ummi tayita yiwa mom magiya akan don Allah kada tafad'awa kowa koda yaya Mahmud ne, wai ita ina zata da wannan abun kunya idan sukaji,

"Ikon Allah, Aikam dama kindena rok'ona, ai wannan abun farinciki ne koban fad'awa kowa ba dole su papi suji" mom tafad'a tana dariya, harararta Ummi tayi kafin tace

"Ai shikenan gaki ga waje, Allah ya mak'awa jaki k'ofo"

"A'a ba amin ba, Allah yabarshi ayanda yake, meye abun kunya ko tada hankali aciki, tunda ni nagama nawa tone d'in, yanzu ke nakine, iya naki d'aukar ciki da haihuwa indai renone bakida matsala kinada wacce zatayi maki"

"Hmmm ai renon ne da wahala yanzu saboda tarbiyar da zaka zaman d'ora yaro akai, kuma awannan zamani wazai zauna zaman yimaka reno tsakani da Allah bisa ingantacciyar tarbiya" murmushi mom tayi kafin tace

"Gani zanyi maki reno mana iya naki kiyita haifarwa nikuma ina tayaki reno kinga shikenan bakida wani tunanin mai reno agabanka"

"Hmm kedai kad'an ma mai albarka idan Allah yabani ina godiya, fatnmu dai Allah yaraya manasu kuma ya albarkacesu"

"Amin ya Allah umminsu kuma da zancenki gaskiya"

Tun tafiyarsu Ummi borno abubuwa gaba d'aya suka dawowa Mahmud sabbi, banda tunanin Billy da kallon fotunansu babu abunda yakeyi, hatta 'yar kulawar da yakeba Basmah tad'an ja baya wanda hakan yasa yakasa fahimtar yawan zazzab'in da take kwana dashi, tana sane da halin da yake ciki kuma ko kad'an bataji zafi ba ko ganin laifinsa, balle ta tayar da hankalinta, kullum addu'ar ta shine Allah yarage masa rad'ad'in da yakeji azuciya narabuwa da masoyiyarsa, yauma zaune suke yayi matashi da cinyoyinta suna kallo amma shi latsar wayarsa kawai yakeyi, gaba d'aya ya manta da Basmah na wajen ya dinga jawo hotunansa na buki da Billy yana kallo, tana kalle dashi amma sai tayi kamar bata san yanayi ba,

Ganin tayi gaba d'aya yayi marking d'insu zai goge tayi saurin rik'e masa hannu,

"Haba yaya meyasa zaka gogesu?" Sai alokacin yatuna cewa ashe tana wajan, jiyayi kunya tarufesa kuma gaba d'aya bai kyautaba da yayi hakan,

"Basmah! Ya salam, don Allah kiyi hak'uri, bansan lokacin da hakan yazomun ba, amma ina so kisani ko kad'an wlh banyi don in b'ata maki raiba, don Allah.." Kafin ya k'yar ta toshe masa baki tana murmushi had'e da cewa

"Babu buk'atar kayi mani rantsuwa mijina, nayarda dakai, bazan tab'a zarginka ko tuhumarka acikin zuciya taba, dolene kaji ba dad'i aranka don haka kada kasamu akan wai don kayi haka raina zai b'aci, ko kad'an banajin haka domin da kai da Billy duka 'YAN UWANA NE don haka ko soyayya bata tab'a gittawa tsakaninku ba, bazanji haushiba tunda nasan 'yan uwan juna kuke, kabar pics d'inku mana kuma ka kallesu aduk lokacin daka buk'ata matuk'ar hakan zaisa kaji sanyi azuciyarka, takaicina d'aya shine yanda nazama katangar da tahanaka kasancewa da abunda kake so, amma wlh ko d'aya bana d'aukar wannan abun da wata fuska, kuma kasa aranka akoda yaushe inyimaka kyakkyawan zato" tak'arasa maganar tana shafa kansa tare da yimasa kiss agoshi sannan yamaida hankalinta ga kallon da takeyi,

Jikinsa asan yaye yatashi had'e da juyo da fuskarta suna kallon juna yace

"Basmah infad'a maki wata magana?" Murmushi tayi had'e da kad'a masa kai yace

"Kinada wani girma da kima azuciyata da zan iya cewa ked'in tamusammance"

"Dagaske yaya?" Tafad'a tana k'ara fad'ad'a murmushin ta da har saida hak'oranta suka bayyana, hannuwa yasa yarik'o fuskarta sannan yace

"Ofcouse Basmah har cikin zuciyata ked'in ta musammance.." Rufe bakinsa keda wuya yakai hannunsa ga wuyanta yana tattab'awa saboda zafin da yaji jikinta yayi had'e da cewa

"Basmah lafiya kike kuwa?"

"Lpy klw amma kusan sati d'aya kenan inajin zazzab'i" tunawa da yayi tun bayan sati d'aya da kusantarta yalura da kamar tana fama da rashin kuzari kuma duk walwalarta taragu shiyasa duk yanda yakejin buk'atar ta yake hak'ura don bayason matsamata har ciwonta yatashi,

"Tashi tashi d'auko mayafinki muje asibiti!" yafad'a hankalinsa atashe,

"Kai yaya bawata matsala cefa ke damuna, ni lafiyata klw babu inda zanje, muna zuwa yanzune zasu sossokewa mutum jiki da alluran nan nasu, gaskiya nidai bazan jeba yaya" sake tab'a jikinta yayi tare da cewa

"Ai baki isaba, kina wasa da lafiyarki ko?, maza kije kid'auko hijab d'inki kafin nakira d'an uwa insanar dashi abunda kikace"

Turo baki tayi sannan taje tad'auko hijab d'inta tafito rik'e dashi ga hannu tana tuk'uburi, karb'e hijab d'in yayi ahannunta yana samata had'e da cewaf

"U're not serious Basmah, kin manta da abunda likita yafad'a makine har kike tunanin bazaki jeba" yana gama fad'ar haka ya d'auki makullan motarsa tare da kashe kayan kallon sannan yarik'o hannunta yajata suka tafi,

Tun akan hanya yakira dr dake dubata yasanar dashi gasunan tafe don Allah yayi maza yazo inbaya asibiti, cikin sa'a kuwa yace "sai sunzo yana nan" yana kashe wayar yajuyo yana kallonta ya dafe kansa tare da dukanta starring motar yace

"Kinga yanda ma kika kumbure ga wani haske kinyi? Mtsss Alla yasa ba jinine bakida ba" sake turo d'an bakinta tayi had'e da cewa

"Nifa nagaya maka lafiyata klw, kadena yimun jaye jayen ciyo"

Har zasu wuce tahango mai guiva tace

"Laa yaya hango guiva acan, don Allah ka tsaya kasiyamun zansha" harararta yayi don shi gaba d'aya hankalinsa yagama tashi inba wajen aikinsa yaje yajawowa yarinyar nan tashin ciwonta ba, tunda likita yace kada yabari tayi abunda zata wahala yasa har zuciyarta tadinga harbawa da sauri da sauri, nunata yayi da hannu kafin yace

"Ke ko?, wato inata lafiyarki amma ke tawani guiva kikeyi, to bazan siyaba" kad'a starring yadingayi da hannunsa yana fad'in "oh my God, ammafa komai ahankali naje dashi how come"

Ita kam da haushin rashin siya mata guiva yakamata fita batunsa tayi tajuyar da kanta gefe tana kallon titi harda 'yar k'wallarta a idanuwa,

Suna isa kallo d'aya dr. Yayi mata yace

"Ah..alhamdulillah, lallai madam tasamu sauk'i sosai, we have seen alot of progress"

"Haba dr kamarya, tafi sati biyufa tace tana fama da zazzab'i duk daren Allah, kuma dubi kaga yanda tayi wani haske kamar marar jini gashi duk ta kumbura, pls dr don Allah kayi mata checkup akan matsalarta kagani ko lafiya take, wlh inajin tsoro sosai"

Murmushi dr yayi kafin yayi mata 'yan tambayoyi tana bashi amsa sannan yakira wata nurse yace suje a d'ibi jininta da fitsari, kuma akawo masa result yanzu yanzu"

"Ok" tafad'a tare da cewa Basmah "muje ko?" Sannan tamik'e suka fita.

Kallon Mahmud yayi da duk yabi yatada hankalinsa yace

"Calm down my friend! your wife is ok in sha Allah, ba kumburine tayi ba kuma tanada jini don haka ka kwantar da hankalinka"

Bayan kamar minti ashirin sai gasu sun dawo nurse d'in biye da ita abaya, dr tamik'awa result d'in sannan tajuya tafita, d'ago kai dr yayi bayan yagama karanta takardar ya kalli Basmah had'e da tabbatar da zagin da yakeyi akanta sannan yaba Mahmud hannu suka gaisa yace

"Congrat malam Mahmud, ur wife is pregnant har na tsawon wata d'aya da kwana uku" wani dmmm yaya Mahmud yaji had'e da cewa dr

"Are you serious?"

"Yes confirmed" yamik'a masa takardar, karb'a yayi yana karantawa tare da yiwa Allah godiya, ita kuwa gaba d'aya farincikin dake kwance a fuskarta yabayyana, azuciyarta kuwa girmama ikon Allah takeyi daya yimata wannan baiwa da ni'ima alokaci d'aya, shikanshi Mahmud mamaki yakeyi ace sau d'aya abu har ciki ya shiga tabbas Allah shiyake tsara komai ayanda yaso, dama wannan rabonne dake tsakaninsu ya haifar da fasuwar aurensa da Billynsa? Godiya yayiwa likita sosai bayan yabasu 'yan shawarwari akan yanda zai kula da ita, da kuma yanda zasuyi renon cikin, Sannan suka bar asibitin kowa da abunda take sak'awa azuciyar.

Wajen mai guiva da tace yasiya mata d'azu ya tsaya ya saye gaba d'aya kwandon sannan suka nufi hanyar gida, tun amota yakira yaya Mahmud yayi masa albishir 'yar uwarsa na d'auke da ciki har na tsawon wata d'aya da kwana ukku,

"Allahu akbar, Allah sarki wato wannan dalilin shine yajawo rabuwarku da my sister" abunda yaya Mahmud yafad'a kenan kafin yafara taya d'an uwan nasa murna, sosai yayi farinciki da yimasu addu'a sannan yace yaba Basmah wayar, juyowa yayi yana kallon yanda ta daddage sai famin cin guivar ta takeyi hankali kwance yayi murmushi had'e da girgiza kai kafin yace masa

"Sorry d'an uwa she's too busy, yaron naku har yafara sanyata 'yan ciye ciye anjima mayi waya" yana gama fad'a masa ya katsiye wayar, murmushi yaya Mahmud yayi yana kallon screen d'in wayar kafin yafara kiran 'yan uwa da abokan arzik'i yana sanar masu da zancen, Bilkisu kad'ai yaji bayada courage d'in fad'awa wannan maganar don haka kawai ya tsinci kansa cikin jin kunyar tunkararta da ita,

Ummice da kanta takirata take sanar da ita zancen wanda tana zaune batasan lokacin data mik'e tsaye ba, ada tana kallon duk abunda yafaru amatsayin mafarki amma yanzu ta tabbatar da cewa gaskiyane, runtse idanunta tayi hawaye suka zubo mata a idanuwa kafin tashiga yiwa 'yar uwarta fatar alkhairi da kuma Allah ya sauketa lafiya, yau dai duk k'arfin zuciyar Ummi da kuma basar da al'amarin da takeyi saida ta tausayawa 'yarta don ta tabbatar da cewa kuka takeyi, rarrashinta tashigayi tare da cewa bai kamata ace tana bari shed'an na bijiro mata da wata dangantaka data tab'a faruwa tsakaninta da mijin 'yar uwar taba har yasa tana shiga damuwa tunda ita ta yankewa kanta wannan hukuncin da kanta, tayi hak'uri in sha Allah Allah zai dubi zuciyarta ya zab'a mata abunda yafi zama alkhairi agareta don haka ta manta da komai ta fuskanci karatunta.

Haka kuwa akayi nan take Billy taji komai yakwanta mata azuciya, kiran Basmah tayi da Mahmud pilot ta tayasu murna tare da fatar Allah ya inganta ya sauketa lafiya, gaba d'ayansu duk saida sukaji ba dad'i alokacin yayinda ita kuma cikin farinciki tare da jin dad'i ta tayasu murna badon wani abuba,

Duk wanda yaji labrin cikin Basmah cewa yake ashe rabone yahana aurensa da Bilkisu Wanda dama haka yake rabon wani na danne wani koma yasa arasa gaba d'aya.

Mahmud kuwa tuni ya lullunka kulawar da yakeba Basmah ada saboda samun cikakkiyar lafiyarta da ita har baby, ga Ummah da ko yaushe take tsaye wajen nemawa Basmah duk wani abun k'walame k'walame da zata nema, ko kad'an babu wata damuwa atare da ita tana samun kulawa takowane b'angare sosai kuma yanda yakamata, yaya Mahmud ma da Batoo da Billyl kusan kullum suna yimata kira fiye da uku don d'ai suji ya lafiyarta da kuma ta unborn d'insu,

Ita kuwa Billy ta tattara komai ta ajiye gefe amatsayin tarihin da bata son tunawa ta maida hankali ga karatunta duk da har yanzu ak'asan zuciyarta akwai zazzafar k'aunar yayanta aciki, tafe take tafito lecture itada k'awarta husnah kawai sukaga anyi parking da mota ta gabansu,

"Ke zo nan" sukaji wanda kecikin motar yafad'a, kallon kallo suka yiwa juna kafin Billy tayi yunk'urin rab'awa tagefen motar zata wucewa, da sauri husnah tarik'o hannunta had'e da cewa

"Don Allah Billy kirufa mana asiri, malam jika ne, kuma kinsan halinsa wlh mugune bayada mutunci, pls tunda kinga ya nace maki yana nema yahanaki shaqat acikin makarantar nan to kisauraresa kiji abunda zaice don Allah kinji?"

Juya idanuwanta gefe tayi had'e da cewa, "husnah wlh bana son kula kowa ayanzu, zuciyata tana buqatar hutu fiye da tunaninki, idan natsaya na sauraresa tamkar na cutar da kaina ne, wlh ahima yafiye nacin tsiyane, ace kimanin watana uku da

Please Login or Register in order to submit comment