Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aiki da wani kamfanin dake kula da zirga zirgar matafiya da 'yan kasuwa daga wata k'asar zuwa wata k'asar.

Cike da girmamawa hajia Hafsat suka gaisa da yayan nata dake d'auke da Junior yana fad'in

"Oyoyo marabanku mutanen borno, barkarku da isowa" yana mik'awa mahmud hannu suka gaisa shima cike da girmamawa

"Yawwa yayana mun sameku lpy?" Tafad'a tana k'ok'arin bin bayan dady daya nufi hanyar part d'in Ummi da ita hannunsa na rik'e dana Mahmud d'in "mutanen sararin samaniya ya aikin injin babu wata matsala, murmusawa Mahmud d'in yayi kansa na duk'e ak'asa yace "Eh uncle Alhamdulillah za'ace"

"To madallah Allah ya taimaka" ya amsa masa da amin

Ummi na kitchen tajiyo muryar dady na shigowa kuma da alama bashi kad'ai yake ba da mutane yake tafe, da sauri tad'aurayo hannunta a sink tasa k'aramin towel d'in dake sargafe acan gefe jikin bango tagoge hannunta tafito muryar hajia Hafsat tajiyo tsakar falo tana fad'in "kina ina matar yayana kuma aminiyata k'awar arzik'i, kifito uwar gida sarautar mata, tumin tsakar gida shaluguden mahassada, anbuga dake anbarki" kunyace tarufe ummi lokacin da tafito ta tarar da qanwar maigidanta kuma masoyiyarta tana kwararo mata wannan washi, da hanzari ta iso gareta cikin fara'a tana cewa "lale marhaba biki tsohuwar albarka ummu babanah gwaggon Babanah" dariya Hajia Hafsat tayi suka rungume juna.

Juyowa tayi tana k'ok'arin gaisheda dady da amsar junior dake hannunsa ya kauda kai gefe yana amsa mata ciki ciki, karb'ar yaron tayi cike da mamakin abunda yayi sai kuma tabasar akaci gaba da gaisawar yau sharabo, duk firar da suke dady na gefe abunsa yanata wasa da hannuwan junior, d'ago kai ummi tayi takalli Mahmud dake gefe tsaye yana raba idanuwa tace "Babana barka da hanya kazauna mana" kujerar dake facing room d'in su Bilkisu ya zauna yana cewa ummi

"Ummi wai ina su Bilkisu ne naji tsit" "suna ciki babana bari nakirata ku gaisa tashi tayi tashiga d'akin tasamu har tasoma yin bacci, bubbuga k'afarta tayi " ke Bilkisu wakeup, meke damunki zakiyi baccin marece bayan kinsan bashida kyau"

"Jina nakeyi so lonely saboda su yayya Basmah da suka tafiyarsu shiyasa baccin yasoma d'aukata"

"To ai sai kitashi gasu umman borno can sun iso sai kugaisa" zaro idanuwa waje Billy tayi had'e da d'an rufesu kad'an tabud'e "um.m.i injin batare da yaya Mahmud sukazo ba" tafad'a cikin i'iniya.

"Mtss...ai sai kiyi zuwa kam don shima yafara tambayarki shine dalilin kiran danazo nayi maki" in zaki tashi kitafi kitashi kinga ni inda nayi. K'afafuwa tashiga shuahurawa tana murje murje akan gadon kafin tadafe kanta tana fad'in "wayyo ni Billy damuwata yazo, don Allah yaya mahmud kashafamun lpy?" Tajima zaune kafin ta tashi tashiga toilet, fuskarta ta wanko had'e da bakinta sannan ta zubo k'atoton hijabinta mai hannu har k'asa, ummi nafitowa ta d'auki waya takira yaya mahmud, yana d'auka tasanar dashi isowar su umman borno, da sauri ya matse wayar tare da wucewa part din mom d'insa ya sanar da ita, d'akinsu Basmah ya shiga suma yafad'a masu sannan yajuya zai fita rik'e dasu Bassam dake faman tsalle wai umman barno tazo zasuga junior da yaya Mahmud. Da sauri Basmah ta dakatar dashi fuskarta d'auke da farinciki "yaya tare da yaya Mahmud sukazo?" Kallonta yayi kafin yace

"Eh ina tunanin haka" wani irin tsalle tayo daga kan gado tace "jirani yaya" harararta yayi yana fad'in "hmmm yarinya kice kema kin fola" don nadad'e da fahimtar son yayancan naki kikeyi" yana gama fad'ar haka yawuce abunsa cike da shauk'in son ganin d'an uwansa da kuma gwaggonsa.

Tunda Billy tafito Mahmud ya tsareta da idanuwa ganin yanda ta canza cikin 'yan shekarunnan dabasu had'u ba, don sharabonsa da ganinta tun haihuwar junior gashi yanzu shekararsa biyu harda 'yan watanni, tafe take kanta aduk'e tana kallon k'asa shi kuwa hakan yabashi damar k'are mata kallo, duk da kasancewar bazasu shekarune da itaba tanada girman jikin da yabayyana surarta baisha mamaki ba saida tak'araso wajen tad'ago fuskarta tana gaida ummin borno da dady, sosai yashafa'a da kallon yanda d'an k'aramin bakinta kemotsawa wajen fitar da zazzak'ar muryarta da yakeji tamkar ana kad'ai sarewa, sau biyu tana gaishesa amma baijiba har saida ummansa tace

"Ikon Allah, Mahmud halama bakaji 'yata nagaisheka, kodai ka lorane" shafa sidebars d'insa yayi da hannu tare da sake kallonta kafin yace

"A'a ummanah ganin 'yar taki nayi kaman kajinnan naturawa shiyasa nake mamaki mutum da k'irar buloras"

Dariya dady yayi da tund'azu sai faman ciccije fuska yakeyi sannan yace

"To ai dukkunne yarona" gaba d'aya palourn sukasa dariya jin abunda dady yafad'a

Ita kuwa Basmah jiki narawa takalli Batool tace "sister don Allah kitashi muje, namatsu inga fuskar yaya Mahmud, fuskar da nadad'e ina mararin son gani, wai kinsan me nifa ina matuk'ar sonsa kuma wannan karon duk yanda zanyi in nuna masa zanyi har yafahimci hakan" rungume pillow tayi had'e da runtse idanuwanta tace "ina matuk'ar k'aunarka yayanah"...


_Tirk'ashi, this is just d beginning, yanzu ma'anar Kalmar *'YAN UWANA NE* Zata bayyana afili, idan kun amince da cigaba da typing, ina jiran *comment* d'inku_

# *Team mahbasmah*#๐Ÿ’‹
โคโค
# *Team mahBilqees*#๐Ÿ’‹


๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FARI๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_ina kike tawan *MEAMAH* dake group d'in rano online, gaisuwa tare da fatar alkhairi agareki, ina matuk'ar jinjina maki wajen bi biyar wannan littafi da kikeyi tare da sharhin a kowane page, tabbas hakan nabani nishad'i tare da k'warin guiwa sosai, ngd ngd jazakillahu bikhair am really appreciate๐Ÿ’‹Allah yabar tare_


๐Ÿ’ŽPage_____41๐Ÿ’Ž


Tirk'ashi! Anya yayya Basmah zaki iya da wannan miskilanci na yaya Mahmud kuwa? Batool tafad'a tana turo idanuwa awaje, "hmmm shi so baya dubin yanayin rayuwar mutum kafin ya shigesa, dacewa ko rashinta, cancanta ko akasinta duka baya dubawa, kwatsam yake shiga azuciyar da Allah yanufi hakan atare da ita, ni bandamu da irin yanayin rayuwar saba, a Mahmud d'insa nake k'aunarsa tsakani da Allah acikin zuciyata, kuma rasashi zai iyasa nima narasa rayuwata, ina k'aunarsa irin k'aunar da bansan taya akayi nayi sakeba har tayi yad'on da zaiyi wuyar cirewa acikin zuciya taba, kawai fatana Allah yasa shima zai soni kamar yanda nake sonsa" ajiyar zuciya Batool tayi had'e da cewa amin ya Allah yayya Basmah ni har kinsa jikina yayi sanyi.

"Kidena zancen jikinki yayi sanyi kawai kitayani addu'a kuma kitashi muje mugaida umman borno kinsan halinta bata fiye son raini ba"

Tashi sukayi suka fara lek'awa wajen mom dake kwance abunta tana latsar waya "mom zamu tafi wajen umman borno mugaisheta"

"Ok sai kundawo, kuma ku kula da kanku tunda abokiyar tsibbon nata tazo kada acutarmun daku" batare da sun amsa taba suka wuce part d'in mom cike da takaicin wannan zargi da take yiwa Ummi,

Tashi Billy tayi zata koma d'aki Ummi tace "ina kuma zuwa? Kije kitchen ki kawo abun tab'awa kafin inzo" kitchen tawuce tashiga har had'a fruit akan wani k'aton tray, sannan ta azo gorunan ruwa masu sanyi tare da lemun hollandia asaman wani madaidaicin tray sai kuma cups da wani tray data d'ora snaks akai, wani bowl tasamu ta zubo soyayyen naman rago da yasha kayan yaji da k'uli shima ta azo agefe. Tray d'in data d'ora ruwa had'e da cups da lemuna tafara d'aukowa tanufo palourn dasu tana shigowa saiga yaya Mahmud shima yashigo tare dasu Bassam, da gudu suka rugo suka rungume ummin borno suna yimata oyoyo, gaisheta shima yayi cikin girmamawa tare da nuna yanda sukayi kewarta sosai sannan ya gaida dady da ummi, juyowa wajen d'an uwansa yayi yana fad'in

"Welcome my big broth" tare da mik'a masa hannu suka gaisa sannan ya rungumesa yana murmushi, don kuwa ba kad'an sukayi farincikin ganin junan suba,

Agaban umman barno Billy ta ajiye tray d'in, cup ta d'auka ta tsiyaya mata ruwan ta mik'a mata "sannu da hanya Umma" tafad'a tana k'ok'arin mik'ewa bayan ta karb'a.

"Yawwa Bilkisu sannu kinji ko? Allah yai maki albarka"

"Amin Umma" k'ok'arin komawa kitchen tayi don kwaso sauran kayan ummi tace "Aww Bilkisu dama haka ake tarbon bak'i? Kin bawa ummanki ruwa shine kika barmun d'a k'isar da yakwaso ahanya tasan yanda tayi dashi?" Kallonsa tayi ya sakar mata wani irin miskilin murmushi tare da cewa "ki k'yaleta Ummi kinsan bak'auya ce"

"Aikuwa naga alama, a ina natab'a ganin haka raba d'aya biyu"

"A'a nikam 'yatah wayayyace tunda tasan karrama iyaye" umman borno tafad'a daidai lokacin dasu Batool suka turo k'ofa tare da shigowa,

"Ai shikenan Umma taje abunta Allah yasa ba ita kad'aice k'anwata ba dana sha haushi" dariya gaba d'aya sukayi harda dady dake latse latsen wayarsa amma da alama hankalinsa na kansu, k'arasowa su Batool sukayi tare da duk'awa har k'asa suka gaida umman borno, cike da mamaki ta amsa ganin sauyin tarbiyar da tayi atare dasu da bata san da itaba, kallon Ummi tayi tace "are they my child" lumshe idanuwa ummi tayi umman borno tamik'o masu hannuwa tana fad'in "kumatso kusa dani 'yan matana, ahh lalle girma da hankali sunzo sai aure" haka ta dinga tsokanarsu cikin irin wasarnan ta uwa da d'ah dake nuna soyayya mai tsanani, juyowa sukayi suka gaida yaya Mahmud pilot ya amsa shima cikin sakin fuska tare da cewa

"Allah yayi ruwa tsiya tawanke, sister Basmah zubomun ruwa nasha k'auyancin qanwarki na nema yasa k'ishirwa tak'arar mun da yawu" yak'arasa zancen yana kallon Billy dake k'ok'arin ajiye tray d'in fruit d'in data kawo tana murmushi, wani irin farincikine marar misaltuwa yadira azuciyar Basmah lokacin da taji yanda sunata kefitowa daga bakin yaya Mahmud pilot, sai takeji tamkar yafi kowa iya fad'ar sunan, murmushin ta mai sanyi tasaki had'e da d'aukar cup tabud'e gorar ruwan ta tsiyaya masa ta mik'o masa kanta na sunkuye ak'asa saboda kwarjinin da yayi mata bazai barta ta iya had'a idanuwa dashi ba, shikuwa da hankalinsa na akan firar da sukeyi da yaya Mahmud koda yamik'o mata hannu tazata ya karb'a ta sakar masa, ashe shi kuma hannunsa bai ida kawowa ga cup d'in ba, kawai sai dai sukaji k'arar fad'uwar cup d'in yafashe ruwan suka zube akan tyles wasu kuma ajikinsa, da k'arfi yajuyo yana kallonta cike da jinhaushi yace "Another bak'auya, waccan tahanani ruwan, ita kuma wannan datazo bani saita jik'ani" yanda yake maganar sai yabawa kowa dariya haddai Billy da keyi da k'arfi tana faman rik'e ciki, d'ago kai yayi ya kalleta tayi saurin gintse dariyar kamar ba itaba, d'an k'aramin tsaki yayi sannan yabar palourn Umma da har lokacin dariya takeyi tace "ina kuma zakaje, ai kinmun daidai Basmah, bashine ciwon baki ba"

"Wlh Umma bada gangan nayi masa ba nazata yarik'a cup d'inne shiyasa nasaki" Basmah tafad'a kamar zatayi kuka,

"Nasani Basmah da gangan nafad'i haka don yaji haushi tun d'azu yasaka k'anwarki agaba yana tsargata shiyasa nayi masa haka" gaba d'aya Basmah bataji dad'in abunda ya faruba duk sai taji badad'i aranta ganin haka yasa Umma ta dinga janta da fira don tad'an saki, anan take tambayarta ina mom d'insu injin dai lafiya take, so take tad'an huta sannan taje sugaisa, nan suke sanar da ita ai batajin dad'i amma da sauk'i, suna gama fad'ar haka suka wuce guading abunsu su uku suna firarsu tare da su bilal dake biye dasu abaya rik'e da hannun junior dama shi yaya mahmud tun d'azu yabi bayan d'an uwansa yana masa dariya had'e da tsokanarsa yana fad'in (another bak'auya, gaskiya broth kerenamun k'anne da yawa), duk da bawani shiri umman barno keyi da mom ba saida taji ba dad'i aranta, cikin kulawa da tausayawa tace

"Ayya Allah yabata lafiya, bari natashi naje na dubota,hajia Aisha ko zaki yimun rakkiyane?" murmushi Ummi tayi kafin tace

"Anya kuwa!, dak'yar gaskiya d'azu nashiga nadubota nida 'yarki duk da naso komawa ko yanzu amma zaifi dacewa ace kitafi ke kad'ai saboda kisamu ku soyewarku yanda ya kamata keda amaryar taki ni kuma sai na kula da yayan naki don da alama yana buk'atar magana dani" kasan cewar babu kowa afalon sai su ukun kuma dukkaninsu babu mai b'oyewa wani damuwarsa yasa dady ya d'ago kai yana kallon Ummi kafin yace

"Wace maganar zanyi dake bayan wacce nariga nafad'a maki jiya akan rashin lafiyar matata" kallon rashin fahimtar inda maganganunsa suka dosa Ummi tayi masa sannan tace

"Kamar ya abu Bilal?"

"Kamar yanda kikaje kika cemata nafad'a maki wai aljanune da ita kuma miyagu" dady yafad'a yana kallon cikin idanuwan ummi murmushi Ummi tayi don tasan dama za'a rina, ko kad'an batayi mamakin jin kalaman saba,hak'uri tasoma basa cikin natsuwa kafin tafara fayyace masa yanda akayi taji zancen mom batada lafiya da zuwan datayi ganinta da duk maganar data fad'a, sannan tace

"Abu Bilal har ga Allah nazata cewa hajia Hussaina tacire tsabar da take yimun araina tadawo da nufin muyafi juna muzauna lafiya kamar yanda kafad'amun shine dalilin dayasa na amincewa zuciyata har naje part d'inta amma tunda abun yakasance kuma har kayarda umman yara muje narakaki daga nan sai nabata hak'uri" tana gama maganar tamik'e tsaye tana jiran tasowar umman borno data saki baki tana kallon dady.

A hankali yataso daga inda yake zaune yarik'o hannunta,

"Kiyi hak'uri rabba'atul bait, ko kad'an banyarda da abunda tafad'a ba kawai nayi hakan ne don nagano gaskiya kuma natabbatar da alk'awarin da tayimun na canza warta"

"Wlh karki yarda dashi k'awata, dad'in bakine yake son yimaki da kuma borin kunya, taya inhar bai yardaba zai dinga wane fuffuskewa ai tund'azu ina kalle dashi, hmmm yaya kabani kunya wlh kamarka ace har yanzu baka banbance munafuki da mumini abayyane, Allah ya kyauta dama tunda mukayi waya kace zata dawo nasan da wani abun aranta, oh ni hafsa wlh albasa batayo halin ruwa ba, Allah dai ya isarwa su papi da b'ata masu tarbiyar da suka bata datayi" umman borno ce kefad'ar haka cike da takaicin yayan nata,

"Haba hajia Hafsat, meyasa zaki fad'i haka nifa gyaran aure nasanki dashi ba b'atawa ba, kuma kinsani badon naso kamanta adalciba bazan fad'a mata komai ba sai dai na cigaba da fushi da ita kuma nad'auki hukuncin da naga dama akanta, plz rabba'atul bait kifahimceni kada kibiyewa zugar 'yar uwata har ga Allah ban gama yarda da zancen ba" ganin yanda dady yad'an marairaice mata yasa tace "shikenan komai yawuce amma daga yau zanci gaba da tsayawa a'inda Allah ya ajeni, inaso kafahimci cewa bana son fitina shiyasa banabi takan matsalolin matarka don Allah tabarni insamu natsuwa plz" katseta umman borno tayi "Ai kuwa yau sai kinso fitinarnan don dole kuhad'u part d'insa tamaimaita abunda tace kinyi mata agabanki inta isa"

"Shiiiiii... Ya isa Hafsat meye ribar yin hakan? Kawai mu manta da komai da alama yanzu yadawo ko hutawa baiyiba, dadyn yara komai yawuce kaje kahuta, ke kuma kitashi kije ku gaisa kafin akira magrib in kuma sai kinyi sallah zakije shikenan"

"Ba inda zanje wlh nama fasa zuwa ganin nata munafuka kawai da bataso azauna lafiya" murmushi Ummi tayi lokacin da taji dady yayi hugging d'inta had'e da cewa

"Thank you for given me a wanderful Peace in my entirely life" hararar umman barno yayi tare da cewa "kid'au darasi 'yar uwa" sannan ya ficewarsa zuciyarsa cike da farinciki sab'anin d'azu da yafito part din mom zuciyarsa a cunkushe anan kad'ai akwai zallar banbanci tsakanin Ummi da mom.

Yana fita Ummi tadawo tazauna akan kujerar da umman borno kezaune tasa hannu ta dafa kafad'anta, cire hannun nata umman borno tayi tana cewa

"Don Allah meye ribarki cikin kwantar da kan da kikeyi akan waccan matar, ke kenan cikin b'acin rai akan matsalolinta wlh ni hak'urinnan naki yafara tunzurani"

"Hmmm Hafsat kenan! Yanzu ke bakiga ribar haka da nake yiba?, dubi yanda mijina yafita yana farinciki, dubi yanda mijina ke lallashina da bani hak'uri abunda bakowace mace kesamun wannan matsayin acikin gidan taba, dubi yanda mijina ya gasgata zancena fiye da nata duk da kasancewar yanada damar k'aryata zancen kamar yanda yak'aryata nata yanzu, ai ko ahaka aka tsaya natabbata naci riba, balle a idanuwansa nahango tsantsar soyayyar data lunku azuciyarsa tawa, bazaki iya fahimtar hakan ba saboda sak'on akaina yayi tasiri shiyasa kike ganin laifina"

"Hmmm! Tabd'i jam dole yaya yace nad'au darasi, tabbas wannan itace kissa a ilmance, saita ingizo maki rigima kekuma saikiyi amfani da ita takoma makamin d'aukaka soyayyar ki azuciyar sa, dole na nemo sabon littafin d'aukar darussa ba darasi ba, madallah da samun nagartacciyar mace da yayana yayi kamarki" rungumeta tayi aranta tanajin cewa babu wanda yakai yayanta sa'ar mata kamar yanda tad'aya b'angaren take ganin babu wanda yayi rashin sa'ar k'arin aure kamarsa.

Tunda faraaha tadawo asibiti take jiran ganin call d'in first luv d'inta amma shiru, bini bani zata d'auko watarta tak'urawa nombarsa ido kozai kira, sai kuma tayi murmushi tare da dukan goshinta tana fad'in "kai faraaha kaffa kizubar da gp d'inki, irin wannan zak'ewa haka da yawa har ina" da zaran taji shigowar kira awayarta zata zata shine sai tad'auka da sauri sai taga ashe bashi bane,

A b'angaren dr. Ahmad kuwa yana dawowa daga asibiti kai tsaye yawuce d'akin maminsa agajiye ya fad'a kan gado tare da runtse idanuwansa, fuskar Batool ce tafad'o masa arai lokacin da yake murza mata k'afar da taji ciwo tana ihu, dariya yadingayi yana dafar cikinsa yana kwaikwayon ta "wayyo yaya Mahmud kataimakeni zan mutu, twiny kizo kusa dani don Allah...." Haka yadinga maimaita suruttan da takeyi yana dariya, mami dake acan bayan d'akin tana shanyar kaya tashigo aguje jin yanda yaron nata kefaman dariya alokaci guda kuma yana ihu, a d'an tsorace ta tsaya bakin k'ofar d'akin tana kallonsa cike da mamakin abunda yakeyi, ganin baida lokacin tsagaita dariyar tasa yasa tayi gyaran murya had'e da shigowa ciki fuskarta ad'aure tarik'o kunnensa tana fad'in.

"Kai meke faruwa da kaine? Bana son irin wannan banzar d'abi'a, meye haka kakeyi?" Tafad'a tana k'ara murd'e kunnensa da take rik'e dashi,

"Awshh...wayyi mamie bani bane, fatima ce, ita takeyi hakan"

"Kai wato kafara shashanci a wajen aikin naka ko?, har ka manta yanayin da muke ciki, tukunama fad'amun waye fatima kafin inzane maka jiki" tana d'an kaimasa duka da hannu a kafad'a,

"Mami fatima itace trouble maker, wacce tasa yau jarumin d'anki yakoma soko agabanta, tasa goshinsa ya kumbura saboda tsananin rakinta, alokaci d'aya kuma tasa ya afka a ramin dake da matuk'ar wahalar fita..."

Baki abud'e mami ke kallon yaron nata kafin tace...





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿ˜ญ_*

๐Ÿ‘ญโค *'YAN UWANA NE!*โค๐Ÿ‘ญ
๐Ÿ’Ž _they're my relatives..!_๐Ÿ’Ž


Written by: *BILLY S FAR. I๐Ÿ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Miliyoyan gaisuwa marar adada agareku masoyana, bakina bazai iya kwatanta godiyar da zanyi agareku ba saboda girmanta, all i say gaba d'ayanku Allah yabaku aljannah da rahamarsa, ina matuk'ar samun kuzari da k'warin guiwa bisa comment d'inku, Allah shine sheda ina sonku gaba d'ayanku harda wud'anda karantawa kad'ai sukeyi basa comment, ina fatan aljannah tazamo wurin had'uwar fuskokinmu aranar k'arshe, aciki gaba da hak'uri dani still mun sake samun page 40 har sau biyu don haka yau a page 42 zamu tashi insha Allah sai akula wud'ancan 2pages sun zama page 40 da 41_


๐Ÿ’ŽPage_____42๐Ÿ’Ž


"Iko sai rabbana, Ahmad yanzu mekake so kafad'amun, kadai san yanayin da muke zaune aciki, kana ganin soyayya tanada muhallin da zaka iya bata yanzu?" Hannuwan mamy yarik'o cikin damuwa yace

"Yazanyi mamy harga Allah bntab'ajin ina son wata mace ba kamar yarinyar nan, narasa ko meye dalilin dayasa nakamu da soyayyarta baccin nasan yanayin da nake ciki, amma abu d'aya nasani samu da rashi duka na Allah ne, natabbata albashina zai taimaka mani wajen ganin nabiya dukkanin basosan dake kan mahaifina, jarabawar rayuwa babu ta yanda bata zowa bawa, fad'awa soyayyata bayana nufin karya alk'awarin mahaifina bane, da yardar Allah saina sauke wannan hakk'in nasa daya rataya awuyana, nidai fatana ki amince mani na nemi auren yarinyar nan don kai tsaye nake so inje da nufin aure bawai nema ba" mamy dake hawaye tace "Shikenan Ahmad, 'yar wane gidace yarinyar? Kuma ta amince tana sonka itama?"

"Ban sani ba mamy yau nahad'u da ita asibiti ankawota taji ciwo ak'afa nadubata, banyi mata zancen soyayya ba, amma naduba file d'inta 'yar gidan alhaji Bashar mai furnitures ce" dafe k'irji mamy tayi tana fad'in

"Haba Ahmad, haba Ahmad, ina kai ina 'yar wannan gidan da babu wanda yasan iya adadin tarin yawan dukiyar da yake da itaba, karufa mani asiri kada kad'auko mana abunda yafi k'arfinmu" tak'arasa maganar hawaye cike tab a idanuwanta, ganin yanayin da mamynsa tashiga yasa ya rungumeta cike da tausayinta yace

"Shikenan, mamy zan barta innemi daidai dani idan hakan zai saki farinciki, amma inaso kisani mom arana d'aya naganta kuma arana d'aya naji k'aunarta araina amma wlh banajin zan iya fishsheta azuciyata cikin rana d'aya" d'agowa yayi daga jikinta yaci gaba da cewa "mamy kinsan meyasa nafad'a son yarinyar? Kawai jikinane yabani cewa zata kula mani da mahaifiyata fiye dani kaina, yanayainta tsarinta sun tabbatar mani da zata sakaki farinciki, zata cire maki kewar abbana daya rasu, amma idan kince in hak'ura da ita zan hak'ura mana tunda dama nikad'ai nake kid'ana kuma nake rawata" rik'o fuskarsa tayi tana hawaye "Aa my son dama ni walak'ancin masu kud'i nake jiyema, amma indai zakayi farinciki da samunta to kaje ka sanar da ita kuma katabbata kanemi aurenta ka kawo mani ita kaji ko, Allah ya dafa maka kuma yayi maka bud'i mai albarka kafin lokacin yayi kuma itama Allah yasa ta amince dakai?" Magana takeyi har lokacin hawaye na zubo mata a idanu, alokaci guda kuma tana murmushi, sake hugging nata yayi yace

"Nagode mamynah, ina sonki" da haka sukaci gaba da fira yana bata labarin abunda yafaru tsakaninsa da Batool tare da nuna mata inda yabugu a goshi har yad'an kumburo kad'an tana tayi masa dariya.


'Dakin yaya Mahmud Mahmud pilot yanufa cike da jin haushin dariyar da aka azamasa, kayansa yafara cirewa sannan ya shige toilet dama yanajin gajiya ya watso ruwa yana fitowa yaci karo da jikkar kayansa yaya Mahmud yashigo masa da ita, bud'ewa yayi yaciro black trouser da sea green d'in shirt yasaka fuskarnan tasa ad'aure, kallon yaya Mahmud dake zaune bisa kujera yana dannar wayarsa yayi yace

"Broth, muje ko?" Batare da ya kallesaba yake tambayarsa ina zasuje ina batun kiran sallar magrib don dama yasan halinsa idan yazo ba shida burin da yawuce sufita sud'an zazzagayo gari, cigaba da dannar wayarsa yayi ganin yaficewarsa batare daya amsa mashiba, dariya yayi had'e da cewa "kaji dashi indai gidannan ne bakaga komai ba wlh, dama ka ajiye wannan d'aurar fuskar agefe" koma shigewarsa yayi cikin kujera yaci gaba da kiran faraaha da tund'azu yake kira ba'a d'aga ba..ita kuwa faraaha dama tana waje wayar nacikin d'aki sai can tajiyo k'ararta, shiga d'akin tayi tare da d'aukar wayar tana murmushi saida takusa tsinkewa sannan ta d'aga had'e da karawa a kunnenta saita tsinci kanta da kasa furta kalma ko d'aya, "hello" yafurta masa aya b'angarensa yana mai sauke wata irin ajiyar zuciya. Lumshe idanuwanta tayi sannan tabud'esu tana murmushi batare da tace komai ba, jin haka yasa yaya Mahmud cigaba da cewa

"Hello my fa..raah!" Ya fad'a cikin wata sigar da dole yasa ta amsa masa da "Na'am" atak'aice.

"Hmmm!...ayiwa raguwar zuciyar nan dake da nacin tsiya, so da kaunar da nakeyi maki shi yajawo mata wannan raunin da bazata iya rabuwa dake ba, keyimun kowane irin hukunci bisa damunki da nakeyi amma banda hukuncin rashin kulawa da kuma hanani jin zazzak'ar muryarki" Murmushin da saida yaji sautinsa akunnensa tasaki sannan tace

"Wannan zuciyar dake tunanin tanada rauni tadad'e da samun tallafin wata zuciyar kamarta, wanda a yanzu yakamata tasani tasamu k'arfin da zata iya yak'ar kowane irin hukunci da zai iya gittowa akanta, bazan hukuntaka ta hanyar rashin kulawa ba ko hanaka jin muryata, amma zantabbatar da nahukuntaka ta hanyar nacewa zuciyarka da kuma ruhinka, zan sakaka azuciyata sannan inbuga maka takunkumin da babu wanda zai iya fiddoka aciki" d'ora kansa yayi ajikin kujera tare da rufe idanuwansa, yana jin wata mahaukaciyar soyayyar ta nafizgar kowane sashe daga jikinsa, a hankali ya furta

"Idan kuwa haka tafaru to tabbas nasamu cikakken adalci wajen hukuntawa, kiyarda dani faraah! sonki nakeyi da gaskiya kuma zan aureki matuk'ar kin amince dani" zaunawa tayi daga tsayen da take saboda yanda taji kalamansa sun yimata dirar mikiya acikin

Please Login or Register in order to submit comment