Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciya" cikin wata irin miskilar murya tace dashi,

"Bazan k'ikaba ko don zamewarka mutum nafarko da yayi dashe acikin zuciyata, amma inaso kabani dama innemi zab'in wanda ya halitto mana zuciyoyinmu don tabbatuwa bisa sirad'in da zai kaimu a ingantacciyar rayuwa"

"Na'amince faraah! Allah yazab'a mana duk abunda yafi zama alkhairi, zanjira amsarki tare dafatar zaki bani dama inci gaba da kiranki don bawa dashen danayi kulawa yanda yakamata"

"Bakada matsala indai akan wannan ne k'orafi yariga daya karb'u" dariya yaya Mahmud yayi kafin suci gaba da firarsu cikin so da k'auna.

A b'angaren Mahmud pilot kuwa yana fitowa ya nufi guarding don yarasa ina zaije yarage zafi, can nesa dasu Billy dake firarsu ta 'yan uwan juna ya zauna yana satar kallonsu d'aya bayan d'aya, Basmah da Batool kyawawan 'yan mata ne da babu namijin da zai kallesu baiji ya fad'awa sonsu ba, kusan kamar su d'aya amma Basmah tad'ara Batool haske sosai duk da itama d'in ba bak'a bace, ko kad'an basada wata k'iba ajikinsu amma hakan bai hana shape d'insu fitowaba, yayinda ita kuma Billy wankan tarwad'ace tanada jiki amma irin na lukutayen yaranda da zaran kadubesu zaka tabbatar da akwai hutawa atare dasu, tanada k'irar matan nan da ake kira da masu shape d'in coca cola, duk da kasancewar tanada k'ananan idanuwa da suka alak'anta yanayinta da mutanen Japanese hakan bai hana kyawon da Allah yayi mata bayyana ba. Murmushi Mahmud pilot yayi kafin yace

"She's very different and unique also she mean something something" yad'an d'ora hannunsa saiti da zuciyarsa yana k'ara k'aremata kallo.

Batool ce talura da hakan, tad'an kizgini Basmah da kafad'a tana nuna mata inda yake da idanuwa, murmushi tayi tana kallonsa tace "sisters kozaku rakani nabashi hak'uri akan abunda yafaru d'azu naga kamar ransa yab'aci sosai"

"Tab babu inda zanje, kiga mutum sai wani shan k'amshi yakeyi akan d'ai an watsa masa ruwa ajiki, sai kace wanda aka watsawa wuta!" Batool tafad'a tana k'ara gyara zamanta akan stone chair d'in da suke zaune, dukanta Basmah tayi cike da jin haushi aka fad'a tace "kinga matsalata dake rashin fahimta amma ai naga dai ko k'ak'ane an b'ata masa kuma yakamata abasa hak'uri ko Billy" tak'arasa maganar tana kallon Billy dake sakace 'yar dattin data shige mata a akaifa da yatsanta.


"Eh" Billy tafad'a atak'aice tana satar kallonsa. Hannunta Basmah tarik'e suka nufi wajensa kanta na sunkuye ak'asa har suka iso, itadai Billy ko kallon inda yake batayi ba, yayin da Basmah tace

"Yaya mahmud don Allah kayi hak'uri da abunda yafaru d'azu, banyi hakan da wata manufa ba, kuskurene kawai" d'ago kansa yayi yana kallonta sannan yayi murmushin da yasa banda Billy dake gefen Basmah da tuni jire ya d'ebeta tafad'i "kimanta kawai sister, komai ya wuce dama ni bake kika b'atamun rai ba, wannan damammiyar k'anwar takice mai fuskar Japanese data azamun dariya tafi b'atamun rai, zo zauna anan kibani labari kuma kice mata ta tafi kafin in mamaketa anan" farincikine ya bayyana a fuskar Basmah wanda alokaci d'aya taji duk damuwar da tashiga ta yaye mata, ita ko Billy najin haka tajuyawarta ba tare da tace masa komai ba don inda sabo tasaba da irin tsarguwar da yake yimata, hakan da tayi sai ya bak'anta masa rai cikin jin haushin halin ko inkula data nuna masa yasa mata k'afa aikuwa tayi baya da baya tafad'i k'asa, da sauri Basmah taduk'o tare dasa hannu biyu ta d'agota shikuwa yayi kamar bai ganetaba, kallonsa tayi idanuwanta cike tab da hawaye ya wani fuske tare da kauda kai gefe. Rik'eta Basmah tayi cike da kulawa tana tambayarta "sisto sannu injin baki jimuba" cije baki Billy tayi sannan ta wafce hannunta daga rik'on data yimata ta wuce abunta rai ab'ace. Mik'ewa yayi had'e da cewa "sister bari naje naji ankira sallah"

"Shikenan yaya sai anjima"

Batool kuwa dake kallon duk abunda kefaruwa dariya ta azawa Billy lokacin data k'araso wajen tana duba hannunta daya d'an tulb'e daga ciki, "sannu twiny wlh kinban dariya, kin kuwa ga yanda kika fad'i? Hhhh wlh yaya ya iya mugunta, shiyasa kikaga nace ba inda zanje koda yake ai duk laifin yayya Basmah ne data wani jaki bataje ita kad'ai ba" tana rufe baki taji an tallafo k'eyar kanta da duka ana fad'in

"To zuga zugi ai dai 'YAN UWANA NE dukansu baki isa ki had'ani dasu ba" d'ago kan da zatayi taga ashe Basmah ce ke fad'ar haka had'e da sakar mata harara, turo baki tayi da niyar magana itama Billy ta sakar mata rank'washi akai tabar wajen aguje tana dariya had'e da fad'in "ko akanki narage zafi" dariya Basmah tabushe da ita lokacin da taga Batool tabi bayanta itama tana fad'in

"Ai baki isaba, kumburi ga doki sakkiya ga jaki, Allah bazan yardaba sai na rama"...











*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*



πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____43πŸ’Ž


Bayan umman borno dake zaune tana gyarawa Ummi yakuwa Billy taje tab'uya saiga Batool tashigo tana faman haki, dube dube tafarayi ta inda zata hangota amma bata ganetaba, kallonta umman borno tayi had'e da cewa "'yan matana daga ina haka kike faman haki, Allah sa dai bagudune kikayi ba?"

"Umma kibarni da Billy ita tasakani wannan gudun shine kuma tazo tab'uya"

"Au dama keta jawo shine tazo tab'uya abayana kuna 'yar gudedeniy?, Iko sai Allah" fitowa tayi daga bayan nata tace

"Plss sorry aunty Batoolu.." Kafin tarufe baki batool tashiga bubuga k'afa tana fad'in

"Umma kinji ta ko?, nafad'a mata banason wannan sunan amma bazata dena ba, wlh Allah zunubinki yazama biyu, gana dukan da kika yimun kuma gana wannan sunan da bana so" ya isa haka Ummi tafad'a lokacin data fito daga kitchen hannunta d'auke da warmer d'in da ta kwashe tuwon semolinan data tuk'a

"Allah ya shiryeku wlh yarabaku da wahala, yanzu Bilkisu tsabar tsokana auntyn taki kike duka, ga shidai alamu sunnuna kungirma amma ko kad'an babu jin magana atare daku, nasha fad'a maku bakyau gudu ga 'ya mace idan ba bak'ar doleba amma bazaku dena ba, ai sai kuyi tayi ga wanda zaiyi maganinku nan ya iso"

"Ummi duk laifin aunty Batool ne, dariya fa tayimun"

"Au ashe dariya babu dad'i kika azama yayanki ita d'azu" Ummi tafad'a tana k'ok'arin karb'ar yakuwar da umman borno tagama yankawa sannan ta shige kitchen tana cigaba da yimasu fad'a. Kallonsu Umma tayi d'aya bayan d'aya sannan tacewa Billy "to mai gadon zinari kije kibata hak'uri sai kuje kuyi sallah, kinji ko? don gaskiya kece mai laifi kuma kudena irin wud'annan wasannin bakyau da haka shed'an kesamun hanyar shiga tsakaninku sai ya ribaceku" rik'e kunnuwa Billy tayi bayan tadawo wajen da Batool take tsaye had'e da cewa "Am sorry my twiny, never repeat it again" d'aga hannu tayi kamar zata doketa ita kuma ta runtse idanuwa saboda yanda take da matuk'ar tsoron duka sai tayi dariya had'e da lak'amo kafad'ar ta suka nufi part d'in mom tana fad'in "matsoraciya kawai, ga tsoro ga ban tsoro!"

Yaya Mahmud kuwa saida yaji ankira sallar magrib sannan ya katse wayar da sukeyi da faraaha yana jinsa cikin wani irin shauk'i da bazai iya kwatantasa ba, kissing d'in wayarsa yayi tare da yin tsalle yana fad'in "yes nasamota" wanda yayi daidai da shigowar Mahmud pilot, cike da mamaki yake kallonsa tare da d'an turo idanuwansa sannan ya mere baki ya wucewarsa toilet yayo arwala, yana fitowa shima ya shiga yayo tasa suka nufi masallaci, dady kuwa yana shiga part d'insa ya samu d'aya daga cikin kujerun dake nan falon k'asa yazauna, jingina jikinsa yayi ajikin kujerar ya lumshe idanuwansa yana tunanin wai yaushene hajia Hussaina zata canza wud'annan mugwayen halayenta, menene matsalarta da rabba'atul bait d'insa da take neman kullum tahad'asu fad'a, tabbas idan za'aci gaba da tafiya haka baya tunanin zai iya jurewa k'arasa rayuwarsa da ita matuk'ar bata canza ba, haka yaci gaba da tunani kala kala azuciyar sa, idan ya sak'a wannan ya kwance wancan babu abunda yake buri arayuwarsa irin yasamu mafita akan wannan matsalar dake cimasa tuwo a k'warya, har aka kira sallar magrib yana wurin zaune batare da yasamu tudun dafawa ba akan wannan matsalar tasa.

A b'angaren Basmah kuwa kai tsaye d'akinsu tanufa lokacin da tabar wajen cike da farinciki, toilet tashiga tayo arwala ta gabatar da sallah tare da addu'ar Allah ya sanya yayanta yazamo miji agareta kuma farincikinta uban 'ya'yanta, tana kammala wa tawuce kitchen, mom d'inta ta tarar aciki tana k'ok'arin sauke couscous d'in data dafa, gaisheta tayi had'e da cewa "mom ya jikin sannu da aiki"

"Yawwa Basmaty, jiki nawarke tunda gani kitchen ina k'ok'arin had'a maku abunda zakuci kuda dadynku"

"Allah to yak'ara sauk'i momyn mu, yanzu mezan rik'a maki muk'arasa" dariya mom tayi kafin tace

"Kinji ki da abun dariya, ke mekike iya in banda latsar waya, kawai jeki abunki zan k'arasa" wani irin tuk'uk'in bak'in cikine yarufe Basmah had'e da takaicin wai yanzu momyn tace da kanta kegoranta mata haka, kenan badon Allah ya taimaketa da zaman da sukayo wajen Ummi tafara nuna mata wasu abubuwan ba shikenan haka mom zata k'yaleta bata iya girkiba har tayi aure taja mata matsaloli gidan mijinta, gashi tun ba'aje ko inaba ita da kanta keyimata gori da bata iya komai ba sai latsar waya, sai alokacinma tatuna da wayarta bata hannunta ranar tabarota a d'akin da sukaje ita dasu suby da babs, 'yan guntayen hawayen da suka zubomata tasa hannu tagoge sannan ta kalli mom dake k'ok'arin nik'a tattasai a blender tace,

"Mom zan fara koyar girki daga yau, insha Allah bazaki koma shigowa kitchen kekad'ai ba, atare zamu dinga yi har saina iya nima"

"Kai! inaaaa haba Basmah ai bazan yarda kilalatamun abinci ba kasa dadynku yakasa ci, kedai kawai kije abunki, inkyayi auren kya koya acan" cike da mamaki Basmah ke kallon mom, wannan wace iriyar maganace haka takeyi, mahaifiyarta da kanta keneman durk'ufe rayuwarta taya zaka koyi girki agidan miji bacin kamata yayi ace kakoya tundaga gida, shiru tayi bata sake cemata komai ba tanemi gefen fridge d'in dake kitchen d'in tayi tsaye tana kallon yanda take had'a miyar k'wai with kidney har ta kammala, tayata gyara wajen tayi duk da sai faman gwatsileta takeyi tana fad'in taje tazauna abunta ita bata fiye son idan tana aiki adinga takurata ba.

Kimanin kwana uku kenan yau kullum dr Ahmad cikin tunanin Batool d'insa yake kuma aduk lokacin da yatuna da ita sai yayi dariya sosai had'e da cewa Yaa Allahu kabani fatima! Yauma dai kamar kullum zaune yake yana duba wata marar lafiya sai idanuwansa suka kai ga d'an gadon da ake duba patient dake cikin office d'in sai yatuna da ihun da Batool tadingayi tana neman taimako, baisan lokacin da yafara kwasar dariya ba harda rik'e ciki, patients d'insa naganin haka ta tashi sad'ab sad'ab tabar office d'in, so yakeyi ya tsaisheda ita amma yakasa magana sai faman d'aga mata hannu yake aikuwa tafice abunta rik'e da hannunta daya sundule mata sosai, saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru had'e da k'urawa wajen idanuwa yace

"Fateema kidena wahalda zuciyata haka, ina matuk'ar azabtuwa da soyayyarki, ina zanganki ta ina zanfara fuskantarki da d'imbin k'aunarki dake cikin zuciyata, gaba d'aya na zauce akanki, na susuce akan sonki sosai fateemah! Ya Allah nunamun tahanyar da zansamu fateemah" kamar daga sama yaji an amsa masa da amin, d'ago kansa yayi yana kallon wacce ke tsaye gabansa tad'ora hannuwa ak'irji itama tana kallonsa fuskarta cike da murmushi da alama taji duk abunda yafad'a, d'an sosa k'eyar kansa yayi alamun yaji kunya, ita kuma tajawo kujera ta zauna sannan tace

"Dr. Ahmad kenan! Kace yau ruwa sunk'arewa d'an kada, irin wud'annan sabbatu da kake zubawa ai sai mufara tunanin kaikai kaga likitan sychartric, tukunama wai wannan fatimar wacece ita, wace mai sa'arce data sace zuciyarka arana d'aya?" Shafa kansa yayi kafin ya kalleta ya nuna gadon dake facing d'insa tajuyo ta kalli gadon itama, ahankali yace "a wancan gadon ne nayi arba da ita, kyawonta, tsarinta, muryarta duka a cikin wannan ranar suka daki zuciyata, a wannan ranar da bazan manta da dafin data sakarmun ba, kuma acikin wannan ranar ne nakamu da soyayyarta wacce kece silar shigata wannan yanayin da kuma babu wanda zai iya taimakona idan bakeba sister faraaha!"

"Tofah! Dr kace abun naka azhimun ne, kafito Filo kayimun bayanin da zan iya fahimta ko Allah yasa nazamo silar magance wannan yanayin da kake ciki na neman taimako" dariya yayi had'e da juya biron dake hannunsa sannan ya ajiye ya sark'e yatsun hannuwansa wuri d'aya yana kallonta, anatse yafara fad'amata fatimar da yake nufi da kuma ranar da sukazo da ita da abunda yafaru tsakanin shi da ita har zuwa yanayin daya shiga akanta cikin 'yan kwanakinnan, ya k'are da fad'ar "natabbata kingane ko wace fatima nake nufi don nasan alak'ar da kike da ita dasu yasa kikazo kika nemi in taimaka maki nadubata ko bahaka ba"

Wata irin ajiyar zuciya faraaha tayi kafin tace....






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_A wasu lokutan samun nagartaccin abokanan tarayya acikin rayuwa kansa su shallake gurbin akirasu da abokanai ko kuma k'awaye saboda kirki, mutunci da karamcin da suke dashi saidai akirasu da 'YAN UWA, a 'yan uwanma irin najini da ake very close dasu, gaisuwa tare da fatan alkhairi agareki *FATEEMA SHI'ITU BUNGU'DU* (Maman arfat) ina so kisani ke 'yar utace dake da gurbin da baya kankaruwa ko musanyawa acikin zuciyata, fatana Allah yakare mani rayuwarki data ahalinki kuma yabaki mafi ingantacciyar rayuwa agidan aurenki tare da mafi girman sakamako agobe k'iyama wato aljannah fiddusi, ur *BIL-SAN* luvs you more than how word can say it_πŸ’‹β€


πŸ’ŽPage_____44πŸ’Ž


Dr.kenan yanzu akan wannan 'yar k'aramar matsala kazauna kana sabbatu a office? Kadena nauyin baki acikin burin zuciyarka kadena b'oye damuwarka gameda abunda kakeso, kuma kada kayi jinkirin bayyana muradinka ga wanda kake fata yazama abokin rayuwarka domin hakan zai iya cefaka amatsalar da zakasha wahala arayuwa idan yagudu yabar ka ko kuma yayi nisa dakai matuk'ar ba Allah yatausaya maka yasake maido maka da abunnan izuwa gareka akaro na biyu, tabbas nafahimci fatimar da kake cikin magagin sonta domin 'yah ce ga alhaji bashar mai furniture's wanda Dr.Jamil shine family doctor d'insu, kuma shine silar shigar wata alak'a tsakanina dasu, kuma ta dalilin ganinsa ranar yasa kahad'u da ita, yayanta abokinane sosai wanda da sannu kuma zai zamo abokin rayuwata nahar abada idan Allah yaso, saboda haka ka kwantar da hankalinka zaka samu fatimarka da yardar Allah saidai kuma a gaskiya kayi sonkai da yawa don yarinyace sosai, she's just 15years" tak'arasa maganar had'e da mik'ewa tsaye zatabar office d'in, da sauri ya tsaisheta cikin rawar murya yace

"Haba sister faraaha, ina kuma zakije, kizauna muk'arasa magana mana, wannan ai tamkar kin k'arawa fetur ruwane idan kika tafi kika barni with out finding the solution" turo idanuwa tayi awaje hannuwanta na cikin aljihun rigarta ta irinta nurses da suke sawa tace "aikifa nake dashi dr., nakawo wata patient ne anan EPDU sai nace bari nal'ek'o office d'inka mu gaisa" agogon hannun dake d'aure a tsintsiyar hannunta ta kalla tace "it's more dn 20m fa ina cikin office d'in nan, gaskiya am going ka kula da patient d'inka inyaso next time zamuyi magana" tun kafin tarufe baki taga yafara har had'a inashi inashi dake saman table d'in dake gabansa yace "Shikenan muje kifara dubani ai nima patient d'inne in yaso daga baya nadawo nadubasu, haba sister faraaha ai kamata yayi kabani taimakon gaggawa da zai ceto rayuwata, bawai kawai kizo kidubani kiwuce ba, haka aka cemaki ana kula da marar lafiya" cike da mamaki faraaha tace "kamarya dr. Bakada lpy?"

"Kin manta mekikace lokacin da kika shigo, zaku kaini naga sychatric doctor, to ai wannan yanayin da yasa kika fad'i haka shine rashin lpyr tawa, plsss sister faraaha yakamata ko akan hanya kid'orani kafin kiwuce, idan kuwa ba haka ba nadinga bibiyarki kenan duk inda kikayi har sai kinsamu lokacin da kike tunanin zaki iya taimakona, ina matuk'ar jin pain anan d'ina kuma duka dalilin fateemah ne!" ya nuna saiti zuciyarsa fuskarsa kamar zaiyi kuka, sosai yabata tausayi ta kalli yanda yake da kyau ga kwarjini da yanda 'yan matan asibitin ke ribibinsa yana wani feeling tare da shan k'amshi akoda yaushe don ko a ward d'insu kusan mace biyu ke sonsa amma yak'i ya basu fuska balle susa ran samun kulawa daga garesa, tabbas shi so babu ruwansa dako kai waye, yau gashi dr. Ahmad da kansa yake begging ataimaka masa akan soyayyar wata mace kuma 'yar k'ank'anuwar yarinya, tsayuwarta tagyara sannan tace "yanzu ya kake so ayi dr?"

"Ki had'ani da ita"

"Idan nayi maka haka shikenan?"

"Eh..in sha Allah" wayarta tajawo takira lambar danaga tarubutawa *All I have* akai sau biyu tayi ringing ana ukkun ya d'aga.

"Hello golden heart" Mahmud da yafad'a da fitowarsa wanka kenan yana tsane jikinsa yaji k'arar wayar, murmushi tayi tamkar tana agabansa tace

"Barka da hutawa ranka ya dad'e, injin dai katashi daga baccin haka"

"Eh natashi amma dak'yar saboda yanda hatta acikin mafarkina kika hana zuciyata sukuni ina neman rasa raina akan sonki, d'aukin da kika kawomun alokacin tare da dad'ad'an kalamanki su suka hanani wucewa har nasamu nafarka daga baccin da nakeyi"

"Hmmm kace nakuru yallab'ai dana zama k'aramar bazawara aduniyar mafarkai" dariya yaya Mahmud yayi kafin yace

"Ya ake ciki my Golden heart, yanzu nake mararin kiranki idan nagama shiryawa sai gashi naga kiranki ya shigo"

"Eh dama ina son yin waya da Batool ne idan kuna kusa"

"Lallai ma kice saboda ita nasamu kira yau daga wajenki, tabbas yazama dole inyi mata kyauta tamusamman ayau, bamu tare amma bari nakai mata wayar"

"Noo..kahuta abunka anjima zankira sai kabani ita duk da dai urgent nake son magana da ita." Dagashi sai dogon wando da farar singlet dake jikinsa yabar d'akin yana fad'in,

"Karki damu gashima nafito zan kaimata" d'an hararar dr Ahmad daya zuba mata idanuwa yana kallo cike da mamakin yanda ta iya soyayya haka tayi kafin ta shagwab'e murya k'asa k'as tace "sorry All have nabaka wahala ko? Nima dai kamawa tayi but i will pay for it anjima kaji ko?" Murmushi yayi daidai lokacin da ya isa part d'in mom Batool na kakkab'e kujeru da alama gyaran palourn take yajawo hannunta, "golden heart karkiji komai ga Batool d'in" yafad'a had'e da manna mata wayar akunne sannan yawuce bedroom d'in mom don ya gaisheta.

"Helloo, assalamu alaikum" Batool tafad'a cikin muryarta mai d'an karen dad'i tana yamutsa fuska saboda rashin sanin wa yaya Mahmud ya had'ata dashi suyi waya, faraaha najin muryarta sai tayi saurin mik'a masa wayar bayan tasa hannu tad'an rufe speaker d'in wayar tace "Gud luck dr Ahmad, iya ruwa fidda kai gaka ga fateemah nibari najiraka daga waje" karb'a yayi hannunsa narawa yakara wayar akunne tare da sassauta d'aurin neck tight d'insa, dai dai lokacin Batool tasake cewa

"Hellooo." Dak'yar yasamu yayi kokuwa da lumfashinsa dake neman d'aukewa ya amsa mata da "He.l.l.o fateemah" had'e da sauke wata irin ajiyar zuciya.

"Na'am ina kwana!" tafad'a cikin mamakin yanda aka kirata da sunan da duk duniya bata tab'a jin ankirata dashi ba, ta amsane kawai don tasan cewa asalin sunanta fateemah ne!, shi kuwa wani irin jirine yafara d'ibarsa jin yanda ta amsa masa amutunce had'e da girmamawa, wata irin sabuwar soyayyarta mai girman gaske yaji tak'ara shiga zuciyarsa cikin sanin murya ya amsa mata da "lpy klw fateemah, hope kintashi lpy" "eh alhmdllh tafad'a atak'aice cike da zak'uwar jin koda wa take waya "kar kisamu damuwa fatima, yanzu zangabatar maki da kaina tare da dalilin da yasa nanemi yin waya dake saboda shine abu mafi muhimmanci daya kamata kifara sani akaina, sunana Ahmad Bashar kuma ni d'an haifaffen wannan jaharce gaba da baya, ina zaune a anguwar G R A tare da mahaifiyata, fateemah tun ranar da Allah yasa nad'ora idanuwana akanki nayi sha'awar nazamo bawa agurinki, tayanda duk wata d'awainiya taki aduniya zanzamo nine wanda zaiyi maki ita, fateemah ina sonki irin soyayyar da bazata barni yiwa kaina uzuri ba aduk lokacin da tunaninki yak'aurace mani, nayi alk'awari zan bauta maki har iya k'arshen rayuwata matuk'ar kika amincemun, kiyarda dani fateemah so nakeyi maki tsakanina da ubangijina kuma zan aureki idan kin amince kuma kinbani damar yin hakan. Don Allah karkicemun A'a fateemah domin hakan zaisa nazamo marar sa'a nafarko acikin sabuwar duniyar dana tsinci kaina" tirk'ashi Batool tafad'a acikin zuciyarta, wannan wane irin mutumne da Allah yayima baiwar iya tsara kalamai, bama wannan ba yanda yake furta asalin sunanta abakinsa shine abunda yafi burgeta dashi, bata sani ba ko zuciyarta zatayi na'am da wannan sabon mutum mai sabon al'amariba amma tabbas taji kalamansa sun burgeta.

Jin shirun yayi yawa yasashi cewa "kiyimun uzuri kuma kiyafeni inhar kalamaina sun bak'anta zuciyarki, zamowarki mace tafarko data b'alle murfin zuciyata tashige batare da saninaba shiya haifar da fitar wud'annan kalaman masu tsauri agareki"

"Babu damuwa, zanyi tunani inkuma auna gaskiyar kalamanka kafin nan in amshi uzurinka" Batool tafad'a had'e da cigaba da kakkab'e kakkab'en kujerunta"

"Godiya nakeyi mai zarkakakken suna zarah!, natabbata tsarkakakkar zuciyarki zata amshi uzurin bawan dake neman agaji daga wajenta, zanjiraki nan da anjima, gobe, jibi ,sati, wata, shekara kai harma nan da zuwa tsayawar lumfashina, fateemah !i do luv you forever, nabaki lafiya, inayiwa kaina fatar kizamo cikin amincin Allah akoda yaushe"

"OK nagode, sai anjima" kafin yace wani abun har takatse wayar tare da kiran yaya Mahmud tamik'a masa abussa, yana amsa saiga kiran faraaha yasake shigowa, d'agawa yayi fuskarsa d'auke da murmushi "hello matar" murmushi tayi kafin itama tace

"Hello mijin, am sorry pls don Allah ka sake baiwa Batool wayar"

"Angama ranki yadad'e" yamik'awa Batool wayar, karb'a tayi wannan karon zaune tayi bisa hannun kujera kafin tace hello atak'aice, muryar sister faraaha da taji yasa tafad'ad'a murmushinta tana fad'in "laa...aunty faraaha morning, ya aiki" dariya tayi tace

"Yau kam aiki yasamu tsaiko daga wajen dr. Ahmad d'inki"

"Kamarya aunty?"

"Eh bayanzu kika gama waya da wani ba, ina dai kingane kowaye ko?"

"A'a aunty faraaha amma dai yacemun sunansa Ahmad Bashar, dama kin sanshine?"

"Hmmm sosai Batool shine dr.Ahmad d'in da ranar yadubaki, har kin manta nafad'a maki sunansa" dariya Batool tafashe da ita kafin tace

"Kice Allah aunty!, lalle dr. Nan ya shammaceni, wato ranar yagama zalintata, shine yau zai kirani yace wai yana sona, no wander zai kuwa gane kud'insa"

"Pls Batool keep joke aside, wlh da gaske yakeyi, wace irin shammata zaiyi maki bayan wacce ke kika yimasa na sace zuciyarsa gabaki d'aya, nidai nahango tsantsar soyayyar da yake yimaki a idanuwansa kuma ina shawartarki daki manta da wancan abun daya faru tsakaninku, inada yak'ini akan in sha Allah zaki samu farinciki awajensa don haka, kibawa Allah zab'i akansa kuma kinemi shawara awajen mutanen k'warai kamar yayanki, nan da kwana ukku zan sake kiranki kinji ko"

"In sha Allah aunty amma wlh Allah ya iya Mugunta" Batool tafad'a tana turo baki kamar tana gabansa.

"Amma ai naga Mugunta ta taimaka maki don ina da tabbacin izuwa yanzu tafiyarki takoma normal" haka dai faraaha tayi ta convincing d'inta akan dr Ahmad kafin nan tace tabawa yaya Mahmud wayar, agaban dr Ahmad tayi masa bayanin abunda kefaruwa da dalilin dayasa tanemi yaba Batool waya, kaf tafad'a masa komai akansa ta yanda zai fahimta batare data b'oye masa ba, murmushi kad'ai yaya Mahmud yayi yace

"Allah yazab'a masu abunda yafi zama alkhairi damu baki d'aya" da haka ya tsinke wayar yana mai tsokanarta da wai tazama mai dalili sunata dariya sannan ta jefa wayarta a aljihu, kallon Dr Ahmad tayi tace

"To dr.shikenan ko? Ina fatar nad'oraka akan hanya, kuma nabaka maganin da inhar kakula dashi da kyau zaka samu lpy, ammafa jarumar taka sai k'orafin kayimata mugunta takeyi, don haka arage cutar patient dr" Dr Ahmad da zuciyarsa kecike da farinciki ya dirko akan taburin da yake zaune yana fad'in

"Sosai kuwa sister faraaha, zankula da maganin har sai yazamo warakar cutata,kuma ina godiya sosai wacce batada adadi, koda fateemah tayi rejecting d'ina kin kincini tukuici domin kin yimun abunda bazan tab'a mantawa dakeba"

"Kar kaji komai dr haka Allah yatsaro

Please Login or Register in order to submit comment