Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sunanta?"

Aza kanta tayi asaman k'irjin Billy tana kallonsa sannan tace

"Mommah" tana murmushi

"Yawwa gud girl, Allah yayi maki albarka" cike da sha'awarsu Billy ta amsa da amin.

Bayan sun kammala karyawa yashiga ya watso ruwa da misalin k'arfe sha biyu na rana sai gasu yaya Mahmud sun shigo zasuyi masu bankwana, kallo d'aya Batool tayiwa Billy takauda kanta gefe tare da rufe baki tana 'yar dariya saboda yanda taga idanuwanta sun kumbura, gaggaisawa sukayi mom taja Billy cikin bedroom had'e da bud'e side mirror wardrobe d'inta tagwada mata kayayyakin gyaran jiki dana sirrukanmu mata ta gwada mata yanda zatayi amfani dasu, itadai Billy tsaye tayi tana sauraren mom kamar ruwa suncita, 'yar nasiha ta sake yimata sannan tafito dama mahmud nacan waje shida yaya mahmud suna d'an firar bankwana,

Suna fitowa Billy tajawo hannun Batool suka shige k'uryar d'akinta tab'ata rai kamar zatayi kuka tace

"Amma dai ke twiny muguwa ce dama kinsan wahalar da zanfuskanta shine harda wani kiransa kisanar dashi, wlh Allah dana san haka soyayyar take da bazanyi ba, kinga yanda jiya ya..." Da sauri Batool tad'ora yatsanta bisa bakin Billy tana girgiza matakai

"Karki sake kifara 'yar uwa, haramunne bayyana shimfid'ar mijinki duk kusancinki da mutum, kiyi k'ok'arin boye sirrin kwanciyar ki da mijinki ga kowa hakan zaisa kimarki da darajarki suk'aru awajensa, laifine kuma haramunne kad'a'an mace taje tana fad'ar yanda mijinta ya takata, yin hakan zai kad'aki cikin fushin ubangiji da tsinuwarsa don haka bani ba komai kusancinki da mutum kada ki kuskura kibayyana masa sirrin aurenki kinji 'yar uwa?, yanda kikaji haka kowace matar aure taji don haka kijure ko meye kuma kazamo mai hak'uri da juriyar iya d'aukar buk'atar mijinki hakan zaisa yak'ara sonki azuciyarsa idan kuma kika zama mai k'orafi da taushe masa hak'k'i to da sannu zaki koya masa yanda zai tsaneki azuciyarsa don haka ki kula kinji" tak'are maganar had'e da dafa kafad'arta, rungumeta Billy tayi tana hawaye tace

"Ina alfahari daku 'yan uwana bisa kulawa da soyayyar da kuke bani, ina rok'on Allah kamar yanda yaba yayya da yaya 'ya'ya kema Allah yabaki naki rayayyu masu albarka" Batool dake d'an bubbuga bayanta ahankali tace

"Amin my twiny tare dake"

Da haka sukayi bankwana Billy rik'eda little tarik'e yaya mahmud tanata kuka, saida Mahmud yayi da gaske sannan yasamu ya rarrasheta takoma cikin gida shi kuma yarakasu har filin jirgi,

Koda ya dawo kai tsaye gidansu Umma ya sameta zaune da wasu cousin's d'insa sunata yimasa sheri wai "yau ba zama maye yayi sabuwar amarya"

Ko kallonsu baiyi ba yanufi inda mom take zaune shima ya zauna tare da d'ora kansa bisa kafad'arta ahankali yake yimata magana

"Umma ina alhaji?, yana ciki?"

"A'a kam yafita yace zaije dubo abokinsa ne dake asibiti injin dai ko lafiya, ina ba matarce zakace bata yimaka ba" d'an sosa k'eyar kansa yayi had'e da cewa

"Umma wa mutum inji mutuwa, dama godiya zanyi maku fa nasama mun farincikina da kukayi" baki bud'e Umma take kallonsa kafin takai masa duka agefen hannu tana fad'in

"Oh ni hafsatu 'ya'yan zamani, d'age kabani waje kafin in mammakeka, marar kunyar yaro, godiyar gidanku, ja'iri" Mahmud yabar palourn yana dariya don dama yasan za'a rina.

Ganin aurensu yanzu almost 3years kenan har yanzu ko b'atan wata Batool batayi ba yasa dr Ahmad yafara kai Batool asibiti ana dubata agani koda akwai matsala haka shima yana k'ok'arin ganin likita saboda ayi investigating d'in lafiyarsa duk gwaje gwajin daya kamata ace su dukansu sunyi sunyi, amma maganar d'aya itace lafiya klw suke, Batool kam tunda taji haka takwantar da hankalinta taci gaba da addu'ar idan alkhairi ce agareta Allah yabata idan kuma babu alkhairi Allah yabata hak'uri da juriya cinye jarabawarta.

Hatta dady da mom rashin haihuwar Batool tana damunsu baranma mom da wani lokacin har hawayen tausayin 'yar tata takeyi, duk da bawani jimawa tayiba bata haihun ba.

Sai yanzune mom ke dana sani da kuma jin haushin abubuwan data tayiwa Ummi lokacin da bata haihu ba, tabbas yanzu tafahimci rad'ad'i da damuwar da mutum keshiga idan Allah ya jarabcesa da rashin haihuwa, wanda gata ita 'yarta ce ma bata haihuba amma duk tashiga damuwa balle ace ita kanta ce aka jarabta kamar yanda akayiwa Ummi, komawa tayi ga Allah tanata istigfari bisa isgilanci da tayiwa abukiyar zamanta wanda yau sai gashi anjarabceta da haka tahanyar 'yarta.

Ummi kuwa duk lokacin data kwatanta takanje wajen Batool tayita bata magana tana buga mata misalai da wud'anda Allah ya jarabta da irin matsalarta amma sukayi hak'uri kuma daga baya sai Allah yabasu, kuma tana lak'anta mata addu'o'in neman haihuwa wud'anda suka inganta daga alk'ur'ani, irinsu

_*RABBI LAA TAZARNI FARDAN WA 'ANTA KHAIRUL WARISIYN, *RABBI HABLI MINLA DUNKA ZURRIYATAN 'DAYYIBA INNAKA SAMI'UDDU'AH, *RABBHI HABLI MINASSWALIHIEYN_ Da dai sauransu, haka kuma tace ta yawaita istigfari da fad'ar _*YAA HAYYU YAA QAYYUM_ insha Allah komai zai wuce kamar ba'ayi ba, sosai kuwa Batool ta maida hankali tare da tsananta addu'o'in cike da imani da kuma yak'inin cewa Allah zai karb'ar mata,
kowa ma dai yana tausayawa Batool ganin cewa tad'an jima bata samu k'aruwa ba don haka tako ina ake tayata addu'ar Allah yabata nata zuriar.

Mahmud kuwa tuni ya bud'e sabuwar rayuwa da shafin soyayya shida Billynsa, wata irin kulawa da soyayya mai k'arfi yake yimata wacce gaba d'aya tasa ta sanar cemasa, matuk'ar suna zaune atare Billy batada wajen zama idan ba a jikinsa ba, wani lokacin haka zaauyita rigimar haye jikin mahmud ita da little yayita yimasu dariya, yauma zaune yake yana kallo ya hangosu aguje suna tsere tseren iskosa, da sauri yabud'ewa little hannuwa tana gab da kawowa ya juyar da hannuwansa zuwa inda Billy tafad'a ya rungumeta sunata yiwa little dariya, dukanta dady tafarayi tana k'ok'arin sai ya sake Billy, tashi Billy tayi had'e da cewa

"Oya musake tunda baki yarda ba" komawa baya sukayi suka sake rugowa ya bud'e hannuwansa har Billy takusa kaiwa yayi saurin juya hannuwansa little tafad'a tanata dariya har da suyiwa mommah Billy dariya.

Fridge ya bud'e ya ciro ruwa yabawa Billy tasha saboda hakin da yaji tanayi, bayan tasha tab'a little itama tasha sannan duk suka zube k'asa suna faman nishi ahankali, ganin wasa naneman canzawa yasa Mahmud ya d'auki little yakai wajen Umma sannan yadawo sukaci gaba da farantawa juna.

Satin mahmud biyu hutun daya d'auka yak'are don haka yafara shire shiren komawa, nan su Umma da alhaji suka sanar dashi yanda akayi akan zancen karatun Billy wanda gaba d'aya shi yama manta da tanayi balle ya tambayeta.

Nan take ya d'aga tafiyar bayan yaroki alfarmar da akara masa sati d'aya wajen aikinsa bisa wani dalili kuma suka amince masa don basa son surasashi saboda ba k'aramin cigaba yake kawowa a kamfanin nasu ba, cikin satin yayi cukucukun had'a bizar Billy data little don yace bazai barta ba da ita zasu wuce.

Ana saura kwan biyu jirginsu ya tashi sukaje kd gaida su dady, yanda Ummi taga 'yarta yatabbatar mata da tana samun farinciki sosai, hakan yasa tak'ara samun natsuwa azuciyarta, gaba d'aya sun canza da ita har little, da suka tashi tafiya mom tasake had'a mata kaya masu kyau sannan suka rakasu da dad'ad'an addu'o'i masu kyau amatsayinsu na iyaye, gidan yaya Mahmud sukaje sannan suka biya gidan papi, Basu wani jima ba suka nufi gidan Batool inda tsabar farinciki kasa hak'uri Billy tayi har su isa da d'an gudu gudu tahaye saman tana kiran my twiny, itama da gudun tafito suka rungume juna, duk da yanda Mahmud baiso sujima ba dole yayi hak'uri sukasha firarsu ta 'yan uwa sunaji tamkar karsu rabu, suna fita sukayi gidansu baba k'arami suma suka gaishesu bayan Mahmud yayi masu alkhairi sannan sukayi masu bankwana suka koma gida safiya na wayewa suka kama hanyar borno saboda gobe tunda safe jirginsu zai tashi,

Muhib ma yayi wayau sosai don har ansashi makaranta, yauma kamar kullum yaya Ahmad yaje d'aukosa yasamu wani abokinsa nata dukansa amma yak'yalesa sai faman kuka yakeyi, tsabar takaici Dr Ahmad kasa cewa komai yayi saida ya d'aukosa yasashi cikin mota, fad'a yayi masa sosai tare da cewa karya sake yakoma zuwa d'aukosa ya isko ana dukansa yana kuka, indai bai iya hak'uri to dolene yarama yagaji da sanyin halinsa.

Har zai wuce ya hango wani mutum cikin motar kanta yatsaya shan mai awani gidan mai kamar Alhaji tukur wato mahaifin muhib, parking yayi agefe yashiga gidan man yana regen fuskarsa aikuwa suna had'a ido alhaji tukur ya washe baki tare da mik'a masa hannu suka gaisa yana tambayarsa ya mamynsa take, tsabar kawaici har suka gama gaisawa bai tambayesa labarin Muhib ba Saida dr.ahmadda kansa yaje yafito dashi cikin motar yakawo masashi, Allah sarki d'a da mahaifi sai Allah, Alhaji tukur na ganinsa ya d'aukesa cike da so, sak fuskar mahaifiyarsa yagani atattare dashi wanda hakan yasa yatuno masa da ita, acan gefen gidan man suka samu waje suka zauna suna tattaunawa inda daga k'arshe dr.ahmadya karb'i address d'insa tare da lambar wayarsa bayan ya nuna masa irin rashin jindad'in da baiyi ba natafiyarsa da yayi wancan karon batare da aun had'uba, kallon Alhaji tukur Muhib yayi had'e da cewa

"Yaya waye wannan?" Rik'osa Dr Ahmad yayi had'e da cewa

"Muhib wannan shine mahaifinka ni kuma yayanka" sannan ya juya ga alhaji tukur yace "kaji abunda ake gudu ace d'anka na cikinka bai sanka ba, ai abun akwai kunya" nan dai sukaci gaba da zantawa har yake basa labarin yayi aure, kafin su d'unguma suje gida tare bayan Alhaji tukur ya bada ajiyar motarsa kafin yadawo, sosai mamy tasha mamakin ganinsa nan aka kira Batool tare da gabatar masa dashi amatsayin mahaifin Muhib. Nan dai yayi masu sallama tare da alk'awarin zai dinga kira kuma idan yashigo zai samu lokaci yadinga kawo masu ziyara
Sannan ya wuce bayan Dr. Ahmad yayi masa alkhairi

Tuni jirginsu Billy ya isa a delhi birnin India tun kwana uku da suka wuce, inda suna isa da sati d'aya batare da b'ata lokaciba ya nemawa Billy gurbin karatu a wata makaranta mai suna _priya higher institution_ haka ma little ya sama mata makaranta daidai k'arfinsa batare daya k'ure kansa ba tunda yanayin tsarin karatunsu ba d'aya yake dana k'asarmu ba, cikin wata d'aya suka fara zuwa makaranta kuma ba laifi suna ganewa sosai, matsalar kawai yaren sune da Basu wani ji, Wanda saida suka d'ansha wuya kafin sufara iyawa, musamman Mahmud yasama masu wanda zai dinga koyar dasu harshen nasu saboda su samu sauk'in mu'amala da mutane, haka kuma duk ranakun da baya zuwa aiki sukazo kuma aka dace da suma basa zuwa school to zai d'auke sune suyita zaga gari cikin farinciki da soyayyar juna, tsabar kamar da little keyi dasu kuwa duk inda suka shiga sai sun burgeka don bazaka tab'a yarda ace maka wai ba Billy ce mahaifiyar taba.

*_After nine (9) years_*

Abubuwa da dama sunfaru acikin rayuwar wannan family, ciki kuwa hadda komawar family na farinciki da kuma akasin haka, yaya Mahmud tuni girma yazo don yanzu yaransa biyar, mu'azzam sai Bashar wanda sukeyiwa lak'abi da abie, sai Fatima, da kuma Aisha (mami), tuni yaya Mahmud shima ya koma makaranta tyahad'o Masters d'insa under business administration, wanda saboda kwarewa da sanin harkar kasuwanci yasa arzik'in mahaifinsa yasake bunk'asa har shima sunansa yafara fitowa saboda wani katafaren kamfaninsa na kansa daya bud'e mai suna *M.BASH FURNITURES*

Ummi ma Allah yasake arzuttata da wata haihuwa bayan little Basmah tasamu Salim da Abdurrazaq sai kuma Amatullah tun tanajin kunya idan tasamu ciki har tahak'ura gaba d'aya tabarwa Allah don shine yayi mata ni'imar data kwashe tsawon shekaru tana bid'a bata samuba sai awannan lokacin don ya nuna ikonsa da kuma iyawarsa akanta.

Mom kuwa tuni tasake tsorata da kuma gano kuskurenta, gadai wacce tayita quntatawa arayuwa saboda ganin ita takeda 'ya'ya alokacin baya yanzu sai Allah mudabbirul amru, dake jujjuya al'amurransa takoma ita takeda 'ya'ya agidan yanzu, tunda ita nata duk sunriga da sun girma sunyi aure, ga Bassam ma da Bilal suma sun zama kyawawan samari dake jida kansu, kasancewar yanzu sune manya acikin gidan babu abunda dady baya yimasu sai wanda baiyi daidai da tarbiyar musulunci ba, yanzu haka suna youganda wajen had'o degree d'insu yayinda little Basmah itama tagirma don yanzu haka tana cikin shekara ta goma sha biyu kuma ashekarar nan zataje j.s.s one, gaba d'aya kamarta sak da Basmah tafad'a fitowa babu abunda ya banban tasu illa 'yar k'iba kad'an da little Basmah ta d'ara waccan Basmah d'in.

Jaddi ma Allah yayi masa rasuwa faraaha tayi kuka sosai har tana kallon kanta amatsayin marainiyar da tarasa gata, amma cikin qanqanin lokaci Mahmud yashafe mata wannan tunani aranta don kuwa duk wata kulawa da gata da macce kenema ita da 'ya'yanta agidan mijinta yabata kuma ita da kanta tasan Allah ya d'aukaka darajarta acikin sauran mata 'yan uwanta shiyasa akoda yaushe take alfahari da Allah ya mallaka matashi amatsayin miji kuma uban 'ya'yanta.

Tuni Billy itama tashiga sahun manyan mata dake amsa sunansu, don tun shekara hud'u da suka wuce bayan Billy tayi nasarar kammala karatunsu a fannin likitanci inda tayi specialising akan harkar kula da matsalolin mata wato "gynecology" nan suka tattaro inasu inasu suka baro India suka dawo mahaifarsu, duk tsawon wud'annan shekarun da suka kwashe haihuwarta biyu mace da namiji,saboda yanayin karatun nata dake buk'atar kulawa da kuma maida hankali, first born d'inta mace sunanta hafsat suna kiranta da (ilham) sai kuma namijin shi kuma mahmud suna kiransa (Abbaty), little Billy kuwa angirma sosai don idan kaganta zaka d'auka girmanta yafi k'arfin shekarun da take dasu, yarinya mai natsuwa tare hankali, gaba d'aya kamannin mahifinta da take dasu tun tana yarinya babu abunda yacanza saima sake bayyana da sukayi, gashi Allah yabata basira da hazak'a, batada hayani shiyasa bata cika son shiga mutaneba kullum tana gida tare da mommah d'inta, hakan yasa duk lokacin da sukaje k.d su amatullah dasu salim ke kama kansu har saita baro garin don sunsan hukunci da zai biyo bayansu idan suka cikata da hayaniya, ko kad'an ba'a b'oye mata rasuwar mahaifiyar taba don tun tanada shekara uku aduniya suka tarbiyantar da ita akan muhimmanci mahaifiya, wannan dalilinne yasa lokacin da tasan cewa tata mahaifiyar bata raye kullum take yimata addu'a Allah yajik'anta da rahama kuma ya gafarta mata, hatta Billy bata mantawa da ita cikin addau'arta tana rik'on Allah ya tsawaita mata rayuwarta bisa kulawa da soyayya da kuma tarbiyar da take bata.

Tunda su Billy suka dawo tamaida hankali wajen taimakon 'yar uwarta wajen aika mata da magungunan dake taimakawa k'wayak'wayin haihuwar ta suk'ara k'arfi tare da magunan dake k'ara vitamin ajiki duk dako tasan cewa batada wata matsala kamar yanda bin cike ya nuna, amma kasancewar batada babban buri daya wuce taga itama 'yar uwarta Allah yabata haihuwa kamar yanda kowanensu keda ita, kimanin shekara hud'u kenan ana abu d'aya amma billy bata gazaba haka itama Batool bata gaki da shan magungunan ba had'e da yin addu'a har Allah itama yabata nata rabon, farinciki awajen dr Ahmad mamy da mom baya fad'uwa balle Billy dako da yaushe bakinta baya gajiya da addu'ar Allah yaba 'yar uwarta haihuwa, nan take family yad'au murna da farinciki don dama burinsu kenan suga jinin Batool aduniya, haka tab'angaren dady shima yayi farinciki tare da fatar Allah ya inganta kuma ya sauketa lafiya, cikin Batool ya zama d'an gata kuma d'an lele tako wane b'angare baranma daya fara girma akayo scanning akace 'yan biyune, wata irin tarairaya da lici take sha awurin a dr Ahmad, motsi kad'an zatayi saiya binciki lafiyarta har zuwa lokacin da cikin yakai wata tara, zama da k'yar tashi da k'yar haka Batool kefama gashi k'afafuwanta duk sun kumbura saboda nauyi da girman da cikin yayi mata sosai, yana neman fitowa ako wane lokaci, yau ana gama sallar asuba tatashi cikin wani matsanancin ciwon mara ga amai da taketa famanyi abun gwanin ban tausayi, hakan yasa dr.Ahmad yanufi part d'in daya k'ank'arawa mamynsa acikin gidan don tuni dama sunkoma sabon gidan daya gina masu naji da gani, yana shiga ya sanar da ita halin da Batool d'in keciki lokacin tana jan tarbaha, da sauri ta tashi cikin rud'ewa tace "subhanallahi wuce muje" tafad'a tana bin bayansa.

Suna isa mamy tace "assha sannu fatima ai gawar bakace takeyi da alama yau insha Allah komeye keciki zai fito" dr najin haka yace "mamy kina nufin haihuwa ce?"

"Eh mana, ai wannan aman da takeyi fawar bakice ko yaushe haihuwa na kusa" ai yanajin haka hankalinsa yatashi don tuni Billy tafad'a masa cewa kada abari tayi yunk'urin haihuwa da kanta tunda haihuwar farice kuma tajima batayiba komai zai iya faruwa,

Nan take shida mamy suka d'auketa suka kai cikin mota sukayi asibiti da ita, suna isa yasa hannu aka shiga tiyata da ita, bayan mintota da basu haura sama da talatinba sai gashi anfito mata da jariranta guda biyu namiji da mace manya manya dasu tubarkallah sai faman tsala kuka sukeyi alamun sunada cikakkiyar lafiya.

Tsayawa fad'ar irin farincikin da dr da mamy suka shiga b'ata lokacine don mamy bakinta kasa rufuwa yayi saboda murna yau gata ga jikokinta har biyu da Allah yayi mata ni'ima dasu lokaci d'aya.

Nan take dr yakira dady da yaya Mahmud yasanar dasu, cikin d'an k'ank'anen lokaci family ya d'au murna Batool tahaifi 'yan biyu, Allah kenan dama dukkanin mahak'urci mawadaci ne, kimanin shekara goma sha biyu kenan da aurensu bata tab'a b'atan wata ba, sai gashi yau hakurinta da tawakkali ga ubangijinta yajawo mata Allah yayi mata ni'ima da kyautar 'ya'ya biyu alokaci d'aya.

Kafin kace me tuni asibiti tacika da 'yan uwa da abokanan arzik'i wajen tayasu murnar wannan kyauta da Allah yayi masu.

Billy kuwa tsabar farinciki jitayi kamar ta take kan jariri, jitake inama zata iya tsuntsuwa taganta agarin k.d da yau babu abunda zai hanata kwana tare da 'yar uwarta, gaba d'aya ita da yaranta sun rud'e gidan da murnar haihuwar dama tuni suka matsu ahaihu don suje kd wajen grannys d'insu abbansu nacewa suyi hak'uri har sai anyi hutu idan mommah Batool tahaihu, shiyasa yau da ita dasu baka iya banbance wayafi farinciki da murna, jitayi Mahmud yajawo hannunta yayi wajen corridor d'in da zai sadaka da bedroom had'e da matseta ajikin bango yana kallon k'wayar idanuwanta d'aya bayan d'aya saboda mamakin yanda yaga tagame ita da yaran sai wasar baki takeyi gaba d'aya ta manta dashi ad'aki kafin yace

"Wai kina nufin duk wannan murnar da kukeyi wa haihuwar Batool ne shiyasa har kika manta dani ad'aki?" Rik'o kwalar rigarsa tayi tana kashesa da wani irin mayen kallo da yasa yaji duk jikinsa ya mace sannan itama tafara turasa izuwa d'ayan bangon tana kallonsa kamar yanda yayi mata tace

"Fad'amun are we not deserve to be happy" tana k'ok'arin aza bakinta akan lab'b'ansa, kamar wani sakarai yasaki baki yana kallonta had'e da rufe idanuwansa yabud'e sannan yatura hannunsa ta bayanta asaman kunkurunta yajawota da k'arfi yahad'e da jikinsa, yanda yaga tana k'yafk'yaf da idanuwa shiya bashi dariya had'e da cewa

"Matsoraciya! Wish ace nima nasamama twins d'in Batool k'anne acikin plat tummy d'innan naki" ya k'arasa maganar yana shafa k'asan cikinta, murmushi tayi kafin tace

"Badai za'aji mutuwar sarki abakina ba, amma kabari idan tayi wari kaji" tana gama fad'ar haka tajuya zatabar wajen tana dariya da sauri yarik'o hannunta don idan har hasashensa yayi daidai da kalamanta kenan tanada ciki, ahankali cikin son ta gasgatasa yace

"K'anwata kina nufin akwai ajiyata atare dake?" Batare data juyoba ta kad'a masa kai, wani irin farincikine ya dira azuciyarsa saikace wannan shine karo nafarko yajawota tafad'a masa ajiki yad'ago fuskarta had'e da cewa

"Da gaske kikeyi noorul hayat?"

Kwace jikinta tayi tare da sake kad'a masa kai sannan tabar wajen tana murmushi tare dajin dad'i akan yanda akoda yaushe yake nuna mata zallar soyuwarsa da kwad'aituwarsa akan abunda zata haifa idan tasamu ciki,

Murmushin shima yayi tare da furta "Alhamdulillah Allah bisa wannan kyauta daka k'ara yimun, ya Allah kasauketa lafiya kuma kabamu ikon tarbiyantar da zuriar daka bamu, ka albarkaci rayuwarsu data dukkanin 'ya'yan musulmi baki d'ai" jitayi an amsa da "amin" ta bayansa juyowar da zaiyi yaga ashe Ilham da abbaty ne da tund'azu suke tsaye suna sauraronsa suka amsa masa suna dariya, saida shima yayi dariyar sannan yayi kamar zai biyosu ya dukesu da gudu sukabar wajen had'e da tserewa suka nufi gidan Umma,

Kitchen yanufa inda ya hango Billy tare da little suna k'ok'arin had'a dinner, yana shiga ya dafa kan little tare da cewa

"Little baba, me ake dafamun?" 'Dago kanta tayi tana kallonsa tare dayin murmushi, kafin tajuya ta wanke hannunta tare dasa kitchen towel d'in dake lak'e ajikin kusa tagoge sannan tace

"Mommah d'in little ke girki Abba bani ba, ni koyo nakeyi tare da rik'a mata 'yan wasu abubuwa" murmushi yasakar mata had'e da bubbuga kafad'arta yace

"Gud girl, Allah yayi maki albarka, haka akeson 'ya'yan K'warai"

"Amin Abba" tafad'a sannan tajuya tare da kallon Billy tace

"Mommanah natafi wajen Umma"

"To kigaishe mani da ita sosai kafin inshigo" Billy ta amsa mata sannan tafice abunta, ai kamar jira yakeyi tafita yazo ya rungomo Billy tabayanta had'e da kurd'o kansa ta wuyanta yace

"K'anwata baki fad'amun ko wata nawa bane ko saina biya?" Yana maganar yana kissing gefen wuyanta, motsa stew d'inta taci gaba dayi batare data d'agoba had'e da cewa

"Ka k'idanya mana kagani adadin yaranka shine watannin babynka including him" cike da farinciki ya d'agata yana jujjuyata ahankali yana fad'in

"Iyyeee..you mean 4month kenan! Wow this baby is a miracle baby, gaba d'aya nakasa fahimtar cewa kinada juna biyu saboda lafiyarsa sai yanzu da kika fad'a, kai Alhamdulillah no wahala, no amai, no any malaises, zamuyi renon abunmu in a peace" Shiru yayi had'e da tunowa da takardar daya tsinta cikin kayansa da Basmah ta ajiye lokacin da zasu maidata gida.

_salam yaya, don Allah idan namutu kada ka auri kowace mace face Bilkisu tabbas zakayi farinciki da ita har iya k'arshen rayuwarka, ina fatar zaka cikamun wannan alk'awarin bayan raina_

Sosai yasake rungumeta ajikinsa aransa yana cewa "kinyi gaskiya Basmah ubangiji Allah yajik'anki ya gafarta maki" ji yayi billy ta amsa da "amin" ashe har maganar zucin da yayi tafito fili.

Turo baki tayi cikin shagwab'a had'e da cewa

"To ka saukeni mana kada garin wannan farinciki naka yasa stew d'ina tak'one" ahankali ya sauketa ta motsa miyar sannan ya juyo da ita ya rik'o fuskarta yana yimata kissing d'inta tako ina har saida yagaji don kansa sannan yace

"You have been the first and will be the only one ever to touch my heart. Ever since the day i met you, my heart stopped beating for me. It beats for you alwas saying i love you with every beat, ina sonki sosai mommah little, ubangiji Allah yayi maki albarka, kuma ya saukeki lafiya" rufe idanuwanta tayi sannan ta bud'e cike da jin dad'in kalamansa da suka daki zuciyarta tace

"Nima ina sonka sosai abban little" rungume junansu sukayi alokaci d'aya kowa najin shine mafi sa'ar abokin rayuwa aduniya.

Bayan kwana uku da yiwa Batool CS aka sallameta, don taji sauk'i sosai, kasancewar tiyatar tayanzu ansamu cigaba bakamar daba, mamy na kimtsar kayansu najinya ita da faraaha saiga dr Ahmad yashigo, ba kunya yaje gefen gadon da Batool kezaune rik'e da hassan tana bashi nono, kallo d'aya tayi masa takauda kai don itakam bata son yanayi mata hakan agaban mamy, shikam dako ajikinsa ya d'auko hussainar dake kwance bisa d'an gadonsu na jarirai yace

"Kinba momynmu tasha kuwa?" Banza tayi dashi yay murmushi yana shafa fuskar babyn don kar yafahimci metake yiwa, faraahace ta d'ago kai tana kallonsa had'e da cewa

"Oh ni dr! Gaskiya rawar kannan naka yayi yawa, kai daya kamata ka tausayawa qanwata amma kai saita d'iyanka kakeyi ko kunyar mamy baka ji?" Saida yaduba gefe gefen d'akin yaga ashe mamy tafita sannan yace

"Kunyar mezanji sister nida 'ya'yanah?, kawai wanda bazai iya gani ba ya kauda kai?" Turo idanuwa faraaha tayi tana dariya had'e da cewa

"Ahhh...lallai abunka azimunne dr, koda yake da gaskiyarka, 'ya'ya rahamane"

"Yawwa sister zaki iya tuna ranar da kika had'ani da fatima awaya, ranar da nagabatar mata da kaina nace maki kici tukuici awajena zaki iya tunawa?"

Shiru tayi kafin can ta d'aga masa kai had'e da cewa

"Yes natuna meyafaru yanzu?"

"Babu komai, dama nasa araina idan Batool tahaifamun 'ya mace zanyi maki takwara Inaa mata faraaha amatsayin goron tukuicinki to sai gashi sunzo su biyu, amma duk da kasancewarsu su biyu

Please Login or Register in order to submit comment