Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwa da abokan arziki, ina muku fatan alkairi a duk inda kuke. Ayi min afuwa na jina kwana biyu shiru da aka yi hakan ya samu asali ne daga wayar, yanzu ma zakuji ni shiru sai yadda hali yayi sabida taki yin dai-dai ko nayi typing dana bud'e data zai goge ayi min afuwa see you next insha Allah na gode....*😘









Mrs Huss@in✍🏻

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NANE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_*Gisuwa mai yawa tare da fatar alkhairi ga d'aukacin masoya wannan littafi, ngd bisa jajircewarku da k'aunar da kuka nuna agareni da kuma wannan lbri mai suna 'YAN UWA NANE! kuma ina yiwa kowa barka da sallah tare da fatar kowa yayi sallah lpy, in sha Allah zaku cigaba da jini akai akai*_

πŸ’ŽPage_____8πŸ’Ž


Da sauri billy tanufi wajen Ummi rik'e da kunnuwa har lokacin tana dariya

"Sorry ummina nice fa, Bilkisunki ta annabi mai gadon zinari" Cikin soyayya Ummi ta d'aga hannunta kamar zata doketa dady yayi saurin jawota har lokacin shima yana dariya

"Haba madan ayimata hak'uri kar asa jinin dady ya hau" kafin ummi ta amsa har dady ya maido kallonsa ga Billy fuskarnan tasa ad'aure kamar bashine yagama dariya yanzu ba, cikin natsuwa yake tambayarta

"Bilkisu me yafaru tsakaninki da auntynki basmah" shiru billy tayi kanta sunkuye ak'asa kafin tajiyo muryar dady yana sake jefo mata tambayar da k'arfi, nan take tayi masa bayanin duk abunda yafaru batare da tayi k'ari ko ragi ba, hannunta dady ya saki had'e da jawo hannun bilal dake rungume ajikin Ummi

"Bilal! Shin gaskiya ne auntynka ta fad'a?"

"Eh dady, amma mun bata hak'uri ko aunty billy" ya k'arasa maganar yana kallon 'yar uwarsa da nan take ta gyad'a masa kai.

Murmushi dady yayi had'e da cewa

"Very good! Amma ina so daga yau Bilkisu dake da bilal karku sake musayar magana da 'yan uwanku hakan d'abiace Marar kyau kunji ko?Ke Bilkisu Basmah Auntyn kuce bakyau ace kina mayar mata da magana akan zata yiwa qanenta hukunci, amma duk lokacin da kikaga tayi abunda ya cutar daku to kifad'amun kinji ko?

"Eh dady, kayi hak'uri bazan k'araba in sha Allah"

"That's my dota, haka nake so, Allah yayi maku albarka"

"Amin dady"

"Oya jeki kishiryawa bilal kema kishirya kafin ingama magana da umminku zamu fita" tsalle Bilkisu tayi tare da cewa dady hadda Yaya Mahmud zamuje?

"Eh idan kunshirya kije kifad'a masa duk da nasan dak'yar inzai iya tunda jikin nasa ba mafita" da gudu billy taja hannun bilal suka nufi bedroom d'in Ummi shi kuma dady ya dawo sit d'in da take zaune kanta ak'asa tana tunanin matsalolin da suke fuskanta agidan na rashin zama lafiya, hannu yasa akan hab'arta tare da d'ago fuskarta tana kallon tasa, lumshe idanunsa yayi ya rufesu tare da bud'esu ya d'age mata gira yana murmushi yace


"Me uwar gidana ke tunani ne?" Murmushin itama tayi sannan tace

"Abunda zai faranta farincikin mai gidanta"

Dariya dady yayi tare da d'ora yatsansa akan lab'b'anta ganin tana k'ok'arin yimasa bayani akan maganar da yagamayi da yaransa

"A'a Aisha kibar maganar a haka, nadad'e da fahimtar komai, nasan bazaki tab'ayin abunda zai raba kan 'ya'ya naba indai ba sharrin shayd'an ya gitta ba"

"Nagode da fahimtata da dyn Mahmud"

Tana rufe baki sai ga Mahmud yashigo falon, ganin yanda suke zaune so close ya sashi saurin juyawa da sauri

"Come in my son" dady yafad'a da k'arfi had'e da mik'ewa tsaye yana mai farincikin ganin d'an nasa da yake matuk'ar k'auna da kuma alfahari a zuciyarsa, kansa duk'e a k'asa ya k'araso d'akin had'e da gaida Ummi

"Ummi ina wuni?"

"Lafiya k'alau yayan B, ya karfin jikin naka?"

"Alhmdulillah Ummi naji sauk'i ya k'ok'ari?"

"Allah ya k'ara lafiya"

"Amin Ummi, inasu lil sis ne naji gidan shiru" yana rufe baki sai gasu billy sun fito cikin shirinsu suna k'amshi, da gudu bilal ya rugo Mahmud ya cab'esa sama yana fad'in

"Eyyee yaron Ummi, wannan gayu sai ina haka?"

Hannu dady yasa a kafad'ar Mahmud dake k'ok'arin sauke bilal ya lak'amo Mahmud yana fad'in...







Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NANE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____9πŸ’Ž


My son ya jikin naka? hope kasamu sauk'i?

"Alhmdulillah dady it's just a little worry dake damuna"

"Being patient my son, in sha Allah komai zai wuce, abunda nakeso dakai shine kaje ka gyaro zamu fita da kai da kuma k'annenka"

"OK dady bari nashiryo" part d'insa ya wuce shi kuma dady yanufi part d'in Small mom, yana shiga ya tadda batool zaune Small mom na gyara mata gashinta shi kuma bassam yana kallon k'wallo gyaran murya yayi bayan ya shigo, cikin gadara Small mom tad'ago kanta tace

"Alhaji kaji tsoron Allah, yanzu abunda kakeyi daidai ne?, ka dubi tun lokacin da kabar part d'innan kanufi part d'in waccan algungumar munafuka ace sai
yanzu zama fito kusan awa d'ayafa kenan kana can kabiyewa k'ananan yara kuna faman dariya sai kace mahaukata, wlh alhaji baka kyautawa"

Batare da dady ya kalli inda takeba ya k'wallawa basmah kira, da sauri tafito daga cikin bedroom d'inta daga ita sai bes da mini siket kanta babu d'an kwali, dady na kallonta ya d'auke kansa sannan yace

"Ki gyara keda qannenki zamu fita"

"Dady ina zamuje ne?" Kallon ta ya sakeyi cikin jin haushin shigar da take ciki yace

"Idan baza kujeba kwa iyayin zaunenku, shashashar yarinya, bassam maza jeka gyara kafin in fito"

"Dady ban iya gyarawaba momy ke gyarani" bassam ne ya fad'i haka har lokacin hankalinsa na akan TV da yake kallo, tsananin takaici yasa dady juyawa yabar part d'in, dariya basmah tayi had'e da cewa

"Cab wlh mom dady ya iya fitina yanzu, daga tambaya shikenan sai ya rufeni da fad'a, shin waima ina zamu jene?"

"Kema dai kyafad'a basmah! ai kune abokanan fad'ansa amma kar kiso kiji yanda yake k'yak'yata dariya da wud'an can jinin mayu" da sauri batool tace

"Cikamun kai nidai mom, wlh Allah idan bamu gyara da wuriba dady tafiyarsa zaiyi kuma munaji muna gani zai fita dasu billy yabarmu gida kuma nikam da haka tafaru k'ara shegen gashin can na yayyah basmah ya tsittsinke" cikin zafin rai basmah tanufo batool tare da finciko gashin kanta

"Bari nafara tsinke naki gashin kafin nawan da kikeyiwa fatan tsinkewa ya tsinke, muguwar yarinya kawai" nan fa suka kacame da rigima suna faman zagin junansu, ana haka saiga Mahmud ya shigo rik'e da hannun bilal, da gudu bilal yanufi wurin bassam yayinda shi kuma Mahmud ya nufi wajen dasu batool ke rigima yana fad'in

"Ke, ke me kuke yine haka, mom dube su kigani sai kace kaji kuma kinsa masu ido, wlh basmah idan baki cikataba saina zazzaneki agidan nan, wannan wane irin rashin mutuncine, kizauna kina fad'a da k'anwarki?" Turo baki tayi tana fitar da lumfashi dakyar kamar wacce tayi wasar athletic s competition

"Yaya aradu wannan yarinyar batada kirki, wai ni take yiwa fatan gashina ya tsittsinke don tana marar kunya"

"Keep quite, stupid girl nizan ida cika fatan da take yimaki tunda bakyason zama da head tied, banda iskanci dubi yanda jikinki yake amma har kya iya fitowa ahaka wlh mom gab nake da b'ab'b'alla yarinyar nan, zaku wucene ku shirya ko sai na b'ata maku rai" gwalo batool tayiwa basmah had'e da dariya sannan kowace ta nufi d'akinta har sun wuce ya jawo batool ta baya yace

"Ke ko? idan na rik'aki zaki game kurenki tunda kin zama marar kunya" soko ya sakar mata had'e da tureta da kad'an ta fad'awa mom, da gudu tabar falon shi kuma mom ta jefo masa harara cikin b'acin rai

"My son kamaida hankalinka, wai meyasa kafiye son takurawa Yaran nan, shikenan kai kullum bakada aiki sai cin zalinsu" a hankali ya tako har inda take zaune shima ya zauna tare da rik'o hannunta

"Mom ya kamata kifahimci cewa su 'YAN UWA NANE ina matuk'ar sonsu shiyasa nake yimasu haka, duk wannan abun da nake yimasu inayine saboda in daidaita rayuwarsu badon in takura masu ba"


"Shikenan naji amma meyasa baka lallaahinsu idan sunyi laifi kamar yanda kake yiwa waccan ma...." Da sauri yarufe mata baki saboda bayason kalmar da zata fad'a mararsa dad'i akan qanwarsa Bilkisu

"Kiyi hak'uri mom in sha Allah suma zan dinga lallashinsu matuk'ar sun gyara in kuma sukak'i dukane zai rabani dasu" kunnensa mom ta murd'e yayi saurin cewa


"Washhh...mom harkin manta da yaronki ba lafiya shine kike neman ciremun kunne?" Sai a lokacin mom ta tuna da rashin lafiyarsa saboda abunda yafaru d'azu data tafito wajen ganinsa ba k'aramin b'ata mata rai yayi ba.

"Ayya sorry my son, ya jikin naka?"

"Am ok mom, nasamu sauk'i alhmdulillah, zamu fita da dady kuma tuwon alkama nake son ci"

"To ku tsaya a restaurant kaci mana kafin kudawo don bazan iya dafashi ba, kannen kama ka nema masu abunda zasuci ni bacci nakeji"

"Pls mom kitaimaka kinsan bazan iya cin abincin waje inba dole ba"

"Haba my son baccifa nace maka zanyi, ko kana son takura nine?"

"Noo..shikenan mom bari mutafi" rai ab'ace yabar falon har yana cin karo da Billy dake k'ok'arin shigowa da gudu

"Washhh.." Tafad'a tana k'ok'arin fad'uwa, da sauri ya tarota


"Sannu lil sis, meyasa kike son gudune ko nauyin jikinki bakyaji, nakusa fara dukanki idan baki dena wannan d'abi'ar ba"

"Sorry dady ne yace in kiraka" tana rufe baki suka had'a ido da mom dake bakin k'ofa rik'e da hannun bilal tana shirin ingizo k'eyarsa waje, sunkuyar da kanta tayi yayinda mom tayi kamar batasan da itaba tace


"Maza wuce kabar nan munafukin yaro, shine zakaje ka tsaresa kuna kallo don bak'in hali bacin kaga ba'a shirya masa ba ga dadynku najiransa" baki abud'e Mahmud ke kallon mom kafin yaje yakamo hannun bilal subar wajen,

Cike da tsana mom ta sake dallawa Billy hararar datasa tabar wajen itama da sauri

Kusan mintuna ashirin su dady sukayi suna jiran fitowar su basmah, can Mahmud ya hangosu tafe basmah saye da wata pitet street gown an tsaga rigar tabaya gashi ta matseta tako ina sannan ta yafo wani siririn mayafin da ko wuyanta bai ida rufewa ba ita kuma batool, a tsorace dady ya kalleta sannan ya maido kallonsa ga Mahmud fuskarsa d'auke da ayar tambaya. Duk'ar da kai Mahmud yayi sannan yafito cikin mortar ransa ab'ace ya nufi inda suke, batool da bassam na ganin haka suka rugo suka shiga cikin mota yayinda basmah taci gaba da tafiyarta cikin hankali kwance duk da zuciyarta cike take da tsoron yanayin da tagansa amma saboda yanayin rigar dake jikinta kotaso tayi gudu hakan bazai yuyuba shi yasa taci gaba da tafiyarta, kafin ta k'araso taga yafara ciro belt d'in dake jikinsa da baya da baya tafara ja amma ina kafin ta ankara har ya cimmata, dukanta yakeyi har saida tafad'i k'asa tana ihu, mom ce tafito aguje tana fad'in.....




















Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Tabbas d'aid'ai kun mutanen k'warai ne kad'ai zasuga kayi wani kuskure acikin alamurranka suyi k'ok'arin yimaka gyara don cigabanka, hak'ik'a zuciyata na matuk'ar alfahari da samunku acikin rayuwata MOM XOXO, SANAH S MATAZU da kuma KHAIRAT UP nagode sosai bisa gyaran da kuka yimun na sunan littafina daga *'Yan uwa nane* zuwa *'Yan uwa na ne* saboda haka readers zamuci gaba da littafinmu da wancan sunan da muka gyaraπŸ‘† ubangiji Allah ya tabbatar da alk'alummammu akan dai dai amin_πŸ‘πŸ»


πŸ’ŽPage_____10πŸ’Ž


Amma kai Mahmud yaron banza ne, zaka k'yalemun yarinya ko saina sameka wajen, gaba d'aya idanunsa sun rufe ko sauraren abunda mom ke cewa batayi sai jibgarta yakeyi, ihun da Ummi taji yayi yawa yasa itama tafito part d'inta aguje tana kawowa mom na kawowa, cikin fushi mom ta finciko sa tare da d'aukesa wani zazzafan mari ita kuma Ummi ta duk'a ta d'auke basmah dake kwance k'asa lagyagya tana kuka.

"Wlh Mahmud ina kusa da in yafeka akan yarana, inyaso kaje ka sake wata uwar an fad'a maka cewa ita jakace da zaka rufeta da duka haka, meye tayi makane inba tsabar tsana da kake yimata ba, an riga ansa maka tsabar 'yan uwanka baka sonsu baka k'aunarsu" afusace ta jiyo ta anshe basmah dake rungume ajikin Ummi tana kuka ta hankad'e Ummi har saida takusa fad'uwa Mahmud yayi saurin tarota.

"Duk abunda yafaru kece sila don kece kika rabamun kan 'ya'ya, kuma wlh sai na tabbatar da nasakaki nadamar aikata haka, kin sawa uba tsanar 'ya'yansa yanaji yana gani za'a illatata gashi zaune amma tsabar k'iyayya ya kasa magana" ta k'arasa maganar tana kallon dady dake zaune cikin mota yana kallon duk abunda ke faruwa,

"Haba mom wai me kike fad'a hakane, yanzu meye laifin Ummi ko kina tunanin ita zatasa in aikata haka?, to kinyi kuskure kullum bata fatar taga Allah ya had'a kanmu, Amma kidubi shigar da basmah tayi sai kace ba d'iyar musulmi ba, shin hakan da tayi mom tarbiyace, shin me kike tunani idan tafita maza suka kalleta, komaifa na iya faruwa, masha fad'a mata tadena shigar banza batada amfani zata iya haifar mata da matsalar da sai tashafi kowa agidan nan especially ku iyayenmu.."

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, yanzu Mahmud lalacewar taka har takai haka, da kanka kake kamanta 'yar uwarka da arniya, kake yimata muguwar fata to da yardar Allah baza kaga haka ba, mugun bakinka ya sauka akan munafukar dake son rabaku"

Jin miyagun suruttan da mom keyi sunyi yawa yasa dady fitowa cikin motar a fusace ya buga gambun da k'arfi ya rufe sannan yabar wajen ya nufi part d'insa ransa a b'ace.

"Kin gani ko mom, duk hak'urin dady saida kika fusatasa, kidena d'aurewa basmah abunda takeyi is not good at all"

Hannun Ummi yaja suka nufi part d'inta yana bata hak'uri akan abunda mom tayi mata

"Bakomai Babanah rashin fahimta ne ya kawo haka in sha Allah with time nasan zata fahimci komai tadena aibatani da yarana"

Saida ya tabbatar Ummi bata tare da damuwar abun ko kad'an sannan ya nufi d'akin mahaifinsu, kamar dai yanda yayita lallashin Ummi haka yayi tayi da dady har sai da yaga shima damuwarsa ta rage sannan yace

"Dady zamu iya tafiya yanzu?"

"No..kabarshi nafasa fitar kaje kafito da k'annenka dake cikin mota"

"Shikenan dady don Allah kak'ara hak'uri da halin mom"

"Tun yaushe kasan nake yin hak'uri da ita tun kafin kazo duniya, bansan meke damun mom d'in kaba, Sam bata son zama lafiya narasa me hajia Aisha tayi mata data d'ora mata karan tsana, babban bak'in cikin dake damuna bai wuce yanda taraba mani kan 'ya'ya ba ta tusawa yarana tsanar 'yan uwansu sannan kuma tana neman b'ata masu tarbiya, tabbas na tafka babbn kuskure arayuwata dana kasa daidaita gidana bazan tab'a yafewa kaina ba matuk'ar namutu da bak'in cikin mamanka"


"A'a dady kadena wannan tunani, Allah shedane akan yanda kake tsaye da sha'anin gidanka, kana k'ok'ari sosai, kana matuk'ar kamanta adalci agidan nan wanda ba duk namiji ke iyayin hakaba sai jajir tacce, in sha Allah zan tayaka kula da 'yan uwana har sai na tabbatar kayi farinciki da alfaharin samunmu, mom kuma kaci gaba da addu'a zata canza da yaddar Allah"


"I hop so my son" da haka ya nufi part d'in mom maganganun dady nayi masa yawo a k'wak'walwarsa, yana shiga ya iske basmah kwance akan 3sitter idanunta arufe fuskarta ta kumbure saboda kukan da tayi, duk sai yaji ba dad'i cikin zuciyarsa gefenta ya zauna tare da d'ora hannunsa bisa kuncinta,

"Basmah!" A hankali tabud'e idanuwanta suna had'a ido dashi ta kauda fuskarta, sake juyo da fuskar tata yayi sannan ya d'ago da ita daga kwancen da take

"Am sorry basmah don't mean to hurt you at all, ked'ince kin fiye kunnen k'ashi ni bana son irin wud'annan shigar da kikeyi, zata tab'a maki mutunci na har abada but Yaya is sorry kinji? Ku 'YAN UWA NA NE ina matuk'ar sonku kawai d'abi'unku da halayenku sune bana so da zaran kun dena zaku fahimci yanda yayanmu ke matuk'ar ji daku"

A hankali takoma ta kwanta ba tare data furta masa kalma ko d'aya ba saboda yanda take jin haushinsa, murmushi yayi sannan ya nufi kitchen inda ya jiyo motsin mom tana girki yana shiga yayi hugging d'inta

"Mom me kike dafawa ne?" Shiru tayi bata cemasa komai alamun fushi takeyi dashi

"Haba mom! Ur son d'inki ke maganafa kiyi hak'uri nagane ban kyautaba dana doki k'anwata, nayi maki alk'awari daga yau bazan sake dukan taba duk abunda kike tunani bahaka bane ina matuk'ar son 'yan uwana fiye da tunaninki kuma in sha Allah zan basu kulawa ta har abada, kicire komai aranki babu mai rabani da 'yan uwana" jin kalamansa yasa ta juyowa tana kallonsa fuskarta ba yabo ba fallasa tace

"Zanyi farinciki sosai idan kalamanka suka tabbata, but nasan haka abune mai wahala matuk'ar kana tare da Aisha, tariga ta shanye.." Hannunsa yayi saurin d'orawa abakinta

"Karki fad'i haka mom, ke mahaifiya tace, banida kamarki kuma banida wanda ya kaiki aduniya, zan tabbatar maki da cewa ni yaron kine, abunda nakeso dake mom shine kiyi hak'uri ki kwantar da hankalinki"

"Shikenan ammafa ka kula wlh idan ka sab'a alkawari sai na baka mamaki don wlh kowa sai yaji ba dad'i agidannan"

"A'a mom banda dady, ya kamata ace izuwa yanzu kin kula da farincikin sa, dady na matuk'ar sonki shiyasa yake jurewa matsalolin dake faruwa don Allah ki janye munannar fahimtar da kike yi akansa"

"Dallah rufemun baki kar kasa raina ya sake b'aci"

Gudun kar tasake birkice masa yasashi fitowa yana fad'in

"Mom mai duniya Allah dai yaja zamaninki, kiyi rai kiyi k'arko mamanah"

Girgiza kai tayi had'e da sakin murmushi tsabar jin dad'in kalamansa

Batool ce ta shigo falon ranta a b'ace tana faman turar baki kamar wacce akayiwa duka, mayafin hannunta tafara jifa dashi kafin can tacire takalmin k'afarta ta watsar dasu a tsakar d'aki, inda basmah take kwance ta nufa a afusace had'e da kai mata wani irin mugun duka a cinya tana fad'in

"Muguwa kawai, wlh Allah ya isana, kurum kinyi mana asarar fita don tsabar iskanci, kin jamana asarar abunda dady zai siya mana"

Cikin zafin nama da rad'ad'in dukan da tayi mata ta tashi ta kaimata naushi abaki nan fa suka kacame da fad'a, kadan cewar Basmah na cikin b'acin rai yasa Allah ya azata akan Batool tayita dukanta, dak'yar Mahmud ya fincikota akanta yana dariya


"Enough Basmah yi hak'uri kinrama dukanki shikenan har lokacin bai dena dariyar da yakeyi ba saboda yasan dama inda zata fanshe dukan da yayi mata take nema sai gashi cikin sauk'i ta samu, fizge hannunta tayi tana faman nishi tace

"Wlh kwanan nan sai kunci duka a hannuna saboda na lura gidan nan ba'a notice d'in dukan mutum sai dai yaji saukar na jaki ajikinsa don haka sai kunsha wahala a wurina keda wancan d'an iskan yaron ta nuna Bassam da ya shigo yanzu yana tuk'uburi, wata irin muguwar harara ya watsa mata shima tare da nuna ta da d'an yatsansa

"Kece 'yar iska bani ba tunda kika ja aka fasa fita don mugunta, shikenan yanzu kinja narasa ball d'in da nakeso dady ya siyamun"

Afusace tayo kukan kura akansa Mahmud ya sake saurin rik'ota

"Kai Basmah yanzu da Bassam d'in zakiyi fad'a, sorry nasan wannan rigimar duka laifina ne amma kiyi hak'uri kinji ko?"

"But yaya Mahmud..."

"Shhhh..ko meye ai nace kiyi hak'uri ko?"

Haka dai suka dinga yimasa rigima inya lallashi wannan ya koma ga waccan har mom ta k'arasa girkinta, cikin jin dad'in yanda taganesa cikin 'yan uwansa tace


"Yau kam nayarda duk tasirin asiri sai yakarye, dubeku gwanin ban sha'awa amma don tsabar hasada ake nema araba mani kanku, dole intashi tsaye nima saboda bazan juri haka ba" Mahmud ne yace

"Mommmm..."

"Rufamun baki samna kazo kazuba abinci kaci"

"Mom kizubo mana mana muci tare"

"Bazaka iya cin abinci da Yaran nan ba don nasan halinka"


"Zan iya mana tunda su 'YAN UWA NA NE"

A tare mom tazubo masa abinci da k'annensa sukaci sannan yabar part d'in, d'akinsa ya nufa ya watso ruwa yayi sallah ya haye gadonsa don ba kad'an yakejin bacci na d'ibarsa ba, acan cikin bacci ya hango lil sis d'insa tana gudu cikin wani makeken daji tana kiran sunansa, mom d'insa kuma na gefe tana faman dariya, a firgice ya tashi baccin duk ransa ab'ace yana fad'in

" _Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, a uzubillahi minashhaid'anirrajim ya fad'a har sau uku ya tofa a hannunsa na hagu sannan ya k'ara da a'uzu bikalimatillahi tammaat, min ghadabihi, wa ik'aa bihi, wa sharri ibadihi, wamin hamazatishhayad'ini, wa anyahduruun_"

Ya matuk'ar tsoratata yanayin da yaga lil sis d'insa aciki don haka ya sauko kan gadon yasa doguwar rigarsa jalabiya sannan ya nufi part d'in Ummi zuciyarsa cike da son ganin halin da 'yar uwarsa take ciki...












Mr's huss@in✍

πŸ‘­β€ *'YAN UWA NA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____11πŸ’Ž


Yana shigowa yaci karo da Billy kwance akan cinyar Ummi tana tsefe mata kai, cike da kasala ya k'araso cikin falon, dak'yar yake takawa tamkar wanda akayiwa duka ya fad'a akan kujerar dake facing d'insu zaune yayi wata iriyar ajiyar zuciya had'e da rufe idanuwansa, tsoron dake hannun Ummi ta saki tana kallonsa yare da karantar yanayin da yake ciki,


"Babanah meke faruwa da kaine na ganka a haka?"

"Babu komai Ummi" ya fad'a ba tare daya bud'e idanuwan saba, murmushi tayi sannan tace

"Allah yasa haka"

"Amin Ummi, lil sis ina abokin rigimar naki"

"Gashi can a kwance, inagan yayi bacci tun d'azu da muka dawo"

"Ayya! Yawwa ya naga ke ranki bai b'aci ba da aka fasa fita" turo baki tayi kafin tace

"Allah ne bai nufaba amma raina yab'aci kuma ba sabida rashin fitar da ba'ayi ba sai don don dukan da kayiwa yayyah Basmah"

"Dagaske?"

"Sosai kuwa Yaya har cikin raina don wlh da nice, k'ilan saina kusa kuka"

"Tab! Allah ya tsare ranar da zakiyi irin abunda basmah tayi don na tabbata yankata zanyi!" Zaro idanu Billy tayi yace

"K'warai kuwa"

Duk firar da sukeyi ita dai Ummi na saurarensu har ta ida kammala tsifar da take yimata, kanta ta d'ago tana kallonsa yanda yake fitar da maganganun sa cikin natsuwa

"Babana wai sai yaushe zaka fiddo da matar aure" da sauri ya wartsake daga yanayin da yake ciki har yana neman sauko wa akan kujerar da yake zaune

"Haba Ummi! Wane aure kuma nida na keda 'yan uwa mata agabana, ai idan kikaga nayi aure to tabbas naga nakai autarsu Billy agidan mijine"

Tunda Ummi tayi magana Billy ke b'ab'b'akar dariya saboda yanda taga yayan nata yayi shock da jin zancen, amma tanajin amsar daya bayar ta d'aure fuska kamar ba itaba, dariyar shima yayi

"Billy Japanese kenan! Wato ke kinga k'eta bari kiyi dariya ko?, to kima ajiye wannan fushin naki agefe don ko bakyaso tabbas sai lokacin da kukayi aure zanyi"

"A'a Babanah kabar wannan zance domin kaine babba acikin su don haka kai zaka farayi daga nan sai su kuma su biyo ba yanka"


"Don Allah Ummi mubar zancen nan, ni banason wani aure billy tafad'a tare tana bubbuga k'afafuwa ak'asa kamar zatayi kuka tabar falon"

Sosai Ummi tayi dariya ita da Mahmud da yabi bayan ta da kallo yana fad'in

"Ai kuwa saidai ki koma Japan ba agidan nan ba"

Bayan kwana biyu dady ya tarasu a main palour d'insa saboda wani makirci da small mom ta shirya akan tana so dady ya raba masu gida, wannan maganar ba kad'an ta tayar masa da hankali ba wanda shine dalilin da yasa yatarasu waje d'aya, sai da yayi gyaran murya sannan yashiga yiwa Allah godiya bisa tarin arzik'i da samun iyali daya azur tasa dasu, bayan haka ya d'ora da cewa

"Hak'ik'a Allah yayi mani tarin ni'ima wacce bazan iya biyan saba, amma nayi alk'awari agaresa zan dage dayi masa biyayya har izuwa lumfashina na k'arshe, ni mutumne kamar Ku bana son shiga hak'k'in d'aya daga cikinku, banason tauye kowanen ku hakan yasa na taraku don neman sasanci a tsakanin ku, hajia Aisha da hajia Hussaina dukkaninku matanane kuma ina matuk'ar sonku wanda hakan shiyasa nake fatar komai tsanani komai wuya murayu atare kuma mu mutu atare, amma kash yau d'ayarku ta bijiro mani da buk'ata mafi

Please Login or Register in order to submit comment