Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farinciki acikin wud'annan shekarun da suka gabata,

Rungume Ummi tayi tana hawaye tare da cewa

"Nagode Ummin yara, ubangiji Allah ya jik'an iyaye kuma ya gafarta masu, ayau nasake tabbatar da maganar papi dake cewa ke baiwar Allah ce kuma kinfini ilimi da hankali, nida kaina yau nayarda cewa ke tadabance kuma ba hankali da ilimi kad'ai kika finiba gaba d'aya kinfini komai" wani irin farincikine yaratsa zuciyar Ummi tare da yiwa Allah godiya daya nuna mata wannan ranar da zataci d'ibar hak'urin da tayi sannan cikin zolaya tana dariya tace

"Kenan kinyarda har awajen alhajinki nafiki" tayi hakanne saboda tana son ta auna abunda mom kefad'a shin har acikin zuciyar tane don tasanta da mugun kishi n da zai iya tayarda da nadamarta akoda yaushe, ai kuwa abunda yabata mamaki shine yanda taji mom tace

"Nayarda mana tunda ke rabba'atul bait d'in sace, nikuma mom d'in yara kad'ai" dariya sukayi atare don kowace ta wanke zuciyarta daga abunda takeji ga 'yar uwarta kafin can Ummi tace

"Kiyi hak'uri 'yar uwa nima kiyafemun don baza arasa abubuwan dana yimaki ba, wud'anda suka b'ata maki rai, kimanta da duk wani abun muyafi juna sannan mufara tsara gina rayuwar da zamuyi anan gaba cikin yiwa juna uzuri bisa kuskure idan anyi had'e da kauda kai don farantawa maigidanmu"

Murmushi mom tayi itama tarik'e hannun Ummi tana dariya tace

"Insha Allah komai yawuce rabba'atul bait, zan biyo bayanki in d'auki darussa don mu faranta zuciyar mijinmu kona samu nima yakirani da koda miftahul qalbin sace" nan suka sake sa dariya tamkar babu abunda yatab'a faruwa tsakaninsu abun gwanin ban sha'awa, kallon kwan don da mom tazo dashi Ummi tayi cikin tsokana irin tasu ta manya tace

"A'a Momyn yara meye kika tanadarwa 'yata haka acikin basket, lallai da alama kinaji da 'yar nan tawa babu batun sarakuta dama haka yaran zamani keso" iya kunya mom tajita don bakin rai girkine tahad'a akaiwa su yaya Mahmud, mik'ewa tayi da sauri tanufi inda basket d'in yake ajiye tana fad'in

"Ai kuwa dama taimakone nayi amma nafasa, indai surakace dama batawa bace takice don haka kararma nafasayi kiji da abukki ke kad'ai nikam nawa nazuwa idan bassami na da Bilal sun girma" had'e da d'aukar basket d'in tabar palourn Ummi nayi mata dariya.

A b'angaren Basmah kuwa koda aka kira sallar asuba mahmud yatashi bai gantaba mik'ewa yayi had'e da bud'e toilet yana tunanin kozai hanta amma ga mamakinsa sai yaga bata ciki, palour ya wuce kai tsaye ya hangota a k'asan tile's d'in kwance tana bacci, da sauri ya k'arasa wajen yana bubbuga k'afarta yana kiran sunanta "Basmah, Basmah" bud'e idanuwanta tayi ahankali suka sauka akan nasa sannan tasake rufewa,

"Oh my God Basmah, meyake dawo dake nan har kika kwanta a sanyin tile's bacin kinsan bakida cikakkiyar lafiya" yafad'a tare da tayar da ita zaune, ganin yanda baccin yayi mata nauyi yasa ya d'auketa cak bai ajiyeta ko inaba sai cikin toilet, fanfo ya kunan had'e da taro ruwan a hannunsa ya watsa mata afuska, nan da nan tasaki wata 'yar k'ara tare da sakin ajiyar zuciya tana goge fuskar tata da hannu, tsaki tad'anji tagefen baki yace

"Kibud'e idanuwanki mana kiyi arwala yanzu za'a tada sallah masallaci" yana gama fad'a yafara arwalarsa yana gamawa yabata waje itama tayi sannan suka fito atare,

"Kifara yin raka'atanil fijir kafin atayar da sallah ni zan wuce masallaci" yafad'a yana k'ok'arin saka babbar rigarsa dake ajiye acan gefen bedside, seda yatabbatar ta tada sallar sannan yafice zuwa masallacin,

Bai dawo gidanba saida rana tafito yabiya tacan gidansu ya gaida iyayensa tare da karb'o masu abun karyawa sannan yadawo gidan, koda yadawo ya iskota kwance ta k'udundune kanta cikin zanen gadon dake shimfid'e akan gadon, girgiza kai yayi tare da zuwa yafara yaye zanen yana fad'in

"Wai dama ke trouble maker ce Basmah, komai naki yasha banban dana mutane, don Allah dube yanda kikabi duk kika nad'id'iye kanki cikin zanen gado, agaskiya in hakane kina wahalda Batool sosai ita dake kwana dake" yanayin daya gatane ya tayar masa da hankali domin gaba d'aya bata motsi kamar babu rai ajikinta, cikin rud'ewa yadinga kiran sunanta, makullan motarsa ya d'auka tare da d'aukarta ya kaita cikin mota, saida yaje yabud'e gate sannan yazo yafiddo motar tare da komawa yarufo k'ofar gidan had'e da gate d'in, aguje yaja motar zuwa asibitin da suka yada zango jiya da suka iso, suna zuwa emergency nurses d'in dake ward d'in suka rugo tare da d'an gadon da ake tura marasa lafiya suka kama masa aka shiga ita, cikin sa'a kuwa suka samu dr daya dubata jiya bai wuce ba, nan take yakarb'i case d'inta suka shiga bata taimakon gaggawa, sun matuk'ar aha wahala kafin su samu suceto rayuwarta,

Kamar yanda likita yayiwa Basmah bayanin halin da take ciki haka shima wannan likitan yayiwa Mahmoud pilot bayanin halinda take ciki, kuma yatabbatar masa da cewa ahalin yanzu matuk'ar wata damuwa mai girma tasake gittawa rayuwarta to tabbas za'a iya rasa rayuwarta don ko yanzu Allah yanufa tanada kwana gaba amma koshi d'in bazatayi walwala ba yanda yakamata kamar yanda sauran mutane keyi saboda raunin da jijiyoyin zuciyarta sukayi gaba d'aya wajen halbawa sassan jikinta jini yanda yakamata, don haka dolene akiyaye shan maganinta akan lokaci duk wani abu da zaisa agajiyar da ita har ya haifar da bugun zuciyarta da sauri da sauri kada abari tayisa ko kuma zama cikin damuwa, dolene abata kulawa yanda yakamata don gudun kada hakan tasake faruwa,

Ba Mahmoud ba hatta alhajinsa da Umma saida suka tausaya mata tare da zubar mata da k'walla, tabbas Mahmud da Umma sunsan da wannan ciwon nata amma basu tab'a tsammanin yayi mata tsauri hakan ba,

Satinta d'aya kwance a asibiti kafin tasamu lafiya sosai, Umma namatuk'ar kulawa da ita yanda yakamata tamkar mahaifiyarta hakama Mahmud ya maye mata gurbin yaya Mahmud d'inta, don kuwa yana iya k'ok'arinsa amatsayinsa na mijinta wajen nuna mata kulawa da duk abunda yakamata batare da nuna gazawar saba, amma kowane lfitar lumfashinsa mak'ale yake da soyayyar Billy acikin zuciyarta, ganin ba'a dad'e da gama hidimar bikiba yasa mahaifinsa yace tunda dama ansan batada lafiya to kada asanar dasu kwanciyarta asibiti har sai anga yada jikin nata yayi su kuma wud'anda suka kawota dama tunda asussubar fari suka d'auki hanya saboda su isa dawuri shiyasa basusan da cewa ranar aka kwantar da ita asibiti, haka kuma bawanda yasan tana asibiti acan wajensu dady iyaka dai insun kira wani lokacin ace tana bacci wani lokacin kuma takan d'anyi k'ok'arin yin magana dasu, ranar da taji sauk'i sosai aka sallamesu suka dawo gida, wayarta tad'auka had'e da komawa can bayan kitchen lokacin Mahmud yaje wajen sallar azahar, lambar mom takira bugu d'aya ta d'auka, bayan sun gaisa tace

"Mom ina 'yar uwata Billy take ina fatar dai tana lafiya kuma cikin walwala"

"Sosai kuwa Basmah babu abunda kedamunta, yanzu nida umminku muna cikin zaman lafiya da k'aunar juna, babu wata damuwa ko tashin hankali atsakaninmu, wlh Basmah sai yanzu nakeji kunyar abubuwan da nayiwa baiwar Allah nan da wud'anda nasa kuka tayi mata, Umminku macece mai sauk'in kai da kuma kyakkyawar zuciya, wlh dana yarda namutu da hakkinta da bansan makomata ba" murmushi Basmah tayi don ita dama tadad'e da sanin hakan kafin tace

"Mom itafa 'yar uwata dana tambayeki? Kinata fad'ar kyakkyawar zuciya irin ta mahaifiyarta amma kinkasa fahimtar ita wace iriyar zuciya ce da ita har kina fad'in babu abunda kedamunta, tabbas ummi macece tagari don ita tasauyawa 'ya'yanki rayuwa alokacin da suka nemi lalacewa kuma ta canza wannan rayuwar taki da zuciyarki dake cike da tsantsar tsana ta sauya da cikakkiyar soyayya, mom har ila yau dai bisa taimakon tarbiyar da tabawa 'yarta ne yasa 'yarki keci gaba da rayuwa agidan wanda takeso kuma take k'auna" jingina wa Basmah tayi ajikin k'ofar kitchen d'in tana goge hawayen da suka mik'a mata fuska taci gaba da cewa

"Mom kifad'amun shin Billy nacikin farinciki kuwa bayan ta sadaukar mani da soyayyarta da masoyinta don d'ai kawai ta ceto rayuwata, abunda ni nakasayi amatsayina na yayarta" rufe baki mom tayi don yanzune ta tabbatar da abunda take zargi azuciyarta kafin tace

"Gaskiya nake fad'a maki Basmah, babu abunda kedamun 'yar uwarki saboda tanada matuk'ar juriya da hak'uri, abu d'ayane nafuskanta shine har yanzu dadynku da umminku fushi sukeyi da ita akan abunda ta aikata kuma takasa zuwa tafad'a masu gaskiya, amma shikenan nida kaina zanje infad'a masu saboda su fahimceta kuma suyi mata adalci"

"Don Allah mom kigaggauta yin hakan don fiddota cikin wannan damuwar, natabbata bazata tab'a iya bud'e baki tafad'i cewa saboda ina son yaya Mahmoud tahak'ura da auren saba, ina matuk'ar bak'in cikin da Billy tasan cewa ciwon da nake fama dashi ta silar soyayyar da nake yiwa yaya Mahmoud ce har yakai gata aikatawa rayuwarsu haka, tarusawa kansu farinciki donta ceto rayuwata, taraba kanta da masoyinta gudun kada narasa rayuwata, tafuskanci fushin iyaye had'e da damuwa duk don inyi farinciki, mom kifad'amun wannan wace irin 'yar uwace nake da ita da take sona fiye da yanda take son kanta, shin ashe batayo gadon kyakkyawar zuciyaba fiye data umminta? Da'ace haka 'yan uwa kenunawa 'yan uwansu soyayya da kuma k'auna aduniya da baza'a tab'a samun lalacewar zumunci ba, shin kinsan maganar Billy akoda yaushe idan za'afad'i wani abu akanmu tun tana k'arama? Cike da so yayyarmu take furtawa kowaye cewa su 'YAN UWANA NE!, don haka mom kije ki daidaita abubuwa ko kuma nida kaina zan kirasu infad'a masu komai akan cewa su yafewa 'yar uwata domin batada laifi"

"Shikenan Basmah hakan zanyi don shikad'aine zai wanke Bilkisu a idanuwan iyayenta" mom nahawaye takashe wayar kafin itama Basmah tajuyo zata dawowa cikin palourn kawai taci karo da Mahmoud...





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____90💎


Da sauri Mahmud ya saita kansa daga rud'ewar da yayi ta sanadiyar jin maganganun da yaji Basmah nayi awaya yace

Basmah dama kina anan? nadawo inata faman kira ban jikiba, keda waye abayan yak'arasa maganar had'e da lek'awa ta bayan kitchen d'in, irin yanzu yazo baisan tana wurinba, juyowa yayi had'e da kallonta yana d'an turo idanuwansa awaje ganin tana k'ok'arin goge hawayen da suka zubo mata a idanuwa yace

"Basmah kuka kikeyi?shiyasa kikazo nan kika b'uya don kar ingani?"

Girgiza masa kai tare da rugawa da gudu tabar wajen, don gaba d'aya jitake shikenan yaji komai duk wani mutuncinta da kimarta da yake gani zasu zube tunda yagano itace silar rabuwarsa da wacce yake matuk'ar k'auna fiye da komai aduniya, bayanta yabi yana kiran sunanta saboda tsoron abunda likita yafad'a masa akanta, bisa gado ya isketa tanaci gaba da kukan yayi tsaye yana kallonta cike da tausayi duk da ransa cewa yakeyi Basmah bake yakamata kiyi kuka ba, nine wanda yakamata na koka, kokad'an banajin soyayyarki araina amma k'arfin jinin 'yan uwantaka bazai bani damar nuna maki hakaba, keda Billy duka 'YAN UWANA NE amma Allah shine sheda itace mafi soyuwa araina akanki, duk wani tanadin rayuwata da ita natsarashi amma dole narungumi qaddarata tunda ke Allah yazab'amun, soyayyar da kikayimun har tajefaki cikin wannan halin itace zata tirsasa zuciyata yimaki adalci tare da danne duk abunda nakeji akan 'yar uwarki saboda kisamu farinciki, kuma tukuicin soyayyarki agareni shine bazan tab'a nuna maki cewa nasan tadalilin kine aurena yafasu da farincikin zuciyata, Ina son Billy sosai kuma bazan tab'a iya dena son taba balle har na iya cireta azuciyata badon haka ba da kema na sama maki gurbi aciki kodon narama maki soyayyar da kike yimun.

Ahankali yafara takowa zuwa inda take kwance abakin gado ya duk'a bisa guiwowinsa saiti fuskarta had'e da cewa

"Don Allah Basmah kidena kukan nan, meyasa amatsayina na d'an uwanki baza kiyi hak'uri da tsarin da Allah yayi atsakaninmu ba kizauna dani? nasani cewa no bazab'inki bane biyayya kikayiwa iyayenmu amma tunda hakane ai sai kiyi hak'uri kidena damuwa da kuma wannan kukan haka kinsan abunda likita yafad'a maki koso kike kirasa ranki don bakya sona"

Shiru tayi tana sauraren kalamansa wud'anda kenuni da gaba d'aya baisan halin da ake ciki ba, gaba d'aya a tsammaninsa tana kuka da damuwane don an aura matashi bata sonsa, kenan baiji wayar da takeyi d'azu ba? tana wannan tunanin taji yace

"Basmah dake nake magana amma kika k'yaleni" shiru tayi har lokacin don batasan mema zata cemasa ba, mik'ewa yayi had'e da cewa

"Shikenan Basmah tunda bazaki denaba zanje insanar da umma idan so kikeyi na sawwk'e maki to zan rungumi k'addara na sawwak'e maki don amatsayinki na 'yar uwara bazan zauna inzuba idanuwa Ina tare dake har ki ollata kanki kikai ga rasa rayuwarki baccin nasan cewa zan iya hana faruwar haka tunda aurena ne bakya buk'ata.

Da sauri ta d'ago kanta had'e da mik'e tsaye tana goge hawayenta tace

"A'a yaya kada kayi haka, zan zauna dakai mana kawai Ina tunanin.." sanin abunda zata fad'a yasa yayi saurin juyowa ya rungumeta don baya buk'atar jin haka, mutuwar tsaye Basmah takusayi had'e da rufe idanuwanta ta bud'e, shin wai mafarkine takeyi ko kuwa, yau itace ajikin yayanta wanda take matuk'ar so da k'auna itace jikinta ke gugan jikin masoyinta da bata tab'a mafalkin zata mallakesa ba, ahankali tarufe idanuwanta hawaye nazubo mata takwantar da kanta bisa kafad'arsa tare da tura hannuwanta tabayansa itama ta rungumesa cikin zuciyarata tana cewa alhamdulilah ya Allah ko yau namutu nasan banida asarar dakon soyayyar da nayi, shikuwa da nan take yaji wata irin kunya da k'aunar Billynsa sun cika zuciya yayi saurin sakinta had'e da rik'o kafad'unta ya zauar da ita akan gadon ya durk'usa agabanta tare da cewa

"Pls Basmah don Allah kidena shiga damuwa, ni d'an uwankine kuma mijinki zan kula dake iya k'arfina, zan baki farinciki iya gwargwado kuma zan sauke maki dukkanin hak'k'ok'anki dake kaina, kiyi hak'uri muyi rayuwar aurenmu da Allah ya tsaro mana batare da sanin junanmu ba kodon mubarranta daga wajen ubangijinmu"

Girgiza masa kanta tayi dake sunkuye ak'asa alamun eh taji, hannunsa yasa akan hab'ar bakinta ya d'ago fuskarta yana kallon manya manyan idanuwanta da farinsu yad'an sauya zuwa ja kad'an ga hawaye duk sun jik'e mata lashes d'insu sannan yace

"Kin tabbata?" Nanma kai ta sake kad'a masa, hannu ya mik'a mata yace "promise me" Saida takalli k'wayar idanuwansa ya sakar mata murmushi sannan itama ta d'ago hannunta ahankali ta d'ora akan nasa tace "in sha Allah"

Kiss yayi mata a hannun had'e da cewa "yawwa koke fa, Allah yayi maki albarka"

"Amin yaya" tafad'a tana k'ok'arin jaye hannun ya rik'e yana kallon fuskarata tare da cewa

"Baza'a taimaka ayiwa yayan nan dariya ba ko kad'anne" murmushi tayi ya lakuto hancinta tare mik'ewa tsaye Yana fad'in

"Yawwa 'yar gaban goshin mom kokefa, bari naje gida ummah tace naje nakarb'o maki sak'o, nikam gaba d'aya naga ummah tadwna kulani sai ke, Allah yasa ba kwacemun ita zakiyi ba" yak'arasa maganar cike da tsokana yana shagwab'e fuska, dariyar da saidahak'oranta auka bayyana yabata had'e dasa tamik'e tashige toilet tanajin wani sabon sauyin yanayi atare da ita.

Mom nagama waya tanufi part d'in Ummi, tana shiga Ummi na zaune tagama had'in doughnut tana fidda shape d'insa, gaisheta tayi had'e da zaunawa takarb'i abun tana tayata fitarwa ita kuma tana ciro mata had'in tana aza mata, sun jima ahaka kafin can Ummi ta kalli yanayin da mom keciki tace

"mom Bassam lafiya kuwa?"

"Me kika gani halan yaya?" Mom tafad'a tanaci gaba da abunda takeyi

"Nagaki kamar yanda nasaba ganinki ba"

"Eh yaya babu komai"

"Anya kuwa"

"Eh mana, kawai gaskiya bana jin dad'in yanda kike yiwa Bilkisu ne!" Murmushi Ummi tayi had'e da jaye tray d'in da mom tagama a'aza shape d'in data fitar na doughnut tana fad'in,

"Mtss indai akan wannan ne kidena damar da kanki, taya za'ayi yaro yayi badaidai ba kuma asa mashi idanuwa, yanzu abunda tayi kid'auka ita kad'ai mahaifinta yake da ita, shikenan ta tozartashi kenan a idanuwan d'inbin mutanen daya taro, kuma shikenan sai akasa nuna mata tayi kuskure, shin kinga haka yakamata?"

"A'a yaya ba haka nake nufiba, ina so kifahimta cewa fushin da kikeyi da ita yin hakan kuskurene, duk da sanin tsakanin d'a da mahaifi sai Allah ina tsammanin tunda abunnan yafaru baki tab'a bata fuskar da zata fuskanceki tayi maki bayanin dalilin aikata haka ba ko kuma ke kitambayeta?"

"Hmmm! mom Bassam kenan yarinyar nan kibarta kawai, babu wani dalili da take dashi in bacin rashin mutunci, ita da kantafa ta iya dubin k'wayar idanuwana tafad'amun cewa wai bata son aurennan, saboda ko anyisa bazata samu farinciki ba, haba momynsu kijifa!, yanzu don Allah wannan wace irin hujja zata bani da har zan gamsu da ita? Ai gaba d'aya ma tagama raina ni wlh"

"Assha Ummansu, ai Bilkisu ita takeda hujja da kuma dalilin abunda ta aikata" mom tafad'a tare da rik'awa ummi gyara wajen da sukayi aikin tanaci gaba da cewa

"Kiyarda dani yaya, ko kad'an Bilkisu batada laifi, garin taimakon 'yar uwarta dake neman rasa rayuwarta tayi wannan kuskuren, wanda rashin tsayawa tayi maku bayani shi kad'ine inda tayi laifi, ranar da aka dawo dinner ciwon Basmah yatashi inda ina d'aki Batool taje takirani aguje tana kuka wai ga Basmah can jini nayi mata tsiyaya ahanci...." Bayani mom tadinga yiwa ummi dalla dalla akan abunda yafaru ranar tundaga farko har k'arshe bata b'oye mata komai ba hatta maganar da yaya mahmud da Batool suka fad'a mata akan soyayyar da Basmah keyiwa Mahmud pilot saida tafad'a mata, wanda daga k'arshe tace "kiyi tunani yaya idan har keda kike mahaifiya ga Bilkisu kina tunanin yafewa wacce tacutar dake na tsawo shekara kusan ashirin da wani abu cikin lokaci d'aya taya za'ayi Bilkisu da take jininin kuma tarbiyarki takasa samun zuciyar da zata iya sadaukar da wani abu ga 'yar uwarta da suke matuk'ar son juna, gaba d'aya wannan abun data aikata koyarwarki ce wacce ni dana gaza yiwa 'yata ita gashi raunin data samu yana nema ya kaita ga rasa rayuwarta wanda wannan shine dalilin da yasa lokacin da Bilkisu taga yanayin da 'yar uwarta keciki kuma taji ta aikata hakan bisa kuskure da yarinta don d'ai kawai ta tsiratar da rayuwarta"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" suka ji dady dake tsaye k'ofar palourn tun d'azu yana sauraren abunda mom kefad'awa ummi yafad'a yana k'ok'arin shigowa tare da cire hular dake kansa, a firgice suka juyo tare da nufowa inda yake suna fad'in "alhaji lafiya kuwa?"

Shiru yayi na wasu 'yqn mintota kafin ya d'ago kansa idanuwansa cike tab da k'walla yace

"Dr dake kula da Basmah ne yakirani yanzu yana fad'amun cewa, wai inbinciki 'yata Basmah inji halin da take ciki akan rashin lafiyarta, shine nake fad'a masa cewa ai tayi aure tun last week yafad'a mun inji in wani abune yafaru da ita idan babu matsala, nan yake fad'amun cewa condition d'in rashin tafiyarta yayi tsauri da yawa wanda yakaiga idan ba'a fitar da ita wajeba zata iya rasa rayuwarta don gaba d'aya k'arfin bugawar zuciyarta yaragu da kaso sittin da biyar bisa d'ari wanda hakan shine nuna kusan fiyema da rabin jijiyoyin dake aiki ga zuciyar tata sunyi rauni, kuma tun sati d'aya daya wuce yaso sanar dani hakan amma tarok'esa akan kada yafad'a har sai bayan bukin 'yan uwanta, wanda hakan yasa yarubuta mata magungunan da zata rik'a sha har zuwa wannan lokaci sai tadawo kak'ara dubata sannan asanar damu amma bayan lokacin yayita jiran ganinta bai gantaba, wanda hakanne ya tayar masa da hankali ya ciro no dake jikin file d'inta har yasanar dani don gudun faruwar wani abun gareta ya haifar masa da matsala wajen aikinsa, to shine nikuma naje can part d'inki hankalina atashe don nasanar dake nasamu bakican sai nayo nan, maganar da naji kunayi itace ta dakatar dani ga shigowa har nasamu tabbacin abunda dr yace acikinta, abu nabiyu kuma shine yanda na wofantar da alamarin 'yata alokacin da take buk'atar kulawar mu saboda tarage rad'ad'in dake cikin zuciyarta na rabuwa da masoyinta, Allah sarki najima ina rok'on Allah ya had'e mun kan 'ya'yana su so junansu, sai gashi yabasu abunda yafi k'arfin akirasa da had'in kai ko soyayya sai dai ace masa sadaukarwa, domin aduk inda aka samu sadaukarwa kasan ba k'aramar soyayya ce da kuma had'in kai a wurinba, Bilkisu kenan baiwar Allah, bacin juriya da hak'uri da Allah yabata sai kuma ya had'a mata da k'ana'ar iya rik'e sirrin 'yar uwarta da mutuncinta, itace k'arama acikinsu amma babba mai hangen nesa, tayarda tafuskanci damuwa da bak'in ciki matuk'ar kowa zaiyi farinciki" Shiru dady yayi cike da tausayin 'yarsa da nadamar marora da bugun daya yimata dad'in dad'awama harda fushi yayi da ita amma tsabar son 'yar uwarta hakan baisa ta iya bud'e bakinta tafad'i gaskiyar dalilinta ba, Ummi kuwa tuni jikinta yagama yin sanyi duk dazai har ga Allah duk abunda take yimata bawai fushine takeyi sa'a itaba don tasan illar da fushin ta zaiyi mata, kawai tana yimatane don taji haushi kamar yanda itama shiriyar da mijinta keyimata kesata jin haushi, wata irin jiwace taji tad'ibeta tana neman kada ita daga tsayen da take, da sauri mom tarik'ota tare da zaunar da ita akan kujera tana fad'in "Ummin yara lafiya?"

'Dan cije baki tayi tana cije gefen bakinta had'e da cewa

"Kawai mamakine da al'ajabin yanda fari yakasa fahimtar cewa asalin fari d'an uwansa bazai tab'a canzawa ba da kuma yanda son zuciya ya rufewa shuwagabanni biyu idanuwa suka kasa fahimtar damuwar wanda suke mulka balle har suyi tunanin sama masa mafita alokacin da farincikinsa ya kucce masa har yafad'a cikin damuwa, wannan dalilin shine yahaifarmun da sarawar kai dajin jiri nad'ibana"

Sosai dady ya fahimci cewa dashi take saboda fushin da yakeyi da ita akan zargin tanada alak'a da laifin da 'yarta ta aikata da kuma yanda dashi har ita suke fushi da Billy tare da kasa bata kula saboda jin d'acin abunda tayi azuciyarsu balle suyi tunanin faranta mata, ita kuwa mom dafarko bata fahimci abunda Ummi tace ba saiga maganarta tabiyu tafahimceta, cikin jin nauyi tace

"Gaskiya abun ba dad'i amma duk laifin Aina Basmah ne data kasa jurewa qaddararta saida ta cinna 'yar uwarta aciki, gashi taja mata rabuwa da masoyinta kuma kuntsiri fushi da ita, alhaji da rabba'atul bait don Allah da girmansa narok'eku amadadin 'yatah Bilkisu kuyi hak'uri kuyafe mata b'acin ran da kuka samu awannan abu da yafaru, kufahimceta kuma ku jawota ajiki koda tasamu rangwame azuciyarta, haba yakamata ku yabawa jarumtarta don da Basmah ce da yanzu ba ita kad'aiba kowama da yaji ajikinsa saboda yanda matsalarta zata addabi kowa da zuwa asibiti"

Tak'asan idanuwa dady ke kallon Ummi data jingina kanta ajikin kujera tana suraron mom, cikin jin kunya yana d'an sosa k'eyar kansa yace

"Koma meye tunda maigama tagama ai sai ayafi juna koba haka ba hajiya hussaina" 'yar dariya mom tayi kafin tadafa kafad'ar Ummi tace

"Yaya Allah ya sawak'e kuma ya k'ara shirya mana 'ya'yanmu yaci gaba da had'e mana kawunanmu, pls don Allah aduba al'amarin nan yaya wanda yayi abun k'awarai tayimasa afuwa amanta da komai wanda kuma ya aikata laifi to inaga shikam maganar dashi kuskuren sa amma nidai 'yata nakeji tunda ansan gaskiya ayafe mata" tana gama fad'ar haka tazagaya tabayan kujeru don tun d'azu tana kalle da yanda dady ke aiko mata da harara shiyasa tafasa bi tagabansa ta zagaya tabar part d'in tana dariyar k'eta k'asa k'asa...



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____91💎


Kallon Ummi dady yayi yanaji gaba d'aya bai kyautaba abunda yayi mata, nan take yaji ya tsinci kansa cikin wata irin kunya da dana sani, tasowa yayi yadawo inda take yazauna kusa da ita dayake kujerar 3seater ce take zaune akai, hannu yasa da niyar tab'ata yana fad'in

"Rabba'atul bait ya ciwon kan da sauk'i dai ko?" Mik'ewa tsaye tayi had'e da kallonsa tace

"Wannan zafin ciwon kan da nakeji bai kai rad'ad'in zafin ciwon fushin da kayi dani ba har natsawon kwanaki takwas ba, don haka idan har ka iya jurewa ganina cikin wancan zafin ciwon ai bai kamata ace wannan d'an

Please Login or Register in order to submit comment