Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nafiso akan duk abunda zai iya zamowa mallakina aduniya, ai kisa aranki soyayyar da nake yiwa 'yarki bazata bari natab'a cutar maki da itaba, wannan alk'awarina ne" murmushi Umma tayi tare da shafa gefen fuskarsa "Mahmud matuk'ar ka aikata haka kuwa zanyi alfahari da samunka amatsayin d'ana har iya k'arshen rayuwata, kuma zanzamo mai saka maka albarka fiye da albarkar da kowace uwa kesawa d'anta aduniya" rungumeta yayi yana fad'in

"Allah yabani iko ummanah, ina sonki sosai"

Yajima a part d'in Ummin kafin yatashi ya nufi part d'in mom don dubo jikin Basmah, yana fitowa ya d'auki motarsa yafice daga gidan, saida yabiya banki ya ciro kud'i sanna ya tsaya daidai wata arniyar plaza da taji komai na buk'atar rayuwa, gefen cosmetic da turarukka yanufa ya kwaso masu yawa da k'amshi sosai adadin yawan da mutun uku zasu iya amfani dasu, har zai wucewa sai ya zagaya tagefen da 'yan kunne da sark'ok'i da zobbuna da agogayye kejere, ahankali yafara duba zobban dake wajen don ya siyawa Billynsa amma har yakai k'arshe bai samu ba, har zai wuce ya hango wani cikin jerin azurfofin dake wajen, ruwan azurfane zallarsu fari k'al sai zanen capital B da aka fidda shape d'inta atsakiya da wani salon rubutu daba kowa ke iya ganewaba don yayi kamar wani salon zanen fulawane amma azahiri idan ka k'ura ido zakaga B ce arubuce, nan take yaji zoben ya burgesa, d'aukowa yayi yana imagining zoben ahannunta yayi murmushi yana zuwa akayimasa totallyn kud'in da zai biya ya biya sannan ya ajiye masu zoben shima aka fad'a masa kud'insa yabiya, kallon zoben yayi saboda tsadarsa ya tabbatarwa zuciyarsa cewa da ita d'in yafi dacewa don dama Billyn tasa tafi tsada tsada, rik'o masa kayan akayi tare da kai masa mota shikuma yakad'a zoben a aljihunsa bayan an saka masashi acikin wata 'yar jikka, yana jan motarsa bai tsaya ko inaba sai _Bebeji plaza_ wajen da ake saida nau'o'an wayoyin hannu kala kala, techno phantom 8 ya siya k'waya biyu tare Samsung galaxy S8+ saida aka yimasa testing d'in kowace sannan aka maidasu cikin kwalayensu bayan an sanya masa aleda yabiya kud'in sannan yad'auko, yana fitowa yanufi mtn office ya sayi layukka guda biyu masu registered sannan yasayi wani k'waya d'aya da ba'ayiwa register ba ya zauna yabada duka information d'insa nan take akayiwa layin register dasu, yana fitowa ya mik'i hanyar gida lokacin ana kiraye kirayen sallar la'asar hakan yasa yana isa kai tsaye yanufi d'akinsu yafad'a toilet yayo wanka bayan yatada yaya Mahmud da ya isko yana bacci, shima wankan yayo yasamu har Mahmud pilot ya shirya cikin k'ananan kayansa da suka karb'i jikinsa sosai kamar bashiba, jeans ne yasa brown colour sai shirt d'in data d'an kama jikinsa kad'an itama brown da ratsin layi fari a gefen hannunsa nadama daga can sama kayan sunyi matukar yimasa kyau sosai, kallonsa yayi yace

"Pls d'an uwa don Allah karakani tun d'azu nake begging d'inka amma ka wofantar dani" murmushi yayi kafin yace

"Shikenan bari mudawo sallah, ai kai d'inne kab'atan rai d'azu kana ganin mutun cikin damuwa bakayi masa solving d'inta ba ka wani d'auko masa zancen rakiya wajen budurwa" mahmud dai bai cemasa komai ba yaci gaba da shirya warsa cikin wata shadda black colour, saida ya kimtsa tsaf sannan ya kallesa yace "d'an uwa kasha kyaufa, yau kace zaka rud'amun k'anwa"

"Nagd d'an uwa, amma kaikam ko shakka banida akan zaka firgita 'yar mutane don gaba d'aya kayannan basuyi maka kyauba, haba d'an uwa irin wannan shiga haka sai kace ba akanka d'aya ba" baki yaya mahmud ya washe tare da mik'a masa hannu yana fad'in

"Alhamdulillah, da gaske kakeyi d'an uwa? Gaskiya naji dad'i sosai don dama hakan nake so, wlh dolece zata sakani zuwa wajen yarinyar nan, Allah yasa tace banyi mata ba"

"Kai amma dai kai mugune, don d'ai haka zakayi mata wannan shigar, duk da shigar batada illa kayanne dai basu zauna ajikinka ba duk sunyi wani oversize dasu haka ballema ayi batun suyi maka kyau..mtss Allah yasama tace taji tagani ahaka tanayi" cikin b'acin rai Mahmud yace

"Kaima Allah yasa tace kai takeso tunda kaine kayi shigar da tayi kyau" yaya mahmud yafad'a tare da ficewa cikin fushi, jin anazancen tada sallah yasa shima yabi bayansa bayan yafeshe jikinsa da turare suka nufi masallaci, suna fitowa sai ga kiran papi yashigo, saida yaya Mahmud yad'an bubbuga k'afarsa ak'asa sai kace yaro sannan ya d'aga wayar har lokacin fuskarsa babu walwala, dariya mahmud pilot yadinga yimasa hadda rik'e ciki ya galla masa harara lokacin da yake cewa papi bayan sun gaisa,

"Eh papi yanzu can zamu tafi nida d'an uwan in sha Allah, eh papi, babu matsala zantafi karka damu" suna gama wayar yacewa Mahmud pilot "ka k'addara kaci bashi d'an uwa ko yaushene zan rama wannan dariyar da ka keyimun"

"Sorry d'an uwa nadena ainikam anriga angama tunda nafad'i zab'ina kafin azab'omun banyi nauyin baki irin naka ba" k'yalesa yayi yawuce abunsa don kar wani yaga shigar da yayi ya tilastasa yasa suna shiga cikin gida yabud'e motarsa ya shige had'e da kallon Mahmud pilot yace "muje ko"

"Baza kasa kod'an turare bane?"

"Bazan saba! Aitunda kasa ya wadatar" yabashi amsa atak'aice

"Shikenan ammafa ni yunwa nakeji ko zamuyi lunch kafin muwuce?"

"Noo.. bana buk'ata jeka kai kayo zan jiraka" kad'a kai Mahmud pilot yayi sannan yawuce abunsa, harara kawai yabisa da ita fuskarsa ba walwala, yana shire rufe idanuwansa ya hango Billy rik'e da warmer tanufi part d'in mom aikuwa Mahmud pilot na ganinta yanufi wajen yana murmushi, "my noor" yace yana k'ok'arin k'arasowa inda take, juyowa tayi suna had'a idanuwa suka sakarwa juna murmushi, shigar datayi sak irin tasace kamar sun had'a baki, doguwar rigar shaddace ajikinta shape d'inta yazauna aciki tayi kyau sosai, bawani aikine aka yiwa shaddarba, shape kad'aine aka fitar mata, giznah ce data karb'i sunanta Brown colour sai k'yalli takeyi light make up ce afuskarata tasaka takalmi brown suma masu d'an tudu da suka k'ara mata tsawo duk da cewa itama tanada nata tsawon ba gutuwa bace, yatsunta biyu tahad'e ta kad'a kai ahankali tace "na'am yayana kayi kyau sosai"

"Allah my noor?" Yace yana fiddo wayarsa daga cikin aljihu, murmushi tayi had'e da jinjina masa kai alamar sosai kuwa, warmer d'in ya karb'a a hannunta ya ajiye gefe yana fad'in

"Ai ga tsantsar kyaunan awurinki, gaskiya da nayi missing kwalliyarnan dana tabka babbar asara" rufe baki tayi tana yimasa dariya kawai taji yana d'aukarta hotuna, duk motsin da tayi wajen yunk'urin hanasa sai yad'auketa hoto yana dariya, tun tana hanasa har tagaji ta k'yalesa yayi iyayinsa sannan yadena,

"Weldone sun isheka haka?" Tafad'a cikin shagwab'a tana d'an harararsa,

"No..one more pls" kafin tace wani abu yadawo gefenta had'e da maida phone camera d'in front ya saitasu, kallonsa tayi had'e da d'an turo baki irin na shagwab'a d'in nan zatayi magana aikuwa ya d'aukesu hoto, "smile my nooor.." Yace ta sigar da dole yasata dariya, tanayin dariyar yasake d'aukarsu har kusan so uku sannan ya tura wayar a aljihu yaduk'a yad'au warmer d'in yawuce gaba ta bisa tana fad'in

"Pls nidai kabani bance ka d'aukar munba" "ai bake kika sakani ba ni naga dacewar haka tunda ina wajen, kinmanta da nayi maki alk'awarin zan bauta maki akoda yaushe?" Bubbuga k'afa tashigayi tare da cin gabansa ta karb'i warmer d'in hannunsa a daidai lokacin da yake k'ok'arin shigewa part d'in da ita. "Thank u here is enough ma kaje kaji ko?"

Dariya yaya Mahmud dake cikin mota yana kallonsu cike da Sha'awa da burgewa yayi had'e da bugun stearing motar

Shikuwa Mahmud pilot kallonta yayi tare da cewa

"Shikenan tunda korata kikeyi natafi, i luv u" yawuce had'e da jefo mata kiss da hannu, cafkewa tayi da sauri ta aza saiti zuciyarta tana dariya tace luv u too yayana" zagayawa yayi yabud'e motar ya shiga tare da cewa "muje d'an uwa nafasa cin abinci now sai mundawo"

Mere baki yaya Mahmud yayi had'e da cewa "dama can bawani abinci zakaciba kai dai kawai kace qanwata kake son kaje ka gani, kuma kaganta, jarababbe kawai"

"Eh naji d'in bakomai, infitsari Banza ne kaza tayi mugani"

Batare daya kula saba yaja motar habu mai gadi yabud'e masu gate suka fita, tafe yake yana tuk'i amma gaba d'aya cikin damuwa yake da qunci, sai da suka kai bakin wani gida dake kan titi yayi parking motar had'e da kallon gefen da Mahmud pilot yake zaune sai faman kallon pics d'in da sukayi da Billynsa yakeyi yace

"'Dan uwa minti biyu don Allah ina zuwa, zan d'an anshi wani abu wajen abokina" bai d'ago kansaba daga kallon da yakeyiwa hotunan kan wayarsa yace "badamuwa sai kadawo"

Bayan kamar minti biyar sai gashi yadawo hannunsa rik'e da wani abu yayi saurin kad'awa aljihu kafin ya iso gaban motar, a hankali yaci gaba da tuk'a motar suka nufi anguwar su faraaha tamkar bayason su isa , baisan cewa sannu bata hana zuwa saidai adad'e ba'a kaiba, da haka suka isa anguwar tambaya d'aya sukayi aka nuna masu gidan kuma akaci sa'a jaddi na zaune a k'ofar gida, parkin d'in motar yayi agaban gidan sannan suka fito cikin girmamawa suka gaida jaddi da fuskarsa tacika fam da farincikin ganinsu, umurni yabasu dasu shigo cikin gida har zaure shi kuma ya wuce ciki, d'akin faraaha yanufa daya iskota har tayo wanka tasanya kayanta masu kyau kasancewar tasan da maganar, sosai yaji dad'in ganin yanda tagyara yafad'a mata cewa ta samu bak'in azaure sun iso sannan yajuya tare da basu hak'uri ya sanar dasu cewa gatanan zuwa yana fita mahmud yaji kamar ya fashe da kuka, juya bayansa yayi don shikam ko fuskarta baya son gani balle yaji yana sonta ko akasin haka, ita kuwa faraaha jaddi nafita tayi irin kwalliyarnan ta k'auyawa sannan tanemi bak'in kwalli tacike gaba d'aya bakinta da gefensa dashi, sannan tane concealer tayi 'yar gira da ita, brown pencil tasa k'asan idanuwanta amatsayin kwalli sannan tanemi jan bakinta 24hrs ja tasama haurunta guda biyu na gaba, ita kanta data dubi madubi taga yanda takoma saida ta tsorata dariya tayi sosai kafin ta d'auko jikkarta ta lak'ame a hamutta, fitowa tayi tare da d'aure fuska tanufi zauren har zata shiga sai kuma ta tsaya, tsaki tayi kafin ta botsare had'e da d'ora hannunta akan cinya tafara tafiyar guragu dama tun jiya da daddare yayita koyon yanda akeyi, kanta na kallon k'asa ta shiga zauren batare datayi sallama ba, shi kuma yaya Mahmud dama yana juyawa baya yaciro haurun robarsa daya aro wajen abokinsa irin masu fitowar nan agaba guda biyu sunyi jajaja da bak'i bak'i ya saka, tunda tadoso wajen Mahmud yafara ja da baya yana tab'in mahmud pilot amma yak'i juyowa, hakan yasa ya daure yace mata "sannu 'yan mata, ya kike?, wannan bazata haka ko sallama babu" wata irin harara ta d'ago kai ta zabga masa da sauri yaja baya saboda yanda yaga fuskarta, yaso yatuna ina yataba ganin irin fuskar amma waccan kyakkyawace kuma ba gurguwa bace, maida kanta tayi k'asa da sauri dariya na neman kucce mata ganin yanda yafirgita, hakan yaba Mahmud pilot damar cewa "'yan mata maida wuk'ar irin wannan uwar harara haka? to banine saurayin naki ba ni d'an rakiyane" tab'o yaya Mahmud yayi yana fad'in

"Dan uwa kajuyo mana kaga masoyiyar ka tunda tak'i magana, kila idan taga fuskarka tayi" cikin b'acin rai yaya Mahmud yace

"Kada Allah yasa tayi maganar, dama hakan bai dameni ba, idan batada abun cewa sai intafi abuna don dama dole aka sani badon ina soba, kuma idanma kinsa rai akaina to kifiddo donni inada wacce nake so" yak'are maganar had'e da juyowa, tunda yafara magana taji kamar muryar all I have d'inta amma saboda baijuyo fuskarsa ba yasa tad'an jira har sai tatabbatar shid'inne sannan tayi magana, yana juyowa suka had'a ido takalli haurun da suka fito agaban bakinsa shima yakalli fuskarta da kyau ya tabbatar wannan faraahar sace, nunata yayi da hannu yana fad'in "My golden" had'e da cire haurun roban da yasa abakinsa, ai faraaha bata san lokacin data nufi cikin gida agujeba har lokacin tana tsingila k'afa saboda yanda tarud'e takasa barin tafiyar gurgurtan, zaune yaya Mahmud da pilot sukayi akan d'an teburin dake cikin zauren suna faman dariya hadda rik'e ciki ita kuwa da gudu tafad'a toilet ta wanko fuskarta sosai ta sako hijabinta, zauren tadawo tana kallon yanda suke dariya itama sai takwashe da dariya tuna yanda taga all I have d'inta da hak'ora biyu zagozago agaban baki kamar zai cijeta..




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Sincerely i will not past dis page with out sending my big greeting and gratitude to you *ZAINAB PINKI🌸💕* you are such a big and adorable fans dt am always proud of her, thank you fd luv sister, thank u for encouraging me and thanks for always been with my write step by step😍 I pray for a wanderful, handsome, and charming husband to u my dear, jaxakillahu bikhair wa'arju anyaj'alallahu min ahlil jannah👏🏻 *much luv fillah❤*_

💎Page_____61💎


K'arasowa tayi cikin zauren tayi folding hannayenta akan k'irji tana kallon yanda yake dariya sai taga ya k'ara mata kyau fiye da kullum, d'ago kansa yayi yana k'ok'arin tasaida dariyar tasa yace,

"My golden wai dagaskene kedince agabana kuma a matsayin zab'in papinah? I can't believe!" Yafad'a had'e da d'ora hannunsa akan cinyarsa yana mamakin yanda ikon Allah ya kawosa har cikin gidansu masoyiyarsa amatsayin saurayin had'i, lumshe idonta tayi tana murmushi itama abun yabata mamaki sosai wanda hakanne ya haifar da ita zama speechless, mik'ewa Mahmud pilot da har yau dariyar acting d'in da masoya biyu sukayi yakeyi, hannuwansa yashiga tafawa yana fad'in "finally finally d game is over tunda dara taci gida, gaskiya kud'innan kuncancanci award na mugwayen duk duniya" nuna yaya mahmud yayi da hannu sannan yaci gaba da cewa "kai da hauru zarozaro agaban baki ga wata muguwar bak'ar shadda oversize daka saka ita kuma tafito tana tsingila k'afa alatilas ita gurguwace ga fuska databi ta b'ata tamkar horanya taya za'ayi idan harku d'in ba masoya bane da kuka san juna har kuso junanku? Wlh Allah danaga fuskarki kad'an yarage inruga balle wannan shikuma k'iris yarage nayi fitsari a wando" ya k'arasa maganar yana kallonta tana faman murmushi"

Gefen yaya mahmud taje tazauna had'e da cewa

"Wannan ai kad'an kagani indai tsakanin faraaha da mahmud ne, zasu iya yin fiye da hakan akan duk abunda yanemi rabasu, kuma wannan itace soyayyar gaskiya da ake kira mutu karaba ko all i have"

"Sosai kuwa my faraah kuma ina alfaharin samunka a matsayin rabin raina domin natabbata zaki rik'eni amana" murmushi tayi tare da mik'ewa tsaye taje takawo tabarma ta shimfid'a masu sannan takawo masu ruwa da kunun aya masu sanyi sosai had'e da kofuna ta ajiye masu,

"Pls all i have, kusha wannan kafin nadawo, kubani just 5mnt i will be back in sha Allah" tafad'a tana k'ok'arin ficewa daga palourn, binta yayi da kallo har tafice, shikuwa yaya Mahmud ya shiga tsarguwarsa, bai tankasa ba illama fiddo wayarsa da yayi ya kira papi, yana d'agawa cikin farinciki yace

"Nagode papi da kazamo silar tabbatuwar farincikina, nayarda da zab'inka kuma na amince dashi ubangiji Allah ya tsawaita rayuwarka cikin amincinsa kuma yasaka maka da alkhairi"

Speechless papi ya zama ya juya yana kallon hajia kaka dake gefensa fuskarsa d'auke da murmushi yace

"Baby kinji abunda mommodunki kefad'a? Wai ya amince da zab'ina!" Yafad'a cikin mamaki, muryar yaya mahmud yajiyo cikin wayar yana cewa

"Papi ba wai bane kuma kadena mamaki don tabbas na amince kawai kutsaida ranar shagali" yana gama fad'ar haka yakatse wayar yana kallon mahmud pilot da yarik'e baki yana kallonsa, basarwa yayi tare da d'aukar gorar ruwan dake gabansa ya tsiyaya a cup yana sha.

Hello, hello, papi ya dinga fad'a yana k'ok'arin jefa masa tambaya amma sai yaji yakashe, wata sanyayyar ajiyar zuciya yayi sannan yajawo babynsa ajiki yayi mata kiss a goshi had'e da cewa

"Alhamdulillah, baby yaronnan ya gamamun komai aduniya, duk da jikina nabani cewa akwai dalilin da yasashi saurin amincewa nayi farinciki sosai" d'ago kai tajiya kaka tayi tana kallon fuskarsa sannan tace

"Gaskiya kam akwai alamar tambaya, amma koma meye, alhamdulillah Allah yatabbatar mana da alkhairin sa" kiss yasake yimata tare da cewa

"Amin babynah" ya rungume abussa,

Cikin mintuna da basu wuce goma ba saiga faraaha tadawo hannunta d'auke da kuloli guda biyu babba da k'arama akan tray da kuma plates da spoon ta ajiye agabansu, cikin natsuwa tafara zuzzuba masu kuskus d'in data dafa yanzu tare da miyar k'wai da yake da electric stop tayi girkin kuma bamai wahala bane shiyasa tayi saurin gamawa, iya tsarguwa da sheri yau sunshata awajen mahmud pilot, sukuma sai dariya suke suna cewa ai duk cikin sone,

Sunci sunsha sosai tare da firarsu cikin so da k'auna batare da sunyi la'akari da Mahmud pilot dake wajen ba, duk da yana ganin abun nasu yafi k'arfin hankalinsa barmasu shimfid'ar yayi yakoma saman tebur d'in dake can gefe yana lallatsar wayarsa, basu baro anguwar ba sai gab da magrib bayan sunyi sallama da jaddi daya dad'e yana mamakin yanda suka samu fuska awajen faraaha har suka samu damar iya dad'ewa haka, suna wucewa ya shiga cikin gidan fuskarsa cike da mamaki, bai sake shiga cikin mamakiba sai daya ga faraaha tarugo da gudu ta rungumesa tana fad'in

"Nagode jaddi da zab'in da kayimun kuma na amince zan auresa, tabbas dana bijere wajen yarda da ganin zab'inka dana tabka babban rashi" d'agota yayi daga jikinsa had'e da rik'o fuskarta yace

"Me kike nufi faraaha?, kenan kin amince da zab'in da nayi maki?" Girgiza kai tayi da sauri tana hawaye tace "Eh jaddi na amince da zab'inka domin shine zab'in nawa shima" farincikin dake kwance afuskar jaddine ya k'ara bayyana yace "da gaske kikeyi shine saurayin naki?, kai alhamdulillah Allah daka sauk'ak'amun burina yazamo zai cika cikin sauk'i batare da k'untatawa wannan 'yar marainiyar Allah ba" rungumesa tayi sosai shima haka tace

"Ina sonka jaddi sosai, Allah ya karb'i iyayena amma yabani wani uba kuma kaka da bazai tab'a bari na wofanta ba, ya Allah kada ka karb'i raina har saika bani ikon faranta zuciyar wannan bawa naka"

"Amin" jaddi yafad'a yana goge 'yan hawayen da suka zubo masa...

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____62💎


Driving yakeyi yana shiga da fita akan titi zuciyarsa cike da tunanin faraaharsa da suka rabu yanzu, hannu Mahmud pilot yakai akan stearing motar yana jifarsa da harara "d'an uwa wai mekake yine haka, ina dai yanzu karabu da ita to meye kuma na tunaninta? Kaga idan yawo zaka dingayi damu saman titin nan toyi parking a gefe na sauka, haba! Wannan abu sai kace Romeo kana neman kashemu akan titi!"

"Sorry d'an uwa am enjoying the mood shiyasa" harara yasake balla masa kana yace

"Don kana enjoying mood d'inka sai kuma ka kashemu! Pls ajiyeni intari napep kaje can kaida mood d'in naka ku k'arasa" dariya yaya Mahmud yayi sosai sannan ya daidaita tafiyar motar akan titi.

Billy kuwa tana shiga ta tadda Basmah nak'ok'arin mik'ewa akan gadon ita kuma Batool na sallah, da sauri ta ajiye warmer d'in dake hannunta ta isa wajen had'e da rungumota gaba d'aya ajiki "haba yayya so kikeyi ne kafad'i baccin kinsan bakida k'warin jiki, zauna annan kifad'amun mekike so inkawo maki" kallonta tayi tana murmushi tace

"Sister u look so beautiful, Allah yasa yayanmu yaga wannan kwalliyar"

"Kai yayya manta da wannan, mekike sone" sake murmusawa tayi kafin tace

"Ke nake so 'yar uwata"

"Naji, nima ina sonki sosai fiye da kankaina"

"Da gaske?"

"Sosai kuwa yayya"

"Ngd sister dama toilet nake son shiga nayo arwala kozaki taimkamun"

"Ofcouse, tashi muje" har toilet Billy takaita sannan tajira tagama arwala tasake rik'ota suka fito, suma fitowa Batool tamik'e daga kan sallayar ita kuma tahau tafara sallah, hugging d'in Billy Batool tayi had'e da jujjuyata tace

"So cute twiny masha Allah, gaskiya kayannan sunfi d'agoki akanmu, may be don kind'an fimu k'iba, kinga yanda kika had'u kuwa? Gaskiya da akwai waya ahannuna da kinsha pics nak'in k'ari" saida Billy tayi murmushi sannan tace

"Thank you twiny,kin riga yayanki fad'a amma yarigaki aikatawa"

"Wow da gaske twiny? Can't wait to see d pics, nasan sunyi maseefar kyannan" dariya Billy tayi had'e da jawo warmer d'in data shigo da ita ta ajiye agaban Basmah data idar da sallah yanzu "yaya here's ur fav food Ummi tahad'o maki kuma tace tana gaisheki da jiki sosai"

"Allah sarki Ummi nayi missing d'inta kwana biyu" bud'e warmer d'in tayi had'e da cewa "awwwn..yummy, luv it much, Batool d'okomun plate naci kafin yawuna su tsinke" faten tsakin masara ne da yasha tarugu da alayyahu da kuma wake sai k'amshi ke tashi.

Dariya suka aza mata ganin yanda take sauri sauri wajen cire hijab d'in data gama sallah tajawo kular agabanta tana nema tasaka hannu, mik'ewa Batool tayi tana fad'in "kai yayya yihak'uri inkawo maki spoon da plate kada ki k'ona kanki, wannan irin zumud'i da kikeyi har ina!" Ganin zata b'ata mata lokaci ta mik'e da k'yar taje kitchen ta d'auko plate tadawo tad'ibi mai yawa sosai ta tasa agaba tafara sha tanayi tana lumshe idanuwa tana murmushi. Kallon Billy Batool tayi sannan tace

"My twiny kinga wani sonkai, ko tayi yayya takasa yimun"

"Hmm bari kawai twiny bansan wane irin so yayya keyiwa fate-fate ba, sanin soyayyar da take yimasa ne yasa Ummi tazauna da kanta tahad'a mata" saida Basmah tacika baki sannan ta d'ago kai tace

"Allah yabar mun Umminah shiyasa nake matuk'ar sonta araina" kallon juna sukayi suka kwashe da dariya suna mamakin yanda take tsananin son fate-fate aranta.

Sai bayan magrib Mahmud pilot yaje wajen motarsa yabud'e ya kwaso sayayyar da yayo d'azu kai tsaye falon Ummi ya wuce yazube kayan acan saman dining table yana tambayar Umma wai ina Billynsa, harararsa tayi had'e da cewa

"Yaronnan nalura rashin kunyarka na nema ya wuce wuri, ni kake kallo ka tambayeni wai ina Billynka take?" Kafin yayi magana Umma tajiyo muryar Ummi tana dariya tare da cewa

"Ai shine daidai uwar zamani sai d'an zamani, meye laifinsa tunda ke kikace a ajiye kunya agefe ke mai 'yah, babu wata rashin kunya tambayar inda k'anwarsa take yayi"

Murmushi Mahmud yasaki had'e da juyawa yana sosa kansa don maganar takoma tsakaninsu, yana shirin fita sai gasu sun turo gambun k'ofar had'e da shigowa, kasancewar Basmah ce agaba don itace tamatsa masu akan suzo tana so taga Ummi kuma tayi mata godiya, kawai saiji sukayi sunyi karo da juna, baya baya Basmah tayi zata fad'i yayi saurin rik'o hannunta, wani irin yarr taji ajikinta, soke kanta tayi k'asa alokacin da taga hannunsa rik'e da nata lumshe idanuwanta tayi tanajin wani sabon yanayin nashigarta, sanin cewa batada cikakkiyar lafiya yasa yak'i sakin hannunta saima jawota da yayi suka shiga daga ciki yanufi wajen dining table d'in da ita yana fad'in

"Sorry sister banlura daku bane da kinsa na ida gawar da batawa ba, sannu kinji? Hop jikin naki da sauk'i" gaba d'aya Basmah da Batool kallo suka bisa dashi ita kuwa Billy dama indai su Ummi na awuri yitakeyi tamkar bata san da shiba, kai tsaye tana shigowa wajensu tanufa tana basu labarin shan fatefaten yayya Basmah tana dariya,

Ganin haka yasa Basmah tayi saurin zare hannunta daga rik'on da yayi mata cikin i'ina tana fad'in "alhamdulillah yaya naji sauk'i" baro dining area d'in tayi tayo cikin falon tanaji zuciyarta na halba mata da sauri da sauri har k'afafuwanta na neman kasa d'aukar gangar jikinta, rik'on da Batool tayi matane yasa tasamu courage d'in k'arasawa tana gaisheda su Ummi, sosai Ummi taji dad'in ganinta tare da yimata ya jiki, Bini bini Billy ke d'ago idanuwanta suna had'uwa da na mahmud pilot dake can zaune yabuga uban tagumi had'e da tsareta da idanuwa, dasun had'a ido sai ya sakar mata murmushi itama saita mayar masa tare duk'ar da kanta k'asa, "Batool zonan keda yayya Basmah muyi firar bankwana kinji" yafad'a yana bud'e ledojin dake gabanshi, tashi su Umma sukayi suka shige d'aki abunsu ita kuma Billy ta nufi kitchen. Ko kad'an Basmah Bataso zuwa wajenba saboda yanayin da take jin kanta

Please Login or Register in order to submit comment