Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskanta daga wajen 'yan uwansa akan sai yak'ara aure amma shi kuma yakafe ya cije akan alk'awarin daya d'aukarwa kansa cewa bazai tab'a auren wata mace ba aduniya matuk'ar matarsa naraye, wannan dalilin yasa maganganun da sukeyi masa suka haifar masa da damuwa maitsanani data zame masa ciwon zuciya, haka sukaci gaba da rayuwarsu kowa na b'oye wa d'an uwansa ciwo da damuwar dake ransa don gudun tayarwa da junansu hankali, Ahmad yataso cikin gata da kulawar karatu har zuwa lokacin daya kammala karatunsa amatakin degree a inda yayi specializing a b'angaren likitan k'ashi, ranar daya dawo itace rana mafi muni da bazai manta da itaba ranar da tazamo silar fad'uwa katangar da suke jingine da ita wato mutuwar mahaifinsa,

Cike da farinciki yanufo gidansu don tabbatar wa da mahaifinsa samun nasarar da yayi wajen karatu domin shine d'alibi nafarko amakarantar da yafi kowane d'alibi maki ashekarar wanda har saida aka karramashi da lambar yabo, yana isowa unguwarsu ya hango cincirindon taron mutane a k'ofar gidan tsaitsaye, da sauri yak'arasa wajen ya hango wani alhaji tukur tsaye yasa ana firfitowa da kayansu ana jehowa waje, hango Abbansa yayi durk'ushe agaban alhaji tukur shida mamynsa suna bashi hak'uri amma ina ko kallonsu beyiba balle susa ran zai karb'i hak'urinsu, aguje yak'araso wajen tare da sa hannuwansa ya d'ago mamy da Abbansa idanuwansa na zubar da hawaye yace

"Haba Abba meyasa zaku k'ask'antar da kanku agaban wanda yake mutum irinku bayan Allah yayi maku daraja, waima meyake faruwane Abba?" Kasa magana yayi saima k'wace hannunsa da yayi yanufi wajen alhaji tukur yana k'ara yimasa magiya akan yayi hak'uri ya rufa masa asiri amma yak'i saurarensa har saida yasa kwad'o yarufe gidan sannan yajuyo cikin fad'a yace

"Alhaji Bashar! Alhaji Bashar! Wlh Allah idan kaga nabaka makullan gidannan ka koma ciki to tabbas ka biyani kud'ad'ena danake biyarka gaba d'aya! Idanko ba haka ba baka ba komawa cikin wannan gida matsiyacin banza matsiyacin wofi" a k'ufule Ahmad yayo kansa had'e da cin kwalar rigarsa idanuwansa sunyi jawur saboda tsananin b'acin rai ,Abba dake duk'e yana sharb'ar kuka yayi saurin dakatar dashi "sakeshi Ahmad gaskiya yake fad'a bayada laifi" sakinshi yai yana wani irin huci sai kace kububuwa sannan yadawo wajen mahaifinsa shima yana kuka, haka itama mamy kukan takeyi kamar ranta zaifita, yunk'urawa Abba yayi zai tashi had'e da d'ago kansa yana kallon mamy dake faman kuka yana girgiza mata kai alamun tayi shiru kawai sai sukaga yafad'i k'asa jini nafitar masa ahanci, da sauri Ahmad yayo kansa ya d'agosa lokacin yana goge jinin dake zubo masa da hannunsa, kallon mamy data k'araso wajen tana kuka yayi tare da rik'e hannunta sosai, wata irin ajiyar zuciya yayi bayan yasake goge jinin dake zubo masa sannan yakai kallonsa ga Mahmud dake fad'in Abba tashi muje asibiti yana kuka, cikin k'arfin hali yabud'e baki yace

"Kuyi hak'uri, sannan kuyafemun wannan abun fad'i dana bar maku, ni nasan bazan tashiba a wannan karon, mamyn Ahmad akwai abubuwan dana b'oye maki baki sani ba, kimanin shekaru 7 kenan ina fama da ciwon zuciya wanda nayita boyewa gudun kada kusani in sakaku cikin damuwa, sau biyu yana yimun tsanani har inkwanta asibiti jinya na tsawon kwanaki amma sai inb'oye maki akan nayi tafiyane idan kika kira saboda ban dawo gidana, likita ya tabbatarmun da cewa kada inkoma bari hakan tafaru akaro na ukku domin barazana ne ga rayuwata, amma kinga yanda Allah yanufa" wani irin tari yayi da yasa saren jinin fitowa daga cikin bakinsa da hanci yana zuba" Ahmad na kuka ya ciccib'i Abba suka nufi titi amma sai ya dakatar dashi,

"Kabarni Ahmad bazan rayuba, kawai kasaurari abunda zanfad'a maka idan Allah yabani iko, ga amanar mahaifiyarka nan kakula mani da ita sosai, kabata farinciki, kuma kayimata duk abunda takeso idan Allah ya hore maka kada kabari ta tab'a yin kuka dakai domin tamatuk'ar shan wahalar rayuwa a dalilin haihuwar ka, wata biyu da suka wuce mamynka tayi fama da ciwo sosai lokacin kana makaranta wanda yakaita ga kwanciyar asibiti, anan aka buk'aci cewa ciwon dake mahaifarta zai iyasa tarasa rayuwarta matuk'ar ba'ayi mata aikiba aka cire mahaifar, kimanin kudin aikin naira dubu d'ari biyar da hamsin sukace suna buk'ata kafin suyimata aikin gashi ina kallonta rai ahannun Allah, gashi alokacin dubu uku ne kad'ai acikin aljihuna, sanin kankane sana'ar da nakeyi karb'a nakeyi in aza tawa ribar idan nasa yar sai inmayar da kud'in ga maisu don haka banida kud'in da zasu isa ayimata aikin, ganin bazan iya zuba idanuwa inrasata ba yasa naje wurin alhaji tukur rancen kud'i amma fir yace bazai bani ba har sai inzan bashi jinginar gidana dafarko dai banyarda ba amma ganin banida mafita yasa nakoma nafad'a masa na amince, inaji ina gani yasa aka kawo takardar yarjejeniya nasa hannu shima yasa abun takaici dubu d'ari uku kad'ai yabani da k'yar ina kuka narok'esa nasamu yacikaman dubu hamsin yarage saura dubu d'ari biyu har yau, hakan yasa nakoma shago na kwashe sauran buhuhun fulawar mutane dake hannuna kusan buhu arba'in da biyu nasa akasuwa nasayar, na har had'a kud'in suka kama dubu d'ari hud'u da tamanin yazamana saura dubu sittin in had'a kud'in aikin mahaifiyarka, da qyar nasamu likitocin suka amince zasuyi mata aikin bisa sharad'in baza'a bamu sallama ba har sai mun biya sauran kud'in, gudun kar inrasata yasa nasake amincewa nan da nan aka shiga da ita wajen tiyatar bayan and'ibi gorar jinina biyu, duk inda yakamata inje neman taimakon sauran kud'in da zanbiya naje amma bansamuba, hatta 'yan uwana hanamin sukayi wai indai da kudinsu zata rayu to saidai tamutu inyaso dole na auro wata, alokacin naso kiranka infad'a maka amma dana tuna semester k'arshe kake bai kamata abari hankalinka yatashiba alokacin saina hank'ura, nabawa wani mak'wabcina aron shagona akan ya aramani dubu sittin d'in inyaso shi sai yaci gaba da sana'a acikin shagon ni kuma duk lokacin dana biyashi sai yabani abuna. Da haka nabiya kud'in kuma alhamdulillah ga mahaifiyarka nan tasamu lpy, wa'adin daya kamata nabiya alhaji tukur kud'insa yacika har yawuce amma banida zarfin biyansa shiyasa ya aikata hakan kuma yanada gaskiya tunda munyi arubuce, inaso in Allah yakarbi raina katabbatar kabiya kud'ad'en da mutane kebiyata ka karb'o makullan gidannan don shi kad'ai na mallaka aduniya, kuyafemun bisa wannan yanayi da zanbarku aciki, gaba d'ayanku Allah yayi maku albarka"

Yana gama fad'ar haka rai yayi halinsa atake mamy tasome wajen, duk mutanen dake wurin sun matuk'ar tausayawa mamy da Ahmad kasancewar mahaifinshi mutumen kirkine kuma ba'a tab'a jin yayi fad'a da wani ba, nan take limamin anguwar yasa aka kwashe kayansu aka kai gidansa sannan aka d'auki gawar Abba Ahmad nakuka aka suturcesa akayi masa sallah sannan aka kaishi gidan gaskiya, mamy kuwa har aka kauda Abba bata farfad'o ba, nan take mutuwarsa ta karad'e garin ta ko ina gaisuwa ake zuwa saboda ansan shi da mutunci sosai, lokacin da alhaji tukur yaji zancen mutuwar Abba gaba d'aya jikinsa yayi sanyi don harda kuka yayi da dana sanin abunda ya aikata masa har yazama silar rasa rayuwarsa, makullan gidan ya d'auka yakaiwa liman tare da bada hak'uri yace suzama sheda yayafewa Abba kud'in da yake bisa duniya da lahira, murmushin takaici Ahmad yayi batare daya ce komai ba amma yasa aransa matuk'ar Allah yahore masa zai biyasa kud'insa kamar yanda Abba ya umurcesa, tunda tun yana raye bai yafe masa suba to babu buk'atar yanzu ya yafe masa, wannan dalilin yasa yana fara kwasar albashi ya biya wanda ke biyar Abba dubu sittin da kuma kud'in fulawar da Abba yasayar ta wanda ke bashi yana sayar masa yacire ribarsa. Yanzu kuma saura dubu d'ari uku da hamsin kud'in alhaji tukur yabiya suma yana kan har had'a masa abunsa. Goge hawayen da suka zubo masa yayi yana kallon mamy dake wanke naman kajin zata zuba atukunya ta d'ora kanwuta, sai yaji wani irin tausanta ya mamaye zuciyarsa, aransa yace Allah sarki mamynah yanzu asanadiyata akacire maki mahaifa badon hakaba da yanzu kin haifi wasu 'ya'yanki kuma k'annena dazan dinga kalla inji sanyi, tasowa yayi had'e da rungumeta yace

"Ina sonki mamy, ina sonki sosai fiye da rayuwata mamynah" murmushi tayi itama tace

"Nima haka amadidinah" duk suka kwashe da dariya atare.

Tun ranar da mom ta koma papi yayi niyar kiran Mahmud tasanar dashi zancen auren da yake son had'awa da 'yar wajen amininsa amma hajia kaka tahana tace yabari har sai ankwana biyu tukuna, yau kam papi yalashi takobin sai ya fad'awa jikansa qudurinsa don haka ya d'auki waya yakirasa akan yazo yana son ganinsa, bayan asa d'aya saiga Mahmud ya iso gidan bakinsa bud'e yana fara'a shida yaya Mahmud pilot dayake dawowarsu kenan sunkarb'o motocin da dady ya saya masu saiga kiran papi yashigo wannan dalilin yasa sukayo nan tare kafin su wuce gida , bayan sun gaggaisa an d'an tab'a wasannin jika da kaka papi yayi gyaran murya cikin dattako yafad'awa Mahmud cewa yaje gidan amininsa da suka gaisa dashi ranar akwai jikanyarsa da sukayi magana dashi akan zasu had'a aurensu idan sun daidaita shikenan sai ajira ranar buki ya huta da zaman gwauran taka papi yak'are maganar cike da tsokanarsa, sanin halin papi da yayi akan magana d'aya yasa yad'ago kai kamar zaiyi kuka yace

"Don Allah papi kayimun rai, wlh da akwai wacce nakeso kuma munyi alk'awarin aure da ita, kai da kanka kasha fad'amun babu kyau karya alk'awari idan kuma nabarta na auri zab'inka ai kaga siffofin munafukai sun tabbata akaina, idan yayi alk'awari ya sab'a koba haka ba papi?" tunda Mahmud pilot yaji zancen papi dariya ta cika masa ciki amma ba halin yinta saboda yanda papi yatsare gida, hajia kaka kam dariya tadingayi tana fad'in to banda abunka mommodu ai kai mijin mace hud'u ne saika had'a duka su biyun ka aura,

"Kai hajia kaka kiyimin adalci kice ni mijin mace hud'u ne to idan nagado papi fa"

"Aaahaf..nafa ganoka yaro, bama zaka gado shiba inkuwa so kakeyi ka gadoshi saidai in zabinka zaka hakura dashi kabi zab'insa kaga shikenan kayo gadonsa" hajia kaka tafad'a cike da tabbatar masa da maganarta. Kad'an yarage yafashe da kuka don gaba d'aya yau ancaza masa kai alamurransa gaba d'aya sun hargitse masa,

"Mahmud katashi katafi ni bashawara nake nemanka ba umurnine kawai nabaka kuma cikin satinnan nakeso katafi kaji ko" papi yafad'a yana kallonsa.

Jiki ba k'wari Mahmud yamik'e yana fad'in "to papi" sai anjima sukayi masu sannan suka fita batare daya nuna masu kyautar motar da dady ya siya masu dayake ta d'aukin zuwa yagwada masuba.

Suna fita Mahmud pilot yakece da dariya hadda rik'e ciki yana cimasa "kaiii gaskiya natayaka murna d'an uwa irin wannan farinjini haka, mata uku ajere congrat Allah ya tabbatar mana da hakan" cike da b'acin rai yaya Mahmud yajuyo dak'arfi yace

"Ba amin ba! Ba amin ba kai bakada tausayine?" d'an ja da baya yayi had'e da cewa

"Cool...d'an uwa 1-1 katuna ko?"

"Mtssss badai cool ba d'an uwa saidai hot....





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Gaisuwa tare dafatar alkhairin Allah da rahamarsa sulullub'e rayuwarki data gidan auren ki my dear sister in-low *MARYAM HAMZA* (Mr's Manir katuka), bakina bazai iya fad'ar farincikin dana tsinci kaina acikiba lokacin danayi karo da dad'ad'an kalamanki dkuma shawarwari agareni, hak'ik'a inajin dad'in yanda kike bibiyar wannan littafi daki daki, fatana Allah yatabbatar da soyayyarki azuciyar yayana tahar abada kuma ya albarkaci 'ya'yanah yasa suzamo abun alfahari agaremu duniya da lahira, LUV U SO MUCH MY IN-LOW🥰❤_

💎Page_____47💎


Suna fita hajia kaka ta kalli papi tace

"Bai kamata ka tirsasa yaron nan ba tunda har akwai wacce yakeso aransa, katuna bamuda wani cikakken Iko akansa kasancewarsa jikane nawajen 'ya mace inda ace mahaifinsa muka haifa to zamu iyayi masa tilas, yanzu idan kuma shi mahaifin nasa ya nuna rashin amincewarsa yazamuyi?" Cikin basarwa papi dake rik'e da 'yar sandarsa yana k'ok'arin mik'ewa yace "karki damu baby nafad'a masa hakanne don natabbatar zaije, idan kuma har baijeba shikenan nasamu amsar da zan dogara da ita wajen bawa aminina hak'uri da fad'a masa cewa yaron yanada wacce yake so, kinga rashin zuwan nasa zai tabbatar masa da haka kuma zai fahimceni"

"To idan kuma yajefa?" Itama tafad'a tare da mik'ewa tabi bayansa, dakatawa yayi da tafiyar daya farayi tare da juyowa yana murmushi

"Shikenan dama hakan nafi buk'ata, sai ahad'a masa duka biyun ya aura" cikin tsokana hajia kaka tak'araso gabansa tana fad'in "idan aka aura masa mata biyu ni kumafa? Ina zai kaini" hannunsa ya d'ora akan kafad'arta ya rungumota ajikinsa yana dariya " sai yabarki wajen mijinki dama can fashine yayimun" da haka suka shiga d'aki abunsu tana addu'ar Allah yazab'awa jikin nata mace mafi inganci daga cikin 'yan matan.

Suna isowa kai tsaye suka wuce part din mom, Basmah na zaune Batool na tsefe mata kai afalo, da sallama suka shigo palourn kan Mahmud pilot na sunkuye ak'asa, Basmah najin muryarsa gabanta yayi wani irin fad'uwa da sauri ta k'wace kanta dake hannun Batool tashige d'akinsu, duk yanda take son ciresa aranta takasa, kullum soyayyar sa ruruwa takeyi acikin zuciyarta, tunowa da kalamansa nad'azu tayi batasan lokacinda hawaye suka zubo mata ba tafara kuka, Batool kuwa saida tagaishesu sannan tabi bayan 'yar uwarta sautin shesh-shekar kukanta da taji yana tashi tun abakin k'ofa yasa tayi saurin K'arasawa wajenta "Yayya Basmah ya da kuka haka?, meyake damunkine? Yanzufa muka gama fira lafiya dake shikenan sai nasameki kina kuka, meyake faruwa da kene?" tak'arasa maganar had'e da tallafo kanta,

"Nashiga uku Batool nakasa dena son yaya Mahmud, muryarsa kad'ai idan naji wata irin wutar sonsa kesake ruruwa acikin zuciyata" juyar da kai gefe Batool tayi kafin tace

"To shine me yayya Basmah, kije kifad'a masa, ke 'yar uwar sace kuma natabbata bazai k'ikiba, idan kuma bazaki iya fad'a masa ba nibari inje infad'a masa" kanta ta ajiye akan katifa had'e da mik'ewa tarik'o hannunta da sauri,

"Don Allah kada kiyi haka 'yar uwata, zan k'ara tirsasa zuciyata akan tahak'ura dashi amma bazan iya yafewa zuciyata ba idan tabari kika aikata haka"

"What? Mekike fad'a, so kike kiyiwa kanki illa akan abunda kike da tabbaci akan samunsa, to tukunama don me bazaki fad'a masa ba kuma bazaki bari afad'a masa ba, haba 'yar uwa bazan iya jurar ganinki haka ba" hannunta tarik'o sannan ta d'ora d'ayan hannunta akai tace

"Saboda bani yake soba, yanada nashi zab'in ransa"

"And so what? Ko kin manta shi mijin mace hud'une zai iya had'a zabinsa dake ya aura"

"Bazai yuyuba!, kuma bazai tab'a yuyuwa ba Batool domin zab'insa jininace da Allah ya haramta masa aurenmu mubiyun kuma alokaci d'aya"

"Mekike nufi yayya, kwata kwata kinsani aduhu ban fahimcekiba" kallonta tayi idanuwanta na tsiya yar da hawaye tace

"Ina nufin 'yar uwarmu Billy itace zab'in yaya Mahmud, da kunnena naji yana fad'awa yaya cewa ita yakeso kuma zai iya rasa rayuwarsa akanta, kinga kuwa matuk'ar zai aureta bazai yuyu ya aureni ba, narasa sa kenan har abada" tasake fashewa da wani kukan, mutuwar tsaye Batool tayi tana furta innalillahi wa inna ilaihirraji'un,

"Amma yayya naga ko shiri bayayi da twiny kuma natabbata shi kad'ai ke kid'ansa ita bata sani ba, mezai hana kisanar dashi kafin yafad'a mata"

"Bazan iyaba, idan nayi haka naso kaina da yawa, karki mantafa nasan yana son k'anwata taya zancutar dashi tahanyar hanasa samun burin ransa, shin ni idan aka yimun haka zanji dad'i?" Cikin tausayawa da kalaman dake fita bakin 'yar uwarta tace

"Shikenan ni zanje nasanar da Billy duk halin da akeciki" zabura Basmah tayi had'e da mik'ewa tarufo k'ofar d'akin sannan tadawo gabanta ta durk'usa tare da had'a hannuwanta waje d'aya tace

"Narok'eki Batool ko mom kada kibari tasan da soyayyar da nakeyiwa yaya Mahmud balle Billy, inaso kiyimun alk'awari komai rintsi komai wuya zaki rufemun sirrina hakan kad'ai zaisa nasan kina k'aunata kinji 'yar uwata" ganin yanda take kuka tana rok'onta yasa tayi saurin saukowa akan gefen gadon da take zaune ta rungumeta " shikenan yayya Basmah bazan fad'aba matuk'ar hakan zaisa kiyi farinciki nayi maki alk'awarin zan b'oye sirrinki har iya k'arshen rayuwata, amma pls kidena wannan kukan zai iya haifar maki da matsala kinji ko?"

"Shikenan nadena bazan komaba, kin ganima nashare hawayen?" Basmah tafad'a tana goge hawayen da suka zubo mata a idanuwa.....


_pls kuyi manage, inabaran addu'arku zuwa ga yayata data haihu yau, kuma Allah ya sauketa lafiya tasamu baby girl nasamu takwarata (Bilkisu) amma allah yayi ba rayayya bace takoma😭😭😭😭, kusata cikin adduarku Allah yabata lafiya kuma yabata juriya da hak'urin raahinta,_"😰👏🏻






*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____49💎


A b'angaren yaya Mahmud kuwa kallon mamaki yabi Basmah dashi lokacin daya ga tabar palourn aguje sai kuma yabasar a tunaninsa k'ilan tayi hakan ne saboda bata so ya rik'eta ayanayin da take ciki, mere baki yayi aransa yana cewa ai anriga angama inji mai kashi gado.

Suna zaunawa saiga mom tafita daga bedroom d'inta zata shiga kitchen, ganinsu yasa tawuce cikin palourn kai tsaye tana murmushi,

"My son da kuma my son again, yaushe kuka shigo yaran basuzo suka fad'a mani ba" tajuya tana kallon inda tabar su Basmah azaune suna tsifar kai,

"Ai yanzun nan muka shigo mom, barka da marece anwuni lpy?" Yaya mahmud pilot yafad'a yana sissinne kai k'asa

"Lafiya klw Mahmud ina kabaro junior sarkin rigima da ummanku duk lpy suke"

"Lafiya klw mom, gashican shida su Bassam suna buga Ball aharabar gida" nan shima yaya Mahmud yaga ida mom ta amsa tana fad'in

"My son meyake damunka nagaka ahaka" murmushin yak'e yayi masa kafin yace

"Farinciki da akasinsa mom" alokaci guda yana kallon Mahmud pilot

"To afad'amun farincikin akasinsa kuwa anemi sauk'insa ga Allah" murmushi pilot yayi had'e da cewa "k'yalesa mom duka farincikine saidai inbayaso kijine kawai" harararsa yayi kafin yace "haka kace ko? shikenan Allah yayi maka yanda yayimun"

"Ba amin ba, kaifa..." Mom na dariya tace a'a to ya abun yakene Mahmud kace duka farincikine amma ya rok'amaka kace ba amin ba, afad'amun naji ko meye tak'are maganar tana kallon yaya Mahmud, kamar su had'a baki atare suka mik'owa mom makullan motar da dady ya siya masu suna fad'in "surprise from our dad, motocine guda biyu ya siya mana yanzu haka suna cikin gidan nan munzo dasu" cike da farincikin dake k'unshe da mamaki tace

"Wow.. masha Allah yaran dady, congrat, gaskiya dady ya iya surprise, irin wannan kyauta haka? to Allah yasa ku kashe da kanku kuma yakarawa dady arzik'i" su duka suka amsa mata da amin, mik'a masu makullan tayi tana fad'in to saura d'ayan farincikin shi kuma ina saurarenku, Allah yasa shi kuma makullan gidajene aka baku" dariya Mahmud pilot yayi sannan yace

"A'a mom ai wannan kyautar tamusammance, d'an uwana kad'ai akayiwa ita" kallonsa yayi sannan yaci gaba da cewa "mom masu zaman gidan aka fara bashi kafin gidan yazo" murmushi mom tayi had'e da dafa kafad'ar yaya Mahmud "my son wannan kake kira akasin farinciki, baka son nima inga 'yan jikokina ne halan" "mommmm" yafad'a tare da rik'o hannuwanta kamar zaiyi kuka, "Ba wannan ne matsalar ba, mata uku fa mom!?"

Tashi Mahmud pilot yayi yana dariya yace "d'an uwa nidai bari naje don nagaji dajin wannan irin raki naka haka, kasameni a part d'in Ummi, mom sai anjima"sannan ya ficewarsa, kallonsa yaya Mahmud yayi batare daya amasa masa ba tare da kallon mom, hannunta tasa a gefen fuskarsa had'e da cewa,

"Kamarya mata uku my son, da wasa kakeyi ko kuma mafarki"

"Taya zanyi wasa da mahaifiyata ga abun da nasan itama zan iya sakata cikin damuwa, da gaske nakeyi mom, inada wacce nakeso arayuwata kuma nayi mata alk'awarin zan aureta, sai ga dady kuma yasanar dani cewa sun yanke shawarar had'ani aure da 'yar gidan amininsa alhaji usman, ina cikin jimamin maganar dady kuma sai ga papi ya kirawoni wai shima yasamar mun mata 'yar wajen abokinsa, mom taya zan iya rik'e mata uku acikin wud'annan shekaru nawa" ya k'arasa maganar kamar zaiyi kuka, shiru mom tayi tana nazarin maganganun yaronta kafin tace

"Ka kwantar da hankalinka babu wanda zai aura maka har mata uku alokaci d'aya dole ko hakan zai faru ya zamana a maban banta lokutan, kai dai abunda nakeso dakai kamar yanda papi ya umurceka katafi wajen wacce ya zab'o maka to katafi, shi kuma dadynka kajira amsar da zidawo maka da ita, ya sunan ita yarinyar da kake sone?"

"Faraaha"

"To kaje nidai babu abunda zan iya yi acikin wannan alamarin banda shawarar dana baka" duk da yaya Mahmud nacikin damuwa saida yayi mamakin mahaifiyarsa domin ko kad'an banyi tsammanin zata amshi wannan magana da sauk'i haka ba, tabbas d'an Adam d'an tara ne, duk yanda kake kallonsa da hawaye marasa kyau to akwai lokutan da idan annatsu za'aga yana da wasu kyawawan halaye daban, yau ga mom d'insa tana magana irin yanda Ummi keyi cike da fahimta da kuma natsuwa, tabbas soyayyar uwa awurin d'anta daban take, murmushi ya sakar mata tare da rungumeta "mom nagode da shawararki, kuma nasamu natsuwa sosai fiye da lokacin dana shigo, in sha Allah zanyi kamar yanda kikace, ubangiji Allah ya zab'a mana mafi k'ololuwar alkhairin sa"

"Amin my son" bari naje na d'ora abunda za'aci naji har ankira sallar magrib, bai bar part d'in mom d'in saba saida yayo arwala yana fitowa ya wuce masallaci kai tsaye yanajin wata 'yar k'aramar natsuwa na ziyartar zuciyarsa.

Izuwa yanzu zuciyar Batool tagama yarda da soyayyar Dr Ahmad d'ari bisa d'ari domin duk bayan mintota sai kalamansa sun dawomata ga kunne, lokaci guda kuma idan ta tuno da kyakkyawar fuskarsa da zati dayake dashi saita tsinci kanta cikin murmushin da batasan lokacin dayake fitowa ba, idan kuma tatuno da yanda yaraza lokacin data sakar masa ihu har ya k'wale kansa saitayita dariya, yama zaune take tana tunaninsa tana dariya saiga Billy ta iso wajen rik'e da hannun junior, kallo d'aya tayi mata takauda kai had'e da samun wuri can gefe da ita kad'an ta zauna, juyowa Basmah tayi tare tsagaita dariyar da takeyi "twiny ya da haka naga kin wani ja tunga gefe?"

"Ai dole inyi haka kafin kishak'o wuyana, wannan irin dariya haka ko control babu" muryar yayya Basmah sukajiyo abayansu tana fad'in

"Kema kyafad'a sister, d'abi'ar data sameta kenan yanzu kullum cikin tunani da faman dariya take, inajin tsoron inba wata cutarce takamata ba" d'ago kai Billy tayi tana murmushi "Yayya Basmah ina wuni barka da marece"

"Yawwa my sisto ykk!?" Hannun junior tarik'o had'e da cewa

"Junior how far? Give me five" hannunsa yabata suka kashe tare da zaunawa tana kallon Batool

"Kai yayya Basmah wannan irin kallo haka, twiny matso kusa nabaku labarin abunda kesakani dariya" tasowa Billy tayi ta dawo gefen Basmah tare da aza kanta akafad'arta "yawwa to muna saurarenki 'yar gidan mom koba hakaba yayya" murmushi kad'ai ta iya yimata batare data amsa ba tana wasa da hannuwan junior. Cikin shauk'i Batool take kallon k'afar data jimu tana murmushi sannan tace

"Kuna tuna ranar da aka kaini asibiti gyaran k'afata, zaku iya tunawa da labarin dana baku akan abun da yafaru tsakanina da dr. n?"

"Eh.eh.sai akayi me?" Billy tafad'a cike da zak'uwar son jin abunda zata fad'a masu, murmushi Batool tasakeyi sannan taci gaba da cewa "shine ranar yakira yaya mahmud da lambar aunty faraaha aka bani shine yace wai soma yake" murmushi Basmah tayi don dama tasan anan labarin zaya dire, ita kuwa Billy kwaro idanuwa waje tayi tace "and ke kuma sai kikace me?" Had'e da dawowa gefenta tana dariya

"Ban bashi amsaba, amma dai nima na fola" dariya suka saka gaba d'ayansu hadda Basmah

"Shikenan yaya Mahmud yasamu 'yar uwar folawa ko yayya Basmah?" Billy tafad'a had'e da mik'a mata hannu suka tafe,

"Kwarai kuwa sisto, yaya Mahmud ya fola, Batool ta fola, yaya Mahmud pilot ma ya fola" tsalle Billy tayi cike da jin dad'i tana fad'in "dagaske yayya Basmah? kice so soon zamusha buki, sauran kema ki fola duka muhad'a mukaiku d'akunanku muhutawarmu ko junior?" Tafad'a tana jamasa kumatu, duk abunda kefaruwa Mahmud pilot yana tsaye jikin tagar d'akin yaya Mahmud yana kallonsu amma baya jin abunda

Please Login or Register in order to submit comment