Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manta daku da alak'ar dake tsakaninmu yaya kai kasan bai taso ba, don kai shedane akan bana iyayin wata banzo gidan nan ba duk da cewa ko kunyimun tsakani dashi"

"Kana zuwa mana amma kafad'amun shin wakake kulawa dashi acikin gidannan idan kazo inba da sashenka da yake mallakinka, shima don kasan cewa hak'k'in kane bamuda ikon hanaka zuwa shiyasa amma natabbata badon hakaba da tuni kamance damu har abada saboda kanada arzik'in da zai iya wadatar dakai daga rashinmu"

"Bahaka bane Yaya Allah shine sheda akan duk kwanan duniya da soyayyarku da k'aunarku nake kwana araina, hatta zuwan da kake gani inayi gidannan don kawai in gankune kuma insan awane hali kuke ciki bawai don inzo inshiga sashene kawai bane, don Allah Yaya kumanta da komai kuyafemun wannan kuskuren da nima na aikata, nafahimci cewa a rayuwa babu abu mafi muhimmanci fiye da 'yan uwa, tarin dukiya ko 'ya'ya da mata bazasu tab'a iya maye mani gurbin 'yan uwana ba"

Alhaji Kabiru daya dad'e da gano duk abunda yafaru laifin sane da har yayi sake ya amince da zancen matansu da makirci akan cewa matar d'an uwansa mayya ce ita take kashe masu yara kuma tana neman rabasu da d'an uwansu ta magancesa baya jin maganar kowa sai tata har suka amince suka tirsasa sa akan sai ya saketa ko kuma yabar gidan don bazasu lamunci haka ba, alokacin hajiyarsu nada rai itama tagoyi bayan haka aka yiwa hajia Aisha k'ask'anci lokacin dady bayanan yayi tafiya ita kuma mom dama da ita akashirya makircin ranar batanan taje anguwa nan aka samu damar korota agidan, kora ta k'ask'anci da walak'anci tana kuka saiga dady yadawo hakanne yajawo duk matsalar data faru har dady yayi fushi ya maida hajia Aisha gidansu lokacin bayada wani arzik'i ita kuma mom yabarta acan saida yasamu gida na daidai zaman mace d'aya sannan ya d'auko hajia Aisha yadawo da ita, yayinda gaba d'aya 'yan uwansa suka d'au fushi da gaba dashi kasancewar shima yaji zafin abun sai yabiye masu ita kuma mom tanaji ya tare can cikin gari shida hajia Aisha ta sake tsunduma cikin damuwa tare da kishi da takaicin hajia Aisha lokacin tana goyon Yaya Mahmud ta dinga fitina ala tilas sai itama takoma acan inda suke, nanma mahaifiyarsa ta goyi bayanta dole yabid'i haya daidai gidan mace biyu itama ya maidota sai yazamana idan kaga yaje can gidan to don mahaifiyarsu kad'aine kuma tana rasuwa ya d'aukewa gidan k'afa na tsawon lokaci bai sake waiwayar kowa ba sai daga baya daya fara had'uwa da matsalolin rashin had'in kan yaransa bayan Allah ya arzutashi, sai yagano illar rarrabewar kan da 'yan uwa kesamu itake janyo babbar matsala tare da wargaza gida, umman borno kuwa sanadiyar tayi fad'a sosai lokacin da abun yafaru tanuna tana bayan dady ba'a kyautaba akan abunda akayi masa yasa itama suka cicci mutuncinta tare da d'aukar gaba mai tsanani a tsakanin dukansu yazamana basa mu'amala da ita duk lokacin da tazo cikin hantararta suke ita da 'ya'yanta sai itama tad'auke k'afarta agidan bayan rasuwar mahifiyarsu, kallon dady alhaji Kabiru yayi tare da cewa

"Mezance d'an uwana, kuskurene yariga da yafaru amma don Allah kaima kayafe mana duk wannan abun sharrin shedanne da muguwar zuciya data amince mana da yarda da zantukan mata"

'Dago kan da dady zaiyi saiga alhaji bukar ya hango yatunkaro wajen yana kallon mutanen dake kwasar kayan cikin motar da suka zo da ita yana fad'in "Ahh alhaji babba yau kuma wane shagali ka tanadar mana agidan naga ana shiga da kaya batare daya lura da dady dake durk'ushe agaban alhaji Kabiru ba, saida ya ida k'arasowa wajen yagansa, juyawa yayi zaibar wajen da sauri dady yataso tare da rik'e masa k'afafuwa yana fad'in

"Yaya kayi hakuri kada kujuyan baya akaro nabiyu, nayarda nayi kuskure kuyafemun, amma don Allah kubarni in rayu daku 'yan uwana, kubari yarana da yaranku sugane cewa su 'yan uwane najini, mumanta da komai Yaya kubarni inrayu daku saboda nafahimci ku 'YAN UWANA NE da banida tamkarku"

"Sai yanzu kafahimci haka Bashar bayan kagama nunawa duniya mu bamudavmuhimmanci agareka kuma ba'a bakin komai mukeba tunda ka iya bada auren 'ya'yanka da kanka, to yanzu mu mezamuyi maka"

"Kuyimun afuwa nayarda da wannan kuskuren amma nayi hakanne saboda tsoron kada tsana da fushin da kukeyi dani ya shafesu idan naturosu wajenku, yazu kuma bawai nazo don kuyimun komai bane face kuyafemun saboda naji bazan iya cigaba da rayuwata ba matuk'ar ban daidaita tsakanina daku ba kuma bazan tab'a yafewa kainaba bisa cutar da 'ya'yana danayi na nisan tasu da 'yan uwansu don Allah Yaya bukar kuyi hak'uri kugafarceni" kasancewar bukar mutumne mai sauk'in kai da sanyin hali yasa nan take jikinsa yayi sanyi yasa hannuwa nsa ya d'agosa suka rungume juna, yace

"Kaima kayi hakuri kayafemu domin duk kuskuren namune, mundad'e da gano hakan amma ganin yanda Allah ya arzuttaka yasa muka kasa fuskantarka don gudun kada kayi tsammanin ko dukiyarka tasa muka karaya akan abunda yafaru, amma maganar gaskiya munji zafi matuk'a daka kasa tunkararmu lokacin da auren yaranmu yazo kanuna bamuda wata daraja da zaka turosu su gaishemu balle harma musa ran zasuzo neman auren 'ya'yanmu awajenmu"

"Yaya nayi kuskure ayafemun natuba"

Sakinsa yayi tare da rik'o hannunsa suka dawo gaban babban yayansu alhaji Kabiru dady ya sake basa hak'uri shima dai nan yayi masa fad'a sosai akan abunda yayi masu na batun auren ya kumace sun yafe masa amma su bazasuje d'aurin aurenba saidai sunayi masu adduar Allah yazaunar dasu lafiya, dakyar da sud'in goshi dady yasake shawo kan alhaji Kabiru ya amince akan zasu tafi kuma amatsayin waliyyan amaren wato 'ya'yansu, nan dai sukayita biya magana daga k'arshe suka yafi juna tare da rungume junansu cikin so da k'auna.

Muzammil kuwa da suke kira baba k'arami har lokacin yana can gefe shibsarkin zuciya sai cika yakeyi yana batsewa yana ganin haka yasaci kallonsu da gefen ijiya tare da yin k'ofa ya juyar da kansa gefe,

Murmushi dady yayi hade da cewa "Ai kayi sake da kabari nazo amatsayin yayanka baba k'arami, inma zakazo muyafi juna to kazo, don duk tajaicinka da kumburin fuskarka saidai ka had'iye zuciya, 'YAN UWANA NE dai sunriga da sun yafemun kuma ina mai alfahari da hakan, kai kuma tunda kace niba d'an uwanka bane to kajira isowar yayarka hajia hafsatu zansa tad'aga mankai inzaneka ko kuma ita tazaneka kuma agaban 'ya'yanka" gaba d'aya su alhaji bukar da alhaji Kabiru sukasa dariya, tasowa yayi had'e da duk'awa agaban dady yace

"Kayi hak'uri Yaya nayi kuskure bisa kausasa kalamaina da d'aga muryata agareka insha Allah hakan bazai sake faruwa ba"

Rungumesa dady yayi had'e da cewa

"Bakomai kaima kayi hak'uri, matsoraci kawai daga kiran sunan auntyn taka harka karaya?" dady yafad'a cikin sigar tsokana, dariya suka sakeyi muzammil nafad'in

"wooo..ba dole ba ai aunty boss ce ko ince wuta, Sam bata son raini ko rashin gaskiya arayuwarta, Ina fani lokacin hatta hajia budema wuta tajeyi idan akayi ba daidai ba balleni, ai k'aramin aikintane idan taji abunda yafaru tayimun fiye da abunda yafi duka, Allah dai yasa tarage fad'annan nata"

Nan dai sukaci gaba da firarsu ta yaushe gamo bayan dady yayi masu bayanin anjima nan zai kawo amaren zasuyi bridal shower tare da fad'a masu yanda sauran shagalgulan bukin zasu kasance har zuwa ranar d'aurin aure.

Sunji dad'i sosai wanda nan take alhaji Kabiru yayi waya akawo masa kaji k'waya d'ari da drinks katam talatin da gorunan ruwa suma katam ashirin sannan suka shiga cikin gida suka sanarwa matansu halin da ake ciki, nan take ake hau shire shire masu murna nayi masu bak'in ciki nayi, dole dai ana kawo kajin duk suka taru aka hau gyarawa sannan aka soye tare da zuzzubasu a inda ya dace aka kai can part d'in dady wanda tuni decoraters sun gama k'ayata wajen had'e da sakin sautin da zai nunawa mutanen anguwa cewa yau ana babbar hidima agidan.

Sai misalin k'arfe biyu dady da yaya Mahmud suka bar anguwar bayan dady ya sake gabatar masu da Mahmud da gaba d'aya sukayi mamakin girmansa da yanda ya canza sannan suka wuce don shiryawa, Yaya Mahmud nakallon dady yanda fuskarsa sai farinciki yakeyi yace

"Dady naga farincikinka ya lunku"

"Ai dole my son, wannan farinciki silar 'YAN UWANA NE da suka karb'eni hannu biyu muka yafi juna" murmushi yayi sannan yace

"Amma dady baba k'arami gaba d'aya ashe dashi d'an uwana da Billy ke kama, kaga idanuwansa kuwa..?" Yak'arasa maganar yana dariya,

Dariyar shima dady yayi sannan yace "kaji dashi idan yajika ai tsohon kane.."



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____80💎


Suna isa gida yaya Mahmud ya wuce part d'insa yana maijinsa cikin wani irin farinciki marar misaltuwa, haka dady shima ayanda yake jinsa yau sai ya kasa banbance shin wane farincikine ya lullub'e masa zuciya, na auren 'ya'yansa kona shirya warsa da 'yan uwansa, wayarsa yaciro yakira Basmah bugu d'aya ta d'auka had'e da cewa

"Dadynmu barka da rana"

"Yawwa Basmah kina lafiya dai ko?"

"Lpy klw dady gamunan muna shire shire, injin dady kasamu ganinsu baba muzammil"


Murmushi dady yayi had'e da cewa "sosai Basmah kuma komai yawuce, yau kuma zaku ganku cikin 'yan uwanku, fatana yanzu shine a kammala taro lpy"

"In sha Allah za'ayi komai yanda yakamata dady kaci gaba da yin addu'a kawai"

"Shikenan, ina k'annen naki sun shirya kuwa don naga saura minti ashirin kuma yanzu nagama waya ga motocin da zasu d'auke kunan akan hanya, so babu buk'atar ajira wani ki tabbatar komai an kimtsa"

Kallon su Batool dake zaune k'wararriyar mai kwalliyar da aka d'auko masu dake _HIM'S TOUCH_ na tsantsar masu make up ita da yaranta tayi tayi murmushi saboda yanda taga cikar kyawon 'yan uwan nata yafito sannan tace

"Eh dady sun shirya, kad'an kawai yarage ak'arasa masu kwalliya"

"To shikenan by 3 kowa yazama cikin shiri za'a fara kwasar mutane akaisu amma keda 'yan uwanki kujira har infito"

Tsayawa fad'ar irin kyawon da amarennan sukayi b'ata lokacine don duk inda kyawonsu ya b'uya yau sai da _Hindu_ ta k'walkwalo masu shi, babu yanda batayi da Basmah akan tazo ayi mata make up d'inba itama amma fir tak'iya tace bataso da k'yar su Billy suka shawo kanta akayi mata light make up aikuwa da yake gwanannar mai kwalliya ce kuma sai tahad'u da kyakkyawar fuska nan take itama Basmah kyawonta yafito idan kaganta zaka d'auka tana cikin amaren. Dogayen rigunane masu d'an karen kyau dark pitch colour suka saka suna ja har k'asa rigunan sunyi kyau har sun sai black net da akayi masu wani nad'in head daya fidda shape d'in flower agefe ya d'an bud'e kad'an yasha stones pitch colour suma sai shining da k'yalkyalin sabun taka sukeyi, black shoes ne half cover masu d'an tsini kad'an a k'afafuwansu sai wata 'yar k'aramar jikka bak'a mai shape d'in heart a hannuwansu itama sai k'yalli takeyi, black chain d'in wuya da hannuwa 'yar sirarai ne ajikinsu sai 'yan kunne sark'ar dake kunnuwansu suma 'yan k'anana, tare da wani dogon k'yalle black shima d'an siriri da aka azo masa daga kan kafad'unsu nadama sunyi round jikinsu zuwa k'ark'ashin hannayensu na hagu an rubuta _BRIDE TO BE_ ajiki rubutun anyisa da pitch colour kai iya kyau sun yishi abun sai wanda ya gani, itama Basmah wani had'ad'd'en black less ne tasa mai kyau fulawowin dake jikinsa kalar baby pink, d'unkin riga da sket da sukabi shape d'in jikinta suka zauna sosai, tayi kyau kamar ba itaba abunka da farar fata sai ya sake haskata, kallo d'aya zaka yimata kasan cewa kyakkyawace tak'in k'ari, donma ciwon da take ciki yasa tad'an k'ara ramewa kad'an.

"Masha Allah" yaya Mahmud ya furta lokacin da suka fito hannuwansu sark'e da najuna fuskarta d'auke da murmushi sukuma su Batool annoce kai k'asa ala tilas su amare, suna kawowa harabar gate d'in cikin gidan inda ake parking motoci sai ga wata had'add'yar mota bak'a k'irar Benz tayi parking agabansu, dr Ahmad ne yafito daga ciki shida yaya Mahmud pilot wanda tuni amaren sun sanyasu zamowa abokai, baki abud'e suke kallonsu had'e da bud'e masu gambun motar na baya, dady dake can cikin mota shima yak'urawa 'ya'yan nasa idanuwa saboda yanda sukayi kyau aransa yanaji inama ace duka su ukunne zasuyi aure, "Alhamdulillah" yafad'a da sauri don kada ya zamo cikin bayi masu butulcewa Allah, yana ganin yanda su dr.Ahmad ke rawar jikin bud'ewa 'ya'yan nasa mota yayi murmushi tare da kauda kansa gefe, matsowa yaya mahmud yayi tare da kallonsu yace

"Am srry gusz ai kuda amarennan naku sai dai kujira ko nan da jibine amma wannan aikin ba naku bane na babban yaya ne ko kunmanta dana fad'a maku dady zai kaisu" cike da jin kunya suka rufe gambunan motar suna dariya tare da nufo wajen kowane yayi gefen tasa yana nema ya rad'a mata irin kyawon da yaga tayi, gyaran murya yaya mahmud yayi suka d'ago kansu atare yace

"Dady na kallonku don yana cikin motar can" ya nuna masu wata sabuwar mota dake can gefe ajiye wacce kana gani kasan sabuwa ce, nan kunya tarufesu tare da k'ok'arin baro wajen yace "no.. kud'an tsaya na d'auke ku hoto don kun maseefar yin kyau" Basmah najin haka tajuya da nufin baro wajen da sauri kowacensu tarik'e hannunta da yake itace a tsakiyarsu,

"Meye haka sister ku cikani bakwa ganin photo za'ayi maku da angwayenku?" Suna wannan rigimarne yaya ya d'aukesu hoto su uku kad'ai, sannan yayi masu wani gaba d'aya su hud'un Basmah na atsakiya, horn d'in da dady yayi masa yasashi cewa "Basmah ku muje ga dady can yana jira" tuntuni anriga da ankai kowa wajen ku kad'ai ake jira,

Ahankali suke takawa har suka isa wajen motar, yaya Mahmud da kansa ya bud'e masu motar suka shiga tare da Basmah sannan ya zagaya gefen driver yashiga tare da tayar da motar yabi bayan motar su dr.Ahmad da suka fice da motarsu yanzu zuwa can family house d'in,

Suna isa suka samu har su Mahmud pilot sun isa gidan suna jingine ajikin motar suna jiran isowarsu. Yanayin parking har dady zai fita yajuyo had'e da cewa kashigo dasu part d'insu yaya bukar acan babban falo kafin ku k'arasa can wajen bukin? Yana fita ya kalli su mahmud pilot yace

"My son kushigo tare dasu kugaisa da yayuna" sannan yawuce cikin farar shaddarsa da har wani mik'o maik'o takeyi d'unkin captani. Yana wucewa suka k'arasa gaban motar tare da bud'e masu gambunan mota suka fito,

Murmushi yaya Mahmud yayi yana girgiza kai had'e da nuna Mahmud pilot da key d'in mota yace

"Kai ko?, wlh kashiga uku, shikenan ka lalata dr. sai faman biye maka yakeyi da wannan rawan kan naka, dubi yanda kasa bawan Allah komawa kamar wani sarkin bud'ar mota wa k'ank'anuwar yarinya, wai anya kaikam baka zauceba"

'Daga kafad'a yayi had'e da cewa "what ever she's our bride to be malan kazo kayi mana kane kane ka hanamu rawar gaban hantsi muda matanmu, kaje mana kaima amaryarka nacan tana jiranka" shidai dr. Ahmad baice komai ba sai faman murmushi yakeyi had'e da kaikaita idanunsu ya rad'awa Batool akunne "My angel kinyi kyau sosai, bana tantama akan cewa ke d'aya daga cikin matana ne na hurul ayn Allah ya sau komun da ita aduniya, Alhamdulillah bukin yau babu maza awajen inba masu kid'annan ba da masu hotuna da vedioting badon haka ba da saceki zanyi dani harke bazamu zaunaba don kada akallemun ke" murmushi Batool tayi batare data tanka masa ba tafara takowa ahankali shi kuma ya take masa baya yayinda Mahmud da Basmah suka shiga gaba sukuma sukabi bayansu kowane tare da matarsa agefe.

Suna shiga palourn gaba d'ayansu suka zube k'asa don mik'a gaisuwarsu ga su baba kabiru da bukar da kuma baba k'arami, bayan sun gaishesu sun amsa dady yanuna Basmah yace

"Yaya wannan itace 'yata ta biyu dake bima Mahmud ita tazab'i tayi karatune kafin aure, wannan kuma itace ke bimata sunanta Batool tare da nunata sannan yaci gaba da cewa ita kuma wannan itace Bilkisu 'yar wajen hajiya Aisha wacce itake biwa Batool kusanma ince tagwayenane don sati uku kacalne a tsakaninsu, nuna Mahmud pilot yayi yace shi wannan kunriga da kunsansa tunda d'ankune d'an wajen hajiya hafsatu tunda yana biyo wajenku inyazo shine mijin Bilkisu in sha Allah sai wannan shima d'ayan surkin kune wato dr. Ahmad Bashar maifulawa mijin Batool, sannan yakallesu had'e da cewa dr. Ahmad

"Nasan kaine zakafi buk'atar sanin wud'annan ko suwaye da matsayinsu agareni, to su 'YAN UWANA NE kuma iyayen matar da zaka aura naduniya da lahira duk abunda zai taso tab'angarenta to kai tsaye kazo wajensu don batada wud'anda sukafisu aduniya kaji ko, wannan shine babban yayana alhaji kabiru, sai wannan dake bimasa alhaji bukar tare da k'aramin k'anenmu baba k'arami wato muzammil" yafad'a tare da jawosa ajikinsa, nan dai su kayita sanya masu albarka tare da tabbatuwar aminci da salama acikin rayuwar aurensu, kallon Basmah yaya bukar yayi had'e da cewa

"Ita wannan kenan babban yaya zata gado da son boko" saboda shikad'ai yayi karatun boko mai zurfi acikinsu don har masters seda yayi, sannan ya dubi Billy had'e da yin dariya yace "wannan kuma gaba d'aya ita da mijin nata tamkar baba k'arami yayi kaki" dariya alhaji Kabir yayi had'e da cewa

"To ai balaifi tunda mahaifin sune, kai bukar kaid'ai alhaji Bashar yayiwa wayo bakada magaji awurin sa" gaba d'aya sukasa dariya sannan baba k'arami ya shiga cikin gida yakira iyalansu maza da mata manya da k'anana tare da iyayensu suka gabatar masu da kawunansu amatsayin 'yan uwan juna, sannan aka sallami su Basmah don dama taron bukin na zallar matane, kai tsaye part d'in da sauti ketashi wata 'yar wajen alhaji bukar mai suna Zainab da bazata wuce sa'an su Billy ba tayi masu iso zuwa compound d'in da aka gyara cikin gidan da Saiti kefaman fitowa daga wajen tana fad'in

"Welcome to the family 'yan uwana" gaba d'ayansu suka amsa da "thank you sis" suna murmushi, suna shiga DJ yasaki sautin wak'ar bukinsu da umar m shareef yayo masu, cikin bin takun sautin kid'an suka isa wajen wanda Batool na juyar da kanta gefe ta hango meamah adaidai k'ofar shiga wajen, cikin jin haushi tab'alla mata harara kamar tana kallonta sannan tajawo Zainab cikin kunne ta r'ada mata

"'Yar uwata don Allah kinga waccan dake jikin k'ofa kije kitsaremun ita kada kibari ko kad'an tafita daga wajennan plsaa kinji?" Tak'arasa maganar daidai lokacin da suka zauna kan kujerun da aka tanadar masu kamar zatayi kuku" murmushi Zainab tayi tare da cewa "kai Batool to wacece ita? Haka baku kuka gayyato taba"

"Pls zee kije don Allah".

Dama tuni DJ isowarau kad'ai yake jira shida mc suka fara gabatar da abubun da yakamata suyi babu k'ak'k'aftawa, tunda nake bantab'a ganin anyi bridal shower irin na wud'annan amaren ba, bukine akayi naji da fad'i cikin natsuwa da kwanciyar hankali daga k'arshe DJ yabuk'aci amaren da sufito su d'an tattaka don nuna murnarsu awannan rana data zamo tafarko a cikin ranakun tarihin da bazasu tab'a mantawa dashi ba, da farko k'in tashi sukayi saida Basmah tarik'o hannuwansu suka shigo filin wajen tare sannan suka yarda, ihu wajen ya d'auka tare da tafi daidai lokacin da yaya mahmud ya shigo waje yana yimasu lik'i da 'yan dubu dubu, haka itama Basmah tadinga mik'a masu 'yan d'ari biyar biyar tana dariyar k'arfin hali don tamanta batasha maganinta narana ba ciwon nayimata barazana, amma sosai ta saki jiki tare da cije yanayin da take jinta ciki akayita gudanar da shagalin cikin farinciki, ganin angwayen na shigowa yasa DJ ya canza sautin wak'arsa wanda nan take suna isowa suma suka b'alle rafar 'yan d'ari biyar biyar suna yimasu kari, idonsa mahmud pilot ne suka sauka akan Basmah daidai lokacin da takoma can gefe had'e da cije baki ta duk'e k'asa wanda hakan yabashi cewa akwai halin da take ciki, wajenta ya nufa ta can gefen da yahango ta shige, yana zuwa yace

"Sister lafiya?" Da k'arfi ta d'ago kanta jin yanda sautin muryarsa yadaki kunnuwanta da zuciyarta, k'arfin hali tayi had'e da cirewa tace

"Bakomai yaya" sannan tarab'a ta gefensa tabar wajen.

Tand'e tand'e aka farayi da lashe lashe wanda acan na hango maku aunty fareeda anci ado tare da make up fuskarta d'auke da glass tawani matsewa tana yatsina fuska saboda itace tajagoranci tafiyar 'yan rano online novels, kasancewarsu manyan mata masuji da kansu kuma clasic yasa hatta abunda aka jere masu suka kasa tab'awa saidai gorar ruwan swan da suka bud'e suna d'an kukkurb'awa cikin yanga, murmushi Hijjah yaks tayi tace bari zakuyi don nikam bazan bar wannan dad'i ya wuceni ba wajen Kurin banza, plate tajawo tadinga cin abinta cikin kwanciyar hankali saida taji tayi nak sannan tacire hannunta tissues paper taga anmik'o mata ashe shama halliruce dake Billy s fari novel itama tajagoranci tafiyar tasu tace k'awa nifa kinburgeni ungo goge hannunki, ke kuwa sai fama nake da 'yan group d'inmu akan suci arzik'i abunsu aubarshi a inda suka iskosa amma sunk'i, waisu bazasu ba aunty Billy kunyaba agansu suna faman kwasar gara tunda kai tsaye ake haska bikin atashoshin yad'a labarai.

Dariya tayi sannan tace "to hango aunty billyn can itama ta ajiye bironta da littafi agefe sai talar naman kaji takeyi dama kinsan 'yar lukutace sai ta ida bud'ewa" ai gaba d'aya naga 'yan rano online da Billy s fari novel sun zubo mani idanuwa kafin kace me sai gashi na hango su sunfara kwasar dad'i abunsu har suna hannu baka hannu akushi, ganin haka yasa itama aunty fareeda ta cire glass d'inta gefe tabaje abunta tana yagar cinyar kaza.

Dariya nayi tare da juyawa ina mamakin yanda gaba d'ayansu suka hallara bukin kawai sai nahango maku Zainab pinki an wani tsuke baki atsakiyar amare ana kashe salfie, itako Ummie rano sai faman kashin wayarta takeyi da hannu ko zata tashi don tad'au salfie itama da amare, murmushi nayi had'e da dafata ina nuna mata gefen da tahango mom hafsat rano zaune irik'e da affan dasu mom zozo, yaya hajja, sainah Ummi minal da fateema tambari, billyn Abdul, aunty YBk, aunty maijidda Musa kai da dai sauran beautiful hajiyoyin dake wajen nace

"Haba Ummie maida wayarki a aljihu kada arenaki kije wajen mom affan ta aro maki iPhone 11d'inta dake hannunta tana latse latse" tsabar takaici batasan lokacin data jefeni da wayar ba nayi saurin kaucewa tare da k'arawa gaba, 'yan taskar littafin Hausa novel nahango oum imaan takarb'o maau sobeniyas suna zancen tafiya suda 'yan musha karatu YBK da sister nassmeenat tajagorance, Mmn sss nahango itama tana mik'a hannu wai abata jikkunan mata rahama suna waje suna jira don zasu wuce tana faman jijjiga babynta dake kuka, kai hatta wud'anda ba'ayi tsammanin gani awajenba sun hallara wannan bridal shower daya koma tamkar wata dinner, don ba'a watse wajen ba sai bayan sallar magrib har ana batun sallar insha'i..



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: 👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____81💎


Kasancewar dady ya dad'e da komawarsa gida shikuma yaya Mahmud yanufi wajen bridal shower d'in amaryarsa wato faraaha tare da rakkiyarsu Mahmud pilot da dr. Ahmad yasa ana kammala taro alhaji bukar ya fiddo motarsa ya d'auki amaren da Basmah ya kaisu har gida da kansa bayan antabbatar da ankwashe duk mutanen da suka samu hallara wajen bukin, su kuma DJ's dama tuni an sallamesu bayan ankashesu da kayan biki da lashe lashe kuma dady yace duka kud'in likin da aka zuba su d'auka duka anbar masu, suna wucewa saiga dady ya dawo tare da masu gyaran gida, abunka da mai arzik'i nan take yace iyalan alhaji bukar dana alhaji kabiru sukuma part d'insa tunda dama d'akunan macce biyune, shi kuma baba k'arami dama matarsa batanan tana garinsu tayi tafiya sai takwana biyu wanda tuni yakirata ya jaddada mata cewa ta tabbata jibi ranar juma'a tadawo saboda bukin 'ya'yan d'an uwansa da akeyi, don haka sai dady yace ita akwashe kayanta a mayar babban falo kafin Angama masu gyaran bisa yardar mijin nata,

Nan take aka b'ab'b'alle silin

Please Login or Register in order to submit comment