Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake sai tunanin maganganun mom wud'anda ya tabbata basuda tushe inba zallar kishin ganinta da Ummi datayi ba.

Ita kuwa faraaha gaba d'aya ta shaga da labrin da ummi ke bata, don ma takasa sakin jiki sosai da ummin saboda atunaninta Umman borno itace mahaifiyarsu yaya Mahmud, ko kad'an batasan da zaman mom ad'akin ba sai lokacin da zata fita, anan ne taga fitarta. Taso ta tambayi ko wacece sai kuma tabari har sai Mahmud d'in da taga yabi bayanta yadawo duk da jikinta yagama bata cewa itace mom d'insa da taji yana fad'a kuma gashi taji Mahmud yakira wacce tayi tsammanin itace da Umma, nan take jikinta yayi sanyi, kallonta ta maido ga Ahmad da shima hakan take awurinsa tace

"Dr. Ni zan wuce, yaya Mahmud Allah ya k'ara sauk'i, ummi sai anjima ina gaida su Bilal"

"Faraaha har zaku wuce? To nagode sosai agaida gida"

"Zasuji in aha Allah" N5000 Ahmad yaciro ya ajiye a gefen pillown da Mahmud pilot ke kwance yayi masa Allah yak'ara sauk'i, duk suka amsa da amin, tare da yimasu godiya suna Allah shiyi masu albarka.

Suna fitowa Dr Ahmad ya kalli faraaha yace

"Sister wai waye wannan mom d'in data fita yanzu itama cikin family naau take" shiru faraaha tayi kafin tace

"Mom sunan da all I have da Batool ke kiran mahaifiyarsu, tunda har kaji all i have yakirata da mom to inada yak'ini akan itace d'ince" shiru shima d'in yayi kafin yace

"Muje inga fatima in wuce don gaba d'aya kaina yad'an kwance" murmushi tayi suka nufi inda suke zaune takirawota acan gefe, tasowa Batool tayi cikin natsuwa ta gaida dr. Ahmad kafin nan faraaha dake kallonsu tana dariya tace "to Batool yau dai gaki ga dr. Ahmad nan agabanki yazo da kansa ba aikeba, ni zan wuce sai anjima, Allah yak'ara sauk'i" batare data d'ago kanta dake duk'e ak'asa ba tace "Amin aunty faraaha Allah ya kiyaye" dr Ahmad kuwa yana jin muryarta ya nemi dukkanin damuwar da ya shiga da fargaba yarasa, murmushi ne kwance fal afuskarsa yanajinsa yau yafi kowane namiji duniya sa'a tunda gashi ga abut k'aunarsa...





*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Hi you guzs, am sorry for hearing me quiet, afuwan afuwan, nakai ziyara to my family and relatives so i was so busy shiyasa bana samun damar yin typing, so kuyi hak'uri zan dinga manage ina yimaku kad'an kad'an before inkoma gida, thanks for those who message and given me a call don suji ko lafiya nake, jaxakumullahu bijannatul Firdausi, wud'an da ma basu samu damar yin haka ba amma ina ransu ngd sosai, luv all am so proud of you_πŸ’‹πŸ˜πŸ’ƒπŸΌ

πŸ’ŽPage_____56πŸ’Ž


Shiru sukayi na kusan mintota kafin ya d'ago kansa yace

"Fatima ykk, ya mai jiki?"

"Alhamdulillah" tafad'a atak'aice, yayi murmushi don ganin yake kamar tafiye yanga da yawa, kuma hakan naburgesa, "ranki shidad'e gani agabanki da k'ok'on barana kitaimaka kijefomun abunda zan dogara dashi wajen ceto rayuwata, gaba d'aya kwanakinnan da kika d'auka wajen yin tunanin amsar da zaki bani a daddafe nayisu cikin shan wahala k'iris ya rage kiganni akan titi ina neman ta inda zanganki, don Allah kifad'amun matsayina domin komawa da kyakkyawan albishir awajen mamynah". Dago kai tayi tana murmushi idanuwansa akanta kafin tace

"idan har dr. zai samu ganin marar lafiyar da yake kula da ita cikin farinciki da walwala had'i da k'oshin lafiya ya kamata yasan cewa tabbas yayi nasara acikin aikinsa kuma yayi achieving goal d'insa, don haka zanyi farinciki idan har kaima kagano amsa da matsayin soyayyar ka agareni da kanka kuma shi zai tabbatarmun da cewa nawan na musamman ne" tana gama fad'ar haka tabar wajen da sauri tana dariya, dunk'ule hannu dr yayi yace "yes alhamdulillah" takowa yayi zuwa inda tadawo wajen 'yan uwansa cikin farinciki yayi nailing down agabanta batare da yaji kunyar Billy da Batool dake gefen saba yace

"Godiya nake fatima bisa karamcinki agareni, tabbas nasamu amsarki tun daga irin tarbar dana samu agareki, ina alfaharin zamowa namijin da yau yafi kowane namiji sa'a acikin wanna safiyar, gani agabanki zuciyata, rouhina da kuma gangar jikina duka nakine na mallaka makisu har iya k'arshen rayuwata amatsayin tukuicin amsar dana samu batare da shan wahala ba." Gefe gefenta ta kalla had'e da turo idanuwa tana ware hannuwanta tace

"Me kakeyi haka dr. U get what u want, so meye nayin wannan abun, baka jin kunyane halan aganeka haka, look at my siblings! they are all watching you, abeg wakeup kaji" tashi yayi yana dariya yana juyi yace

"Thank you fatima, i luv you so much" yafad'i i luv you d'in da k'arfi tayanda wad'an suma dake nesa dasu zasu iya jiyowa, kunya ce tarufeta da sauri ta tashi tanufi wajensa cikin wani shauk'i dake d'ibarta ta tace

"Pls dr..." Katseta yayi ta hanyar matsowa kusa da ita sosai had'e da kallon fuskarta yana fad'in "yes my fatima i do luv you so much, bana shakku ko haufi akan kowa yaji domin ina yimaki soyayyar da zan iya baki rayuwata tunda kema kina sona don haka kibarni inshedawa duniya cewa ni d'in nakine batare da shayi komai ba"

"Ya isa haka dr. Kanasa inajin kunya sosai, nayarda da kai d'ari bisa d'ari kuma nagamsu da soyayyarka nima ina sonka ina k'aunarka!"

"Are you serious?" Yafad'a yanaji tamkar ya rungumeta tsabar farinciki, jinjina masa kai tayi tana tabbatar masa had'e da cewa "kaga bari inje wajen 'yan uwana nabarsu su kad'ai, ina fatar kasamu kyakkyawan albiahir d'in da zakajewa mamynmu dashi kamar yanda kake buk'ata?"

Cike da soyayya yake kallonta yanaji kamar ace yau tagama zama mallakinsa ta har abada kafin yace

"A'a kada kitafi kibarni fatima, bangaji da kallon ki ba, ai nima 'YAN UWANA NE, natabbata zasu yimun uzuri subarni insamu natsuwata tare dake kona minti biyar ne, hak'ik'a kin k'ara samun matsayi azuciyata yanda naji kin ambaci mamynah a matsayin mamynki kema, darajarki da martabarki sunk'ara girma acikin zuciyata, ina sonki fatima ina sonki sosai" ganin yana nema yafara yimata sabbatu yasa tace

"Nima haka dr. Ina sonka, sai anjima ka gaida mamy" tajuya tana dariyar yanda wicked dr d'in da take tunani yakoma tamkar wani susu akan sonta, kafeta da idanuwa yayi har tabar wajen yanajin k'aunarta na ratsa dukkanin sassan jikinta. Juyawa yayi tare da ciro wayarsa yana lalabar lambar Khalid abokinsa ita kuma tanufi wajensu Billy zuciyarta cike da farincikin samun irin wannan soyayya daga wajen dr, wani shu'umin kallo Billy tabita dashi ganin yanda sai faman murmushi takeyi,

"Batool gaskiya ki rik'e gayen nan sosai domin ba k'aramin sonki yake ba, dubi yanda yake yimaki wani irin mahaukacin so, congrat sister kekam kinyi sa'ar soyayya" Basmah tafad'a itama tana kallonta, da sauri Billy tace "fad'amata yayya wlh ni har mamaki yabani, irin wannan so ko a littafin soyayya da finafinai ban tab'a ganiba ballantana a tarihin Wasu tsofaffin masoya" dariya Batool tayi kafin tace " ittaqillaha my twiny ai duk soyayya tabiyo bayan ta yaya Mahmud pilot, dubifa yanda tsabar so yasa yanemi rasa ransa, kawai kice salon sane ya burgeki don bak'arya nima ya burgeni sosai" gaba d'ayansu sukasa dariya tare da mik'ewa suka nufi d'akin da yaya Mahmud pilot yake.

Faraaha nafitowa bakin get sukaci karo da yaya Mahmud yadawo yana k'ok'arin kunno kan motar tasa zuwa cikin asibitin ransa adagule, yana ganinta ya fasa shigowa yayi reverse da motar ya daidaita parking d'insa yafito, wajenta yanufa had'e da karb'ar hand bag d'in hannunta batare da yace mata komai ba yakoma wajen motar, gidan gaba nacan gefen ya bud'e had'e da ajiye jikkar sannan yayi tsaye yana kallonta dafe da marfin gambun motar, ganin yana jiran isowarta yasa taga batada zab'in da yawuce itama tabiyo bayansa tashiga motar, matsawa kad'an yayi yak'ara bud'e mata gambun motar tashiga ta zauna sannan yarufe ya zagaya yashiga cikin motar shima had'e da tadawa sukabar wajen, atsanake yake tuk'in maganganun mom d'insa nadawo masa akai, cikin siririyar muryarta datafi tafiya da zuciyarsa tace

"All I have lafiya kuwa?"

"Lafiya klw my golden heart" yabata amsa had'e da kallon fuskarta yana murmushi, murmushin ta mayar masa itama sannan tace

"Akwai alamun damuwa a fuskarki amma tunda bakaso nasani, ko meye ma Allah ya yaye makashi"

"Amin babynah, ina sonki"

"Nima haka sweetheart" Harararta ya d'anyi "banason wannan sweet d'in abarni a all i have d'ina, yanzu ina muka nufa?"

"Eh to da gidan qawata shamsiya naso inje" b'ata rai yayi had'e da cewa "bazakije ba, nifa banason kina zuwa ko ina inba asibiti ba koshi don yana taimakon alummahne babu yanda zaniyi saboda kada ayimun sakiyar da babu ruwa beside yau so nakeyi nafara zuwa gidanku na gaida jaddi"

"Pls.." Kafin tace wani abu kiran papi yashigo a wayarsa, yana dubawa yaga sunansa gabansa ya fad'i, kallon fuskarta yayi kafin ya d'aga wayar ita kuma tayi kamar batasan da abunda yakeyi ba, cikin girmamawa yace

"Hello papi ina wuni?" Cikin b'acin rai papi yace

"Lpy, wai mahmud yau kwana nawa da maganar mu amma har yanzu najika tsit, idan baka buk'atar zab'ina ai saika fad'amun amma ka barni cikin duhu haka, kodon banine nahaifeka ba?"

"Subhanallahi papi mekake fad'a haka, ko kamanta annabi cewa yayi matsayin kakanni awurin jika shima iyayena? Don Allah kayi hak'uri dama d'an uwanane ba lafiya yanzu haka muna asibiti an basa gado amma insha Allah gobe zanzo sai kabani address inje, shikenan hakan yayi maka" murmushi papi yayi had'e da cewa

"Eh yayi Allah yayi maka albarka, kagaida mana da Mahmud d'in Allah yabashi lafiya, in sha Allah anjima zamuzo nida baby mudubasa" da haka suka katse wayar ita kuma faraaha da tanajin duk maganganun da sukeyi kuma tagama fahimtar akan maganar yarinyar da papi keson had'asa da itane kuma har yace gobe zaije yasa takauda kanta tana kallon gefen titi ta glass had'e da goge wasu zafafan hawaye da suka zubo mata"

"My golden.." Tayi saurin katsesa cikin muryar data tabbatar masa da hawaye kezuba daga cikin idanuwanta tace "Pls kawai kakaini gidansu shamsiya nace, basai kaje gaida jaddi ba idan nakoma zanfad'a masa kana gaishesa" da sauri ya taka burkin motar yana k'ok'arin kallon fuskarta data juyar acan gefe...




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____57πŸ’Ž


Faraaha! Me kikeyi? badai kuka kikeyi ba akan wannan matsalar da tun safe muma riga muka kai k'arshenta, kinsan damuwar da nake ciki kuwa akan wud'annan matsalolin duk don insamu inga cewa kud'in kin zamo tawa?, kinsan irin abunda nakeji idan naga b'acin ranki da har kike k'ok'arin sake jefani cikin damuwa?, don Allah kiyimun afuwa kitanada wud'annan tsadaddin hawayen naki har lokacin da abu mai muhimmanci zai ziyarto rayuwarmu, zuwa gano zab'in da papi yayi mani bashine amincewata ba, wlh duk duniya babu wata mace da nakeso da aure idan ba keba don haka ki kwantar da hankalinki, ina tabbatar maki da cewa ni Mahmud Bashar mai furnitures mallakin faraaha ibrahim ne har abada saboda haka ki kwantar da hankalinki kinji all I have?" Wani irin sanyi taji azuciyarta dayasa nan take taji damuwa da kishin da takeji ya gusar mata, juyowa tayi tana kallonsa hawaye kwance a fuskarta yaciro handcachif fari a aljihunsa ya mik'a mata "Pls my faraah! Kigoge hawayen nan dake da matuk'ar tsada kafin kisa hannayena suyi kuskuren isa ga fuskarki don goge makisu" karb'a tayi tana murmushi had'e da cewa

"Duk tsadarsu, bazai hana kwaranyar suba idan sukaga wata katangar na neman shiga tsakanina dakai, all I have bana tunanin zuciyata zata iya jurewa rashinka domin kai haskene dake jagorantar rayuwata izuwa mafificiyar sabuwar duniyar daban tab'a shiga ba"

"Indai akan wannan ne kid'auka hasken nan yana tare dake har izuwa k'arshen rayuwarki don tare zaku rayu kuma tare zaku mutu" saurin tada motar yayi had'e da cewa "bari na ajiyeki wajen shamsiyar amma idan kika tashi komawa gida ki kirani in saukeki, don yau inaso inga jaddi shima ya ganni kafin yaturo zab'in nasa" yi tayi tamkar batasan meyake fad'a ba don tatsani maganar gaba d'aya. Sai da sukayi nisa sannan tafara kwatanta masa inda anguwarsu shamsiya take, yana ajiyeta ya juya yakoma asibiti,

Misalin karfe biyar da rabi aka sallami Mahmud pilot suka wuce gida, idan kagansa bazaka tab'a cewa shine aka d'auko da safe asheme ba, motsi kad'an idanuwansa na akan Billynsa itakuma da sun had'a ido saita sakar masa murmushi, yanzu kam gaba d'ayansu aahirye suke dasu bayyanar da soyayyarsu wajunansu kuma agaban kowa don zukatansu sun gama amincewa da surayu a inuwa d'aya, haka ta b'angaren Basmah itama yak'i takeyi da zuciyarta sosai don ganin ta manta da Mahmud pilot gaba d'aya arayuwarta kuma amatsayin masoyi tana k'ok'ari matuk'a wajen gusar da tunaninsa da soyayyarsa atare da ita.

Kusan kira uku dr.Ahmad yayiwa Khalid bai d'aga wayar saba hakan yasa ya tari okada ya hau yakaishi gida, Allah Allah yakeyi ya biyasa kud'insa yashiga gidan don yiwa mamynsa albishir, yana shiga yasamu mamy na sallar azahar, safa da marwa yashigayi kafin ta sallame fuskarsa d'auke da farinciki, tana sallamewa bai tsaya yin komai ba ya rungumeta yana fad'in "mamy albishirinki?" Tari tayimasa alamar bata gama abunda takeyi ba don ko azkar d'in da akeyi bayan salloli bai bari tayi ba, hakan yasa yayi zaune agabanta had'e da lank'washe k'afafuwansa ya zuba mata idanuwa, sosai yakusa sata dariya ganin yanda ya zubo mata idanuwa, gajarce addu'o'in da takeyi tayi had'e da tofawa a hannuwa tashafe a fuskarta, kamar yanda tayi shima yayi yana fad'in "amin mamynah Allah ya karb'a" hannuwanta yarik'o tana dariya "mamy addu'ar ki takarb'u fatima ta amsa tana sona"

"Kai masha Allah nayi farinciki, Allah yayi mata albarka kuma yasa ka dace"

"Amin mamynah, kinsan me?..." Nan ya shiga bata labarin yanda takasance tsakaninsa da Batool yana dariya hadda kwatanta mata yanda ta furta cewa tana sonsa cikin kwaikwayon muryarta tare da fad'a mata cewa tace tana gaisheta, dariya mamy tayi sosai kafin tace

"Allah sarki 'yata, ai ni yakamata nagaisheta data iya d'auke rigima irin ta d'ana" tak'arasa maganar had'e da mik'ewa ta nufi kitchen, bayanta yabi yana cigaba da bata labrin Batool da irin tsari da natsuwar da Allah yayi mata, kai tun mamy na dariyarsa har saida tace

"Anya amadidi fatimar nan taka zaku daidaita da ita, irin wannan uban surutu haka daka tsirarwa kanka ai idan kayi matashi sai kasa kanta ciwo kuma kasan bazan lamunci hakan ga 'yata ba" hannunsa tarik'o kafin yace wani abu tadawo falo d'ayan hannun nata narik'e da warmer da plate d'in abinci, zaunar dashi tayi akan kujera tare da ajiye masa kular agabansa.

"Kadaure kaci abinci kada kasa yunwa tabiyo bayan wannan farinciki naka ta tarwatsashi" tafad'a had'e da bud'e kular ta zubo masa jalof d'in shinkafa da waken datayi da tasha bak'in busashshen kifi irin gasasshen nan, dr Ahmad da gaba d'aya yunwa ta b'ace masa yakarb'a tare da k'ok'arin sake yin magana mamy ta dakatar dashi had'e da d'aure fuska,

"Ahmad bana son wasa, maza kaci abinci, inyaso idan ka k'oshi kaci gaba da bani labarin 'yar TWA kaji ko?" Ganin yanda tayiwa fuskarta yasa yaci gaba dacin abincin yana faman murmushi, girgiza kai mamy tayi had'e da mik'ewa don takawo masa ruwa.

A b'an garen Umma da ummi kuwa tuni sunfara d'ago wani sabon al-amari tsakanin 'ya'yan nasu guda biyu wanda anan take Batool tazo tafasa k'wan gaba d'aya tana dariya, murmushi Ummi tayi don har cikin zuciyarta taji dad'in wannan alak'ar sosai haka itama Umma harda gud'a tayi tsabar tafarinciki tana fad'in


"Shikenan tuwona maina, mai abu maganin akwatsesa, Allah yakaimu lokacin buki musha shagali" tsananin kunya tasa Billy mik'ewa tabar wajen tana jifar Batool da harara ita kuma tana dariya,

"Ina zakije 'yatah dawo kizauna abunki, babu wata kunya atsakanina dake, ni mahaifiyar kice kuma gwaggonki kar kisake kid'aukeni amatsayin suruka, don nikam nayi murna Allah yatabbatar mana da alkhairinsa"..




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Uwa ko kuma ince mahaifiya ab'ace mai daraja dake zama ginshik'i ga 'ya'yanta idan tana raye harma da bata raye, kasancewarta itace cikakken jigon rayuwa dake d'auke da mafificiyar soyayyarta acikin zukatan dukkanin mutane aduniya yasa bazan iya wuce wannan shafiba har sai na mik'a gaisuwa ta tamusamman tare da fatan alkhairin Allah ya tabbata agareki mahaifiyata da d'auka cin tak'warorinki dake duniya wud'an da nasani da wud'anda ban saniba, matuk'ar kina d'aya daga cikin wud'anda suka albarkatu da wannan suna mafi daraja agareni wato *HAFSAT* to gaisuwar takice don kun cancanci hakan agareni dukkaninku ina yimaku, fatan Allah ya albarkaci rayuwarku yakareku aduk inda kuke, *UR DOTA LUVS YOU SO MUCH*πŸ’‹β€_

πŸ’ŽPage_____58πŸ’Ž


Bayanta Batool tabi tana dariya had'e da cewa

"Iyyee my twiny kin zama 'yar gata, mijinki yayan ki, surukarki gwaggonki, babanki kawunki, kekam wayafiki sa'ar aure? Gaskiya ba k'aramar sa'a kika taka aduniya ba" tak'arasa fad'ar haka daidai lokacin da suka shigo d'akin Billy, da sauri Billy tajawo hannun ta tamaida gambun k'ofar d'akin tarufe tana harararta had'e da cewa

"Don Allah twiny meyasa kika fad'iwa su Umma wannan maganar, yanzu ya kike so inzauna cikin gidannan dasu? Allah kinb'atamun tsari don bahaka naso ba, naso har Umma sukoma batasan da wannan zancen ba, amma gashi tsabar surutu irin naki kinsa sunsan da komai" zaro idanuwa Batool tayi had'e da rik'e baki cikin mamaki tace

"Saboda me?, to idan har basu sani yanzuba ai ko yaushene sani zasuyi, beside ai wannan abun farincikine da yakamata ace kowa yasan dashi"

"Eh hakane twiny amma ai sai nake gani kamar yayi sauri idan maganar takai kunnensu yanzu, ko yayana babu yanda baiyi dani akan cewa zai sanar da dady nace masa yabari bayanzu ba"

"Lallai to kitsaya kallon ruwa wlh su ciki don ko yaushe dady na iya had'asa da wata, ranar inaji suna firar wai dady ya had'a 'yar gidan amininsa aunty fareeda da yaya mahmud d'inmu kuma kinsan yanda suke son juna shida aunty faraaha sosai, yanzu haka yana nan abun nadamunsa, kinsan meya jamasa? To wlh nauyin bakin da tayine wajen sanar da dady yanada wacce yakeso"

"Allah twiny?"

"Hmmm to kitambayi yaya Mahmud d'in kiji, nidai nafad'a maki gaskiya sauran ya rage naki" tana gama fad'ar haka tafice abunta ita kuma shiru tayi had'e da zaunawa agefen gado tana nazarin kalaman 'yar uwar tata.

Koda faraaha tafito gidansu shamsiya k'in kiran yaya Mahmud tayi gudun karta takurasa, rakota shamsiya tayi har bakin titi ta tarar mata adaidaita sahu tashiga tawuce gida, tana isa ta samu jaddi abakin k'ofar gidana zaune yana tilawar alqur'ani, duk'awa tayi har k'asa tagaishesa ya amsa had'e da cewa

"Malamar asibiti har adawo?"

"Eh jaddi barka da gida"

"Yawwa ya maijikin?" "Da sauk'i jaddi"

"To masha Allah, Allah yak'ara sauk'i"

"Amin" tafad'a had'i da mik'ewa, har tabar wajen tana batun shiga cikin gida jaddi yakirata, dawowa tayi ta zuk'una had'e da cewa "Gani jaddi, Allah sa dai rud'un tsufa bai fara d'ibarmun kai ba" murmushi yayo kafin yace

"Kedai kika sani, dama ina sone infad'a maki cikin satinnan yaronnan zaizo don haka kizama cikin shiri, bayan haka ina so kifad'awa shi saurayin naki da kike so yazo ina nemansa idan har da gaske yakeyi" turo baki tayi cikin jin haushin nacewar da jaddi yayi ta adole saidai zab'in nasa yazo yace

"Wai jaddi har yamzu kana akan bakanka"

"Habawa faraaha karku maidomun da hannun ago baya mana, ina kekikace kin amince yazo ko?"

"Eh jaddi, shine akansa kake cewa wai saurayina yazo inda gaske yakeyi?, yo aima duka laifinane yai babu yanda beyi dani akan yanaso yazo ya gaisheka ba nace a'a" tayi maganar cikin sigar shagwab'a har tana b'ata rai, baki abud'e jaddi ke kallonta kafin yace

"To nikuma meye nawa dakike yimun wannan sangarcin, ai da yaso tuntuni yakamata ace yasan k'ofar gidanku amma dayake da wasa yad'auki abun ai kinga bai zoba, shikenan kuma sai don nafad'i hakan yazama laifi" raurau tafarayi da idanuwa tana son tayi kuka yayi saurin cewa "to sakin rigima shikenan basai munkai ga haka ba, jeki kindaiji menace maki ko?" Mik'ewa tayi tawuce jaddi yabita da kallo zuciyarsa cike da tausayinta tunawa da yayi tataso hannunsa shida matarsa baba wacce yanzu watanta goma kenan da rasuwa cikin maraici na rashin uwa da uba, shiyasa yayi sha'awar had'ata da d'an gidan papi saboda yanda ya yarda da tarbiya da mutuncin gidansa yasan zasu rik'e masa ita amana ko bayan ransa, amma gashi ita gabad'aya takasa samun natsuwa da gamsuwa akan zab'in da yayi mata, girgiza kai yayi had'e da cewa "ya Allah kazamema wannan 'yar marainiyar yarinya gata"

Arayuwa ita zuciya batada k'ashi duk yanda mutum yakai mak'ura wajen tsananta hak'uri da juriya dole wata rana zuciyarsa tagaza takasa shanye masa wata damuwar, to kamar hakane ab'an garen Basmah koda yaushe tana kauda kai tare da b'oye damuwarta akan soyayyar da takeyiwa Mahmud pilot duk da takan fuskanci barazana sosai awajen zuciyarta saboda yanda Mahmud ke gudanar da soyayyarsa shida Billy cikin kwanciyar hankali batare da shayin kowaba don yanzu babu wanda baisan da zancen soyayyarsu ba agidan hatta dady yasan da hakan saboda lokacin daya kirasa don yabincikesa meye silar damuwarsa data sakashi cikin halin daya kaisa ga kwanciya asibiti kai tsaye yafad'a masa cewa akan Bilkisu ne, yana sonta kuma ita yakeson a aura masa, sosai dady yayi masa fad'an jefa kansa cikin damuwa da yayi sannan yayi farinciki sosai tare da tabbatar masa da cewa yabashi Bilkisu don haka yakwantar da hankalinsa, daga k'arshe dady ya had'a meeting gaba d'aya gidan kowa da kowa ya sanar dasu burin Mahmud pilot kuma ya tabbatar masu da cewa ya amince da qudurinsa don k'ara dank'on zumunci duk dako bai tuntub'i ta bakin Billy ba yaji tana sonsa ko bata sonsa nan take ya amince da hakan d'ari bisa d'ari, kowa yayi farinciki da murna da jin wannan labari, baranma masoyan guda biyu dakeji tamkar suzama tsuntsaye sutashi sama tsabar farinciki hatta ita kanta Basmah lokacin tanuna farinciki da jindad'inta har cikin zuciya tare dayi masu fatan d'orewa cikin k'auna da soyayyar junansu har abada, sosai yaya Mahmud da Batool suka tausayawa 'yar uwarsu saboda ganin yanda tatirsasawa zuciyarta hak'ura da abunda takeso aduniya don d'orewar farincikin 'yan uwanta, misalin k'arfe biyu na dare wabi irin matsanancin ciwon zuciya yatada Basmah cikin bacci saboda yanda take matsawa zuciyarta akan saita hak'ura da abunda Allah yariga yad'ora mata sonsa, tun tana hak'uri har kuka yafara cin k'arfinta hakanne yayi sanadiyar farkawar Batool daga nannauyan baccin daya dad'e da d'ibarta a firgice ta tashi jin yanda 'yar uwar tata ke kuka, rungumota tayi cikin tashin hankali tace " yayya Basmah lafiya kuwa?" Saiti zuciyarta tashiga nuna mata cikin kuka tana cewa "zan matu sister, wani irin ciwo nakeji azuciyata" tasake fashewa da kukan,

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiuun yayya Basmah don Allah kidena fad'ar haka, bazan iya jurewa ba yazama dole infad'awa dady matsalarki asan yanda za'a maganceta, nagaji da kallon bak'in k'arfin halin da kikeyi kina cutar da kanki bayan inada masaniyar inda za'a samo maganinta" rumk'e hannunta tayi sosai kafin cikin k'arfin hali yace

"Batool wlh babu abunda kedamuna, ciwone kad'ai Allah yajarabceni dashi kada tunaninki yakaiki ga abunda bashine ba.." Shiru tayi sakamakon tarin daya tirnik'eta tana kuka cikin lokaci guda saboda yanda ciwon zuciyar ya tsanan tarmata, kuka Batool tafashe dashi tare da ficewa tanufi d'akinsu yaya Mahmud saboda mom na part d'in dady. Nocking biyu tayi saiga yaya mahmud yazo yabud'e mata k'ofar bayan yatambayi kowaye tafad'a masa itace,

"Yaya kazo yayya Basmah batada lafiya kuma mom na part d'in dady" bai tsaya wata wataba yafito tare da bin bayanta cikin tashin hankali, suna shiga d'akin suka isko Basmah asheme, jijjigata mahmud ya shigayi amma yaga bata motsa ba da sauri yaje ya d'auko ruwa a fridge ya yayyafa mata afuska, saida yayi hakan kusan sau uku sannan tafarfad'o daga sumar datayi tana ganinsa tarungumesa.

"Yaya zanmutu, kuyafemun duk abunda nayi maku" tanarike da saiti zuciyarta dake yimata wani irin azababben ciwo, agogo yakalla yaga dare yayi

Please Login or Register in order to submit comment