Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

illa antassubhanaka inni kunya minazzalimeyn_ can kuma sai kaji tace wash yaya,

"Kiyi hak'uri in sha Allah ba abunda zai sameki kinji ko?" Yafad'a daidai lokacin daya fita da ita, yana kaiwa bakin mota saiga Umma tashigo hankalinta atashe don dama ba wani nisa tayi ba tana cikin anguwar, kama masa ita tayi suka sata cikin mota, sannan yakoma gaba yashiga, ita kuma Umma ta tsaya baya tana rik'e da ita tana yimata sannu, da gudu alhajinsa yabar gidan har suka iso haifa specialist hospital, ko kad'an Mahmud bai jira nurses suka iso wajen ba yad'auki Basmah ya shiga da ita maternity yna kiran nurses, da sauri suka k'araso wajen tare da rik'ata suka k'arasa ciki da ita, sosai Basmah nada dauriya domin inba addu'a da wash d'in da take fad'a idan yazo babu abunda takeyi, cizon baki daine tayishi yafi ak'irga kuma take kan yinsa,

Wayarsa yaciro ya kira dr dake kula da ita ya sanar dashi suna asibiti Basmah ce zata haihu, nan take likitan yace yajirasa ga yanan zuwa, ba'afi minti uku ba saiga likitan ya iso dama da yake yana kusa da ward d'in, kota kan Mahmud baibi ba yawuce d'akin da yaga ankai Basmah hankalinsa atashe don yasan akwai matsala idan aka bari ta haihu da kanta, yana shiga yafara duddubata yaga haihuwarce gadan fad'an don har takai 3cm, nan take yasa aka cike mata file akan za'a shiga da ita emergency theater yanzu yanzu sannan yafita indasu Mahmud suke tsaye shida alhaji da Umma,

A gurguje yayi masu bayanin cewa due to problem d'in da take dashi na cardiac disorder bazai yuyu abari ta haihu da kanta ba domin zuciyarta batada k'arfin da zata iya k'arfafa mata wajen nak'uda, idan kuma akace abarta tahaihu da kanta tofah komai zai iya faruwa da ita, don haka dole zasu yimata theatre don ceto rayuwarta da kuma abunda ke cikin cikinta, file d'in ya mik'awa yaya Mahmud had'e da cewa

"We need you sign here" ya nuna masa wani d'an layi inda zaisa hannu dake jikin takardar, jikin yaya mahmud narawa yasa hannu sannan likitan yakoma cikin d'akin, gaba d'aya jikin Umma da alhaji sunyi sanyi jin abunda likitan ya fad'a baran Mahmud da sai faman safa da marwa yakeyi yana addu'ar Allah ya sauketa lafiya, likitan ne sukaga yafito da sauri saiga Basmah wasu nurses sun biyo bayansa da ita bisa wani d'an gado da ake turawa, da sauri Mahmud yanufi wajensu tare da rik'o fuskarta yana fad'in

"Ki kwantar da hankalinki Basmah, insha Allah babu abunda zai faru dake" manyan yatsunsa yasa yana goge mata hawayen da suka zubo mata tare da yimata kiss agoshi yace

"Ina sonki Basmah.." Bai rufe baki ba yaji nurses d'in sunja d'an gadon da sauri ganin yana shirin b'ata masu lokaci, ji yayi tarik'o hannunsa cikin juriya tace "nagode yayana" sannan aka wuce da ita yana biye dasu, sai faman fad'a mata takwantar da hankalinta lafiya klw zata haihu in sha Allah yake.

Sosai yaba alhaji tausayi ganin yanda duk yabi yarud'e yaje yarik'o hannunsa had'e da cewa

"Ka kwantar da hankalinka kaima kuma dukanmu muyi mata addu'a tare da fatar Allah ya sauketa lafiya..



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_Awasu lokutan nuna zallar farincikinka ga masoyi bisa kulawa da farantawa da yakeyi maka kad'ai bazai wadatar ba har sai baki da zuciya sunyi gamayya wajen furtawa abayyane, Gaisuwa tare da fatan alkhairin Allah agareku *SHA'AWANATU ABUBAKAR* (MAMAN QUEEN) DA *SHAFIHA M SAMBO* tabbas ku aminaine da keda matuk'ar muhimmanci atare dani domin kun zamemun hannayena na dama da hagu wajen bani kulawa da kariya, nagode sosai da soyayyarku ubangiji Allah yabar qauna atsakaninmu, maman queen Allah ya albarkaci zuria, aunty Shapy ke kuma Allah yakawo miji nagari mai albarka ranar aunty billy ta girgiza kwankwaso_πŸ€­πŸ™ˆπŸ’ƒπŸΌ

πŸ’ŽPage_____98πŸ’Ž


Maganganu masu dad'i iyayen nasa suka shiga bashi ganin yanda hankalinsa yatashi kafin su samu yanatsu, ciro wayarsa yaciro ya Kira lambar yaya Mahmud, bugu d'aya ya d'aga, yanda yaji muryarsa ya tabbatar masa da akwai damuwa hakan yasa nan take shima hankalinsa ya tashi,

"'Dan uwa gamu asibiti Basmah zata haihu amma ance tiyata za'a yimata, pls kuyimata addu'a" duk inda hankalin yaya Mahmud yake saida yatashi, amma saboda kada ya karyar da zuciyar d'an uwansa yasa yace

"Karka damu d'an uwa zamuyi mata addu'a, kaima kayi addu'a sosai don ita tafi buk'ata, wannan ba lokacin damuwa bane kaji" d'aga kansa yayi kamar Yana gabansa kafin ya kashe wayar,

Suna gama waya yaya Mahmud yakira mom ya sanar da ita halin da Basmah keci amma sai yab'oye mata zancin tiyata za'ayi mata don ta tashi hankalinta ko zancen haihuwar yafad'a matane saboda sanin muhimmanci da tasirin addu'ar uwa ga d'anta don tayi mata, badon haka ba da bari zaiyi sai anhaihu sannan suji komai, Allah sarki uwa da d'a mom natsaye ba tasan lokacin data fad'i zaune akan kujera ba, addu'a tadinga jerowa 'yar tata tare da fatar Allah ya sauketa lafiya, sannan ta tashi tafad'a toilet tayo arwala tafara nafilfili tanaci gaba da rok'awa 'yar tata sauk'i wajen Allah, ji take inama zata iya zuwa takarb'ar mata wannan zafin nak'udar da akeji, tabbas ko acikin 'ya'ya Allah yasanya fifikon soyayyar wani d'a akan wani, gaba d'aya cikin yaranta babu wanda tafiso kamar Basmah, kuma hakan yasamo asaline tun tana k'arama saboda tausayinta daya zauna aranta narashin shan isasshen nonon da batayi ba saboda cikin Batool daya haifar dayin rurrutsa atsakaninsu,

Gaba d'aya bakin k'ofar d'akin suka koma shida su umma sun kasa zaune sun kasa tsaye kowane bakinsa d'auke da addu'a tare da fatar Allah ya yassare mata kuma yasa ayi aikin cikin sa'a.

Jin irin nishin da Basmah keyi yasa suka k'arasa shiga da ita d'akin tiyatar aguje, suna shiga nan take aka sauya mata kaya dama tuni angama shire-shiren kayan aikin da za'a yimata tiyata dasu, cikin gaggawa aka d'orata bisa gadon likitocin suka rufa mata, ai kamar jira takeyi ana k'ok'arin yankata sukaji tafara wani irin nishi mai k'arfi dake nuna cewa haihuwa tariga tazo, kafin suk'ara wani yunk'urin ana dubata sai dai sukaga kan jariri yafara b'ullowa, dole yasa gaba d'aya nurses da doctors d'in suka dakata suna kallon sarautar Allah, banda juye juye da cizon baki da addu'a cikin rai ba abunda Basmah keyi, cikin ikon Allah taji wani irin nishi yazo mata da k'arfi da yasa duk juriyarta saida tasaki wata irin k'ara alokaci saiga kan jariri yafito gaba d'aya, da sauri likitan yazo ya ida taimaka mata aka ida ciro jaririn da uwa akaba nurses d'in da zasu gyrashi, kanta likitocin suka koma ganin gaba d'ya bata motsi ga saitin bugun zuciyarta baya tashi, lumfashinta ma yayi k'asa gaba da'ya nan take suka jawo oxygen suna bata taimkon gaggawa, sunfi minti ashirin akanta suna k'ok'arin ceto rayuwarta kafin su samu lumfashinta yafara daidaita da taimakon oxygen, zaune babban likitan yafad'i lokacin data ga lumfashinta ya dawo don gaba d'aya sun gama katsewa akan ba tada rayuwa domin abunda akayi gudu shi yafaru amma cikin ikon Allah saiga lumfashinta yadawo fiyema da yanda suka tsammani, "wannan wani sabon miracle me daga Allah" sukaji wani d'aya daga cikin doctors d'in da kristcher ne yafad'a yana kallon na'urar dake nuna adadin lumfashi da daidai tuwar bugawar zuciyar mutum keye,

Mahmud kuwa da gudu yanufi k'ofar d'akin tiyatar yana jijjigawa lokacin daya jiyo k'arar da Basmah tayi, securities d'in dake tsaye abakin k'ofarne suka rik'esa alhaji yazo ya jayesa yana fad'in "meye haka zakayi Mahmud?"

Nuna k'ofar d'akin yayi tare da cewa

"Alhaji baji sautin k'arar Basmah ba?, don Allah kubarni nashiga naga halin da take ciki, nasani tanada buk'atar kasancewata awajen, natabbata zata samu k'warin guiwa sosai idan taganeni, bana son wani abu yasameta ko kad'an har sai ta tabbatar birinta yacika akaina, alhaji Basmah tamatuk'ar shan wahala akaina bana so kuma ace ta sanadina yanzu zata rasa rayuwarta" yak'arasa fad'a hawaye nazubo masa ga idanuwa, itama kanta Umma kuka takeyi saboda tausayin yarinyar, tabbas duk abunda Mahmud yafad'a gaskiyane, akwai buk'atar Basmah tasamu tabbacin soyayyarta awajensa.

Rungumesa alhaji yayi tare da cigaba da rarrashinsa yana bashi magana,

Saida likitocin suka tabbatar komai ya daidaita angyara baby cikin wasu kaya overall blue colour da asibitin ta tanada ga kowane jariri da aka haifa asibitin a matsayin welcoming don taya murna da farincikinsu na zuwan yaron duniya kuma a hannunsa, sannan suka fito d'aya bayan d'aya jiki a sanyaye, aka baro sauran da zasuci gaba da duba lafiyarta.

Da gudu Mahmud yak'araso wajen babban likitan da dashi zai yimata tiyatar yana tsaye da likitan dake dubata suna tattaunawa akan matsalar da Basmah tasamu na collapse d'in jijiyoyin zuciyarta, wanda basa tunanin k'arfin d'aya rage masu zai iya sa tarayu fiye da kwana goma aduniya, cikin tashin hankali Mahmud yace

"Dr Ina matata?, awane hali take yanzu?" Yana rufe baki yaji wata nurse tafito daga cikin d'akin tana fad'in "Ina mutanen Basmah?" Ai bai jira amsar da doctor zai bashiba yanufi wajen nurse d'in har suna rige rige tsakaninsa dasu Umma wajen fad'in

"Gamu"

"Yawwa ga wannan kuje akawo yanxu yanxu, Ta sauka lafiya, ansamu baby girl" tamik'a masu takardar wasu magunguna da oxygen d'in da zasuje sukawo sannan tajuya zata koma ciki,

"Don Allah nurse ya mahaifiyar take?"

"Alhamdulillah itama tana lafiya, kuje ku kawo abubuwan da ake buk'ata" tafad'a had'e da juyawa tabar wajen,

"Alhamdulillah" duk sukace ammashi jikinsa nabashi kamar akwai matsala, komawa wajen likitan dake kula da ita yayi amma sai ya samu gaba d'aya basa wajen, dole yadawo shida alhaji sukaje sawo kayan da ake buk'ata,

Bayan sun dawone Umma takira dady ta sanar dashi Basmah tahaihu ansamu baby girl, amma har yanzu da ita har Babyn ba'a basu damar ganinsu ba amma antabbatar masu da duk suna cikin k'oshin lafiya,

Sosai dady yayi farin ciki tare da adduar Allah yaraya ita kuma yamayar mata da lafiyarta,

Batool dake zaune palour tarafka uban tagumi saboda safiyar yau gaba d'aya koda ta tashi haka kurum ta tsinci kanta cikin wani yanayi marar dad'i gaba d'aya tarasa meke damunta, tayita Kiran lambar Bilkisu da itama ab'an garen nata batajin dad'i ko lecture bata fitaba shiyasa tasa wayarta silent amma bata d'aga ba, tana zaune saiga mamy tahawo saman rik'e da muhib saboda gaba d'aya yau bata ganeta ba shiyasa tahawo saman don ta dubata tagani ko lafiya, tana ganin mamy ta zame akan kujera had'e da karb'ar muhib tana gaida mamyn, murmushi mamy dake k'ok'arin zama akan kujera tayi tana fad'in

"Fatima lafiya kike?, naga duk yau banganki ba?"

"Lafiya klw mamy yau jikina ne baya yimun dad'i"

"Ayya to ubangiji Allah ya sanya alkhairi kuma ya sauk'ak'a duk abunda ya tsananta, amma ai ba zama zakiyiba kiyi tagumi, idan zaki iya kije kiyo arwala kiyi koda raka'a biyu ne, ko kuma ki karanta alqur'aninki kinji ko? Ina tunanin komeye Allah zai yaye maki, kada kiyarda kiba damuwa muhalli acikin zuciyarki domin zatayi nasarar tarwatsa maki farinciki wanda ni bana fatar haka gareki"

Kanta na ak'asa duk'e tana wasa da hannun muhib tace "insha Allah mamy"

"Yawwa 'yatah ko kefa, Allah yayi maki albarka, kinga kawo wannan yaron, kada ya k'ara maki gajiya"

"Amin mamy nagode" tace sannan mamy takarb'i Muhib d'in da sai faman wangalewa Batool baki yakeyi sabo yasan itace mai yimasa wasa da kuma k'ilbasa, tana fita ta tashi tayi kamar yanda mamy tace mata, tana cikin karatun ne kiran mom ya shigo wayarta, da sauri ta d'aga tare da cewa "hello mom ina wuni"

"Lpy klw Batool, ya kike ya mamyn taku da Muhib"

"Duk lafiya klw mom"

"Masha Allah, to 'yar uwarki ta sauka ansa baby girl, yanzu haka tana asibiti kuyi mata addu'a kinji.."

Ai mom bata k'arasa fad'aba Batool tasauka k'asa tana fad'in "Yeeee mamynah 'yar uwata Basmah tahaihu" da sauri mamy tafito itama cikin farinciki tana fad'in

"Alhamdulillah ya Allah, ubangiji Mungode maka, Allah yaraya mana ita, ashe halin da 'yar uwarki keciki yasa kema kika jiki cikin wannan yanayin, Allah sarki, 'yan uwantaka kenan amusulunci ya kasance duk abunda yasamu d'an uwanka kaima zakaji tamkar yasa meka wannan shine k'auna" manta sukayita murnar haihuwar tata, mamy kuwa na addu'a cikin ranta itama Allah yaba fatima da d'an nata rabi mai albarka kusa kusa, don bata so tayi afili yarinyar taji damuwar haka,

Lambar Billy ta sake gwada kira acikin sa'a tasameta itama lokacin suka gama waya da mom ta sanar mata da zancen yayya Basmah d'insu tahaihu, cike da farinciki suke rige rigen taya junansu murna da fatar Allah ya mayarwa yayyarsu da lafiyarta, nan Billy ke sanar da ita yau da zazzabi itama ta tashi tun safe take ko lecture bata samu ta tafiba, ashe yayya take tamawa nak'uda sunata dariya.

Kafin kace me, tuni labarin haihuwar Basmah ya zagaya ko ina tsakanin 'yan uwa da abokanan arzik'i, Ummi kuwa jitayi inama ace itama ta haihun saboda nauyin da cikinta yayi mata haihuwa ko yau ko gobe.

Murna kuwa awajen yaya Mahmud ba'a magana, nan take yafara shire shiren tafiya don dubo halin da 'yar uwarsa keciki, saboda matsuwa da d'okin ganin ya isa da wuri kai tsaye kud'in jirgi yabiya ya saukesa garin na maiduguri, babu yanda faraaha batayi dashi suje tare ba amma yace a'a tayi hak'uri tunda ko arba'in batayi ba, kuma ai nan za'a dawo da ita ayi suna.

Sai bayan awa 7bakwai da haihuwar Basmah sannan aka basu damar shiga wajenta don ko jari riyar ba'a kawo masu ba sai lokacin da suka shiga suka ganeta, kallo d'aya zaka yiwa Basmah nafahimci irin tsanin ciwon da take ciki ga oxygen ga bakinta da aka samata na biyu don nafarko yak'are tuntuni , gaba d'aya tausayintane yarufe yaya Mahmud da tun d'azu ya iso baisan lokacin da hawaye suka zubo masa a idanuwa ba,

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" yadinga fad'a amma ina kasa tsayawa yayi wajen yabar d'akin yana kuka, shikuwa Mahmoud kota kan babynta bebi ba yarik'e hannunta ahankalin yana kiran sunanta "Basmah, Basmah, don Allah kada kitafi kibar little d'inmu, bud'e idanuwanki kaga kyautar da Allah yayi mana, kitashi kigani Basmah gaba d'aya Allah yacika maki burinki yanda kike son babynmu tazo ahaka tazo don Allah kibud'e idanuwanki kinji Basmaty" ganin ko motsawa batayi ba sai lumfashinta kawai da suke gani yana fita da sauka ahankali yasa Mahmud yafashe da wani irin kuka mai ban tausayi, dafasa alhaji yayi had'e da cewa

"Be strong my son" d'ago kai yayi yana kallon mahaifinsa kafin yace

"It's all my fault, nine silar shigarta cikin wannan halin Abba taya za'ayi bazanyi kuka ba"

"What ever dai, hak'uri zakayi, muci gaba da yimata addu'a Allah yatashi kafad'unta, k'ananun kukan da jari riyar dake hannun Umma tafarayine ya maido hankalin Mahmud gareta, hannu ya mik'awa Umma ta azomashi ita yana binta da kallo, gaba d'aya yarinyar dashi take kama, babu ta inda tabarosa, gata babba tubar kallah kamar ba yau aka haifeta ba, cike da soyayya yabita da kallo ya karata daidai saiti fuskar Basmah had'e da cewa

"kitashi Basmah ga little d'inmu, ki samata duk sunan da kike buqata, wannan alk'awarina ne"

"My son yakamata kayi hakuri hakanan, katashi kaje kunemowa yarinyar nan abunda zataci kafin mahaifiyarta ta farfad'o don da alama tafara jin yunwa" Umma tafad'a had'e da karb'ar yarinyar a hannusa.

Dai dai lokacin yaya Mahmud yadawo cikin d'akin idanuwansa jawur saboda kukan da yayi, nan Umma tahad'asu tayita basu hak'uri kafin tace

"Kubiya gida akwai kaya na nan acikin wani pink trolley bag cikin wardrobe a d'akina ku d'auko sannan kabud'e loka d'in mirror akwai dabino da ruwan zam zam kahad'o dasu inyaso idan zaku dawo saiku biyo da fida da kuma zuma sai afara bata mugani"

Tare suka fita kowa ransa babu dad'i, shima alhajin suna fita ya fita don ankira sallar isha'i, saida yayi sallah sannan ya wuce siyo masu abunda zasuci dama tun k'arfe d'aya da suka kawota babu wanda ya koma cin abinci, yarage Umma kad'aice zaune awajen tana kallon yanda jaririyar gaba d'aya ta kwashikke d'anta da d'an uwanta baba k'arami, lallai Allah da iko yake, duk wanda yaga babyn aka tambayesa waye mahaifiyarta zai iya rantsewa yace Bilkisu saboda yanda kamarta tafi fitowa dasu akan mahaifiyarta,

Ana haka suka dawo tare da kayan da suka d'auko, yaya Mahmud ya karb'i baby ita kuma Umma ta anshi fida da ruwan zam zam d'in da sukazo dasu, Mahmud tabawa dabinon tace ya tattauna har sai yayi laushi sai yaba yarinyar abaki, ita kuma ta had'a ruwan da zuma acikin fida,

Bayan ya tattauna dabinon kamar yanda Umma tace yayi yaya Mahmud ya mik'a masa ita,

Ahankali ya aza harshensa dake lak'e da dabinon abakin jaririyar idanuwansa na akan Basmah yana kallon fuskarta, aikuwa da sauri babynta tafara tsutsar dabinon da harshensa tamkar tasamu nono, rufe idanuwansa yayi cike da tausayin yarinyar yanajin soyayyarta na ratsa kowane lungu da sak'o dake cikin zuciyarsa. Saida ta tsotse dabinon tas sannan ya zare harshensa, aikuwa tanajin haka tsanyara ihu,

Gaba d'aya murmushin k'arfin hali sukayi kafin Umma ta karb'eta da sauri tasa mata fidar abaki, sosai tayi tashan had'in ruwan zamzam d'in da zuma har saida takusan shanye rabin fidar sannan Umma ta jaye mata, ba'afi minti biyar ba bacci ya d'auketa Umma ta maisheta cikin d'an gadon jarirran dake gefen gadon mahaifiyarta sannan tafita taje tayi sallah tadawo cikin d'akin taci abincin da alhaji yakawo masu sannan yayi masu seda safe yawuce gida, tafi minti biyar tana amsa wayoyin da aketa faman kiranta ana tambayar yaya jikin Basmah kafin tagama, gaba tasa mahmud shida yaya Mahmud saida sukaci abinci sannan tace suje gida su kwana ita zata kwana anan"

Gaba d'ayansu k'in yarda sukayi sukoma gidan sai dai sukace nan suma zasu kwana tare da ita koda za'a buk'aci wani abun, haka kuwa akayi daren ranar babu wanda yayi bacci acikinsu har safiya tawaye,

Misalin k'arfe tara na safe likitoci sukazo duba Basmah, dubata sukayi sukaga komai ya daida ita yanda ake buk'ata, waccan matsalar d'ai ce da basusan taya zasu iya fuskantarsu da itaba, tsakanin jiya da yau saida aka saka mata oxygen har sau biyar yana k'warewa amma har yanzu bata farkaba,

Suna cikin tattauna matsalarta tsakaninsu Basmah tafarko amma maganganun da taji sunayi su sukasa takasa bud'e idanuwanta, sosai taji fargaba da tsoron abunda taji suna fad'a amma sai taji cewa babu wanda ke mutuwa sai lokacinsa da Allah yad'ebo masa yayi don haka duk tsarin da Allah yayi mata alhamdulillah.

Suna fita tabud'e idanuwanta ahankali sannan tajuyar da kanta gefe tana kallon jaririyarta da Allah ya bata, wacce takasa banbance tsakanin 'yar uwarta da kuma mijinta dawa babyn tayi kama, murmushi tayi hawaye nazirarowa ta gefen idanuwanta cike da tausayin yarinyarta da take tunanin bazasu rayu tare da itaba kafin tace

"Alhamdulillah, Allah nagode maka daka cika mani burina, kabani farinciki da soyayya awajen mijina kuma kahad'a mani da kyautar 'ya wacce nake burin faranta zuciyar 'yar uwata da ita bisa sadaukarwa da soyayyar data nuna mani, ya Allah karaya mana Bilkisu bisa turba ta islama kuma kasa tayo gadon takwararta, tabbas zatayi rashin mahaifiya idan ta Allah tazo gareni amma inada tabbaci akan bazata tab'a kukan rashin uwa aduniyaba matuk'ar tana a hannunki 'yar uwata"..


*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*

πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

*_Akwai kuskure da kuma raunin imani ga duk bawan da baya tunanin mutuwa arayuwarsa, laifine bawa yadinga tunanin cewa bai dace wata rayuwa ta mutuba saboda rayuwar ba'a hannunsa take ba, Allah yana karb'ar rayuwar bawa aduk lokacin da yaso kuma alokacin da yaga dacewar haka agaresa, yarda tare da yak'ini akan zuwan mutuwa akowane lokaci shikesa bawa barranta daga sab'on Allah, tunani da kuma sakankancewa akan cewa ai bai kamata wane ya mutuba saboda wani dalili shine shiga hurumin Allah, muyarda da ikon Allah da kuma tsarinsa akoda yaushe saimu samu barranta daga garesa, Allah baya barin wani don wani domin da kansa yacewa jabrilu ya fad'awa annabinmu cewa " INNAKA MAYYITUN WA ANTUM MAYYITUUN"_*😭


πŸ’ŽPage_____99πŸ’Ž


Kwanan Basmah uku asibiti ta samu sauk'i sosai tunda dama ba yankata akayiba aka sallamesu, bayan doctor yayiwa Mahmud bayanin halin da take ciki amma bai fad'a masa cewa ga kwanakin da zata iyayi aduniya ba, ya dai fad'a masa cewa due to cardiac disorder da take fama dashi kuma anyi k'ok'arin ganin anyi mata operation kafin faruwar wani abun amma da yake haka Allah ya tsaro kafin sukai ga fasata tahaihu da kanta, sanadiyar haka veins d'in jijiyoyinta sunyi damaged da bazasu iya aikinsu yanda yakamata ba, saboda haka aci gaba da bata kulawa yanda yakamata kuma ta tsare shan magungunanta, inyaso sauran abarwa Allah don shi yake da rayuwa kuma shi yakeda mutuwa.

Iya tsorata Mahmud yayi don ga yanda yaga likitan nayi masa bayani yasan akwai matsala, amma abu guda yasa aransa shine, mutuwa wajibi ce ga kowace rayuwa sannan duk mumuni yasan akoda yaushe tana tare dashi ko yanada lafiya ko bayada lafiya kuma babu wanda ke mutuwa har sai lokacinsa yayi, Allah yaga damar ya d'auki ransa ahida yake da lafiya yabar Basmah da akw tunin mutuwarta akoda yaushe kuma akowane lokaci, wannnan ikon sane don haka yabarwa Allah daya wanzar da duk tsarin da yayo akansa.

Bayan kwana biyu da sallamoau asibiti alhaji da kansa shida Umma da yaya Mahmud suka hau shire-shiren maido Basmah gida, dama ana sallamota asibiti yaya Mahmud yakoma, dady kuwa duk da yana son ganin 'yar tasa hakan bai hanasa yima 'yar uwarsa kawaicin cewa abarta acan har sai bayan suna sannan adawo da ita amma Umma tace tunda dai tasamu sauk'i sosai kuma ba tiyata akayi mata ba yabari amaidota cikin 'yan uwanta kamar yanda akeyi a al'adance, hakan yasa dady ya tura mata kud'i masu yawa yace subiyo jirgi zaifi sauk'i akan tafiyar mota.

Zaune take gefen gado bayan tagama shiryawa cikin wani had'ad'd'en less pink da touch na white tanaba baby nono kafin sutashi tafiya shi kuma yafito wanka d'aure da k'ugu a kunkurunsa, kallo d'aya tayi masa ta d'auke kai tana gyarawa baby nonon abakinta, murmushi yayi had'e da zaunawa gefenta Yana kallon fuskar jaririyar tace

"Yaya ba kunya!" Zaro idanuwa yayi awaje tare da cewa

"Ikon Allah, danayi me oum little?"

"Agabana kake k'urawa yarinyar nan idanuwa haka kaman zaka cinyeta" rik'e hab'ar bakinsa yayi da hannunsa yana kallonta idonuwansa cikin nata kafin yace

"Tab..yanzu Basmaty ni da ke wayafi zama marar kunya keda kika kware nono agabana kina bata"

"To ai wannan dolene yaya so kake nabarta da yunwa?"

"A'a ranki ya dad'e ni kuma so kike incuci kaina tunda yau guduwa zakuyi kubarni, ai dole nakalli 'yata son raina, wai bama wannan ba, wane suna kika zab'a mata?" Yafad'a tare da mik'ewa yana k'ok'arin gyara kanshi don shi kad'aine ake jira duk su umma sun gama shiryawa, a hankali ta zarewa nonon abakinta saboda tasmu yin bacci sannan ta ajiyeta akan gadon tare da gyara rigarta tanufi inda yake,

Karb'ar d'an k'aramin towel d'in dake hannunsa yana tsane jiki tayi taci gaba da goggoge masa ruwan ajikinsa, sannan tajawo mai tana shafa masa, idanuwa ya bita dasu ganin yanda ta sauya masa gaba d'aya, ga wani kyau da 'yar k'iba da tayi kamar ba Basmatyn daya sani ba, d'ago kai tayi tana kallon idanuwansa tare da d'aga masa gira tana dariya tace

"Abban little wannan kallon haka fa?"

"Kinyi kyau oum little"

"Nifa kadena kirawa yarinyata little ba hakane sunanta ba" hannunsa yasa ya d'agota da duk'en da take tana shafa masa mai ak'afafuwansa shi kuma yana zaune abakin gado ya zaunar da ita akan cinyarsa sannn yace

"Ranki ya dad'e fad'amun sunan mana tun muna asibiti nake tambaya aketa faman jamun rai, ataimaka afad'a mani koma bar 'yatah a little d'inta"

"Afuwan yaya, sunanne na musamman kuma da tsada sai anbiya, idan kana so kaji to kabiyani nikuma yanzun nan zan fad'a maka.." kafin ta ida rufe baki kawai taji bakinsa cikin nata yana yimata wani irin passionate kiss da yasa jikinta mutuwa nan take, saida ya shanye gaba d'aya

Please Login or Register in order to submit comment