Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yimaza kaje kajiko?" juyowar da Bilal yayi yaga yanda mom ke dariya saboda farincikin ganin 'ya'yanta datayi yasa shima sai ya samu courage d'in rugawa ya rungumeta kamar yanda Mahmud ya umurcesa da yayi, yana kaiwa mom tasa hannuwa biyu biyu zata ingijesa cikin tsorata yayi saurin rintse idanuwansa zuciyarsa nabugawa, sai ga papi nafitowa daga bedroom d'insa, mom na ganinsa saita waskewa ta d'aga Bilal sama tana fad'in

"Oyoyo autan dady kana lpy?" zuciyarta na rad'ad'i don bahaka tasoba gudun cin mutuncin da papi zai yimata idan yaga abunda tayi niyar aikatawa yasa tayi hakan, wata irin muguwar harara ta watsawa Mahmud dake dariya har kyawawan hak'oransa na bayyana da sauri ya juyar da kansa gefe had'e da shafa k'eyar kansa yana mai gintse dariyar dake neman sake fito masa da gudu su Batool suka nupi inda papi ya zauna akan kujera suna gaishesa shi kuma Mahmud ya k'araso inda mom yana Sosa k'eyar kansa

"Mom ina wuni" batare data amsa gaisuwar tasa ba tace "ina 'yatah Basmah?" Cikin rashin damuwa akan amsar da zai bata yace "tana kan hanya nan da minti ashirin nasan zata k'araso" zaro idanuwa wajenta awaje tayi sannan tace "kamar ya? Halama ita wa zai kawota ne?"

"Haba mom kowa kinyi masa tarba mai kyau hatta d'an autanmu Bilal yasamu kyakkyawar tarba daga wajenki saini ne zaki tarbeni ta hanyar wud'annan da tambayoyi"

"Ka amsamun abunda natambayeka yanzun nan koka fuskanci fushina"

"Ehh to ita dai zata kawo kanta da k'afafunta don nasan girman kanta bazai barta tahau napep ba" ya k'arasa maganar yana d'an sosa bayan kunnensa, suna had'a idanuwa da mom baisan lokacin da yafara yimata bayanin abunda yafaru ba shine shikuma da ransa ya b'aci yace tafitar masa a mota,

"What? Kana nufin atiti kabaromun yarinya? Wlh minti biyar nabaka ka koma ka d'aukota" hak'uri yabata sannan ya nufi wajen papi dake rungume da Bilal agefensa na dama yayinda ya tokare sandarsa da hannunsa na hagu, cikin girmamawa tare da tsokana Mahmud ya karb'i sandar tare da ajiyeta gefe yana fad'in

"Yallab'ai yo ai sai ka ajiye wannan sandar tunda kazauna, irin wannan abu haka sai kace tsohon daya fara rud'ewa " saida papi yayi dariya sannan yace

"Uwarka gatacan ita tafara rud'ewar da takasa banbance gaskiya da kuma rud'in zuciya"

Ya k'arasa maganar had'e da nuna mom dake can gefe zaune, don tun ranar da tazo yakira dady yaji abunda yafaru tsakaninsu yake fushi da ita kuma baya shiga alamurranta dashi har hajiya kaka wato mahai fiyarta,

"Allah yabaka hak'uri papi abun baikai haka ba" gaishesa Mahmud yayi tare da tambayar ina hajiya kaka, ai kuwa da sauri papi ya d'ora yatsansa akan baki yana kallonsu Bassam dake wasa suna d'aga murya

"Shiiiiii.....kuyi shiru karku tadamun da masoyiya bacci" kafin yarufe baki Batool da Bilal da suka fahimci tana bedroom d'insa suka rugo aguje shima Bilal yabi bayansu suka shige d'akin suna fad'in

"Hajiya kakaaaa.."

Sandar papi dake gefe ya d'auko yana kwalar Mahmud da ita wai duk shi yaja zasuje sutayar da ita, dariya Mahmud ya kwashe da ita had'e da tashi zaibar wajen papi ya rik'e masa riga

"Ba inda zakaje sai kafito mani da ja'iran k'annen can naka masu zubi da aku" ba Mahmud kad'ai ba hatta mom dake cika tana batsewa saboda abunda Mahmud yayi saida tayi dariya, aranta tanaji inama ace itama ita kad'ai take ga dadynsu Bassam yayi mata irin son da papi keyiwa hajia kaka ya bata kula kamar yanda papinta ke bawa hajia kaka. Muryar Basmah ce tafito da ita duniyar tunanin data lula da sauri ta iso inda take tana dudubata.

"Sannu Basmah ashe haka yaron nan yayi maki? Kibarni dashi sai yagane kurensa, injin k'afafunki basa yimaki ciwo"

Batare da Basmah ta lura da papi dake falon ba tace

"Wallahi Allah mom Yaya mugune, badon Allah yasa inada wani guy dake da motaba nakirasa yazo ya d'aukeni da saidai ink'araso gidannan ak'afa, kinga ma ice cream yabiya dani ta ten 'o seven ya siyamun" ta d'ago ledar tana nunawa mom

"Allah sarki yaron kirki, dubi yanda yayi maki abunda yayanki ya kasa yimaki, Allah dai yayi masa albarka"

Mom narufe baki taji saukar sandar papi ajikin Basmah jikinsa har cira yakeyi yanata doka mata ita a duk inda yasamu, duk da yake bawani k'arfine da papi ba sosai take jin zafin dukan da yake yimata hakan yasata b'uya a bayan mom da yake idanunsa sunrufe ya had'a harda mom d'in yana dukansu, hakan yasa mom taja Basmah suka bar falon shikuma papi Mahmud yarik'asa ya zaunar dashi akan kujera yana faman nishi d'aya bayan d'aya kamar wanda yayi wani ja aiki, tafa hannuwa Mahmud yashigayi yana fad'in

"Sannu papi, gud job" da sauri papi ya d'aga sandarsa shima ya doka masa a k'afa har saida yayi d'an tsalle "washh papi ni kuma meye laifina"

"Tirr...... ai wannan duka laifin kane da baka tsawatar mata tunda kaine babba agidan, nasan shi dadyn naka yafiye sanyin hali da yawa ba lallaine taji tsoron saba ita kuma mahaifiyar taku shashashace ko kanta batayiwa fad'aba balle tayiwa 'yarta, kai yakamata ace kasa ido akan k'annenka amma dubi yanda tsabar rashin kunya yanda take fad'ar wani namiji ya d'aukota hadda biyawa wani wajen da ita, ita kuma sakaryar harda wani samasa albarka allah ya tsare bata damu da sanin koshi ya dad'e da samun albarka 'yar tataba"

"A'a papi kadena fad'an haka wlh muna iya k'ok'arin mu Basmah ce tacika rawar...." Sandar papi yasake d'agawa kafin ya iyar da maganar sa da nufin sake doka masa yana fad'in

"Maza fice kabani wuri kafin kalma na nuna maka naka kuskuren"

Aguje Mahmud yanufi wajen hajiya kaka yana dariyar yanda papi baya shakkar dokawa kowa sandarsa, yana shiga ya tarar dasu Batool gaba d'aya akan gadon sun tada ita suna faman yimata surutu amma dayake baccin bai ishetaba sai faman gyan gyad'i takeyi sukuma suna yimata dariya...


*_A BIG HAPPY JUMA'AT TO ALL MY FANS😘😘 LUV U SO MUCH❤_*















Mr's huss@in✍

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____18💎


Dariya shima yayi sannan ya tako gaban kantareren gadon

"Batool kutashi kufita yanzun nan zakuga papi yashigo kuma kar kunsan halinsa inya iskoku, ku kyale hajiya kaka kutafiyarku wajen mom, indai itace nasan bazata tashi baccin nan yanzu ba" yana rufe baki sai ga papi yashigo yana takawa ahankali, rufe k'ofar da zaiyi ya juyo ya hango masoyiyarsa a tsakiyar gado zaune tana faman gyan gyad'i sukuma sun sata agaba suna faman dariya, murmushi yayi had'e da tak'ara sandarsa yana takowa a inda suke kamar irin shima abun yabashi dariya, ganin haka yasa gaba d'ayansu suma suka sake kece da wata dariyar, yana isowa bakin gadon Mahmud yaja baya yayinda papi ya d'a sandarsa ya dokawa Batool a gefen kafad'a yana fad'in

"Malfar iyayenku, kunjimun shashashun yara, babyn ku keyiwa haka, yau duk sai kunci k'wakwarku agidan nan" zagayen d'akin suka farayi da gudu suna dariya shikuma yana binsu don yabugesu, ya matuk'ar shan wahala bai kama ko d'ayan suba saida Mahmud ya rik'e masa Batool a bayanta ya doka mata sandar tayi tsalle tabar d'akin aguje dama tuni su Bassam suka samu damar bud'esa suka fece Mahmud nata yimasu dariya


"Kun ganemun ja'iran yara daga zuwa suna neman tayar mani da hankalina dana baby"

"Yihak'uri papi kaga harma babyn taka tariga da tashi" Mahmud ne yafad'i haka had'e dayi masa nuni da gefen da hajia kaka ke neman saukowa daga kan gado, juyowa papi yayi yana murmushi tare da takowa har inda take

"Baby kikoma kikwanta, nizan tsareki babu wanda zai dawowa anan har sai kingama baccinki" cikin muryar da zata tabbatar maka da cewa tabbas hajia kaka bata yau bace tace

"Inaaa, ai wannan bacci bazai yuyu yanzuba tunda suka iso, kuka tafashe dashi tana fad'in ina baccina mai dad'i suka tadani" wurinta Mahmud ya k'araso cike da ladabi yana gaisheta, saida ta amsa sannan tak'olomasa idanuwa had'e da rik'e masa kwalar riga,

"Kagansu nan haddashi aka tadani bacci da kuma ja'irar amaryar nan taka"

"A'a baby wannan fa mommodi d'inkine , Sam shibaya cikinsu Batulu dai ce da k'annenta su Bassam da Bilal"

"Haba kakaa! To kicikamun riga tunda kinji bana daga cikin su, irin wannan cacuma haka sai kace kura tasamu nama adawa" gaba d'aya suka kwashe da dariya tana mai shafa gefen fuskarsa had'e da sanya masa albarka, saida suka sake gaisawa sosai cikin kamala tare da ajiye wasar jika da kakanni a gefe suka fara zayyano masa matsalolin mahaifiyarsa da dady ya fad'amasu, ko kad'an baiyi musun abu d'aya daga cikiba kuma ya tabbatar masu da faruwar hakan saidai shi baisan ya zaiyi da mom tafahimcesa ba shiyasa yakasa kawo k'arshen matsalolin, shiru hajia kaka tayi kafin tajuyo ta rik'e hannun papi tana kallonsa,

"Wlh ni har tsoro yarinyar nan take bani, bansan a ina takoyo wannan zazzafan kishi haka ba, ta isko matar nan agidanta tabi tahanata sakewa ita da yaranta don tsabar mugun hali, kadubi yanda yaronta yafita hankali.."

Cikin kuka tak'arasa maganar had'e da fad'awa ajikin papi, bubbuga bayanta ya dingayi yana bata hak'uri tare da nemawa 'yar tasu shiriyar Allah, Mahmud dake gefen su zaune yashiga tunani tare da lalubo kota ina mom d'insa tasamo halinta amma ya gagara samu, muryar hajia kaka yaji tana fad'in,

"Kahutar da kanka maigidana ni kaina nayita wannan tunanin amma bansamo amsar tambayar ba, haline kawai Allah ya halicceta dashi, saboda haka sai kuyita hak'uri kuna lurar da ita har Allah yasa tagane"

A b'angaren mom kuwa Basmah tasa agaba tana tambayarta abunda ke faruwa acikin gidan hadda tambayoyin da basu kamata ba tayi mata ba, ita kuma ta daddage tanata bata labarin k'arya da gaskiya, hadda cewa ai agabansu idan dady yadawo Ummi ke rungumesa ko kunyarsu bataji, shikuma yata biye mata ko damuwa dasu dake yimasa sannu da zuwa bayayi, gaba d'ai yanzu babu ruwansa dasu saidai Ummi da yaranta, wani zubinma fita yawo sukeyi a mota sukuma abarsu agida bazasu dawo ba sai kusan sha biyun dare" muryar Batool suka jiyo abakin k'ofa tana fad'in,

"Laa ilaha illallahu, kai yayya Basmah kiji tsoron Allah, kefa ba agidan kike kwana ba balle wuni taya akayi kikasan haka, wlh Allah mom kada kiyarda da zancenta k'arya takeyi" yatsine fuska mom tayi had'e da d'agawa Batool hannu alamun tazo, tana zuwa takama kunnenta ta murd'e sosai cikin fad'a tace

"Kina nufin Auntyn takice ke k'arya? Wannan abun data fad'a tabbas yafaru da basuyi ba taya zata gani harta fad'a inbanda rashin sanin ciwon kai irin na dadynku da rashin kunya agaban 'ya'yansa zai zauna yana wud'annan abubuwa ko kunyar Allah basaji" cikin dask'ararriyar muryar dake neman saka Batool kuka saboda rad'ad'i da zafi da kunnenta da mom ta rik'e keyi tace

"Kada kiyarda da kalaman yayya Basmah, wallahi mom ba gaskiya tafad'a makiba, kuma idanma hakanne meye laifi aciki Ummi fa matar sace duk abunda suka aikata a tsakaninsu ko agaban waye har ga Allah basada laifi, meye wani abun aciki da za'ace ko kunyar Allah bayaji, bakiga yanda indiyawa, turawa harma da larabawa keyin abunda yafi runguma agaban 'ya'yansu ba, yin hakan samfa ba laifi bane soyayyace.." Buge bakinta mom tayi cikin zafin rai tana cewa

"Rufemun baki samnar yarinya, kice kema Aisha ta b'ata mani rayuwarki ta asirce manike kamar yanda tayiwa yayanki, asheko tajawowa kanta dala ba ganwo" mere baki Basmah tayi tana kallon Batool

"Kinji ko mom, ai dama nafad'a maki Ummi gaba d'aya gidan yanzu juyashi takeyi babu mai girgiza mata ko ganin laifinta, tazubawa kowa a abinci ya cinye sai yanda tayi dashi" fitina mom tafarayi da maseefar don mema dady ya d'aukar mata 'ya'ya yabawa Ummi gashinan yaja mata suna neman lalace mata to wlh ita bazata yaddaba dole yamaido mata yaranta ahannunta sannan tafice tabar d'akin har lokacin tanaci gaba da banbami, kallon Basmah Batool tayi cike da jin haushinta tace

"Yayya Basmah shikenan kinyi farinciki ganin yanayin da mom tashiga?, shin meye ribarki acikin wannan k'aryar da kika shimfid'a?, meye Ummi takeyi maki datayi deserving all dis from you? Saida ta tashi daga inda take zaune sannan tace

"Banida lokacin amsa wud'annan tambayoyinki domin inada abinyi"

"A'a yayya kidawoma hanyar gaskiya domin ad'an zaman da nayi da Ummi na fahimci cewa tanada kyakkyawar manufa akanmu"

"And so what? Wannan fa duka munafuccine, taya zata nufi alkhairi damu bacin bata k'aunar mahaifiyarmu tana nema tarabata da dady"

"Baki fahimta bane yayya kyawawan halayentane ke neman fifita akan na mom awurinsa amma ba rabasu take son yiba, duk da mom mahaifiyar muce kidubi gaba d'aya yanda tafiye son kanta da yawa, wlh da Ummi fitinanniyace mai biyewa kausasan kalaman da mom keyi mata da tuni gidammu ya watse gaba d'aya, kuma bazata tab'a yadda tazauna damu ba har tabamu kulawar da itakanta mom saida taga canji ajikin mu, don Allah yayya Basmah kifito gurb'atacciyar duniyar da muke ciki kifahimci gaskiya"

"Mtssssss...am tired of ur noise, kirik'e gaskiyarki" Basmah tafad'a tare da ficewarta, wani irin dogon iska Batool tafitar had'e da cewa

"Allah kaganar da mom d'inmu da kuma yayya Basmah, nikam nagane sharrin da zuciya keyi mani domin itama Ummi uwace agareni, su Billy kuwa tabbas 'YAN UWANA NE na jini kuma makusanta, tun ranar da Yaya yaganni zaune ina kuka akan Ummi tayi mani fad'an yin sallah akan lokaci ina ganin kamar tana takura mani ne yalurar dani cewa don tana sona yasa tayimun fad'a bawai takuranine take yiba yayita yimun nasiha nafahimci cewa Ummi alkhairi ce arayuwarmu amma kash duk da haka har yanzu yayya Basmah takasa gano hakan,


A asibiti kuwa Ummi ce zaune bakin gadon da Bilkisu ke kwance tana faman bacci hankali akwance bayan sun dawo daga wajen scanning ta rabka tagumi hawaye na zubar mata a idanuwa akan halin da take ciki na matsalar abokiyar zamanta gashi har yakai ga 'yarta nason itama tadinga yimata rashin mutunci, izuwa yanzu tafara tsorata da alamurran Basmah yanda take nunawa tamkar itace kishiyar tata, itakam ko kad'an bazata iya cigaba da zama da itaba gwanda dady yaje ya dawo da mom d'insu hakan zai fimata kwanciyar hankali, a hankali Bilkisu tabud'e idanuwanta akan fuskar Ummi da hawaye suka yimata kwance akai, firgigit ta tashi zaune don gasgata abunda tagani, yatsa tasa ta lakuto hawayen sannan ta kalli Ummi

"Ya salam! Umminah kuka kikeyi?, miyafaru dake?" Batare da tace mata komai ba tajawota ajikinta tarungume

"Ba komai Bilkisu amma ina so infad'a maki cewa aduk inda kika tsinci kanki ki kasance mai tsoron Allah a rayuwarki, ban yarda kicutawa matar mahaifin kiba domin itama uwace agareki, ban yarda kiguji 'ya'yanta ba komai rintsi komai wuya domin su 'yan uwanki ne, ina jin zafi sosai idan Basmah tayimun wasu abubuwan fiye da zafin da nakeji idan mahaifiyarta tayi mani, sau da dama akan yimaka abune idan kayi amma ni Allah shine sheda ban tab'a yiwa matan mahaifina rashin kunya ba balle hakan tafaru dani, amma nad'auki abun a matsayin jarabtani ne Allah keyi, don haka kigujewa aikata hakan gudun kema haka tafaru dake"

Hannu Billy tasa tagoge mata hawayen ta sannan tace

"Zanyi yanda kikace Ummi, amma bazan samu damar aikata hakan ba matuk'ar zandinga ganin hawayen ki, hakan zaisa inji nayi loosing courage d'in yin hak'uri har inyi k'ok'arin kasa rama abunda akeyi maki"

"Bilkisu zuciya batada k'ashi fitar hawayen shike kashe rad'ad'in da nakeji a zuciya, amma ina tabbatar maki da babu komai duk abunda sukayi mana ko zasu yimana to nayafe masu fatana dukkaninmu Allah ya ganar damu kuma ya d'oramu akan gaskiya"

"Amin Ummi, yanzu yaushe zasu bamu sallama? Allah ni nagaji da kwancin asibitin nan" takardar sallama da akaba Ummi tajawo acikin jikkarta ta mik'a mata

"Nakira dadynki na sanar dashi, yanzu yayanki muke jira yadawo, amma sunce banda gobe mudawo karb'ar result"
















Mr's huss@in✍

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_A rayuwar kowane mutum yanada wahala yamanta da mutane masu tarin d'inbin alkhairi acikin ta da kuma alamurransa😍 to nima kamar hakane awurina, dukkanin mataki da cigaban da zan samu arayuwata bazan tab'a mantawa da irin k'warin guiwar da akoda yaushe nake samu daga wajen ki ba *AUNTY MAIJIDDA MUSA* fatana Allah ya dawwamar da amincinsa acikin rayuwar aurenki, yaraya maki zuriarki ya albarkaceta sannan yayi maku kyakkyawan sakamako da aljannah fiddausi bi gairi hisabin wala ik'abin👏🏻ina mik'o gaisuwa mai tarin yawa da kuma jinjinata agareki Allah yabar tare🤝 much luv aunty mj😍_

💎Page_____19💎


Shikenan Ummi bari nafara harhad'a kayanmu kafin su dawo, sister faraaha ce tashigo cikin d'akin fuskarta ba yabo ba fallasa cikin sauri Billy ta ajiye blanket d'in dake hannunta tana ninkewa ta rungume faraaha

"Congratulate me sis anbamu sallama yau zanje gida, missing home sosai wlh" murmushi tayi had'e da rik'o hannunta suka dawo inda Ummi take "Ummi kinga lil sis d'in Yaya Mahmud sai farinciki takeyi tunda tayi nasarar tirsasani anbata sallama" tana kallon Billy take maganar, zaro ido Ummi tayi

"Faraaha dama had'a baki kukayi aka sallameta lokaci beyi"

"A'a naga mutuniyar tawa tagaji da zaman kuma gashi result ne kad'ai zai zaunar daku na tsawon kwana biyu shiyasa kawai naga bari ayi hakan, inyaso bayan kwana biyun idan yafito saiku dawo saboda ina tsoron tayi mana absconding" tak'arasa maganar tana dariya, girgiza kai Ummi tayi tana murmushin irin wayon yaran zamani shine Bilkisu tayi mata kamar batasan da maganar ba hartana tambayar ko anbasu sallama, kai yara Allah dai ya shirya mana tafad'a cikin zuciya, kallon Billy faraaha tayi cikin damuwa tace

"Sisto bakida kirki k'irik'iri kike nunamun farincikin ki zaki tafi gida abunki batare da ko irin zakiyi missing d'ina ba"

"Kai aunty faraaha zaman asibitinne babu dad'i ko kad'an kinga kuwa dole inyi farinciki da samun sallama kuma kema kinsan ko ban fad'a ba zanyi kewarki sosai"

"Hmmm kamar da gaske"

"Aikuwa dagaske nakeyi, Ummi aramun wayarki na copy number ta aciki don ta tabbatar" mik'amata wayar Ummi tayi tana fad'in

"Maza ki kwafa kibani ink'arasa azkar d'in kafin magrib tayi na manto da hisnil Muslim d'ina agida" da sauri ta fad'a mata digit d'in tayi copy akan wayar sannan tafita d'akin saboda akwai statement d'in da take son cikawa ita kuma tamik'awa Ummi wayar sannan taci gaba da shirya masu kayansu.

Cikin b'acin rai mom ta sauko k'asa tare da nufar d'akin papi saida tayi knocking sau uku sannan aka bata izinin shigowa, yanayin da sukaga tashigo ya tabbatar masu da akwai abunda yafaru, d'aure fuska sosai papi yayi sannan yayi mata nuni da tazauna akan kujerar dake acan gefen wardrobe, anyi kusan mintuna biyar yana kallonta kafin can yace da ita

"Lafiya kuwa"

"A'a papi maganar gaskiya da akwai matsala" tashi Mahmud dake zaune agefen hajiya kaka yayi daniyar fita papi dake k'ok'arin gyara zamansa akan gado don sauraren abunda tazo dashi yace masa ya koma ya zauna,

"Inajinki meke faruwa ne?"

"Papi nidai so nake kayiwa dadyn yarannan magana ya maido mani da yarana hannuna bana buk'atar suzauna tare dashi ab'ata masu tarbiya" ba papi ba hatta hajia kaka da Mahmud saida suka zaro idanu had'e da bud'e baki suna mamakin kalaman dake fita abakin mom, kallonta papi yayi yana dariyar Ikon Allah sannan yace

"Meye dalilinki da kuma hujjarki akan abunda kika fad'a" aikuwa kamar jira mom keyi tabud'e baki bakunya ta zayyane masu duk abunda Basmah tafad'a mata k'arya da gaskiya kumafa papi inba son ab'ata yara ba har rungume rungume sukeyi agaban yaran, ni dai..." Katseta yayi cikin b'acin rai "ubangiji Allah ya rabaki da wahala Hussaina, yanzu meye amfanin wud'annan maganganu da kike fad'a agaban yaronki?,"

"Saboda suma hujja papi.."

"Rufamun bakinki, tir da yawanki ai wannan ba hujja bace shirmene, atafi suna aikata hakan shin haramunne? Sannan wayakai idanun yaran harsukai ga gano abunda bai shafesu ba"

"Papi kafahimta mana, agaban su akeyi"

"Mtsssss..wannan shi ake kira da bakin wahala, duk da banda tabbas akan abunda kefa ruwa yallab'ai natabbata wlh k'aryane hakan bai faruba don yanda nalura da halin hajia Aisha da shikansa maigidan nasu bazasu tab'a aikata hakan ba wlh, wannan duk k'ullalliyar yaran tane da gurb'atawa tunani ta b'ata masu tarbiya" hajia kakace ke fad'ar wannan maganar cikin fushi tare da b'acin rai, Mahmud dake zaune ya sadda kansa k'asa tunda mom tafara magana yace

"Mom wlh kiyarda dani wannan magana ba haka takeba, taya Ummi tasamu aikata duk wud'annan abubuwa ita da kullum cikin aikin kulamaki da yaranki take itada ko yaushe tana hanyar zuwa asibiti wurin jinyar 'yarta, na tabbata wannan matsalar Basmah ce tahaifar da ita, to bari kiji gaskiya mom ita kanta Basmah a asibiti take kwana, saida safe idan naje ita kuma saita jegida tayi wanka taci abinci lokacin Ummi tagama gyara komai sai sudawo tare kuma lokacin dady baya gida shin taya za'ayi tasan abunda yake faruwa, kiyi tunanin wannan maganar mom"

"Rufamun bakinka dama nasan kai bazaka yadda ba tunda ko yaushe bayanta kakebi tariga ta gama da kai da mahaifin naka" murmushin takaici papi yayi yana kallonta yace

"Tabbas muma d'in bamu yadda ba sannan kafin inrufe idona in bud'e inaso kibar d'akin nan shashashar banza da batasan ciwon kanta ba, inyaso muma d'in kice tagama damu kinji ko?"

Sumui sumui mom tabar falon zuciyarta na zafi da k'una akan rashin samun goyon bayan iyayenta aranta takai k'arshe akan cewa daga wannan karon bazata koma k'unsar bak'in cikin Aisha ba dolene bak'in yanayi ya juya akanta.

Tana fita papi ya kalli Mahmud dake kuka yace

"Kayi hak'uri kaima jarabawa ce Allah yayi maka da mahaifiya mai murd'ad'd'en hali kamar yanda muma ya jarabcemu da ita amatsayin 'ya" shafa kansa yayi tare da cigaba da lallashinsa har saida yaga yayi shiru sannan ya cigaba da cewa

"Dama Bilkisu bata da lafiya shine baka sanar damu ba kuma shima dadyn naku koda mukeyi magana dashi bai fad'a manaba abu har ankai ga kwanci asibiti gaskiya duk kanku baku kyautaba"

"Papi ni nazata tunda kunyi magana dashi yafad'a maku abunda kefaruwa" nan Mahmud ya zayyane masu duk abunda yafaru ranar da silar kwanciyar Bilkisu a asibiti, "Allah sarki Mahmud mahaifinka mutumne nagari, wlh gaba d'aya bai fad'a mana wannan maganarba amatsayin abunda yasa yace ummanka tayo gida, sab'anin da ya had'asu har takai ga sheganta masa 'ya'ya don banata bane shi kad'ai yafad'a mana, ya Allah kishirya mana wannan yarinya, gaskiya bata kyautaba ko kad'an kuma tayi kuskure sosai"

Shiru Mahmud yayi yana mamakin hali irin na mahaifinsa, tabbas duk hak'urinsa dole ya hukunta mom akan wannan abunda tayi masa,

Sunjima suna tattaunawa akan matsalolin mom tare da baiwa Mahmud shawarwarin yanda zai dinga lurar da ita, daga k'arshe papi ya tabbatarwa da Mahmud insha Allah gobe zasuzo suduba Bilkisu da jiki kuma yabawa dady hak'uri kafin suzo yafad'a masa basusun cewa Bilkisu batada lpy ba sai yau daya fad'a masu, sannan kafin sutafi ya kira Basmah da Batool yayi masu fad'a sosai tare da nuna masu suso 'yan uwansu domin ita duniya batada tabbas, babu yanda mom batayi ba don tasake keb'ewa da Basmah amma da hajia kaka talura da haka ta kasa ta tsare afalo har saida taga sunbar gidan sannan itama tanufi hanyar bedroom d'in papi ta d'ibo masa ruwa abuta saboda sallar magrib data gabato kuma dama shi bayason yin arwala a toilet yafiso yayi ta awaje hakan yafi sama masa natsuwa,

Ana kiraye kirayen sallar magrib suka isa asibiti don haka Ummi tace yaje yayo sallah kafin nan suma sunyi sannan sai suwuce,

Bayan sun iso gida yana yin parking da mota Billy tafito aguje tana fad'in.

"Home sweet home, missing u so much" tana maganar tana bud'e hannayenta asama tare da shak'ar iskan dake kad'awa, hasken fitillun dake zagaye da bangon gidan su suka taimakawa Mahmud wajen hango farincikin dake shimfid'e a fuskarta, dariya yayi tare da fad'in

"She's always different, dt's my lil sister"

Gaba d'ayansu part d'in Ummi suka nufa agajiye kowanensu yazube akan kujera ita kuma direct d'akinta ta nufa cikin zumud'i tana shiga taci karo da manyan akwatuna guda biyu wanda kemata nuni da anan 'yan uwanta suke zaune, ko kad'an ranta bai b'aciba ta wuce toilet ta watso ruwa, wardrobe d'in kayanta tabud'a suna nan kamar yanda tabarsu agyare, taciro wata doguwar riga ta material amma cotton anyi mata d'inkin nan da

Please Login or Register in order to submit comment