Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma gefen da yaya Mahmud kezaune akan gado tana sharar k'walla tace

"Ayau nagano kuskuren da nake aikatawa bakowa yake cutarwa ba face ni kaina da kuma 'ya'yanah, gaba d'aya idanuwana sunrufe wajen son kaina nakasa magance matsalata da kuma ta 'ya'yana saboda wani dalili dake cikin zuciyata, amma ina so kuyafemun daga yau bazan koma yin abunda zaisa kushiga damuwa ba, zanbaku kula da kowace uwa ke baiwa 'ya'yanta , zanzamo uwa tagari kamar yanda mahaifana ke buk'ata, zanyi k'ok'ari inmanta da wasu abubuwan koda ba duka bane, amma inaso kusani kowace irin k'iyayya nada asali haka kuma kowace sosayya itama tanada nata asali, Na amince kowanenku ya auri wanda yakeso bazan koma hanaku muradin zuciyoyin kuba kuma ina maraba da wud'anda kuke so nima ina son su har cikin ziciyata,

Tana gama fad'ar haka tamik'e tawuce d'akinta cike da nadama da dana sani.

Fad'a sosai yaya Mahmud yayiwa Batool da nasihohi akan abunda tayiwa mahaifiyarsu ya nuna mata kuskuren data aikata da kuma fushin Allah da tajefa kanta aciki dabata rok'i mom tayafe mata ba, har d'aki tasake bin mom tana k'ara bata hak'uri da neman yafiyarta, shi kuma yaya Mahmud ya kalli Basmah yanda tayi duhu da rama yace

"Basmah ciwon nan yana matsamaki don haka dole yau muje asibiti, nagaji da ganinki cikin wannan yanayin duk da nasan kina k'ok'arin cire komai aranki dolene yau sai munje kinga likita koda asirrancene"

"Don Allah yaya kadena batun zuwa asibitin nan har sai bayan aurenku, banaso wani abu da zai kawo cikas awannan lokacin, kana gani dai yanzu muka gama shawo kan wata matsala kar kuma mujawo wata dazata iya watse farincikin da mom tagama tabbatar mana da samunshi daga wajenta, alhamdulillah ina samun sauk'i sosai, d'a zuma dana shiga wannan yanayin saboda nakasa jurewa ganin yanda 'yar uwata ke kuka akan tasamu amincewa akan abunda takeso awajen mom, to sai nayi tunanin kada tafad'a irin tawa matsalar ga abunda takeso akusa da ita har shima yana sonta amma takasa samunsa, to ina wannan tunanin ne kuma daga nan bankoma sanin abunda yafaruba saida nabud'e ido naganni ajikin mom, damuwa da tunani sune kesa ciwon na tasarmun amma tunda yanzu zasu k'auracewa rayuwarmu natabbata in sha Allah itama zata dena ciwon, amma kaima ya kamata kaje asibiti kaga likita" harararta ya d'anyi kafin yace

"Babu inda zanje nima ko kin manta inada tawa likitar agida" dariya tayi kafin tace

"Point of correction yaya kana dai da malamar jinya agida amma kam ba likita ba" rank'washi yakai hannu zaiyi mata akai da sauri tayi baya takwanta ajikin kan gado tana dariya, ita kuma mom don d'ai tacirewa Batool damuwar dataga tashiga akan abunda tayimata kuma ta tabbatar ta yafe mata yasa tace taje tabud'e bedside wardrobe ta d'auko reza tayi mata yankan k'umba, haka ta tashi cikin sanyin jiki ta tashi taje ta d'auko rezar tadawo gefenta ta zauna kanta ak'asa tanaji duk ta tsargu, murmushi mom tayi data fahimci hakan tadinga jawo mata fira kala kala har saida taga tasaki jikinta sannan tamik'a mata hannu tafara yimata yankan k'unban sunayi suna labari...

NOTE

_A wannan gab'ar 'yan uwa yakamata mufahimci cewa ita uwa duk mugun halinta da shed'ancinta baya halatta ga d'a yamunana mata ko yacutar da ita da halshenta, yin hakan babban kuskurene a musulunce da kuma aladance matuk'ar d'an nagarine mai neman yagama lafiya da duniya, sannan mufahimci cewa ba'a yanke tsammanin shiriyar bawa akowane lokaci duk mugun halinsa ta sanadiyar wani abu daban, kamar dai yanda yau bazato ba tsammani mom tacanza halinta ta sanadiyar yaranta, badon sun kasance masu girmamata da bata hak'k'inta na uwaba da hakan bazai tab'a faruwa ba_



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____69💎


Izuwa yanzu abubuwa sun sauya sosai agidan dady domin mom ta ajiye komai agefe tarungumi mijinta da 'ya'yanta tana basu kula yanda yakamata wanda hakan bak'aramin sauya rayuwarsu yayi ba ta b'angaren dady kuwa duk da canjin da yagani daga wajenta da irin kulawa da biyayyar da takeyi masa hakan baisa yadena fushi da itaba, saboda yanda yasan halinta idan ya amince mata yasaki jiki da ita zata iya sake b'ullo da wata matsalar daban, tunda mom take bai tab'a fushi da ita haka ba, gaba d'aya yadena cin abincinta, maganama sai idan takama dole yake amsa mata shima baya wuce um ko a'a, yadena sakar mata fuska, ranar girkinta kuwa yana k'asa palour abunsa ita kuma tana sama ita kad'ai tayi basa hak'uri har tagaji amma yak'i hak'ura kullum sai tsaurara fushinsa yakeyi akanta, ya matuk'ar juya mata baya fiye da tunaninta wanda duk yayi hakanne don hukuntata bisa kuskuren da tadad'e tanayi yana samata ido, amma aransa kwata kwata bayajin dad'in hakan da yake yimata, ita kuma ganin hakan yasa tadena zuwa part d'insa aranakun girkinta, amma takan shirya abincinsa kowane lokaci tasa akai masa, yanda akakai na safe haka za'a d'aukoshi idan anje kai narana batare daya tab'a ba haka kuma nadare idan ankai haka za'a d'auko naranar baiciba kullum haka yakeyi har tafita girki kuma hakan baisa tadena dafa masa ba, idan kuwa yafita baruwansa daya kira wayarta har yadawo, hakama idan yadawo kawai zai shiga part d'inne don yaduba lpyrta data yaransa amma ko kallon inda takeyi bayayi balle har tasaran yayi mata magana, inkuma tayi masa ciki ciki yake tanka mata kuma batare daya kalli inda takeba, tun abun baya damunta yanzu har yafara damunta, fiye da wata d'aya kenan yanzu kullum cikin kuka take da nadamar abubuwan datayi, tasani cewa iya so da k'auna ya nuna mata arayuwarta, bai tab'a cimata fuska ko mutunci ba agaban abokiyar zamantaba, yana iya k'ok'arinsa wajen kyautata alak'a da zamantakewarsu ita da matarsa amma tarufe idanuwa tanata cuzgunawa rayuwarsu akan wani d'an k'ank'anen laifi daya aikata mata wanda yakamata ace tuni tamanata da hakan, gashi yanzu tajawa kanta tsanar da batasan makomartaba awajensa,

Gaba d'aya yaranta sun fahimci halin da take ciki amma saboda suma suna son canzawar mahaifiyar tasu yasa suka kauda idanuwansu ga abunda ke faruwa, amma suna iya k'ok'arinsu wajen ganin sunrage mata damuwa sosai, duk abunda zaisa tayi farinciki shi suke yimata, kuma alhamdulillah tana cire damuwa idan tana tare dasu zasu zauna suyita firarsu irin ta uwa da d'a wani zubin sai taji cewa ba kad'an tamatuk'ar cutar da kantaba abaya data kasa samar da irin wud'annan lokuttan farinciki tsakaninta da 'ya'yanta sai yanzu da take gab da rabuwa dasu kowace zataje gidan mijinta, hatta Billy da Bilal yanzu dinga canji awajen mom saboda tadena takura masu idan sunje wajen 'yan uwansu duk da koyanzu acikin ranta bata son ummi dasu kansu amma kuma babu ruwanta dasu, gaba d'aya ta shafe cewa akwai wata Ummi da yaranta agidan cikin ranta, rayuwarta kawai takeyi da 'ya'yantah batabi takansu balle har ranta yab'aci.

Yauma dai kamar kullum zaune take a guiding abubuwa duk sun isheta, gashi su Basmah basunan sunje gidan papi yimasa weekend shikuma yaya Mahmud yana wajen faraaha Ummi kuma tun safe taje anguwa yau ita kad'aice a gidan sai maigadi, gashi har magrib takusababu wani da zai d'ebe mata kewa, mik'ewa tayi da niyar komawa part d'inta sai ga motar dady tahango tana shigowa, tsaye tayi tana jiran fitowarsa har yagama parking d'in motarsa yafito don yau kwananta biyu bata sashi a idoba, wata irin soyayyarsa da k'aunarsa ke fizgarta wanda shine dalilin daya sata tsayawa tagansa ko rad'ad'in dake damunta azuciya zairagu, zagayawa taga yayi ta d'ayan gefen yabud'e murfin mota Ummi tafito tana dariya, nuni yayi mata da hannu alamar ta shige gaba suje, rausayar da kai tayi had'e da mak'e kafad'arta wai saidai shi yafara wucewa gaba, dariya yayi had'e da d'ago kansa karaf sukayi ido hud'u da mom dake tsaye tana kallonsu, d'aure fuska yayi tare da tura murfin motar ya rufe sannan yarik'o hannun Ummi suka nufi part d'inta yana murmushi, saida ya kalli mom sannan yakai hannunsa ga fuskar Ummi yana d'an goge mata k'asan idonta.

'Dago idanuwa Ummi tayi tana kallonsa had'e da cewa "meye haka abu Bilal karfa ka tsolemun ido"

"Ni na isa intsole icon rabba'atul bait d'ina, wani abune na kakkab'e maki" yafad'a yana k'ara kallon gefen da mom take idanuwanta Sunci ka tafe da k'walla, da gudu tabar wajen tanufi part d'inta hayen na ziraro mata afuska, wani irin kishi da tsanar Ummi na sake taso mata acikin zuciya, a tunaninta da sanin ummi kuma da amincewarta duk dady keyimata wud'annan abubuwan, tabbas idan hakane bazata tab'a sonta aranta ba sai dai kawai tazauna da ita zaman lafiya don samun farincikin 'ya'yanta dana mijinta, ita kuma Ummi gaba d'aya bata san abunda kefaruwa tsakanin mom da dady ba hatta abubuwan da dady keyi yanzu batasan inda yanufa ba, tunaninta d'aya shine soyayyar tashice ta motsa don haka tashige abunta jikinsa tana fad'in "dadyn yara kullum kai baka tsufa akowane lokaci sake sabunta salon soyayyarka kakeyi"

"Allah ko rabba'atul bait?"

"Sosai kuwa, shiyasa nake ganin munfi duka matan duniya dacewa da masoyin namiji daya sangartamu, natabbata arayuwata babu wani namiji dazai iya tasiri acikinta face kai kad'ai, madalla da ni'imar da Allah yayi mana tasamunka amatsayin miji agaremu" murmushi yayi had'e da yimata kiss agoshi sannan suka k'arasa daga ciki wani gefe nazuciyarsa cike da damuwa, kawai yana jurewa kansa yiwa mom wasu abubuwane don koya mata darasi amma badon yanajin dad'iba.

Sosai mom ke kuka tana fad'in, "Allah natuba kayafemun bisa kurakuran danayi agareka da kuma mijina dake matuk'ar sona, ya Allah ka maidomun da hankalinsa agareni, nayi alk'awarin zan zauna dashi bisa kyautatawa da kuma biyayyar aure har iya k'arshen rayuwata, zanjure dukkanin abunda nakeji inbasa farinciki da kwanciyar hankalin daya rasa awurina" ganin kukan bazai yimataba yasa tashiga toilet tayo arwala ta tada sallah tana hawaye batare da tasan metake karantawa acikiba, Allah sarki rayuwa kenan, shi namiji haka yake duk yanda yakai k'ololuwa a soyayyarka bazai hana ya shayar dakai ruwan mad'aciba wani lokacinma ruwan guba, duk ko yanda kake yimasa biyayya balle ga wacce batayi irin mom, sai gashi yau tayi sake hak'urin da yatayi da ita can baya ya koma mata bak'in ciki, b'acin rai da kuma damuwa.

Kasancewar yau zata karb'i aiki da daddare yasa bayan anyi sallar isha'i tafad'a kitchen ta d'ora sanwar tuwon alkama dama tanada miyar shuwaka datayi yau da safe tayi warming d'inta, cikin mintuna ashirin ta kammala sannan takoma d'aki tawatso ruwa, har zatayi makeup saita tuna da cewa wanda zatayi donshi ai yanzu bata gabanshi kawai tafasa, doguwar rigarta tasa tare da lullub'e jikinta da mayafi sannan tanufi kitchen ta d'auki kulolin abincin data d'ora akan tray tanufi part d'insa saboda yaran basunan dako zuwa bazatayiba don tasan baci zaiyiba, da sallama tashiga parloun tanufi dining area shikuma yana zaune akan kujera 3sitter ya d'ora k'afarsa d'aya akan d'aya yana karatun jarida, ciki ciki ya amsa mata had'e da bin bayanta da kallo sannan yamaida kansa ga jaridar da yake karatu, tad'an jima tsaye bayan ta ajiye abincin kafin tajuya tanufo inda yake kanta aduk'e tace

"Barka da dare, ga abincinka nan nakawo maka" d'ago kansa yayi had'e da cewa "ok" yaci gaba da karatun jaridarsa, duk da batada tabbacin cewa zaici abincin hakan daya fad'a tad'anji sanyi aranta, taso ta sake bashi hak'uri a lokacin amma yanayin da taga fuskarsa a d'aure tamkar bashine d'azu yagama kwasar dariya da matar saba yasa tajuya tafice abunta ranta cike da k'una, aranar kwana tayi tana salloli akan Allah yakarkato da hankalin mijinta agareta ya yafe mata laifukan datayi masa abaya, yanzu tagano cewa, makirci, fitina, mugunta, k'azafi, tashin hankali da sauran abubuwan zalinci aduniya basu isa susa ka iya mallakar zuciyar mijin kaba har sai inka koma ga Allah, wanda hakan yasa tazubar da komai aranta takoma ga Allah saboda bakad'an mijin nata yajuya mata baya ba.

Har aka saka ranar auren faraaha da Mahmud dady bedena fushi da itaba yadai d'an canza kad'an tawajen cin abincinta da kuma yimata magana idan takama amma zancen sakin fuska da walwala tsakaninshi da ita haryau babu, ansa ranar auren yaya Mahmud nan da wata biyu wanda hakan yasa yau dady yakirasu Ummi ita da mom yayi masu bayani da ganan kuma ya shawarcesu akan cewa idan sun amince yanaso yahad'a da auren su Batool da Bilkisu ayi arana d'aya, dukkaninsu sun amince da hakan tare da fatar Allah yasanya alkhairi kuma yasa ayi cikin nasara, ba dady ba hatta Ummi tayi mamakin amincewar mom alokaci d'aya amma sai tabar abun azuciyarta.

Iyayen dr Ahmad sun kawo kud'in sadakinsu dubu hamsin kamar yanda aka yanka masu amma da yake dady bayanan yaya Mahmud kad'aine sai yakarb'a hannu biyu bayan yayi masu iso ababban falon dady nak'asa sannan yayi masu bayanin cewa ga ranar da akasa d'aurin auren saisu sanar da d'ansu idan lokacin yanada hali, sun jinjina maganar sosai saboda tunanin kamar ank'uresa nan da wata biyu amma abun mamaki koda suka koma suka sanar dashi nan take ya amsa da cewa ya amince kuma ashirye yake cikin farinciki da murna kamar zai taka kan jariri ya rungume mamy yana sanar da ita.




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMU👏🏻😭_*

👭❤ *'YAN UWANA NE!*❤👭
💎 _they're my relatives..!_💎


Written by: *BILLY S FARI💎*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


💎Page_____70💎



Wata 'yar madaidaiciyar jikka yad'auko cikin wardrobe d'in Ummi ya ajiye agabanta yana fad'in mamynah zoki gani.

Jid'owa mamy tayi da kan gadon tadawo k'asa inda yake tazauna tanabin jikkar da yake k'ok'arin zuge zip d'inta da kallo cike da mamaki, zabura tayi da sauri had'e daja baya tana kallon kud'in da yake cirowa daga cikin jikkar, "innalillahi wa inna ilaihirraji'un, ahmadi ina kasamo wud'annan kud'ad'e haka? Kadafa kace kafara...Allah dai ya tsare""

Murmushi yayi tare da zazzage kud'in agabatanta wud'anda gaba d'aya d'aurin 'yan dubu dubune, ajiye jikkar yayi gefe sannan yagyara zamansa yana kallon kud'in yana murmushi yace "Kud'i masu gidan rana"

"Kai kafad'amun a inda kasamo kud'ad'en Ahmadu, gaba d'aya a tsorace nake nan inba zuwa kayi kad'aukomun abunda yafi k'arfina ba" rik'o hannunta yayi kafin yace "mamynah ki kwantar da hankalinki, bazantab'a yin abunda zaijawo maki b'acin raiba, nayi alk'awari ga Allah insha Allah bazantab'a ciyar dake ko fatimata haramunba don haka kidena kokonta akan yaronki wud'annan kud'ad'en da kike gani mallakina ne kuma halak malak" shafo sumar kansa tayi tana kallonsa kafin tace

"Banida kokonto ko kad'an anan tarbiyar da muka gina maka nida mahaifinka amma wannan duniyarce dake cike da rud'i da abun mamakice banida tabbas da akanta shiyasa kaji ina tambayarka, amma tunda kace haka shikenan fad'amun a ina kasamesu"

"Mamy kinsan yau kimanin watana shida kenan da fara aiki kuma duk kwanan wata ina d'aukar albashina dubu d'ari uku da hamsinne a matsayina na consultant, to sune duk lokacin dana kwasa baya wuce muyi amfani da dubu 20 zuwa 30 ga wata sauran kuma sai na dinga tarasu acikin account saboda in samu inbiya alhaji Tukur kud'insa sannan in sake bud'e shagon Abba tunda da dad'ewa na karb'esai hannun wanda yabawa jinginarsa tundana biyasa kud'insa sai inzuba flaour nima infara sayarwa, ina so inyo gadon wannan sana'ar da Abba yaci damu ya shadamu kuma yatufatantar damu da ita tayanda lak'anin sunan bazai tsaya akansaba kad'ai har d'iyan d'iyansa sai sunyi gadonsa da izinin Allah" idanuwan Ummi nahawaye tarik'o fuskarsa tare da kissing forehead d'insa tace

"Ubangiji Allah yayi maka albarka, Allah yajik'an mahaifinka kuma ya gafartamasa, naji dad'i sosai da wannan shawarar daka yanke amma mezai hana kamanta da zancen bud'e shagon mahaifinka har sai nan gaba tunda ga zancen aurennan naka yataso kuma kaga bakada wani muhalli gashi ka amsa masu da cewa ka amince da ranar da suka sa inyaso sai inkoma gidan liman tunda akwai d'akuna nasan bazai hanani d'a yaba sai kayi k'ok'ari ka gyara nan d'in kafin lokaci yayi"

"Shikenan mamy duk yanda kikace ayi haka za'ayi, amma agaskiya banyarda daki koma gidan liman ba, duk inda zaki to dolene ina tare dake domin kece hasken rayuwata, to idankika tafiyarki can aikinga kinbarni acikin duhu dani har matar tawa dazan kawo, meye amfanin gidannan idan babuke aciki mamy?"

"A'a Ahmad taya wannan gidan zai ishemu, don Allah kada ka takura kanka, kayi hak'uri inkoma can har Allah yahore maka inda zamu zauna awadace, kuma ai kaga da nan da gidan liman babu wani nisa kullum zaka iya zuwa kaduboni koba haka baj" fir dr.Ahmad yak'i yadda da hakan daga k'arshema yashiga lissafa mata abunda yakamata afarayi da kud'in don bayason zancen, kud'in alhaji Tukur yafara cirewa dubu d'ari uku da hamsin sannan yamaida sauran acikin yace

"Mamy ga wannan ki ajiye, gaba d'aya kud'in milayan d'ayane da dubu d'ari da ashirin ancire wud'annan dubu d'ari uku da hamsin zanje inkaiwa alhaji Tukur abunsa yarage saura dubu d'ari Bakwai da saba'in daga can zanzo da masu gyaran gida sai suduba sugani nawa gidan zai buk'ata"

Juyawa mamy tayi tana kallon gabas tayi sujudush shukur ga Allah daya nuna mata wannan rana da yaronta ya sauke hakk'in da mahaifinsa yabar masa yabiya na mutane wanda ta tabbata yau rouhin mijinta zai samu salama saboda wannan nauyin da aka sauke mata tajima kafin ta d'ago kanta tana sake sanyawa d'an nata albarka sannan yafice zuwa gidan alhaji Tukur, Allah Akbar tabbas alk'awarin Allah baya tashi duk abunda kayi sai anyima, abunda dr.Ahmad yagani lokacinda mai mashin ya ajiyesa a k'ofar gidan alhaji Tukur ya matuk'ar bashi mamaki da ban alajibi, sosai ya sake gaakata alamarin Allah tare da imani dashi, Wasu mutane ya hango s biyar a k'ofar gidan cikin kayansu riga da wando bak'ak'e sai rigar ciki light blue wuyansu d'aure da necktie sunsha bak'ak'en takalma cover shoes da alama ma'aikatan bankine suna k'ok'arin rufe gidan alhaji Tukur duk'e agabansu yana magiya da basu hak'uri ga matansa uku da yaransa kusan goma aha d'aya a zagaye dashi suna kuka d'ayar matarma d'auke take da ciki wanda gadukkan alama yatsufa sosai, k'arasowa yayi wajen yana kallon ikon Allah da kuma tarihi dake maimaita kansa, nan take yatuno da mahaifinsa yanda ranar yake durk'ushe agaban alhaji Tukur yana basa hakuri da neman yayi masa alfarma amma yawofantar dasu har yayi silar rasa rayuwarsa sai gashi yau shima yana raye ya gansa durk'ushe agaban wasu yana neman alfarma ikon Allah kenan wato duk abunda kashuka to tabbas shizaka girba, goge hawayen idonsa yayi daidai lokacin da wani d'aya daga cikin jami'an bankin da bayama jin hausa sosai kecewa alhaji Tukur

"alhaji, alhaji, kinga gida wenan bizaki doki komai acikiba har sekinbiya kud'in banki da kika cinye, zamuyi gonjonsha ga maisho nan da kwana uku iden baki kawo kudinba yarage ruwanci"

Cikin kuka da magiya alhaji Tukur yace "Yallabai don Allah kuyimun afuwa zuwa nan da wani d'an lokaci zan kawo, kutaimaka kubud'emun gidannan gani da mata ga yara da yawa ina kukeso naje dasu"
"Kitambeye kenki.mudai aiki akeshamu kuma mungama, to baruwana da danki kece kika haifeshu don haka shekisan yanda jakiyi dashu" mutumen yafad'a tare da juyawa yabarsa nan wajen a duk'e yana kuka, ga yaransa suma suna tayasa, duk'awa dr. Ahmad yayi yasa hannu ya d'agota daga durk'ushen da yake yana goge masa hawaye, d'ago kai alhaji Tukur yayi yana kallon dr.Ahmad nan take yatuna da abubuwan da suka faru watanni bakwai da suka wuce, cike da kunya yamaida kansa k'asa yana fad'in

"Ahmad kaga yanda Allah ke ikonsa ko?, kaga yanda hak'k'in mahaifinka kebibiyata, wlh tun ranar nayi dana sani da nadamar abunda na aikata masa har ya zamo silar barinsa duniya amma duk da haka kadubi yanda hak'k'insa yayi dani"

Goge hawayensa yayi sannan yace "karka damu alhaji dama lokacin Abba yariga da yayi ranar koda hakan bata faru tsakaninkuba natabbata tabbas dole zaibar duniya aranar don haka kadena wannan tunanin, yanzu kamata yayi ka k'arfafa zuciyarka kadena wannan kukan haka agaban iyalanka insha Allah komai zai dai daita"

"Ahmad kenan taya zakace haka bayan kimanin dubu d'ari bakwai banki kebiyata kuma banida halin biyansu, ga shagona dake kasuwa nayi gobara komai yak'one k'urumus taya abubuwa zasu dai daita agareni"

"Kayi imani mana alhaji kuma karok'i Allah natabbata zai kawo maka d'auki" k'arar matar alhaji dake tsaye tana sharar k'walla saboda azaba data zamemata kashe biyu tun d'azu ta bak'incikin halin da suke ciki data yaron cikinta dake nemanan hanyar fitowa suka jiyo, da sauri alhaji yajuyo yaganeta k'asa asheme jini nazuba ta k'asan k'afa fuwanta ga abokanan zamanta su biyu sun zagayeta suna kiran sunan, fad'uwa zaune yayi had'e da d'ora hannuwa akai yana fad'in

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun nashiga uku wayyoni Allah na"

"Haba alhaji meye haka, bakaga halin da matarka take ciki bane?, jini ke zubar matafa!, idan har baka hanzarta kaita asibiti ba zaka iya rasa rayuwarta da ita har abunda ke cikinta"

"Ahmad taya zankaita asibita bayan banida ko sisi a aljihuna, ubangiji Allah dai ya tausaya mata ya saukete lapy," nuna matansa yayi yace kutallabeta kushiga mak'wabta har muga yanda Allah zaiyi da ikonsa" gidan wani mak'wabcinsu suka nifa da ita da sauri Ahmad ya dakatar dasu yace

"Kudawo, wannan haihuwar akwai matsala bata buk'atar azauna gida dole sai an dangana da asibiti, kujirani anan ina zuwa" da sauri yanufi titi yataro mai keke napep, rik'ota yasa suyi amma takasa tafiya hakan yasa yajuya ga alhaji daya buga uban tagumi yace

"Don Allah alhaji katashi karik'ota sanyin jikifa ba naka bane" mik'ewa alhaji yayi jiki bak'wari ya nufi inda take zube akwance ya cirata amma yakasa ga jinin sai zuba yake sakeyi sosai, tsufa da rashin kuzarin da yake ciki yasa yakasa d'aukarta gashi dama tak'ara nauyi saboda cikin dake jikinta daya girma, tsoron kada arasa rayuwarta kota yaron yasa dr Ahmad k'arasowa wajen yace dashi

"Zan iya taimakonka?" Kad'a masa kai alhaji yayi nan take dr Ahmad yaciccib'i matar batare daya damu da jinin dake zubo jikinta ba, a napep d'in yasata sannan yace alhaji ya shiga ya rik'eta, kallon mai napep d'in yayi yace

"Kayi sauri ka kaisu specialist hospital, ganinan biyowa bayanku"

Kallon iyalin alhajin yayi yace "kushigar da yaran mak'wabta sai kuzo mutafi ko?" To suka amsa masa dashi shikuma yanufi titi ya taro mashin da wata keke napep, suna fitowa yace su shiga shikuma ya hau mashin d'in yacewa mai napep d'in yabiyo bayansa.

Suna zuwa asibitin suma suna isowa nan take yabiya masu napep d'in kud'insu sannan da sauri nurses sukazo aka dauki matar bisa d'an gadon d'aukar mararsa lpy aka gungurata zuwa emergency, kasancewar ansan dr Ahmad yasa ba'a tsaya wata wataba aka shiga tearter room da ita bayan anba alhaji Tukur wata takarda yasa hannu, saboda tazubar da jini sosai yasa akace tearter za'ayi mata don bazata iya haihuwar da kantaba gashi d'an d'an ya gicce mata aciki, gorar jini uku aka buk'ata wanda da k'yar aka samu d'iyar gora d'aya ajikin babban d'and'an alhaji Tukur, duk inda yakamata asamu cikon gora biyu asaye dr yasa anema amma saboda jininta mai wuyar samune wato blood 0- ba'a samuba, hakan yasa dr Ahmad yaje yakwanta aka d'ebi gora biyu ajikinsa saboda irin jininne agaresa, sosai faraaha tadinga zolayarsa akan jini yayi masa yawa ko yanzu za'a iya d'ibar wata gora biyun ajikinsa don dama da ita ake zirga zirgar komai tunda suka shigo yakirata awaya akan tazo yana neman taimakonta, shidai murmushi kawai yayi sannan yamik'e bayan tafasa masa madara peak data bayar aka sawo masa a canteen dake can gefen asibiti yasha,

Shidai alhaji tukur zaune d'ai yayi jugum wasu hawaye nabiyar wasu cike da kunya da nadama ganin wanda ya cutar yau shine ke taimakonsa, shikuwa dr Ahmad wajen biyan kud'i yanufa yasayi duk abubuwan da yakamata ya biya sannan yaje yabiya kud'in tearter dubu talatin tare da kud'in gadon jinyar da za'a bata na kwana biyar dubu goma sha biyar ganin yanda ake kallonsa duk inda yabi yasa yashiga dubon kayan dake jikinsa yaga ashe gaba d'aya duk sun b'aci da jini, kasance warsa mutum mai tsananin tsanda nan take sai yaji duk ya tsargu, wajen alhaji yanufa ya mik'a masa takardun receipts d'in kud'ad'en daya biya sannan

Please Login or Register in order to submit comment