Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaso yatambayeta amma ganin halin da take ciki yasa ya ajiye maganar yashiga rarrashinta tare da kwantar mata da hankali" d'ago kanta tayi had'e da cewa

"Dr kayimun alk'awari zaka rufe wannan sirrin nawa don Allah" kallonta yayi kafin yace

"Shikenan indai hakan zaisa kisamu farinciki, amatsayina na likitan dake kula dake tare da ceto rayuwarki nayi maki alk'awarin bazan fad'awa kowa ba yanzu, amma bisa sharad'in nan da sati d'aya dole nasanar da iyayenki domin suyi gaggawar fita dake waje, saboda acan za'a iya samun k'wararren likitan da zai iya samo maganin wannan matsalar taki, idan kin amince shikenan" sanin cewa komai ya kammala alokacin yasa tayi saurin amincewa. Nan yarubuta mata duk maganin da yakamata tasha kafin nan da sati d'ayan yabata ta karb'a had'e da yimasa godiya sannan ta tashi tawuce, girgiza kai yayi har zata fita yakira sunanta cikin sanyin murya had'e da cewa

"Basmah idan son samune kinisanta kanki da wannan abun dake sakaki tirsasawa zuciyarki lalle saikin hak'ura dashi domin wannan tirsasawar da kike yimata itake k'ara tsananta rauninta" murmushi tayi masa sannan tafice abunta kamar babu wata matsala atattare da ita, kasancewar akwai kud'i a hannunta yasa ta tsaya pharmacy d'in dake cikin asibitin tabasu takardar akayimata bill d'in adadin kud'in tabiya sannan aka saka mata maganukkan acikin leda takarb'a tawuce gida, tana isa bakin gate taci karo da yaya Mahmud, da sauri tab'oye ledar cikin hijabinta sannan tak'arasa wajensa tana murmushi.

"Sannu yayanmu angon autynmu faraaha, ina kabaro d'ayan angon" harararta yayi sannan yace

"Daga ina kike tun d'azu inata nemanki, faraaha nason magana dake, tace tayita kiran wayarki bakiyi picking ba"

"Laa..am sorry yaya wlh nabarta agidane saboda ina sauri inje gidan papi nakarb'owa mom sak'o"

"Bana son k'arya Basmah har mom natambaya tace bata san inda kika jeba, saida natambayi habu yafad'amun cewa kinfita tun d'azu, hakan yasa natsaya jiranki anan"

"Allah yaya gaskiya nafad'a maka saidai idan hidimace ta d'auke mata hankali ta manta da cewa ta aikeni"

"Shikenan koma meye kije zan sanar da ita cewa takira wayarki kindawo" wata ajiyar zuciya tasauke had'e da rab'awa ta gefensa ta wuce, shi kuma yabita da kallo alamun kamar yana son gano wani abun,



*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_

_*TAMBIHI* Tabbas duk abunda yayi farko zaiyi k'arshe don haka kuyi hak'uri masoyana, kuci gaba da bibiyar littafinnan sannu ahankali domin inada tabbaci akan zaku amfana sosai, ni kaina inajin tausayin Basmah amma bayanda zanyi dole inci gaba da rubuta littafin ayanda tsari labarin yazomun, karku manta base on true life story ne, kuma nazab'i in rubutasane saboda al'ummah su k'aru kuma su fahimci muhimmanci da girman soyayyar 'yan uwantaka, raunin da muke fuskanta tsakaninmu da 'yan uwanmu akan wata 'yar k'ank'anuwar matsala da zata b'ullo daga wajen iyayenmu ko kuma mukammu, sai kaga zumunci ya lalace saboda rashin hak'uri, juriya da kuma rashin fahimta, shiya tunzura alk'alamina wajen kawo maku wannan labarin, don haka ina rok'onku duku cigaba da hak'uri, kad'an yarage mu ida kammala littafinnan, gaggawa batamu bace domin ita aikin shed'ance, ngd da zafafan comment d'inku Allah yabar so da k'auna, saboda haka idan har kun kasance ku 'YAN UWANA NE nasan bazaku tab'a bani kunya ba, zakuci gaba da kasancewa dani har zuwa k'arshen wannan littafi kuma ina da yak'ini akan haka in sha Allah, idan kunyarda da hakan ina jiran zafafan comment d'inku fiye da wud'anda kukeyi akoda yaushe, masu k'orafi akan Basmah afuwan afuwan, yakamata ace kun fahimci cewa shi so cutane, kuma yin hak'uri akansa lalurane babba kafin yazamo magani, don haka dole Basmah ta cutu saboda tsantsar hak'uri da juriyarta, sannan masu cewa Basmah tafad'i halin da take ciki, to matuk'ar tafad'a ko dr yafayyace gaskiyar ciwonta to tabbas dole sai kan wannan family ya rabu biyu tunda Billy dai nason Mahmud, son da zai iya rufe mata ido takasa gane irin jarumta da sadaukarwar da 'yar uwarta tayi mata har yakai ga shed'an yashiga zuciyarta tayi tunanin kawai so ake arabata dashi don anga Basmah bata samu miji ba wanda hakan zai kaisu ga samun sab'ani mai girma saboda idan tambarin so ya doki zuciyar mutum duk tarbiyarsa da iliminsa suna iya k'aurace masa alokacin da yaga ana shirin gina wata katanga tsakaninsa da abunnan da yake so, sai kaga idan shed'an yayi nasara akansa idonsa sun rufe ya aikata abunda ko jahili bazai aikatashiba, amma mutum da kansa ya fahimci wani abun na musamman daya bada gudun mawa awajen k'arfafa masa soyayyarsa kan iyasa yayi sadaukarwa bisa ra'ayinsa da kuma muradinsa, dafatar kun fahimceni, thank you once agains my proudly fans, LUV U FILLAH_😍❀😍


πŸ’ŽPage_____78πŸ’Ž


Tana shiga cikin gidan taci karo da mom hankalinta atashe tafito hanyar guarding tana dube duben inda zata hangota sai gashi sunci karo, rik'o hannunta tayi had'e da cewa

"Basmah ina kika shiga anata nemanki tun d'azu?, hatta yayanki babu inda bai dubaba wajen bid'arki kinsa gaba d'aya duka hankalinmu yatashi"

"Oh my God mom bafa nisa najeba, zaku wani tada hankalinku haka, to idan da mutuwace nayifa ya zakuyi?" jitayi an tallafo k'eyar kanta da duka ana fad'in

"Ba abunda zamuyi tunda lokacin kine yayi, duk kinbi kinsa hankalin kowa ya tashi saboda rashin ganinki" juyowa tayi taga ashe Mahmoud pilot ne yafad'i haka tare da kallon mom da tuni ta sandare wajen saboda yanda kalaman Basmah suka saka jikinta yayi sanyi sosai, turo baki tayi tana kallonta tace "mom kingansa ko?"

"Ai yayimun daidai, don me zaki fad'i haka kuma meyasa kika fita baki sanar damu ba?, duk kinsa hankalin 'yan uwanki yatashi "cikin sanyi murya had'e da kallonta tun daga sama har k'asa mom taci gaba da cewa

"Basmah fad'amun daga ina kike? Kodai ciwon nakine ya tashi? Dakewa Basmah tayi don kar mom taganota jin yanda tayi saurin d'agota kafin tace

"Laa a'a mom, ko kad'an ni lafiya klw nake, ba me kika gani halan?"

"Ba komai am just asked, amma kada ki k'ara furta kalaman da kikayi yanzu, saboda sunyimun nauyi azuciya kinji ko?"

"Shikenan mom kiyi hak'uri nadena, dama nafad'i hakane saboda ganin yanda hankalinku yatashi don d'ai ba'a gane niba na mintoto"

"What ever dai" mom tafad'a tare da wucewarta zuwa part d'inta batare da tabi tankan Mahmud pilot dake tsaye yana latsar wayar saba, juyawa Basmah tayi itama zatabar wajen cikin sadar tauba santaka yace

"Ba wani can idan zaki fad'i gaskiya kifad'a, don natabbata zance kika fitayi, kwana biyar yau yarage, kawai kifad'awa dady yaturo iyayensa ahad'a da naki muhuta, inkuma kika tsaya kallon ruwa kwad'o yayi maki aski" yak'arasa maganar had'e daci gaba da dangwalar wayarsa. Gabanta ne yayi wani irin mugun fad'uwa jin kalaman da suka fito bakinsa, kaddai ace yaya Mahmud yagano tana son sa? Tirk'ashi! Innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun tafad'a cikin ranta kafin tabasar had'e da juyowa tana kallonsa cikin dakewa tana murmushi k'arfin hali tace

"Yaya kenan! Karka manta ni yanzu awani b'angaren auntyn kace, tsokanarka awajena bazatayi tasiri ba balle har tasa in aikata abunda banyi niyaba, kai kake batun aure agabanka ammani kuwa baya gabana domin nadad'e da zab'arwa kaina turbar karatu akansa, kuma kabi ahankali ko insa 'yar k'anwata tahukunta mani kai" dariya yayi don damashi tsokana tasa yafad'i hakan kafin yace

"Ahh, rufamun asiri ai hukuncinta bazai zomun da kyau ba, yihak'uri aunty Basmah tuba nakeyi kafin amaryata tajini"

"Ai kuwa kayi sake don duk abunda kafad'a akunne ya sauka, kabada girma ga auntyn mu inba haka ba sai nace nafasa..." Yaji Billy dake ida k'arasowa wajen ita da Batool tafad'a tare da rungume Basmah tana kallonsa tana dariya.

"Haba matar, kar muyi haka dake, indai girmane zan batashi fiye da girman dutsen uhudu" yak'arasa maganar yana rissina kansa agaban Basmah had'e da cewa "ayi hak'uri babbar aunty"

Dariya Batool tayi kafin tace "tab lalle yaya shine hadda wani rusunawa, Allah ya agajemu kada kazamo mijin tace duk da yake ina fatar Allah yasa kai da my twiny kumallake kanku da kanku"

"Saboda me kikace haka sister" Billy tafad'a tana kallonta

"Saboda ke dashi 'YAN UWANA NE, bana fatar wani abu da zai tarwatsa farincikinku agidan aurenku har yahanaku samun natsuwar mallake junanku ko kad'an"

To yanzu dai ba wannan ba, yayya ina kikaje munata nemanki mun had'a maki wani surprise amma babuki babu labarinki"

"Sorry kuyi hak'uri nad'an je wani wurine" tana gama fad'ar haka tajuya tare da nufar part d'in mom, bayanta suma sukabi suna lak'ame da juna abun gwanin ban sha'awa.

Cike da soyayya irinta 'yan uwantaka Mahmud pilot yabisu da kallo yana murmushi, don had'in kansu ba k'aramin burgesa yakeyiba, shidai ko azamanin da bai tab'a jin tarihin yanda 'yan uwa ke k'aunar juna kamar yanda sukeyi ba balle a yanzu da zumunci ya samu rauni, ajiyar zuciya yayi tare da folding hannayensa akan k'irjinsa har lokacin idanuwansa na akansu yace

"Allah yakareku da sharrin shaid'an da dukkanin abunda zai tarwatsa wannan zumunci naku mai cike da tsabtatacciyar soyayya"

juyowar da Billy zatayi ta kallesa saboda yanda jikinta yabata har yanzu yana tsaye wajen yasashi surin d'auke idanuwansa akansu had'e da barin wajen yana shafar k'eyar kansa fuskarsa d'auke da murmushi.

Suna isa Billy tasa hannuwa tarufewa Basmah idanu adaidai lokacin da take k'ok'arin shiga d'akinsu suna fad'in surprise yayya, murmushi Basmah tayi had'e da d'ora hannuwanta bisa na Billy data rufe mata idanuwa sannan tace

"Can't wait to cee it my sisterss.."tana dariya, saida suka shiga cikin d'akin sannan tabud'e mata idanuwan daidai saitin wasu akwatuna guda biyu da kit sky blue colour ank'awatasu da kalar yellow daga wajen kansu da tayun dake jikinsu, idan kagani zaka d'auka irin akwatunan nanne na k'ananan yara saboda yanda suka sha k'awa sukayi sosai, "wow who own dis" tafad'a tare da zaro idanuwa cike da mamaki,

"All is urs" suka fad'a tare da krik'ata suka k'arasa wajen akwatunan suna dariya

"Batool, Billy stop kidding me? don Allah waye da akwatunan nan gaskiya sun burgeni sosai"

"Allah yayya nakine" Batool tafad'a tana k'ok'arin fara bud'e akwatunan.

Hijab d'inta tacire ta zauna gefen gado tana cewa

"Lallaima yarannan kuyimun yaso da hankali tunda Kinga juna shirin tserewa kubarni"

"Kai yayya meye kuma nafad'ar haka? kika sanima ko tare za'a d'aura mana auren" Billy tafad'a cikin jin haushin abunda 'yar uwar tata tace, murmushi Basmah tayi had'e da cewa

"Hmm taya za'ayi haka bacin ni banida masoyi a hannu, idanma inada ai yayimun nisan da babu yanda za'ayi na auresa awannan lokacin kawai kidena wannan tunanin 'yar uwa domin kina rud'ar kanki ne" jin yanda Basmah ke magana yasa Batool matsowa taja hannunta tana fad'in

"Yayya zokiga kayannan, wlh ba kad'an dady ke jinki ba, d'azu ya aiki akiraki bayanan shine yakiramu yace mushigo maki dasu wai nacin bukine" kayane masu kayan gaske da tsada tun daga kan atamfa, shadda, lace, material, boyel, jikka, takalli, unders wears, sark'a, 'yan kunne, 'yan hannu, agogayye, zobuna, mayukka, mayafi kai komai dai dazata buk'ata abukin dady ya had'o mata sababbi gal acikin kwatunan, bud'e baki tayi tana bubbud'a kayan ahankali tana jinjinawa dady, "Allah sarki iyaye rahama, wato duk don tayi farinciki dady itama ya had'o mata wud'annan kayan na musamman tamkar wani lefe, hawayene suka zubo mata a idanuwa tsabar farinciki ta d'aga hannunta tace

"Ya Allah kaci gaba da tsawaita rayuwar mahaifinmu, yanda yake faranta mana shima Allah ya faranta masa" amin duk suka amsa tare d'agota daga duk'en da take agaban akwatunan suka nufi gaban wardrobe d'in dake cikin d'akin da ita, inda taka jera kayanta suka bud'e mata tare da ciro wata k'atuwar leda guda biyu suka mik'a mata "Yayya wannan kuma namune muka d'unka maki kici buki dasu"

Binsu tayi da kallo bayan takarb'i ledar nanma wasu kayanne sababbi d'unkakki masu kyau guda biyar Billy taciro kala uku acikin lefenta ita kuma Batool kala biyu da yaya Mahmud zaikai d'unkunan faraaha nabuki suka bashi sukace don Allah ad'unkowa yayya d'insu taci buki, sannan suka had'o mata kayan shade shafe da kwalliya da turarukka suma kusan leda d'aya, ganin haka yasa yaya Mahmud shima yace baza'a barshi abaya ba tahad'o mata set d'in mayafi da takalma da jikka masu kyau dake shiga cikin kayan da zai kawo bayan and'unkikke ya gamo mata dasu, har ga Allah wannan abun yamatuk'ar k'ara mata k'aunar 'yan uwanta sai takeji inama ace bazasu tab'a rabuwa dasu ba har abada suna tare amma ina koda ace aure bai rabasu ba dole muguwa zata rabasu, ahankali tabud'e baki farinciki kwance a fuskarta tace "Me zance daku 'yan uwana?"

"Kar kice komai yayya domin duka kinfi k'arfin wud'annan abubuwan" rungumesu tayi idanuwanta nazubar da hawaye tuna ciwon da take ciki ba lallene yabata tarayu da 'yan uwanta ba koda kuwa kowacensu na gidan aurenta, k'ank'amesu tayi sosai tana fidda kuka mai sauti kafin tace

"Ina matuk'ar k'aunarku 'yan uwana, bazan manta da halacci da soyayyarku agareni ba, ngd ngd sosai Allah ya sanya albarka acikin aurenku kuma yazaunar daku lpy da mazajenku tare da zuria masu albarka" gaba d'aya Batool da Billy saida jikinsu yayi sanyi saboda yanda sukaji tana kuka, tabbas da ace iyayinsu zasu amince dasu da bazasuyi wannan aurenba har sai lokacin da 'yar uwarsu itama tasamu miji a had'asu tare ayi masu, amma sun sani hakan abune marar yuyuwa, rarrashinta suka shigayi cikin tausayawa suna masu fatar itama Allah yakawo mata miji nagari wanda zai kula masu da ita sosai.

Duk wani shire shire da yakamata ayi agidan amaren tuni angama don tuni dady yasa angama jere gidajen amare da kayan d'aki na musamman kuma naji da fad'a, haka kuma da kansa yaje har gidan Batool yasa aka canzawa mamy kayan d'aki masu kyau bayan angyarawa Batool nata wanda hakan yamatuk'ar sanya dr Ahmad farinciki tare da k'arawa mahaifin Batool da ita kima acikin zuciyarsa, a b'angaren faraahama, bayan angama jera mata kayan da iyayenta suka yimata yasa aka sake sauke motar wasu kayan d'aki masu kyau da tsada yabasu a hannunsu yace ajere mata cikin d'ayan d'akin mallakintane duniya da lahira yabata amatsayin kyauta da tukuicin da zai bata nashigowa cikin ahalinsa da tayi, 'yan uwanta kuwa sunyi matuk'ar farinciki da murna tare da yimasa addu'a Allah yasaka da alkhairi, tsabar farinciki jaddi kam da kansa yaje yayiwa dady godiya hadda 'yan k'wallansa, dady yace ai ba komai, shiya kamata ace yayi godiya da 'yarsu tayadda kuma ta amice tana son d'ansa kuma tana k'aunarsa har tayadda zata auresa, hakama acan borno gidan Billy duk abunda dady yasa aka sakawa Batool shi aka sakawa Billy daidai da spoon babu inda ya banbanta inba ga colours ba, komai yaji ya zauna daram yanda ake buk'ata abun sai wanda yagani masha Allah don duk wanda yashiga cikin gidajen to tabbas zaisan cewa tabbas 'ya'yan mai furniture's ne fad'in malam bahaushe yace 'mai abu da abunsa" yanda dady yaje yazubo gidan Batool da Ahmad haka yayi tattaka narana d'aya shida mahmud pilot da yaya mahmud sukaje har borno batare da yaji wata kunyaba ko duba alak'arsa da iyayen mahmud pilot ya dubo gidan Billy, kuma Alhamdulillah yaji dad'in yanda yaga antsara komai yanda yakamata tamkar na 'yar uwarta, babu wani banbanci inba girma da yalwar wajeba da gidan Billy yafi na Batool kuma shima nan take yayi addu'a Allah yabud'awa dr Ahmad shima ya mallaki isasshen muhalli da zasu rayu cikin farinciki shida mahaifiyarsa da kuma matarsa haka kuma bai baro garinba saida yazubewa Umma dubu d'ari da ashirin yace tak'ara tayi hidima, duk da Umma tagama hidimar komai hakan bai hana takarb'i kud'inba tayi godiya tare da addu'ar Allah yabar zumuncinsu don tasan idan taki karb'a bazai ji dad'i ba. Sanarwa kuwa ba'a magana ko ina tuni gari ya d'auka, gidan redio da kafafen yad'a labari cewa 'ya'yan Alhaji Bashar mai furniture's zasuyi aure, musamman dady yasa akayo manya manyan symbol d'auke da invitation d'in auren 'ya'yansa yasa aka kafa amanya manyan titunan garin don gayyatar mutane zuwa taron d'aurin auren, za'ayi safiyar yau da zasu fara program d'insune dady yakira iyalansa ya sheda masu cewa tabbas dolene suma sushiga cikin 'yan uwansu kafin suyi aure kuma yayi maau nasiha akan surik'esu hannu biyu koda suzasu walak'an tasu don yagaji da jiran ranar da 'yan uwansa zasu wai wayarsa kuma yabasu hak'uri akan suyi masa afuwa akan laifinsa narashin nad'azu da 'yan uwansa sai yanzu saboda babu yanda zaiyine , ako da yaushe zaman jiran su waiwayesa yakeyi amma sunk'i shikuma ganin shiyake akan daidai kuma bisa gaskiyarsa yasa yak'yalesu har sai sun fahimci hakan wanda ayanzu yagani cewa haka dayayi laifine kuma ya tafka kuskure babba, nan yasake sanar dasu cewa bridal shower d'in da zasuyi yau wanda a invitation akasa za'ayi sa agidan papi to anfasa su shirya zuwa anjima da kansa zai kaisu family house d'insu dake can anguwar nasarawa inda yayunsa alhaji kabir da alhaji bukar da kuma k'anensa muzammil ke zaune acan za'ayi, don haka sukira k'awayensu da mak'wabtan da zasuje su shaida masu duka suzo nan gida za'a kawo motocin da zasu kaisu wajen da za'ayi bridal shower d'in.

Sosai kowa yaji dad'i da farincikin wannan matakin da dady ya yanke duk da cewa bai fad'a masu dalilin yanke alak'arsa da rabuwarsa da 'yan uwansa ba bayan anagari d'aya saboda suma yau zasu had'u da 'yan uwansu da suka dad'e suna alayin ganinsu.


Lokacinne yana sallamarsu Basmah tanufi asibiti shi kuma bayan fitarta ya aika kiranta don yabata surprise d'in kayan da ranar da tazab'awa su Batool kayan d'aki yace zai bata batanan, shine dalilin da yasa yakira su Billy yace su kwaso su kawo mata kafin tadawo, nan takira dady a waya tayi masa godiya sannan takira yaya mahmud shima tayi masa godiya, sannan suka tashi sukaci gaba da shire shiryen zuwa bridal shower a inda basu san da wace fuska za'a kallesu ba duk da sudai cikin farinciki suke zasuga 'yan uwansu.

Dady nafita yaje wata hotel shida yaya mahmud yasaye abinci mai yawa sannan suka biya wani hole yanemi da abashi k'wararrin decoraters da masu k'ayatar da waje da kid'a, daga nan suka wuce sky crown yayi oder d'in snacks kala kala, dama andad'e da bugo kayan printing wanda aka rubutawa _THANKS FOR COMMING OUR BRIDAL SHOWER_ kad'ai batare da ansa sunayen angwaye da amareba yabiyasu aka sassanya masu komai cikin manyan jikkunan da akayi suma dai hakanan aka rubuta masu, suna gama had'a masa suka wuce kai tsaye family house d'in su dady tare da mutane da aka d'auko da motar kayayyakin da za'a gyara waje dasu da komai da komai, suna isa babban ya'yanah daya d'an manyanta sosai donma akwai d'an rufin asiri yana k'ofar gida zaune shida k'anensa muzammil, kasancewar bayan wasu 'yan lokutta yana zuwa gidan ya duba part d'insa amma basa kulashi ko kad'an yasa suna ganinsa suka d'auke kai, wanda shi yayansa tuni yadad'e da yin nadama akan abunda yafaru tsakaninsu kawai kunya ce tasa yakasa bari suhad'a idanuwa dashi, murmushi dady yayi tare daba Mahmud umurni daya shiga ciki da masu gyaran sannan shi kuma yanufi wajensu zuciyarsa na bugun uku uku na rashin sanin ko zasu iya daidai tawa tsakaninsa da su...


_Mukama anjima in sha Allah luv u all❀, dafatar nagoge laifin_πŸ™ˆπŸ˜…




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*
[9/18, 7:35 PM] Teema Gabsss: πŸ‘­β€ *'YAN UWANA NE!*β€πŸ‘­
πŸ’Ž _they're my relatives..!_πŸ’Ž


Written by: *BILLY S FARIπŸ’Ž*

Dedicated to: *FATIMA TAMBARY*

Bestowed to: *BILLYN ABDUL AND AUNTY MAIJIDDA MUSA*

_A SHORT AND TRUE LIFE STORY OF THE YEAR 2019_


πŸ’ŽPage_____79πŸ’Ž


Har Yaya Mahmoud ya wuce sai kuma ya dawo yanufi inda suke had'e da gaishesu cikin girmamawa, alhaji Kabiru ne kad'i ya amsa Masa cikin sakin fuska shikuwa muzammil hangosa da yayi tare da dady yasa yai tamkar bai jisaba ballema har yasa ran zai tanka masa, murmushi Yaya Mahmoud yai duk da yaji Babu dad'i aransa tare da kallon dady dake k'ok'arin isowa wajen sannan yawuce zuwa cikin gidan, dady na isowa wajen yayi sallama tare da mik'awa alhaji Kabir hannu suka gaisa fuskarsa ba yabo ba fallasa sannn yajuyar da kansa gefe, wata uwar harara muzammil yabi dady da ita tare da mik'ewa tsaye yana fad'in "To yaya ni zan wuce sai anjima"

"In kuma zakaje muna magana muzammil halan bakaga d'an uwan kabane" batare day kalli gefen da dady yake zaune ba yace "aini banida wasu 'yan uwa aduniya idan bakai da Yaya bukar ba" ya k'arasa maganar yana k'ok'arin sanya takalmansa yabar wajen,

"Dawo kazauna muzammil" alhaji kabiru yafad'a cikin sanyin murya don dama shi yadad'e yana jiran wannan ranar tazo saboda tuni yayi nadamar abunda suka aikata ga d'an uwan nasu akan abunda shi yake da mallakinsa ba suba, dole tasa muzammil yadawo ya zauna tare da juyawa dady baya yana faman kumburar fuska, russunar da kai dady yayi had'e da cewa alhaji Kabiru

"Ina wuni yaya? barka da rana" zucuyarsa na bugun uku uku saboda ganin yanda yayan nasa yad'aure fuska fiye da yanda yake yimasa aduk lokacin da yazo gidan don karya samu damar yimasa magana, banbancin kawai shine yanda ya amsa masa kamar babu komai aransa don kuwa baimayi tsammanin ko kulasa yayiba balle yasa ran zai amsa masa.

"Lafiya lau alhamdulillah bashar, Ina dai ko lafiya?"

Shiru dady yayi yana tunanin ta inda zai soma basu hak'uri bisa kuskuren da shima yayi duk da kasancewar yanada gaskiya da kuma hujja, ganin shirun yayi yawa yasa muzammil kallon alhaji Kabiru yace

"Nifa yaya inada abunyi, bazai yuyu inzauna asani agaba ana kalloba don tak'amar mutum yanada arzik'i, gaskiya bazan iyaba ai wannan renin wayone da wulak'anci tunda mutum ba aji..." Katsesa alhaji Kabiru yayi kafin ya ida maganarsa ta hanyar cewa

"Anya muzammil kanada hankali?, to maza ka kamamun bakinka kafin nasab'a maka, kar ka kuskura insake jin bakinka kace wani abun inba so kakeyi inb'ata maka rai ba ko kamanta cewa shi yayan kane kuma d'an uwanka"

"A'a Yaya kabarni inyi magana, nidai duk duniya nasan banida want d'an uwa idan bakai da yaya bukar ba don haka kadena kiransa amatsayin yayanah don babu ruwan hanyar jirgi da mota"

"Muzammil ni kake fad'awa haka, kaifa k'anena ne kuma jinina, don me zaka furta wannan kalmar mai tsananin zafi azuciyata" dady yafad'a idanuwansa cike da k'walla, cikin b'acin rai muzammil ya juyo yana kallonsa don dama yafi kowa cikinsu bak'ar zuciya da hasala yace

"Kai malam dakatamun da d'an uwana da yasan muhimmancina da kuma darajata nake magana bakaiba, don haka karik'e mutuncinka kafin kanemesa karasa"

"Muzammil kamamun bakinka kana jina ko" alhaji Kabiru yafad'a tare da nunasa da d'an yatsa, sannan ya maido kallonsa ga dady yace

"Injindai ko lafiya alhaji Bashar, Ina ce dai bawata matsalace ba, don shekaranjiya naga yara sun soma shiga gefenka to gudun kar suyi maka b'arna kasan halin yara yasa nasa akaja katanga a tsakaninmu" jin haka ya k'arfafawa dady tunkarar yayan nasa had'e da durk'usawa agabansa yana fad'in

"Don allah yaya kuyi mani aikin gafara bisa kuskuren danayi, nasan ni mai laifine agareku bisa bijire maku da nayi nafifita ra'ayina akan zama tare daku, natuba Yaya don allah kuyafeni" wata uwar harara muzammil yabisa da ita tak'asan ido tare da komawa gefe can nesa dasu kad'an,

"Haba Bashar ai bakayi kuskureba, mune nan da laifi, muda muka nemi rabuwa dakai bisa gaskiyarka akan abunda bamuda iko dashi, mun manta cewa Allah shi yake bayarwa kuma shiyake amsa, kai kuma saika biye ma zuciyarka ka k'ullacemu arai, don haka kai zamuba hak'uri tunda har ka iya yafemu kamanta da alak'ar dake tsakaninmu ta 'yan uwan taka"

"A'a Yaya kada kafad'i haka kamanta da kanku kuka koreni akan matuk'ar bazanbi umurnin kuba kun yafeni kuma bakwa buk'atar ganina, Yaya anan wajen katuro k'eyata nida matata kana fad'in kar insake in sake nuna cewa nasanku koda akan hanya ne domin ka dad'e da yanke duk wata alak'a dake tsakaninmu bakwa buk'atata dani har ahalina acikinku" ya k'arasa maganar yana nuna gefen gate d'in gidan, goge hawayen idonsa yayi tunowa da wannan ranar kafin yaci gaba da cewa

"To kafad'a mun Yaya tunda Ina son matata, Ina so narayu da ita don me zuciyata bazatafi k'arfina ba nayi nesa daku kuma na sanya tsakani tsakanin ahalina da naku tunda haka kuka buk'ata bayan abunda kuke zargi da jifar matata dashi ba hakan bane, batun na

Please Login or Register in order to submit comment