Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazan karya wannan alk'awari danayi ba, tun ranar da aka haifesu nayi masu hud'uba da sunan FARHAAN DA FARAAHA koba komai macen sunan mom gareta da nauyi mudinga kiranta da sunan shiyasa nayi masu kinaya da wud'an nan sunayen, ina fatar Allah yayi masu albarka" speechless faraaha tazama jin tasamu takwara, kasa bayyana zallar farincikinta tayi saidai ta anshi babyn tare da zuwa kusa ga Batool dake kallonta tana dariya ta rungomota ajiki tace

"Thnk you sister da kika haifa mun takwarata, ngd sosai Allah yak'ara maki lafiya kuma yaraya mana farhaan da faraaha"

Kallon dr tayi shima tayi masa godiya sosai da karamcin daya yimata,

Mahmud kuwa bai bari Billy tazo ba sai ana gobe suna, tayi tunzure tunzurenta da fushi har tagaji tahak'ura tadena,

Dr Ahmad kam anyi hidima sosai kuma ya nuna bajintarsa da godiya akan ni'imar da Allah yayi masa, yayi masu kayan barka masu kyau da tsada sannan ranar suna aka yanka raguna manya manya guda biyu da sa, musamman faraaha tahad'owa twince da mamansu akwati biyu don nuna yabawarta ga takwarar da akayi mata,

Ranar suna maijego da yaranta sunsha kyau sosai kamar basu ba, haka kuma dr yasa aka had'a walima ta musamman da marece sannan kowa ya watse ana yiwa babys addu'a tare da fatar alkhairi, Billy na hango tsaye da aunty fareeda tana bata hak'urin rashin gayyatarta aureta da batayi ba ita kuma tana cewa

"Ai wlh abun yayimun zafi, ace bikinki ko gayyata babu, ainazata saboda bakya son in more shiyasa"

Dariya Billy tayi kafin tace "haba tuba nakeyi, yanzu haka kinga nakusa juye maku na ukku insha Allah zan kiraki, kodon ki kula mani da naman suna kada su aunty meamah da zainab pinki dasu Nana hauwa'u su wawushe" tsalle aunty fareeda tayi tare da gyara jikkarta dake d'an k'are da naman sunan twince sannan tace

"Kai Allah dai yabarki da pilot d'inki, ai wlh shiyasa nake mugun sonki, Allahu Akbar Allah yajik'an 'yar uwarki yayya Basmah" muryar little Basmah dake sak data yayya Basmah aunty fareeda tajuyo abayanta tana fad'in

"Laa banfa mutu ba aunty fareeda kidena yimun fatar mutuwa mana" arazane aunty fareeda tajuyo had'e da cewa

"Nashiga uku ni fareeda daga addu'a?"

Both Ummie da kubra dake tsaye gefe suna jiranta da Billy suka kwashe da dariya, dafa kafad'ar aunty fareeda Billy tayi da sauri tajuyo idanuwanta awaje Billy tace

"Kai aunty fareeda kwantar da hankalinki, little Basmah ce, kinsa gaba d'aya babu ta inda tabaro yayya, wannan kuma 'yatace little Billy" tak'are maganar tare da jawo hannun Billy dake tsaye tana kallonta fuskarta d'auke da murmushi,

"Eh nagani itama sak babu ta inda tabaroki, to nikam sai da safe Allah yaraya maku yaranku kuma yashirya maku su" aunty fareeda tafad'a tare da wucewa tanayi tana wawayen Basmah da take ganin kamar yayya Basmah ce data dawo.

Da safe Billy na zaune rungume da farhaan ita kuma Batool rungume da faraaha ta k'walawa Basmah kira, fitowa tayi aguje Ummi nashigowa tazo duba ya 'yan biyu suka tashi da kad'an ta bugeta,

Kallonta Ummi tayi had'e da cewa

"Oh ni Basmah Allah ya shirya mani ke, baza dai kidena wannan gujegujenba ko? Bari Bilal yazo shine maganinki zansa yakoya maki hankali"

"Kai Ummi aunty Billy cefa takirani shine nayo sauri kisan maau ciki da saurin hasala"

"Mtss Dallah rufamun baki jeki"

Kusan tare suka isa wajen Billy nadaria tace

"Wlh little Basmah bakida dama, ke kuma ahaka halinki yazo, mudai yayyammu ba haka takeba Allah yajik'an rai"

"Amin ummi tafad'a tare da amsar farhaan ahannun Billy tana fad'in "morning my fresh sweetheart" duk suka kwashe da dariya, ita kuma Basmah data b'ata rai don ance bahaka yayya take ba cikin k'unk'uni tace

"Amma dai ai komai bamu d'ayane harma da muryarmu"

"Eh naji, don Allah jeki ki toyamun wainar fulawa" Billy tafad'a tana dariya

Haka little Basmah tashige kitchen tana k'unk'uni gashi dai bata wani iya wainar fulawa ba saboda ummi bata sonta shiyasa bata tab'a gada yintaba balle takoya, ganin yanzu aka gama yimata sheri yasa takasa fad'ar bata iyaba don haka tayi tsaye tana tunanin ta ina zata fara, tunowa tayi da taga sauran wainar da akayi jiya tabuki data rage mom tasa a fridge don tanaso yau taci,

Da sauri ta kunan gas nad'ora faranfam awuta ta zuba mai aciki sannan ta bud'e fridge d'in taciro k'waya uku har tana fad'in wannan "wainar zata isheta tunda manya ce, bari na raba biyu" nan ta d'auko fulawa ta tankad'a sanan ta d'ebo ruwa ta ajiye agefenta, tana fad'in "banda abun aunty Billy wai wainar fulawa taya za'ayi ta toyu ba'a saka wainar aruwaba kafin asamu fulawar tazauna ajikin wainar" tsunbula duk yankan wainar data d'oko ta dingayi sannan tasaka cikin fulawar ta birkideta saita jefa cikin ruwan mai, haka ta dingayi har saida tak'arar da yankan wainar, little Billy ce tashigo kitchen d'in had'e da cewa

"Momcy" don haka take kiranta, mekike soya mana haka!" tare da d'okar yankan wainar da ya soyu da fulawar tana jujjuyawa

"Bari kawai doty aunty Billy ce tace in toya mata wainar fulawa da sanyin safiyarnan, don ma Allah yataimaka mom ta ajiye sauran tajiya a fridge ai data wahalar dani" zaro idanuwa little Billy tayi had'e da cewa "what momcy? Wainar fulawa ahaka?" Kafin takwashe da dariya tanufi inda suke tana cigaba da dariya had'e da rike ciki tana fadin "mommah..mommah" takasa iyarwa saboda dariyar dataci k'arfinta,

Little Basmah kuwa ko ajikinta ta d'auko plate d'in tanufo falo dashi, mik'awa Billy tana fad'in

"Gashi Aunty Billy" ta nad'awa little Billy da har yanzu takasa dena dariya duka abaya "kekam kinshiga uku da muguwar dariya.

Ai kafin tarufe baki taji Billy data tsurawa plate d'in ido sannan takalli Batool itama ta kalleta suma sun fashe da dariya.

Saida sukayi mai isarsu sannan sukace atare " yayya Basmah delious returned" saboda tunowa da ferfesun kaifin da yayya Basmah tayi tare da kunun gid'a.

Cikin dariya Batool tace "kai gaskiya Basmah kin biyani yanzu twiny zata fahimci cewa dake da yayya Basmah abu d'ayane babu banbanci"

Ummi kuwa kunya ce tarufeta, tafahimci cewa tayi kuskure, bai kamata ace don uwa batacin abuba tace bazata koyawa 'yarta shiba saboda batasan wataran inda rana zata fad'iba.

Kallon Billy little Basmah tayi data kasa tayarda dariyarta kafin tace

"Kufa 'YAN UWANA NE..amma kuka azamun wannan dariyar, shikenan dama ai nasan bakwa sona yaya mahmud da yaya Bassam kad'ai ke sona idan suka dawo zanfad'a masu" tamik'e zatabar palourn da sauri Billy tarik'ota had'e da jawota ta zaunar da ita tsakiyarta da Batool suka rungumeta atare sannan sukace

"Sorry Basmah muma muna sonki sosai fiye da tunaninki"

_ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ANAN NAKAWO K'ARSHEN WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA *'YAN UWANA NE*, INA GODIYA GA ALLAH DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI LAFIYA, INA FATAR DANI DAKU ALLAH YA YAFE MANA KURAKURAN DA MUKA AIKATA KUMA YASA MUYI CU'DANYA ACIKIN LADAR DA MUKA SAMU ACIKI YABAMU IKON AMFANA DA DARUSSAN DAKE CIKI, INA GAISUWA TARE DA FATAN ALKHAIRIN ALLAH GA DUKKANIN MASOYANA BISA HAK'URI, JURIYA DA KUMA JAJIRCEWARSU HAR ZUWA WANNAN LOKACI DA MUKA KAMMALA WANNAN LITTAFI LAFIYA, NAGODE DA ADDU'O'INKU DA KUKEYI AGARENI DA KUMA MAHAIFINA, YA ALLAH KAJIK'AN ABBIENA DA KULLUHIM MUSULMI BAKI 'DAYA, ALLAH YA HASKAKA ROUHINKA YA YALWATA KABARINKA,😭 MASOYANA KU *'YAN UWANA NE* A MUSULUNCE KUMA INA ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE DOMIN DUK WATA NASARAR DANA SAMU ARAYUWA TA DALILIN KUNE, KUMA INA ROK'ON WANDA DUK NA 'BATA MASA RAI YAYIN RUBUTA WANNAN LITTAFI DAYA YAFEMUN SABODA HALIN RAYUWA, NAGODE SOSAI 'YAN UWA SAI KUNJINI A SABON LITTAFINAN A SHEKARAR 2020 MAI SUNA........πŸ˜œπŸ˜‡IN SHA ALLAH 🀝 *MISSED U AND LUV YO ALL FILLAH*β€πŸ’žπŸ’‹_

_Comment d'inku shizai tabbatar mun da kun nishad'antu, kun ilmantu, kuma kun amfana da darussan dake cikin wannan littafi, hakan kuma zai bani k'warin guiwar cigaba da rubuta maku sabon littafina mai suna........πŸ˜‰_ asha

*karatu laafiyaaa*




*_ALLAH KA JIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_*





An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment