Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

BARIKI GADO NAH Complete Hausa Novel Document by BARIKI GADO NAH


BARIKI GADO NAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17191



BARIKI GADO NAH

Reading Time: 1 Hours

Added On: 19, Aug 2024

Author: Oum Aphnan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09065990265

Book License : Free

Category: Romance 18+ Novels

File Size: 95.87 kb

File Type: txt

Views: 1953+

Download: 1418+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [5/31, 22:11] 😘😘😘: *💙🤍BARIKI🤍💙*
_(Gado nah)_
Book 1
Page 1&2

Oum Aphnan✍️
Bismillah!

_Gargaɗi_
Ban taɓa zagi akan littafi ba ,Amma bana duk wacce ta karanta mun littafi bata biya ba ,ko aka ɗaura mun Littafi a wani shafukan sada zumunta ko utube mutum shi da Allah. Don haka in kinsan zaki siyane don ki ba ƙawarki kawai na hutar dake karki siya,haƙƙin mallaka nane naki karantawa.


_Paid Book_
Regular 300#, Vip 500# , Special 1000# via Hassana Mohammad 7782217014,Fcmb or wxp dix Number 09065990265


_Laraba,2pm._

"Malam kaiwa darajar tsohuwar ka ,yau dai ka barni in shiga Dan girman Allah!,makona uku kenan ina sintiri ka hanani shiga"
Wata wahalalliyar mata da a ɗebe zamu bata shekaru 25 da haihuwa amma tsabagen wuya,duba da yanda bakinta ya bushe ya tsage yina fidda jini ta tsakiyan leɓenta na ƙasa,ga hijabinta tamkar anci wasar sallah akai,ƙafarta sai kace wacce ta kewaye Nigeria da ƙafa,ya daddare da faso gashi yayi buɗuɗu, Kallon Farko sai an bata shekaru Arba'in . Haka ta manne a jikin ƙarafunan get ɗin ta kakkama tana cigaba da roƙon sikyuritin dake jingine da get ɗin wajen ,saidai tamkar baisan tana magana ba ,sai latsa baby Nokiar wayarsa yike . Alamu dai ya nuna inda sabo ya saba da Nacinta

Sarewa da roƙonsa tayi ,don haka taja wata doguwar Ajiyar zuciya ,saiga hawaye masu raɗaɗin fita suna gangaro mata a dakalin kuncinta

"Ya Allah,Ya Sarkin da kayi talaka kayi mawadaci ,kayi mugu kayi wanda ake zalunta Ubangiji na,ka kawo mun wanda zai tausaya mun ,ya dubi rauni na ya Rabbb" wani shasheƙane ya sarƙeta maganar ya daina fita kawai sai ta haukace da tarin Azaba saboda yanda numfashinta ke barazanar ɗaukewa a ƙirjinta.


Alhaji Saddam Mamman Tamkar wanda aka tsikara ya kalli agogon dake manne a katafaren office ɗinsa, zumbur ya miƙe ganin lokacin azuhur ya shiga ,yina fitowa daga ofishin sa kuwa ma'aikata dake dakon jiransa ,suka dafe masa baya ɗuuuu sukayo waje ,zasu nufi masallacin dake ta bayan wajen .

Har zuwa lokacin bata fasa tari ba ,ga idanuwarta sun duddulo waje sun jajir tsabagen Azaba .

Alhaji Saddam dakatawa da tafiya yayi sannan ya ƙwalawa securityn kira

"Malam Tukur!"

Zumbur yayi ,sannan ya yi saurin jefa wayar a aljihu ,ya amsa a furgice ,sannan ya waigo inda take yana mata alamar gargaɗi da yatsa.

"Dakata!,meke faruwa ne anan wajen?"
Sunkuyar dakai yayi ,ya ɗanyi gungunan maganar da baza'a taɓa fahimta ba

"Shikenan ban son jin komai a buɗe mata ta shigo"
Ji yayi kamar kar yabi umurninsa amma ya ya iya?

Buɗe mata get ɗin yayi ,aikuwa cikin bala'in gudu ta shigo harabar tana cigaba da tarin taje ta zube a gabansa
"Yallaɓai kayi mun rai ka ceceni kasheni zai yi ,kwanakin mutuwa na a ƙiddidige yike yau saura kwana biyar!!!"

A mamakance ya ɗan kalli gabansa da ta turmusu, ya ɗan tattare giran sama da ƙasa

"Baiwar Allah tashi tsaye ,ban fahimceki ba ,waye zai kashe ki ɗin"

"Mijina ne yallaɓai, mijina ne "
"Mijin ki?!" Ya tambaya a mamakance
"Eh,wallahi da gaske nike ku taimaka mun,Allah shine mai hukunci ,amma kuna taimako,ku taimaka mun kune ƙarshen fatana ,idan kuma baku taimakeni ba,to zan haƙura zan koma maƙabarta da kwana har zuwa ranar mutuwata don nasan tsimayinta nike!"

Kallon wani ɗan sanda dake gefensa yayi "A bata ruwa da Abinci ta natsu muna dawowa daga sallah"

Yina gama bada umurnin ya ɗauki hanyar masallacin ,ya daɗe rabon da yaci karo da irin mutanen nan ko don yakai ƙololuwa ne oho!

****
Bayan minti Arba'in

Tananan zaune yasa aka kirawo ta ,jikinta ko na azaban rawa ta bi bayan massenger Alƙalin

"Baiwar Allah meye kuken ki?"
Hawaye ne ya cigaba da mata Ambaliya a fuska ,da ƙyar take basa bayani cikin azaban raunin ta ,tsam da rai yayi ,kafin ya umurci massenger ɗinsa da ya kira wanda zai rubuta ƙaran ,sai a kai ma mijin nata sammacin kotu

"Baiwar Allah meye sunan wanda ake ƙaran?"
Shiru tayi ,ta ƙi magana

"Malama ,faɗi sunan mijin naki" cikin sadaƙarwa da raunin murya tace

"Alhaji Sallau Achisu ,Inkiya MAYE!"

Ai bata rufe baki ba ,fuskokin kowa na ofishin ya sauya.,mai rubuta ƙarar a hanzarce ya kekketa takardan Hannunsa
"Wannan matsalar ku ce ta cikin gida Malama ,bazaki tsoma rayukan mutane da yawa a watangariri ba ,tashi ki fita!!" Ya daka mata wani mugun tsawa ,wanda saida taji kamar zata tsullo fitsari a wando

"Me yasa zaka koreta ehem muntari?,A taƙaice ma me ta faɗa da zafi daya tunzura ka?"

"Ranka shi daɗe ,MAYE fa kaji ta ce shine mijinta? Maye fa ,mutumin da ko tsuntsu ya gifta ta inuwar garden ɗinsa kwanansa ya ƙare ......yallaɓai case ɗin matar nan sanannen case ne da ta saba zaga kotuna da ofisoshin ƴan sanda da dama a ƙasar nan kuma kokenta ɗaya shine Su raba mata AURENTA da maye......Amma saidai duk mutumin da ya karɓi ƙarar a ranar baya kwanan duniya !! ,Nikuma a gaskiya ban shirya maida yarana marayu ba ,Matana bazawarai!!..."

Tsam ta miƙe jiri da hajijiya na kwasarta ,a ranta tana Ayyana nan ɗinma babu Nasara,har ta fice ta nufi harabar kotun ,sam bata damu da Muryar dattijon da yaso taimakonta ba dake faman ƙwalla kiran "Baiwar Allah"

A daf da get taja ta tsaya saboda get ɗin da aka kware ma wata ƙatuwar mota ƙirar prado Baƙa da baƙar tint,cak ta tsaya tana jiran su shige ta fice

"BEEEE!!" Wani zabura tayi ta fara waige² tana son ganin ta inda zata mutum ɗaya jal a duniya dake kiranta da Wagga suna

A hankali aka buɗe murfin motar ,wani Ingarman namiji ne ya fito ma'abocin choco skin cikin Black suit da sukayi bala'in kwanciya a jikinsa

Cikin Izzah wanda ya gama bin jinin jikinsa ya ja ya kwanta a jikin motar sannan yasa hannu ya ɗage baƙar shade ɗin da ya sakaye ƙwarar idonsa

Cikin dakuwar bugun zuciya ta nuna shi da yatsa
"SARKI ! .... " Kawai sai hannunta ya fara rawa

Ko a jikinsa da halin da yaga ta shiga saima hannunsa daya nitsa a cikin sumar kansa ,cikin lallausar muryarsa yace

"Na'am MAKAMA TA!...Zo nan "

Kallon kanta tayi tun daga sama har ƙasa ,bata taɓa zaton sak ta zama bata da banbanci da mahaukaciya ba sai yau,ina ita ina raɓar Sadiq a haka? ,aikuwa da sauri ta ciɓa ƙafarta tayi waje harda ƙarawa da gudu da sassarfa


"Ku bita kar ku bari ta ɓace" yina bawa yaransa umurni ya danna kai cikin kotun ransa na azalzalarsa

"Me ya kawo ta ?me take so?"
Tambayar da ya soma jifansu dashi kenan ,cikin rawar murya suka labarta masa mai ya faru da tarikhin waye shi mijin nata

Da ƙarfi ya dunƙule hannu ya daki tebur ɗin gaban alƙalin wanda yasa printer ɗin dake kai yayi tsalle ya faɗi gefe ya farfashe

"Zanci uwarka maye ,Sai na raba auren dan uwarka ,yau ina so in bar duniyar"

Abokinsa Yusuf fagachi da sauri ya zo ya dafa kafaɗarsa "Allah ya huci zuciyar yareeman mu,a bi sannu yallaɓai"

A zafafe ya juyo ya watsa masa Idanuwarsa da suka rine suka zama jajaye nan take

"Ina wasa da kaine Yusuf?"
Shiru yayi sannan ya sunkuyar dakai don ba ƙaramar aikin Prince Sadiq bane yanzu ya tsinke sa da mari batareda ya duba abokantakarsu ba.

"Allah ya huci zuciyar yareema" fuuu ya fice ,wanda suka zo tare suka dafe masa baya


Shikuma Yusuf fagachi lafewa yayi a jikin mota ya kwaɗawa Gimbiya Ramlah kira a waya

Ramlah da tashinta a barcin kenan tun da tayi break fast ko kayan barci bata cireba,wani mugun miƙa tayi ta saki Hamma ,sannan ta ɗan jawo wayar ta saki tsaki gamida ɓata fuska

Muryarta can ƙasa a dushe "Fagachi yadai? Ina mijina yike?"

Ɗan jan fasali yayi ,kana ya magantu


"Ranki shi daɗe ,ina tunanin yaufa akwai ƙura ,koda sarki ya dawo ki lallaɓasa don kafiyarsa da taurin kansa da ya sassauto shekarun baya da suka wuce ,to ina ganin ya dawo ,mutum na haiƙe masa yina iya fyarɗe sa,murus mutum zai shaiƙa barzahu "

Zare ido tayi sannan ta dafe ƙirjinta da sauri kamar yina tsaye yina kallonta

"Yusuf? Kana haukane ? Yariman kake jifa da miyagun zantuttukan nan? Ni ban auri ɗan ta'addaba kar ka sake kiran min miji da siffofin nan,wani shashanci kenan ,kar kayi tunanin don yarimana ya kasance abokinka bazai iya maganinka ba..."

"Ki dakata ki saurareni " ya faɗa a daidai sanda yike shiga motarsu

Tsaki taja ta kasha wayar tana cigaba da ƙunƙuni ,kafin ta fara ƙwallawa kuyangarta kira .

******
Yareema kam tun da ya shige mota ya manne fuskarsa da baƙar shade ɗinsa bai ƙara tamka kowa ba ,tunanin sa ya tafi wajen tuna Abubuwan da suka faffaru a baya ,har abada bai taɓa tunanin Bilqees zata tsinci kanta a kwatankwacin irin wannan Rayuwar ba.

Haɗe Hannuwarsa yayi waje ɗaya ya matsa da ƙarfi sukayi ƙara
"Ni na ja maki
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download BARIKI GADO NAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album