Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

SHALELEN ALHAZAWA Book 1 Complete Hausa Novel Document by SHALELEN ALHAZAWA Book 1


SHALELEN ALHAZAWA Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 47263



SHALELEN ALHAZAWA Book 1

Reading Time: 3 Hours

Added On: 30, Jun 2024

Author: Asmeetar Haidar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : +2348168210896

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 240.5 kb

File Type: txt

Views: 582+

Download: 496+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: *SHALELEN ALHAZAWA*

*Writing and story*

*By*

*Asmeetar Hydar*


(Asma'u Ayuba)


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


*BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM*

*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad s a w, yau ma kamar kullum na ƙara kawo muku shahararren book ɗina me taken Shalelen Alhazawa, ina fatar za ku bibiyeni domin jin yanda zata kasance, ban yi wannan littafin dan na ci zarafin wani/wata ba duk wanda ya yi daidai da rayuwarsa to akasi ne, ban yarda a juya min book ta kowacce suffa ba, idan kunne ya ji jiki ya tsira, kar wanda ya yi gangancin ɗora min book a Website ko You tube ba tare da izini na ba, idan aka yi hakan za ka iya ganin sammaci daga kotu dan haka a kiyaye, ni ce ta ku har kullum Asmeetar Hydar marubuciyar littafin
Gidan Mulki
Mayaudari. Littafin Shalelen Alhazawa akwai faɗakarwa ilmantarwa gami da nishaɗantarwa uwa uba al'ajabi, ku dai ku bibiyeni domin jin yanda zata kasance*


*08082589590*




P. 1




Tun da ta fara ratsa unguwarsu take rufe hanci saboda warin da ke tashi, kayan jikinta kawai idan ka gani zaka ce ɗiyar wani hamshaƙin me kuɗi ce, kaya ne na alfarma zai kai kimanin dubu ɗari biyu, handbang da takalman ƙafarta kuwa sun kai dubu ɗari, wayar hannunta ƙirar iphone 13promax ce, tafiya take cikin iya taku da karairaya har ta fito daga unguwar tasu, sai da ta yi tafiya me nisa kafin ta shiga wata unguwar, daga nesa wata bugaggar mota ce da alama ita ake jira.

A gadarance ta ƙaraso tana sakin murmushi, ba tare da wata fargaba ba ta shige motar tana mai rufe ƙofa.

Alhajin da ke ciki kuwa zai kai kimanin shekaru arba'in, haƙoran makka biyu ne a bakinsa, washe baki ya yi kafin ya ce "Barka da zuwa Zinariyar mata"

Ɗan gyara zaman mayafin jikinta ta yi wanda sai cikakkun ƴaƴan masu kuɗi zasu iya saka shi ta ce "Thanks love am very tied tun safe muke abu ɗaya, waɗannan talakawan kullum cikin yi musu kyauta ake, yau Dad ɗina be samu damar zuwa ba shine fa ya ce na wakilce shi" Ta faɗa tana fari da ido.

"Eyyeh gaskiya akwai gajiya amma be kamata Dad ya turo kyakykyawar mace kamar ki irin wannan unguwar ba, but ina Driver ne?"

Da sauri ta katse shi da faɗin "No ai bana buƙatar Driver because ba kowa nake son ya san ko ni wacece ba"

"Okay zamu iya tafiya ko?"

"Yes we can go dan ina son mu yi sauri mu dawo kafin Dad ya dawo gida, ya tafi Meeting a ƙasar Dubai yau zai su shigo".


Gyaɗa kai Alhajin ya yi alamar gamsuwa tare da kunna mota yana mai barin unguwar.

Wani haɗaɗɗen Hotel suka nufa wanda sai manyan masu kuɗi ne zasu iya shigar sa, ɗagewa Gate ɗin ya yi sama, Alhajin kuwa ya danna hancin motarsa a ciki, Najmeer kam tun lokacin da aka shigo ta ƙara haɗe fuska tamkar ɗiyar shugaban ƙasa, a mota ta tsaya shi kuwa ya shige daga ciki domin biyan kuɗin room ɗin da zasu sheƙe ayarsu, mintuna uku ya ɗauka kafin ya fito yana sakin murmushi.

A tare suka nufi ɗakin tana rungume a jikinsa, wani ƙayataccen room ne wanda ya gaji da haɗuwa, mayafin da ke jikinta ta ɗora kan makeken bed ɗin da ke baje a ɗakin tana mai fara yaye kayan da ke jikinta, Alhajin kuwa ya zuba mata ido kamar zai haɗiye ta ganin yanda shape ɗinta ya fito sosai, daga saman ƙugunta zuwa ƙasa ya buɗe, can bayan mazaunanta ya ɗago sosai gwanin sha'awa, cikinta ya shafe har ya hana cibiyarta fitowa, a hankali ta juya tana mai girgiza jigidar da ke ɗaure a ƙugunta, wani mugun numfashi Alhajin ya ja wanda ya yi sanadiyar faɗawarsa kan bed be san lokaci ba, tun da Allah ya halicce sa be taɓa ganin mace me kyan diri irin na Najmeer ba, rigar jikinta ta fara cirewa tana faɗin "Ka haɗa mun ruwan wanka ina son na shiga" Kamar wani Dolo haka Alhajin ya shige toilet ɗin yana mai juyowa dan ko kaɗan baya son ɗauke idanunsa daga barin kallonta.

Sai da ta gama sauke duk kayan da ke jikinta kafin ta zauna kan bed tana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, gashin kanta da ke yawo har ƙarshen bayanta ne ta ɗaure dan yana takura mata, baƙi ne sosai me laushi ga wani ƙamshin da ke tashi tamkar an yi ɓarin turaren gashi a kai, na shanunta kuwa sun ɗago sama ƙyam gwanin sha'awa, su ba girma ba kuma ba ƙaranci ba masu masifar kyau da jan hankali, Najmeer fara ce sol wanda haskenta me ɗaukar ido ne, macece me kyau wadda duk unguwarsu ake kwatance da ita, a iya binciken da aka yi babu wata macen da ta kai ta kyau a duk faɗin unguwarsu, kyawunta na ƙara mata farin jini gurin maza musamman manyan Alhazawa, bata harka da yara ko talakawa, idan ka ganta tare da namiji tabbata hamshaƙin me kuɗi ne, ƙwarjinta ma baya bari wasu mazan tunkararta, idanuwanta manya ne masu kyau da ɗaukar hankali, ƙwayar idon nata kuwa blue ne siɗik shiyasa wasu ke cewa ba mutum ba ce, wasu ma suna faɗin Aljana ce shiyasa kyawunta ya yi yawa, bakinta ɗan ƙarami ne me ɗauke da pink lips haƙoranta kuwa sirara masu haske, a tsakiya sun raba kaɗan sai haƙoran suka ƙara kyau tamkar ita ta jerewa kanta, hancinta dogo ne daga sama har ƙasan shi, gashin girarta baƙi siɗik ga yawa har ya kwanta ƙasan idanuwanta, Namjeer macece wadda ta haɗa duk wani abun da cikakken namiji me ji da kansa ke buƙata, kayan da take bugawa sun wuce ɗiyar sarkin garin Jos ta saka su, Najmeer yarinya ce ƴar shekaru goma sha bakwai wadda kana ganinta ka san yarinya ce amma yanayin jikinta zaka iya cewa ta fi hakan, domin duk wasu halittu na jikinta sun fito tamkar ita ta tsarawa kanta, cikakkiyar shuwa'arab ce me ji da tsagwaron kyau da kwarjini gaban manyan mutane, iyayenta sun rasu tun tana da shekaru uku a duniya, tana zaune tare da Kakarta ta gefen Mahaifiyarta wadda suke kira da Mamu, iyayen Najmeer kuwa ita ce kaɗai ƴarsu a duniya daga ita basu sake samun haihuwa ba, bayan shekara uku da samun Najmeer Mahaifiyarta me suna Maryam ta rasu sakamakon ciyon cikin da ya kama ta, ko wata ɗaya bata yi da rasuwa ba gobara ta kama gidansu Mahaifinta Malan Bala da sauran jama'ar gidansu Allah ya yi musu rasuwa, itama Najmeer ɗin da ƙyar aka samu damar ceton rayuwarta, ta yi saukar Alqur'an tana da shekaru takwas a duniya, ta yi haddarta lokacin da ta cika shekaru goma sha biyar, batun makarantar boko kuwa babu shi dan Primary kawai ta yi ta daina zuwa, babu yanda Mamu bata yi ba dan ta koma makaranta amma abin ya gagara, rana ɗaya ta daina zuwa islamiyar ma gaba ɗaya, a kullum za ta fita tun safe sai dare take dawowa, tun Mamu Kakarta na kuka da damuwa har ta daina, Mamu ce kawai ke haƙuri da ita dan babu yanda ta iya, duk ƴan Uwan Mahaifinta sun ce kar ta sake zuwa gidansu tun da ta zama karuwa, kasancewar Najmeer akwai zuciya ne ya sa ta janye ƙafarta daga gidan, amma duk da haka suna zuwa dan cin arziƙinta, tun tasowar Najmeer bata da ƙawa ko ɗaya a cewarta bata son munafurci, duk mutanen da ke unguwar sun san wacece ita, inhar za'a yi kwatance idan ba ka ce Shalelen Alhazawa ba babu wanda zai gane, duk ƴan unguwar da sunan da suke kiranta kenan, rashin jin maganarta kuwa sai ƙaruwa yake dan wasu lokutun ma a waje take kwana.



Miƙewa ta yi daga inda take zaune tare buɗe Handbang ta ciro wata farar leda tana sakin murmushi, Frigd ɗin da ke gefe ta buɗe tana mai ɗauko Drink ta zuba a Cup, da sauri ta maida kallonta kan Alhajin da ya fito daga toilet fuskarsa na kallonta, cikin basira da ƙwarewa ta zuba maganin kamar guda uku tana sakar masa murmushin da ya tashi ɗimauta shi, gaba ɗaya hankalinsa na kanta be san wainar da take toyawa ba, a hankali ta ɗaga Cup ɗin tana mai nufar inda yake, wani irin juyi ta yi wanda ya ƙara firgita shi, "Ga wannan ka ɗan taɓa kafin na fito wanka My sweet Guy". Najmeer ta faɗa cikin zazzaƙar muryarta, karɓar Cup ɗin ya yi yana mai kaiwa baki, sai da ya sha sosai kafin ya ce "Thank you Baby Girl am waiting for you, and this your kayan marmari" Ya ƙarasa maganar yana shafa bayanta, sai da ya ja mugun numfashi jin wani mahaukacin laushi ya...


Read / Download SHALELEN ALHAZAWA Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album