Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DUNIYA MAKARANTA 2 Complete Hausa Novel Document by DUNIYA MAKARANTA 2


DUNIYA MAKARANTA 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8468



DUNIYA MAKARANTA 2

Reading Time: 0 Hours

Added On: 04, Jul 2024

Author: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08064661666

Book License : Free

Category: Education

File Size: 44.33 kb

File Type: txt

Views: 616+

Download: 161+

Last download: 3 days ago

Description/Story: DUNIYA MAKARANTA

2
(Hikimomi 251-500)

Rubutawar
Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

1

Bugawa da Yadawa:
Bugu na farko 1437H/2016
Haqqin Mallaka @ Mawallafi

[email protected]
isbn 9960-49-972-3

2

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Gabatarwa
Yabo da godiya da’iman wa abadan su qara tabbata ga Allah. Tsira da sallama da
gaisuwa zuwa ga Annabinmu fiyayyen halitta, shugaban Annabawa, jagoran
Manzanni; Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki xaya.
Wannan shi ne littafi na biyu a jerin darussan Duniya Makaranta da muka fara
bugawa, wanda tasharmu mai farin jini ta Wisalhausatv take yaxawa a duk
marece da safiya.
Babu shakka na samu qwarin guiwa matuqa daga karvuwar da littafi na farko ya
samu, musamman ganin yadda aka riqa buga shi a garuruwa daban daban ana
rarrabawa kyauta ga jama’a a lokutan bukukuwan aure da makamantansu.
A dalilin wannan maraba da aka yi da littafin na duqufa ga inganta shi ta hanyar
rubuta wani sabon littafi mai suna “Abokin Fira” wanda yake kawo labarun kunne
ya girmi kaka masu tabbatar da sahihancin waxannan darussa na Duniya
Makaranta. Littafin yana gaf da kammala kuma da yardar Allah kashinsa na farko
zai fito ba da daxewa ba.
Mai karatu zai lura mun sanya ma waxannan darussa lambobi, ci gaba a kan na
farko don sawwaqe komawa gare su.
Allah nike roqo ya karvi wannan aiki, ya amfanar da ni da waxanda suka karanta
shi.
Baban Ramla
Jum’ah 8 ga Rajab 1437H
(15 ga Afrilu 2016)
A Sakkwato Babban Birni

3

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
251.

Idan za ka faxi magana ko za ka bayyana wani ra'ayi kada ka xauka maganarka ta

fi ta kowa ko ra'ayinka ya fi na kowa. Duk wanda ka gani yana da ra'ayi, yana da fahimta.
Fahimta fuska ce, ra'ayi riga ne; kowa da irin tasa.

252.

Ba dole ne a kowace magana ya kasance kana da wani ra'ayi ba. Idan kana da shi

ba dole ne sai ka faxa ba. Idan ka faxi ba dole ne kowa ya goyi bayanka ba. Wanda bai
goyi bayan ra'ayinka ba ba dole ne ya zama maqiyinka ne ba. Mu koyi zaman duniya.

253.

Idan kana savani da wani ba dole ne sai ka qaurace masa ba. Idan har ka buqaci

qaurace masa ba dole ne kowa ya qaurace masa ba. Sa'ar da kake qin wani sannan wani
yake son sa. Kowa da kiwon da ya kama shi.

254.

Idan ka ji kana son mutum ka bayyana masa kana son sa, sai danqon zumunci ya

yi qarfi a tsakanin ku. Idan ka ji kana qin mutum ka voye masa. Wataqila nan gaba zai
amfane ka, ko ya taimake ka, ko ka ga wani alheri tare da shi, sai sabuwar soyayya ta
qullu a tsakanin ku.

255.

Tsuntsu a kan reshe ba ya damuwa da kariyewar sa. Ba ga reshe ya dogara ba, ga

fukafukansa. Saki reshe, kama tushe. Saki kowa, kama Allah.

256.

Ka koyi kawaici kamar yadda kake koyon magana. A lokacin da magana ta kasa

amfanin ka kawaici zai iya kare ka .
4

257.

Idan kana tunanin za ka iya canja duniya, to ka hanzarta ka yi tun ba ka yi aure ba.

Idan ka yi aure ko canja tashar talabijin a gidanka sai ya gagare ka.

258.

A lokacin da kake saurayi burinka shi ne aure. Idan ka yi aure sai ka riqa addu'a

kana son 'ya'ya. Idan sun girma sai ka riqa fatar ka rabu da su, su ma su yi aure. Daga
baya za ka gaji da aiki ka buqaci ritaya. Sai ka sake komawa kai kaxai, kewa ta dawo
maka. A da, hawa kake yi, a yanzu gangara kake yi. Kana son hardace Alqur’ani amma
qwaqwalwarka ba ta xauka. Kana sha'awar koyon larabci amma ba za ka iya ba. Sallar
dare da yawan azumi duk suna ba ka shawa amma lokacinsu ya wuce. Wannan shi ne
labarinka a duniya. Ka nemi lahira tun da wuri kafin lokaci ya qure maka.

259.

Idan ka ji alamar girman kai zai shige ka, ka duba qarqashin qafarka ka kalli qasa

wadda ita ce asalinka, ka faxa ma zuciyarka "Daga can muka fito, kuma a can za mu
koma".

260.

Abu biyu kada ka yi sakaci da su: Abokin qwarai da Aikin qwarai. Abu biyu

kuma ka ci moriyar su tun ba su wuce ba: Dama da lokaci. Abu biyu kada ka gajiya da
neman su: Lafiya da zaman lafiya.

261.

Abu uku suna hanzarta tsufa: Fushi da Hassada da Yawan damuwa. Babban

maganin su shi ne Yafiya da sanin Allah da bar ma Allah.

262.

Duniya fuska huxu gare ta: Murna da Damuwa da Ciwo da Lafiya.
5

263.

Tsadar kaya da araharsu duk ba su hana xan Adam cin arzikin da aka rubuta masa.

Nemi halaliya. Saurin nema ba ya kawo samu.

264.

Tufafi su ne suturarka ta zahiri. Tsoron Allah shi ne suturarka ta baxini. Yi qoqari

ka gyara ciki da wajenka.

265.

Idan kana cikin damuwa ka yi shiru. Idan an vata ranka ka yi Haquri. Idan kana da

kuxi ka yi kyauta.

266.

Ba yarda da kuskurenka ne yake da muhimmanci ba, xaukar matakin gyarawa.

267.

Kauce ma maqiyi guda xaya ya fi yin aboki xari.

268.

Wasu mutane kamar Sukari suke a cikin rayuwarka. Ko ka daina ganin su amma

xanxanonsu yana nan.

269.

Idan ka tuna yadda magabata suke duqufa ga karatun Alqur’ani sai ka duba yadda

muke duqufa wajen latsa wayar hannu. Kowa da kiwon da ya karve shi.

270.

Idan za ka roqi Allah ba sai ka sa kati a waya ba. Ba sai ka yi booking

appointment ba. Babu jakada, babu shamaki. Idan ka fara roqon Allah ba buqatar sai ka
xaga murya, don ya san abin da ka faxi da wanda ba ka faxi ba.

271.

Sassafta muryarka, amma ka gyara zancenka. Da Ruwan Sama ne ake samun

shuka ba da tsawa ba.

272.

Idan mutane suka riqa gwamatso da kai a sha’anin duniya, bar ma su ita kawai.

Amma idan suka gwamatse ka ga sha’anin addini da samun lada yi sauri ka wuce su.
Allah yana ba da duniya ne ga kowa da kowa, amma lahira kam sai masoyansa.

6

273.

Hudahuda ya yi dalilin musuluntar mutanen qasar Yaman. Tururuwa ta canja ma

Annabi Sulaimana hanyar tafiya. Giwa ta qi karbar umurni a lokacin da Abrahata yake
nufin rusa Ka'aba. Ko cikin dabbobi akwai masu basira.

274.

Wanda yake cikin ginin gilashi ba daidai ne ya yi wasar jefa dutse ba. Lura da

ayubbanka da zunubanka, ka manta da na mutane.

275.

Banbancin Ilimi da kyan fuska: Allah ya bai wa Annabi Yusuf (Alaihis Salam)

ilimi da kyawo. Kyawonsa ya kai shi kurkuku, iliminsa ya fis she shi.

276.

Sallah ita ce abu na farko da za a tambaye ka gobe qiyama. Kada ka mayar da ita

qarshen abin da ya dame ka.

277.

Duniya kowa tafiya yake yi. Hanyarmu xaya ce, amma masauki kowa da nasa.

Wasu za su sauke kayansu a aljanna, wasu ko qarshensu makamashin wuta. Ya Allah ka
yi mana garkuwa daga shiga wuta.

278.

Ababe uku ne suke maganin wahala: Addu'a, da Godiyar Allah, da Taimakon

mabuqata.

279.

Wasu mutane kamar madubin likita suke. Laifi qarami girmama shi suke yi.
7

280.

Hawayenka littafinka ne. Babu mai karanta shi daidai sai masoyanka.

281.

Idan za ka yi hukunci kada ka saurari vangare xaya. Sau da yawa mayaudari yake

kuka, ga mai gaskiya a gefe yana kallo.

282.

Kada ka zama kamar alawa a shanye ka. Kuma kada ka zama kamar maxacci a

furzar da kai. Ma fi alherin al'amurra shi ne na tsakiya.

283.

Nasiha: Kada ka ci abinci bayan ka qoshi. Kada ka yi magana in da babu buqata.

Kada ka zauna da wanda ba ya qimanta ka.

284.

Da abinci a hannunka kake bin tsuntsu yana tserewa saboda ya fi son 'yanci da

abinci. Wasu' yan Adam a nan tsuntsu ma ya fi su.

285.

Annabi Musa Alaihis Salam ya ratsa tekun Maliya a cikin akwati shi kaxai ya fita

lafiya qalau. Fir’auna ya ratsa tekun a cikin dubun dubatar jama’arsa amma ya nutse a
ciki. Idan kana tare da Allah lamarinka duk mai kyau ne.

286.

Idan kana kula da lokacinka, kana jin sauqin ibada, ba ka jin wahalar yin sadaka,

kana kwaxayin bin Sunnah, kana kusantar mutanen kirki, to kai ne kake cikin Rayuwa
Mai Daxi.

8

287.

Ba da kuxi kawai ake sadaka ba. Zikiri da addu'a, da Murmushi da Fara'a duka su

ma sadaka ne .

288.

Tsakanin Miji da Mata: Idan ya yi kuskure za ta nuna damuwa sai ya ba ta haquri.

Idan ta yi kuskure zai nuna damuwa, sai ta yi kuka, sai ya ba ta haquri! Mata ‘yan gata. In
ba ku ba gida.

289.

A wuri biyu ne ake gane kirkinka: Yin Haquri idan ka rasa, da bayarwa idan ka

samu.

290.

Sau dubu ashirin da huxu ne xan Adam yake shexawa tsakanin wuni da safiya.

Ni'imar Allah dubu ashirin da huxu kenan. Me kake yi ma Allah don godiya?

291.

Ka yi abota da duk wanda kake so, amma ka sani abu xaya ne zai abokance ka a

cikin qabarinka; shi ne aikinka da ka aikata.

292.

An tambayi wani malami mai hikima, ko ka san wanda ake karvar addu'arsa? Sai

ya ce, a'a. Na dai san wanda yake karvar addu'a. Wannan shi ya san Allah. Wani kuma
mahaifiyarsa ta fashe da kuka yana cikin halin mutuwa, sai ya tambaye ta, idan ke za ki
yi min hisabi za ki sanya ni wuta? Ta ce, a’a. Wallahi ba zan iya sanya ka cikin wuta ba.
Ya ce, to, Allah yana so na fiye da ke, kuma yana tausayi na fiye da ke. Wannan shi ya
kyautata zato ga Allah.

9

293.

Da ace bankuna suna cire mana kuxi idan muka ci naman wani su jefa ga akawun

xin sa, da mun
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DUNIYA MAKARANTA 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album