Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

DARASI Complete Hausa Novel Document by DARASI


DARASI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13067DARASI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 22, May 2023

Author: Ummu Maher ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 70.51 kb

File Type: txt

Views: 960+

Download: 285+

Last download: 4 days ago

Description/Story: *🌈DARASI!!🌈*


BOOK 1

✨Rabiatu Bashir
Ummu maher(miss green)🍀💚
*@Wattpad link*

https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_campaign=invitefriends*@Arewa book link*

https://arewabooks.com/chapter?id=62a48949772e179ad6e54443Tsokaci:ban yadda wani ko wata yayi amfani da wannan littafin ba wajen canza wani abu ba,wannan littafin mallaki na ne a kiyaye doka ce.

Bismillahir-Rahmanir_Rahim.


*_My parents_*

01


......."Wai ni indo me kika dauki kanki ne da ban isa in gaya miki magana kiji ba,kullum sai kin dorawa wannan yarinyar tallah saboda me zaki ringa kokarin keta duk wata doka da zan saka agidannan?".


"Mlm bafa ka isa ka hanani dorawa wannan yarinyar tallah ba tunda ba kaine kake daukar dawainiyar ta ba,matukar kanason in daina dora mata to kadinga kula da komai nata ciki harda ciyar damu dukkanmu",tana kaiwa nan tayi tafiyarta tana yan kunkuni da karfi.


Shiru Mlm yayi ya goge wata kwalla da ta zubo masa a Idanunsa.

Talla ne akan Fahima itama tana goge hawayen daya cika mata kurmin idanunta sannan ta shigo gidan,ta karaso inda mahaifinta yake ta ce"Baba don Allah kayi hakuri ka daina biyewa Amma saboda ranka zai dinga baci ni kuma banason abinda zai bata maka rai don Allah kayi hakuri".


shafa kan kyakkyawar yarinyar yayi sannan yace"Fahima Allah yayi miki albarka kinji,kema Allah yabaki masu yi miki biyayya kinji".

Cikin tausayin mahaifina na ce"Amin Baba".

Ina tafe ina waiwayen mahaifina da ya kasa fita har yanzu yana nan wajen dana barshi,haushin mahaifiyata ya kara ninkuwa acikin zuciyata,da wannan tunanin na karasa shiga cikin gidan.


"Ke!"

Da sauri na kalli Amma wacce ta kasance mahaifiyata sannan ta ce"Saboda kinyi tsiyar taki kin zubarmin da kudi shine ko sallama ba zakiyi min ba kawai sai ki shigo gida kina neman fadamin kan tukunyar girki ki jazamin siyan maganin da ban shirya ba".


Kallon mahaifiyata nayi wadda na mayar kamar tv tun shigowa cikin gidan,wato ita babu ruwanta da konewa ta ita kudinta ne ya dameta,Amma kenan ita babu ruwanta kudinta kawai ta saka a gabanta.

Jiki na a sanyaye na shige cikin dan rubabban dakinmu wanda kana ganin ginin gidan kasan tsohon ginin ne,runtse idanuna nayi na kalli silin din dakin ina tunanin rayuwar da mahaifana suke yi,kwatata Amma wato mahaifiyata bata mutunta mahaifina kullum cikin fada da gaya mishi bakaken maganganu kawai don bashi da kudi,ina cikin tunanin Kannena suka shigo dakin da na ke,Khalil,sai nusaiba,da Haruna,kannena ukune kacal don Amma tun kan Harun tace ta daina haihuwa da babanmu wai ta gaji da haihuwa ba'a yi mata ragon suna,don haka yanzu shekarun Harun Biyar Amman Amma ta daina Haihuwa,hatta Harun Amma Bata ji kunyar Dora masa talla ba,duk kannena suna talla,kowa da Safiya tayi zai tafi nashi tallan.Muryar Nusaiba ce naji tana cewa,Anty Fahima wannan mutumin nan da kika hanani zuwa wajenshi,shine yau ya kirawoni wai inzo zai Bani alewa shine ni kuma na gudu.

Kallon yarinyar na Shiga yi hawayen tausayin yarinyar suka Shiga zarya a idanuna,"Anty kuka kike don Allah ki daina kuka idan kina kuka Nima zanyi".


"Ba kuka na ke ba y'ar kanwata,ki gayawa Amma wannan maganar kinji,don ba'asan zuciyarshi ba ".


"Wallahi Anty Amma ba zata yarda ba dukana za tayi rannan ba na Gaya mata ba,shine tace wai k'arya nake kuma wai Kada na sake in gayawa kowa,idan ba haka ba zata zaneni".


"Amma n ce tace Miki haka"?.

"Eh wallahi Anty haka tace wai ko ke da Baba Kada na Gaya muku idan ba haka ba zata k'unani in mutu".


Rungume Yarinyar nayi ina sheshshekar kukan tausayin Nusaiba Yarinyar da Bata fi shekara8 ba Amman har wani Dan iskan ya Fara hakar rayuwarta,gaskiya ya Zama dole asan abin yi,don tasan halin Amma ko don cinikin da Nusaiba ta ke mata zata iya barin Yarinyar har aje a lalata mata rayuwa a banza.Da daddare muna zaune muna cin tuwon Dare Amma kuma taje barkar haihuwar kawarta,na kalli Mahaifina da yake ta cin tuwonsa cikin farin ciki,na ce"Baba inason zamuyi magana ne"?.


"Ina Jin ki Fahima".


"Baba daman Akan Nusaiba ne,wai kullum ta dauki talla sai wani ya kirawota shagonsa wai zai Bata alewa,da ta fadamin sai nace mata ta dinga guduwa,shine yau ma mutumin ya Kara tare ta",na Fadi hakan ina sheshshekar kuka,don a rayuwata ina matukar son kannena musamman Nusaiba.


Shiru Baba ya yi min baice komai ba ya sha ruwan Dana debo masa ya wanke hannunsa ya saka ta kalminsa ya fita.

Wata kwalla ce ta sauka akan fuskata,to me hakan yake nufi?shima Baba ya Fara bin goyon bayan Amma ne ko me?ai Naga koda na fada masa ya nuna damuwarsa tunda yarsa ce Amman me yasa baiyi wani Abu ba?,duk ni kadai nake wannan surutun daga bisa ni,kuma na koma cikin dakinmu zuciyata babu dadi.


Cikin dare na jiyo hayaniyar Iyayenmu,Baba na yana cewa Amma"Wallahi duk ranar da kika Kara dorawa Nusaiba talla to a bakin aurenki,shasha wacce Bata San inda yake mata zafi ba,kowa yana tattalin nashi yayan Amman ke Banda ke,saboda wani dalili mara tushe da kike tutiya dashi,iya abinda naji Kenan daga nan Mahaifina Bai Kara magana ba sai Amma ce naji ta bude kofar gida ta fita a cikin wannan Daren, Mahaifina ya biyo ta yana Kiran sunanta.Wani kuka ne ya kufcemin a shekaruna wadanda Basu Gaza 14, ba Amman babu abinda bana ganewa a game da Zaman Iyaye na.


Da k'er Baba na ya shawo Kan Amma ta dawo tana ta sababin fadanta,wai wallahi ita ba zata Kara dorawa Nusaiba talla ba Amman fa ya dinga Nemo abinci a gida.


"Eh naji Insha Allah Zan dinga nemowa da dai a lalatamin rayuwar Y'aya na".

To daga haka kuma ban karajin bakinsu ba,Baba ya rufe kofar ya shigo ya kwanta.

Sai da na Dade banyi bacci ba daga Baya baccin ya daukeni,ina tuna caftar Baba da Amma don Baba na a rayuwarshi ya tsani b'acin ran Amma yanzu zakiji sunyi fada an jima zasu shirya.
****************

Wani kyakkyawan gida na hango me kyau da kuma tsari,colour din Gidan fari ne k'al,tun daga bakin kofar Gidan sojoji ne fal tsaye da bindigunsu sun sai ta gabas dasu,a cikin gidan kuwa wasu flowers ne masu kyau koraye da kuma pink sun haska gefe2 Gidan tsakiyar kuwa yaji wani rantsatstsan interlock me matukar kyau,gida babban gida Wanda idan Ka shige Shi ma sai kayi 2hour ba kaje wani wajen ba.


Wow Kada dai na Gama cikaku da surutu kyaun wannan Gidan sai Wanda ya gani,don Gidan Yadda kukasan white House na America.

Wata mata na hango zaune a wata farar kujera wacce ta gaji da haduwa a garden din Gidan matar ba zata wuce 35 ba,tana waya da wata tana cewa"Falmata wallahi abinnan yana damun kwakwalwata, Haihuwa na ke son Samu ko ta halin kaka,wajen da kika rakani rannan nake son ki sake rakani,zanzo Maiduguri gobe ki rakani,don Yallabai Baya nan sai nan da kwana 3 zai dawo.

Daga cen b'an garen Falmata tace"oky ranki ya dad'e ina jiran zuwanki,yawwa ni kuwa kin Samu kinje Yola din kuwa wajen Maman Yallabai Ammar?".


"Banje ba kuma bazan je,don wallahi na rantse Miki da Allah abinda matarnan tayi min Nima saina Rama,don tana tutiya d'anta ne ni kuma ina tutiya da mijina ne".

"Hhh mutuniya ta Kenan shiyyasa na ke son ki,kiji dadinki matar Yallabai,Insha Allah sai kin haifi magajin Gidan Yallabai Ammar".

Wata dariya Sakinat tayi sannan ta ce"ai ni wando Ce dai dai nake da k'ugun kowa"itama dariya Falmata tayi sannan tace"to ina jiran zuwanki don akwai Wanda mukayi alkawarin fita dashi.

Suna Gama wayar ta shigo cikin sashenta Wanda fadin iya haduwarsa ma b'ata Baki ne,har zata Shiga dakinta sai kuma ta dawo sannan ta nufi wajen wani kyakkyawan hoton wani matashi Wanda ya saka kakinsa na soja,yayi bala'in kyau sai Ka kasa gane Balarabe ne ko kuwa wani half-caste ne,don yana da wani irin sirrin kyau na ban mamaki.


Shafa hoton Sakinat tayi sannan tace"ilove u mijina inason Ka da yawa".

Ganganci ne mace ta rabe Ka,na sani ko ban sani ba ciki kuwa harda wacce ta kawoka duniya,don ni kadai a kayi Ka General Ammar Muhammad Lamido ina matukar so da kaunarka,dafatan Ka wayi gari lfy tana fadin hakan tayiwa hoton kiss ta shige daki abinta,tana kulla Yadda za tayi don itama taga ta ajje kwanta a acikin wannan babbar gonar.


Ammar yana zaune cikin k'aya taccen office dinsa Wanda ya gaji da haduwa,kyakkyawan matashi ne wanda ya gaji da haduwa cikin kayansa na kaki,ya d'aga kansa yana wani tunani,Anya kuwa yana yiwa kansa da mahaifiyarsa adalci kuwa,rabonsa daya saka k'afafunsa a Yola yau shekara 5 Kenan fa,yaso ace kafin wannan tafiyar da ta kamasa zuwa kasar Tunesia yaso yaje,Amman ya dauki alkawari Insha Allah idan ya dawo zai je,ya share wata kwalla da ta cika mishi idonsa,yana cikin tunanin yaji k'arar wayarsa Wanda yasan ba kowa bane illa matarsa Sakinat don ita kadai ce...


Read / Download DARASI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album