Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
*ASY KHALEEL💕*


*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*😻
*BILLYN ABDUL*🌹



*SHAFI NA D’AYA (1)*


*Daga shafi na d’aya xuwa na biyar na ki ne uwar d’aki na,ni kadai banda Hafsat Rano😆.Sis UMMI AISHA👌🏾*💕


بسم الله الرحمن الرحيم


*ABUJA*

*A* jiye yaron da ke hannunta tayi akan gadon sa tare da d'ora kansa akan pillow irin na jarirai dinnan, wanda lokaci d’aya ya keta sharar baccin sa, ta shafe shi da addu'a,sannan ta dauki macen dake ta faman wangale wawulon bakin ta da babu hakori a ciki.

Kallo d’aya zakai wa yaran kasan cewar 'yan biyu ne.Tashi tayi ta dinga zagaye parlorn da yarinyar a hannunta, tana d'an jijjiga ta har sai da tayi bacci, sannan ta kwantar da ita a kusa da tagwai d'in ta.

Komawa tayi gefen su ta rage volume d'in tv da ketayi a tashar Africa magic yoruba. ‘jenifa’s diary’ ake yi lokaci zuwa lokaci take d'an murmusawa, da alama sosai take jin dad'in drama series d'in.

Wayar tace ta fara rurin kara ‘Miftahul qalb’ shine sunan dake ta yawo a samab screen d'in wayarta ta, da azama ta d'auka tare da karawa a kunne had'e da mikewa a hankali tabar wajen gudun kada ta tashi yaran nata dake ta baccin su.

“Assalamu Alaikum Qalb..”

“Wa’alykm Salam sugar, yanzu na sauka fa” Cewar *SAIFULLAHI* dake janye da akwatin sa madaidaici a harabar airport d'in Lagos .

“Wayyo! Sannu qalb.. ka sauka lapia?!
Ubangiji Allah yasa albarka a abinda akaje nema, rabbi ya dawo daku lapia, yanzy dai ka samu abinci kaci banda shan abu mai sanyi dan Allah...kaji?”

Ajiyar zucia ya sauke, Allah ya sani yana matukar son matar sa da yaran sa, dole ce tasa yake nisa da su saboda yanayin aikin nasu, muryar tace ta sake dawo dashi daga tunanin su daya tafi ida take cewa.

“Kaji Zawj?”

“Na..Naji Love! Insha Allah bazan sha ba”

“Toh! Bari na kyale ka, ka huta tukunna anjima sai na kiraka muyi video call kaga 'yan biyun ka dan tuni sunyi bacci babu dadewa”

Shafa kwantaccen sajen sa dake kwance luf-luf a saman fuskarsa yayi, dan ba kad'an ba yana jin wani shaukin sonta na kuma ratsa shi yana lalata duk wani jini dake shiga jikinsa..

Cikin kasalalliyar murya ya furta,

“Okay love..! Yanzu zamu wuce ikoyi da Abbas anjima kuma zamuje ikeja filling station d'innan saboda traffic d'in lagos da safe..will call you when I’m done idan dare be yi nisa ba..”

“Okay zawj.. I love and miss you sai anjima..”

Sallama suka yiwa juna, bayan kowannen su ya sakarwa d'an uwansa zazzafan kiss ta wayar, cike da kadaicin junan su kowannen su ya katse kiran had'e da nannauyar ajiyar zuciya.

Komawa tai parlor wajen 'yan biyun ta dake ta bacci cikin nutsuwa. Tuni har angama shirin jenifas diary an shiga yin wani kuma, kallon agogo tayi 11 saura.

“Wai..haka dare yayi?..”

A gaggauce ta dau yaran nata ta takai d'aki, bayan ta canza musu kaya izuwa kayan bacci, band'aki ta fad'a wandake cikin d'akin tayo wanka hade da dauro alwala ta fito. Sai da tai nafilfilinta sannan ta koma kan gado tai azkhar na bacci hade da addu’oi na kariya ta tofe su sannan ta dauki wayar ta tana dannawa, ganin har sha biyu tayi bai kira ba, tasan lalle aiki ne ya rike sa. Gajeren message ta tura masa kamar haka,

_“Every day, I fall in love with you more. I don’t know how that’s even possible when I’m sure that I couldn’t love you more than I love you now. I guess you just have this thing about you that makes loving you so easy and natural. I miss you already. Sleep now,honey. Sweet dreams. Allah ya yi jagora a abinda akaje nema”_

Ajiye wayar tayi a gefen bedside drawer dake gefen ta, ta bud'e ta zaro photo album d'insu na secondary school, wato BRITISH NIGERIAN ACADEMY(ABUJA)tana kalla..

Memories ne suketa dawo mata kallon 'yan ajin nasu take yi, d’ai-d’ai har tazo kan 'yan gidan da suke uba d’aya dasu wato Hafsat Khaleel Mai Mota sai ta biyu wadda sunan ta ke rubuce da Hidaya Khaleel Mai Mota, sai babbar kawarta Haleema Sameer Ameer sai kuma hotan ta dake k’arshen Page d'in rubuce da Bilkisu Khaleel Mai Mota *(ISLAM)*

Murmushi fadad'e a fuskarta take bin kowan ne hoton 'yan ajin nasu da kallo, tun daga kan matan har zuwa mazan ajin nasu take kallo abubuwan da suka faru na dad'i dama akasin haka take ta tunanowa harta gama ta rufe photo album d'in wanda suka kammala makaranta a shekarar dubu biyu da goma sha hud'u (2014).

“Such is life” (haka rayuwar take) Shine abinda Islam take ta maimaitawa kafin ta kwanta bayan ta kara yin wata addu’ar.

Kwanciya tai zuciyarta fal da abubuwan da suka faru a baya, idan na kunya ne ta rufe ido, Idan na dariya ne ta murmusa ita kad’ai.

Haka bacci barawo ya sace ta, zuciyarta cike take da tuna bayan rayuwar ta, tana ta shek'a baccin ta saifullahi yayo mata reply,

_"Sugar pie.It does not matter how my day was, I always long for the night, to cuddle you all night as you quench my heart.It was a stressful night,aiki muke tayi yanxu ma muna construction site na ikeja... A shafa min kan Arya da Aryan...I love you more than life itself. Goodnight my love.."_

Asubah ta gari masoyan juna.. *SAIFUL_ISLAM*💕

Da wannan Ni Nana hafsatu nace shin wacece ISLAM?wacce irin rayuwa tayi da har take tunanin ta haka?!..Ya kamata mu koma shekarun baya don ganewa idanuwan mu abubuwan da suka shud’e🏃🏽‍♀

***** *ASALIN LABARIN*


*BRITISH NIGERIAN ACADEMY...SS1b*

Zaune kowannen su yake a kujerarsa da yake monday ce duk yawanci ransu a b’ace yake musamman da yake first period maths ne.

Back sitters babu abunda suke sai ciye-ciye sai kuma 'yan lovey dovey squad dake hirarrakin soyayya da yake mix school ce (makarantar mata da maxa a hade).. Sai 'yan seat d'in gaba wato su ISLAM madam serious ita da kawayenta, kowannen su kansa a kasa suna ta karatu kafin malamar maths din ta shigo..

Shigowa Miss Abigail tayi daga ita sai mini skirt da top d'in riga tasha attachment a kanta, mikewa class d'in suka yi masu hararta nayi mazan nata faman sakin fito a hankali, da yake rabin su sun tsani maths, kuma a jin sune sahun gaba a rashin ji, Da karfi 'yan gaba suka fara;

“Good morning ma..! we are happy to see you ma’am, God bless you ma..” Banda 'yan baya dake cewa,

“We are not happy to see you ma.. God punish you ma” A hankali yadda bazata jisu ba.. Ita kuma sai washe baki Miss Abigail d'in take yi tana cewa.

“God bless you too..Thank you.. have your seats please”

Juyawa tayi tana rubutu a board, ‘Matrix and Matrices’ shine abunda ta rubuta kafin ta juyo ta dube su..

“Okay class..Today we are going to discuss and solve Matrix and Matrices’ I’m going to solve Number one question and one of you will come and solve the other.. I’m I clear?!”

“Yes Ma..” Suka fad’a da karfi.

“Good..”

Ta fad'a tare da juyawa tana solving banda su Islam, babu wanda yake sauraronta sai ma cigaba da hirar su da suka yi har ta gama tayi musu bayani sannan ta kalli class d'in tana cewa.

''Okay who’s going to solve the next?”

“Maa..” Islam da ta d'aga hannunta alamun zata iya, had'e da gyara zaman medicated glass d'inta.

“Good..” Cewar Miss Abigail tana mikawa Islam d'in marker..

“Mtcew” Hafsaat da suke uba d’aya sannan tana d'aya daga cikin 'yan back seat taja tsaki a hankali tana furta,

“Sai dai nacin karatu kawai da san iyawa, banxa mai bakin jini..”





_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*



*NA*



*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*



*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_



*SHAFI NA BIYU (2)*


Sam Islam bata bi takan ba’ka’ken maganganun da Hafsat da kawayen ta ke gasa mata ba,Tana jin su suna aiba tata suna mata mugayen fata,haka tai ficewar ta gaban board,babban burin ta bai wuce tai solving equation dinnan dai-dai ba..

Kaman yadda Miss Abigail da kawayen Islam suka tsamma ta akan Islam, hakan ce kasance, domin dalla-dallah Islam ta kalkuke maths din, Tafi (round of applause)Miss Abigail tasa yan class din suyi nan suka fara ji kake.

“Raf raf raf..”

Ajin ya dauka da tafin masoya da kawayen Islam amman banda bangaren su Hafsat wato ‘yan back sitters da suke jifan Islam din da harara.

10marks sukutum Miss Abigail ta bawa Islam,kan idan exams tazo tanada additional ten marks,godia Islam tayiwa Miss Abigail tare da ‘yan class sannan takoma seat dinta ta xauna.

“Lam Lam all the way..Go gurl..”

cewar Haleema Sameer Ameer wadda suke kira da Lee, itace babbar kawar Islam kaf BNA sai sauran kawayen ta su Hafsat Rano,Fatma Bichi,da Hanan, Leesa da kuma namijin cikin su wato Kamalu,wanda sukewa laqabi da K-boy shine class rep,Islam kuma itace assistant class rep..

Bayan fitar Miss Abigail,Mr okafor physics teacher dinsu ya shiga class din,sosae su Hafsat suka shiga nutsojin dan ba kadan ba yake basu punishment idan ya kama wani ko wata suna yi masa sakarci acikin aji, Saboda makarantar ba’a duka kowa ubansa wani ne a garin kama daga k’usa a gwamnati ko kuma shahararren dan kasuwa ne a kasar. Duk ‘ya’yan masu farcen susa ne,shi yasa kowannen su yake baje hanci yana shi ma fa ubansa yana cikin jerin who is who..wannan kenan!

A cikin BNA ‘ya’yan Dr Khaleel Mai Mota su uku ne Bilkisu (ISLAM), Hafsat,da kuma Hidaya.Kowanne uba suka hada amman uwa kuma kowa da tasa.Hafsat da Islam sune suke science, while Hidaya tana Art class, kasancewar hakan yasanya Hidaya hostel dinta daban ne,Islam da Hafsat kuma hostel dinsu d’aya..

Tsangwama, kyara, ba’a, mugunta, hassada,gulma,tsegumi kai wataran harda rabon duka Islam ke samu awajen su Hafsat saboda sun tsaneta,tsana mai tsanani wadda takai kololuwar xarce mizanin mai karatu..

“shin ko me yasa hakan? oho muje zuwa...!”

DR IBRAHIM KHALEEL MAI MOTA: shine mahaifin su Islam,Asalin Ibrahim khaleel dai haifaffen garin kano ne kauyen y’ar gaya, mahaifin dr khaleel shine marigayi malam tasi’u mai guga tare da mahaifiyar su inna Bilkisu dake kauyen na y’ar gayan,

Su uku ne wajen mahaifan su, Yaya Bala shine babba sai dr khaleel sai kuma kanwar su hansa’u..Hakika su dr khaleel sun taso cikin matsananciyar rayuwa, domin tun mahaifin su nada rai suna kanana guga ce sana’ar sa, tahaka yake ciyar dasu daganan bayan rasuwar sa kuma mahaifiyar su tafara sana’ar wankau dan rufawa kanta asiri da marayun ta dan takan je tayi gidah gidah ko kuma a kawo mata tayi,

Da wannan suke samun rufin asirin su,har dai babban wansu Bala ya fara sana’ar shoe shiner, duk ranar talata kasuwar karkarar yake zuwa yin dako samu yai musu awun hatsi da yan canjin sa na shoe shiner, har wayo yafara kama Khaleel inda yataso yaro mai kaifin basira yanada saurin daukar karatu na boko da arabi.

Inna Bilkisu batai kasa a gwiwa ba sosai takeson tacika burin khaleel na zama shahararre a fagen ilimi tunda yataso da zuciyar yi, itada Bala da dan kudin da Hansa’u ke samu wajen tallar kayan koli da su akeyi masa amfani .

Allah abun godia kwanci tashi ba wuya wajen Allah, burin inna yacika domin khaleel yagama sakandire kuma har yasamu fannin karatu na d’aya a sashen karantar halayyar dan adam, da kuma zaman takewar yadda k’asa take wato (sociology)result d’insa yayi kyau,yafito da first class take aka bashi scholarship na k’asar Egypt inda ya samu gurbin karatun Msc psychology.

Shekara biyu yayo acan yadawo gidah sunyi sunyi su rikeshi ya xauna acan ya dinga koyar wa,amma afatau yak’i, domin yana kishin k’asar sa nijeriya Abubuwa da dama sunyi sauk’i,Yaya Bala yatafi lagos neman kudi,Hansa’u tayi aure sosai yanzu basuda wata sauran matsala sannu ahankali da yan kudin sa daya dawo dasu yagyara musu gidan su,Ya sai y’ar Mota golf domin yin haya,da lodin gari gari ga form na PhD ya siya a jam’iyyar bayero ta kano,kasancewar sa matashin mutum a kauyen daya fara siyan mota yasan ya ‘yan kauyen yi masa laqabi da ‘Khaleel Mai Mota..’ kuma sunan ya bishi!

Sannu ahankali komai na tafiya dai dai da lodin da yakeyi na gari-gari,

sanyayyar safiyar asabar gashi lokacin damuna ne ya ‘dau lodin yan jihar yobe xuwa maiduguri idanuwansa sukai masa tozali da matashiyar budurwar,da kallo d’aya xakai mata kasan babarbariya ce kyakkyawa da dan bular hancinta a gefen dama,kwarai matuka tatafi da zuciyar ibrahima khaleelu,inda yaji duddunia bayan mahaifiyar sa babu abu na biyu daya ke so ya xamto mallakin sa irin wannan y’ar budurwa,

Sosai tayi nasarar cafke zuciyar khaleel,bayan ya dire su a bornu ya sakko ya nemi samun number ta,da alama itama yatafi da ita cikin ‘kan’kanin lokaci takaranto number ta harda doriyar sunan ta.

Arziki aka ce kashi ne,sosai khaleel fa Allah ya dubi talaucin su da maraicin su lokaci d’aya kofar arziki ta budewa Khaleel da yaya Bala,abun dai sai sam barka kawai cikin wannan yanayin ne khaleel yai aure da sahibar tasa Aysaa,a kuma wannan yanayi yaya Bala ta biyu ya kara da yake shi xamansa yama fi yawa a lagos yanzu,domin yaxama babban dan canji a garin na legas nan dai aka kai masa amaryar sa..

Dare yaxama safiya,safiya taxama yamma,yamma taxama dare,hakik’a Allah mabuwayi ne gagara misali,a haka dai bayan wasu shidewar shekaru ‘Dr Ibrahim Khaleel Mai Mota’ ya zama babban mutum mai mata hudu ta hudun ce ma ba’afi shekaru 5 da auren ta ba.

Ya tara iyali,sai dai duk mata ne Allah bai bashi namiji ba,yaso hakan amma Allah be yadda ba,domin dadin karin auren sama duk dan hakane,sai dai kash amarya na kamuwa da juna biyu lokacin haihuwarta nayi ta juye masa yan biyu duk mata,to abun dai sai godiar rabbil izzati domin shidin ma mallakin komai ne.

Hajia Aysaa itace matar sa tafar ko
inji hausawa suka ce ta ladan noma Tanada yara uku,da cikon na hudu a cikin ta.Taso ta cire cikin,domin aganin ta,ta manyan ta da kara haihuwa,tana yi ya'yanta nayi,Ina xata kai kunya?!acewar ta.Dr khaleel ya kwararo rantsuwa ya dire,tare da doriyar idan tai kuskuren cire masa ciki,wallahi tallahi sai ya mugun sab'a mata.Haka ta dauki hak’uri ba wai dan tana so ba, ba’asan mai zata haifa ba Allah ne kadai yabarwa kansa sani.

Safa da marwa yan biyu ne ta haife su wanda har sunyi aure,safa na lagos tana aure,Marwa kuma tana Manchester.Sai Bilkisu,wadda taci sunan mahaifiyar sa ake kiran ta da Islam da kuma dan baba,da ake tsumayin haife shi/ta...!

Sai matar sa ta biyu,wato Hajia Karimatu y’ar kano,ce cikin y’ar unguwar yakasai, tanada yara uku itama.Khadija,Sajeedah da kuma auta Hafsat data ci sunan kanwar sa hansa’u,

Duk sunyi aure bada jimawa ba suna zaune a Abujan,Hafsat ce kawai batai ba,sa’ar Islam ce, sai dai Islam ta girme mata da shekara d’aya,amma ajinsu d’aya..

Sai ta ukun Yafendo,ba fulatana ce y’ar yola, tanada yara uku itama... Hissah, Nusrah da kuma auta Hidaya..Hissah tayi aure Nusrah kuma tana law sch amma an kusa yin auren.

Sai ta hudun amarya ce y’ar kasar chad Helwa nawarma, ya aureta ne ko Allah xai cika masa burin sa na ‘ya’ya maza, sai dai kash Allah bai yadda ba,domin tana samun ciki akai scanning yan biyu ne,doki awajen dr khaleel ba’a magana sai dai me?! Yan biyu zankad’a zankad’a mata ta juye aka sanya musu Afrah da Arfah.Abun dai sai sam barka kawai ga mai hankali.

Rashin wannan buri nashi na samun yara maza yasanya dr khaleel daukar babban mataki na ‘ya’yan sa sai sunyi zurfaffen karatu both arabi da boko domin bature yace ‘what a man can do a woman can do better’...

Kaf yaran sa banda yan biyu ‘kananan, da su Islam dake babban ajin sakandire na d’aya gaba d’aya sauran daga doctors, sai lawyers da bankers..
Wannan kenan..!

*****

*B* *N* *A*
(BRITISH NIGERIAN ACADEMY)

*Elizabeth Arden’s hostel*

Zaune Islam take,hannun ta rike da littafin chimamanda mai suna,’purple hibiscus’........!


Ba kullum zan samu yin posting ba pls.Ayimun uzuri naso sai dana gama project da nakeyi,na fara littafin☹mistakenly hannu na ya danna Page d’aya xuwa grp dina😫sanadiyyar haka ya sanya ruguntsumin dole na dinga wantsalo muku shi😉 Kanwataa Rano kece sila kinci bashi😹👍



_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SHAFI NA HUDU (4) *


*Z*aune Haj Aysaa take a parlorn ta, dake d’aya daga cikin duplex’s apartments dinnan guda bakwai, cikin nan nata ya k’ara k’asa alamun haihuwa tazo kenan, lokaci xuwa lokaci takan furta,

“Ya Allah ka sauqaqa mana lamuran mu, Allah ka kare mu da kariyar ka, kayi mana katangar k’arfe daga sharrin masu sharri, ya Allah kasau keni lapia da ni da duk wanda haihuwa tazo wa, ya Allah kafini sanin abunda yasa ka azurtani da wannan babban arziki, rabbi kasa...”

Bata k’arasa ba sakamakon wani azababban ciwo daya taso tun daga tafin k’afarta xuwa marar ta, dakyar tasamu ta sakko daga kan kujera tana k’ok’arin danna intercom dake kan center table, dakyar ta danna cikin wahalalliyar murya take cewa,

“Falmata..”

Falmata mai aiki dake can sama tana mopping parlorn sama tajiyo muryar Haj Aysaa, dake tunda haihuwar tazo kusa Haj Aysa tadawo dakin kasa taxama tana jiran Allah ya sauketa Lapia, da sauri Falmata ta saki moo tasheka k’asa a guje don dajin muryar Hajian kasan ba lapia ba,

Temakawa Hajia Aysan tayi tasaka hijabi suka k’arasa wajen mota a waje, driver ya bude hajian ta xauna kafin Falmata takara shekawa a waje ta dakko akwatin kayan fa suka tanada na baby unisex (wanda xa’a iya sawa mace ko namiji) suka siya dan hajian taki yara tayi scanning, a cewar ta wannan Duk harkar yarinta ce, ita data manyanta tacire ran haihuwa tuni kuma saiga Allah yayi ikonsa, Allah kenan qadirun ala manyasha’u,

Ta window Haj Karimatu taga fitar su, dogon tsaki taja kafin takoma kan doguwar kujerar datake xaune tun farko ta xauna,

“Allah ya raka taki gona, ya kara miki yan hudu mata akan ukun dakike dasu, domin aikin Malam na dotsa kamar yankan wuka yake kuma ya tabbatar mun hakanne xai faru, mu zuba mu gani, la’ananniya” duk maganganun nan Haj Karimatu ita kadai takeyin su babu kowa a parlorn, tamkar dai sabuwar tab’i, tanayi tana k’ok’arin neman wata number a waya da alama kira xatai.

Zanklin asibiti sukaje dake nan kusa dasu ba awani dau lokaci ba aka shiga da Haj Aysa maternity room, sunyi sunyi akira mijin agaya masa don qa’idar sa ce tunda regular patients dinsu ne Ha Aysaa taki, kan lallai yana can senate board meeting na d’aya daga cikin university din da yake lecturing.

Cikin hukuncin Ubangiji domin shidin mabuwayine gagara misali ya sauki Haj Aysaa lapia,

“In yaaa” shine kukan jarirai har biyu yan maza zankad’a zankad’a sukeyi, dayan na tsotson hannun sa dayan kuma na mimmike jikin sa, hakan ya yi nuni da lapiyayyu ne , kallo d’aya xakai musu ka sake maida kallon ka kansu domin healthy babies ne kuma kyawawa, sai dai muce TubarkAllah kawai,

Tuni bacci yai awun gaba da Haj Aysaa yaran sai tsala Kuka sukeyi, babu shiri dr James ya kira lambar dr khaleel bugu biyu ya daga bakinsa dauke da sallama kafin yace,

“Yes dr James..”

“Sir! Congratulations”

Dr Khaleel yana zaune a meeting ya mike yana,

“Congratulations?! I beg your pardon”

“Oh sir! I mean your wife safa’s mom..”

Be karasa ba dr Khaleel ya katse kiran a kidime ya fice daga board meeting ko takan sauran board members be saurara ba dake dakatar dashi,

A 330 ya karasa asibitin, da Falmata ya fara cin karo tana ta murmushi, tana magana cikin harshen kanuri da alama Allah takewa godia,

“Álà bárgà càkkó,Álà bárgà,Álà kámbò”

“Alaji hajia ta sauka lapia,”

“Alhamdulillah ya Allah,Tana cikin dak..”

Shiru yai sakamakon nurses biyu da suka nufo shi da babies a hannun su mika masa su sukai,

Kasa magana yayi sai kallon ikon Allah daya tsaya yana kallo, saurin sujjada yai tagodia izuwa rabbis samawati mamallakin komai daya azurtashi da wannan babban rabo daya jima da hakurin haka a zuciyar shi,

Dagowa yai daga sujjadar ya karbi yaron be wani dau lokaci ba yayi musu kuthba, ya kira sallah a kunnuwan su tareda tauna dabino yai addua yai drop kadan a bakin su, a take ya sanya musu suna,

“Allah ka raya mana Abubkhar (sunan mahaifin Hajia Aysa ‘Alhaji Bukar Goni’) da kuma sunan mahaifin sa marigayi Malam Muhammad Tasi’u”

Dakin da Haj Aysaa ke bedrest ya shiga tana kwance tana bacci, numfashin ta yana futa a hankali da alama tasha wahala domin an dade ba ‘a haduba..

Gefan ta ya zauna yana gyara mata dankwalinta cikin murya cikeda farin ciki yake shafa fuskarta yana fadin,

“Allah ya miki albarka Aysa, kinbiyani kin cikamin burina duk abunda kike bukata a duniyar nan kigayamin komai tsadar sa xan cika miki burinki ko menene ko mai tsadar sa”

Mutumin naku dai sai surutan sa yake ,Falmata dake waje dadi kashe ta yau Hajian su tacikawa oga burin sa,

Cikin lokaci kankani ya kira yan uwa da abokan arziki ya gaya musu wannan daddadan labari, kafin minti 30 asibiti fa yafara cika da yan uwa da abokan arziki,amma duk abunnan babu keyar Haj Karimatu da Haj Yafendo, Helwa ce kawai taje amaryar, da kuloli shake da abinci,

Tuni Haj Aysa ta tashi daga bacci don masu xuwa barka sun hanata yin baccin, dr Khaleel kuma yak’i barin a karbi yaran minti kadan da an dauke su

Please Login or Register in order to submit comment