Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaysa gaba d’aya maxan wajen da matan had’e da kyakkyawar runguma da sumba a gefan kumatu.

Kan kace me? Table ya cika da maza, harda wanda suka jajjanyo sit dinsu dawo kusada Islam, ita dai sai raba ido take tana binsu da kallo, domin san bata taba engaging kanta a irin wannan abubuwan ba, addu’oi kawai take a zuciyar ta, na Allah ya fiddasu lapia daga wannan wajen, had’e da cin alwashin sai tayiwa Riri tatas, data kawo nan wajen.

Leefa d’aya daga cikin mazan dake table din ya kai hannun sa zai taba cinyar Islam, da sauri Islam ta matsa tana bige masa hannu, ware ido yayi yana duban Riri alamun tambaya, daria Riri tayi tana kashe masa ido d’aya kafin tace,

“Uhm uhm Leefah, Bar wannan scaredy-cat ce, ko mọ ohunkohun” (batasan komai. Ta fad’a cikin harshen Yoruba.)

Kamar maye haka Leefa ya tsaya yana duban Islam, kakkauran miyau ya had’iye, tamkar yaga wani nama. Kafin cikin harshen yarabanci yace,

“Mo rii o, chai ọmọbirin naa ni ara.”
(Nagani, Kai amma yarinyar nada jiki mekyau).

Ita dai Islam batasan mai suke fad’a ba domin ba jin yarabanci take ba, haka ta xauna kamar kurma, duk wanda yazo wajen haka yake ‘karar surutunsa ya tashi ya tafi, kanzil bata had’ashi da Islam. Ji take kaman ta tashi tabar gurin, matsalar batasan kan garin bane, da tuni ta ware gidah.

Tana ganin yadda maza suka saka Riri a tsakiya suna shafata, su kisses and hugs, touch-touch duk shi sukeyi, sam bata lura ashe shegun kayane ajikin Riri ba sai yanzu, domin wata figaggiyar vest ce da wando leggings, sai ta ‘dora jilbab har ‘kasa akai. Yanzu kuwa da sharholiyar tasu tayi yawa, tuni Leefa ya fige shi gaba d’aya yana yadda yaga dama da jikin Ririn.

Baki, hanci kai harda idanuwa Islam ta gwalalo tana duban su Riri, dakyar da kamo addu’oi ta janye kallon ta daga garesu, tana neman gafarar ubangiji daya yafe mata wannan zinar ido data gani.

Sai gab da magrib suka koma gidah, Sam Islam bata bari sun hada ido a mota da Riri ba, hakama ko magana Ririn ta ‘dakko, ita dai Islam nata uhm da uhm uhm ne kawai, har suka ‘karasa gidah.

Sai bayan sunyi shirin kwanciya ne Islam ta d’akko zancen da,

“Riri meyasa kike aikata abunda kinsan haramunne?”

Yatsina fuska Riri tayi, domin tasan za’azo wajen, ganin yadda Islam din tayi sak ‘daxun, tasan sarai tanada tarin tambayoyi akanta,

“Anzo dai-dai wajen kenan, Toh malama menayi wanda Allah ya hana?”

Tasowa Islam tayi ta kama hannun Riri cikin nata, kafin tace,

“Riri, yadda naga kuna tab’e-tab’en junan ku sam ba a jiyan kuka fara ba, da alamun kin dad’e kina zuwa wajen.”

Dogon tsaki Riri taja, kafin tafara ‘babbaka daria,

“Kina nufin ki cemin bakya rage zafi ke? Kenan ke ko ‘dan kiss baki taba yi da wani ba, wai ke a hakan kina nufin kice ko gaisawa da maxa bakyayi?! Talk less of se....”

Katseta Islam tayi tana girgixa mata kai,

“Wallahi tallahi bantab’a ba, ni dai da hankali na, na tab’a namiji ko na rungumeshi kai har kiss yashiga ko gaba da haka ma, wallahi ban tab’a ba, Nasan nayi mix school amma irin haka be tab’a faruwa da ni ba. Allah shine shahidi.”

Gyada kai Riri tayi, kafin cikin tabe baki tace,

“Ke yanzun wallahi rayuwar sai da dan tab’e tab’en kake aure, kashi sittin na ‘yammata abunda sukeyi kenan, kuma su ne ke auruwa, amma xakiga yarinya kullum cikin hijabi ko babban mayafi wai ita saliha, to wallahi maxan yanxu basason wa’ennan, domin gani suke ai basu waye ba.”

Tunani Islam tashiga, ganin kuma wallahi hakanne, tasan wanda suke hakan kuma suke auren, babban misali gashi nan yafaru dasu Hafsat, ita dake lullube jikinta tana hana maxa tab’ata ai gashi batai auren ba, ko saurayi batada shi ma, duk gudunta suke, kamar wata mujiya mai ba’kin jini.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace,

“Hakane Riri, gaskia yanzu slay queens ke aure, amma idan kika auna abun a mizanin hankali, zaki ga cewar ai Allah yayi hani mace da namiji su keb’e ma, talk less tab’e tab’en juna.

“Toh madalla shekiya malama ustaxiya Islam, rike shawararki banaso, ki nanan Kina killace jikin ki tayaya xasu gani suce suna sonki? Ni kuwa wallahi sai hamdala samari harda na siyarwa sai na sayar.”

Murmushi kawai Islam tayi, kafin ta mike tashiga band’aki.


*ABUJA*

Zaune Haj Karimatu da Yafendo suke, sai ‘kus ‘kus sukeyi, bakajin ‘karar komai sai ‘karar TV, Karimatu dake aikin taunar chingum taja wata shegiyar majina kafin tace,

“Ai wallahi tallahi tunda y’ar iskar matar nan ta shiga tafita don ganin anyiwa ‘yayanmu fyade, bata hakura ba ta sake bunka tsafin nata, tasa santolon (Dr Khaleel) yai musu auren dole, to wallahi baxan yadda ba nima, sai nayi mai yiwuwa rayuwar tata ‘yar ta lalace, ta ‘kas’kance, ta shiga dunia, sai ta maida gidan can bariki, taxama gansamemiyar karuwa.”

Tana fad’a Yafendo na jinjina mata hannu, kafin tace.

“Wallahi kuwa Yaya, ai bazamu yadda taci banza ta kwana lapia ba, yo bana gaya miki danaje wurin na ‘kan tudu’ mai yace ba? ‘Kwarya ya nuna min yace ki kalla na minti 5, duk fuskar da kikaga ta fito, to itace mai yi muku sihiri, duk wani cigaban ku ta datse shi, kamar wajen tafiyar ruwa agine shi. Abunda yace kenan, yace kuma wallahi dana kawo wannan million biyar ‘din, da saniyoyi uku, da tattabaru biyu farare ‘aure’, da sabon haihuwa ‘kyan’kyashasshen ‘kadangare, yace kamar ‘kiftawa da bismilla, rayuwar Aysa xata tagayyara. Za’ai mata kurciya tabar garin anemeta arasa, xa’a sanya mata hauka, sannan duk ‘ya’yanta na gidan aure zasu rabu da mazajen kowacce ta shiga dunia ta lalace, ita kuwa Islam nace yayi me yiwuwa ai mata fyade mai cike da ‘kas’kanci, a tura mata ba’kaken aljanu su hanata aure, nace ya ‘kara mata da tsumammen d’oyi, ta dinga hamami duk inda taje mutane su dinga gudunta kada su rab’eta...”

Daria Karimatu ta shiga bankawa, Yafendo na taya ta, sai da sukai mai isar su, kafin Karimatu tace.

“Ai Insha Allahu zuri’ar Aysa kaf sai sun tagayyara, sun shiga ‘kuncin rayuwa mai cikeda tausayawa...”

Sam basusan duk maganar da suke an d’auke wuta ba, Dr Khaleel dake tsaye yagama jin duk zantukan da sukai, hawaye ne ke gangarowa daga idanun sa, dakyar ya iya sanya kansa ya shiga parlorn bakinsa d’auke da sallama..

Dede lokacin, Yafendo da Karimatu sun had’a baki wajen fad’ar,

“A hayye nanaye...”
‘Casss’ suka had’a hannuwa, suna tafawa.

Ganin sa yasa duk suka shiga nutsojin, Karimatu cikin ki’dimewa tace,

“Yawwa Yafendo sai ki fara wanke alba....”

Bata k’arasa ba Dr Khaleel ya ‘daga mata hannu, alamar ta dakata...........


*USA 🇺🇸*
Harvard University (Cambridge)

Saifullah ne zaune a garden na school hannun sa rik’e da wata paper yana zana(drawing) wani gini dake can gefan inda suke a zaune, lokaci zuwa lokaci yake dan ‘daga kansa yana gyara zanen,

Zaune suke da sam, Jeremy sai Abbas (Abbas abokin sa tun na farkon littafin da su kaje Lagos tare), kowanne da abunda yakeyi acikin su, cikin haka wata matashiya ‘yar Nigeria ce itama, da kallo d’aya xakai mata kasan Hausa-Fulani ce, mai suna Ameerah wadda ake kira da ‘Meerah’.

Zama tai a kujerar da saifullah yake, ganin ta yasa ya saki tsaki a hankali, tamkar yaga kashi, ya mike yana karkade jikin sa, ya koma d’aya kujerar, bata damu ba, ta fadada murmushin ta, siraran hakoranta suka bayyana, kafin tace,

“Genius” (haka suke kiran saifullah a school din, saboda k’ok’arin sa).

Tamkar bai jita ba, ya cigaba da abunda yakeyi, sau uku tana kiran sunan sa, mikewa yayi xai bar wajen Abbas yai hanxarin riko hannunsa yana girgixa mai kai, alamar a’a. Cikin rad’a yace mai,

“Ka saurareta pls, stop shunning her, Kaga masu jajayen kunnuwan nan sai suyi mana daria.”

Cewar Abbas, yana fada kuwa ya kira su Jeremy kan su koma su zana wani sabon waje a bayan school din. Suna barin wajen ta ‘dan durk’usa tana niyyar kamo hannunsa, saurin janyewa yayi yana galla mata harara, da manyan idanunsa TubarkAllah. Cikin daddad’ar muryar sa, so melodious and sweet yace mata,

“Pls respect your self Ameerah... Respect is reciprocal, ke macace, maintain your dignity and decency, ta haka xakiyi earning respect. And secondly, na fada miki several times cewar ki abiding rules d’ina. My time is priceless, inada lokacin komai pls, yanzu ina cikin aiki kin katseni, bayan na miki warning yafi a ‘kirga..”

Ita sam ba maganar da yake ce ta dame ta ba, sanyayyar muryar sa me kama da sarewa itace ke tafiya da ita, har wani lumshe idanu take. Tsaki Saifullah ya saki a karo na ba’adadi. ‘Dan buga drawing pen d’insa yayi akan seat din da take, juyawa tai tana binsa da kallon soyayya.

“Ameerah..”

“Na’am”

tafada cikin za’kuwa, don ba karamin dadi take jin yadda yake kiran sunan taba, aganinta yafi kowa iya fada ma.

“Get lost pls...”

Ajiyar zucia ta sauke, kafin ta tashi dakyar ta tafi, tana tafiya tana kallon sa, gaba d’aya she’s half naked, kayan da tasa sosai suna nuna surar jikin ta, cikin fusgar da iskar bakin sa, ya furta..

“Sam ba kamin kai.. ughh! so annoying”


****
_Assalamu Alaykum sisters_
_Masu maganar ban kyauta ba dana had’a saifullahi da Nusrah, akan lallai mai yasa ban kashe Nusrah na aura mai Islam ba? kuyi hak’uri sannan ku fuskanci wani abu d’aya🤗 Na taba rubuta saifullahi yana son Islam?! No bantaba ba, Tabbas nace sha’awarta yake ba sonta yake ba, haka zalika bance Islam na son Saifullahi ba, sai dai ko Khaled. Ko a gaske sha’awa ba soyayya ba, bata da dad’i. Domin da mutum ya kauda wannan sha’awar tasa, to fa daukar macen xaiyi kaman fankon ashana, batada wani amfani, sai dai idan Allah ne yayi dama dole sai ya xauna da ‘ita har ‘k’arshen rayuwarsa, Abu na biyu wallahi dama haka na tsara littafi na da sunan su su biyu, *SAIFULLAHI* cousin din Islam, sai kuma *SAIFULLAH* wanda zai zama mijinta nan gaba, Saboda haka ni bana tab’a canxa yanayin yadda na ‘dakko littafi na, yadda na tsara haka nake tafiyar dashi, bana canza aqalar alqalamina, yadda sauran littafai suke nawa yasha banban 🤗Abu na biyu kowa da irin farin jinin sa pls, yakamata adinga saka reality into fictional stories, shi farin jini kowa da yanda Allah yayi sa, wata na dashi sosai kuma lokaci d’aya take aure, Saboda yawan masu sonta, wata nata ga maxa rututu amma bana auren, wata kuwa babun badhiluhu ne😉ma’ana duka babu digon farin jinin balle samari. So yakamata ku ‘dauki hakan a sabon salo🙏🏾dole ne kowane littafi sai yarinya tayi farin jini?😫 duk inda tai farrr samari kamar ruwan sama😒 ku barni na ‘karasa littafi na pls kamar yadda na tsara shi, ta yadda xamu gane akan me ya fadakar😻idan ba haka ba😕Toh zanyi shafi d’aya na gama shi a haka, duk mutaru mu kasa fahimtar akan me aka yi shi🤣😉_
_Conclusively Hafsatu fa na da ciwon idanu. Thou nasan yawanci kun sani, Yes da glass nake amfani sometimes🤗. _ _so I can’t be squeezing and pressing my precious eyes anyhow ba😹 kunsan ido sai ana d’an lallab’ashi, _so typing da nake yawan yi babu break, yasanya idanun fara fushi yana hautsinewa😌xamu fara ‘diban break.._
_With love,_
_ME, MY EYES AND MY GLASSES 😹🙏🏾_




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 28-29_*

_INA ‘YAN GROUP ‘DINA NA, *HOME OF NOVELS*?, TO KU MATSO KUSA, SHAFIN YAU NAKU NE SISTERS😘KUYI YADDA KUKA GA DAMA DASHI, JAZAKUM ALLAH KHAIRAN! DA YADDA KU KE BIBIYAR LITTAFIN, *SAIFUL_ISLAM💕* _

nanahafsat.wordpress.com


Gyaren murya Ya Bala yayi, yana mai nuni da su Haj Karimatu. Da yatsan sa na biyu dake hannun daman sa, cikin muryar fushi dake tattare da damuwa yace,

“Hakika kun bani mamaki, yadda na ‘dauke ku, ashe kun xarta hakan, wannan wacce irin musibace? Shin kuna tunanin duk abunda kuke yi Allah baxai kama ku da laifi ba ne ko kuwa? Wane irin haukan kishi ku ke yi ne ? Da ya xarta tunani? Ni da ku, shekarun baya na ja muku kunne, had’e da tausasa zuciyar Khaleel, ya hakura ya dawo da ku ‘dakunan ku, dukkoda yadda kuka ‘kulla sharri akan yarinyar da batada masaniya akan hakan, daga ni sai ku, sai su Khaleel, aka rufe maganar ba’a bari tafi to ba. Sai daga baya na gane ba kishi bane, tsantsar mugun tace.. Tirr! Da hali irin naku wallahi.”

Shiru yayi, gaba d’aya ya rasa mai zai sake cewa, ganin haka, yasanya Inna Bilkisu dake gefe cewa,

“Duk dan akan kishi kuke hakan ko? Shinma menene kishi? Tunda naga kamar bakusan ma’anar sa ba, da yadda ake yinsa. Shi kishi wani yanayi ne na so da kauna da burin kare abun da ake son daga kamuwa da cuta. Ana kishin kasa kuma ana kishin sana’a da abokan zama.. Duk inda akwai kishi mutane na ganin cewa akwai so, har ma wasu kan ce “kishi so ne”. Duk dan Adam bai cika mutum ba sai ya kasance yana da kishi. Ko dai ya kasance yana kishin kansa, kishin iyalinsa da dai makamantansu.,

“Hausawa na cewa “kishi kumallon mata.” Amma a zahiri ba mata kadai ke da kishi ba, har mazan ma suna da shi. Mutane da dama na ganin cewa maza sun fi mata kishi, kawai dai matan sun fi nunawa ne. Wannan abu ne da za a iya muhawara a kai. In har hakan ne, akwai abubuwa da dama da ke silar hakan. A addinin musulunci da kuma al’adar mutanen Afirka da yankuna da dama, maza ne suke auren mace fiye da daya. Su kuma mata miji daya kadai suke aure. Wannan shi ke sa mata su yi ta jin tsoron kawo musu abokiyar zama wadda ake kira kishiya. Kalmar kishiya kanta bai dace ana fadar ta ba, kasancewa zama aka zo yi tare da miji daya ba wai wasa ba. Ita kalmar ke kara wa mata da dama tsoro cikin zukatansu da zarar an furta ta. Sannan kuma maza da dama sukan fara wulakanta uwargida idan amarya ta zo. Ita da ‘ya ‘yanta su zama ko oho. Su ma amaren su yi ta jin dadi cewa ana wulakanta uwargida, ba sa tunanin cewa su ma idan aka yi sabuwa, haka za a yi masu. Hakan na matukar tsoratar da mafi yawancin mata, har ma ka ji suna cewa “ba kishiyar ake tsoro ba sai sharrin ta,

“Yarda da amincewa na da matukar muhimmanci a dukkan tarayya, musamman ma ta aure. Da zarar babu yarda a cikin zaman aure, zargi zai shigo ciki kuma ba za a taba samun zaman lafiya ba. Ya kamata mu rika gina aure bisa yarda da amincewar juna, don hakika su ne gishirin zaman aure. Rashin yarda ne ke kawo rashin jituwa har ta kai ga rikici, a wasu lokutan ma har da kisa,

“Kusani cewa, Kishi wata dabi’a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A’isha tana cewa : “Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, duk da cewa ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi s.a.w yana ambatonta” Bukhari 1388, Kishi mai tsafta, shi ne : kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, Akwai Jahilci : ta yadda mata da yawa suka jahilci, hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni a kara aure, kamar;rage yawan zawarawa da ‘yammata, da kuma yawaita zurriyar Annabi S.A.W.,domin da za su kalli wannan da kishinsu ya ragu. Mummunan zato, yawanci uwar gida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwar gida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima.Amma idan da ace kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba’a samu matsala ba.,

“Rashin adalci daga wajen namiji, yawanci maza su kan karkata zuwa amarya, wannan sai ya haddasa fitina, saboda uwar gida za ta ce ba ta yarda ba. Amma idan kuka duba anan zaku ga cewa, shi maigidan ku sam ba haka yake ba, hakika yana k’ok’arin adalci a tsakanin ku, Saidai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne : babu yadda za’a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya, Annabi s.a.w. ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A’isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, sukan ‘kirkidi ranakun da yake dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, saidai abin da sharia ta hana shi ne, rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum. Wanda ku Kan ku kunsan maigidan ku na kamanta adalci a tsakanin ku, sannan akwai Munafukai, masu cece-kuce, idan da ace kishiyoyi za su daina daukar guzuri-zoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli. Amma ku duk kunyi fatali da wannan idanuwan ku sun rufe, kun ‘dauki zugar shed’an kun d’orawa zuciyar ku, kuna aikata shirka, domin wallahi had’a Allah da wanin sa shirka ne, zuwa wajen duba, da yan tsibbu suna gaya muku ‘karya da gaskia, kuna zama akai, kun cusa mummunar ‘dabi’a aranku, kun ‘dau wani qudri na ganin kunyi mai yiwuwa kun fidda wasun ku daga gidan, to ku gayamin da ta tada rigima kar a auro ku, Allah ba za’a yin ba, dandai bakusan k’ok’arin da baiwar Allahn nan tai muku bane da har ta bari aka auro ku,

“Dan ni ‘dinnan da kuke gani, ca nai sam a’a, kada ya ‘kara aure, Aysa ta isheshi zaman dunia da ‘yan ‘yayan su, yace rufa muku asiri zai yi, barin ke Karimatu” inna bilkisu tafadi hakan tana mai nuna da Karimatu, Kafin tace,

“Bazawara ce ke, mijin ki ya miki duka ya sakeki, Allah ya temaka babu rabon ‘yaya a tsakin ku, kawun ki ya samu Khaleel da zancen ki, ya rufa miki asiri ya aure ki, Ke kuwa Amina(Yafendo), ta tallan nonon shanu, Allah yai auren ku zai had’u, ta sanadiyyar kad’e ‘kanin ki da drivern sa yayi, yaji tausayi bayan an kammala komai, yace xai aure ki ya temakawa Baffan ki da hidimar ku, ganin kunyi yawa awajen sa, amma duk hakan bai isheku yin hankali, kun zauna da abokan zaman ku lapia ba, Sai tada fitina da neman yadda zaku fiddasu daga gidan, Ku na jifansu da sharri da sihiri kala-kala, wanda duk daga ‘k’arshe idan da zakuyi nazari kan ku yake dawowa, kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa. Ko kunsan,

“Hukuncin sihiri, da bokanci da abunda suka ‘kunsa? To ku sani baya halatta ga ko marar lapia ya je wajan bokaye da suke ikirarin sanin abubuwan da ke boye, wai don ya gano masa rashin lafiyansa, kamar yadda baya halatta ya gasganta su cikin abinda su ka bayar da labarin sa ba, domin su suna maganine ko kuma su kirawo aljanu domin su taimaka mu su akan abinda su ke so, to wadannan hukuncinsu shi ne ‘kafirci’ idan sun yi ikirarin – ilimin gaibi, hakika Muslim ya ruwaito cikin ingantaccan littafinsa, lallai Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce;
((من أتى عرافا فسأله عن شيء لم تقبل له صلاة أربعين يوما))

Ma’ana: “Duk Wanda ya je wajan dan’duba sai ya tambaye shi wani abu to ba za’a karbi sallar sa ba ta kwana arba’in”. Kuma daga Abuhuraira Allah ya kara masa yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:

((من أتى كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

رواه أبو داود وخره أهل السنن وصححه الحاكم عن النبي صلى الله عليه وسلم بلفظ ((من أتى عرافا أو كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

“Ma’ana: “Duk wanda ya je wajan boka sai kuma ya gasganta abinda ya ke cewa, to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi”. Abu dawud ya ruwaito shi kuma ma’abota littattafan sunnah hudu sun fitar da shi, kuma Hakim ya ingantashi daga Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi da lafazin:
“Duk wanda ya je wuri dan’duba ko boka sai ya gaskanta abinda yake cewa to hakika – ya karficewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi”.
Kuma daga Imran dan Husaini Allah ya karama sa yarda ya ce: Manzon Allah tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:
((ليس منا من تطير أو تطير له أو تكهن أو تكهن له أو سحر أو سحر له، ومن أتى كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد
ﷺ‬)). رواه البزار بإسناد جيد

“Ma’ana: “Baya cikimmu duk wanda ya ke yin camfi ko a ke yi masa camfi ko ya yi bokanci ko ake yi ma sa bokanci, ko ya yi sihiri, ko ya sa ayi mishi sihirin, duk kuma wanda ya je wajan boka sai ya gaskantashi a aduk abinda yake cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi”. Bazzar ne ya ruwaito shi da Isnadi mai kyau.
“ saboda haka ku sani, A cikin wadan nan hadisai masu girma akwai hani game da zuwa wajan ‘yan’duba da bokaye da masu sihiri (asiri) da makamantansu, da kuma hukuncin tambayarsu da kuma hukuncin gasganta su da bayanin narkon azaba akan haka. Domin hakika manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hani akan zuwa wajan su da kuma tambayar su da gaskanta su, domin abinda ke cikin haka na muni maigirma da hatsarin da ya ke babba da mumunar makoma kuma domin lallai su makaryatane fajirai, kamar yadda ya ke cikin wad’annan hadisai dana baku, wadannan Hadisai dalili ne cewa boka kafirine da mai sihiri domin su biyun basu cimma manufar su sai ta hanyan yi wa aljanu hidma da bauta musu koma bayan Allah kuma wannan kafurcewa Allah ne da kuma yi masa tarayya – tsarkakken sarki,

“Kuma mai gasganta su cikin abinda su ke cewa na sanin gaibu ya kasance kaman su ne, kuma dukkan wanda ya karbi wadannan al’amura na abinda su ke bayarwa to hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya barranta da shi, kuma baya halatta ga musulmi ya yarda da abinda su ke rayawa cewa magani ne. Domin lallai wannan yana daga cikin bokanci da rudar da mutane, kuma wanda ya yarda da hakan to hakika ya taimaka musu akan barnarsu da kafircin su,
Hakanan kuma baya halatta ga wani mutum musulmi ya jewajansu – domin ya tambayesu gameda wanda. Zai aurar da dansa ko wani makusancinsa ko kuma abunda ke iya kasancewa tsakanin ma auratan biyu da danginsu na soyayya da cika alkawari ko kuma kiyayya da rabuwa da makamantan haka;domin wannan yana daga cikin gaibi wanda babu wanda yasansu sai Allah tsarkakke mada’au kaki.

“Kuma sihiri yana daga cikin abubuwa haramtattu na kafirci kamar yanda Allah mai girma dad’au kaka yace cikin sha’anin mala’I kunnan biyu cikin suratul Bakarah: ﴿وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتلُواْ ٱلشَّيَطِينُ عَلَى مُلكِ سُلَيمَنَ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ وَلَكِنَّ ٱلشَّيَطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحرَ وَمَا أُنزِلَ عَلَى ٱلمَلَكَينِ بِبَابِلَ هَرُوتَ وَمَرُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة فَلَا تَكفُر فَيَتَعَلَّمُونَ مِنهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَينَ ٱلمَرءِ وَزَوجِهِ وَمَا هُم بِضَارِّينَ بِهِ مِن أَحَدٍ إِلَّا بِإِذنِ ٱللَّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَلَقَد عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشتَرَىهُ مَا لَهُ فِي ٱلأخِرَةِ مِن خَلَق وَلَبِئسَ مَا شَرَواْ بِهِ أَنفُسَهُم لَو كَانُواْ يَعلَمُونَ١٠٢﴾

Ma’ana: “Kuma basu sanar da kowa ba balle suce: mu fitina kawai ne, saboda haka ka kafirta,” balle har suke rarrabwa tsakanin mutum da matarsa dashi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) basu zama masu cutar da kowa da shiba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma baya amfaninsu, kuma lallai ne, sun sani tabbas wanda ya saye

Please Login or Register in order to submit comment