Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannuwa alamun ban hak’uri tafara magana,

“Uncle B! Wallahi tallahi saurayin Hafsat ne, tun farko da.. da..”

“Da uban uban ki, xaki gayamin ko sai na karairayaki?”

Cikin kidimewa ta hadiye wani kakkauran yawu kafin tace,

“Wallahi tallahi Uncle B.. Sas..Saurayin Hafsat ne da farko da ita suke yi, yana taba nononta wai tanaso suyi girma sufi na Islam, shi.. shi..Shine nima na sameshi nace inaso nawa su fara girma nima yamin haka, kuma...Kuma shine daga baya yafara saka...”

Bata ‘karasa ba Ya Bala ya bata kyawawan mari guda uku a jere, ji kake ‘tas tas tas’ ,duhu ne ya mamayeta kafin tafara jin kamar tsuntsaye na zagaye kanta, tsabar xafi sai da taga wuta a mari na biyu , Ana ukun kuma kunnuwan ta suka toshe.

A zuciya Ya Bala ya sa aka kira Hafsat , gabanta sai faduwa yakeyi tashiga parlorn. Gaidasu tayi tana xama nesa da Hidaya, jikin ta yabata itama yanzu xatasha nata dukan, ganin Hidaya wadda aka canxawa halitta lokaci d’aya tamkar ba ita ba.

“Ke..”Ya Bala ya dakawa Hidaya tsawa,

Dawowa tayi a razane hannunta dafe da kuncinta,

“Maimata abunda kika fad’a.”

Maimaitawa tayi,Hafsat tuni jikin ta yafara rawa, Ya Bala ya dubu Hafsat yana cewa,

“Wanene yaron, kuma ‘dan gidan uban waye shi? Tinkiyoyo kawai, da har kuka tsaya, tsatso d’aya kuka fito amma namiji guda d’aya ya ‘bata rayuwar ku, wannan wane irin dabbanci ne? Idan aure kuke so ayi muku mana, tukunna ma dukda dai bana tunanin haka, kuma bana fatan hakan,babu Islam acikin wannan abin naku ko?”

‘Daga kai sukayi, Hafsat jiki na rawa tace,

“Wallahi Uncle B, ni dai sau d’aya ne muka...Mukayi, Nace banaso kada ya sake saboda wani wa’azi da naji, shine fa ya koma kan Hidaya kullum kullum..”

“Ya isa” cewar Ya Bala, gaba d’aya yaran sun fara bashi tsoro.

“Wanene yaran?”

“Sunan sa Hilal ‘dan gidan Ambassador Umar Gumi ne”

Gwalalo ido Ya Bala yayi yana maimata sunan Amb Umar Gumi, cikin in’ina yace,

“Amb Umar Gumi dai recent Amb dake wakiltar Nigeria a Johannesburg?”

Gyadai kai suka Hidaya da Hafsat suka yi, Ya Bala ya juya suka hada ido da Dr Khaleel, a hankali ya furta,

“The mafia kenan... Subhan’Allah”

Sallamar su Hafsat da Hidaya Ya Bala yayi, sun jima a parlorn kowa da abunda yake saqawa a zuciar sa, ajiyar zucia Inna Bilkisu ta sauke kafin ta dubi Ya Bala tace,

“Wannan yaron(da ke ‘dan fari ne) yanzu ya xa’ai kenan?”

“Inna wato a zahirin gaskia mahaifin shi yaron da sukai wannan babbar ta’asa, Idan duk duniya zasu taru suce ga abunda ‘dansa yayi wallahi baxai yadda ba, ‘dan rigama ne Inna, Idan kinji ana ‘The Mafia’ Toh shine, hatsabibancin sa ya xarce tunanin mutum wallahi..”

Hannu dafe da hab’a inna tace,

“Toh Allah ya kyauta, domin acikin su ma ba’asan wa ya fara jan ra’ayin wani ba. Allah ya shrya..”

“Ameen” suka baki d’aya.

“Ni ina ganin had’a su a aurar dasu baki ‘d’aya shi yafi muhimmanci, Tunani nake ma acikin yaran nan wa za’a had’a a rufawa juna asiri.” Cewar Ya Bala.

Sun jima suna tattaunawa, tareda bawa Dr Khaleel hak’urin wannan bakar ‘kaddara data afka masa. Ya Bala da kansa ya tasa qeyar Hafsat da Hidaya ciki harda Islam zuwa asibiti. Gwajin farko aka fito da Islam virgin ce ita komai ruf a muhallinsa. Hidaya kuwa har ‘dinki akai mata sannan sun samu mummunan virginal infection Hafsat da Hidaya, sanadiyyar fingering da Hilal yake ma muka hannunsa acikin gaban su. Su biyu dai result yafito ‘baro ‘baro su ba virgin bane, kuka wiwi kowaccen su tayi, banda Islam da taka godewa Allah daya tsameta bata fada wannan mummunan ‘kaddara ba.

Bayan sallar isha’i aka fara meeting, da maganar auren su Nuradden aka fara, inda Nuraddeen xai auri wata y’ar ‘kanwar gwamnan kaduna, Kabeer da Ibrahim kuma ‘yayan mutum ‘d’aya xasu aura amma kowacce babar sa daban, uba suka had’a. Daganan aka dakko maganar auren Yusuf, kowa yayi mamaki amma an tayashi fatan alkhairi. Sai aka ‘karkare da zancen su Hidaya.

Karimatu na gefe ta lailayo wani ashar, tana kumfar bakin wallahi sai dai sihiri aka jefe ‘yarta dashi, ko kuwa ture akai mata na gardi ya keta mata haddi a makarantar, Hakama Yafendo da ke ta kama sunan Haj Aysa tana qullalliya suka shirya dan kawai araba yaran su da budurcin su, a zuciye Dr Khaleel ya mike yaja niyyar basu ragowar sakin su, dakyar Inna Bilkisu ta haneshi, domin har sai da ta mike tana rike kafadar sa, gaba d’aya idanuwan sa sunyi jajir shi kadai yasan tashin hankalin da yake ciki.

A lokacin Ya Bala yace su Hafsat kowacce ta maimaita abunda yafaru, babu kunya suka fayyace komai, Haj Aysa dake gefe har kukan tausayi tayi, tana ‘kara jaddada girman ‘kaddara, na irin tsaron da Dr Khaleel yakewa yaran sa amma ace haka tafaru? Kuma iya xamanta dashi tasan baida wani mummunan hali na bin mata ko akasin haka.

Fada sosai Ya Bala ya shiga yi, ta inda yake shiga, batanan yake fita ba, ya ‘karkare xancen da,

“Saboda haka satin sama ne bikin su Nuradden, mun yanke shawara wanda Idan duk duniya xasu taru su hana, Indai ba Allah ne ya ‘kaddara hakan baxai faru ba, wallahi summa tallahi sai mun had’a auren su Hafsat a satin.”

Gaban Islam ya yanke yafadi, tuni jikin ta ya soma rawa, Ya Bala ya cigaba da cewa,

“Saboda haka zamu had’a auren Hafsat da ‘Alhaji Saminu Taura’ na kano, Hidaya kuma..”

Bai ci gaba ba, Karimatu tai hanzarin katseshi tana hawaye,

“Yaya kayi hak’uri dan Allah, Alhaji saminu fa, wannan tsohon mutumin mai mata biyu? Fisabilillahi ka duba lamarin nan Yaya”

Tsaki Ya Bala yaja yana kauda kansa gefe, cikin fushi yafara magana,

“Idan ba shi ba wa kikeso a bawa? Shi dinma shine tun kwanaki yace yanason d’aya daga cikin yaran gidan nan, kuma itace dai-dai domin ai ba budurwa bace yanzun, shima temaka mata xaiyi”

Rufe baki Karimatu tayi tana kuka, Sosai da hawaye, Hafsat dake gefe tai shiru itama hawayen na fita daga idanun ta, domin ko a mafarki bata tab’a xaton haka rayuwa xata canxa mata ba. Yafendo kuwa kasa kunne take tana jiran taji wane hukuncin xa’a yanke akan Hidaya.

“Yawwa sai ke Hidaya. ‘Alhaji Muzammil Rimi’ dake Zaria, shi muka yanke hukuncin baki shi a matsayin mijin ki, kun san shi dai wanda yazo ya duba Inna rannan, yanada mata uku kece ta hudu, zai ajiye yi agidan sa dake Zaria.”

Tusar wannan karan da Yafendo ta saki kowa yaji ta, a fusace Ya Bala ya juya yana dubanta da duk ma yan parlorn,

“Haba Amina, wannan wane irin abune wai? learn to growl up pls” cewar Dr Khaleel had’e da wurga mata harara.

A kidime Yafendo ta rarrafo kusada Ya Bala dayai hanxarin toshe hancin sa da hannu ‘d’aya, domin warin tusar data saki ba karamin babban bomb bace, Rokansa tashiga yi, kan ya janye ra’ayin sa, ita kuwa Hidaya dake gefe tunani take ina nema Zaria,saurin rufe baki tayi tunanowa da suna tsayawa a garin suyi sallah Idan xasu kano, kuma sun tab’a zuwa dubiyar matar mutumin, sam gidan baiyi mata ba, don mutumin ba mai kudi bane kamar Dr Khaleel (To ai dama hakane, dan mahaifinka mai kudi ne bai xama lallai sai ka auri mai kudi ba, ita dunia ai Up and down ce, kuma dama life is dynamic).

Ya Baka ko takan Yafendo dake bashi hak’uri ya janye ‘kudurin sa bai bi ba, sai ma sanya ‘kafa dayai ya shure hannun ta, dake makale da ‘kafar sa, gyaran murya yayi, kafin yace.

“Saboda haka duk sati mai kamawa za’ai ‘daurin auren, Ke kuma Islam sakamakon irin k’ok’arin ki, da yanayin tarbiyarki da kyawawan ‘dabi’unki da kike dashi, baki zubarda mutuncin ki ba, ha’ki’ka kin cancanci babbar gudunmawa daga gare mu, amma duk da haka nan bada wani lokaci ba zamu aurar dake, saboda haka da xarar kin samu me son auren ki, ki fada sai ayi bincike ayi auren, sannan yanzu bayan anyi ‘daurin auren su Hafsat, zamu nema maki gurbin karatu a jami’a anan garin, zancen fita waje kuyi karatu yanzu an soke shi, Kiyi hak’uri Insha Allahu xamu cika miki burin ki, Medicine xakiyi da yardar Allah, sannan inaso ki je ki nutsu kafin sakamakon ki yafito muji wacce makaranta zaki yi, idanma a Lagos wurina kike so, to duk ba matsala. Allah yasa albarka..”

Haka Inna Bilkisu ma ta sake yin fada mai ratsa jiki sosai, sannan aka watse akabar su Inna suna tsara yadda al’amarin bikin zai kasance.

***

Rana bata ‘karya, sai dai uwar ‘diya taji kunya, domin ranar asabar da yamma bayan anyi ‘daurin auren Nuradden da safe a kaduna, da rana aka ‘daura na su Ibrahim, Kabeer, Yusuf. Sai na ‘Alhaji Saminu Taura da amaryar sa Hafsat Khaleel Mai Mota, sai ‘Alhaji Muzammil Rimi’ da amaryar sa Hidaya Khaleel Mai Mota. A satin ne kuma Nusrah matar Saifullahi ta haihu, tasamu ‘diya mace, aka sanya mata Nabeelah sunan mahaifiyar Saifullahi, amma xa’a dinga kiran ta da Nana.

Yawan mafarkai kala-kala da yawan firgita su Haj Aysa keyi akai-akai , gaba d’aya ta zabge, sihiri ba karya ba kallo d’aya xakai mata kasan jifanta akeyi, hakan yasanya Yakolo yiwa Dr Khaleel shawara kan ya canzawa Aysan gidah. Domin kishiyoyi sun sata a gaba, Hakana Helwa data samu ciki sai ya b’are. Ganin haka yasanya Dr Khaleel gyara wani gidan sa dake kusada gidan su Humairah wato gidan Alhaji Mommodu Mele. Nan ya mayarda Haj Aysa da Helwa, Ai kuwa sun sami sauk’i bayan anyiyyi musu add’uoi sun kuma yi amfani da ganyen magarya. Can gidan kuma yakoma daga Yafendo sai Karimatu, wanda har yanzu ba su sauke ‘damarar shiga malaman da suke yi ba.. Abun dai sai dai muce Allah ya kyauta kawai...


*GIDAN ALHAJI MOMMODU MELE*

Shiirye-shryen tarbar dawowar Khaled ake daga ‘kasar Spain, masu aikine keta kara-kaina........









_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_🧕🏼
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 22-23_*

_SHAFIN YAU NA KUNE ‘YAN GRP DIN *HAJJAH CE NOVELS*, MUSAMMAN *@MAMANSADEEQ💗💗💗 & @PRETTY JIDDAHLURV_ *._INA GODIYA ‘KWARAI DA YADDA KUKE BIBIYAR LITTAFIN *SAIFUL_ISLAM*_

_nanahafsat.wordpress.com_


*GIDAN AJI MOMMODU MELE*

Shirye-shiryen dawowar Khaled akeyi daga ‘kasar Spain, gaba d’aya masu aikin gidan ne keta kara-kaina a kitchen suna had’a masa abinci komai atsare. Lokaci zuwa lokaci Haj Latifa (mahaifiyar sa) kan shiga kitchen ‘din don ganin anyi komai a tsare, kuma cikin tsafta.

Haj Latifa na tsaye jikin kitchen cabinet, tana gyarawa wata mai aiki yadda xata hada ‘coleslaw’. Humaira tashiga cikin kitchen ‘din, tana tafe tana gyara zaman agogon ta dake ‘daure a wutsiyar hannunta. Sanya take cikin abaya baka tayi rolling kanta, hannun ta rike da y’ar purse ‘dinta.

Hannu tasa ta ‘dan gutsiri maras da ake yayyan kashi ta jefa a bakin ta, kafin tace,

“Umma. Zanje gidan su Islam, zandawo kafin a ‘dakko Ya Khaled a airport.”

Kad’a kai Haj Latifan tayi, kafin tace,

“Karki jima Humaira, nasan halin ku idan kuka had’u da Islam.”

“Insha Allah Umma.. Sai na dawo” ta fada tana ficewa daga kitchen din

“Allah ya tsare... “

Sai kuma ta juya wajen Kande mai aiki, tana gyara mata yadda take ‘kokarin danna naman akan abun gashi.

“Ha’a Kande ki bari naman yayi marinating kafin kiyi grilling mana haba.”

*DR KHALEEL’s*

A kitchen Humaira ta tarar da Islam tana tuk’in tuwo, ta rage gas tana jiran ya turara ta sauke shi, da gudu Islam tai hugging Humaira cike da jin dad’i, Humaira ta yatsine fuska tana bin Islam da kallo,

“Ke kam kinason girki, ‘karama dake kike girki? bayan ga masu aiki.”

Girgiza kai Islam tayi, tana jaddadawa Hari mai aiki ta kwashe tuwon, cikin murmushi tace da Humaira,

“Babes, wallahi tun banaso sai da na koya, Ammi tace hakan nada kyau idan nayi aure na huta, Ai kuwa tuni yanzu kinga yadda na iya abinci kala-kala kuwa?”

Tabe baki Humaira tayi, kafin tace.

“Hu’uhm! Ni kuwa na tsani girki, kuma idan nayi aure masu aiki Umma xata dakko su dinga yi mun”

Kad’a kai kawai Islam tayi, taja hannun ta sukai sama, dakinta suka shiga, Animation cartoon ta saka musu na ‘princess and the frog’. Suna cikin kalla Lee tazo, nan suka kafa dabar hirar school, zancen auren su Hidaya ya shigo, Humaira ta tsunture da daria tana rufe baki, kafin tace.

“Naga mazajen su Hafsat a album na ‘daurin aure, wannan ai sun haife su.”

Lee ce ta amshe tana,
“Maganin su kenan, sun janyo at early age anyi musu aure.”

Islam dake gefe ta katse su tana daga hannuwa,

“Abeg abeg, enough. Su ai yanzu sun huta tunda sunyi auren su.”

Lee da Humaira suka tafa, suna kyalkyala daria, kafin Lee tace.

“Kowa zeyi ai, ni kin tunomin ma Dawood ya isheni da maganar aure wallahi, nace mishi ni ba yanzu xanyi aure ba yaki yadda”

Humaira ta kwashe da daria,
“Wallahi nima Yaseer ya isheni, nace mi shi sai na zama accountant tukun sa..”

Lokacin jin Islam ya dauke, tuni ta fada duniyar tunani. Ita kam haka xata xauna ba xatai aure ba kenan? Shin me tayiwa maza da ba sa sonta haka?, Ta jima tana tunani sai da zazzafan dundun da Lee ta zuba mata a baya ya dawo da ita dunia. Cikin daria Lee tace,

“Haba girly, tun daxu muke magana kinyi shunning dnmu, bama wannan ba tashi mu raka Humaira gidah, brother dinta ya dawo.”

Mikewa Islam tayi, a tare suka sauka kasa parlorn Hajia aysha suka mata sallama, sannan suka tafi gidan su Humaira.


*GIDAN ALHAJI SAMINU TAURA*

Zaune Hafsat take tana tsiyayar da hawaye agefen murhu, tunda aka kawo ta gidan take aikatuwa, Haj Larai babbar matar Alh Saminu ta takura mata da tsangwama, yau ma dakyar ta iya ‘karasa tuka tuwo a babbar tukunya mai cin kwano biyar, duk ya ‘kone ya koma tamkar amala.

Daga ‘dakin ta Haj Larai tafito, da yake kowannen su ‘daki d’aya da parlor ne mallakin sa, sai yammata xagada xagada ‘yayan Haj Laran, wanda kowannen su ya girmewa Hafsat nesa ba kusa ba. Rissinawa Hafsat tayi tana cewa,

“Aunty na kammala..”

Ashar Haj Larai ta lailayo ta ‘durawa Hafsat, Tare da bata kyakkyawan ranqwashi a ‘kwanyar kanta,

“Yanzu ke a gidan uban ki haka ake tuwo? Okay na tuna fa ke shafaffiya ce da mai, renon kwanfilas (cornflakes), to bari kiji bar ganin Alhaji na rawar takashi akan ki, wallahi tallahi idan kika ci gaba da ‘kona abincin gidan nan sai na lahira ya fiki jin dad’i.”

Cikin tsawa ta sake cewa,

“Wuce ki bani waje, banza mamugunciya, jia kin dafa taliya ta koma tamkar kunu, yau kin maida tuwo kamar..”kasa ‘karasawa tayi tana haki, cikin iko tasa babban hannun ta tana dungure mata kai.

Bata hak’uri tayi had’e da yin sum-sum ta mike ta koma ‘dakin ta, lokaci xuwa lokaci hawaye ke y’ar tsere akan fuskarta, a hankali cike da tausayi take mai-maita,

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”


*GIDAN ALHAJI MUZAMMIL RIMI*

Hidaya ce tsaye a tsakar gida tana tular wankin braziers da su pants na ‘yammatan Haj Deluwa matar Alhaji Muzammil, tana yi tana d’aga hannayenta tana share gumin dake kwararo mata,

“Ke..” Fareedah babbar ‘yar Haj Deluwa takira Hidaya,

“Na’am” Hidaya ta amsa jikin ta na ‘bari.

“Ungo nan ban had’a miki da shi ba, yanzu na cire shi, kisa hypo ya wanku tatas..”

Sa hannu Hidaya tayi ta karba tana kukan zuci. Domin pant ne gaba d’aya ya jike da jinin al’ada, sai ‘karni yake.

A ruwa ta jikashi tana mai canza mai ruwa lokaci zuwa lokaci. Sosai tafara hawaye ganin Fareedah tabar wajen. Ko’a mafarki bata tab’a tsammanin irin wannan rayuwar ba, ita kanta panties dinta a washing machine take sa su lokacin da take Abuja, amma yau wai itace mai wanke na wasu mai ‘dauke da jini, jinin ma na al’ada. Wani abun takaicin ma Haj Deluwa idan ‘yan rashin kirkin suka tashi har sakar ‘duwawu takeyi ta narka uban kashi ta kuma tashi ta barshi, Hidayan kuma ya xama dole ta kora ruwan(flushing). Da dare kuma Alh Muzammil ya maida ita sex machine, budurinsa yake akanta, ko tunanin ita ‘din yarinya ce baya yi.

*BAYAN WANI LOKACI*

Sosai Islam shakuwa ta shiga tsakanin su da Khaled , takanas yake zuwa har gidan su suyi hira, ko kuwa ya kira ta wayar Ammin su yaita janta da hira, hakan ya sanya Islam sawa a ranta lalle khaled sonta yake da aure kuma.

Ganin irin muguwar shakuwar da sukai, Humairah ta tseguntawa Umman su wai soyayya Islam da Ya Khaled suke yi, cike da jin dad’i Haj Latifa ta samu Khaled da maganar Islam, tashin farko ya kwaso rantsuwa ya dire tare da ‘doriyar,

“Tab! Umma kenan. Ni wallahi ba son Islam nake da aure ba, na ‘dauketa tamkar Humaira a zuciata, kuma yarinyar she’s fun to be with. Tanada ‘ko’kari..”

“Naji-Naji... Amma duk wannan alamun soyayya ne Khaled, wallahi yarinyar mutuniyar ‘kwarai ce, kuma mahaifiyar ta baka ga yadda muke mutunci ba..”

Daria Khaled ya shiga yi harda rike ciki, harara Haj Latifa ta xabga masa ,hakan yasanya shi rage sautin dariar sa, cikin gaskiyar sa yace.

“Allah Ummah.. Dagaske ba son Islam nake ba, already ina da wadda nake so wallahi, kuma har munyi alqawarin aure”

Fushi Haj Latifa tayi da Khaled, ta mike tai ficewar ta, shi daria ma abun ya bashi wai suna soyayya da Islam, yana cikin daria wayarsa tafara ‘kara, Islam shine sunan dake yawo akan screen din wayar sa, ‘dagawa yayi ya kara a kunnensa,

“Hello Ya Khaled” zazzak’ar muryar Islam ta doki kunnen shi.

“Sisto!” Yafada yana ‘kara gyara kwanciyar da yai akan pillow.

“Ya Khaled inason maka wata magana.”

Mikewa yayi yana gyara button din rigar sa,

“Magana sis? Yaushe kikeson gani na?”

“Ko yanzu ma.” Tafada tana jan ‘maa din.

“Okay I’m on my way.”

Ya katse kiran bayan sunyi sallama, a gaggauce ya canxa kayan jikinsa ya fesa turaruka, da kafa ya tafi gidan su Islam domin ba wani nisa. Yana zuwa ya kirata. A parlorn baki ta same shi, sanye take cikin laffaya baka tayi kyau sosai. Cikin salon maganar sa dake tafiya da ‘yammata yace,

“Kinyi kyau Mi lady.”

Murmushi tayi tana wasa da zoben yatsanta. Cikin shagwababbiyar muryar ta tace,

“Ya Khaled ina yini?”

“Lapia lou kanuri babe.. Ya su Ammi?”

“Ammi tana parlor, lalle ake mata”

Kad’a kai yayi yana sipping ruwan data kawo masa, yasha sosai kafin yace.

“Toh Mi Lady gani ko”

In’ina (stammering) tashiga yi,

“Ya Khaled da..Dama.. ca..nai”

“Menene Mi Lady uhm?” Yafada yana sake komawa kujerar dake kusa da tata.

Rufe fuska tayi, kafin cike da kunya tace.

“Ya Khaled, dan Allah kazo muyi aure, tunda kaga muna soyayya da kai.”

Baki bude yake kallon Islam, inde shirin da suke ta dauka soyayya ne, lalle ya yadda batasan meye soyayya ba, ba kuma tafara taba har yanzu. Cikin dakewa yace,

“Ni zaki aura? You are not serious” Yafada hade da mikewa tsaye.

Durkusawa tayi tana k’ok’arin zubar da hawaye,

“Wallahi Allah ina sonka Ya Khaled, dan Allah ka yadda ka aure ni kar ayimin auren dole, Na yadda ko ranar daurin auren ne kace kafasa aure na dan Allah, ko kuma ka...”

Dakatar da ita yai, ta hanyar ‘daga mata hannu, cikin ‘dagawar murya yace,

“Haba Islam, dududu shekarunki nawa? Idan kinyi nisa kiyi sha takwas, shirin da muke irin na yaya da ‘kanwar sa shi kika ‘dauka a matsayin na saurayi da budurwa? kowa da kike gani idan har Allah yayi yanada rabon aure wallahi zeyi, kuma wani baya auren matar wani, haka zalika wata bata auren mijin wata. Duk inda kike a fadin dunia wallahi mijin ki na nan zuwa, Kiyi hak’uri Islam, wallahi ni ba son aure nake miki ba, na daukeki a zuciata tamkar Humaira. Kisani cewar slowly but surely khairan Insha Allah... Naki readymade din mijin na nan zuwa, wanda yafini komai da izinin Allah. Kiyi hak’uri pls , ki yafemin dan wallahi inada wanda naiwa alqawarin aure.”

Yana gama fada ya fice yana goge hawayen dake neman zubo masa, Islam kuwa tuni ta sulale awajen tana kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara, a yau takara tabbatarwa ita din bakin jini ne da ita, wanda lokaci d’aya ta cire soyayya da son aure a ranta. Dakyar ta iya mikewa ta koma sama, Ya Bala takira a waya ta sanar masa da tananan zuwa wani satin Lagos, zatai hutu kafin su fara lectures a nan Nile university dake Abuja.

***

Khaled yana komawa gidah ya hada kayan sa a akwati, sallama yaiwa Umman su kan zaije Lagos gidan Uncle Faruk( wan babansu) ya ‘dan kwana biyu kafin Vissa d’insa tafito ya koma Spain ‘karo karatun Masters.

Bata hana shi ba, domin fushi take dashi, ita ta dauka akan maganar da sukai da ita ne daxu yasan yashi ‘kaura daga garin, Batasan yayi hakanne don ya baiwa Islam lokaci ta cire sonsa a ranta.

*LAGOS*

Karfe 5 dai-dai jirgin su ya sauka a airport din Murtala Muhammad dake Lagos. Dakyar Khaled ya ciro waya ya kira Uncle Faruk cewar ya iso azo a ‘dauke shi.

Dake weekend ce Alhaji Faruk Muhammad(Uncle Faruk) yana gida da iyalin sa, matar sa Haj Zuwaira ita kadai ce sai ‘ya’yan sa mata biyu, da maza biyu.

Aisha, Fatima, Adnan sai ‘dan autan su dake karatu a America mai suna... *SAIFULLAH*









_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER; MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 24-25_*


_SHAFIN YAU NA KI NE *ZEE YABOUR* xeexeecism 😘Habeebtyn-Habeetyn baby Yasmeen💕Allah ya ‘kara basira ki cigaba da wantsalo mana FETTA_

_nanahafsat.wordpress.com_

Alhaji Faruk Muhammad ‘dan uwan Alhaji Mommodu Idris ne.Yaya ne ga Alhaji Mommodu domin iyayen su daga tsatso ‘d’aya suka fito. Ma’ana ‘dan wa da ‘dan ‘kani suke. Mahaifin Alhaji Muhammad Idris shine Yayan mahaifin Alhaji Faruk Muhammad. Zaman sa ya koma hannun mahaifin Alhaji Muhammad, domin iyayen sa duk rasuwa sukai. Anan yai karatu, har Allah ya kai shi babban matsayin da yake na likita, (surgeon).

Ya hadu da Mahaifiyar su Saifullah, wato Hajia Zuwaira a garin kano,’ bangaren galadanchi, a asibitin Aminu kano. Lokacin ita kuma sun kawo mahaifin su baida lapia, anan ‘kauna ta’dore mai tsanani har ta kai ga aure.


*4:00pm*
LAGOS (IDIROKO, MARYLAND)

Zaune Islam take, hannunta rik’e da Novel ‘din, ‘chasing Red by Isabelle Ronin’. Kusan kullum hakan take ko dai kaga Qur’an, ko littafin daya ‘kunshi harkan medicine, sai kuma novels, da suka zamar mata addiction.

Farida (Riri) ‘kanwar Haj Nabeelah ce, a gidan take a zaune tun lokacin tana ‘karama, domin sa’ar su Islam ce, tashiga ‘dakin da Islam take, zama tai akan gadon tana duban Islam da sam batasan shigowar tata ba,

“Peek a boo” Riri tafada da ‘karfi tanawa Islam gwalo, Ai kuwa Islam din ta ‘dan tsoro ta, harararta tai cikin wasa tana tura baki gaba,

“Toh shagwab’abbiya, ke kam mijin ki yaga ta kansa da tsagwaran autanci, to ni dai tashi maza, zamu ‘danje outing kiga gari.”

‘Dan yatsina fuska Islam tayi, kafin tace.

“No, not today pls, banason katse karatu na”

“Ke wallahi baki isa ba, Haba yarinya sai kace kunkuma, sannu matar ustax. Kullum kina ‘daka kamar sabuwar amarya, da anyi magana kice this and that, abeg tashi muje nan kusa ne ba jimawa zamuyi ba.”

Takaici kamar ta shak’e Riri haka take ji, a dole ta shiga band’aki ta ‘karayo wanka. Doguwar riga ta saka mai launin sararin samaniya, ta yane kanta da mayafin rigar. Fita sukai itada Riri’, domin su kad’aine ‘yammata a gidan yanzu, duk kowa ya watse. Mazanma sai dai ‘yan uwa na ‘y’ar gaya ko ‘yan uwan matan Ya Bala ‘din.

Riri ce ke driving, wani joint suka je, ba abunda akeyi sai zuk’ar shisa, joint ne daya amsa sunan joint, domin clubbing ne na maza da mata, sai raye-raye akeyi ana busar shisa. Gefe d’aya kuma kayan ‘kwalam da ma’kulashe ne. Gaba d’aya Islam kallo d’aya xakai mata kasan a matukar tsoroce take, domin sai takurewa gefe d’aya take a bayan Riri, musamman da idanun maxan wajen ke kanta. Wani table mai cin mutum biyar suka xauna, bayan Riri ta babbasu hannu sun

Please Login or Register in order to submit comment