Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

enlarging saboda kana tab’a mata su ne.”

“Get straight to the point abeg”

“Tohm.. ni..Nima xan iya yadda ka dinga hakan dani, please Hilaal save my soul”

Girgiza kai yayi alamun a’a, ya mike yana wata shegiyar mik’a ta ‘yan iska sannan yace,

“I’m sorry Hidaya.. I can’t, I won’t”

Wucewarsa yayi bayan ya d'an bubbuga kafad'ar ta, cikin kuka Hidaya ta koma hostel, Hilaal kuwa daya mike cafeteria yaje inda yaga su Islam na zuwa suna cin abinci kamar ko yaushe suna zaune ita da friends d'inta.Tashi sukai xasu bar wajen, Islam ta tsaya tana gyara leggings d'in cikin skirt d'inta, Nan santala-santalan cinyoyinta suka bayyana. Hilal ya had'iye yawu mai kauri kamar wani maye,

Gurin biyan kud'i sukaje yai hanzarin mika Atm card d’insa da yake da shi suke amfani, tsayawa sukai suna kallon sa, Shafa k'eyarsa yayi yana duban Islam tamkar zai had'iyeta,

“Excuse me please.” Cewar Islam tana k’ok’arin wucewa domin ya tare mata hanya.

Saurin tsayar da ita yayi ta hanyar sanya hannun sa d’aya ya kare k'ofar, ganin hakan ya sanya su Lee yi masa godia had'e da fita suna dariya, gaba d’aya 'yan cafeteria d'in sai kallo ya koma wajen su, jan hannun Islam yayi tana ta turjewa amman yak’i sakin ta, sai da sukai nisa ya saki hannun ta yana binta da kallo, gaba d’aya komai na jikin ta irin sa yake so tamkar kim kardashian haka yake ganin ta a idanun sa, ciki-ciki yace da ita,

“Islam..”

D'aga kai tayi tana kallon sa, sai kuma ta mayar kasa tana wasa da yatsin hannun ta, kamar xatai kuka tace dashi,

“Please.. ka kyaleni na tafi dan Allah ka tsayar dani mai zanyi maka ne?.”

Sosai muryar Islam ta kara narkar dashi don kunsan a baya itace 'yar autar d'akin su kafin zuwan 'yan biyu, Shi yasa gaba d’aya komai na autan ci take yi, shagwababbiya ce don haka take magana ma kamar wata baby,

“I like you..No! I love you Islam.” Gwalalo idanuwa tayi tana duban sa,

“Ni d'in?” Ta fad'a cike da mamaki don ba’a tab'a cewa ana sonta ba tunda take.

Kad’a kai yayi, “Eh! Ke Islam, I love everything about you, your body structure, your voice, your romantic eyes.. Kai komai naki is my heart desire”

“Sorry what?” Cewar Islam.

“Abinda kikaji nace dai shine, I love.” Saurin katseshi tayi ta hanyar cewa,

“Naji.. but I’m sorry! Banda lokacin wani Love a yanzu, beside baxan tab'a cheating sister na ba.”

Daria Hilal ya kyalkyale da ita, “Wacce sister d'in naki daga ciki?”

“Hafsat..” cewar Islam.

“Well.. Ban tab'a cewa ina son Hafsat ba ita tace tana so na, and Hidaya ma d’axu sai da tazo begging for my dear love nace a’a, amma ke nazo wajen ki shine zaki min rashin mutunci..?”

Ganin irin kallon da yake mata, ta tuno sanda ta hango hannun sa dumu-dumu a cikin rigar Hafsat, saurin kad’a kai tayi tana ja da baya,

“Kayi hak’uri...I’m not your type, Thank you” kawai tace ta bar wajen cikin sassarfa.

Dunkule hannun sa yayi ya buga ajikin bango yana fadin, “Goddamn it!”

A week d'in ne kuma aka nad’a sababbin prefects, ‘yan SS3 sune manya, yawancin babban mukami duk su aka baiwa, kananun post kuma aka bawa SS2, Islam itace ‘sanitary prefect’ Lee kuma ‘labour prefect’

Toh haka rayuwar ta ci gaba da tafia, a SS2 sukai moc exams, kuma successfully kowa ya wuce sai wanda grade d'insu ya kara k'asa, sati biyu aka basu hutu na mid term break suka dawo gidah sukai suka sake komawa. Abun fa na Hilal ba sauki domin ya dage ya zama d'an iskan k'arfi da yaji.

Ranar wata laraba Hafsaat taje hostel d'insu Islam, zaune Islam take tana karanta qur’ani, k'arar kwan chewing gum d'in da Islam taji ya sanar mata da zuwan Hafsaat d'in, karasa kai aya tayi ta d'aga kai tana bin Hafsaat d'in da kallo wadda yanzu ta rage tsoron su domin da sauki abun da suke yi mata sosai, zama Hafsa tayi tana tab’e baki,

“Ke! Bani Toilet key d'in staff” Girgiza kai Hidaya tayi alamun a’a,

“Gaskia a’a, ga na student nan ki shiga nan mana, Mrs Abigail ta hana ashiga staff toilet wallahi.”

“Malama kawai ki bani, yanzu fa xan dawo ba cinyewa xanyi ba”

Tsaki Islam tayi, ita kam tagaji da wannan rayuwar, mika mata tayi tana fad'in,

“Dan Allah kiyi sauri, idan kaki bari wani teacher d'in yagan ki babu ruwana.”

“Fine..” Hafsaat ta fad'a tana mikewa,

Fita tai da sauri, da hannu taiwa Hilal alamar ta karb'o key d'in, daga kai yayi sai data wuce sannan yabi bayanta, mai karatu na karkare muku xance dai haka Hilal ya raba Hafsaat da ‘yan matacin ta kuma martabarta yayi dis virgin d'inta, don iskanci yana kallon videon yadda aka yi haka yaraba Hafsat da budurcinta. Tasha kuka kuwa tayi dana sanin amsa masa datai kwarai matuka ta rena kanta. Hilal sai dad'i yake ji. Da kyar ta iya gyara kanta da yake cikin dare ne sannan ta koma hostel d'insu, mukullin ma kawarta ta bawa ta mayar wa da Islam.

Kafin safiya ido ya raina fata, tuni zazzabi yayi awun gaba da ita, clinic na cikin nan aka kaita, basu d'auki komai ba aka bata anti biotics da allurori na pain reliever.

D'an iskan kuwa sai ya koma kan Hidaya bai rabata da mutuncin taba amma yanakan hanya domin yaga itama kalar Hafsat d'in ce, don gaba d’aya yadda sukai da Hafsaat ta shigar dashi wani yana yi. Sai da tai kwana uku a gadon asibiti tun daga sannan taki yarda ya kara, don ta tsorata ba kad'an ba.

***

*B*'angaren ango Saifullahi kuwa ya shiga wani hali dan sai da ya cire kunya ya kai karar Nusrah gidah, ai kuwa tasha fad'a a dole ta bada kai bori ya hau, amma fa kullum sai yayi roko da taushiyar baki kafin ta yadda tabashi hakkin sa,

Ya yi mamaki aganinsa sai mace dirarriya ce kawai mai ni’ima banda siririya, ya rena kansa da tunanin sa kai dama ilimin sa a kanta ta yadda yanzu yake girmama mace duk k'ank'antarta, haka sukai ta auratayya kullum tana kukan zafi yana kukan dad'i shi kuma gashi akwai juriya da jarumta.

*BAYAN SHEKARA D’AYA*

*B N A*

SS3 su Islam suka shiga, Bilkisu khaleel (Islam) itace head girl gaba d’aya school d'in, jama’a xaku yi mamaki idan nace muku tak'ara yin kyau ga girma, gogewa kai tamkar ba ita ba sam ta dena tsoron su Hafsat da duk wata wadda zata kawo mata raini, mulki take xubawa sosai dan ba’a kawo mata raini a school d'in, bata rashin mutunci shi yasa kowa yake yabonta a students, k'ok'ari kuwa tamkar 'yar gidan google dan komai ta sani.

Toh haka rayuwar taci gaba Hafsat gaba d’aya ta dena yadda da Hilal saboda yadda taji labarin mutuncin ‘ya mace da budurcinta gidan miji, Hidaya ce dai ta xama tamkar matar Hilal d'in..

A haka suka gama BNA, Islam ce best student kuma most descent star of BNA. Sai sauran squad d'inta kowa ya samu prize. Sun kammala wa’ec and neco d'insu Lapia suka koma gidah.

Sun xama 'yan mata bama kamar Islam 'yar shekara goma sha bakwai amma yanayin siffar jikin ta tamkar 'yar 20plus. Hafsat ta kara lalacewa, Hidaya kuma ji tayi ko’ina na jikin ta ya cika, sosai kumai gashi tayi fari.

***

Washe gari su Islam suka koma gidah bayan anyi prom night da graduation dinner of BNA class of 2k14, duk tsawon shekaru biyun nan babu wanda yace yana son Islam ko cikin mazan ajin su, sosai wannan lamari ya fara bata tsoro hankalinta duk ya tashi musamman idan taga yadda su Hafsat suke tara su kamar ledojin pure water.

Da wuri suka koma suna shirin zuwa sunan matan Ya Mu’utaseer, aunty Hafsy wacce ada take Miss Hafsy ita kadai ce ta haife namiji, sauran duk mata suka haifa banda Nusrah ita cikin ta da sauran lokaci....


*GIDAN AJI MOMMODU MELE*









_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA ASHIRIN (20)_*

_Shafin yau naki ne *AUNTY RABI’A* fatan alkhairi agare ki, Allah ya raya mana Umayma da Farouk_💕

_nanahafsat.wordpress.com_


*GIDAN AJI MOMMODU MELE*

Alhaji Muhammad Idris, ‘dan asalin ‘kauyen damboa ne dake jihar bornu. Kasuwancin bututun mai yake yi(oil mogul) yanada mata d’aya da yara biyar. Haj Latifa itace matar sa, yaran sa biyar ‘din kuma uku daka ciki maza ne sauran biyun kuma, mata ne. Muhammad, Fatima, khaled, Humaira sai autan su Fahad.

Muhammad da Fatima kowannen su yayi aure, Muhammad na kaduna, Fatima kuma tana aure a kano. Khaled yana karatu a Spain. Gidah ya xama daga Humaira sai Fahad.

Unguwar su ‘d’aya da gidan Dr Khaleel, amma su a ‘kasan layin suke. Humaira itace sa’ar Islam domin makarantar su d’aya ma, ita Humaira na accounting shysa class ‘dinsu ya banban ta, amma kawaye ne su tun suna ‘kanana, komai tare ake musu, hakan yasanya aka sasu makaranta ‘d’aya ta sakandire.

Sanadiyyar zazzafan ‘kawancen su, hakan ya ‘kulla babbar shak’uwa tsakanin iyayen su, sosai Dr Khaleel yake da share a d’aya daga cikin kamfanonin bututin man Alhaji Mommodu. Hajia Latifa kuwa ‘kawance sosai sukeyi da Haj Aysa, kusan kullum tana gidan suna zantawa.

***

Shiryawa kowaccen su tayi cikin shiga ta alfarma, lokacin da xasu tafi gidan sunan a time din Marwa tadawo tana ta sauri flight dinta yakusa tashi xata koma ‘kasar su, sallama sukai da Islam wadda duk tasake jin ba dad’i, ganin yanzu sai ita kad’ai babu kowa sai yan biyu dake ‘dan ‘dauke mata kewa suna tafiya ko’ina dan tuni har an yayesu, surutu a bakin su tamkar gidan radio.

Gidan sunan suka tafi, Farfajiyar gidan nan tasha decorations, ga abinci nan kowa xeyi serving kansa, masu jego sunci ado su Shema’u sai felek’e akeyi ita ga wadda ta haihu, ‘Aunty Rama’ ma tasha kyau, tana tsaye suna buga selfies da yan uwanta, wanda kallo ‘ ‘d’aya xakai musu kasan ba ‘yan Nigeria ba ne. Sashen ‘Aunty Hafsy’ suka shiga ganin bata wajen sunan, tana zaune tana gyara kwantacciyar sarkar gwal din ta,’ mai makeup na gyara mata ‘daurin ‘dankwali ,

Tana ganin su ta fad’ad’a murmushin ta, tana musu sannu da xuwa,

“Kinyi kyau Aunty Hafsy” cewar Hafsat,

“Godia nake ‘kanwata, baki da lapia ne?” Aunty Hafsy tafad’a tana ‘karewa Hafsat kallo.

‘Daga kai Hafsat tayi alamun eh, kafin tace,

“Eh wallahi Aunty, typhoid na keyi”

“Ayyah, Sannu Allah ya sawwake.”

“Amin”yan ‘dakin suka amsa.

Aunty Hafsy ta sake cewa,

“Sunan Daddy(Dr Khaleel) aka saka wa babyn, amma zamu dinga kiran sa da ‘Sultan’” Ta d’ora da,

“Yammatan gidan mu, gaskia kunyi kyau, yadda muke da yammata zankad’a-zankad’a haka gaskia billionaires zamu samo duk mu aurar daku”

Yatsina fuska Islam tayi tana tura baki gaba, ita sam auren ma ya fice akanta, gani takeyi batada rabon yin sa, dubada ba wanda yake sonta, sai dai su so jikin ta, ita kuwa tafison wanda zai sota tsakani da Allah, ya ‘kaunace ta ba dan yanayin siffar jikin ta ba, cikin ‘kunkuni tace,

“Gaskia aunty a’a badai yanzu ba, duka-duka fa shekaran jia muka gama secondary school, talkless of university ga medical stuffs.”

“Yen yen yen, Abeg duk kwayi a ‘dakin maxajen ku” cewar Aunty Hafsy.

Ita dai Hafsat dake gefe danne-dannen wayar ta take yi, Hidaya ce ma mai saka baki, tana maganar ita kam ko gobe a ‘daura mata aure a shrye take.
Sun ‘dan taba shafta, kafin su sauka ‘kasa wajen suna, an sha suna, anci an gyatse, an yi rabo, kowa ransa yayi fes, Nusrah ce kawai ke lallab’awa don itama takusa haihuwa, har aka gama tana zaune, sai da sukai isha’i sannan suka koma gidah.

Ganin Dr Khaleel ba ya ‘kasar, hakan ya baiwa su Hafsat da Hidaya damar tsayawa suna xance a waje, ita Hidaya Hilal ne yazo mata sallama zai tafi ‘kasar waje inda aka bawa mahaifin sa ambassador for peace dake wakiltar Nigeria a Johannesburg, Hafsat kuma wani saurayin ta ne da suka hadu a Twitter.

Islam ce kawai tashiga gidah, sashen su ta nufa ranta duk ba dad’i, ta rasa mai yasa ita har yanzu ko da wasa wani bai taba cewa yana sonta ba, sai dai don siffar jikin ta, ajiyar zucia ta sauke, dede lokacin Yakolo tashigo janye da hannun su Areef.

“Ke kuma menene kike faman magana ke kadai..?”

Yakolo tafada tana zaunar dasu Areef a kusada Islam, ai Islam batasan ma maganar zucin da take tafito fili ba, cikin ‘karfin hali tace,

“Wani littafi nake memorizing sunayen ciki..”

Murmushi Yakolo tayi, cikeda jin dadi tace,

“Yadda kike son karatun nan Allah ya cika maki burin ki ki zama cikakkiyar likita,”

“Ameen Aunty..”

“Yawwa ga yan biyu na nan, ku zauna zanje wajen Alhaji Gali”

(bazawarin ta ne, kuma babban abokin Dr Khaleel ne, domin ta sanadiyyar ziyarar da yakawo gidan ya ‘kyallara ido ya hango Yakolo, Tuni tatafi da zuciar sa, shi kuwa yace yayi mata, don dama matar sa bata jima da rasuwa ba).

“Tohm Aunty..”

Har taje ‘kofa ta juya,

“Yawwa. Karki tashi Yayya(Haj Aysa) bacci take yi, kuma kakki bari yan biyu na su fita dukda matan gidan ba sanan, Akwai sanyi yau”

Kad’a kai kawai Islam tayi, Yakolo tafice tanata zuba kamshi, Kallon cartoon Islam ta kunna musu, a madedeciyar Tv dinta dake jikin bangon ‘dakin. Sannan ta muskuta ta kwanta sosai tana zubda ‘kwallar wannan dankararren bakin jini dake tattare da ita, mamaki take yi wai har Yakolo dake bazawara ruwan farin jini ne da ita, amma ita ‘kemad’agas babu ko ‘digo.

Karimatu ta biyawa kanta kudi ta tafi Dubai ,Yafendo da Helwa kuma kowannen su yaje ganin gidah, gidah yarage sauran Haj Aysa kawai da Inna Bilkisu, wadda tazo ganin ‘yayan da jikokin ta suka haifa mata (tattab’a kunne).

Kwana biyu da suna Dr Khaleel ya dawo daga international conference ‘din da yaje halarta a America. Wurin Inna Bilkisu yaje ya kai gaisuwa, sannan ya wuce sashen Haj Aysa ya baje ya huta, yaci abinci. Da safe kuma ya tara yaransa ya babbasu tsarabar su. Amma baiga Hidaya ba, ya tura akirata akace bacci take batada lapia.

Da kansa yaje sashen Yafendon, Islam ce kawai sai yan aiki, domin Yafendon taje ganin gidah, dakinta yashiga ya sameta rike da ciki tana ‘murkususun ciwo. Da sauri yasa mai aikin su ta gyara mata jikin ta, ya sata agaba su tafi asibiti, likitoci ne suka rufu akanta suna gwaje-gwajen su. A waje kuma Dr Khaleel ne dafe da kansa yana girgiza shi, tabashi tausayi yadda take rike da marar, cikin fuzgar da iskar bakin sa yace,

“Kila ciwon su ne na mata”

Dr Hindu ce ta fito daga emergency area tana nufar inda Dr Khaleel ke zaune, tana tafe tana cire hand-gloves din hannun ta, ganin ta yasanya shi saurin mikewa,

“Dr..” yace da ita yana jiran tabashi ‘karin bayani.

Numfasawa tayi kafin tace dashi,
“Na’am dr, nace yarinyar tana ‘d’aya daga cikin yaran ka da akai auren su ne?”

Girgiza kai yayi, cikin dakiya yace,

“No bata ciki, Hidaya ce wannan, d’aya daga cikin ‘kananan yara na”

Dan yatsina fuska tayi, kafin tace,

“Toh, nayi mamaki gaskia s..”

Bata k’arasa ba Dr Khaleel yai hanxarin katseta ta hanyar cewa,

“Dr.. get straight to the point pls!”

Ajiyar zucia ta sauke kafin tace,

“Kayi hak’uri, abunne da ‘dan rudani aciki, at first mun ‘dauka menstrual cramps ne, to se bayan da cikin ya ‘kara hautsinewa muka fara ‘k’ok’arin mata scanning, nan kuma jini yafara fita daga ‘kasanta, atakaice dai tayi ‘barin cikin dake jikin ta, da mukai scanning m..”

Katseta yai, yana ‘daga mata hannu,

“Look Dr Hindu, Hidaya dai yarinya ta da tagama secondary satin baya? She’s just 17.. No it can’t be.”

Murmushin takaici Dr Hindu tayi,
“Kayi hak’uri, amma wannan kasan aiki na ne, Gynecologist ce ni, baxanwa yarinyar ka sharri ba, wallahi ‘karamin ciki tayi ‘barin sa, domin inaga kamar ya ‘dan fara kwari ma.”

Gaba d’aya ji da ganin Dr Khaleel sai suka ‘dauke na ‘yan wasu da’ki’kai....





_Have a blessed weekend ahead_💕





_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 21-22_*

_Shafin yau naku ne ‘yan *RANO ONLINE NOVELS*, Ha’kika duk wata writer da ke cikin group ‘dinnan kuna ‘kara mata ‘kwarin gwiwa da da’da’dan comments ‘dinku,Nagode k’warai da yadda kuke bibiyar littafin *SAIFUL_ISLAM*. Allah ya saka da alkhairi🙏🏾💕_

_nanahafsat.wordpress.com_

Tuni numfashin sa ya fita, ji kake tim ya fad’i a ‘kasa, cikin kidimewa dr Hindu ta kira drs maza suka dauke shi aka fara bashi temakon gaggawa, ita kuwa Hidaya tana can tana bacci saboda allurar da akai mata,

Jin shiru basu koma ba, yasanya Haj Aysa kiran wayar sa, bai ‘daga ba domin tana silent, director din asibitin ta kira inda yake sanar mata Ai da shi da y’ar duk an kwantar dasu, cikin firgici ta shirya ta nufi asibitin itada Yakolo. Sai dai har lokacin Hidaya da Dr Khaleel basu farka ba sai washe gari,Duk wani gwaje-gwaje anyi masa babu wani abun da ya same shi sakamakon bugar da yau, kawai dai yasamu rauni a gefan goshin sa, da kuma ‘dan yatsan sa na hagu da yai targad’e.

*WASHE GARI*
Da safe tuni asibitin ya cika da yan uwa, ganin duk sun farfad’o ba wani matsala, yasanya likita sallamar su bayan yabasu magunguna.

Hidaya dai batasan me ke faruwa ba, haka ma Dr Khaleel babu wanda ya fad’awa, sai da suka warke sukai ras lokacin da sati ya zagayo duk yan uwa sun hadu xa’a fara bikin Nuraddeen ‘dan Ya Bala da ya’yan Hansa’u su biyu Kabeer da Ibrahim banda autan su Yusuf. A time din Dr Khaleel yace yanason ayi general meeting bayan anyi isha’i.

Ya kuma kira Yafendo da Helwa kan lalle su dawo a ranar, dama ita Karimatu da safe jirginta ya sauka, tayo siyayya fal. Kafin lokacin meeting, Yusuf ‘dan Hansa’u yaje sashen Inna Bilkisu, matashi ne ba canba amma, domin baifi shekaru ashirin da biyu ba.

Bayan ya gaisheta, ya sa hannu yana shafa ‘keyar sa, Tana lura dashi, ‘dan murmushi tayi kafin tace,

“Me ke tafe dakai Yusuf”

“Inna dama..Dama” sai kuma yayi shiru, kansa a ‘kasa.

“Dama me?! Fad’i ina jinka, kaga ba kowa daga ni sai kai sai Allah”

Cikin rawar murya yace,
“Inna dan Allah.. Dama so nake kiyiwa Baba(Ya Bala) magana, Dan Allah ni..Nima ai mun aure.”

Baki bude Inna take bin Yusuf da kallo, sai kuma ta rufe tana jinjina kai,

“Toh shikenan babu damuwa, amma yanzu kai Yusuf kanada wacce kake so ne? Shin zata iya auren ka, alhalin yanzu kake bautar ‘kasa ko aiki baka dashi?”

Cikin dakewa ya ‘daga kai,
“Eh inna ina da ita, domin iyayen tama sun amince sunce na turo manya na.”

“Dakyau..” Inna tafada tana daria.

Sosa ‘keyarsa yayi yana saurin mikewa ya fice,

Kusan karo sukai da Ya Bala da Dr Khaleel dake k’ok’arin shiga parlorn wajen Inna, ganin su yasanya ta fad’ada murmushin ta,

“Yawwa ku kira Hansa’u ma tazo, zamuyi magana”

“Tohm Inna” dukka suka amsa a tare.

Dr Khaleel ne ya daga waya yakira Hansa’u, mintina kalilan sai gata tashiga wajen su, gaggaysawa sukai aka taba hira, sannan inna ta sako zancen Yusuf.

“Yawwa wannan yaron, Dan Allah inaso a had’a auren nan ayi dana Yusuf..”

Gwalalo ido sukai dukkan su kafin ya Bala cikin kidimewa yace,

“Inna! Yusuf dai Yusuf namu?” Yafada yana nuna bakin kofar da suka hadu fa Yusuf,tamkar Yusuf dinne awajen.

“Eh shi dai..”cewar Inna..

Hansa’u da Dr Khaleel suka hada baki wajen cewa,

“Inna meyasa kika yanke hukuncin haka?”

Ajiyar zuciya inna ta sauke kafin tace,
“A har kullum idan yaro ya nuna yana son aure gwara ayi masa, kafin ya janyo abun kunya. Domin duk yaran da kaga ya bude baki yana cewa ai masa aure to lalle gwara ai masa, domin ya matsu ne, kuma gata ne sannan ‘kara kamalar su ce da shirya kai dama ceto rayuwar su daga fadawa kogin halaka, da ace anayin haka da yawan zinace-zinace ya ragu.. Yadda ya fadamin ma yace iyayen yarinyar ma sunce ya turo magabatan sa, kunga kuwa Alhamdulillah”

Jinjina kai sukai, kwarai sunyi na’am da xancen, Dr Khaleel yace,

“Masha Allahu, kwarai naji dadi, kuma ni nayi alqawarin daukar dawainiyar auren sa, gidan da xai xauna ma ya xabi apartment d’aya a estate din da su Mu’utaseer suke. Allah yasanya albarka”

Addu’a sukai gaba d’aya duka, suna ‘kara mamaki. Sai da aka nisa sannan Dr Khaleel yace,

“Toh inna dama nima abunda ke tafe dani zancen Hidaya ne, na so sanar da ku kuma , sai kika kwanta zazzabi na har maganar duk sanda kika wartsake sai na sanar da ku duka..”

Shiru sukai suna sauraron sa, hakan ya bashi damar ci gaba,

“Toh Nide satin baya ne, nadawo daga tafiya na babbawa yaran nan tsabar su banga Hidaya ba, na aika akirata akace batada lapia, to na sata dai a gaba mukaje asibiti..” shiru yai yana ‘dan tari hade da sauke nannuyar ajiyar zuciya. Hawaye fal idonsa yake karasawa,

“Mukaje asibiti likitoci sukai gwaje-gwajen su, Na karkare zance dai Hidaya ashe ‘bari tayi, wai ciki ne d..”

Be k’arasa ba, suka hada baki wajen fadar,

“Ciki?!”

“Kwarai ciki, amma tayi ‘barin sa” ya karasa fada hawaye na zirarowa daga idanun sa.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un..” shine kalmar da suketa maimatawa,

Gaba d’aya sai parlorn yai tsit sai kakarin kukan Hansa’u da Dr Khaleel, Ya Bala ne yai ‘karfin halin magana,

“Amma meyasa sai yanzu ka fada Khaleel?! Shin wane mataki ka ‘dauka a kai kenan?”

Cikin kuka yace,
“Yaya wallahi gaba d’aya na kasa samun nutsuwa, ni da anawa shirmen na dauka irin wannan abun sai mutum ya aikata zina ne ake ramawa akan ‘ya’yan sa, wallahi kwana da kwanaki tunanin da nakeyi kenan, shin ko na tab’a aikata irin wannan mummunan zunubi ne a baya, batare da na sani ba?”

Girgiza kai Ya Bala yayi, cikin muryar ban hak’uri yace,

“Wallahi a’a Khaleel, babu nutsatstse kaf dangi irin ka, kanada ladabi, biyayya, da zumunci , wallahi qaddara ce kawai da dama can muqaddari ne daga Allah, wanda bamu isa mu canxa ba, sai dai yanzun abunda na keso na sani shin ina ita Hidaya take?”

Hansa’u taja majina, kafin tace.
“Amma Wannan yarinya ta cucemu, Allah dai ya..”

Katseta Inna Bilkisu tayi ta hanyar ‘daga mata hannu,

“Kowa da tasa qaddarar Hansa’u, kuma xai iya yiwuwa ko fyade aka mata, tunda ciki lokaci d’aya yake shiga ,Toh kila anan tasamu”

Girgiza kai Ya Bala ke tayi yana magana shi kadai, kafin ya dubi Dr Khaleel yace,

“Shin ko hakanne yasa kace akwai general meeting yau?”

Kada kai Dr Khaleel yayi alamun eh.
Waya Ya Bala ya janyo ya kira Yafendo, bugu biyu ta ‘dauka yasa ta turo masa Hidaya sashen Inna Bilkisu.

Hidaya bata dauki lokaci ba, tashiga ciki bakin ta dauke da sallama, bata kawo komai aran taba, domin batasan ma anyi hakan ba, shigar cikin, samun sa ballantana ‘barewar sa.

Gaishe su tai, sannan ta nemi waje ta zauna tana fadin,

“Uncle B! Gani.”

“Hidaya..” Ya Bala ya kirata

“Na’am Uncle B.”

Ya sake maimaitawa har sau biyu,kafin yace.

“Sau nawa na kira ki Hidaya?”

“Sau uku Uncle B”

“Yawwa...Shin inaso ki gayamin gaskia tsakanin ki da Allah waye yayi raping dnki?”

“Rape..?!”

Ta maimata a fili, kada kai Ya Bala yayi yana nazarinta,Babu alamar tsoro a tattare da ita, domin da hakanne jikin ta zai nuna, ‘dan yatsina fuska tayi kafin tace,

“Uncle B. Wallahi ba wanda yai raping dina.”

“Okay likitoci ‘karya suke yi miki kenan? Ke!” Ya daka mata tsawa.

Jikinta ya hau rawa, tana jin sanda fitsari ya zirara a pant ‘dinta. Maka mata harara yayi, tuni launin fuskar sa ya canxa, jijiyar goshin sa ta ‘dad’daga ya sa yatsa yana mai nuni da ita,

“Kinga Hidaya , ki kuka da kanki idan har baki fadamin gaskia ba.”

Kuka tafara tana yarfe hannuwa,
“Uncle B, dan Allah kuyi hak’uri.”

“Hakurin uban ki, xaki bude baki ki gayamin wanda ya miki ciki ko sai na kira makarantar da kaina na tambayi da wane shegen kike mu’amala..”

Nan tagano ashe Hilal ne, abunda suke aikatawa shine ya sanya ta awannan halin da take ciki, Hawaye d’aya nabin ‘d’aya, majina na kwarara daga hancin suna y’ar tsere akan fuskarta, tasa

Please Login or Register in order to submit comment