Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne akan son yin aure? Basu san komai lokaci bane da baza su hakura ba har sai sun wulak'anta kansu a gurin mutane. Ya karajin haushin ta ya kuma raina ajinta uwa uba yaji tsanarta a cikin zuciyarsa yana tunanin ma 'yar iska ce tunda har take cewa maza su aureta dan yasan ba wai Khaleed ta fara furtawa hakan ba.

'”Wai kana jina sai nayi ta maka magana kana jina dan wulak'anci ko?'” Khaled yayi maganar yana kallan inda Saifullah yake, sai da ya d'ago ya kalli Khaled sannan yace.

'”Yah ina jinka amman me kake son nace maka a cikin maganar taka? Kace min kana jin tausayin kuma ta nuna maka buk'arta na son ka aureta kace kana da wata, toh ina tausayin da kake mata ya tafi? Menene yasa ba zaka aureta ba kodan ka ceci rayuwarta daga fad'awa auran sa'an mahaifinta?” Khaled ya kallesa da sauri yana zaro idanuwa yace.

'”Wai kana nufin na aure su duka biyun?”

'”Eh mana ai zaka iya tunda kanada ragowar imani.'” Da sauri Khaled ya fara girgiza kansa alamun ba zai iya wannan b'arnar ba wadda Saifullah yake k'ok'arin cusa shi.

'”Bazan iya ba gaskiya, zan dai cigaba da yi mata addu'a Allah ya kawo mata mai kaunarta, amman gaskiya ni ba auranta zanyi ba sabida akwai wadda ta shiga can cikin zuciyata.”

Tattare kayan Saifullah yayi tare da barin d'akin domin Khaled ya isheshi da surutun da shi kansa bashi da mafitarsa, uwa uba kuma dama jiran lokacin da ya bashi ya gama magana ya cika, fita yayi can zuwa study room dan nan ne kawai gurin da zaije yaji dad'in zama kuma yasan Khaled ba biyosa zai yi ba domin ko ya biyosa yasan ba kulashi zai yi ba.

Can b'angaran su Islam kuwa gabaki d'aya Riri ta isheta da maganar Khaled, har zancen yasa Islam ta fara zargin wani abun tace da ita.

'”Wai Riri menene a cikin zuciyarki daga ganin yaya Khaled?”

'”Ah mekika gani?'”

'”Ji nayi tun a hanya sai tambaya ta kike yi akansa, nace miki aure zai yi kwanan nan kuma wallahi ba zai soki ba domin...”

Sai kuma tayi shiru ta kasa fallasa sirrin zuciyarta dan kar Riri ta sake rainata, cikin yatsina fuska Riri tace.

'”Toh dan zai yi aure so what? Ni kawai so nake mu zama abokai dashi bawai muyi soyayya ba na gansa zai kankaro min mutunci idan muna tare da kawaye na.”

'”Allah ya shiryeki Riri wallahi halinki sai ke ni bazan iya miki ba.”

Daga haka Islam bata sake kula Riri ba sai ma kwanciya da tayi akan gado saboda tayi bacci ta huta.

*ABUJA*

Saukar sa kenan a garin Abuja, a gidan su Khaled ya fara sauka kafin yaje can inda zai gudanar da aikinsa, Umman su Khaled sai murna take yi yau ga Saifullah a gidan ta dan ba zuwa yake yi ba sosai ya dad’e, khaled yafi shi zuwa can lagos, koda yake yanayin su ba daya bane kasan cewar Saifullah baya shiga cikin mutane komai da yake yi yana da lokacin yinsa koda kuwa aski ne yana da ranar da yake yi da kuma lokacin yi bare kuma zuwa gidan 'yan uwa da abokan arzuk'a.

Lafiyayyun girke-girke aka kawo masa duk da cewar basu san ranar zai zo ba, amman ya samu abinciccika na alfarma wanda Umma bata rabuwa dasu ko ba'a cinye ba za'a bawa almajirai da mabuk'ata basa zubar da abinci dan abban su Khaled bai bada kofar almubazzaranci ba a gidan, hakan yasa kowa yake kiyayewa dan ko zubarwa kayi sai ka tsince ka cinye na kasan, shi yasa kowa yake kaffa-kaffa da abinci idan ya zubo ko idan an jera a dining table ko wani gurin inda aka tanada dancin abinci.

Bayan ya gamaci sun d'an tab'a hira da Umma dasu Humaira ya tashi ya nufi sashen Khaled, kasan cewar shima yana da nashi key din ba sai ya nema ba kuma shima d'akinsa dake can lagos Khaled din yana da key, kowa zai iya shiga ba tare da ya jira d'an uwansa ba. K'ananun kaya yasa wando jeans baki da farar riga mai dauke da rubutu a gabanta an rubuta wonderful da d'igo-d'igon stone a jiki baki da jah Saifullahi yayi kyau dama gashi masha Allah sai wanda ya kallesa shine zai gama tabbatar da irin kyautar da Allah ya bashi. Kuma fitowa yayi ya koma wajan su Umma da alama hira yake ji dan sai fara'a yake yi idan anyi abin dariya shima ya dara abin gwanin ban sha'awa.

Kwanansa uku da zuwa garin abuja da sassafe bayan ya shirya ya fito motsa jiki ya had'u da Islam abinda ya daure masa kai, kodai aljana ce wannan yarinyar ganin ya barota a lagos ya dawo nan kuma sai ya sake ganinta, shin menene yasa bata bari sai ya koma ba sannan ta dawo?ko dai Khaled ya sanar da ita cewar ya dawo nan?idan hakan ne to meye alak'arsu da har zai fassara wannan had'uwar tasu? Dole ya dauki kwakwaran mataki akan yarinyar dan yaga kamar kiruciya tana damunta gashi wani irin mugun tsanarta yake ji a ransa, amman dole yana son koyar da ita wani darasi, yana son ya nuna mata duk macen da ta furtawa d'ah namiji kalmar so a wannan zamanin toh ta siyarwa kanta wulak'anci da rashin ganin kimarta, dole yayi amfani da wannan damar tasa wajan sanin kanta da kanta.









_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 34-36_*

_SHAFIN YAU NA KU NE GROUP ‘DIN MAMMY NA (KAUTHAR M HASSAN) WATO ‘YAN *MUSHA KARATU GROUP*, FATAN ALKHAIRI AGARE KU, MUSANMAN MAKARANTA SAIFUL_ISLAM💕_

_nanahafsat.wordpress.com_


*ABUJA*

Lectures su Islam suke yi sosai, domin exams ma xasu fara ta first semester, gaba ‘d’aya ta cire maza a ranta, aganinta bata da rabo, tana fatan Allah yasa hakanne mafificin alkhairi. Ta ‘Bangaren Saifullah ma ya mai da hankali wajen zuwa place of primary assignment ‘dinsa, amma sam baya son wajen. Domin matan wajen sun uzzurawa rayuwar sa, sai kace shi kad’ai ne namiji. Shi abun har mamaki yake bashi da takaici.

*5:35*

Yana gama idar da asubahi a masallaci ya fita jugging da ya saba, shine first morning routine ‘dinsa, alokacin itama Islam tafito tana da gilashin ta, tana tafe tana zikiri. Can Saifullah ya hangota murmushi yayi, yana ‘kiyasta yadda xai mata magana, inde tabada Kai bori ya hau, to tabbas she’s not classy, da shegen killer smile ya ‘karasa yana shawo gabanta, tsayawa tai tana kallon sa, ganin bata san waye ba yasanya ta dan rissinar da kai, cikin kunya tace,

“Gud morning...”

Mamaki ne ya cika saifullah, tsayawa yayi yana duban ta da kyau, ba laipi for the first time in history muryar ‘ya mace tayi masa dad’i. ‘kisisina’ ya furta a zuciyar sa. Cikin melodious voice ‘dinsa yace,

“Morning.. How was ur night?.”

Ta muryar sa tagane shine daya bigeta kwanaki har wayarta ta fad’i. Domin dama bataga face dinsa a lokacin ba sai yau, rabawa tayi zata wuce ya kara tare ta,

“Ke kiddo!”

“Kiddo?!” Ta maimata tana kallon sa”

“Yeah ai itance.”

Girgiza kai kawai tayi, ta bar shi nan tsaye yana dubanta, yayi niyyar ya sake binta sai shima ya basar kawai, yai tafiyarsa tare da cin alwashin sake tareta. Don so yake ya koya mata darajar mace. Kullum sai sun hadu ya jata da magana, wata ta amsa wata ta basar, a kwana na biyar lokacin sun gama exams washe gari suka hadu dashi.

“Little one...” ya kira ta da ‘karfi

Juyawa tayi tana kallon sa, mutumin nan ya takura mata da yawa, gashi idan ya tsaida ita ba maganar arziki suke yi ba,

“What again?” Ta fada cike da ‘kosawa.

“Kiddo! Yau ba gaisuwa?”

“Morning..”

Tace tana kallon gefe, wani killer smile yayi, har saida dimple dinsa suka lotsa, cikin rad’a-rad’a yace,

“How was ur night?!”

“Twas great..”

Tana gama fad’a tai gaba, binta ya shigayi kamar jela, tsayawa tayi tana kallon ‘kasa. Ganin haka yasanya shi, langwabar da kai yana duban fuskar ta. A hankali yace

“Little one, Ina ne gidan ku?!”

Yana so ya tabbatar idan tanada aji ko batada shi, Shawara ta shiga yi da zuciyar ta,shin tafada masa ne ko kuwa? Wata zuciyar tace ‘aa Islam kakki soma, kila yaudararki zai yi ko kuma jikin ki yake sha’awa kamar sauran maza. Har tayi taku d’aya, d’aya zuciyar tace, ‘uhm uhm Islam, kila Allah ne ya dubi zuciyar ki, ya kawo miki shi, duk da dai bacewa yayi yana sonki ba, kawai dai kuyi mutunci., cikin shagwababbiyar muryar ta tace,

“Idan kayi corner ‘din can street din, first house by the left shine gidan mu.”

Girgiza kai kawai Saifullah yayi, cikin zuciyar sa yace, ‘ba aji’. zahiri kuwa ca yai,

“Oh ashe ba nisa da gidan su Khaled. By the way sunana SAIFULLAH... And you?!”

“ISLAM....” tafada tana ci gaba da tafiyar ta, shima juyawa yayi yai tafiyar sa gidah.


*BAUCHI*

A gajiye lik’is Dr Khaleel ya shiga harabar gidan sa, inda Karimatu take yanzu. Mai gadin ne ya tafi a sukwane zai karbi jakar hannun sa, dakatar dashi yayi kafin yace,

“Basshi lawwali nagode, ai ba bu nauyi. Ya badai wata matsala ko?”

Sosa ‘keya lawwali ya shigayi yana sunkuyar da kansa a ‘kasa. Ganin haka yasanya Dr Khaleel hanzarin shiga cikin gidan. Har ya fara hawa matattakalar bene ya jiyo muryar Karimatu da Sidiya ‘yar uwar ta, yana mamakin taurin kai irin na Karimatu. Ya haneta da shiga harkar sidiya amma taki yadda, duk wani shedananci Sidiyar ce ke ‘dora ta akai, wato saboda nan ba Abuja bace, shiyasa take yadda taga dama kenan, no wonder lawwali yake inda-inda ashe ashe makirar sidiya ce tazo. Dai-dai matattakalar bene na takwas ya jiyo muryar Karimatu na cewa,

“Sidiya kinga ni Alhaji ya hana fita, ballantama garin nan bansan kowa ba wallahi, Kinga ko makota ma babu nan kusa, so nake duk yadda zaki ki fadawa mallam komai, jibi ni kuma zance masa hajia ba lapia, yabar ni naje kano, nasan zai bani bugun Abuja. Toh dasu zan bawa mallam ladan aiki, fatana ni dai Aysa ta haukace gaba d’aya, shegiyar ‘yar tata da suke tare ta iskance ku...”

Bata ‘karasa ba dr Khaleel ya shiga cikin parlorn bakin sa ‘dauke da sallama, Sidiya sai ta fara neman hanyar guduwa, gaisheshi suka shiga yi, Karimatu harda in-ina,

“Alhaji da..Dama zaka zo yau ne? Na dauka sai...jibi ai,”

“Karki damu wani unexpected abune ya kawo ni..”

Kad’a kai tayi tana fatan Allah yasa bai ji zancen da suke ba dai, Sidiya jiki ba kwari ta mike tana gyara xaman mayafinta, kafin tace.

“To yaya ni zan koma garin mu, sai kinzo, jikin Hajia dai ya matsa.”

Murmushi Karimatu ta ‘ka’karo, kai da ka ganta kasan ba lapia, cikin dauriya tace.

“Insha Allah ina nan tafe, tunda ma ga Alhaji yazo, sai na sanar mai.” Juyawa tayi tana kallon Dr Khaleel kafin tace.

“Alhaji jikin hajia (mahaifiyar ta) ya matsa, sai dai a kwantar a tayar, shine Kawu ya taso Sidiya, yace tazo ta sanar mun, dama ina shirin kiran ka awaya sai ga ka.”

“Allah ya bata Lapia”

Abunda ya ce kenan, yana latsa wayar sa, a zahirin gaskia, yadda zai rabu da Karimatu yake tunani, Don yaga alamar bazata tab’a canzuwa ba. A hankali ya ‘dan dubeta kafin yace

“Nima yanzu zan koma Abuja inada abun yi, idan zakije ki duba Hajian yau ma shikenan..”

Washe baki tayi, aganin ta baiji komai ba, cikeda murna ta shiga godia, ‘daki ya mike ya shiga, yana shiga ya yagi takardar littafi ya rubuta,

“Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, Ni Khaleel Muhammad Tasiu, na saki matata Karimatu saki ‘d’aya, dama na mata saki biyu shekarun baya, ya kama saki uku kenan, xaman mu ya ‘kare, Sakamakon wani babban dalili data aikata, Ina fatan hakan zai zamto silar shiryuwarta nan gaba, Allah ya had’a kowa da rabon sa. Bissalam.”

Yana gama rubutawa ya linketa ya zura a envelop, ya kara ‘daukar wata envelop din ya zura aciki, kafin ya dakko bandir din yan dubu d’aya guda d’aya ya had’a akai ya fito parlor. Sai murmushi take yi, mika mata envelop din yayi yana jaddada mata,

“Wannan envelop ‘din Kawu zaki bawa, munyi magana dashi, sannan wannan kudin kuma gasunan ko zakiwa Hajia siyayya..”

Ido ta bude tanabin kudin da kallo,

“Ah! Madalla angode Alhaji.. Allah ya saka da alkhairi.”

“Ameen..”

kawai yace ya koma cikin ‘dakinsa, gaba d’aya ya hakura da Karimatu. shiysa yaji bazai iya sanar da su Ya Bala ba, domin cutawa zai tayi. Wasu textbooks ya ‘dauka dama dansu yazo. A tare suka fita, driver yajashi zuwa airport, ita kuma ta tukasu zuwa Kano itada Sidiya. Sam ko a mafarki Karimatu bata kawo komai ba. Haka suka shiga kano, a hanya ta tsaya ta siyi biredi na dari uku da lemon ‘bawo na dari biyu wai zata kaiwa Hajia, siyayyar ‘dari biyar dai cif acikin dubu ‘dari da aka bata. Suna ta hira suka ‘karasa cikin unguwar yakasai.

Ranta taji gaba d’aya ya baci. Sam batason unguwar su yanzu, ballantana gidan su. Wani yaro ne rike da mangwaro a hannunsa yana sha, ruwan sai zirara yake a rigar sa, bako wando ajikinsa, majina sai yar tsere suke a fuskar sa. Kyakkyawan rankwashi Karimatu ta bashi akai kafin tace,

“Tafi gida, ‘dan kan uba, kai yaran unguwar nan ‘kaxamai ne wallahi”

Sidiya dake gefe tayi daria,

“Yaya ‘dan zulfa’u ne fa (‘kanwar Karimatu da auren ta ya mutu).

Ashar Karimatu ta lailayo tana duban sa, rike haba tayi, cikin mamaki tace.

“Wallahi kuwa ga nason bakin nan irin na ubansa haladu mai kayan koli.”

Sidiya dai darawa take tayi, a Haka suka shiga cikin gidan. Gaban Karimatu sai faduwa yakeyi, domin ta tsani gidan nasu, dan ‘kukut dashi ga shegen ‘doyin masai data cika, take barazanar ‘burmawa. Duk sai ‘kaurin icen da mahaifiyar su ke alalar siyarwa. Gefe ta zauna tana rufe hancinta. Kallo d’aya hajian tayi musu tana ‘dauke kanta, domin Karimatu idan ba aikin asirin tane ya kawo taba, bata zuwa ganin gidah, ko kuwa mai xai faru sai dai ayi ba ita. Shiysa a dangi ake cewa batason shiga harkar dangi saboda ba masu kudi bane. Tana zaune ‘kannenta suka fara zuwa suna gaidata, wasu tafadi sunan su, wasu ta amsa da kai kawai. Sai data mulaa ta huta don kanta sannan ta mike tana nufar hanyar kitchen, a tsaye yadda take ba rissinawa bare girmamawa tace,

“Hajia ina yini?”

“Da ban wuni ba kya ganni Ina alala?”

“To fah.. Alhaji yana gaida ki.”

“Nagode masa, yaron kirki”

Biredin da lemon ‘bawon takai gaban hajiar tana wani tabe baki,

“Hajia ga tsarabar Bauchi.”

Bin ledar Hajia tayi da kallo,biredi mai yanka-yanka (slice bread) guda d’aya sai lemon da baifi kwaya goma ba. Murmushi kawai Hajian tayi, tana gyara xaman kular da take juye alalar, zind’e Karimatu tayi, kafin ta koma ‘dakin da take sauka ta zauna a kan wata yarkacacciyar tabarma, cikin ‘daga murya tace,

“Alawiyya..”

Da azama Alawiyyan ta ‘karaso dakin tana haki, Don tasan irin rashin mutuncin Yayar tasu, kowa bata bari ba, domin kwanaki da tazo, ita suna waje suna hira da saurayin ta, Karimatun ta lek’a ta bashi ‘dari biyu ya karbo mata awara, ya siyo kyauta ya bata, ta sake cewa ya koma da dari biyun ya siyo mata balangu a y’ar kasuwa. Tun daga ranar bai ‘kara zuwa ba.

“Aunty gani..”

“Ungo rik’e.. Ki je gidan asabe mai abinci, ki siyomin shinkafa da taliya ta dari uku, da hakarkarin kaza na ‘dari biyar. Yawwa da lemo mai sanyi guda biyu da ruwan roba. Kiyi sauri yunwa nakeji.”

Cike da azama Alawiyya ta mike tatafi, tana tafe tana ‘korafi. Gand’amemiyar budurwa da ita, amma kullum idan Aunty tazo saita uzzurawa rayuwar ta. Tana tafe tana kukan zuci haka ta ‘karasa gidan ta siyo ta kai mata, ba ko godia Karimatu ta karba tashiga narkawa cikin ta. Sai da tai nak sannan ta mimmike tana hutawa. Nan Sidiya tashiga tana mata sannu,

“Yawwa.. kaiwa Kawu takardar nan, da alama kudi ya tambaye shi, aita zubarmin da kima dai” cewar Karimatu tana mikawa Sidiya takardar da yace abawa Kawu.

Karba Sidiya tai tana murmushi,

“Bari Yaya, ai wallahi sam banajin dad’in yadda ake zubar miki da mutuncin ki wallahi. Zamu kamo bakin zaren dai.”

“bar ‘dan nema kawai, mamugunci idan nasa ‘yayan ne ai bazai musu haka ba.”

Ita dai Sidiya saka kai tayi ta fita, bayan ta kunna Karimatu dake ta faman mita tamkar zata amayo kayan cikin ta, duk ‘yan gidan sun tsakure kowa a tsorace yake da ita. Hajja ce kawai dai-dai ita, Don sam bata raga mata. Sidiya na kaiwa Kawu ya karba, sai da yaga tatafi sannan ya bude ya fara karantawa, don dama ya masa bayani a waya da ya je airport. Karantawa yayi yana jinjina kai kawai. Dama yasan za’ai haka, domin duk wanda baya ganin ‘kimar iyayen sa bazai ga da kyau ba. Mahaifinta na kan gadon asitbiti ba lapia ya nemi da tazo yaganta, taki zuwa wai haka kawai ba zata kwashi cuta ba. Sai da yarasu da kwanaki uku sannan tazo. Sai bayan sallar isha’i yaje gidan, kallo d’aya yai mata ya ‘dauke kansa. Gaysawa sukai da Hajia, aka kawo masa dadduma ya zauna akai, sai da yaran suka gaggayshe, sannan Karimatu ta ‘dan daga murya tana,

“Ina wuni..”

“Lapia lou.” Ya amsa yana cewa da Hajia,

“Gurin ki fa nazo, zamu ‘danyi magana ne.”

Zaure suka koma suka zauna, Karimatu ta tun tsire da daria tana fadin,

“dole ka sammata ai, sarkin ‘yan kwadayi. Wannan mutumi badan ance ‘kanin uba na bane, bazan yadda ba.”

Hajia kuwa, Kawu na gama gaya mata yadda akayi tasa hawaye, Allah sarki uwa. Kai Allah ya shiwa iyayenmu albarka, ya biya musu bukatan su, Allah yasa aljannatul frdaus makoma ce agare su. Kawu ya shiga bata baki. Dakyar tayi shiru tana goge hawayen dake neman zubo mata, cikin tausayawa tace,

“Yanzu Amadu abunda Karime tayi ta kyauta kenan? Dubi yadda yaran nan yake mana abun arziki, gidan nan fa shiya siya mana da haya muke, cinmu shan mu duk ya ‘dauke yana kokarta mana. Shekaran jia fa ya turawa Dauda kudin makaranta. Amma yarinyar nan sai da tasa hakurin ta ya ‘kare ya rabu da ita? Shin ko yammata da zawaran gidan nan basu isheta ishara ba? Mu bakwai duk kanmu d’aya, gata ta takwas ta kashe aure, na shiga uku ni Salamatu”

“Kiyi hak’uri Hajia, wallahi karime halin ta sai ita, mutumin nan yanada mugun hak’uri duk yadda akai bango ta kaishi, wallahi bakiga hakurin da yake bani ba a waya. Idan kinji abunda tayiyyi masa zaki mamaki, da wani ne da tuni ya rabu da ita, ta sanyawa uwargidan sa da amaryar ido ta hanasu xaman lapia, sihiri da sharri kala-kala, ni wallahi duk sai kunya ta mamayeni.”

Tsaki Hajia tayi tana rakfa uban tagumi. Kafin tace,

“Ita ba’a auren aka aure ta?, ko kuwa nan gidan ni kadai ta tashi taga Ina rayuwa ba tare da kishiyoyi ba?, Dan Allah yayi ma bamasu zama bane, ko kuwa kaf dangin mu kafadamin banda Nura waye baida mata fiye da uku?. Ai ga gidan nan gata, kuma wallahi sai dai ta koma gidan ka, bade nan ba. Bazan zauna suna kaso aure suna takurawa rayuwata ba.”

Girgiza kai Kawu yayi, cikin sauri yace.

“Ba dai gida na ba Hajia, taje can wani wajen tayi zawarcin ta wallahi, duk k’ok’arin da nake mata bata gani, duk zagin da takemin yana zuwa kunnena, ai ita nan can d’aya sokuwar batasan abunda ke faruwa ba. Catai bakida lapia, Don ya tambayeni ya jikin ki? Nace toh da sauki Alhamdulillah.”

“Allah ya shrya.. Allah ya kyauta, tunda rayuwar da ta zabawa kanta kenan sai tazo ta zauna ai, shashasha, sakarai kawai. Babbar banza, babbar wofi.”

“Kiyi hak’uri Hajia, ta ta ‘kaddarar kenan.”

“Kaddara? Wannan sakaci ne da shirka, ai ga hukuncin nan, ta fara fuskanta tun a dunia.”

Haka dai Kawu ya shiga bata baki. Ya kuma sanya aka kira masa Karimatu, Hajia ta mike tabasu waje tana goge hawayen ta, ita kadai take kalla taji dadi, Don ita ce kawai mai aure, duk sauran yaran basuyi aure ba, uku daga ciki kuma zawarawa ne gata taxama cikon ta hudu. Kawu na sanarwa Karimatu, ta saki wata ‘kara mai razanarwa. Take ta yanke jiki ta sume. Kanta ‘yan gidan suka yi, suna tambayar ba’asi, Kawu ya sheda musu. Sidiya ta sulale tabar gidan, dama ita y’ar kanwar Hajian ce. Tatafi yada auren Karime ya mutu a unguwa.

*DUTSE*

Zaune Yafendo take tana yanke farce, ba laifi ta’dan kara kiba akan da, domin tayi ciwo sosai, bayan komawarta dutse. Dr Khaleel ya shiga bakinsa ‘dauke da sallama. Gaisawa sukai , kafin ta jere masa abinci a dining, serving dinshi tayi tana zaune a kujera mai kallon sa, wayar shi tai ‘kara, ‘dauka yayi yana karawa a kunnen sa,

“Assalamu Alaikum.. oh! Na’am Kawu. Bakomi, ni zan baku hak’uri. Allah ya bata wani daya fini..”

Nan jii da ganin Yafendo suka ‘dauke, dakyar ta iya furta,

“Alhaji kai da wa kuka rabu?”

“Karimatu”

yafada yana danna lomar abinci a baka. Ji kake ‘s...iiiit’, ‘birrr, ‘bubur.. bot’ Yafendo tashiga sakin iska ba ‘kak’kautawa, tana sakin tusa tana magiya,

“Alhaji.. Ni dai dan Allah karka rabu dani, wallahi na kintsu yanzu, Allah ba ruwana da kowa...”
‘Birrrr’

Ta ‘karasa maganar tana sakin wata bahaguwar tusa mai shegen ‘doyi, mikewa yayi yana yakice hannunta data rike nasa, cikin dauriya yace,

“Sakar ni Amina. Da me zanji yanzu? Da shegiyar tusar ki mai doyi ko kuwa hannun ki da ke dauke da shawarma sauce duk jin shafamin.. ni sake ni dan Allah.. kiyiwa Allah ki cikani, wallahi bakiji ciki na ba.” Yafada hannunsa toshe da hancinsa,

Dakyar Yafendo ta sake shi tana,

“Alhaji kakka rabu dani ni, dai dan Allah,”

Can ‘k’arshen parlor ya koma yana fifita hancin sa da murfin flask. Dakyar yace,

“Bodara kawai, ki rage shan madara wallahi da kayan kwadayi, ki guji nacin cin starchy food. Ko kiga likita, Gaskia ba lapia ba, gashi ke ko ajikin ki.”

Tashi tai zata biyoshi biyoshi yai hanzarin dakatar da ita,

“Ki bari ta huce wallahi. Zan mugun sab’a miki idan kikazo nan Amina. Can anjima ki hadomin coffee ki kawomin.”

Yana gama fada ya shiga ‘daki ya murza key. Ita kuwa safa da marwa tashiga yi a parlorn. Sam nutsuwarta bata jikin ta, gani take kawai saura nata takaddar sakin. Cikin kidimewa tashiga kamo addu’oi tana yi, ciki harda ta hawa abun hawa.


.....

_Masu neman SAIFUL_ISLAM daga farko kuje blog dina na nanahafsat.wordpress.com, dan bana posting a wattpadd.. wattpaddians hiyam sorry😻 zaku iya wantsalawa fans grp na SAIFUL_ISLAM💕, don samu daga farko_

https://chat.whatsapp.com/FCICopl029LGkPU2TmA5ov


_HML FIDDAUSI SODANGI💕MAY ALLAH BLESS UR NEW HOME🎊._




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 37-39_*

_WANNAN SHAFIN NA KINE, MASOYIYAR ‘KWARAI, NANA HAFSATU NA GODIA DA YADDA KIKE BIBIYAR LITTATTAFANTA, DA MA ITA KANTA😻 *~Halymah saminu El-jibrin*_ 💕_ THANKS FOR THE HERBAL REMEDY🤟🏼_

_nanahafsat.wordpress.com_

Yafendo ta kasa hak’uri, sai da takira Inna Bilkisu ta zayyane mata komai, tareda ‘doriyar tasa baki, kan dan Allah kada Dr Khaleel itama ya bata takardar sakin ta, a daren kuwa Inna Bilkisu ta kira Dr Khaleel tashiga balbaleshi da fad’a, ta inda take shiga batanan take fita ba. Hak’uri ya shiga bata tareda d’oriyar,

“Inna ba zaki gane bane, wallahi nayi hak’uri sosai da matar nan, taki ji, taki ta shiryu, babu abunda ya ragu a halayenta saima dad’uwa. Zama da irin su Karimatu inda tamkar annoba ce, dan bakiji abubuwan da suke fad’a zasu aikata bane itada wannan y’ar uwar tata Sidiya, Kinga fa har kashedi na mata akanta amma tak’i. Shiysa bazan iya wani hakurin su cutar da baiwar Allah da ahalin taba, hak’uri na ya kare. Kiyi hak’uri Inna.”

Shiru kawai Inna tayi tana sauraransa, Tabbas duk abunda yafada, Karimatu zata iya aikata fiye da hakanma, kuma yanke hukuncin dr Khaleel lokaci d’aya ,

Please Login or Register in order to submit comment