Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lalle babban abune, dan baya tab’a zartar da hukunci saida shawarar manyan sa. Cikin dattako tace,

“Shikenan! Allah yasa hakanne yafi alkhairi, Allah ya maka albarka. Ita kuma Allah yasa hakan ya zamto silar shiryuwarta, Allah ya ‘kara kareku da kariyar sa...”

Haka tashiga yi masa addu’oi da kalamai na kwantar da zucia, har saida ta tabbatar komai ya wuce, sannan sukai sallama. Fada sosai ya shiga yiwa Yafendo saida ya mata tatas tukun sannan ya ji sanyi a ransa, dakinsa ya koma ya cigaba da nazarin wani littafi da yakeyi, domin a satin gaba ne, za’a bashi shedar farfesa. (professorial title).

Karimatu kuwa na a asibiti, da kudin da ta karba na ‘karyar hajia ba lapia, zata bawa malaminta ladan aiki, dashi aka kaita asibiti, sam takasa motsa ko‘ina na jikin ta, hawaye ne kawai ke gangara daga fuskar ta. Lokaci d’aya ta ‘kanjame kamar wadda ta shekara tana ciwo. Dakyar Hajia takira Hafsat da sauran yaran tace suzo mahaifiyar su ba lapia. Da niyyar idan sunzo ta sanar musu auren tama ya mutu.

*ABUJA*

Shirye-shiryen tafia Nile University suke yi, inda za’a bawa Dr Khaleel matakin Farfesa(prof). Duk ‘yan uwa na nesa dana kusa sunje Abujan. Kowa ya kintsa cikin shigar sa, suka ‘dunguma a zungureriyar motar da aka tanada musu, ta kai su Nile. Anyi addu’oi aka fara da abunda taron zai ‘kunsa, daga nan kuma aka kira Dr Khaleel , da za’a bashi farfesa na ‘bangaren psychology. Tafi aka fara yi kowa daka ganshi kasan yana cikin farin ciki.

Can gefe kuwa Khaled da Saifullah ne, cikin tawagar mutanen, kallo d’aya zakai wa saifullah kasan takura masa akai yaje. Sai kumbure fuska yake yi, baturiyar mai magana wato Mrs Brown ta ‘kara kiran Dr Khaleel tana,

“May I please call on stage, our amiable man of honor, Dr Khaleel Muhammad Tasi’u...”

Cikin isa da takunsa na dattako ya ‘kara stage din, bakin sa ‘dauke da murmushi, sai yanzu Saifullah ya tabbatar dagaske ‘dan uwan mak’ocinsu ne na legas(Ya Bala) domin suna kama, sai dai wancan yafi manyanta. A take professors suka yo kansa, kowanne saida yayi bayanin hazakar Dr Khaleel, kafin a rataya masa professorial gown da hula, da wani yadi dake ‘dauke da tambarin professor of psychology, da wasu littattafai, tukun sannan akai announcing ‘dinsa da zama cikakken farfesa, aka kuma fadi matakinsa tun daga kan Bsc, Msc, Misd, Mnia, Phd. Sannan Professor a yanzu.

Gaskia an gwangwaje, kuma anyi farin ciki, Inna Bilkisu kuwa hawayen farin ciki ne ke reto a fuskar ta. Wai yau Khaleel ‘dinta ne ke tsaye cikin dubban mutane ana ‘kara masa girma/matsayi a ilimi. Anyi hotuna sosai, an ci kuma ansha anan, kafin a koma gidah kuma ayi wata walimar da Haj Aysa ta shirya. Riri kuwa dadi kasheta hango Khaled datayi, bude baki tayi ganin harda wannan arrogant saifullah din makocinsu dake lagos. Tabe baki tayi tana mamakin dama yana shiga mutane haka.

Saifullah kuwa jan hannun Khaled yake tayi, yana marai-raice masa su tafi gidah wai time ‘din karatun sa ne, Khaled ya tuntsire da daria yana kwace hannunsa,

“Wallahi bazan tafi ba, haka kawai me xanje nayi a gida?, kai ungo Key dinma kaja motar kaje da kanka.”

Yana fada ya zaro mukullin motar ya mika masa, ‘kin karba Saifullah yayi yana wani langabar da kai, nan Riri da Islam suka doso su suna tahowa, sanye Islam take cikin laffaya, orange color. Ba kadan ba tayi kyau, gashi laffayar ta kwanta a jikinta, duk coca-cola shape dinta ya bayyana, Riri kuwa sanye take cikin Kimono ta ‘daura ‘dankwali kalar rigar, sai karairaya jiki take tunda ta hango Khaled, itacema ta ishi Islam suje wajen su, Don ita batasan yazo bama. Saifullah kuwa gaba d’aya nazarin Islam yake, mace har mace amma take cewa tanason namiji, Tarasa wane namijin ma sai Khaled. Tsaki ya saki yana kauda kansa gefe, Ganin Riri, sarai yasan yarinyar nan a legas batajin magana, saboda unguwar su d’aya, ta tab’a shiga rayuwar sa ya shek’a mata mari.

“Yaya..”

cewar Islam tana washewa Khaled baki. Murmushi ya saki yana sake binta da kallo, tayi masa kyau kwarai,

“Mi lady.. Kin fito sak kanuri babe. You look breathtaking..”

Saifullah dake gefe ya saki tsaki, yana,

“Bani car key din, I’m going”

Sarai Khaled ya gano dan yace wa Islam hakane, yarasa mai yasa saifullah ya tsani harkar mata gaba d’aya. Sai asannan Islam ta hango Saifullah, cikin murmushi tace,

“Ah... Sai., Ya saif!”

Juyawa yai yana kallon ta, idanun sa suka sauka akan ‘dan bakinta dayasha jambaki, cikin dakewa cikeda basarwa yace,

“Sannu ko..”

Mamaki ya cikata, gyada kai kawai tayi, yayi wucewar sa mota ya figeta a guje. Khaled baiji dad’in yadda Saifullah yaiwa Islam ba,

“Kin sanshi ne?” Cewar KHaled

“Yeah.. Muna haduwa idan na fita jogging. To anan ya gayamun sunan sa”

“Just., ignore the fool. So ya school sissy?”

“Alhamdulillah Yaya. Ya naku baka tafi ba kuma”

“Eh wallahi, sun hanani visa suna ta renamin hankali, Baba kuma yaki saka baki. So kawai na hakura, zan bari muyi aure da madam sai mu wuce can gaba d’aya, itama ta fara karatun acan.”

Islam ta bude baki kenan zatai magana, Riri dake gefe takasa hak’uri, cikin kissa tace,

“Yaya.. Ina yini?”

“Ah lapia lou Fareedah. Ya garin?”

“Alhamdulillah, rannan na maka magana a WhatsApp, you shunned me!”

Khaled daya gaji da maganar ta yace,

“Ni? Anya.. ze iya yiwuwa na bude chats din amma ban karanta ba, I’m sorry”

“Issokay, yau zan ‘kara maka ai.”

Murmushi kawai yayi, Islam dake gefe ta danne dariar ta , sun ‘dan taba hira kafin su koma gidah a ‘kara shan wata walimar. Saifullah kam cayai wa maman su Khaled shi baida lapia, dan dazuma ita tayi forcing d’insa suka tafi.

Bayan kwanaki biyu aka fara maganar had'o kayan lefen khaled wanda murna ta gama cikawa, yana son Fatima wadda ake cewa Dr Teema, wato wadda zai aure hakan yasa baya iya ganin ko wace irin mace duk kyawunta duk dirinta yana ganin bekai na Fatiman sa ba.

Saifullah na gefe yana jin yadda suke shirya komai, amman ya kasa sanya musu baki ba saboda a ganinsa ba huruminsa bane.

Sai da suka rubuta abubuwa da yawa kafin su ajiye da nufin idan an tuno da wani abun sai a rubuta dan kar sai anje kasuwa a fara tunanin mai za'a siyo.

Maman su Saifullah aka bawai ragamar shirya kayan lefe, tunda ta fara take jin ina ma ace harda yaronta saboda yanzu ba ta da burin da ya wuce ace Saifullah nada iyali, tayi nasihar tayi fad'an amman kullum maganarsa shine bashi da wadda yake so har yanzu, duk kayan da ta siyawa matar Khaled sai da ta sayi na matar Saifullah, Saboda tana so a had'a da nashi tunda bashi da wadda yake so ita zata aura masa 'yar kawarta tunda ita yarinyar tana son shi.

Sai da ta gama had'a komai akwatuna arba'in ashirin na matar Saifullah ashirin na matar khaled, koda aka kai kayan gidan su khaled sunyi murna domin komai yayi musu kyau, hatta Islam sai da taje ta gano kayan tayi Allah ya sanya alkairi,Haj Aysa ma taje ta gano sunyi musu murna sosai. Ana sauran kwanaki uku akai kayan khaled Maman su Saifullah tazo abuja domin harda ita za'aje kano akai kayan auran wanda kowa yake jiran zuwan ranar bikin.

Zaune suke a cikin d'aki suna hirar duniya kowa yana fad'ar abinda yake damunsa Maman Saifullah taja numfashi tare da kama kumatunta tace.

'”Ni yanzu damuwa tayi yawa, duk da cewar aure lokaci ne dashi amman ace Saifullah ko zancen budurwa bayayi? Da naje had'a kayan lefen nan harda nashi nayo da nufin idan na gama zan yiwa ‘kawata magana akan zamu had'a aure tsakanin 'yarta da d'a na, wallahi na gaya muku sai da na gama komai na yi mata magana take shaida min ai yarinyar sickle ce da ita, ban san lokacin da na fashe da kuka ba saboda tausayinta da kuma tausayin Saifullah domin nasan idan ba yi masa auran aka yi ba, toh shi kam ba yi zai yi ba dan karankansa.”

'”Banda abinki menene na damuwa dan Allah? Auran Saifullah lokaci garesa, ita yarinyar itace abar tausayi domin kafin a samu wanda zai aure ta za'a jima.”

Cewar mahaifiyar su khaled, haka dai suka ci gaba da tattaunawa har Umman su khaled take cewa.

'”Ni kuwa da zaki gwada wata 'yar k'awata anan makotan mu take, wallahi yarinyar nan ita da iyayenta suna da halin dattako har khaled na yiwa sha'awar yarinyar nan ya aure ta, toh kinsan d'an yau ka haifesa hali kuma sai wanda aka zo maka dashi, wallahi k'ememe yace min shi yana da wadda yake so, mai zai hana ki gwada Islam d'in kona rana d'aya ne kiga yadda take da nutsuwa da kamun kai, watakila kiga sun dace da yaron namu.”

Cewar Haj Latifa tana murmushi yayin da Haj Zuwaira (mahaifiyar Saifullahi) ta gyara zama tare da cewa,

“Uhmm kina ganin khaled ma yayi rejecting ina ga Saifullah mai tsattsauran ra'ayi? Kina ganin zai so yarinyar ko kuwa kina ganin kawai nayi masa dole akan sai ya aure ta?' Haj Latifa ta kad'a kai tare da cewa.

“A'ah Haj Zuwairah ba haka nake nufi ba, ina nufin zan kirata nan gida ki ganta idan yaso in tayi miki sai ke kuma ki nunawa Saifullah ita kiji mai zai fad'a, mudai fatan mu Allah ya basu mataye na gari masu kaunarsu da gaskiya”

“Toh shikenan hakan ma yayi, Allah yasa shi kuma idan nayi masa maganar ya amince.”

''Amin ya Allah.''

Haj Latifa ta kad'a tana sake gyara zama suka ci gaba da hirarsu.

Washe gari kuwa Haj Latifa tasa akaje aka kirawo mata Islam, tare da Areef suka taho ta durk'usa har kasa ta gaida su tana murmushi tace.

'”Umma gani aka ce kina nema na?”

Cewar Islam tana gyarawa Areef zamansa akan cinyarta, Saboda duk tabi ta tsargu gani take kamar kowa ita yake kallo, taji muryar Haj Latifa na cewa.

“Eh Islam cewa nayi a kiraki na tambayeki ko zakije kai kayan yayanku can kano saboda a tanadar miki wajan zuwa.”

Nannauyar ajiyar zuciya Islam ta sauke jin ba wani laifi tayi ba, cikin sunkuyar da kai tana murmushi tace.

“Lahh Umma wallahi naso zuwa amman yanzu babu hali sabida Ammi ba tada lafiya duk komai yana kaina, ina musu fatan alkairi Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya Umma, idan lokacin bikin yazo ayi damu.”

Ta k'arasa maganar tana dariyar ta mai burgewa, dama tunda ta shigo idanun Haj Zuwairah yake kanta har zuwa yanzu da ta mik'e zata tafi tayi musu sallama suka bita da fatan alkairi.

“Toh Haj Zuwaira ya kika ga yarinyar? Kuma mahaifiyar ta ma y’ar Bornu ce, babarbariya ce” Cewar Haj Latifa bayan Islam tabar gidan.

'”Gaskiya tayi hajiya ni kam ko Saifullah baya so toh ba zamu rasa yarinyar nan da shigowa cikin family d'in muba.” Maganar suka bari da nufin idan Saifullah yazo zasu yi masa zancen Islam d'in.

Sai da aka kai kaya aka dawo lokacin shima Saifullah yazo gidan a nan ne mahaifiyarsa tayi masa zancen Islam, abu na farko da ya fara zuwa cikin ransa shine tazo tace asa shi ya aure ta, ya rasa gane kan yarinyar akan son yin aure amman zai yi amfani da wannan damar wajan auranta ya nuna mata cewar bawai kayi ta jarabar son yin aure ba shine a'a ka samu wanda yake sonka yake tausaya maka yake jinka a can cikin ranka, sai da ta sake masa magana sannan ya kauda kai gefe yace.

'”Allah ya nuna mana lokacin.” Haj Zuwaira tayi murmushin jin dad'i tare da cewa.

'”Amman fa mu san samu a had'a bikin da na khaleed kowa ma ya huta ko ya ka gani?” Sai da ya yatsina fuska sannan yace,

'”Duk d'aya ne ayi hakan ma.'”

“Alhamdulillah Allah yayi maka albarka Saifullah yasa Abokiyar arzikinka ce, dama abinda nake buri kenan naga lokacin da zan aurar da d'an auta na, gashi yanzu lokaci yayi ashe ma muna tare da matar a kusa damu, wani abun dadin itama tanada jin bare-bari, kasan fa da a Al'adar auren Kanuri ta samo asali ne tun daga lokacin da Kanurai suke karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno, a sannan a kan yi auren ne bisa umarnin iyaye wato kai tsaye iyaye ke yima junansu kamun surukansu. Daga baya kuma da suka koma Dikwa sai kuma aka tsuri al'adar cewa an daurawa yarinya igiya wato a wannan lokaci yarinyar takan san waye za ta aura shi ma mujin zai san wadda zai aura. Amma bayan sun dawo Maiduguri sai abin ya sake daukar wani salo na yadda yaro zai ce ya ga yar wane yana so kuma a shige gaba a nema masa auren, Allah ya maka albarka auta, Ashe duk autoci ne, itama autar mata ce”

Duk aka yi dariya amman banda shi sai ma tashi da yayi yabar parlourn yana jin tsanar Islam, tabbas zai shayar da ita ruwan mamaki domin sai ya koyar da ita illar zuwa neman wanda zai aure ta da take yi, tsoransa d'aya karya aureta taga bata samun wasu abubuwan ta fito masa da munanan halaye dan yaga alamar idan bata fara ba a yanzu da take, toh tabbas zata yi a gidan sa, ai kuwa da taci kaniyarta domin kafin ya rabu da ita sai yayi mata shegen duka sannan.

Da wannan tunanin yaci gaba da harkokinsa sam ba shi da labarin su Maman shi sunje gidan Dr khaleel har sunyi maganar auran, kuma an bashi domin ta hanyar su Haj Latifa suka bi shi yasa ba ai wani dogon lokaci ba aka basu Islam. Anyi sarte (sa ranar aure), anyi tambaye-tambayen ‘sigga’ (yarjewa na anbada auren/ the act of asking and acceptance between the family of the bride and groom and their witnesses)

Tuni har Yakolo sun fito da ankon dangashe da mandil (kayan wushe-wushe) na ankon Islam. Ita kuwa Islam tun ranar da aka sanar mata da maganar Saifullah ne xai xamto mijin ta take kuka, mai tsuma zuciar duk wanda ya saurara, sosai ta rame ta fad’a, Ganin haka yasanya Ya Bala ‘dauketa ya kaita Lagos kafin ranar bikin suzo, acan ya kira ‘Madame Yerwa’ mai gyaren jiki tun daga bornu tafara yi mata, duk abunda takeso yi mata yakeyi, domin har kano ya barta taje bikin Hafsat Rano. Gaba d’aya Islam fushi take da kowa, ciki harda Lee da Humaira ,aganinta sune manyan munafukan da suka sanya xa’ai mata auren dole, auren dolen ma da wanda bataso baya sonta, zaman doya da manja....

...,

Ni miss xoxo Nace wooo Balu tawan (billyn Abdul) Takusa xama ‘dakko riga, ta kusa xama ‘dakko wando, takusa xama tashi ki had’amin coffee🤪🤤... Ko ki gyara ko na sashi ya auro ta biyu yasin😑🤟🏼 don bazan auri shiekh Aliyu mai mata biyu ba, ke kuma SAIFU ke kadai ce awajen sa, bayan ba sonki yake ba😹kinyi mai yiwuwa kinsa an ‘ka’kaba masa ke, tawan ki ja ajinki gaskia😫🤪 ko kiga aikin ahalin barebari😹🤟🏼



_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 43-45_*


_nanahafsat.wordpress.com_

*KANO*

Tuni an sallamo Karimatu daga asibiti, domin kudin jinya ya ‘kare. ‘Yar wayarta tuni ta siyar da ita, da wanda ‘yayanta suka tallafaa mata dasu duk sun ‘kare a magani. Kamar kullum a sheme take kwance kamar shekararriyar saniyar dake jinya. Lokaci zuwa lokaci takan saki murmushin takaici, da alama dai mutuniyar taku tuna baya take yi.

Wata waya ‘kirar nokia wadda akewa laqabi da rakani kashi ta ‘dakko a gefan inda take kwance, tasha ‘dauri da kyauro, gefe da gefe kuma an nane da super glue. Can ‘k’arshen wajen chaji kuwa an nannade da salatef (seal-tape). Duk screen ‘din ya faffashe kana hango cikin wayar, madannan sun goge sai da biro aka zana kowacce lamba. Dakyar ta iya gano lambar Sidiya, takira ta yafi sau goma kafin ta ‘dauka dakyar,

“Toh baxan ‘kara ba, sai kinzo.”

Shine kawai abunda Karimatu tace, ta ajiye wayar a gefe. Can wajen bayan minti talatin sai ga Sidiya tana cika tana batsewa, kallo ‘d’aya taiwa ‘yan gidan ta ‘dauke kanta. Hajia dake gefe ta tab’e baki kawai tana ci gaba da ‘kulla alala a leda. Kamar yaki Sidiya tashiga ‘dakin da Karimatu take tana wani yatsina fuska, gashi ta tsaya ‘kerere akanta. Ganin ta yasanya Karimatu ‘dan muskutawa ta gyara zaman ta dakyar.

“Ki zauna mana Sidiya.”

“Kai gaskia a’a, kin ji wani shegen zarni dake tashi a jikin ki kuwa, kuma fa nagaya miki kidena kirana da yawa, fisabilillahi baban Gali(mijin ta) sai fad’a yakemin, nifa gaskia ba zaki kashemin aure ba Karime”

Shiru kawai Karimatu tayi, tana sauraron masifar da Karimatu ke zazzaga mata, babu ma Yaya da take kiranta a da, sai Karime gatsal. Tana cikin tunani, muryar Sidiya ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi.

“Wai me zan miki ne da tun asubahi kike dokawa waya ta kira?”

Cikin taushasshiyar murya Karimatu tace,

“Da..Da..Dama kudi zaki aramun asiyo min gurasa da...”

“Kutma.. Cab lalle ke dinnan ma, kiji da kudin lapiar ki ma a’a sai ta biyewa dad’in baki? To wallahi bani dashi, ni idan kin samu ma ki biyani dari uku na ta shekaran jia, bazan iya da cin bashin ki ba.”

“To ko zaki aiko mun da abincin da ki kai?”

Kyakkyawar harara Sidiya tayiwa Karimatu, kafin ta buga zani kawai, ta fice abinta, girgiza kai Karimatu kawai ke yi, ganin yadda Sidiya ta juya mata a baya, ada itace gatanta, ta’dauke ‘dawainiyar ‘ya’yanta ma gaba ki d’aya. Tana cikin tuna baya, Alawiyya tashiga ‘dauke da kwano sai ‘kamshin man ‘kuli ne ke tashi. Shinkafa ce da wake na gidan asabe mai abinci.

“Gashi inji Hajia..”

cewar Alawiyya, ta duk’a ta ajiye tafi ta. Cikin hanzari jiki na bari Karimatu ta bude kwanon abincin, shinkafa da wake da yasha man ‘kuli da yajin tafarnuwa, sai yankakken tumatir da albasa, ga maggi guda d’aya a gefe. Kamar mayunwacia haka Karimatu ta shiga ‘durawa cikinta abincin, tana kad’a kai da alama yai mata dadi. Ashe Hajia duk taji yadda sukai da Sidiya, uwa mai dad’i, ta ciri dari biyu cikin kudin alalar tabawa Alawiyya ta siyo mata abincin. Ko kad’an ba tabada sigar da su Alawiyya xasu rena Karimen ba, dukkoda tarin abubuwan da ta yiyyi musu. Tana gama ci ta koma ta kwanta da ‘d’ayan barin, domin ‘barin hagun ta baya aiki sam. Shiysa takan sau fitsari wani lokacin a zaune idan robar fitsarin ta goce.

Gaba d’aya hakurin Khaled ya ‘kare, domin duk kawaicin da yake musu yaga basa ganewa, a bashi matar sa an ‘ki, tun shekaran jia aka kawota amma ko fuskarta ‘kememe an haramta masa ganin ta, zaune yake akan kujerar ‘dakin sa shida Saifullah dake sketching wani zane . Sake sakin tsaki Khaled yayi a karo na ba adadi kafin ya turo baki gaba cikin tausayawa yace,

“Saboda tsabar an tsaneni ba, Wannan ai rashin adalci ne.”

Saifullah daya gaji da mitar Khaled ya mike yana tattara kayan sa zai bar masa ‘dakin, cikin azama Khaled ya riko shi yana rausayar da kai,

“Dan Allah guy, kayi wa su Umma da Aunty magana su bani matata..”

Sakin baki Saifullah yayi yana duban sa, cikin tabe baki yace.

“Saboda mace kake mita awa da awanni dama?”

Kad’a kai Khaled yayi yana wani taune ‘kasan lips ‘dinsa,

“Ba zaka gane ba Guy, na shirya ne, a matse nake wallahi. Su bani ita mu tafi sunki wai sai lokacin tafiyar yayi tukun na, sai kace ba mallaki na bace..”

Yakice hannunsa Saifullah yayi, yana goge wajen da handkerchief, Ganin haka yasanya Khaled girgiza kai kawai yana murmushi,

“Toh ni meye nawa aciki?”

“So nake kayiwa Umma da Aunty magana su bani matata, hak’uri na ya ‘kare. Ita kanta nasan a matse take.”

“Haka tace maka?” cewar Saifullah, Yana mai dubar agogon hannun sa.

“Lapiyayyar macece fa, wallahi itama nasan ta matsu, dan iska, kai saboda yau za’a kai maka taka shiysa ai baka damu ba.”

“Wa?”

“Matar ka..Islam mana”

Tabe baki Saifullah yayi yana yatsina fuska, kamar an kira sunan kashi. Cikin nuna ko ajikin sa yace.

“Kai mata suka dama..”

Mikewa tsaye Khaled yayi, yana wata y’ar iskar miqa, kafin yace.

“Tabbas mata sun dame ni wallahi, tunda ababen more rayuwa ne ku..”

Be karasa ba, Saboda wani dogon tsaki da Saifullah yayi.

“So suffocating...” ya fada yana barwa Khaled dakin gaba d’aya.

Saifullah na fita sukai kicib’is da Haj Latifa, da wasu baki dake shirin tafiya rakiyar amarya Islam. Sosa ‘keya saifullah yayi, Haj Lateefa tayi murmushi kafin tace.

“Lalle Ango, shine kayi shigewar ka ‘daki kana ji su Gwaggo na tambayar ka, to kayi sauri dai ka sauya kaya dan Allah..”

“Toh Aunty..”

shine kawai abunda Saifullah yace, yai gaba yana tura baki alamun shagwab’a. Dakin da yaga mahaifiyar sa tashiga ‘daxu nan yayi, yayi sa’a kuwa ba kowa a dakin sai ita kadai tana shirya wasu kaya a akwatuna, tana ganinsa ta fadada murmushin ta,

“Auta...”

Da sauri ya ‘karasa, yana dora kansa kan jikinta, shafa sumar sa ta shiga yi,

“Auta na..”

“First love..” ya furta cike da shagwaba.

“Auta, yanzu fa ka girma, gashi yau za’a kaika gidan ka fa. Kaga kayan amaryar ka ne nake had’awa su Fatima su tafi dashi yanzu. Ra’aki ne da kususuram”

‘Daga kansa yayi yana duban akwatunan kalar hoda, guda hudu da Kit, shake da kaya harda kwando cike da turaren wuta da khumrah. Cikin murya cike da tausayawa yace,

“First love ni dai gaskia tayi zaman ta a gidan su.”

Ware idanuwa Haj zuwairah tayi tana duban Saifullah, ‘kin yadda yayi su had’a ido. Murmushi kawai tayi kafin tace.

“Saboda me zata zauna a gidan su? Bayan an daura aure, Duk adon mace ace tana gidan mijin ta shine auta.”

“First love... Ni nufi na kowa acikin mu ya zauna a nasu gidan, If she needs anything...”

“Sai kace a garin gab’a-gab’a Auta? A’ina aka tab’a yin haka? Ayi aure miji da matar kuma kowanne na gidan iyayen sa, anyi ba ayi ba kenan.”

Shiru yayi kaman zai yi kuka, Haj Zuwairah tacigaba da sha fa kansa tana bashi hak’uri,

“Kayi hak’uri Auta, haka dama rayuwar auren take. Kuma kaga naji Baban ku na cewa ma kila muma cikin shekaran nan mu dawo Abuja, Saboda yana so ya dawo da asibitin sa nan.”

Cikin murna Saifullah ya d’aga kansa alamun yayi na’am. Haka dai tashiga yi masa nasiha da dabarta masa yadda ake zamantakewar aure, yadda zai rike y’ar mutane da amana, ta ‘kar’kare da,

“Na bawa Abbas sak’o idan zaka je gidan naka sai ka karba. Tashi kaje ka shirya, Allah yayi muku albarka, yasanya alkhairi da farin ciki a rayuwar ku.”

Kad’a kai Saifullah yayi yana goge hawayen daya zubo masa, Haj zuwairah ta dafe baki kawai tana daria,

“Ah lalle ango da kukan barin gida, Lalle auta na ya kafa tarihi.”

Ta fad’a tana mai mayar da nata hawayen daya taho. Zai fita daga dakin Khaled ya tunkaro kai yana sallama, ganin Saifullah yasanya shi fad’ad’a murmushin sa,

“Iyye Angon Is..”

Harara Saifullah ya wurga masa, yana furta kalmar da ta zamar masa ta dolen fad’a.

“So...s..”

Be karasa ba Khaled ya riga shi yana
“Suffocating mutamina!”

Ficewa Saifullah yayi yana tsaki, shi kuma Khaled ya samu waje ya zauna bayan ya gayda Haj Zuwairah. Sun ‘dan fara magana Fatima da Humaira suka shiga ‘daukar kayan Islam na ra’aki da kususuram. Bayan sun fita dasu ne Haj zuwairah ta dubi Khaled dake sake sunkuyar dakai kasa kamar sabuwar amarya, tuni ta gano jirgin sa amma ta danne,

“Yawwa ina jinka Khaled”

“Aunty...Temako na zaki yi”

“Temako kuma?!”

“Eh aunty dan Allah wallahi ba kiji ‘kirji na ba”

“Subhan’Allah Khaled baka da lapia ne?”

“Kusan hakanne Aunty, akan Fatma ne”

“Matar ka?”

“Eh ita Aunty..Dan Allah ba wanda zan iya kawo wa ‘ko’kon bara na ya amsa min sai ke, ki dubi girman Allah Aunty, kiwa su Ummah magana su bani...”

“Matar ka Fatma”

Sosa ‘keya yayi, yana wasa da gashin carpet. Murmushi kawai tayi kafin tace.

“Khaled kenan, gata fa akai maka, sanin kanka ne gidan da zaku zauna anan garin yanzu ake

Please Login or Register in order to submit comment