Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga d'aukar hotuna, Saifullah na k'ak'ume da hannun Islam kamar gaske, mintuna kad’an ya juya ya gasa mata bak’ar magana a kunne. Duk Islam a takure take dan haka suna tafia taji dad’i a ranta, nan ta koma cikin 'yan uwa aka cigaba da shewa lokaci zuwa lokaci maganganun saifullah na mata yawo a zuciya suna kuma susar ta idan ta tuna kalamansa.

“Wai na zubar da class d'ina a titi, toh mai yake nufi da ina yi kenan?! Ya Allah”

Haka Islam ke fad'a a hankali idanuwanta sun ciko da hawaye, da wannan su Yayya Yaburra suka sake d'aukar ragamar shirya Islam don zuwa wushe-wushe, an yarfa mata 'kela yaske’ (kitson gaba), gana lalle baki da ja, kamshi ta ko'ina tashi yake daga jikin ta, ita dai Haj Aysa nata idanuwa ne kawai domin duk k'annenta sunyi kanai-kanai akan komai, wani dandatsetsen cotton lace ta sanya aka nad’a mata laffaya wadda taci sunan ta 'yar gaske, komai na al’adar kanuri tasa, sarkar k'afa data kai ga kuma b'ular hancinta tasha ado da ‘yar barima itama, komai dai tsab abun ba’a magana sai dai a ce tubarkAllah kawai.

K'arfe bakwai aka fara tafiya wushe-wushe ango Saifullah shima yasha shiga cikin komai na al’adar barebari, ba kad'an ba yayi kyau, abokan sa sunsha ado suma, k'awayen Islam ma sunci ado cikin dangashe da mandil peach color, 'yan uwa kuma sun sa blue and black. A convoy suka tafi inda xa’a gudanar da sha’anin. Motar Saifullah da Amarya Islam itace a k’arshe, tunda ta shiga cikin motar yake kallonta ta gefen idonsa, ba kad'an ba tayi masa kyau, amma abunda ya dasawa zuciyar sa akanta ba zai iya furta komai ba. A haka suka k'arasa inda za’a gudanar da event d'in,

Sai bayan kowa ya shiga mc tai announcing shigowar couples SAIFUL_ISLAM, a tare suka shiga hannun su sarke dana juna, da abokan su dake binsu a baya mace d'aya namiji d'aya suna bin taken gangaa kura kowanensu yasha kitson gaba abindai sai sam barka kawai... Can baya kuma 'yan uwa ne su Yakolo, Yaburra da sauran ahalin prof Khaleel. Tuni aka fara xubawa makad'an gangaa kura yirne, waje kuwa jin kid'a yana tashi yasa aka fara sakin al’adar durum kageye, su kaka deeja kuwa sa bada nagaya ka ajiye suke(turaren wuta).

Riri ce ta bada tarihin amarya inda take cewa.

''Amaryar mu dai ta kasance 'yar autar mata a wajan iyayenta, sannan tana da kuka dan duk abinda aka yi mata ko hararta aka yi, Sai tayi kuka dan haka ango sai ka kiyaye dan karka ce ba'a sanar da kai ba, sannan amarya tana da hakuri uwa uba kawar da kai akan abinda duk ba'a sanyota a ciki ba, tana da ilimin ta dai-dai gwargwado na arabi dana zamani, sannan akwai shagwab'a, ga karatun novel’s da son girki, My bestfren is amazing to the extend that no word could describe how sweet she's. Ga 'kamshi malam, Angonmu xaka sha 'kamshi. dan haka ango Saif sai ka shirya dan wasu abubuwan sirri ne sai kunyi aure zaka binciko su.' May your new home be forever blessed.”

Gabaki d'aya gurin babu wanda bai yi dariya ba, shi kansa Saifullah banda yana jin haushinta yaso ya dara sai kuma yayi ta maza ya basar. Riri na komawa wajan zamanta Abbas ya taso wanda shine zai bada tarihin ango, yana sosa saman hancinsa yace.

''Kowa dai daga gani yasan angon nan ba baya ba, shalele ne d'an gata d'an auta kuma d'an gayu. Ni abu na farko da zan bawa amarya shawara akai shine, kiyi ta hakuri domin kuwa mijin nan naki akwai 'yan mata gashi sune suke kai masa hari, abinda zance dake shine kisan yadda zaki wajan kama zuciyarsa ya zamo naki ke kad'ai. Sannan Saifullah yana da hakuri wanda ba kowa zai shaida hakan ba sai wad'anda suka zauna dashi, Toh Aboki na dai miskili ne gaskia, mr arrogant ba hehe, amma azahirin gaskia he's fun to be with, Saboda bestie na komai yanada time awajen sa, yace time dinsa is priceless. Amma amaryar mu kinyi sa'a saboda saif is kind, attentive and most caring wlh.. sannan lastly Kiyi hak'uri da addicted kalmar sa ta kullum wato so suffocating. Nima dai a karshe zance amarya ba zata gama sanin waye ta aura ba sai sun fara rayuwa, Allah bada zaman lafiya ya kawo kazantar d'aki bata sharaba ta....''

Saifullah kuwa cikin makoshi ya furta,
“So suffocating”

Gabaki daya gurin sai ya hargetse da surutu, wasu suce Allah sarki Islam wasu kuma suce ai itama tana da kyau wasu suce idan ta kama wata na soyayya da mijinta taci kaniyarta, da alama dai Abbas yabar gutsiri tsoma a wajan yayin da shi kuma yana gefe yana bankar dariya harda rike ciki.

Amarya Islam na dosar tsakiyar fili wace jikinta ya kuma yin sanyi jin yadda mijinta yake, aka canxa waka xuwa na shuwas wato can dangin mahaifiyar su baban Saifullah, wakokin khamal yaqub/mansur ne ke ta tashi dana Amina rawaram.. Islam na xama aka fara gudanar da al’ada, komai a tsare Saifullah da Islam sai magana suke a hankali, kai kace hira suke yi, amman ina warning yake korawa Islam kan tacigaba da acting it suits her, idan ta nuna akwai wani abu a tsakanin su, sai ya dizgata a gutin ita kuwa cewa take ya kyaleta, yana kara damke hannuwanta har wani lumshe idanu yake.

Anci ansha ankuma gyatse, can na hango 'yan Saiful_Islam fans group da home of novels suna lafta loma, idanuwa hud'u mukai da rano dake saye kisre tana dannawa a nursing bag d'in affan girgiza kai kawai nai don tasaba, Can gefen Hall kuwa rano Online novels ne da ya hajja ce novels keta lomar abinci, excellent writers members ma can na hangosu irin su nafee anker da didi sai danna snacks suke a jaka..

Cikin basarwa nace wa Ya Hajja dake gefe ''Gaskia k'awayen Billyn nan (billyn Abdul) basu hadu ba, kallesu suna yarfa mu a idanun mutane.'' dota billy s fari dake gefe taja tagumi tana cewa, ''wallahi Mom sai a hankali kam, mu tafi kawai so uncomfortable.''🤟🏼

Washe gari akai English party wanda su Ya Safa suka had’a. Daganan akai bud'an kai da safe a gidan su Saifullah dake Abuja, Saboda rankatakaf k'wansu da kwarkwatar su tun biki na sati hudu suka dawo Abuja da xama, hadadd'en gidah mai kyau na mace d’aya sama da k'asa Alhaji Faruk mahaifin Saifullah yabasu kyauta su zauna shida matar sa, anan unguwar Asokoro. Tunda aka fara maganar kaita gidan ta Islam take kuka mai tsuma zuciyar duk wanda yake sauraro.


_kunji shiru kwana biyu ko? Wlh rasuwa akayi mun, Banda nutsuwar typing shiyasa. Thanks for the messages and call. Allah ya bar zumunci💕_



_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 46-49_*

_SHAFIN YAU NA KI NE MYRIAM💕FATAN ALKHAIRI AGARE KI TAWAJE NA🌹ALLAH YA BIYA MAKI BUKATINKI NA ALKHAIRI, KUMAO🤟🏼_

_nanahafsat.wordpress.com_


Nannauyar ajiyar zucia Islam ta sauke bayan fitar Saifullah. Sai raba idanuwa take yi. Dakyar ta iya jan sayyadar ta, tashiga ‘bandaki, alwala tayo tayi sallah, ta bude drawer dinta da su Yakolo suka shirya mata kaya, riga da wando kakkaura ta ‘dakko ta saka. Tabi lapiar gado, Don dama tayi sallah d’axu. Wayar ta, ta ‘dakko ta shiga WhatsApp, messages rututu tagani ana tayata murna da Allah yasanya alkhairi. WhatsApp family group ‘dinsu ma na ‘Y’ar Gaya Fam Bam’ duk maganar bikin ake yi, sai na secondary school dinsu na BNA 2k14. Shima sai yad’a zancen akeyi, ita dai dariya kawai takeyi, sannan ta turawa kowanne grp emijo na love ❤. Nan aka shiga maganar ‘ya amarya da yin reply,ina ango,’

“Yana gaida ku, sai da safe..”

Tacewa kowannen su, kafin ta kashe data dinta ta kwanta, ko takan reply din Lee dake cewa ‘sai tazo gashin amarya da safe’ bata bi ba, nannauyan bacci lokaci d’aya yai awun gaba da ita. Da asubah ta mike jin kiran sallan masallacin mak’otansu, hawaye ne ya ciko fal idanunta na ganin dagske dai tabar gidah har abada, kiran sallar ma ba ‘daya bane, Ta furta aranta.

Bandaki ta fad’a, tayo wanka had’e da alwala, sallah tayi da azkhar. Kafin ta dakko littafin anatomy tashiga karantawa, haka wani baccin gajiyar ya sake awun gaba da ita akan sallayar sallan. Saifullah kuwa da kyar ya tashi yana murza idanu, bandaki ya shiga yana had’a hanya don bacci ne fal idanun sa, ya sakarwa kansa shower. Sai da ya fitar da baccin daga idanun sa, sannan ya ‘dauro alwala ya fito ya zira jallabiya ya fita masallaci, ana idarwa kuwa ya shiga bakinsa dauke da adduar shiga gidah,Kamar ya shiga ‘dakin da Islam take sai kuma ya fasa yana haurawa sama abunsa, wayar sa ya janyo yana duba time table d’insa, ‘jogging time’ shine abunda yakamata yayi a lokacin. Kayan exercise dinsa ya ‘dakko yana feshesu da turare, sannan ya zura su ya fice motsa jikin daya saba. Haka yai ta jogging har takwas saura kafin ya koma a matukar gajiye, ya bude gidan don ba’a kawo musu mai gadi ba tukun.

Lokacin kuma Islam ta gama turara kayanta akan kabbasa, dinkin riga da skirt, cikin dakakkiyar atamfa Holland, pusher pink and black color, mai zanen agogo. Ta gyara ‘dakin duk da ba wani datti yai ba, haka ta karkad’e ko’ina tana yaba tsarin gidan. Ba kadan ba yayi mata kyau, sosai kayan da aka zuba sun ‘kara ‘kayatar dashi. Simple ‘dauri tayi ta fito hannunta rike da burners guda biyu da ledar magic coal, ta jona burner ‘d’aya a corridor ta zuba turaren halut, a parlorn ‘kasa kuma ta jona ‘d’aya ta zuba ‘sandal bange’. Kitchen ta nufa da ledar magic coal a hannunta tana yaba tsaruwar kalar kitchen cabinets din, domin orange and black ne, sai kitchen utensils kuma duk silver color aka zuba mata, santin komai take yi tana shi wa iyayenta albarka. Nan da nan ta kunna gas ta dora coal igniter ta kunna coal biyar aciki, suna kamawa ta zuba a kasko, tuni ta barbad’e shi da turaren wutar Hawi. Jama’a gidah dai ya tashi da ‘kamshi kala kala, ba a magana kawai, Ga na jikin ta dake tashin turaren kaya dana khumrah’s.

Heater ta jona, ta ‘dora ruwan zafi na tea. Don taga komai akwai shi wadatacce a kitchen din, domin store dinma shak’e yake da kayan gara, tea yana tafasa ta juye a royal flask dinta ta kai kan dinning ta’ajiye. Ajiyewar ta yayi dai-dai da shigar Saifullah parlorn, bakin sa ‘dauke da sallama. Amsa masa Islam tayi duk a rud’e take. Tunowa da jawabin Inna Bilkisu datai hakan yasanya ta hanzarin tsugunnawa, cikin siririyar muryar ta tace,

“Ina kwana?!”

Tabe baki Saifullah yayi, bayan yagama kalleta sama da ‘kasa, ga ‘kamshi na dukan hancin sa na jikin ta da turarukhan wutan, cikin turo baki gaba yace,

“Yana kwano.”

“Me za’a dafa maka?” Cewar Islam, kanta a ‘kasa..

Ware idanuwa Saifullah yayi, yana mata kallon renin hankali kafin yace,

“Ni zaki dafawa abinci?! Lalle ma yarinyar nan.”

Yana gama fad’a ya haura sama abunsa, tab’e baki Islam tayi, ta koma kitchen, cikin minti biyar ta kammala dafa indomie d’aya had’e da soyayyen kwai guda biyu. Daki ta koma abin ta, tana ci, sannan ta koma kitchen ta wanke duk abunda ta ‘bata. Ta zauna a palor tana tunanin cakwakiyar zaman da xasuyi da Saifullah. Tana jiyo ‘burin ‘burin ‘dinsa a kitchen din sama. Ashe coffee ya had’a a coffee machine. Sai tara dai-dai aka kawo musu abinci daga gidan su Saifullah, Fatma da Humaira ne suka kawo, sai tsokanar ta sukeyi itadai murmushi kawai take. Cikin haka kuwa Saifullah ya sakko, sanye cikin dakakkiyar shadda galila golden datasha aikin hannu milk color, hular sa a hannu milk color yana gyara karin ta, Kallo ‘daya yai musu dukkan su ya maida kansa kan hular sa, Fatima yayar sa ta mike tsaye tana nufar inda yake,

“Autan mu..”

“Ya fati..”

“Na’am Auta, yauwa ga abinci can aunty tace akawo muku, naga amaryar mu ma har da wahala, tayi tea gashi can a dining.”

“Tohm angode”

Cewar Saifullah, Humaira dake gefe tace,

“Ya Saif ina kwana?”

“Humaira..” abunda yace kenan kawai ya sa kai zai fice, Fatima ta riko rigar sa,

“Ina zaka ango da sanyin safiyar nan? Indan mune dawo ka zauna, yanzu zamu tafi. Dama sallama nazo muku yau zamu koma mu.”

Ware idanuwa Saifullah yayi, cikin sauri yace,

“Komawa kuma?! So soon haka? Amma banda Mami ko?”

“Duk ‘yan lagos yau kowa zai tafi bare ni da ke port-harcourt,k..”

Ai be jira ta gama ba ya fice cikin sauri, Islam dai duk tana jinsu bata tanka ba, nata dai murmushi ne kawai, Fatima da Humaira suka shiga hirar su, lokaci zuwa lokaci islam ke samu su baki, sam kunya take ji, haka kawai taji har Humairan take kunya, uwa uba kuma Fatima yayar Saifullah.

A ‘dari Saifullah ya figi motar sa, sai gidan su, yana zuwa ya tarar kuwa yan uwa nata shirin tafiya, duk sai yake jin ba dadi, haka dai ya amsa gaisuwar kowa awajen a kunyace musanman yadda suke tsokanar sa, ‘dakin Haj Zuwairah ya nufa, lokacin ta fito kenan daga kitchen hannunta rike da kofi da kunun tsamiya aciki. Fad’ada murmushin ta tayi, tana karasawa cikin dakin.

“First love..” cewar Saifullah,cikin shagwababbiyar murya.

“Auta na.. kadde kace su Fatima ba su kai muku abincin ba, yau naji shirme a wajen yaran nan.”

“No sun kai.. Ni first love zuwa nai wajen ki, I love and miss you, dakyar nai bacci jia” ya karasa fada yana dora kansa a cinyar ta.

“Shine ka baro yarinyar mutane acan? Ni auta yaushe zaka san ka girma ne? Tashi ka tafi”

Make kafad’a ya shiga yi, yana jijjiga kansa alamun a’a. Cikin cuno baki yace,

“Ni fa first love kinsan inde ba siblings dina ba da ku, da sauran family i barely eat with strangers.”

Salati Haj Zuwairah ta rafka tana ‘daga kansa daga cinyar ta,

“Wacace stranger auta? Islam matar taka ce ta koma bare kuma? To tashi tun muna shaida juna ni da kai ka tafi gidan ka, ko na mugun sab’a maka. Akan yarinyar nan Allah auta zamu ‘bata dakai, ka kasa sakin jikin ka da ita, kar dai kacemin kana mata wannan halin naka itama.”

Cikin cuno baki gaba yace,

“First love, Ya Fati ce fa tace yau zaku tafi..”

“Sai akai yaya da tafiyar mu? kai fa nace ka kwantar da hankalin ka, Baban ku yace zamu dawo muma nan ‘din cikin shekaran nan, to menene abun damuwa kuma uhm?”

Shiru Saifullah yayi, gaba d’aya tamkar zaiyi kuka haka fuskar sa ta koma, ganin hakan yasanya Haj Zuwairah, tausar sa, don tasan halin autan nata baya cin abinci sai ta tasa shi agaba, kamar yaro, bayason abinci, yawanci sai abu mai ruwa-ruwa, kuma bana ko’ina yake ci ba, sai na gida, Sam bayason na roadside ko na wasu restaurants din. Abincin ta zubo masa, da kunu sai da yaci sosai, sannan ta tasa ‘keyar sa suka tafi, dama tayi niyar zuwa ta gano gidan daganan ta musu sallama, fal suka cika motoci uku, sukaje gidan . Lokacin itama Islam yan uwan Ammi sunzo fal na bornu suma duk yau zasu juya hakama na ‘yan ‘kauyen y’ar gaya. Tuni gidan ya kacame, Ita dai Islam na dakinta tana canza wani kayan, domin tayo wanka na biyu. Ta shirya cikin wani lace ja, doguwar rigar A shape, hannun kuma peplums akai masa. Ba kadan ba tayi kyau. Light makeup Lee keyi mata,

“Lam Lam ba ki labarta mun first night ba..”

Dariarta Islam ta danne, ko da hakan ta kasance ai ba zata tab’a fada ba domin Yayya Safa tace karta soma bawa kowa labarin yadda sukai auratayya da mijin ta, dama duk wani sirri dake tsakanin su, don babu kyau. Murmushi tayi kafin tace,

“Bari kawai, ba’a magana it’s beyond your imagination, ki shirya hajjaju..”

Lee ta bude baki, ganin da gaske labarin da take ji akan hakan ashe gaskia ne, Yatsina fuska Lee tayi kafin tace.

“Tab zan iya yadda kuwa?”

“Da me fa” cewar Islam, cikin zakuwar abunda Lee zata fada.

“Wallahi ina gaya miki, Fahad ya matsa shi aure kwanannan, Naga abun nasa na neman zautar dashi nace yafadawa Baba sunfi kusa, shine jiya yake cemin cikin satin nan za’a kawo komai, kuma biki bayaso ya wuce nan da wata ‘daya.”

Cikin murna Islam tace,

“And so?! Kakki wani damu wallahi, Allah yasa hakanne yafi alkhairi, mu gwangwaje mu rak’ashe.”

“Waye zai barki ki rak’ashe ki gwangwaje? Lokacin ma akwai little unborn, beside Ya Saif baze yarda ba”

Tab’e baki Islam tayi, cikin cuno baki tace,

“To y’ar ciki baki, sai ki hana ai..”

“That aside.. Ni kuwa kinji labarin cousin d’inki Saifullahi, zai fara lecturing a school namu ko, as visiting lecturer amma, shi zai ‘dauki course ‘din: Introduction to Humanities and community medicine”

Tabe baki Islam tayi, kafin tace,
“Lalle, Za’a sha ruwan carryovers”

Lee ta kyalkyale da daria kafin tace,
“Kiji tsoron Allah Lam-Lam, dan jinin ku bai hadu ba sai ki laqaba masa sharri, in sha Allah zamuyi passing kowanne course with flying colors..”

Islam ta mike tana kallon kanta a wani mudubi, dogo fari kal, kana kallon kanka full dnka ta ciki. Ba kadan ba ta yaba kwalliyar da Lee ta mata, ta faffesa perfumes kafin tace,

“Can ta matse muku ke da shi, yanzu dai tayani kwaso ledojin nan, Ammi tace na babbawa duk wanda sukazo zasu tafi..”

Kad’a kai Lee tayi, tana duban ledojin, atamfa ce guda d’aya, da kwalba cike da turaren wuta, sai kasko da hair dryer set a kowacce leda, kin kima sukai, suka kai parlor, Islam duk ta takure da irin shegen kallon da Saifullah ke jefanta dashi, in sun had’a ido kuma ya sakar mata harara, ita abunma daria yake bata.

‘Y’ar walima dai akai na yan uwa da suka zazzo, yan bornu ne suka fara yi mata sallama suka tafi, ta bisu da ledojin su, daga nan yan Y’ar gaya suka ‘daga suma, bayan sun tafi da awa d’aya su Haj Zuwairah suka fara mikewa don tafiya, Saifullah yayi rau-rau da idanuwa kamar zai yi kuka, sosai ‘yan autancin suka motsa masa, sai da Haj Zuwairah ta tasa ‘keyar sa ‘daki, daga shi har Islam din ta sasu agaba, ta dubi Saifullah tana murmushi kafin tace,

“Haba auta, ai sai matar taka ta rena ka, ‘katoto dakai zakai kuka”

Ai kuwa daria ta tahowa Islam ta gimtse ta dakyar, Nan de Haj Zuwairah ta shiga yi musu nasiha da jan hankali na yadda zasu gina rayuwar auren su, ta ‘kark’are da,

“Wannan sabuwar rayuwa ce kuka shige ta, wadda ba irin ta baya bace, sai kunyi hak’uri da juriya akan komai, ga ku duk ‘yan auta, ni dai auta ga amanar Islam nan, kaga itace karama dan Allah ko menene zatai maka kayi hak’uri, komai ‘dan hak’uri ne, ke kuma Islam ki bishi sau da ‘kafa, karki bi zugar ‘kawaye ko shawarar su wurin munanta masa, yi nayi bari na bari, nasan Auta na jan ido ne sai da magani, sai kina hak’uri dashi, amma idan ki kai hak’uri zaki ga ribar sa, domin shi mutum ne mai saukin kai, Allah ya muku albarka..Duk abunda kike bukata ki gayamin kinji auta ta?”

Murmushi Islam tayi tana rufe fuska jin itama ana kiranta da auta, Mami tai daria kawai kafin tace,

“Sai maganar abinci, sai kin matsa masa bayason abinci, tun yana ‘karami muke fama, ungo nan, lists ne na duk abunda yake ci.” Ta karashe maganar tana mika mata wata takarda, kafin ta sake cewa,

“Kema ki dinga cin abinci kinji auta ta, duk abunda kike so kici ki girka kinji, idan an kawo miki y’ar aiki ma sai ta dinga tayaki da wasu abubuwan, Allah ya muku albarka..”

“Ameen..” suka amsa gaba ki d’aya.

Dakyar dai Saifullah ya bari su Haj Zuwairah suka tafi, har ‘dan zazzabi yai, domin duk dunia yafison mahaifiyar sa, ya shaku da ita fiye da komai, bai tab’a soyayya ba, bai san ya ake yi ba, domin duk ‘yammatan dake nuna suna sonsa ba ya taba basu fuska, ya ‘dauki mata marassa kamin kai, aganinsa duk haka mata suke, domin yadda suke farautar zuciar sa abun har mamaki yake bashi, shiysa ya jingine kalmar So gaba d’ayanta ballantana soyayyar kanta. Shi kadai yake rayuwar sa, ko kadan bai taba sawa a zuciar sa, zai yi soyayya ba bare aure nan kusa ba ma, sai gashi rana tsaka anyi mai auren dole. Auren dolen ma da yarinyar dake rokar maza su aure ta, take kuma zubar da mutuncin ta a titi....

Haka dai rayuwar gidan *SAIFUL_ISLAM*, ta cigaba. Kowannen su harkar gaban sa yake, gwara ma Islam tana k’ok’arin saukar da hakkinta na gaisuwa dana abinci, amma sam bayako kallon dinning table, kullum sai dai ya hada porridge yasha, gashi scent din abincin ta na shiga har hanjinsa don tsabar dadi, amma saboda fadin rai da miskilanci irin na Saifullah ko kallo mai abincin da abincin basu isheshi ba..

Haka dai ta koma makaranta, haduwar su kullum sai magrib, ta gaisheshi ya amsa a dak’ile, har bikin Lee ya ‘karaso, da ita aka karbi lefe da komai, aka fara shirin biki, su bridal tea party da duk sauran events da akai Islam taje, domin Ya Bala ya aiko mata da kyautar mota, tuni harta koya cikin sati biyu ta kware. Ita ta tuk’a kanta ko’ina, ita har addua take yi Allah ya kawo k’arshen wannan ‘kaddararren auren nata da Saifullah, tunda ta gano baya sonta ba kuma zai tab’a son taba a cewar ta, domin shekaran jia abunda yace mata kenan, ‘baya son ta ba kuma zai tab’a son ta ba’. Ta ajiye kalmomin sa a kundin zuciyar ta, sosai tai musu kyakkyawan mazauni.

Ranar lahadi aka kai Lee gidan ta dake nan garin Abujan, domin basu da nisa sosai ma da gidan Islam din, shiysa ma Islam ta ‘kara jin dadi, ganin ta samu y’ar uwa kusa da gidah. Monday da sassafe Islam ta gama gyaran ko’ina na gidan lungu da sak’o, ta sassaka turarukan wuta, riga da skirt tasa na English wears ta ‘dakko after dress shara-shara a hannu zata yafa, da babban mayafi wadatacce saboda yanayin zafin garin. A lokacin Saifullah ya sakko shima, sanye cikin Kaki na NYSC zai je monthly clearance, yana tafe yana taje sumar gashin sa, kallon kallo sukai ya dauke kansa, Islam ta daure ta dan rissina tana,

“Ina kwana?!”

“Lapia.” Ya fada a takaice yana wani shan kunu.

Ita dai Islam kitchen tayi abinta, ta had’a kayan breakfast dinta a wata y’ar jaka, ta zuge ruf abunta, a kitchen ta zura rigar ta yafa mayafin,bakin nan ya sha jambaki ja,Ta koma parlor inda yake, daga tsayen tace masa,

“Toh ni na tafi school, and I might be late today, Saboda yanayin lectures din namu na yau.”

Tana gama fada ta juya zata tafi, Don kullum idan tayi masa sallama zata tafi baya tankawa, Ita dai tana k’ok’arin binsa ne kawai,

“Ke..” ya fada yana wani yatsina fuska,
Juyawa tayi tana kallon sa.Batare daya kalleta ba yace,

“Koma ki saka hijab, ki rage wannan lip stick din yan ‘kauyen da kika sa, you luk so suffocating..”

Tabe baki tayi,cikin kasa da murya ta furta,

“Latsi..”

“Kika ce mene?”

“Da kai na nake..”

Ta bashi amsa da sauri tana komawa daki,gudun karta makara, kayan gaba d’aya ta canza, zuwa wani material blue and pink, ta zura jilbab tafito, Sam ta manta da maganar janbaki, zata wuce yai taku d’aya biyu ya riko ta,tuni jikin ta ya fara rawa, siririn tsaki ya saki yana harararta,cikin isa yace,

“Wato saboda ga sa’an ki ko? Na miki magana ki goge jambaki shine kikai ignoring ko?”

Shiru Islam tayi, tana raba idanuwan wannan bakon al’amari, k’ok’arin kwatar kanta take ya hana, ta hanyar riko hannayenta ya jasu can k’arshen corridor ya jingina ta,hannun sa sakale da kugunta, kafin tayi aune sai ji tayi ya had’a bakin sa da nata ya shiga yi mata wata irin sweet and passionate sumba mai ratsa jiki, mutumin ku daga shanye jambaki ba sai ya rike lips din yarinya ba, har wani lumshe idanuwa

Please Login or Register in order to submit comment