Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai harara, kamar daga sama taji yo muryar Aji Mommodu yana cewa,

“Zaki ci gaba da zama da shi? Ko kuwa ya sawwake miki?”

Sau uku yana maimaitawa, Islam kanta a ‘kasa tana murza hannuwa, cike da kunya tace,

“Baba ya sawwake min...”

Take ji, da ganin Saifullah suka ‘dauke, na’urar memory card din kansa ta chake, subscription din yayi expire, duk wani gig take tattare zance yayi ‘dif daga bakin sa, a hankali ya sulale a ‘kasa ya fadi.... ji kake d’if, numfashin SAIFULLAH FARUK MUHAMMAD ya tsaya chak.....

XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽


DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 69_*

“Zan koma ‘daki na Baba..”

“Masha Allahu, Toh Allah yasa ki koma a sa’a, Allah ya kad’e fitnah a tsakanin ku, ya baku zaman lapia mai ‘dorewa, ya baku zuri’a ta gari, mai ‘dimbin albarka, Ameen”

Kanta a ‘kasa, cike da kunya tace,

“Ameeen...”

A lokacin kuma Alhaji Faruk suka shigo shi da Abbas, Bayan su kuma Saifullah ne. Da alama ‘dakko su yayi daga asibiti, garin kallon Islam da Saifullah keyi sai da yayi tuntub’e zai fad’i, Abbas dake nazarin sa yai saurin rik’o shi yana daria kafin yace,

“Aboki! Easy mana...”

Gaishe su tayi kanta a ‘kasa, Abbas yayi musu sallama ya tafi gidah, parlor yadawo daga Aji Mommodu sai Aji Faruk da Saifullah, sai Islam dake gefe, Haj Zuwairah ta fito daga mab’oyarta da Fatma wadda ta haye sama, ita kuma Mami tashiga parlorn tana murmushi kafin tace,

“Sannun ku da dawowa, ya jikin na ka?”

“Na warware first love”

“Masha Allahu! Allah ya ‘kara afuwa”

“Ameen” suka amsa baki dayan su

Alhaji Faruk ya ajiye robar ruwan daya kwankwad’a kafin yace,

“Toh sai mu ‘dora daga inda muka tsaya ko?..”

“Akan me fa?!”

Cewar Aji Mommodu dake gefe yana ajiye wayar dake hannun sa, Alhaji Faruk ya nuna Islam yana cewa,

“Ta Islam, tunda tace gwara ya s...”

“Tace zata koma ‘dakin ta ai, mun gama magana..”

“Alhamdulillah abu yayi kyau, Toh Allah ya tsare gaba.”

Alhaji Faruk ya fada, murmushi fad’ad’e a fuskar sa, Saifullah dake kan kujera ya sauka daga kai yayi sujjadar godia ga Allah, abisa wannan daddad’an labari daya doki kunnen sa, cikin hanzari ya mike yana cewa,

“Mungode Allah ya saka da alkhairi, Tashi mu tafi.”

Ya karasa yana mai nuni da Islam wadda kunya ta mamayeta ganin idon Saifullah ya rufe ya ma rasa agaban su wa yake, su Haj Zuwairah kuwa baki bude suke kallon sa, Sai itace ma ta ‘dan bata fuska kafin tace,

“Wai ni auta ina ka kai kunyar ka ne? Agaban namu kake cewa ta tashi ku tafi? tukunna kai ka kawo ta ne? Toh ba zata tashi ba sai..,”

Aji Mommodu ya dakatar da ita, ta hanyar daga hannun sa da yai mata alamun ta dakata kafin yace,

“Toh tunda yace haka ku bashi itan mana..”

Suka ‘kyalkyale da daria dukan su, Saifullah ya fara sosa ‘keya da alamun ya manta a gaban su wa yake, Haj Zuwairah tayi murmushi kafin tace,

“Zata je ma gidan barkar matar yayan su data haihu, anan Ganges street dake maitama ko auta ta?!”

Cike da kunya Islam ta ‘daga kanta alamar Eh, kafin tace.

“Eh Mami..”

“Yawwa to ga abinci can a dinning, Daddyn su da Abban Khaled ku ci kar yai sanyi dan Allah..”

Mikewa sukai su ka nufi dinning area, Haj Zuwairah ta shiga serving ‘din su abincin, Islam tai kitchen tana had’o musu lemonade Saifullah ya shiga, rufe ‘kofar yayi ya ‘karasa da sauri yai hugging dinta, Sam bata san da mutum a bayanta ba, sai ki tayi an bata wani huge mammoth hug, ‘Kara zata yi yai saurin rufe bakin ta da hannun sa, a rad’a-rad’a yace mata,

“Scaredy cat kawai, calm down Mrs Saif, Ni ne, I love and miss you, Kwana biyu baki zo asibiti ba, ance kuna practicals ko?..”

“Uhm..”

“Allah ya baku sa’a Love.”

“Amee....”

Ta kasa ‘karasawa, cak kalmar ta tsaya mata a mak’oshi, Saboda ganin Mami ta shiga ciki tana kiran Islam, ja Haj Zuwairah tayi ta tsaya, ganin Saifullah a kitchen yayi kanai-kanai a tsaye ya ‘kwakwume Islam a kirjin sa, hannu ta shiga tafawa kafin tace dashi,

“Toh ‘dan anace, sake ta ka fita, wannan yaro abun naka ya zama sai addua, tun d’axu su Abban Khaled na jiran akawo musu, ashe kai ne ka hana? Toh ‘bacemin da gani anan, kuma ba zata koma yau ba, ehe”

Islam tai tsiri tsiri da idanuwa, Saifullah kuma so sa ‘keya yashiga yi da shafa hanci, a hankali yace,

“First love kiyi hak’uri, Kinga gidan za a basshi kango idan bata koma ba.”

Haj Zuwairah ta gimtse dariar data taho mata. Kafin tace,

“Oh Allah? Da da kake gidan kai kad’ai bai tab’a zama kango ba kenan? Sai yanzu, Toh idan ma za kai tafiyar ka ka tafi, Dan yanzu ma barkan y’ar yayanta zamu je, y’ar yayan ki ce ko Islam”

Cike da kunya Islam tace,

“Eh Mami, shi Ya Saifun dai first cousin ‘dina ne, ita kuma Ya Nusrah step sis ‘dina ca..”

“Masha Allah! Auren zumunci ne ashe, Allah ya sanya alkhairi”

“Ameen..”

Islam ta fad’a a nutse, Haj Zuwairah ta zabgawa Saifullah harara, da sauri ya fice yana kallon Islam, ita kuwa ta ‘dauke kanta kamar batasan yana yi ba, ta gama hadawa ta kai musu parlor, daga nan ta wuce sama ta fara shiryawa zuwa barkar Nusrah, ta haifi ‘da namiji an saka masa Nuradden, yaci sunan Nuradden ‘dan Ya Bala, wato wan Saifullah, suna ce masa ‘baby Nour’.

Haj Zuwairah bayan ta gama dasu Aji Mommodu, sama ta hau. Dakin da Islam da Fatima suke, samun Islam tayi harta gama shiryawa, Haj Zuwairah ta dubeta murmushi fa’da’de akan fuskar ta kafin tace,

“Auta ta! Har kin gama shiryawa? Kin gani ko sake wankan banyi ba, yanzu xan je, ko zaki siyo kayan barkar a nan dunes, kin ga kafin ki dawo nagama sai mu wuce kawai..”

Kan Islam a ‘kasa tace,

“Toh Mami..Hakan yayi, bari naje”

Kudi Mami ta lalo ta bata, Islam ta sunkuya ta karba tana godia, kan ta tsaye ta wuce parking space, ta zura key kenan Saifullah ya karasa wajen, ya bude ya shiga motar, tabe baki tai ta shiga, a zuciar ta tana nanata kalmar,

“Sabon salo...”

“Where to?”

Yafad’a yana binta da mayataccen kallo, kanta a k’asa tace,

“Ba ka karba ba dai kana driving..”

Rausayar da kai yayi, yana wani magana slowly,

“Haba Mrs Saif, tuba nake, ai muddin ina nan toh worry not, i will be ur very own professional driver.. Ina zan kai ki please uhm?”

“Dunes..”

Ido ya ware yana nanata,

“Dunes kuma?! Me zaki yi”

Cikin ‘kosawa da maganar sa tace,

“Kayan babies zan siyo na maza da takalmi da wasu abubuwan ma..”

“Okay...”

Kawai yace, ya shiga yin wak’a a hankali, wadda Islam tasan da ita yake, ganin yadda yana rerawa yana matse hannun ta, ita kam ta shjga uku, ganin yadda yake takurawa rayuwar hannun ta da yawa...

“You don't understand how much you really mean to me, I need you in my life, you're my necessity yeah, But believe me you're everything that just makes my world complete, And my love is clear the only thing that I'll ever see, You're all I ever need. Baby you're amazing..”

“Uhm..”

Kawai Islam tace tana juyar da kanta gefe, muryar sa ta jiyo yana cewa,

“Dan Allah ki cewa su First love za ki bi ni mu tafi, ki dubi girman Allah ki fada musu..”

“Meyasa zan bi ka? idan kai baka kunyar su Mami,ni wallahi ba zan iya ba.”

“Fine to ai ni ne mijin ki, Saboda haka umarni na baki ki fada..”

Wani kallo ta masa, ya shiga inda-inda kafin ya sake cewa,

“Ba umarni ba, rokon ki na ke dan Allah..”

Shiru Islam tayi har suka karasa shagon siyayyar, ya hana ta fita, da kansa ya shiga yayi siyayyar ya dawo ya bude ya sa mata akan cinya, ya koma driver seat ya fara driving, bubbud’awa ta shjga yi komai na maza, gashi ya iya zab’e, cikin murmushin yaba kayan tace,

“Sunyi kyau wallahi, dama ka san kan kayan babies haka?”

Cikin lalubo hannun ta ya ‘kara damke shi yace,

“Eh mana a dole na koya, Saboda unborn dinmu masu zuwa..”

Islam tai shiru taki magana, ashe bashi da kunya? Mamaki sosai ta shiga yi, har suka ‘karasa gida, Haj Zuwairah tayi mamakin ganin su tare, za tai magana Saifullah ya ‘dora mata kudin siyayyar da taba Islam akan cknya. Kafin yace,

“Bar kudin ki first love, na siya a tawa kayan barkar..”

Mami ta zabga tagumi, kafin ta bisu da kallo, Islam kanta a ‘kasa, Saifullah kuma ya zura wa Islam ‘din kallo, cikin ajiyar zucia Mami tace,

“Toh ka kyauta Auta, Dakyau, wato aiken da na mata ma sai ka bita kenan?bita zai-zai, Toh bazan iya ba, idan muka dawo daga gidan barkar kazo ka ‘dauki matar ka ku tafi can gidan ku.,”

Murna awajen Saifullah baa magana, yai kan Haj Zuwairah zai rungumeta ta ja baya tana daga hannu sama, binsu ya kuma yi, Haj Zuwairah tace

“Na shjga aljanna ni Zuwairah, gidan barkar ma binmu zaka yi? Toh ba zaka je ba, matsa kafin na sharara maka mari”

Matsawa yayi yana daria su kuma suka tafi gidan barkar, sun wuni lis acan, kafin su dawo gidah a gajiye, sama kawai Islam tahau ta shiga bandaki, ta sakarwa kan ta shower, wanka tayi da ruwan dumi, sannan ta fito ta shirya cikin kayan Pakistan, riga da wando bak’ake sun sha design din red, lip balm kawai tasa, ta baje akan gado, Nan Fatma ta shjga ta same ta, Islam ta yankura zata tashi tana cewa,

“Ya Fati!..”

“Na’am Islam, Kiyi kwanciyar ki, magana nake so muyi da ke ta fahimta, kuma inaso ki ‘dauke ni tamkar da Safah ko Marwa kike magana, shawarwari zan baki, wanda idan dai kikai riko dasu Insha Allahu rabbi zaki samu riba sosai agidan mijin ki..”

Cikin ‘kasa da kai Islam tace,

“Tohm Ya Fati! In sha Allah....”

___________
_Ya labarin Karime? Tana can rai a hannun Allah, rashin lapia kullum ‘karuwa take yi, sai dai adduar Allah ya yafe mata kawai, ta nemi gafarar su Haj Aysa, kuma sun yafe. Domin har dubo ta sai da suka niki gari har Kano suka dubo Karime, wadda ta dulmiya a kogin ciwon mutuwar jiki(paralyses), hepatitis (ciwon hanta) da kuma ciwon kansar mama, (breast cancer)., Yan uwa dayawa sun guje ta, domin lokacin da take cikin SAMU, bata dama wa dasu, Su kuma yanzu suke ramawa tunda tana cikin RASHI...._

_Yafendo kuwa tusa sai gaba take yi, sannan kullum sai aljanu sun firgitata, da alama turen da tai a baya ne suke bibiyar ta, da temakon Allah dai ta warke da ‘kyar, amma ta kamu da ciwon ‘kafafu mai tsanani, wanda ta kai ga tadena tafiya, da alama dai mutuniyar taku ababe marassa kyau data taya Karimatu suka shuka, shi take girba, har waje an fitar da ita, anyi gwaje-gwajen su MRI, X-RAY, SCAN amma duk komai normal ne, daga ‘k’arshe sai rugar Baffa Ardo, Prof Khaleel ya mai da ta, kan idan ta warke sai a ‘dakko ta.. ga tusa ga ba iya tafiya, data saki ‘daya ake darewa, Saboda tsabar wari, amma ta ‘dau hakan ta ajiye a matsayin alhakin su Haj Aysa ne yasa ta koma haka, ta kuma godewa Allah da sakayyar da ta samu kad’an ce, tafiya dai tadena yin ta har abadah, Sai dai fatan Allah ya kawo sauki._

_Hmm Bangaren Hilaal kuwa rashin virginity din Hibba yana damun sa, domin ya gano y’ar iska ce kawai aganin sa, Saboda daya tursasata ta fad’i gaskia ca tai shima taji labarin haka yayiwa mata biyu a Nigeria har su biyu, kuma ‘yan gidah d’aya. Ya mike zai daketa ta dire tsallen albarkar wallahi bai isa ba, yana dukanta zata rama, kuma ta kai ‘kararsa wajen iyayen sa, kuma aure da sukai na zobe ne, babu yaji bare SAKI. Kyaleta kawai yayi amma duniya ta chake masa, gaba d’aya kwakwalwar sa ta zama malfunction.ya fadawa wani malami yadda ake ciki, bai boye masa komai ba. So sai malamin yaja hankalin sa, ya ‘kar’kare masa da cewar,_

_*YANA DAGA CIKIN ILLOLIN DA ZINA TAKE HAIFARWA TUN ANAN DUNIYA...._*

_1-RUSHEWAR TATTALIN ARZIKI: annabi (saw)ya bayyana acikin hadisi cewa dukkan, society da suka ta‘allaQa da aikata al-fasha. Allah madaukaki yana dankwafar dasu ta fuskar tattalin arziki dss,_

_2-GUSHEWAR KUNYA: annabi (saw) yace da imani da kunya dan-juma ne da dan-jummai, muddin 1 ya tafe to 1n ma baya zama,_

_3-YA‘DUWAR ANNOBA / CUTUTTKA: annabi,(SAW) yace zina bazata bayyana ba kowa, yana aikatawa ba shuwagabanni da, mabiya face sai Allah me girma da daukaka ya saukar wada mutane annoba / cututtuka, Dan-uwa ka dubi yanda HIV/ AIDS yake kashe mutanenmu, Allah ya kyauta,_

_4MUDDIN KAYI SAI WANI YAYIWA NAKA: annabi (SAW) yace ita zina BASHI ce, inkayi sai an maka, Duk wanda yayi zina da “yar-wani ko uwar-wani ko yayar-wani, to shakka babu sai anyi da nashi akwana atashi, Allah sarki hakan ya faru a yankin mu, Wani mutum ya kasance me tsanani wa yarsa (mace) kasancewar ta girma ya hanata fita koda makaranta ne, kullun haka---Rannan saiga “ya“ da ciki, Karshe yasa mata wuk’a awuya kota fa‘da, wanda yayi mata ko ya yanka ta, Qarshe tace - ina wannan Qawarta me zuwa yau-da kullum akace ‘ei‘ tace ba mace bace, namiji ne, Kaga illan zina kenan, yana tunanin ya tsira, sai gashi har gidah anzo anyi wa ‘y’ar sa._

_5-GUSHEWAR MUTUNCI/KIMA ACIKIN JAMA‘A:,ka kula duk wanda yake zina to Allah saiya, cire masa kima da kwarjini acikin jama‘a, zaka ga bashi da kima acikin mutane._

_6-MUTUWA BA IMANI: annabi yace duk me, aikata zina al- fasha o Allah ze zare imani, daga gareshi Qarshe ya mutu ba imani_

_”Annabi yace duk wanda yayi zina da matan, aure- to Allah ze kwashe dukkan aiyukan sa, na al-khairi yabawa mijinta, Aranar tashin al-Qiyama kuma Allah ze masa, azabar rabin wannan al-ummah ita matar ma haka. Innalillahi wa‘inna ilaihir-raju‘un !!_
_Annabi yace babu laifi da Allah yafi kyama, sama da mutum ya saka;_

_AL-AURANSHI A CKIN FARJIN HARAM !!_

_”Dan-uwa na ka sani aduniya dayan shirka wa Allah da kisan kai babu laifi dayafi girma sama da zina !! Allah ka mana katangar Qarfe da aikata zina_”

_Take hawaye suka fara reto daga idanuwan Hilaal, tuni zuciar sa ta yarje masa ya koma Nigeria ya nemi gafarar Hidaya da Hafsaat...._

<><><><><><>>>

XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽


DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 68_*

_SHAFIN YAU NA KI NE *LIEEMERH😍*💕, FATAN ALKHAIRI A GARE KI, NAGODE DA YADDA KIKE BIBIYAR LITTATTAFAI NA, JAZAKILLAHU BIL JANNAH🤲🏻💙_

_nanahafsat.wordpress.com_

*Dr* Jalaludden ne ya shiga ‘dakin da Saifullah yake jinya shi da su Mami da Fatima, daga baya kuma su Aji Mommodu ne da Alhaji Faruk, Islam na ganin su taja baya tana sunkuyar da kanta a ‘kasa. Saifullah kuma yak’i ‘dauke idanun sa daga kallon ta, kan sa su kayi suna tambayar sa ya jikin na sa? A hankali yake basu amsa, dr Jalaludden yai ‘yan rubuce-rubucen sa a file ‘din Saifullah dake hannun sa, kafin ya dora hannun sa akan goshin Saifullah yana cewa,

“Ya kake ji yanzu?”

“Kai na ne yake ciwo sosai, sai zucia ta, tana mun zafi”

Saifullah ya ‘karasa fada yana ‘dan cizan leban sa alamun zafin ciwo, Dr ya kad’a kai kafin ya sake cewa,

“It shall be well Insha Allah, duk zasu dena..”

Ya sake mai da kansa gurin su Aji Mommodu kafin yace,

“Zamu ‘dora shi akan magunguna na kwana uku, da ‘karin ruwa saboda yaji ‘karfin jikin sa, yanzu dai a kawo masa abu me ‘dan ruwa-ruwa, sai kuma a bar mutum daya ya taya shi kwana ki ukun sa, sauran kuma su koma gidah, Saboda yana bukatar hutu, banda hayaniya...”

Yana gama fad’a ya fice, bayan ya musu sallama, duk maganar da ake da Saifullah idanuwan sa na kan Islam, duk tabi ta rud’e da yadda ya rufe ta da mayataccen kallo. Cikin haka Abbas ya shiga shi da su Aunty Lateefa, hannuwan su rike da food flasks na abinci, da sauran abunda za’a bukata..
Bayan sun gaggaisa ne Aji Mommodu da Alhaji Faruk suka fita, kan za su dawo anjima.

Haj Zuwairah ta zuba wa Saifullah kunu a cup, Abbas ya taya shi ya zauna, yana sipping kunun a hankali, sai daya shanye tas, Mami ta mike tana cewa da Abbas,

“Abbas ka zauna a wajen Saifullah pls, har a sallame shi. Kwana uku ne kawai, da safe mu sai mu dinga zuwa kai kuma ka tafi gidah, adai dinga shifting, sa..,”

Bata ‘karasa ba Saifullah ya ‘bata fuska yana cewa,

“First love ni dai abar Islam pls, wane Abbas kuma, ni dai-ni dai kawai Islam ta...”

Mami ta dankara masa harara tana masa dak’uwa kafin tace,

“Saboda me za’a bar Islam? Shin zata iya daukan kane ta kai ka bandaki ko kuwa zata juri daga ka ka zauna? Toh bazata zauna ba kaji na gaya maka, Abbas dai naka shi zai zauna ya taya ka jinyar, danma an temaka ma, da ni bashiru mai gadi zan sa yataya ka kwanan ma sai kuma ga Abbas nan yazo.”

Abbas dake gefe ya shiga daria yana rufe baki, idan sun had’a idanu da Saifullah kuma ya masa gwalo, Saifullah ya shiga kumbure-kumburen fuska yana kunkuni shi kadai, sallama su kai masa suka fara fita, Haj Zuwairah ta dubi Islam kafin tace da ita,

“Auta ta! Ko zaki kwana anan din?”

Islam tai saurin girgiza kai, alamar a’a, Hajia Zuwairah ta sake cewa,

“Toh kuyi sallama, zamu jira ki a waje.”

Kamar bango ya tsage ta fada, haka Islam taji, Abbas ya fice shima, daki ya zama saura su biyu, mika mata hannuwa yayi kafin yace,

“Come to me love...”

‘Karasawa tayi tana tab’e baki, saurin kamo hannun ta yayi yana matsawa, ciki-ciki yace,

“Meyasa kika ce da first love ba zaki kwana anan ba?”

“Saboda ba na so”

Murmushi yayi kafin yace,

“Okay fine! Yanxu dai me zan samu na goodnight?”

Ware idanuwa Islam tayi, cikin turo baki ta..... taji ya hade bakin su, silent Greece kisses ya shiga bata, hawaye ya fara zuba daga idanun sa, Islam taji danshi a fuskar ta, ta shiga kiciniyar ‘kwace kanta ya hana, Saifullah ya zare bakin sa daga nata ahankali ya sa hannun sa yana shafa kanta zuwa bayanta, a kunnen ta ya shiga rad’a mata,

“You make me fall in love darling... I love you, I love you, Dan Allah kakki guje ni, duk rintsi kakki bari a raba auren mu, wallahi wallahi ina son ki Islam, Meyasa bakya so na? Idan akan lefin da nai miki a baya ne, I’m ready to sacrifice my everything just to make you happy, me zanyi ki yafemin?! Kinji.. Islam... uhm? Talk to me.. I’m going gaga.. Love. ki mun magana pls”

Yafad’a yana hura mata a iska a kunne, harshen sa ya zura yana licking kunne, cikin zuciar ta tace

“Mutumin nan dan iska ne tab”

Dakyar ta ‘kwace kan ta, tana gyara mayafin ta, sai da takai k’ofa sannan ta juya tace dashi,

“Get well soon..”

Ta fice cikin sauri, nan ta samu su Haj Zuwairah na jiran ta, cikeda kunya ta shiga motar suka fice, shi kuma Abbas ya koma ‘dakin, ya tasa Saifullah a gaba yana masa daria, sai da yai mai isar sa kafin cikin gwada muryar Saifullah yace,

“First love da ma Islam aka bari..”

Ya shiga daria harda rike ciki, Saifullah ya zabga mai harara yana juya mai baya kafin yace,

“Ai ni an cuce ni wallahi, da za’a rasa wanda za’a had’a ni da shi sai kai, ‘katon banza da kai, gwauro marar mata...Mts”

“Eh ana dai had’a, kuma dole da katon banzan zaku kwana a ‘daki d’aya, jarababbe bakada lapiar ma sai ka ‘kwakwume yarinyar mutane, banza marar ta ido( kunya)..”

“Eh naji, ai halaliya ta ce, matata ce ai, So suffocating.”

Tsaki Abbas yayi, kafin ya shjga daria sai da yai mai isar sa kafin yace,

“Kai baccin ka kawai, angon Islam, autan Mami ‘dan gidan Uncle Modu bada kanka asare..”

Haka dai Abbas ya shiga tsokanar Saifullah suka raba dare suna abu d’aya... Cikin kwanaki ukun nan Saifullah a daddafe yayi su, domin ko sau d’aya Islam bata sake zuwa ba saboda hot practicals suke yi, kuma mostly night lectures ake musu,

A ranar da za’a sallamo Saifullah ne Aji Mommodu ya kira Islam ya tambayeta zata zauna da Saifullah ko ya sawwake mata? Ya ‘kar’kare da,

“Kar kiji komai Islam, idan har bakyason Saifullah kar ki cu ci kan ki, idan kuma ki na son ki koma ‘dakin ki to, duk dai zab’i ya rage na ki...”

Kanta a ‘kasa tana wasa da jelar hannun rigar ta tace,

“Zan koma ‘daki na Baba...”

Haj Zuwairah da Fatima da ke labe suna sauraron su, jin abunda Islam tafada yasa su sakin lallausan murmushi......

——-


XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽


DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_

[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 70_*
_*EPISODE FINALE (KARSHE)_*

_nanahafsat.wordpress.com_

“Toh..Zan danja hankalinki akan yadda ya kamata ki dinga tarairayar Auta ta siga daban-daban kamar; kissa, jan hankali da kuma ladabi da biyayya kowanne xan daukeshi d’aya bayan d’aya namiki bayani akansa, Kisani dukkan xamantakewar rayuwar aure ba xata yiwu ba saida kissa, idan akace miki kissa ta kunshi abubuwa da yawa, kissa ta kasu kashi biyu akwai kissa marar kyau akwai kuma kissa me kyau, Mara kyau itace ta shirye tuggu da makirci da sihiri, Za ki ga kishiya ta kullawa kishiyarta sharri ko idan ta daidaici ta gama girki taje ta tsuga mata gishiri ko yaji ko kananzir ko kuma tai k’ok’arin fitar da ita daga gidan ma gaba d’aya, zaki ga mace

Please Login or Register in order to submit comment