Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonta Islam batai ba, saboda yadda kanta ke matukar sara mata, yatsina fuska Hidaya tayi tana hararar Hafsat din a fakai ce, duk dan saboda ganin datai musu da Hilaal. Juyawa Hafsat tayi tana kwankwasa gaban driver, dake baya akwai dan window daya kare tsakanin driver da passengers.

“Yes..sifik(speak)”

Cewar driver dinsu wadda suke kira da Delman, sunan yasamo asali ne, bayan yakai wasu shekaru yana aiki tare da ahalin na Dr Khaleel. Dan kauyen Dal ne dake garin Kano. Suke mai laqabi da ‘Na Dal’, cu’danya da yare na yau da kullum da yake a habujan, yasa shi fara ‘dan jin turanci. Nan dai ragaya ta sauya masa ya canza sunan sa da ‘Delman’ del a ganin sa a turance yana nufin Dal sai kuma kalmar Man ta ingilishi.

Daria Hafsat ta tuntsire dashi, jin yadda yake turanci ka’in dana’in. Sai da tayi mai isarta kafin tace dashi,

“Dan sa mana wakar joeboy ‘baby’ dinnan”

Kada kai yayi yana sauya wakar daga ‘Mad over you’ zuwa ‘baby’ din da tace.

A haka suka karasa unguwar su, Hafsat ce kawai keda liver din bin wakokin da Delman yake saka mata, Banda Hidaya datai tagumi ta fada duniyar tunanin yadda xatai snatching Hilaal karfi da yaji.

Islam kuwa tun da sukayo hanyar exclusive store, wani mall dake unguwar su take jin gaban ta na tsananta faduwa. Sosai yake bugawa yana mata barazanar fadowa daga k’irjin ta, har suka shawo kwanar gidan su bai dai na bugawa da ‘karfi ba.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” shine kalmar da take ta faman maimaita wa.

Zaune suka hango mazan gidan gaba d’aya awaje, har da yan lagos dukkan su, ciki harda Najibulla mijin Marwa dake Manchester, duk sunzo, saboda babban buri ne Allah ya cikawa Dr Khaleel, kuma abune da ya zama dole a yi masa barka.

Sosai Islam ta shiga rud’i jin yadda gaban ta ke ta faman ‘fat fat fat’ ba ‘kak’kautawa. Horn Delman ya danna yana jiran masu gadi su bude, dake motar ba tinted glasses bane, kana iya hango na waje, suma suna iya gano ka.

Mudasser da Mu’utaseer suna tsaye suna duba wata takarda ajikin bango, shi Mudasser ya jingina yana nuna ta, shi kuma Mu’utaseer ya watsa hannu baya yana magana yana daria, da alama dai musu suke.

Kamaludden kuma da Ibrahim ‘dan Hansa’u da Shamsudden wot suke bugawa akan benchi. Sai Kabeer, Ibrahim da Yusuf su kuma suna kan tabarma dasu da sauran samarin makotan su, sai zuba hira suke, suna musun siyasa.

Mubassher,da Nuradden kuma suna tsaye, da yarinyar yaya Safa a hannun Nuradden. Baby Aysha,sunan Haj Aysa taci, suke kiran ta da ‘pinky’. Sai zuba surutu takeyi,suna kyalkyala daria.

Gate mai gadi ya bude,Delman ya zura Kan mota dai-dai lokacin Saifullahi dake zaune a balcony ya d’aga kansa yana kallon motar, karaf idanuwan sa suka sarqe dana ISLAM...



_sau uku ina typing, yana gogewa wlh😫pls ignore all typos_



_Ashe haka masoyan littafin _SAIFUL_ISLAM._ _ku ke da yawa? Kai Masha Allah.. _ _Duk Ina ganin ruwan comments dinku wlh, kuma ana gayamin duk wanda bana gani, Ana sanar min, knw that I appreciate every single heartwarming feedbacks of urs. _ _Jazakum Allahu khairan. Lobiyu ol fisabilillahi❤_




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
*ASY KHALEEL💕*


*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*😻
*BILLYN ABDUL*🌹


*SHAFI NA 12-13*

_This page is dedicated with love and appreciation to my little sissy..STYLISH BCH,#habeebtyn habeebty.. Mamma Yasmeen😻❤_

nanahafsat.wordpress.com


Babu kowa a wajan, ya jata tare da rik'eta gam, dai-dai kan bakinta da yasha nude lipstick yasa hannunsa ya bige mata shi da k'arfi,

“Ouch..” cewar Islam tana rike da labb'anta wad'anda suke yi mata zafi da rad'ad'i.

“Mugu..azzalumi” Ta fad'a cikin zuciyar ta.

Ture ta yayi can gefe yasa hannunsa yana karkad'e jikin sa kamar wanda ya gogi kura a jiki, yatsansa yasa yana mai nuni da ita yana cewa,

“Bana son na baki kunya ne a gaban friend d’inki wallahi, amma da agaban ta xan sharara miki mari.”

“Toh da nai maka me Ya Saifu?” Cewar Islam wadda lokaci d’aya hawaye ya soma zirara daga cikin idanun ta.

“Da zaki had’a kazamin jikin ki da nawa mana, jiki na one in town ne, amman saboda tsabar kin renani shine kika cacume ni. Ke sai na baki punishment ma wallahi”

Cike da mamaki take kallon sa jin abinda ya fad'a, shifa ya kwakume mata jiki a nasa, sannan k'iri-K'iri yayi musu amman shine yake cewa hakan. Maganar da ya sake fad'ace ta bata mamaki jin yace,

“Tun ba yau ba ina lura da ke so kike ki dinga tab’a jiki na, kin dauka ni irin mazan nan ne masu tab'a mata..”

“Kutu..” Ta furta cikin tsantsar mamaki dajin abinda ya fada kafin tayi shiru tana jinjina kai.

“Ahh! ‘Karasa zagina mana, ga makaryaci ya saki ‘kwan k'aryar daya saba yi miki ko?”

“Haba Ya Saifu. Wallahi ni ba ni ce na tab’a kaba, fad'uwa zanyi kayi saurin ta..”

Bata k’arasa ba sakamakon wani zazzafan rankwashi daya sakar mata a tsakiyar kai,

“Ko da wasa naji kin k'ara bud'a kazamin bakin ki kina musanta abunda nafad'a...Hmm! Zaki sha mamaki na yarinya.”

“Allah ya baka hak’uri.'' Ta fad’a tana kunkuni,

“Karki sake attempting tab’a ni wallahi, Idan kika kara Allah ya isa..” Dariya abunma ya bata, murmushi kawai tayi kafin tace,

“Ai nima ba 'yar iska bace, saboda Ammi tace, duk macen da take bari namiji yana tab’a ta, to zatai ciki ta haihu”

Baki Saifullahi ya bud'e yana binta da kallo, shi ba abunda tace bane ke bashi mamaki, No! Yanayin yadda take motsa bakin tane d'an k'arami dashi awajen, sai yau ya lura tana da wani irin idanuwa masu fassara abubuwa.

“Ke! shekarar ki nawa ne?”

“15 years” Ta fad'a tana gatsine baki. Murmushi kawai ya yi. Kafin yabar wajen da sauri.

“Allah ya isa na, d'an iska kawai”

Ta fad'a a hankali, barin wajen tayi da sauri bayan ta gyara fuskarta ta waya datake kalla. Tsaye tasamu Lee tana vid call dasu Hafsat Rano da Fatima Bichi, su basu samu zuwa ba suna can kano, ko 'yan uwa basuda su a habujan😹

Gaisawa sukai dasu Hafsat Ranon, kafin subar wajen su shiga filin rawa, lokacin su Ya Marwa ne aciki suna taka rawa.

Sabuwar shiga Haj Aysa tayi cikin wata rantsattsiyar Laffaya kalar ‘Amber orange’ , tamkar ba ita ba, domin kwalliyar da akai mata kwarai matuka ta sake bayyana ainihin kyawunta!.

Tuni photographers sukai kanta suka shiga d'aukar hotunan ta, manyan ‘Kawayenta ne ke take mata baya, tana shiga filin DJ ya canxa waka zuwa ta shaba wacce akewa laqabi da, ‘uwar gidah ran gidah’

Wayyo zo kuga bak'in ciki awajen mahassada, komawa gefe sukai, suka yi cirko-cirko, kallo d’aya xakaiwa Haj Karimatu kasan kukan zuci take yi, Yafendo kuwa na fili takeyi a hankali tana sharewa tsabar hassada da tsantsar kiyayya ko ‘yay’an su dake gidajen aure basu bari sunzo sunan ba. Sosai Haj Aysa ta shammace su domim basu san haka xatai kyau ba, duk kuwa da tarin dukiyar da suma suka kashe wajen ganin sun fita kyau amma hakan ya citura.

Hankulan su bai qara tashi ba saida Dr Khaleel ya shiga cikin filin rawar shida abokansa, kowannen su ya balle hancin naira, sai zubasu suke yi. Nan dai DJ ya sake canza aqalar waka zuwa ‘perfect ta Ed sheeran’ Wayyo, nan Dr Khaleel ya yage kunya daga zuciyar sa ya bawa matar sa da ‘yan biyun sa kyakkyawar rungumaa,

MC ya cigaba da zuba kirari, mutane sai ihu suke yi, nan dai aka canza waqa zuwa ganga kura, mutan bornu 'yan uwan Haj Aysa suka mimmike, kowannen su ya shiga taka rawa yana hura hanci.

Sum-sum Haj Karimatu ta mike ta baya ta sulale ta arce zuwa sashenta, bata jima ba Yafendo ta bi bayanta bayan ta zuzzundumawa su Haj Aysa kwandon d'auke albarka a zuciyar ta.

Ganin bata sashen ta, ya sanya yafendon juyawa zuwa b'angaren Inna Bilkisu. Tana tsugun ne a qasa tana matsar hawaye Inna Bilkisun na bata hak’uri, da alamu dai mutuniyar ku ta kasa riqe tsantsar hassadar da takewa Haj Aysa na yau, sosai ta shirgawa Inna Bilkisu k'arya.

Inna Bilkisun tana hakimce a doguwar kujera, hannun ta rike da casbaha tana ja, a hankali take mata magana, kan Karimatun yana qasa,

“Kiyi hak’uri Karimatu, karku sawa kanku damuwa kan hakan, ita ai Allah ke bada ita ko?”

“Kwarai kuwa Inna”

Cewar Yafendo wadda ta zauna daga k'asa, ta shiga yiwa Innan tausar munafunci.

“To kuyi hak’uri kun san dama xa’ai haka, tunda kunga ya jima yana burin samun hakan Allah bai yadda ba sai yanzu, kuyi hak’uri ku cigaba da addua, Idan kuna da naku rabon sai kuga ya baku kuma”

Kad’a kai suka yi suna had’a baki wajen fad'ar,

“Hakane Inna, Allah ya yarda.”

Amma fa ba hakan suka so ba, sun so ta ci mutuncin Haj Aysa, ta fadi maganganu marassa dad’i. Sai dai kash! sam ba haka Inna Bilkisu take ba, domin mutuniyar kwarai ce, wadda tasan dattaku!

Can wajen 'yan rak'ashewar suna kuwa sai tular rawa suke yi, su Lee sai rawa suke amma cikin nutsuwa, haka aka watse bayan kowa yayi hoto da mai jego, sannan kowa yaci ya sha sannan akabi kowannen su da k'atuwar jaka ta rabo, mai d'auke da sunayen 'yan biyun ajiki, tarkace ne na rabo fal aciki domin harda turmin atamfa, akwai kuma extra leda ta snacks.

Daga nan Haj Aysa ta sake canza shiga zuwa atamfar super wax inda sukai anko da Helwa, red color ce tasha stone work, sashen Inna Bilkisu suka nufa da masu hoto, suna shiga suka tarar da su Haj Karimatu da alama suma basu yi tsammanin ganin su ba, domin turus sukai suna raba idanuwa.

Hakan yai nuni da sun qulla qullalliya kenan a wajan, murmushi kawai Haj Aysa tayi, ta karasa wajen Inna Bilkisu, Inna Bilkisu dake kishingid'e ta mike tana tafa hannuwa,

“Maraba da masu gidana,..Bismillahin ku” Ta fad'a tana karb'ar Abeed dake faman kallon ta kamar yasan mai take cewa,

Har dasu Haj Karimatu akai hotuna ransu bai so ba, ganin Inna Bilkisu yasa suka daure suka yi, amma kallo d’aya xakaiwa hotan kasan ransu bai so ba, domin mai d'aukar hotonma sai jaddadawa yake yi,

“Hajia ku biyu d'innan ku d'an yi murmushi mana, Yawwa hajiya” Aikuwa ya karbi nashi rabon hararar, domin Yafendo da xata fita sai data bangaje shi.

“Ikon Allah..” Ya fad'a yana karkad'e rigar sa, domin shi bai masan su din su waye ba.

Haka dai akaita shagali har sati d’aya, kullum sai anyi d'an k'aramin party, a satin ne kuma Safa ta koma lagos, Hakama 'yan bornu duk sun koma amman banda Yakolo da tace ita kam taga gidan zama, tunda sun rabu da mijin ta.

Sam su Haj Karimatu basuji dad'in xaman da zatai ba domin duk tayi kanai-kanai akan komai, ta hana su ai watar da mugun nufin su akan jariran. Idanun ta nakan komai, amma idan tasan wata ba tasan wata ba. Matan Ya Bala ne basu koma ba sai wani satin saboda ana musu gyaren gidah. Kuma Inna Bilkisu zata tsaya ayi sa ranar Nusrah ‘yar Yafendo.

***

Satin nayi ya zo da magana marar dad’i, domin gidan su ‘Aliyu’ wanda yake neman auren Nusrah, sune suka aiko cewar sun janye batun sa rana da aure baki d’aya, domin d'ansu baxai auri marar mutunci ba, acewar su.

Zo kuga kuka a wajen Yafendo, taita d'ura ashariya tana asiri Haj Aysa da Helwa sukaiwa ‘yarta, don sunga zata shiga gidan jin dad'i ta dandali arziki shine sukai asiri suka hana. Tai ta hauka tana birgima.

Aliyu Anas Askira d'an gidan senator Anas Askira ne, shine babban d'a namiji awajen iyayen sa, domin mahaifiyar sa ce kawai matar Anas Askira, su uku ne sauran biyun duk mata ne. Aliyu ya had’u da Nusrah ne ta sanadiyyar kanwar sa Hibbah, da sukai school d’aya suka qulla zumunci mai tsanani, har Aliyu yai sabo da Nusrah, soyayya ta shiga tsakani, suka qulla alqawarin aure. Amma kash Aliyu matashi ne mai son ace ya tara 'yan mata da yawa, yayin su yake kamar hular sawa, yasa ya cire, haka yake tayi.

Ta haka ne kuma ya had’u da d'iyar gwamnan bornu, ta fad'a masa baxata iya hak’uri ba, kuma da aure take son sa dan tuni ta fad'awa mahaifin ta, shi kuwa ganin tilon ‘yar sa na neman sadaukar da rayuwar ta akan d'an sanatan da ya d'orashi akan kujerar mulki yayi hanxarin kiran uban Aliyun ya sanar masa komai, jiki na b'ari jin ya masa alqawarin tsayar dashi a d'an takarar gwamna idan ya sauka.

Hakan kuwa aka yi, ya kira Aliyu ya sanar masa, ko ajikin sa shima ya ji kudi ya amsa da ba matsala. A take suka kira Dr Khaleel suka sanar dashi su fa sun janye.

Ransa duk ba dad’i ya bawa Yafendo hak’uri, don kowacce uwa baxata tab'a so akawo kud'in auren ‘yarta ace anfasa ba kuma. Nan dai yabar Karimatu harda kukan munafunci tana ta k'ara mata famfo kan ai wlh su Haj Aysa da Helwa ne xasu shiga su fita, tunda ai Alhaji Anas Askira d'an kauyen Askira ne dake Bornu.

Sashen Inna Bilkisu Dr Khaleel ya wuce, zaune ya sameta akan sallaya tana addu’a, a tare suka shafa yana cewa,

“Ameen Inna”

Sai data babbashi baki akan dangana da rashin mutuncin da su Alhaji Askira sukai masa, ya kuma bata labarin yaji duk yadda akai har hakan ta faru, gyara xama tayi kafin tace dashi,

“Toh.. Ni kuwa a gani na, mai zai hana a had’a auren Nusrah da SAIFULLAHI...?”








_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER; MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
_ASY KHALEEL💕_


*TUKWICI NE GARE KU:*
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_



*SHAFI NA 14-15*

_This chappy goes to you *MISS HAFSY* favorite co-writer and a dearest friend of mine_😻🌹❤

nanahafsat.wordpress.com


Saurin d'aga kansa Dr Khaleel yai, yana duban Inna Bilkisu. Jaddada kai yai alamun yayi na’am da zancen, Murmushi ya fad'ad’a akan fuskar sa yace,

“Wannan abu yayi Inna..Wallahi yayi, dama na jima ina son had’a Saifullahi da wata acikin yaran nan, sai dai duba da su d'in duk yara ne duka- duka sha biyar suke, kuma ko gama makaranta basu yi ba.”

“Haka ne.. Amma ai ana aurar wa ko k'asa da hakan, sai dai yanzun ba kamar lokacin mu bane tunda inaga Islam ce ma kawai tayi shekaru goma sha biyar ko?”

“Eh haka ne Inna, ashe akwai tazarar shekara d’aya tsakanin su da Hafsat, ita Hidaya ce dai suke sa’anni da Islam.”

“Eh..To amma fa ba cewa nayi lallai ba, ba kuma cewa nayi dole ba, kuyi shawara da d'an uwan naka yadda kuka ga ya dace sai ayi hakan.”

“Haba Inna, ai wannan kyakkyawar shawara kika bayar kinga dama fa aiki yake yi, duk sa’annin sa sunyi aure, kuma shine dai-dai da Nusrah, saboda kinga ta gama komai na karatu, rantsar da su kawai xa’ai watan gobe su zama lauyoyi..”

“Masha Allahu, Allah ya sanya albarka a abinda aka karanta. Munyi waya da wannan yaron, (Ya Bala) yace shima yau zai shigo Habujan, amma ban sanar masa ba tukun sai yazo sai ayi komai a gama ko?”

“Kwarai kuwa Inna.. Hakan yayi wallahi sosai, Allah ya k'ara miki lapiya da nisan kwana mai amfani, Allah ya jikan Malam (mahaifin su) yasa aljannatul firdaus makoma ce agare shi.”

“Ameen ya Allah.. Allah yayi muku albarka”

“Ameen Inna..Bari naje ciki na gaya musu a yiwa Ya Bala girki kafin ya k'araso.”

“Eh hakan yayi. A gaida su”

“Za suji Insha Allahu, yau mazajen naki basu shigo miki bane Inna?”

“Ni nace abarsu garin ya d'an rufa tukun na, sai akawo min su, kaga yanzu da d'an sanyi yau.”

“Eh haka ne kam.. Toh bari naje Inna sai na dawo.”

“Yawwa d'an tsaya..”

Gani yai ya tsaya daga tafiyar daya soma yi ya dawo ya tsugunna cike da girmamawa yace.

“Maganar su Karimatu ne, dan Allah nasan kana adalci sosai a tsakanin su, kar ka gajiya da hakan, ka cigaba . Allah yayi maka albarka.” Kansa a k'asa cike da girmamawa yace,

“Insha Allahu Inna..Na gode k’warai”

Mikewa yai ya fita bayan ya mata sallama, ko bata fito ta fad'a ba, sarai yasan kishi ne ya rufe idanun su jiya suka zo suka yi masa sharri. Murmushi kawai yayi yana cewa,

“Mata.. Kai Allah ya shirya mana zuri’a”

Sashen Helwa ya fara shiga don anan yake, ita kadai ce sai ma’aikatan ta don 'yan biyun ta ma kullum a sashen Haj Aysa suke wuni, sai dai bacci ya dawo dasu. Wani lokacin ma acan suke baccin.

Sun d'an taba hira nan yake sanar mata zuwan Ya Bala. Kitchen ta shiga bayan fitar sa don yin abincin tarbar yayan mijin nasu. Daga nan ya nufi sashen Haj Aysa, ya jima yana d'auke da 'yan biyun sa, gefe kuma su Arfat sai d'ane k'afafunsa suke yi, Islam dake kusa dashi ta zumburo baki,

“Daddy...”

“Na’am Mamana”

“Daddy yanzu kafison su Areef. Sam baka sona kaman da” Ta k’arasa fad'a tana shagwabe fuska.

Murmushi yai yana riko hannun ta da yake a kusa dashi take, cikin muryar lallashi yace,

“Haba nina isa?! Mamana ai kece gaba da komai, kawai dai kinga su ne ‘yan fari a maza amma kuma ai kece 'yar auta a mata ko?” ‘Daga kai tayi tana murna.

Sai da ya jima sosai anan har Haj Aysa ta fito daga wanka ya sanar mata zuwan Ya Balan, kafin ya shiga wajen Haj Karimatu tana zaune tana aikin taunar cingam (chewing gum) dan ya zamar mata al’ada.

Gefen ta kuma Hafsat ce tana kwance rigingine sai shek’ar bacci take.Tashin ta yayi yace ta koma d'aki ta kwanta had’e da jaddada mata karta sake kwanciya a rigingine ba kyau, duk abunnan da yake haj Karimatu danna waya take, sai daya mike zai tafi ne ya dubeta yana fad’in,

“Sai faman danna waya kike, Wai ni ban gaya miki cewar hasken waya na cutar da ido ba ko kuwa?”

“Alhaji wani littafin hausa nake karantawa wallahi, ba kaji dad'in sa ba”

Jaddada kai yayi yana mamakin wannan k'arfin halin nata,

“Toh Ya Bala dai yana nan tafe, anytime from now, za’a d'akko shi a airport..”

“Toh.. Allah ya kawo shi Lapiya”

“Ameen!” Kawai yace, yai ficewar sa sashen Yafendo.

Tana zaune itada Nusrah sai rusgar kuka suke yi, shi abinma dariya yaso ya bashi wallahi, abu ya k'ici ya k'i cinyewa, zama yai kusa da Nusrah, gaishe shi sukai dukkan su, ciki harda Hidaya data fito daga kitchen da indomie a hannunta,

“Daddy ga indomie..”

Kallon ta yayi ita da indomien, murmushi yai yana kad’a kai,

“Nagode Hidaya amman na koshi, indomie sai ku ‘yan indomie generation”

Daria Hidaya ta kyal-kyale da ita tana zuba lomar indomie a baka,

“Daddy kenan, Allah indomie na da dad'i amma kai baka so”

“Zaki koya munci ne?”

“Eh Daddy..” Ta fad'a tana dawowa kusa dashi da plate a hannun ta,

“Haa bakin ka to daddy” Murmushi yayi kafin yace,

“A’a ba yau ba fa sai wani lokacin. Yanzu kije d'aki zamu yi magana dasu Umman ki” (Yafendo da Nusrah).

Amsa mishi tayi da toh, kafin ta haye sama abun ta. Juyawa yai yana fuskantarsu baki d’aya.

Ajiyar zucia ya sauke mai nauyi, hakan yasanya su juyawa su maida kallon su gare shi.

“Nusrah..”

“Na’am Daddy.!”

“Kisani shifa komai na duniya muqaddari ne daga Allah, Wallahi bamu da tsumi ko dabara ta canza yadda komai yake tafiya a rayuwa face Allah ya yadda da hakan, Ina ilimin ki ya tafi? Common and Islamic law kika yi, Duk Ina tarin tauheedin da ku kai yabar kanki? wallahi tunda kikaga haka Allah ne zai musanya miki da mafificin alkhairi, ita rayuwa baka isa ka tsarawa kanka yadda kake so ba, komai kud'in ka, ko mai k'arfin mulkin ka, kai kowacce irin sarauta ce gare ka wallahi sai Allah ya yi ikon sa akan ka, saboda haka ki kwantar da hankalin ki, Insha Allahu rabbi alkhairi ne wannan abu daya faru, dama can shi d'in ba mijin ki bane, kisa hakan a ranki, ki cire damuwa kina jina ko kuwa da iska nake maganar?”

Saurin kad’a kai tayi,

“Abba duk naji, na kuma gode Insha Allahu zan sanyawa zuciata hak’uri.”

“Masha Allahu.. Ni kuma na miki alqawarin wata babbar kyauta nan ba da jimawa ba, zan cika maki ita da yardar Allah..”

Murmushi tayi cike da murna tace,

“Daddy Nagode, Allah ya saka da alkhairi”

“Yawwa..” Ya fad'a yana maida duban sa ga Yafendo data rafka uban tagumi ta dulmiya duniyar tunani,

“Aminah(Asalin sunan ta kenan)”

“Na’am Alhaji.”

Rausayar da kai yayi, hakan ya sanya Nusrah saurin tashi ta basu waje, kalamai masu dad'i yake yi mata, had'e da qarfafa mata gwiwa akan ribar hak’uri, ya jima kafin ya tashi yana fad'in,

“Yawwa, Yaya Bala zai zo yau a kowa ne lokaci zaku iya tsammatar sa”

“Allah ya kawo shi lapia..”

''Ameen.'' kawai yace yasa kai ya fice.

Wurin matan Yaya Bala yaje suka gaggaysa, duk sun caba ado suna jiran mijin nasu ya shigo, shi abinma dariya ya bashi ganin yadda sukai ado kamar wad'anda zasu zab’en kyau. Ya jima suna hira kafin ya koma sashen sa yana nazarin (research) wasu litattafai.

***

Karfe 4 dai-dai Yaya Bala yana parlorn Dr Khaleel, an shirya masa abinci kamar wani restaurant, ya d'anci ba laifi, nan Inna Bilkisu da ke gefe ta shiga sanar masa da komai akan Nusrah kuma kwarai yayi na’am da xancen domin fuskar sa ta nuna hakan,

Shafa sank’on kansa yai, cike da murmushi yace,

“Inna wallahi wannan zance yayi min dad'i ba kad’an ba, shi yasa yau na tashi duk zuciya ta tana dad’i, ashe abunda xai faru kenan, to ni Ina ganin me zai hana kawai a had’e ayi gaba d’aya da nasu Mudasser da Mu’utaseer, don suma sunzo sun sameni da maganar yaran da suke nema, wasu yara ne anan Abujan, ita yarinyar da Mu’utaseer ma yake nema yace k'awar su Marwa ce, Toh Kamaludden ma dama ina shawarar had’asu da Aysha 'yar Hansa’u, Toh kuma ga maganar Saifullahi ma daddad'a tazo. Toh zan yiwa Nuradden magana ma kan lalle ya tsayar da wadda yake so, shi kuma Shamsudden tunda naga mata basa gaban sa, Ina ganin a had’asu kawai da Shema’u, duk mu’aurar dasu mu huta Inna, Kinga nan gaba da an tashi nan da wasu shekaru sai na su Islam, su ukun suma sai a had’e ai nasu ko kuwa ya kuke gani?”

Hansa’u dake gefe sai gud’a take tana rangad’awa jin wannan daddad’an labarin,

“Abu zai yi dad’i, idan yaran zasu bada had'in kai”

Cewar Hansa’u cike da farin ciki, don dama a kauyen 'yar gaya 'yan uwan mahaifin su Shema’un sai gulma suke yi suna yada maganar yara sun zama gand’ama-gand’ama amma taki ta aurar dasu, bayan ga sa’oinsu nan sun tara ‘ya’ya, dan tsabar iskanci ta kwashe su sun koma legas sun iskance gaba d’aya.

“Mu fa muka haife su ba su suka haife mu ba, aure tamkar anyi angama ne da yardar Allah babu mai kawo cikas a cikin su, kuma watan gobe farko ko tsakiyar sa Insha Allahu xa’ai bikin, kowannen su ya tare a gidan sa, Alhamdulillah tunda kowa yana nan ba sai ance a jira wane ba.”

“Allahumma Ameen! Allah ya sanya albarka, ya bamu sa’a a cikin wannan lamarin.”

Cewar Inna Bilkisu wadda fara’a gaba d’aya ta cika mata fuska. Su hud’u ne dama a parlorn, daga Ya Bala, Dr Khaleel, Hansa’u sai Inna Bilkisu. Tsaida shawara sukai kan anjima za’a yi General meeting don a shaidawa kowa abinda aka yanke....



_Munada biki jama’a..💃🏿🥰❤ anko na kece raini za’a fitar🤗_








_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_🧕🏼

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_



*_SHAFI NA GOMA SHA SHIDA(16)*_

_Wannan shafin na kune ‘yan *SAIFUL_ISLAM💕FANS GROUP* Ina son ku, kuna ‘karamin ‘kwarin gwiwar rubutu, Musanman *Aunty Bilk😘, Juwairiyya Ummee*_da *Mamuxee Sule and Ummuh Islam*_ _kai da duk ‘dauka cin ku, Fatan Alkhairi gare ku hazik’an makaranta🙏🏾 jazakum Allahu khairan🤗❤💕__

_nanahafsat.wordpress.com_

Bayan sallar isha’i rankatakaf ‘din yan gidan kowa ya hallara, jikoki kawai aka cire, sai su Arfat da ba wani gane kan zancen zasuyi ba, duk suna sashen Haj Aysa, wajen Yakolo, Safa ce kawai wadda bata nan itada mijin ta Mubassher. Amma dukda hakan anayin live video call dasu, tamkar dai suna wajen.

Addu’a aka fara, gaba d’aya banda su Dr Khaleel babu wanda yasan

Please Login or Register in order to submit comment