Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne, domin shi din la’a..”

Bata ‘karasa ba shamsu ya katse ta, tunda tafara magana yake buga biron hannun sa akan desk din ofishin sa, an rubuta CEO., kwantaccen sajen sa da turawa ke kira da sideburns ya shafa, wani shegen murmushi yai iri na gefan bakin nan kafin yace,

“Pls leave my office.. Get lost”

Zatai magana ya daka mata tsawa, yana fadin,

“Walk out... shameless being kawai.”
_______

XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽


DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 60_*

_nanahafsat.wordpress.com_

_*WASHE-GARI_*

Islam na zaune, ta gama shirya wa zata tafi lectures a ‘dakin da aka bata ta kwana Haj Zuwairah ta shiga, dauke da tray shak’e da abinci. Da sauri ta ‘karasa ta karb’i tray ‘din hannun Haj Zuwairah. Cike da ladabi ta durk’usa tana gaida Mamin.

“Mami Barka da safiya, an tashi lapia?!”

Murmushi fad’ade a fuskar Haj Zuwairah tace,

“Lapia lou auta ta, har kin shirya zaki tafi kenan?”

Kanta a ‘kasa tace,

“Eh Mami.”

“Yayi kyau, Amma ki ‘dan ci wani abun ko? Ba dadi tafiya da yunwa school. Bari na miki packaging snacks sai kici da break.”

“Toh Mami, Nagode Allah ya ‘kara budi”

“Amin auta ta, Bari naje.”

“Toh Mami..”

Bubbude warmers din Islam tayi, chips and egg ne da slice bread, sai plantain da sauce din hanta sai tafarnuwa ce ke tashi, gefe d’aya kuma karamin flask ne, cike da ruwan green tea sai tashin kayan kamshi yake. Ta ‘danci kadan ta mike tana gyara jikinta, sanye take cikin bak’ar abaya mai kauri, ta yane kanta da mayafin abayar, har ta goga purple nude lips ta goge, tunowa da kashedin Saifullah. Mild(marar ‘karfi) turare ta shafa, ta rataya side bag dinta na Dkny. Kitchen tabi Mami, don Alhaji Faruk sassafe yafita suna da board meeting na clinic dinsu.

“Har zaki tafi Auta?”

“Eh Mami nagama”

Mika mata lunch-bag ‘din Mami tayi, Islam ta sun kunya har ‘kasa ta karba, Mami ta fad’ad’a murmushin ta, Sosai take jin son Islam har cikin magudanar jininta, yarinyar na da hankali da biyayya ga tsafta, cikin sakin fuska tace,

“Toh Auta ko na zo na kai ki, ko kuma driver yayi dropping d’inki?”

Kai a ‘kasa Islam tace,

“A’a Mami, na hutasshe ku, ai hannuna ya fad’a sosai, Ina driving ko’ina.”

“Masha Allah.. That’s nice, Toh sai kin dawo, Allah ya bada sa’ar karatu, should in case idan yan gidan ku sun kira, kice kina nan gidan, zan ma dai fadawa Hajian taku.”

“Okay Insha Allah Mami, na tafi.”

Islam na gama fad’a ta fi ce daga kitchen din tana wasa da car key din hannun ta, Sosai ta ke jin Peace of mind a gidan ba kamar prison din da take ba a da wato gidan saifullah, zata fice daga gidan ne a bakin kofar da zata sa da ka da babban parlorn gidan su kai gware da Saifullah, wanda shigowar sa kenan. Ita tana tafiya kanta a ‘kasa bata lura, shi kuma yana tafe yana danna waya, ji kake ‘kauu’, sun gwara kai, Kowanne acikin su yaja baya yana mulmula goshin sa, tare suka zabgawa juna harara, Saifullah ya shagala da kallon Islam sam bai lura da ta fice ba, bin ta yayi a baya yana sauri, zata bude ‘kofar motar ta shiga ya rike handle ‘din kofar yana kallon ta sama da ‘kasa, ba kadan ba tayi masa kyau, sai kace ‘Black Ethiopian’. Ganin ba shi da niyyar matsawa, yasanya ta turo baki gaba, cikin shagwaba tace,

“Dan Allah ka matsa, zanyi late a lectures fa..”

Kissable lips dinta ya kalla, yana licking lips ‘dinsa kamar maye, bata fuska yayi, kafin yace.

“Me nace miki akan shafa jambaki?”

“Jambaki kuma?”

“Eh gashi nan kin shafa”

Ya fad’a yana mai nuni da lips dinta da hannun sa, saurin gocewa tayi gudun karya tab’a mata labbanta, da sauri ta shige cikin mota, tana k’ok’arin tashin ta ya bude ya shiga shima, cike da mamaki Islam ta bude idanu tana kallon sa kafin tace,

“Malam ya haka?!”

Hararar ta yayi, yana gyara zaman seat belt ‘dinsa, kafin yace.

“Hakan ce ta kawo haka malama.. just drive”

Yatsina fuska tayi, had’e da tabe baki,

Ta manni motar a ‘dari tai hanyar makarantar su, So yake ya mata magana amma miskilancin sa ya hana, itama kuwa taja mutuncinta tana sake ‘dage kai, hannunta d’aya na kan sitiyarin mota dayan kuma ta d’ora shi akan volume na cd, tana ‘karo muryar wakar ‘tarhani’.

Har suka ‘karasa cikin school, ‘faculty of medicine’ nan tayi parking, Tana k’ok’arin zare mukullin motar ya riko hannunta, ta fizge tana yarfe hannuwan ta kaman ta tab’a kashi. Cikin zare idanu yace mata,

“Me kika gayawa first love akai na? Meyasa zaki shiga tsakani na da mahaifiyata?! Uhm?”

Kallon tara saura kwata ta watsa masa, kafin ta fice daga motar, fitowa yayi shima, tayi hanzarin saka lock tayi gaba abunta, ya fara binta da takadar dashi ta hanyar ‘daga hannunta, cikin takaici tace,

“Wanda aka damu dashi, shi ake kai wa ‘karar sa, ni wallahi Idan na raina kasuwa ko sautu bana bayar wa. I’m done”

Tana gama fada, tayi gaba abinta tana sakin tsaki, Saifullah ya daskare a tsaye jin kalaman Islam, Sam bai bi takan yammatan dake maitar kallon sa ba, domin inda sabo ya saba, Uber ya kira ta kai shi wajen ppa dinsa.

_*KANO_*

Karimatu sai tauna hakoranta take, tana gatsa harshen ta, tana neman cire kayan jikin ta, sai wasu irin surutai take faman yi tana sakin kashi da fitsari a zaune,

Kawu Amadu ya jinjina kai, cike da tausayi yake duban Hajjan Karime kafin yace,

“Toh wai ina Sidiya ne?”

“Amadu Sidiya fa jia da rana auren ta ya mutu..”

Kawu Amadu ya sake dafa ‘karfen gadon asibitin da Karimatu ke kai kafin yace,

“Kina nufin ki ce garzali ya saki Sidiya itama?”

Hajia dafe da kuncinta hannu bibiyu tace,

“Wallahi saki uku ma yayi mata, ya gano wai tanabin malamai, shine ya dankara mata saki har uku, ya kuma ce idan bokayenta sun iya asiri su bokance shi ya maida ita, cin mutunci dai babu kalar wadda beyi ba”

Tabe baki Kawu Amadu yai, kafin yace,

“Ai ga irin ta nan, abunda aka hanesu da kada suyi, ai ‘ki sukayi, yanzu gashinan wa gari ya waya?”

Ajiyar zucia Hajia ta sauke, kafin tace,

“Amadu ‘dan kira yaron kirkin nan ka gaya masa yadda ake ciki, ka dubi girman Allah ka kira shi, don zumunci zakai ba don Karimatu ba.”

Kawu Amadu( Kawun Karimatu)ne yai ta maza ya kira Prof Khaleel, bugu biyu ya ‘dauka, sai da suka gaysa cike da mutuntaka, tukun sannan Kawu Amadu ya shiga maganar abunda yasa ya kira Prof Khaleel tun farko. Ya ‘kark’are da,

“Toh yanzu haka maganar nan da muke da kai, Karime na can a yashe, ta kamu da cutar mutuwar jiki duka, da shan inna, kamar harda farfad’iya ma, wallahi yarinyar nan ba dan albarkacin mahaifiyar ta ba, bazan taba temakon taba, to ‘dan abunda yan uwa suka tara duk ya ‘kare akanta, wanda ‘yayanta suka aiko shima babu, shine mahaifiyar ta tace, dan Allah idan da temakon da zaka iya mana, ko da ta ‘bangaren ganin babban likita ne. Wallahi tana cikin wani hali Alhaji, Kayi hak’uri dan Allah..”

Ajiyar zucia Prof Khaleel ya sauke, Wanda kawu Amadu ya jiyo ta, ta cikin sifikar (speaker) wayar. Ya jima kafin yai magana, dakyar yace.

“Ba damuwa kawu, akwai wani neurologist anan asibitin Aminu kano, zan ki rashi, yanzu kuna gidah ko asibiti ne?”

Cikin rawar murya kawu Amadu yace,

“Muna nan asibitin murtala, dakta zai bamu sallama yanzu.”

“Okay toh shikenan, yanzu idan kuka gama sai ku wuce can asibitin Malam bangaren speciality, ni kuma zan kira likitan na sanar masa, Allah ya bata lapia. Ameen”

“Ameen Alhaji, Mungode Allah ya saka da alkhairi.”

“Ba komai kawu, zan turawa likitan komai na jinyarta, Allah ya tashi kafadunta..”

Nan kawu ya shiga yiwa Prof godia, shi dai katse kiran yayi ya cigaba da abunda yake yi.


(Dama hausawa sun ce idan zaka gina ramin mugunta, gina shi gajere, domin baka sani ba wataran ko kai zaka fad’a ciki, ‘Yan uwa kunga yadda ‘k’arshen Karimatu ya kasance, mugun halinta shi ya janyo mata, Sannan ga ‘bangaren Hillaal ma, yayi k’ok’arin ganin ya samu kintsattsiyar mace mai tarbiya, yasan mai ya shuka a baya, sai dai kash Allah baya bacci, domin shid’in mubuwa yi ne, gagara misali, cikin hukuncin sa da sarautar sa yasanya Hilaal girbe mummunan aikin daya shuka, hakama ‘bangaren su da Hidaya, Toh Allah katsare mu, ka nisan ta zuciyar mu daga aikata aikin haram, kayi mana katangar ‘karfe daga sharrin masu sharri, Allah ka kara kare mu daga sharrin shed’an la’ananne. Yan uwa muyi taka tsantsan, domin KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE, ALLAH ZAI BAYYANA MAI GASKIA😊👏🏻)


_*ABUJA_*

Gaba d’aya ranar, Saifullah a wajen ppa baya mai da hankali, closing hour na cika kuwa ya mike yai ficewar sa, gidan su ya koma dake anan ya bar motar sa da safe, Daganan yabi Islam school dinsu, shysa a zuwa da dawowa (to and from) duk a Uber yai yawo. Bai ga motar Islam a parking lot ba, hakan yai masa nuni da bata dawo ba kenan, bakin sa ‘dauke da sallama ya shiga parlorn. Haj Zuwairah ce kawai a zaune a parlorn sai y’ar aikin ta a gefen ta a ‘kasa, suna kallon wani tsohon hausa film. ‘Sangaya’.

Haj Zuwairah ta amsa sallamar aciki ciki, ganin sa yasanya ‘sumayya mai aiki😹’ ta fi ce da sauri tabar wajen, tana susar kanta. Harara Saifullah ya watsa mata, yaki jinin y’ar aikin tasu, kazama ce, yarasa me yasa Mami ke sonta, sai kace ‘yarta, tai ta gatan tata. Shi kuma ‘kazantar yarinyar ne ke bashi haushi, wanka sai an sata dole take yi, idan kuma ba’ a tursasa taba to sai jumu’a-jumu’ah. Durk’usa wa yayi yana cewa,

“First love barka da rana...”

Hajia Zuwairah dake hakimce akan kujera ta dube shi a yatsine, tana ‘kara danna tufar(Apple)hannunta a baka. Sai data had’iye, sannan ta dube shi, yana tsugunne, sanye cikin shadda blue anyi mata dinkin hannu Golden color, ba hula akansa sai pcap golden color da aka rubuta S a jiki, cikin tabe baki tace,

“Barkan mu..”

“First love.. Dan Allah ki dena fushi da ni, wallahi I’m ready to amend my mistakes, please kiyi hak’uri first love.”

Dogon tsaki Mami taja kafin tace,

“In dai abunda ya kawo ka kenan tashi ka fita, tashi ka tafi bana buk’ata.”

Rarrafawa yayi zai rike kafarta ta goce tana dankara masa harara, be hakura ba ya dafa kujerar da take, Sosai Mami ta hango damuwa a idanun sa, ta danne kawai, Don so take ta kankarowa Islam mutuncinta.

“Zaka matsa ko sai na sharara maka mari..?”

“Allah ya baki hak’uri first love”

Ci gaba tayi da kallon ta, hankali kwance, ya ‘kara saisaita murya yana fad’in,

“Toh first love zanci abinci pls”

Sai daya maimaita sau uku kafin Mami ta mike tana barin wajen, sai da tabar tsakiyar parlorn kafin tace,

“Ba agidan su Khaled kake cin abinci ba?! Wane taohon kinibibin ne yasa kazo nan zaka ci?! To babu, abinci, na iya mu na dafa ban had’a da na waje (outside)ba, idan ka fita ka janyomin k’ofar.”

Jiki ba ‘kwari Saifullah ya mike ya fita waje, farfajiyar gidan ya tsaya yana kallon sararin samaniya kawai, duniyar fa tafara yiwa mutumin ku zafi. Gefan famfo ya zauna a wani ‘dan tudu yana wasa da wani tsinke a gefe, azahirin gaskja zancen zuci yakeyi, ‘nan Islam ta danno hancin motar ta, har ta kashe motar bai dena kallon ta ba, ta ‘dora lab-court akan rigar ta, tana tafe tana k’ok’arin cire ta, Saifullah ya sha gabanta, cike da takaici tace,

“Malam matsa zan wuce..”

“Idan naki fa?”

“Karka so ma wannan kuskuren, dan wallahi sai nayi maka ihun gardi.”

“Waye gardin?”

Yafada yana ware idanu, cikin yatsina fuska tace,

“Waye gardi anan bayan Kai, excuse me pls..”

Ta fada tana wuce wa ta gefen sa, Saifullah ya saki baki yana kallon ikon Allah, Duk abun nan Mami na kallon su ta sama, Islam na shiga ciki ya tada mota a zuciye yabar gidan, ya ‘dauki hanyar gidan su Khaled. Sai da Islam tayi wanka taci abinci ne Mami ta sameta da maganar abunda yasa tadawo da ita gidan, ta ‘kar’kare da,

“Kada ki sakar masa fuska ya ‘kara rena ki, nasan halin auta na, Kiyi duk me yiwuwa ya fara binki ya baki hak’uri ba ke ki bishi ba, kingane nufi na?”

Cike da kunya Islam ta d’aga kai alamun eh, a sanyaye kuma ta furta,

“Toh Mami Insha Allah..”

Haj Zuwairah na fita, Islam ta dakko wayarta ta gayawa Lee yadda ake ciki, itama ta ‘kara ‘dorata akan network din da zatai subscription din Saifullah😉. Sun dan taba hira da Lee, kafin ta shiga groups din hausa novels din favorites writers ‘dinta a WhatsApp. Wato (RANO ONLINE NOVELS na Hafsat Rano, da HOME OF NOVELS na miss xoxo &HAJJAH CE NOVEL GRP na Ya Hajja), Sosai take jin dad’in groups din musanman da za’a fara littafan ZAFAFA BIYAR, na DAURIN BOYE na Huguma, BURI DAYA na mamu gee, SAUYIN KADDARA na Hafsat Rano, da WUTSIYAR RAKUMI na tawan billy, sai KAI MIN HALACCI na matar sheikh Aliyu wato miss xoxo 😤, tana gama karanta ‘dan’danon kowanne tayi musu transfer din dari biyar 500, aka sanyata a grp din ZAFAFA BIYAR.. da haka wani daddad’an bacci yai awun gaba da ita, cike da mafarkan yadda za’a sha ruguntsumi a cikin wannan dad’adan littattafai, masu dinbin darussa....



———-
Ina kike AYSHA KANYA? Sak'on ki ya iso gare ni😹, Ina fatan an baki ma'anar suffocating😉na gode da yadda kike bibiyar littafin SAIFUL_ISLAM, tate da 'yan KUNDIN HASKE duka😍🤩

_______________
XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽





_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_*

[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 61-63_*

_GAISUWAR BAN GIRMA GARE KI *YA HAJJA TAH*, LITTAFIN NAN GABA ‘DAYA TUKWICI NE A GARE KU, KE DA TAWAN (BILLYN ABDUL)FATAN ALKHAIRI A GARE KI, OUM IHSAN WA AREEF❤INA MIKI SON ‘KAUNA FISABILILLAHI, ALLAH YA BARKI DA UNCLE ABADAN DA’IMAN🤩💕🤲🏻. WANNAN SHAFIN NA KI NE KE KAD’AI., KI YI YADDA KI KE SO DASHI🚴🏼‍♀_

_nanahafsat.wordpress.com_

Saifullah na barin gidan ya nufi gidan su Khaled kansa tsaye, jijiyoyin kansa duk sun tashi, bugun zuciar sa ya canza, Sosai kansa yake ciwo tamkar zai bar gangar jikin sa. Ko gyara parking dai-dai bai yi ba, yai fitowar sa yana mikawa driver Aunty Lateefa mukullin, da hannu yai masa alama da yai parking dinta, kansa tsaye ya wuce part din Khaled na da, wanka yayi ya ‘daura alwala ya yi sallar nafila, ya jima zaune akan prayer mat yana addua, kafin ya mike jiki sanyaye ya nufi sashen Aunty Lateefa. Samun su yayi a zaune itada Humaira, suna shan fruit salad, zama yayi a kujerar mutum biyu dake kusa da wadda Haj Lateefa take, Humaira ta gaishe shi ya amsa, ta mike ta haura sama abunta, bin bayanta yayi da kallo, sai yanzu ya lura fushi take dashi, sunku yawa yayi yana gayda Haj Lateefa, ta amsa murmushi fad’ad’e a fuskar ta kafin tace,

“A kawo maka abinci auta? Favorite dinka a kai, faten dankali, wannan karan an saka kifi.”

“Okay Aunty, a zubo amma kad’an.”

Mikewa tayi ta shiga kitchen din su dake k’asa, mintina kadan tadawo da food flasks guda biyu, da plate da serving spoon, sai wani jug dake cike da zab’o da yasha kayan had’i aciki anyi decorating dinsa da ice blocks. Zuba masa tayi yace ya isa, ya ‘dan caccakuna ya barshi, tana hankalce dashi, zobon ya sha sosai, ya goge bakin sa da tissue yana hamdala kafin yace,

“Aunty! Wajen ki nazo fa”

“Toh auta, Allah yasa alkhairi ne”

Murmushi yayi, yana shafa ‘keyar sa, kafin yace.

“Aunty..a..Akan maganar Islam ne”

“Islam kuma? What about her?”

“Aunty nasan kin sani, dan Allah temako na zaki yi, ki bawa Mami hak’uri.”

Murmusawa Haj Lateefa tayi kafin tace,

“Auta ka daina zurfin ciki kaji? Damuwa na damun ka, ka samu wani kuyi shawara, sai kaita barin abu a ranka, sai yaci yacinye ka sannan kazo kana magana a ‘kurarren lokaci, in dai akan Islam ne gaskia bani da abun da zan fada maka, Tunda zance ya koma wajen manya.”

“Aunty kiyi hak’uri, ni fushin da Mami take dani yafi damuna akan komai wallahi.”

“Wato auta har yanzu baka fara saka Islam a cikin ranka ba kenan? Kuma fushin da Mamin keyi ai duk akan hakane, ni banida abunda xan iya maka auta, kai zaka dage, fight for ur dear self, kayi lefi admit it, shikenan fa, amma duk wannan ‘kunbiya-‘kunbiyar da kake ba zai maka amfani ba..”

Tana gama fada ta mike ta shiga kitchen, domin halin Saifullah na ‘kona mata rai, gashi ta sanadiyyar ta akai auren, ko kadan ba taso hakan ya kawo ruguntsumi ko rabuwar kawuna. Tana shiga kitchen ya hau sama wajen Humaira, a parlorn sama ya tarar da ita tana danna waya, kallo d’aya tai masa ta mai da kanta kan littafin da take karantawa. Zama yai a kujerar dake kallon tata kafin yace,

“Humaira...”

Ya fada cike da damuwa, ‘daga idanu tai ta dube shi, kafin ta ajiye littafin agefe tace,

“Ya saif..”

“Kin san meyasa nazo wajen ki?”

Girgiza kai tayi alamun a’a, ya jaddada kai shima kafin yace,

“Akan ‘kawar ki ne Islam, deep down na san kina ‘boyemin wani abu, ki fadamin me na yi mata? Ita Islam din.”

“Babu komai Ya Saif.. Allah ni Islam bata fad’amin komai ba”

“Toh waye ya gaya miki? Ki dena nuna bakisan komai ba, kin san halina dai sarai.”

Sanin indai ya canza yanayin sa bazata ji dadi ba, yasanya ta saurin bashi labarin abunda taji game da maganar da Islam suka yi da Lee, ta ‘kark’are da,

“Kuma Ya Saif, wallahi nasan wacece Islam duk zargin ta da kake wallahi ba haka halin ta yake ba, wallahi duk inda kamilar mace ta kai, Allah Islam ta zarce, ba wai dan ‘kawata bace, ko kuwa dan yanzu matar kace, tsakani na da Allah nake gaya maka, idan hankali da nutsuwa ne ma wallahi tafi ni, nasanta tun primary school, childhood friend dina ce, Saboda haka bayan ni da Lee ba wanda yasan halin Islam kamar mu.”

Tana gaya masa halin Islam yana ‘kara ganin ‘kimar Islam din a zuciar sa da gangar jikin sa, Humaira ta tsaya tana kallon sa ganin yana murmushi shi kadai, sai da yai mai isar sa kafin yace,

“Wannan Riri din, wacece ita?”

“Sunan ta Farida, sister din matar Uncle dinsu ce da yake a Lagos, tun tana ‘karama take wajen yayar ta ta, Haj Nabila matar shi Uncle Bala din.”

Kad’a kai yayi alamun gamsuwa kafin yace,

“Ina ganin ta ai a Lagos, Meye alak’ar su da Islam?”

Murmushi Humaira tayi, kafin tace

“Ba komai, sai zumunci kawai, tinda idan da kara kaga ai ta zama y’ar uwar su, tunda tun tana ‘karama take gidan Uncle dinsu.”

“Yadda na lura kaman ‘kawar ta ce sosai..”

“Kawai zumunci ne Yaya, nothing beside that, ‘kawayen Islam daga Lee sai ni, sai su Hafsat da Fatima, suma kuma duk sunyi aure, acikin su ma ni kadai ce banyi ba.”

“Allah zai kawo nagari sis.”

Cije ieb’e yad’an yi kafin ya sake cewa,

“I heard ita da Khaled sunyi soyayya ko?”

Ya canza maganar, ware idanuwa Humaira tayi kafin tace,

“Soyayya da yayan? Anya? kai a’a gaskia, na san dai itada yaya suna mutunci sosai, So ni I thought son ta yakeyi, Saboda duk cikin friends dina ba wanda Yaya yake mutunci da ita kamar Islam, so sai nagaya wa Umma, nace soyayya suke yi, na kuma dinga pressuring Islam kan Yaya na sonta, ya kasa fad’a mata ne, Saboda a lokacin anyi auren step sister’s dinta ba dad’ewa, saura ita kadai kawai, So shine ta gaya mishi fa, kuma Islam nada masu son ta da yawa, tanada farin jini, ko a school baka ga yadda classmates dinsu suke cewa suna sonta ba, Saboda ni ina art class amma mazan ajin mu ma suna sa muna kancewar su dai suna son Islam.”

Ta ‘kara da ‘y’ar ‘karyar ta, Don bataso Saifullah ya rena ajin Islam din, jin ta gama yasa shi jaddada kai, alamun gamsuwa da zancen ta, kafin yace,

“Oh okay.. Thank you sissy!”

Mikewa yai zai fita, har ya kai ‘kofa Humaira tace,

“Ya Saif, Ka dena zargin Islam da aikata wani abu, wallahi nasan wacece Islam, duk inda descent mace takai, Islam ta kai, ta zarce ma.”

Kad’a kai yayi kawai, yafi ce batare da ya tanka taba.

On a cold Thursday evening, Haj Lateefa taje gidan Haj Zuwairah, suka tattauna akan maganar Saifullah da Islam, domin Saifullah ya takura mata da zancen, ta fadawa Haj Zuwairah komai akan maganar da sukai da Saifullah, ciki harda zancen Riri daya gansu da Islam a joint. Lokacin Fatima tazo ganin gidah, a parlorn gidan aka shiga maida maganar kowa yana tofa albarkacin bakin sa, Fatma ta shiga ‘dakin da Islam take ta hilato ta suka fito parlorn, a lokacin Saifullah yazo shima, Don Fatima ta kira shi tana san ganin sa, duk suka hallara a parlorn, Fatma ta shiga jan hira da Islam, domin ta naso ko yaya su samu evidence, wanda zai kau da zargin da Saifullah ya kewa Islam.

Sosai ta shiga bugun cikin Islam, Islam ta fada mata komai dangane da zaman su da Saifullah, nan dai Fatima ta shigar da zancen joint na lagos da sanda 4gig ke yafa mata mayafin. Don Saifullah ya bata labarin komai, A wayonce take tambayar ta wanene shi meye alaqar su?, dan saurayin ‘kawartane a Lagos. Kuma ita tagan su, and kawar is feeling uneasy. Fatma ta ‘kark’are da,

“yanzu ya za’ai mu samu information dinsa, tunda kince ko sunan sa baki sani ba.”

Islam ta ‘dakko wayarta tayi dialing number Riri, bugu biyu ta ‘dauka, a speaker Islam ta saka Riri, sai da suka gaysa kafin tace,

“Riri ni kuwa time din da motan mu ya lalace, a bayan plaza dinnan na idiroko ya sunan wajen please?”

“Oh time din da mota ba ruwa dinnan, ba canai ki shiga ba kika ki? Mena tambaya na ynxu?”

Islam tayi murmushi tace,

“Dallah wannan wanda yake tsokana na dinnan ne naga wani kamar shi a live show yanzu”

“Oh wai 4gig daya kwace miki mayafi ya ‘dauka ke ki ‘y’ar hannu ce? Sunan sa Basher, wallahi rannan kuwa yake cewa wai na ‘kara baki hak’uri daya ja mayafin ki.. Ni kwa nace masa ai kai ka fiya renin hankali, tunda ba gani kai ta shigo ciki ba, a waje ka ganta dan ma motor dinsu ya lalace ne, nace masa ke y’ar Abuja

Please Login or Register in order to submit comment