Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xaisa a miko masa su, yanzu ma Haj batul matar kawu Ndume kawun Haj Aysaa ce ta karbi Abubkhar tana gyara masa diaper, dr Khaleel yace Falmata ta karboshi babu ko kunya bare kawaicin sirikace fa inda kara,

Ai kuwa ta hana da ike itama y’ar neman rigima ce,

“Ni fa nayi sabon ango dakta, daga yau har mu bar asibitin nan”

Daria yayi yana shafa k’eya ganin ta gano shi, dakyar dai da kuma yadda aka yanyame dakin yasashi ficewa bayan ya jaddadawa Falmata kan lallai,
‘Ta goya d’aya ta bawa iya Amuna (dayar mai aikin su) dayan su goya su.

Ita dai Haj Aysa murmushi kawai take, Ashe abunda Allah zai azurtata dasu Kenan?Lallai da tayi babban kuskuren lokacin datai wautar zubar da cikin. Mama tabasu suka sha suka koshi bayan sunyi video call dasu safa, likita ya kara mata allura kafin zuwa washe gari su tattara su tafi, don sosai likitan karakainan surutun masu zuwa barka sun isheshi, shiyasa ya rubuta musu discharge leave kan da safe su ware gidah kawai ta karasa bedrest din acan.

Zagaye parlorn tashiga yi, zaninta a dage, gashinta duk awaje se surutai take kamar sabuwar tabi,

“Ina..Baxai yiwuba walahi, makirci ne walahi..”

Yafendo ce takaraso parlorn Karimatun tana sallallami kafin tasamu waje ta zauna ta zabga uban tagumi,

“Malam na dotsa ya tabbatar mun da taurarin jarirai biyu yagani mata, anya ba musanye tsinanniyar nan tayi ba” cewar Karimatu cikin kidemewa

“Hmm yaya walahi nima sakawa nake Ina warewa, domin ni kaina falalu na kan tudu haka ya buga kasa ya fadamin, ai Kadan daga makircin su nifa yaya gani nake yi xuwa tai a ka cire wa’incan aka saka mata maza biyu”

“Allah ko?!” Cewar Karimatu cikeda gasgata abunda Yafendon tafada,

“Yo abune da yaxama ruwan dare, zuwa kake a sa maka yaya, ke kinji muryar Alhaji kuwa daya kirani yana sanarmin ta waya walahi yadda kikasan ansashi cikin aljanna”

“Bar can d’aya gaula sallamamme, yanacan yana rawar duwawu uwargidah ta sauke masa abunda yake muradi..” Karimatu takarasa tana Jan tsaki a karo na ba’adadi

“Hmm walahi kam, ana haihuwar dan yan mintuna shegiyar can (Helwa amaryar) tafice zuwa asibitin waya sanima ko bakin su d’aya”

Ashar Karimatu ta lailayo ta dura shi tareda sauke kwandon tsinentaka akan sunan Haj Aysa da Helwa,cikeda huci take cewa,

“Bar dangin asiri ai tsatson su d’aya Allah wani lokacin ma ni gani nake da saninta Alhaji ya auro ta, gaba d’aya saikace itace ta haifeta sai wani binta take tana mata biyayya”

“Ni bama wannan ba, yanzu yaya Meye abun yi?!”

“Rabasu da iska shine babban buri na Yafendo” Karimatu ta karasa ko gezau babu a furucin ta,

Gwalalo idanuwa Yafendo tayi cikin kidimewa take,

“Yaya kisa, kisa fa kikace?! Tukunna ma wa kikeson kashewa Aysan ko helwan”

“Ana maganar serious kina sako wasa da kashe su Xanyi tuni Van aiwatar da kudurina ba.Da yan biyun da aka haifa nake, natsanesu walahi,Baxan iya hakura Ina numfashi a gidan nan da gilmawar yaran nan ba”

“Tab yaya kenan, Ai kwa wannan abune da baxai taba yiwuwa ba Kema I san yanzu yaran nan ko quda Alhaji ba zai so yataba su ba”

“Yafendo kenan. Wani lokacin kikan manta da irin hatsabibab cina,to kizuba ido ki kallo”

“Toh yaya Allah ya baki iko” Yafendo ta karasa murya a raunane,

Tafada duniyar tunanin har ga Allah batasan abunda Karimatu xatai silar barinta daga gidan nan domin igiyar auren ta saura biyu karimatun kuma saura d’aya, kuma Karimatun ce tajanyo abunda aka sausu.. Fisabilillahi tasaba da jar miya anan ina xata iya rayuwar rugar su, baxata mantaba lokacin da aurenta ya mutu na saki d’ayan da girman ta baffah Ardo xaisa ta tatso nonon shanu,kuma kullum abincin su furace sai dan abunda ba rasaba na fulanin jaubawa, gaskia baxata sabuba, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace,

“Yaya ki sake shawara gaskia..”


******

*B* *N* *A*

Islam ta wanke undies dinta tana shanyawa, Hidaya dake ta saman hostel dinsu ta hangota bata bata lokaci ba ta zunguri bucket dinta dake cikeda underwear’s ta sauke kasa wajen famfo, don ana musu wanki kayan ciki (underwear’s) kawai suke wankewa,

Saida gaban Islam ya fadi ganin Hidaya , mugun murmushi Hidaya tayi kafin ta muka mata bucket din hannun ta, hannu Islam din tasa ta karba, cikeda nuna isa Hidaya ke cewa,

“Ki wanke su ki goge mun kayana kafin karfe 9 saboda xanyi bacc...”

Bata karasa ba Hafsat Rano kawar Islam ta karaso da gudu tana haki,

“Lam Lam guess what?”

“HR! Munci biology test duka?”

“Wrong ..yanzu Mrs Daniel tace agaya miki maman ku ta haihu yan maxa”

Ai Islam bata karasa jin HR ba tabar wajen da gudu HR na biye da ita, ai Hidaya ma bata tsaya ba ta wuce wajen Hafsat dake zaune itada Hilaal (yaran da ake yayi a sch din)suna hira hannunsu sarqe dana juna,

Bata rai Hidaya tayi don itama fa tana son Hilal dinnan gashi dan ajin su nema amma saboda tsabar yadda take shakkaar Hafsat ko kadan bata nunawa sai dai Idan Hafsat din bata wajen, shi kuma yafison Hafsat saboda takoya masa taba jikin ta.

Murya cikeda haushin ganin su tare tace,

“Maman Islam ta haihu yau, maza”

“Kutmar ubancan, Karya kikeyi” cewar Hafsat da lokaci d’aya ta burkice idanunta sun rufe sak dai irin halayyar Haj Karimatu..





*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼*
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SHAFI NA UKU (3)*


*B N A*..


Elizabeth Arden’s hostel...

*Z*aune Islam ta ke, hannun ta rik’e da littafin chimamanda mai suna ‘purple hibiscus’, kasancewar dare ne tuni yawan cin ‘yan dakin sunyi bacci, da yake kowan ne d'aki mutum shida ne ciki. Da Ita kanta a cikin d'akin sai Lee da Hafsat da suke uba d’aya, sai Hafsat Rano da suke kira da HR, sai kuma Fatma bichi da suke kiranta Zarah, sai Iffy kawar Hafsat kanwar Islam sune a d’akin su 6, gabas da yamma kudu da arewa na dakin ko Ina gado biyu ne inda yayi making 6 bed kenan.

Had'add'an d'aki ne kai kace gida ne idan ka shiga, harda d'an parlorn su da tv a ciki, can gefe kuma study ne da bookshelves ajiki, kowa gadon sa da kalar sa, da mini cooler fridge kowan ne da nasa, ga kuma yalwataccen band'aki wanda yaji komai abun dai sai sam barka kawai, Domin makaranta ce mai karshen kyau, kuma ta amsa sunan ta don kwarai matuka suna samun karatu, kama daga na boko zuwa arabi ciki harda k’arin karantar harshen faransan ci (French).

Kasancewar shi harshe na biyu da ake ji dashi a duniya bayan English saboda mahimman cin sa a duniya ko a international court of crimes na duniya daga French sai English kawai ake yi. Wannan kenan.

Haleema Sameer Ameer ‘kawar Islam itace ta fito daga band'aki, da alama wanka tayi dan gashi nan tana tsane kanta da karamin towel kafin ta d'akko dryer tana drying gashin kanta, duban Islam take da gaba d’aya hankalin ta na kan littafin da take karantawa, da alama ma ba ta san Haleeman ta shiga band'aki ba balle kuma fitowar ta.

“Aikin dai kenan” cewar Haleema ta ajiye dryer tana k’ok’arin daure gashin ta da ribbon..

“bae boo”cewar Islam tana k’ok’arin cigaba da karasa karatun ta,

“Wallahi baki isa ba”Lee ta fad'a tana wafce littafin daga hannun Islam,

“Ki dinga hutawa dan Allah, Shi kenan ke bakida aiki sai karatu ne?ko gajia bakya yi, beside ke fa ba Art student bace for heaven sake..”

“And so, reading is one of my fave hobby yarinya” Cewar Islam had'e da rolling idanuwanta cike da tsoka na,ta mika hannunta ta kwace littafin ta, hade da saurin mikewa tabar wajen Lee.

“Zaki dena ne..Ni bama wannan ba bari na dakko physics ki kara sa coaching dina”

Kad’a kai Islam tayi, ita kuma Lee ta tashi ta shiga study wajen karatun su inda books d'insu yake..

Tashin ta keda wuya Hafsat ta shigo d'akin tana wake-waken ta, sosai gaban Islam ya shiga fad'uwa don batasan yau kuma da wanne kalar rashin mutunci Hafsat din zatai mata ba.

Bata karasa tunanin da take ba, Hafsa ta dire mata plate akan littafin ta, har cheese na fallatsuwa a idanun Islam, da sauri Islam tasa bayan hannunta tana goge idanun ta, gashi tana da ciwon idanu lokaci d’aya ya karade ya zama ja..

Kwan chewing gum Hafsat ta saki guda uku lokaci d’aya ji kake k’as-k’as-k’as kamar tsohuwar karuwa. Hannu d’aya kuma tana danna waya, gashi an hana amfani da waya a sch din. Idan aka gani ma seizing ake yi, amma Hafsat da Hidaya asace suka zo da tasu, bayan ko agidah ma Dr khaleel bai basu daman rike wayar ba. yace kowannen su sai ya gama secondary school zai rike waya,

“Reheat that for me..”cewar Hafsat ga kuma harara tana makawa Islam din,

Islam bata ce komai ba ta ajiye littafin ta a gefe, ta mike da plate d'in a hannunta cheese burger ce akai, tafiyar daba tayi taku goma ba ta isa ga microwave d'in su dake gefen tv stand, tana k’ok’arin saka plate d'in aciki Lee ta fito daga study room.

Tsayawa tayi tana duban Hafsat, kafin ta maida kanta ga Islam dake danna minutes ajikin microwave, ganin idanunta sunyi ja ya sanya Lee tsarguwar ko dukan ta Hafsat tayi? Domin hakan tasha faruwa in bata wajen sai tana nan nema Hafsat din ke sarara mata, Da sauri ta karasa wajen Islam tana tambayar ta.

“Dukan ki tayi ne?!”

Girgiza kai Islam tayi alamun a’a, tana murmushin karfin hali, Zafi burger din yayi Islam taciro tana mikawa Hafsat.

“Water..”cewar Hafsat dake sake gyara xaman ta akan gadon Islam din tayi male-male akai,

“What the fuck..Mehn cut this shit up, dan tsabar rainin hankali itace xata miko miki ruwan bayan ga ki ga mini cooler din a kusa dake?”

“Don’t let me repeat my self..”cewar Hafsat tana wa Islam kallon tara saura kwata, kallo d’aya xakai wa Islam kasan tana cikin tashin hankali.

“Ba xata dakko ba”Lee tabata amsa tana k’ok’arin dakatar da Islam daga d'akko ruwan,

“Bari Lee, Kiyi hak’uri ki bari na d’akko mata.” Da sauri ta karasa ta dakko ruwan tana mikawa Hafsat.

‘'Bud’e shi..” Hafsat ta sake bata order. Karba Islam tayi ta bud'e ta mik’a mata,

“Banza loser, bumbling idiot kawai, tana kanwar ki tana baki order.”

Lee nagama fad'a ta koma study room cike da haushin Islam. Sum-sum Islam ta fice parlor bayan ta dau littafin ta,

Dariar mugunta Hafsat ta shiga yi sai da tayi mai isarta sannan ta mike ta shiga bathroom, wanka tayi tasa pajamas dinta ta kwanta akan gadon ta,

Ko takan plate d'in dataci burger din batai ba gashi kaca-kaca tayi da sashen Islam din, ta zubar da burger da gani da gangan tayi, kafa d’aya Kan d’aya take chatting da wayar ta hankalinta kwance, guntun message ta turawa Hidaya(wadda suke uba d’aya),

“Just made the loser shed tears again, turn dnki ne yanxu sissy..”

Bata wani jima ba bacci ya dauke ta bayan ta boye wayarta a maboya. Sai past 12 Lee tafito daga study tana hamma sosai bacci take ji, batabi takan Islam ba dan har yanzu haushin ta takeji ta karkad'e kan gadonta ta kwanta bayan tayi addu'a.

Sai alokacin Islam ta dawo dakin ta ajiye littafin a bookshelves ta shiga band'aki tayo alwala, sai da tayi sallar nafila, sannan ta koma ta gyara kan gadonta, ta kunna turaren wuta a burner, komai ya kintsu sannan ta koma kusada Lee tana dan bubbuga bayanta a hankali cikin sautin rarrashi tafara mata magana ,

“I’m so so so sorry best fren”

Buge hannun Islam Lee tayi tana Kara matsawa can gefe,

“Leave me alone, yeye fowl”

“Habba mana dan Allah..The one who forgives owns the biggest heart. kiyi hak’uri pls”

Shiru Lee tayi tana kumburo baki ita adole tayi fushi da yawa,

“Oh plss babes..”

“Fine joor,na hakura”

“Yay that’s my better half” Ta fad'a had'e da hugging Lee.

Milkshake Islam ta hada musu suna sha suna suna ci da cookies, tuni baccin yai kaura daga idanuwan su, basu kwanta ba saida suka yi tutorials na physics da xasuyi da safe sannan suka kwanta bacci.

Banda Islam wanda ta fada kogin tunanin yadda su Hafsat suke nuna mata zallar k’iyayya sai kace ba jinin su ba, kullum sai anji kansu sai bare sun raba su..Haka ta taso taga iyayensu ma suna yiwa Ammin ta(Hajia Aysa) dan ma amaryar da mahaifinsu yayi wadda bata wani jima ba (Helwa nawarma) itace kawai ke ganin girman Ammin nasu ta ke kuma kara darajata musanman da suke kaman sun fito tsatso d’aya ita Ammi bornu ita kuma amaryar 'yar Tchad.

WUSE 2 Ademola Adetokunbo; GIDAN DR KHALEEL...

Gida ne da zamu kira shi da mansion yes mansion xance saboda tafkeke ne, dauke yake da duplex apartments (gidan bene)guda 7, gefe d’aya kuma islamia ce da computer room ga swimming pool da gymnasium area, Kai kada na cika ku da surutu komai dai yaji sai dai muce yadda gidan yake haka ko akwai kwanciyar hankali cikin sa kuwa? To oho dai sai mun shiga daga ciki.

Securities ne fal a k'ofar gidan wanda xamu iya kiran su da mopols, layin gidan ma sunan dr khaleel ne ajiki ‘Dr khaleel MM link’ shine sunan dake rubuce wanda idan mukai naxari MM din na nufin ‘Mai Mota’ sunan sa dai tun na ‘kauye da aka sanya mishi shine ya bishi har yaxaga duniya domin ko scholarly definitions na articles d’insa according to dr khaleel MM ne ajiki.

Zaune Haj Aysaa take a parlorn cikin nan nata ya kara kasa alamun haihuwa tazo kenan, lokaci xuwa lokaci takan furta.....







_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*



*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SHAFI NA BIYAR (5)*


Mrs Daniel ce ta kira wayar Haj Aysaa wadda alokacin tafito daga bandaki kenan, saurin dagawa tayi tana tana murmushi,

“Ammi”Islam tafada cikin zakuwa

“Na’am Islam, ya school?”

Daria Islam tayi, cikeda murna take wa Ammin magana,

“Ammi Nda dubdo,”

“Dubdo silewa,àskəŕ à Álàyè ya studies?” (Lapia qalau Mungode Allah)

“Ammi duk lapia, Ammi wai wai kin..”

“Na haihu Islam, kinyi kanne gasu nan yan maza su biyu, daddyn ku yasa musu sunan kakannin ku..”

Hamdala Islam ke tayi tana murna cikeda farin ciki tace,

“Toh Ammi ansaka musu nick name ne?”

“A’a mai kikeso a dinga ce musu”

“Areef da Abeed”

“Insha Allahu haka xa’a dinga kiran su.”

“Toh Ammi,Nagode”

“Ba dai wata matsala ko?”

Kamar tace akwai sai kuma tai saurin kada kai, don tasan mahaifiyar tata ma hak’uri take da babannin su Hafsat din bata so takara mata wata damuwar akan wadda take da ita araunane ta furta,

“Babu Ammi..”

“Toh shikenan, zan aiko da hotan su sai Mrs Daniel ta nuna miki”

“Toh shikenan Ammi nagode, sai anjima”

Ta katse kiran cikeda jin dadin adduar da Ammin tai mata ta kuma kara ja mata kunne kan taja mutuncin ta kada ta dinga bari tai gogayya da maza domin Idan ta kuskura tabari namiji ya na tabata ko hannunta ya taba to fa sai ciki da haihuwa.

Cikeda jin dadin yan kannen datai ta karasa inda tabar kayan wankin ta karasa wanka inner wears dinta takuma wanke na Hidaya,

Bata bar wajen ba saida suka bushe ruwan jiki kadanne sannan takoma daki tai ironing dinsu ta kaiwa Hidaya, Sam hidaya bata mata rashin mutunci ba saboda gaba d’aya hankalinta ya lula kan Hafsat da Hilal yadda tagansu kwarai matuka ya tada mata da hankali, ta jima tana son Hilaal amma shi gaba d’aya Hafsat ce agaban sa, muryar Islam ce tadawo da ita daga tunanin da take,

“Gashi..”

Juyawa tayi ta dube su tsaf braziers dinnan sun wanku da underwear’s ciki harda tarin pants, ya mutsa fuska tayi,

“Ajiye ki tafi”

Sum sum Islam tafice abunta, komawa tayi daki inda ta tarar Lee tadawo daga library tana baje akan gado gajiya ce sosai ajikin ta,

“Lee”

Babes, Nagaji” taja numfashin gajia

“Sannu., yaya kinyi solving equations din kuwa?”

“Bari kawai Lam lam nayi, gashi na tarawa kaina gajia”

“Sannu, me zaki ci?Zaki sha coco pops?”

“Yes pls..Thank you love”

“Guess what?!” Cewar Islam bayan ta mike tsaya tana zuba madarar ruwa acikin bowl.

“Meya faru” Lee tace fuskarta cikeda fatan Allah yasa alkhairi ne

“Ammi ta haihu fa”

“Dagaske dan Allah dagske?” Lee tabata amsa cikeda farin ciki

“Wallahi dagaske yan biyu maza”

“Kai Masha Allahu.. Alhamdulillah! Kin zama mai kanne kenan you are no ...”

“Nasani Last born”cewar Islam ta katse Lee tana daria,

Hirar su suka cigaba da yi cikeda farin ciki nan hirar yan maxan aji ta tashi,

“Ni fa Bassam ya ishe ni Lam lam, Nace masa ya dena takuramin shin wai ana so dole ne?”

Murmushi kawai Islam tayi tana kara kora sanyayyan yoghurt din dake hannun ta, zungurin ta Lee tayi tana hararar ta,

“ ke sai mutum yai ta miki magana kina wani basarwa bansan haka walahi”

“To ni meye nawa aciki?! Me zan miki ni ba Love expert ba.”

Tsaki Lee taja,

“Ke walahi kinada rainin hankali wani lokacin duk sanda xa’ai maganan maza kindin ga janye jikin ki kenan Kina ke bakisan komai ba, duk ina karatun novel’s dnki yatafi da bakisan komai akai ba”

Murmushin dayafi kuka ciwo Islam tayi,

“Bakin jini ne da ni Lee, dagaske maganar dasu Hafsat ke fada gaskia ne, tunda kike dani kintaba ganin wani yace yana sona?! Tun kindergarten muke tare dake gashi har munxo ss1 sanin kanki ne ba wanda yataba cewa wa yana so na ko nayi Karya uhm?”

Sanin dagaske hakanne yasanya Lee yin shiru cikin kawar da maganar tai saurin cewa,

“Toh sai me?duka duka a ss1 muke fa going to 2 ga ss3 kuma sannan ga university Ai da sauran lokaci, irin ku ne time daya miji yake zuwa ayi aure ba sai kunyi xance ba, ni dama ni ce walahi ace inada sharp brain irin naki sannan kuma samari basa kulani sai na gama university kawai miji yazo ya aure ni..”

“Hmm! Karki wa kanki fatan haka Lee, dan kuwa depression (damuwa) ne xai maki yawa, Allah at our age yaya safa da yaya marwa samarin su basa kirguwa, danma saida yaya safa tafara houseman-ship dinta daddy ya aurar dasu lokacin kuma yaya marwa tama xama lawyer, Allah ni kadai ce mai bakin jini a gidan mu”

“Ke dalla kema samarin xasu zo, duka duka shekara 15 muke fa, kuma nagaya maki Zaid yana nuna alamun yana sonki kawai dai kunya yake bai gaya miki ba”

Tsaki Islam taja,

“Kede karyar ki bata sallah walahi Lee” ta karasa fada tana mikewa, da sauri ta shiga bandaki ta rufo don batason ta cigaba da sauran karyar da Lee take shirgawa, wai Zaid yana sonta wannan yaran da ko magana bata taba hadasu ba.

Itama Lee mikewa tayi tashiga study dinsu nan ta tarar da sauran yan dakin suna karatu da yake sun fara midterm tests.

“Ka bari mana haka da zafi walahi..”

cewar Hafsat wadda Hilaal ya matse ta a dede kofar corridor din hostel dinsu, ya zura hannun shi cikin skirt dinta, cikeda jin dadin abunda yake yace mata,

“Zai dena xafi Idan kika dena motsa jikin ki”

Sosai takejin xafin yadda yake kwakula hannunsa cikin kasanta, gashi ya matse ta a bango,

“Allah yanzu xakaga Miss Nathaniel(mai kula da hostel din nasu) kuma kaga ta hana ku shigowa hostel din mata”

Kada kai yayi domin sosai yake jin dadin abubuwan da yake mata wanda gaba d’aya ita takoya masa,Duk yadda xai mata komai har ya kware kuma kullum suna cikin yin hakan safe,rana, dare.

Hannuwan sa cikin rigarta bayan yagama yamutsata ya gyara mata ma ballan rigar yana wani kallonta ta kasan ido,

“Zan tafi..” abunda yace kenan don bai so xai kyaleta haka ba.

Gyara jikin ta tayi, tabashi peck a gefen kumatun sa,

“Shikenan Love sai da safe..”

Kada kai kawai yayi ya wuce nasu hostel din cikeda jin dadin yadda zamantakewar su shida Hafsat din take, don bayan haka harta waya suke kallon tsiraicin su kullum ta chatting, Sosai yake kuma jin dadin hakan, shiyasa baya kula kowacce mace ta makarantar fyace ‘Hafsat Khaleel Mai Mota’

Cikin Hostel Hafsat tashiga tana wake-wakenta wadda suka xamar mata tamkar itace shedar sallamar ta, babu kowa a parlor jin duriyar surutun yan dakin ya tabbatar mata da suna cikin library,

Bandaki tashiga tafara wanka, tanayi tana kallon kirjin ta, sosai take jin dadin yadda suke kara girma, Shiysa takeson Hilal yadinga taba mata su ,saboda tayi googling taga amfanin hakan, don so takeyi itama nata su xama tamkar na Islam sumafi na Islam din ,

Don Islam din sosai kirar jikin ta abar kallo ce tamkar ba y’ar shekaru goma sha biyar ba, ‘baka ce bata cika baki wuluk ba, tanada tsayi dede shekarun ta, lips dinta baki ne wanda suke daukar kowanne kalar jambaki, tanada dogon hanci TubarkAllah kamar ita taxana abunta, tanada bular hanci irin na Ammin su don su safa ma duk suna dashi a gefen daman hancin su tunda al’adar suce,

Tanada yalwataccen gashin kai dana gira daidai misali, dirarriya ce gaskia domin Idan ka kalleta baxaka taba kawo tanada kankancin shekaru haka ba ,domin ko’ina na jikinta ya cika sosai, shiyasa Ammi tace Islam din tadinga saka uniforn extra large kuma ko kayan gidah duk babbar number ake dinka mata,

Toh abin dai sai dai muce TubarkAllah kawai, domin Islam tana sahun mata wanda akewa laqabi da ‘coca-cola shape’..

Asubah tagari ‘ISLAM KHALEEL MAI MOTA’.




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO🧕🏼_

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
*ASY KHALEEL💕*


*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*😻
*BILLYN ABDUL*🌹


*SHAFI NA SHIDA (6)*


*WASHE GARI*

*D*a wuri aka sallamo Haj Aysa suka rankayo dukkan su suka koma gida, kafin nan babu yadda dr Khaleel bai yi ba da Haj Karimatu taje asibitin taga yaran tare da duba Haj Aysan amma kememe taki, ta kafe akan batada lapia ba zata iya fita ba, to hakama Yafendo itama bataje ba, nata uzurin ta bayar, a dole dr Khaleel ya kyalesu domin shi mutum ne da bayason rigima, ba kuma yasan hayaniya kwata-kwata,

Shi yasa kawai ya kyale su, saboda idan ya matsa suje, ba suje d'in ba to rayukan mutane da yawa ne xasu b'aci, saboda babban mataki yake yankewa idan ransa ya kai ‘kololuwar b'aci,

Shi yasa farkon rigimar da Karimatu da Yafendo sukai masa, makota ne suka raba su, yana xuwa da labarin yazo kunnen sa, ya dankarawa kowaccen su saki d’aya, dama ita Karimatu ya taba yi mata d’aya lokacin da taiwa Safa 'yar Hajia Aysa sharri.

Gayawa mai karatu yadda aka sake gyara b'angaren Haj Aysa bata lokaci ne, domin kunsan dai yadda gidan yake, kuma kunsan yadda Dr Khaleel yake burin samun d'a namiji, Toh Allah ya cika masa burin sa, d'aki d’aya a ‘kasan ta aka gyara shi da gadajen babies maza komai blue, abun dai sai wanda yagani kawai.

Cima kala-kala Dr Khaleel yasa ake jibgewa a gidan, ga abokanan sa da matan su sai kara-kaina suke agidan, sosai Haj Aysa ke samun kayan barka, tun abun nabata mamaki harta dena,

A kuma ranar ne Dr Khaleel ya tura zungureriyar mota taje Gazarganu Road Area: Bulabulin, Maiduguri, Borno State,Nigeria. Asubar fari tayo lodin yan uwan Haj Aysa, domin suma sunce baxa’a barsu a baya ba,

Tuni parlor ya kacame da 'yan uwa sai yarawa suke yi ana cin cima kala-kala, jarirai kuwa sai nan nan ake dasu, a yinin ranar dr Khaleel yayi zarya agidan nan yafi a ‘kirga,

Kuma duk dan dai ya sake ganin yara sa ne, duk universities dayake lecturing ya bawa students kowa kyautar maki biyar, yayi sadaqa kala-kala a masallatai,

Yaya Bala ma yazo da matan sa duka su ukun, Haj Halima da Haj Nafeesa, da Haj Nabeelah. Haj Halima nada ‘ya’ya biyar maza uku mata biyu, da Mubassher da Mudasser da Mu’utaseer sai matan da Aneesa da Meena sai ‘ya’yan Haj Nafeesan su hudu ne kuma duk maza ne Kamaludden, shamsudden, Nuraddeen da Najibulla sai Haj Nabeelah ita matan ta biyu namiji d’aya. Saifullahi, Amina sai auta Nadia.

Ba laifi gidan Yaya Bala yafi d'an zaman Lapia amma suna d'an tab’a nasu ruguntsumin, saboda duka

Please Login or Register in order to submit comment