Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi, baya da wani rabo lahira. Kuma tir da abinda Suka sauar da raukansu da shi, da sun kasance suna sani)). Suratul Bakara, aya ta: 102,

“Sai kuma waccan ayar maigirma da ta yi nuni akan cewa lallai masu sihiri suna raba tsakanin mutum da matarsa. Kamar yadda ta yi nuni kuma cewa lallai sihiri baya tasiri don karan kansa ta fuskar amfanarwa ko cutaruwa, sai dai yana tasiri ne da iznin Allah wan ya riga ya kaddara kuma ya kasantar, domin lallai Allah tsarkakke madaukaki shi ne ya halcci alkhairi da sharri, hakika cutar ta yi girma kuma zaluncin ya yi tsanani ga wadannan masu kirkirar, wadanda su ka gaji wadan nan ilimomi daga mushrikai su ka zo suka rikita masu raunin kwakwale da su, lallai mu daga Allah mu ke kuma lalle mu gare shi zamu koma, Allah ya isar mana kuma madalla da wakili wanda yake shi ne Allah.,

“Ma’aikin Allah ﷺ‬ Ya sake cewa kuma

((من أتى عرافا أو كاهنا فصدقه بما يقول فقد كفر بما أنزل على محمد صلى الله عليه وسلم)).

“Ma’ana: “Duk wanda ya je wajan danduba ko boka sai ya gaskanta shi da abinda ya ke cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukar wa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi”.

“Anan zan dakata, ku sani duk wannan ayoyi da hadisai na kawo su ne domin ku, saboda ku tabbatar abunda kukeyi ba mai kyau bane, babban shirka ne, ko da nan gaba hakan zai zamto silar shiryuwar ku, Ta haka har Allah yasa ku janyo ra’ayin masu hali irin naku, zuwa turbar gaskia. Abunda na fada dai-dai Allah yabamu ladan, kura-kuren dake ciki rabbi yayafe min.”

“Ameen...” suka had’a baki d’aya wajen cewar hakan.

Ya Bala da Dr Khaleel ne suka ce da Inna Bilkisu,

“Toh! Inna Allah ya saka da alkhairi, mun ‘karu muma gaskia..”

Sannan Ya Bala ya ‘kark’are da,

“Toh Karimatu da Aminatu yanzu zamu ji daga bakin shi mai gidan naku kan wane hukunci ya yanke abisa hakan. Domin a zahirin gaskia ni na cire hannuna a harkar ku, babu ruwana, baxan dinga tilastashi ya hakura ba, akan yadda kuke cutar dashi. Saboda haka Khaleel ka yanke hukuncin ka kawai, bansan Inna ba dai, amma ni duk hukuncin da ka yanke, Ina bayan ka, domin sun cancanci kome kayi musu wallahi.”

Dr Khaleel ya ‘daga kai yana kallon su, Dan murmushin takaici yayi, kafin yace,

“Toh inna ni da na yanke hukuncin sallarmar su kawai, domin baxan iya xama suna cutar da ni da ahali na ba, nan gaba bamusan mai zasu aikata ba.”

Wata gigicacciyar ‘kara suka saki, cikin zabura Karimatu ta fara sumbatu, Yafendo kuwa rarrafawa tayi ta ‘riko ‘kafar Inna Bilkisu,

“Inna kiyi hak’uri, mun tuba, ba zamu sake ba wallahi, ni de.. Ni.. dai dama Yaya ce ke sa ni aikata duk wani mummunan aiki, tace idan ba haka ba zata fiddani daga gidan..”

ashar Karimatu ta lailayo ta ‘dura mata, kafin kace me? Tuni duk sun to nawa kansu asiri, baram-baram sukai da junan su, kowanne yana kwashe wa ‘dan uwan sa albarka. To dama ance komai nisan dare gari zai waye, Allah zai bayyana mai gaskia, a ranar dai gaba d’aya duk wani b’oyayyen al’amari sai da suka bayyana shi, har da yanda aka qullawa Safa makirci. Duk kansu sai suka koma suna hararar junan. Dama haka ne rana dubu ta ‘barawo ce, d’aya kuma dal ta mai kaya.

Inna Bilkisu tai hanzarin girgiza kai, kafin cikin dattako tace,

“Kar kai haka Khaleel, nasan kayi hak’uri, kana kanyi ma, karka zamto sauran maza masu saurin yanke hukunci Khaleel, kayi hak’uri ka dubi girman Allah, ka sauqaqa hukuncin da za kai musu, su ci darajar ‘ya’yan dake tsakanin ka dasu. Kayi hak’uri Khaleel, mata sunyi yawa yawa agari, yan mata da zawarawa, hakika duk sanda akai saki, al’arshin ubangiji girgiza take, kaga kuwa ba ‘karamin abu bane. Kayi hak’uri Khaleelu, Allah ya dubi hakurin da kai, ya cika maka burikan ka, dunia da lahira, Allah ya muku albarka, ya tsare ku ya ‘kara kareku daga sharrin ma sharranta.”

Sam Dr Khaleel bai so ba, amma ya xaiyi? Hakika zab’in iyaye shine zab’i nagari ba son rai ba. Cikin taushasshiyar murya yace,

“Ameen Inna. Sun ci darajar ki, da wallahi hukuncin da na ‘dauka shine sawwake zaman mu dasu tare, Allah yasa zab’in da kikai shine mafificin alkhairi, na janye qudurina, amma zamana dasu a Abuja ya ‘kare Inna. Ita Karimatu zan mayar da ita can Bauchi inda gidan gona ta yake, ita kuma Amina zata koma jigawa, saboda zan fara part time lecturing acan. Ina ga idan akai haka, komai zai yi sauki, tunda zama waje ‘d’aya shine yakawo had’uwar kan su, dama cusa mummunan ra’ayi a zukatan su.”

Jinjina kai Inna Bilkisu da Ya Bala sukai, alamun sun amince da hakan, Karimatu da Yafendo kuwa sun ‘danji sauki a ransu. A washe-gari kuma aka ‘dakko su Hafsat daga kano, hade da Hidaya dake Zaria. Sosai sun canxa tamkar basu ba, dukkan su, suka rankaya gidan Haj Aysa, takanas daga umarnin Inna Bilkisu wacce ke jagorancin tafiyar. Hak’uri sosai suka shiga bata, tamkar basu Karimatu ba, duk sunyi laushi, fadakarwar da Inna Bilkisu tayi musu, ta matukar canza su, sai dai duk da haka Karimatu da Yafendo sun ‘dau mummunar gaba a tsakanin su, Dan ko d’aya na magana, d’aya bata saka baki. Haka suka dawo gidah, suka kara neman gafarar, Dr Khaleel. Ganin hakanne yasanya Inna Bilkisu baiwa Dr Khaleel shawarar ya ‘dan saiwa su Hafsa da Hidaya matsakaicin gidah kowacce a garin da take aure, saboda zama waje ‘d’aya da kishiya babu dadi. Hakan kuwa akayi, da sati ya zagayo kuma kowacce cikin matan biyu, wato Karimatu da Yafendo, ta koma sabon gidan ta, Karimatu a bauchi. Yafendo kuma a Dutse/Jigawa.

LAGOS IDIROKO.

Bikin Fatima, yayar Saifullah aka yi, aka kaita gidan ta dake port-harcourt. Da sati ya zagayo kuma Islam ta koma Abuja, Don fara lectures din first semester na MBBS.

*USA 🇺🇸 *
Harvard University(Cambridge)

Sosai convocation hall ya cika da students ,parents da kuma teachers. Kowa ka gani da graduation gown a jikin sa, can na hango Saifullah. Sanye cikin graduation gown, tayi matukar amsar jikin sa, ba kadan ba, kyakkyawa r fuskar sa ta kamala ta ‘kara cika da annushuwa. Chancellor ‘din makarantar ne ya kirashi, nan aka bashi award na, best student of the year. Da kuma first call student na department of Architecture. Awards dai kala-kala haka aka dinga kiran sa ana bashi, Muslim student society of Cambridge ma sai da suka bashi award na, Mufti of the year. Kai abun sai sam barka kawai, ba’a cewa komai.

Saifullah faruk muhammad, saurayi ne ‘dan shekara ashirin da takwas a dunia, ya kammala senior secondary certificate d’insa anan Lagos, inda ya tsallaka nahiyar turai ya karanci fannin architecture a first degree d’insa (Bsc. Architecture), bai dawo ba ya ‘dora da degree na biyu a matakin harkar kasuwanci, wato master of business administration (MBA) .

Fari ne, amma ba irin dau ‘dinnan ba, kallo d’aya xakai masa kasan Allah yayi kyakkyawar halitta, dogo ne sosai, sannan ba shida jiki, sannan bai cika rama ba, zamu iya kiransa moderate. Yanada yalwataccen gashin kai dana gira, domin girarsa ta kusa had’ewa ma, tsabar cikar ta. Yana da kwantaccen saje a gefan fuskar sa, wanda turawa ke kira sideburns. Idanuwan sa dara-dara ne TubarkAllah. Hancinsa kuwa tamkar shiya zana shi dan tsawo, bakinsa dan ‘karami ne jawur dasu kamar ya shafa jambaki. Kai bayyana yadda saifullah yake tamkar bata Lokaci ne, sai dai muce TubarkAllah kawai. Allah yayi halitta.

Yana karbar certificate d’insa yai apartment d’insa, ko takan friends d’insa dake kiran sa bai-biba, domin bayason hayaniya. Shiysa yace su Baba(Uncle Faruk) ba sai sunxo ba ya yafe, burjik ya tadda gifts boxes kala-kala da kati, duk na tayashi murna,

Girgiza kai yayi, shi sam mata suna bashi mamaki, yadda suke gaya masa suna sonshi, ko su rubuto masa wasik’a, yawancin gifts dinma duk sunan ‘yammata ne akai. Ko takan su bai-biba ya tattake wanda suka tokare mai bakin ‘kofa yai wucewar sa ciki, bakin sa ‘dauke da sallama, jefar da gown din yayi a kan sofa, yana sakin siririn tsaki, kafin yace.

“So uncomfortable...!”






_banyi edit ba,pls ignore all typos_




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 26-27_*

_An amazing page, goes to an amazing person, this page is dedicated with love and appreciation to my day one niggurh, my sissy and always a favorite fan of my novels.. *MISS PINKY*, _😻🌹🤗.

_nanahafsat.wordpress.com_


*ABUJA*

Kallo ‘d’aya zakai musu kasan a matuk’ar tsorace suke. Karimatu jikin ta in banda rawa babu abunda yake yi, Mutuniyar ku, Yafendo kuwa sai sakin tusa take yi. Girgiza kai Dr Khaleel yayi kafin ya haura saman Karimatu abun sa, duk jikin sa babu dadi yake jinsa, a ransa kuwa ya qudiri niyyar yanke zama dasu Karimatu, don kwarai xasu iya kisa, sam basu da imani.

Cikin hanzari ya ‘dakko wani brief case a gefan gadon sa, takaddu ne fal ciki, dake ‘dauke da transcripts na students ‘d’insa, ‘kasa ya sauka. Ko kallo basu isheshi ba. Secretary ‘dinsa mai suna ‘Mamman’ ya bawa y’ar jakar, yana jaddada masa da,

“Dan Allah Mamman kakkai wasarai-rai da sak’on nan, a yanzu ba sai anjima ba, ka taimaka ka kaiwa ‘senate board members’. Saboda nagaya maka a yanzu haka wani aikin ne agaba na.”

Gyad’a kai Mamman yake tayi, alamun girmamawa da kuma cika alqawari, cikin ladabi da jakar a hannun sa yace,

“Insha Allahu oga yanzu zan kai musu, karkaji komai. Your happiness is what matters me most.”

Murmushi Dr Khaleel yayi, kafin ya sake bashi hannu suyi sallama, sashen sa ya koma ya xauna, addu’oi kawai yake ambata a bakin sa, hannuwan sa duka biyu dafe da kuncinan sa, idanuwan sa kuwa, zubar da hawayen bakin ciki suke yi, abun tausayi. Kallo d’aya zakai masa, ka tabbatar yana cikin babbar damuwa. Rasa yadda xai yi yayi, cikin hanzari ya ‘dakko paper da biro yana k’ok’arin rubutawa kowaccen su saki. Wata zuciar tace masa,

“Rubuta musu uku-uku kawai, hakan shine dai-dai”

Gyada kai yayi, alamun ya aminta da yadda zuciyar tashi tabashi shawara. Yana cikin rubutawa dayar zuciyar tace,

“Uhm-uhm Khaleel, kakka soma yanke ‘danyen hukunci irin wannan, kanada magabata fa, shin xasu ji dadi idan suka ga ka tsallakesu kayi gamon kanka?”

Jefar da takardar yayi yana lumshe idanu, zafafan hawaye masu ‘dumi ne ke faman raito daga idanun sa, cikin murya gwanin ban tausayi yace,

“Hasbuna-Allahu wa ni’imal wakeel”

Haka ya dinga maimaitawa, kafin ya samu nutsuwa, mikewa yayi ya shiga band’aki, ya dad’e aciki kafin yafito ya canxa kaya, sallar nafilfili yayi. Ya jima yana zaune yana addua . Kafin ya mike ya ‘dauki wayar sa dakekan dressing mirror.

Kiran Ya Bala yayi, Kan idan babu damuwa, yanason ganin su gobe, tareda Inna Bilkisu, domin bayason yanke ‘danye hukunci. Ganin bai sanar masa ko akan me bane, hakan yasanya Ya Bala jaddada masa, lalle yayi hak’uri, ya samu qur’ani ya karanta ko yasamu nutsuwa. Jirgin safe zasu biyo da yardar Allah.. Bayan yagama wayar jiki ba dad’i ya koma bakin gado ya zauna, Qur’ani ya ‘dakko ya karanta, har saida yaji nutsuwa kafin ya tashi, ranar ko takan direba dake tambayar ina xai kai shi baibi ba. Da ‘kafa ya taka har gidan sa, dasu Haj Aysaa ke ciki. Domin dama shidin ba gwanin zuwa majalisa bane, kullum yana school yana research, ko yana gidah cikin iyalinsa. Jefi-Jefi ne yakan zagaya wajen abokansa su d’an tab’a hira. Saboda bashida wani lokacin kansa, kullum hidimar iyalinsa ce da ta ‘yan uwa, sai ta ‘dalibansa da ma’aikatan sa, da jama’a masu nemon temako.

Karimatu da Yafendo kuwa duk sun zauce, Yafendo sai sakin Iska takeyi, minti kad’an kaji ‘bot’ ‘bobot’ ‘siit ‘ ‘sirrr’ . Yanzu ma ji kake ‘birrr’ takai-kaice ta sauta, cikin hanzari Karimatu ta rufe hancinta tana hararar Yafendo kafin tace,

“Kede kamar sabuwar tab’i wallahi, Haba Yafendo, kin saki ‘duwawu kina sakin tusa, idan anyi magana kice kin ‘dimauce ne, ko jinin ki ne ya fara hawa. Gaskia ba zata sab’uba. Haba sai kace mai ‘duwawun iska, minti kad’an ki saketa kamar wani abun arziki, bazai yiwuba wallahi, haka kawai ba zaki rud’an ciki ba, gata da shegen wari kamar shekararren mushe, Tashi ki fita gaskia, ki koma ‘bangaren ki.”

Yafendo tashiga girgiza kai, tana riko ‘kafar Karimatu, cikin tashin hankali tace.

“Yaya wallahi bazan iya komawa rugar mu ba, Allah idan Alhaji ya sake mu bazan iya rayuwar can ba, na saba da jar miya anan, ga Ac tana gyaramin jiki, inci abunda naga dama, nai yadda nake so anan, wallahi acan Bappah Ardo bayan ya sani tatso nonon shanu, Allah harda talla zai sa nayi da su ‘kanwar ‘kanwata joda, a kasuwar birnin-jimeta, ba...”

Bata k’arasa ba Karimatu ta shure hannuwan ta, tana banka mata harara. Kafin tace,

“Bakida aiki sai zancen Baffah kaza, Haba ki kyaleni mana, da wanne zanji uhm? Da sakin daze mana ko kuwa da rayuwar ‘yata dake hannun sa’an ubanta?! kishiya na yadda taga dama da ita? Kamar Hafsa ace itace ke ‘dora girki a babbar tukunya, tana wanki, tana aikatuwa kamar ‘yar aiki? Yarinya ta data taso cikin gata? Komi yi mata akeyi, batasan babu ba, amma tsabar rashin imani Alhaji ya ‘dauke yarinyar nan ya bada ita ga wanda bashida tausayi. Idan har zan bar gidan nan to sai da Hafsa da takardar sakin ta a hannun ta. Wallahi ba zai yiwu ba. Ai Allah ya shiwa Furera albarka da ta sanar da ni ‘kuntacciyar rayuwar da Hafsat ke ciki, shiyasa Alhaji yace kar muje gidajen su, ashe yasan abunda yayi. (Furera! Y’ar leken asirin su ce dake kano, itake kawo rahotan gidajen su Hafsa da Hidaya)

Yafendo taja majina tana matse hawayen ta,

“Hakane Yaya, amma mu fara kashe wutar gabanmu tukun na.” Cewar Yafendo, Wacce gaba d’aya jikinta yayi la’sar, tsantsar tashin hankali ta bayyana a tattare da ita.

Tsaki Karimatu taja, tana ‘kara wurgawa Yafendo mugun kallo, kafin tace,

“Ke kam zuciyar ki kamar kare ya cinye, Toh banda ke da abun ki duk wanda yai rik’o da Malam na dotsa ai aikin sa kamar yankan wuk’a ne, ki kwantar da hankalin ki, domin yanzu zan kirashi na sanar dashi cewar yayi yadda xaiyi a rufe bakin Alhaji, sannan ya shafe wannan zancen dayaji a kunnuwan sa yanzu, ya sanya masa fushin wani abun daban, kafin safiya ya manta. Na miki alqawarin iya damuwar su Hafsat kawai zamu saka aranmu, yadda xamu ‘bullowa lamarin su yanzu shine agaban mu, ga garin magani nasa Furera ta karb’a, yadda zata barbad’a shegun su tsallaka shine aiki, don tace kullum gidan arufe yake,”

Ajiyar zuciya Yafendo ta saki, kwarai tafara na’am da zancen Karimatu. Sai data kurbi ruwan dake gefanta kafin tace,

“Wallahi Yaya maganar yaran nan na damuna, hakika suna cikin *MATSALAR RAYUWA* (littafi na) . Kamar wa’enda akai *AUREN BASHI* ( littafi na)dasu? Wallahi na ‘dauka Alhaji acikin ‘ya’yan Yaya (Ya Bala) ko Ya Hansa’u, zai samu wani ya dubi *SO KO SHAKUWA?* (littafi na) dake tsakanin su ya aurar dasu.”

K’wafa Karimatu tayi, tana faman jijjiga ‘kafa, cikin isa tace,

“Yo ai gani yakeyi idan ya bar su sun zabi *SON RAN* su, akwai matsala, shiysa ya basu sa’annin sa a matsayin *ZAB’IN IYAYE*, (littafi na (SON RAI KO ZAB’IN IYAYE?), kuma Allah sai yayi mana hisabi dashi, tunda muma munada iko akansu, namiji hankaka gabansa fari bayan sa bak’i, banda butulci irin na d’a namiji, mu sha wahalar rainon cikin yaran, mu haife su, mu shayar dasu, kafin wahalar yayen su, amma rana d’aya ka ‘dauki babban mataki, har ka yanke ‘kazamin hukunci haka, ai wallahi Yafendo tunda ga *RAYUWAR MARYAM* (littafi na) ‘din gidan mu, na tabbatar da maza mugaye ne. Amma humm! Idan yasan wata bai san wata ba ai.”

Yafendo ce tashiga bata baki, tamkar marok’iya, kai idan ka gansu tashi d’aya, zaka ‘dauka mai gidan ce da y’ar aikin ta, domin Karimatu na hakimce akan doguwar kujera, Yafendo kuma na ‘kasanta a tsakure. Wai nan kishiya da kishiya ne, kuma ta uku data biyu. Sam ba tsari.

Dr Khaleel kuwa yana gidan su Haj Aysa, wannan karan duk zurfin cikin sa, ya kasa b’oye mata damuwar sa, tashin farko data tambayeshi menene? Ya xaiyane mata komai, hak’uri tashiga bashi, kan kada yai saurin yanke hukunci dan Allah, tareda ‘doriyar shai’danne kawai ke ‘dawainiya dasu, ta ‘karkare da,

“Komai nisan dare, gari zai waye, wallahi Allah, xai bayyana mai gaskia Alhaji. Kama dena damun kanka , Insha Allahu babu abunda zai faru da ni ko zuriyata. Allah yai mana katangar ‘karfe da shed’an domin a har kullum babban burin sa shine, ya sanya bil adama aikin sabon da Allah zaiyi fushi dasu, shiysa Allah yace mu nemi tsari daga garesa, Saboda sharrin shed’an la’ananne. Kayi hak’uri Ibrahim-Khalellullah. Iya sani na da kai, kai d’in jarumi ne, baka sanya damuwa a zuciyar ka, kakka wani damu first love, Ungo ruwan sanyi, sha ko kaji sanyi a ranka..”

Tunda take magana yake jin wata nutsuwa da kwanciyar hankali acikin ransa, gaba d’aya idan yana tare da ita baida lokacin kowa da komai, tun suna saurayi da budurwa har kamawa yau , bata taba sab’a masa ba, sai dai abunda ba’a rasa ba na yau da kullum, domin tsakanin harshe da hak’ori ma ana sab’awa ballantana mata da miji.

‘Dagowa yai yana dubanta, cikin tacacciyar ‘kauna marar gauraye, hannun sa yasa ya kamo nata yana murzawa, ahankali yafara mata magana cikin rad’a-rad’a.

“Nagode uwargida na, hakika kin zamto haske da ke mamaye dukkan duhuna, kece tauraruwata cikin taurari, Allah ya saka miki da alkhairi. Dan Allah har abada kakki rabu dani, domin zan iya shiga ‘kuncin rayuwa.”

Kanta akasa take murmushi,
“Amin Alhaji..”

Duban hannuwanta yake, yana ‘kara shafa yatsun hannun. Cikin kasalalliyar murya yace,

“Waya miki lalle? Yayi kyau, ya miki kyau Aysaana”

“Yakolo ce”

“Ah dole nayi mata kyauta, mutumin ta kuwa yace cikin watan nan yakeso ta tare fa.”

“Haba?”

“Wallahi, ai ya mato da yawa, gaskia ta biyani dole na biya tukwicin lallen nan, amma kafin nan kema taso na baki naki tukwicin”

Tasan me yake nufi, shiysa cikin sauri tayi ‘daki tana murmushi...


*LAGOS*
(IDIROKO,MARYLAND, 12b)

Zaune suke a parlor, Uncle Faruk, Haj Zuwaira, Fatima, da Khaled. Plate ne shak’e da fruits akan center table. Kowanne da toothpick a hannun sa yana ‘dakkowa yana ci. Hira suke sosai, suna shewa cike da farin ciki, nan hira tayi hira, aka ‘dakko zancen auta Saifullah.

Uncle Faruk yace,

“Ni kuwa Khaled, kuna waya da mutumin naka kuwa?”

Khaled ya ajiye zucia yana murmusawa, cikin shafa ‘keyar sa yace,

“Uncle muna ‘dan tab’awa, kasan saifullah ‘dinne sai a slow. Sai ya gindaya wasu sharad’od’i...”

Kafin ya gama fada, Fatima dake gefe ta amshe da,

“Yanada time din bacci, karatu, gym (walkout), da kuma family time.”

“Ah, excellent! Wallahi haka yake fada Uncle, jia dana kirashi, ca yai na dinga duba timezone din tukunna, Wai time din ball d’insa ne, kaji fa Uncle. Kamar ni banda abun yi.”

Uncle Faruk ya shiga ‘babbaka daria ba ‘kakkautawa, Haj Zuwaira dake gefe ta dan’kawa Fatima da Khaled dak’uwa tana,

“Ungo nan! Haba. A kyale auta ne dan Allah, Naga kowa yanada tsarin sa a rayuwa, ku godewa Allah ma da yakeda family time dinku.”

Khaled dake gefe ya kyalkyale da daria, yana cewa.

“Kai Aunty! Shi fa nashi abun yayi yawa, idan ka kira shi fa cikin wannan shagwababbiyar muryar tashi, xaki ji yana cewa,uhum ina ji, kayi sauri pls akwai abunda zanyi.” Ya fad’i hakan, yana mai gwada muryar saifullah.

Haka dai su kai ta hirarrakin su, gwanin ban sha’awa, suna ‘kara tsara yadda bikin Fatima zai kasance. Don dama wanda zata aura take jira ya dawo daga Russia, inda ya zama anesthesiologists’. To yanzu ya dawo, dama an gama komai, kawai biki za’a gwangwaje dashi.

*IDIROKO 17b*

Riri ce zaune da Islam a parlor suna kallon wani show na ‘Grey’s Anatomy ’. Gaba d’aya Islam ce ma ta maida hankali tana kallon, saboda sosai show din yake ‘kara mata *WANI HASKE* dake tattare da ‘bangaren medicine. Ya Bala ne ya kira Islam a waya kan taje suyi sallama, don su zasu je Abuja, kuma zasu kwana biyu ko uku,

“Babu wata matsala dai ko Islam?” Cewar Ya Bala.

“Babu Uncle B.”

“Toh ba abunda kike buk’ata kafin dawowar mu?”

Nanma ta gyad’a kai alamun babu. Bundle ‘din yan ‘dari biyar guda ya ciro ya mika mata, k’in karba tayi tana cewa,

“Aa Uncle B. Wallahi bana buk’atan komi, kudin daka bani wancen week dinma sunanan, sun isheni haka Uncle B.”

Murmushi yayi, kafin yace.

“Toh shikenan, Allah ya miki albarka.”

“Ameen Uncle B.”

Sallama tayiwa Inna Bilkisu, suka rangad’a duka airport harda Riri, sannan suka koma hanyar gidah. Tun a hanya Riri ke jaddadawa driver, ya sauketa a KFCJ(Kentucky Fried Chicken Joint). Islam tayi k’ok’arin hanata, Sam Riri ta nuna batasan zance ba. Hakan kuwa akai, suna sauketa, suka koma gidah. D’aki Islam ta wuce ta zauna. Gaba d’aya ji take ba dadi, ba wajen zuwa, friends dinta duk a Abuja suke, kad’anne ‘yan Lagos. Kuma bawani shiri suke ba, wayar ta ta janyo sabuwa dal, wadda Ya Bala ya siya mata. Numbers din siblings dinta ne kawai aciki sai na friends, Sam bata social media activities ko d’aya, dan babu applications ma. Kiran Lee tayi suka gaysa, wadda itama ke kaduna taje hutu, sun ‘dan tab’a hira, takira Fatima Bichi. Inda Zaran take sheda mata ai ankawo kudin auren ta, nan bada wani jimawa ba za’a sha shagali. Daganan ta katse ta kira Hafsat Rano, ringing biyu ta ‘dauka. A speaker Islam tasaka wayar, tana gyara kwanciyar da tai akan kujera..

“Hello Lam-Lam!” Cewar Hafsat Rano cikin zak’uwa.

“Na’am future biologist. Ya kike?” Islam tafada tana mai rage volume na TV.

“K’alau fa, ya Lagos. Hope kinyi new catch?! Ki tabbatar kin samo mana Lagosian breed.”

Daria Islam ta kyalkyale da ita, kafin tace.

“Ku kam yaran nan kun shiga uku da harkar maza, ni rabu dani da wasu samarin Lagos, ‘dan Abuja zan samu.”

“Toh Allah ya kawo Lam-Lam. Ke ‘dince tsoron maza kikeyi, shiysa ma kilan suke shakkar miki magana.”

“Ko?”

“Kwarai kuwa, That aside, ke na kusa aure fa”

“Dan Allah dagske?” islam tafada, cike da farin ciki .

“Wallahi na kusa..Ba nagaya miki dana dawo na fara sana’ar wainar fulawa (flour) ba?” (Littafi na, (RANO MAI WAINAR FULAWA)

“Yeah! Haka kika fad’a. What about it?”

“Toh yazo siyan wainar ne, ya ganni, irin love at first sight ‘dinnan, sunan sa Nasser wallahi”

“Ah.. Masha Allahu! Congratulations babe. So karatun fa, yanzu ya xakiyi kenan?”

“Zanyi Insha Allahu a gidan sa, ai Kinsan biology ne, a nan BUK zanyi”

“Oh yeah hakane. That’s nice wallahi, I’m happy for you. Allah yasanya alkhairi babe.”

“Ameen Lam-Lam. Allah ya kaimu naku, idan anfito da ashoebi xan turo miki, ki bude WhatsApp pls.”

“Ameen ya Rabb. Okay babe. I will soon. Insha Allahu!”

Hira suka ‘danyi kafin Islam ta katse wayar,ajiye ta tayi a gefe, tana tunani gashi har mutum biyu a a set dinsu xasu yi wani auren. Plus Lee ma anytime soon kila za’ai nata. Dafe kanta tayi, dake barazanar fad’o mata, cikin murya mai d’auke da damuwa ta furta,

“Subahan’Allah! Ya Azeezu sa’adneey min kullu Amr.”


*ABUJA*

Gaba d’aya sun hallara a babban parlorn Dr. Khaleel, Ya Bala, Inna Bilkisu, Dr Khaleel, Haj Karimatu da Haj Aysa... Inna Bilkisu na hakimce a doguwar kujera, Ya Bala da Dr Khaleel na gefan ta a ‘kasa, domin basa iya zama a kan kujera idan har tana kai. Can gefe d’aya kuma Karimatu ne da Yafendo a rakub’e, sai raba idanuwa suke yi munafukai. Gyaren murya Ya Bala yayi yana.....

***
_Love is patient love is kind it does not envy it does not boast its not proud it does not dishonor others,it is not self seeking,it is not easily angered it keeps no record of wrongs,Love does not delight in evil but rejoice with the truth,it always protects,always trusts,always hopes,always perseveres_ #SAIFUL_ISLAM💕 2k19.


_Assalamu Alaykum dearies💕 Thank you so much for the love and care, The calls, messages, WhatsApp

Please Login or Register in order to submit comment