Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga tsakanin d’an mijinta da mijin,

“Ta cikin dabara ko mace tashiga tsakanin mijinta da iyayensa da makamantansu wannan kissa mara kyau sede muce tur da ita. Allah ka ganar da masu irin wannan kissa, Amma kissa mai kyau itace kulawa da mai gidah da tarairayarsa kamar kwai wanda daga ciki akwai, Kissar magana, kissar tafiya, kissar kwalliya, kissar abinci, kissar tsafta, kissar kallo mind you ba kallon film ba to kallon miji nake nupi, yawwa se kissar shagwaba da kissar kwanciya se kissar kula da jikin mai gidah suma xan d’auki kowanne nai miki bayani akansa Ina fatan kina ganewa?!,

Cikin k’asa da kai Islam tace,
“Eh ya Fati..”

“Kissar magana: idan xakiyi magana da mijinki ki kasance cikin nutsuwa da tauna magana da xaki gaya masa kafin ki fadeta don gudun gaya masa maganar da baxai ji dadinta ba ko bata masa rai, Ki dinga magana cikin sigar hankali karki dinga bud’e masa muryarki kala kala wani lokacin ki maketa wani lokacin ki dan budeta wani lokacin ki dinga yi a hankali kamar bakyason magana, wataran kuma idan kinason gaya masa magana mai dadi ko ta soyayya kice saiya baki kunnensa xaki rada masa. Sai kissar mu ta gaba,

“Kissar tafiya; idan xakiyi tafiya kuma kin tabbatar yana gurin ko yana kallonki daga inda yake ki dinga tafiyar da xata dauke masa hankalinki xuwa gareki misali ki dinga tafiya a hankali kamar bakyason taka k’asa wani lokacin ki dinga tafiya kina karairaya kina dan jujjuya jikinki wani lokacin kuma sauri sauri xaki dingayi kina juya maxaunanki idan ta gaba yake kallon ki kisan yadda xaki dan dinga girgiza kirjinki cikin hikima bata sigar da xai gane ba, amma fa Islam mijinki kad’ai xaki dinga yiwa wannan kala kalar tafiyar cux kikaiwa wani xaki dau zunubi ne,”

Cigaba da koyamata kissoshi tadingayi kama daga kissar kwalliya, da kissar abinci kissar tsafta, da kuma kissar kallo ciki harda kissar shagwaba data kwanciya, wanda sosai Ya Fati taja kunnen Islam akan kissar kwanciya ta kar kare mata da yadda xatai kissar kula da jikin mai gidah,

“Hope kingane?!”

“Nagane Ya Fati” cewar Islam datai wiki-wiki da idanuwa wai yau Ya Fati ce take hira da ita, hirar ma ta manya duk kunya ta davaibayetaa

“Yawwa to sai dan karin jan hankali daxan miki wanda idan kika dumfafi yinsa tabbas xaki xamo shalele awurin mijinki yaxamto ba wacce yakeso da gani sai ke hanyoyin jan hankalin sune,

“Kula da duk wani abu da mijinki yafi so,ki kula sosai da duk wani abun da bayaso ki lura da abinda yake damunsa da hanyar da xaki kula da iyayensa da danginsa da yadda xaki xauna lafiya da kowa babu ruwanki da wani kishi na banxa da wofi wanda xe kaiki ga hypertension, kishi dole ne ba ace karki ba amma akwai irin kishin da akeyi bana yanxu da yaxama na hauka ba, kede babu ruwanki don baki taso kinga anayi a gidan ku ba...

Islam ta daga kai, tana tuno irin buga kishin da ake a gidan su, Fatima ta ci gaba da cewa,

“Na ga, ga Ammi nan da Maman Arfat kamar ya da kanwa haka suke abun sha’awa ba’a taba jin kansu ba ina fatan kina ganewa?!”

Kad’a kai Islam tai tana wasa da yatsun hannunta cikeda nutsuwa. Ya Fati ta cigaba da yi wa Islam jan hankali akan rayuwar gidan miji ta k’ark’are da,

“Abu na k’arshe shine ladabi da biyayya, babbar magana kenan domin duk abubuwan dana fada abaya idan ba ladabi da biyayya yaxama na banxa don duk iya tafiyar ki ko iya farinki idan bakya yiwa miji biyayya meye amfaninsa?! Misali kinyi kwalliyar jan hankali kinyi masa kalar girkin dayake so jira kike ya dawo yaga kwalliya, Yaci abincin da kika tanadar masa amma yashigo ba sannu da xuwa ba karbar kayan hannunsa saidai ki bishi ki dire masa abincin da kika yi masa tana iya yiwuwa ma alokacin ki fara masa k’arar ko kudi da makamantansu toh tell me tayaya zaiga kyan kwalliyar sannan kuma yaji dadin abincin?!,

“Ko kiga wasu matan miji na magana suna yi suna fada sosai fad’i in fada bai dace ba sam kamata yai idan mai gidah yana fadansa kiyi masa shiru idan yagama sai ki bashi hak’uri idan kuma ke aka batawa baxaki iya bada hak’urin ba tunda ranki yakai kololuwa a baci to kiyi shiru kawai kuma ko menene yace kiyi masa koda kuwa ran naki a bace yake don kansa shima xe sakko ku shrya, Wasu kuma matan xaki ga suna yawan korafi akan maxajen su don abinda ba abin fada ba sai su rufe su da fada wasu ma kawai xakiga sun fice daga harkar matan kwata kwata inkinga sun kusancesu to sede idan rabo ya tsinke yawanci kuma xakiga akan maganar da mukai d’axu ne akan rashin gamsuwa damu da maxajen mu ba sayi xakiga mace har mace, Kamar ita tai kanta don kyau sai kiga sun had’a kishi da wadda bata kaitan ba harma xata xamto itace mai fada aji gurin mijin xakiga yana Allah Allah girki ya xagayo kanta don yafi gamsuwa da ita xakiga wasu matan suna yawan tambaya to meyasa wata macen ake gamsuwa da ita wata ba’ayi?!,

“Ba komai bane yake kawo haka kisani sai kowa da irin ni’imar da Allah yai masa misali kowanne jinsin halitta akwai maza akwai mata kuma both ana samun farare da bak’ake dogaye da gajeru mai kib’a da siriri ke kowanne abu dake jinsin bil adama xaki ga nawani yafi nawani to haka ma ni’ima take ajikin mata da maxan wata macen tanada ni’ima sosai bata buk’atar kari wata kuma tsaka tsaki ce wata ma bata da ita se d’an abunda ba’a rasa ba,

“Don haka Islam kisani kamar masu bukatar karin jini da ake cewa ga abubuwan daya kamata suci haka ma matan masu neman k’arin ni’ima ajikin su akwai abinda yakamata suci domin ance idan kanada kyau to kadad’a da wanka,sai dai wasu matan suna amfani da magunguna barkatai wanda wasu ma basusan komeye ba sudai suci susha buk’atar su ta biya kawai shikenan, Wanda xakiga yin hakan xakiga yana haifar da cututtuka barkatai ga mata,shawara ta dake Islam karki xamto cikin irin wa’innan matan masu bankawa cikinsu kowane magani suka ji ance yanayi aa sam karki soma kowaye yakawo ko yaxo maki dashi karki soma amfani dashi kinji de na gargadeki domin hakan yana haifar da toshewar mahaifa,hana haihuwa ko canxawa yaro kamanni kamar wata k’awata sumayya matar ma’aruf wallahi abinda yafaru da ita kenan,Tahaifo yaro marar cikar halitta abun tausayi saboda ita komai cusawa take ta bankashi a baki duk bamu sani ba se bayan da xata haihu a asibiti dr tace har cancer magungunan suke sawa dakyar aka mata cs don kasa haihuwan tayi abu nabiyu ga kaikayin gaba wato infection,Da kurajen gaba plus ciwon ciki ke da abubuwa da dama de kede ki lazimci shan fruits kamar yadda kikaga ana saki sha anan su,

“Kankana,gwanda,ayaba,guava,lemo,tumatir,rake,aya,kwakwa,dafaffiyar gyada xuma,nono,madara,madaran shanu gurji cukwi,zogale da ruman da inibi se tuffa da kuma xaitun kina ganewa kuwa?!”

Nodding kanta kawai Islam tai gaba d’aya jikinta yayi sanyi se yanzu tasan tabbas aure aka mata batare da ya fati tadamu da damuwar da Meenah tashiga ba tacigaba da maganar ta,

“Se abu na k’arshe naga lokaci na ja, Auta yana ji ranki a kasa,Addua wato kirik’e addua, wallahi Islam addua makarin mumini ce ke duk wanda ya lazimci addua wallahi baxe taba tabewa ba azkhr dinnan kidinga yawaita yinsu nataho maki ma da wasu littafin du’as din suma ki rik’esu gidanki kullum yaxamto cikin karatun qur’ani musanman suratul baqra domin duk gidan da ba’ayinta ance kamar kango yake, Ki yawaita yin addu’oi na neman tsari ga korar shaid’an ya kuntata masu ya karyasu ke dama mutane ma sharranta masu nufarku da sharri, addu’a tana jawo yardar allah ta’ala, suna gusar da bakin ciki da bacin rai a zuciya,suna janyowa zuciya farin ciki da nishadi,suna karfafa zuciya da jiki,suna jawo arziki suna kara imani da tawakkul da sabr ke sunasa komai na mutum ya daidata ya samu peace of mind ki kama Allah Islam, kirike addua da qur’ani Insha Allah rabbi xaki bani labari,anan xan tsaya seki fad’i tambayoyin ki karkiji kunya ta Islam, ko tsoro saki jikinki ki fad’amun abinda baki gane ba.,

Shiru Islam tai tana k’as k’as da yatsun hannunta kunya dukta isheta jin shirun yayi yawa ne yasa ya fati sake tambayrta,

“Uhum Islam ina jinki”

“Ba..Babu komai ya fati duk nagode JazakillAhu khairan”

“Ameen..To shikenan dukde abunda baki gane ba ko kikeda karin bayani akai seki kirani awaya yawwa nasanki dama ke sarkin kamshi ce amma ki kara xage damtse khumras dinnan na wanka dana wanki da jiki dana moping duk fa kidage wajen amfani dasu kingade yadda mijin ki ke son kamshi, ki sake kaimi da sauran turarukhan jiki dana tsugunno dana kaya dana gidah du kulaccams dinnan duka kiyi amfani dasu, Idan sun kare kiyi waya ayo miki wasu koki had’a da kanki irin kamshin da kikeso aikin iya ko?!”

“Eh ya fati”

“To shikenan Allah ya miki albarka ki shirya, ga kaya nan da laffaya inji Mami, wannan kuma tsumin chad ne ki sha yanzu, karki mike sai bayan minti goma, wannan kuma cinye shi zaki tas, idan kin gama sai ki sakko, Allah ya sa ki koma a sa’a ya kad’e fitnah, ya baku zuri’a dhayyi ba...”

Cewar Ya Fati.. Ta karasa fada tana mai nuna mata komai da amfanin sa, a kunya ce Islam tace,

“Nagode Ya Fati, Allah ya saka muku da alkhairi, ya sa ki sauka lapia, Ameen.”

“Ameeen”

Cewar Fatima, ita kuma Islam ta mik’e ta shiga shirya wa...Hankali kwance ta gama kintsawa, tayi amfani da duk abun da Ya Fati ta bata tayi, admiring kanta ta tsaya yi ta cikin mudubi, ba kadan ba kayan sun mata kyau, lace din pink ne laffayar kuma pusher pink. Ganin su kadai ne ba kowa, yasa ta shafa pink jambaki, Ai kuwa ya mata kyau sosai, dan karamin bakin ta ya kama sosai da jambakin, abun dai sai fadar; soo masha Allah. Kasa ta sauka tun daga nesa Saifullah ya tsurawa Islam kallo, tamkar yau ya taba ganin ta, Haj Zuwairah da sauri ta ‘karasa ta rik’o Islam, Islam kuwa ta ‘barke da kuka, Don ba kadan ba takeson Haj Zuwairah, ganin ta ‘dauke ta kamar ‘yar data haifa, tare suka dinga kukan, domin Fatima ma sai da tai hawaye, sun bata tausayi, kuma ta lura mahaifiyar tasu na yiwa Islam din wani irin so tamkar ba sirikar ta ba.. Daga k’arshe dai Haj Zuwairah daki kawai ta shige ta rufe, Saifullah ya kama hannun Islam suka tafi, dai-dai bakin kofa ta cije tana shesshekar kuka, Ai kuwa yai mata ‘daukar jarirai ya direta a mota itada kayan ta...

A hanya ya tsaya ya sai kaji da kayan ‘kwalam da makulashe, suka nufi gidah yana aikin bawa Islam hak’uri, ba abunda yake kara tunzura kukanta irin first night din da Lee ta tsoratar da ita, Suna komawa gidah tai hanyar dakin ta, komai a killace a tsaftace, da alama Saifullah yasa an gyare gidan. Wanka ta sake yi ta feshe jikin ta da turarukha, nan Saifullah ya shiga shima da kayan baccin sa, dauke da plate cike da kaji da sauran mouthwatering kayan dadi, a hankali yace mata,

“Love ga abinci sakko ki ci pls..”

Bin kazar tai da kallo ta ‘dauke idanun ta daga gare sa, durku sawa yai kafafuwan sa zube a kasa yayi kneeling down, hawaye fal idanun sa, tuni suka fara wanke kyakkyawar fuskar sa, kafin yace.

“Dan Allah love kiyi hak’uri, ki yafemin, hakika nayi kuskure a da, amma inaso ki dau hakan ki ajiye a matsayin past life, love ko Allah da ya haliccemu muna masa laifi kuma mu roke shi ya yafe mana, so pls ki yafemin Love, kwatankwacin haka ma bazan sake miki ba insha Allahu, wallahi wallahi ni ba ma SO na ke miki ba ‘KAUNAr ki nake, domin ‘kauna bata karewa kullum daduwa take yi, So kuma yana raguwa kuma wani lokacin har dena yin sa ake yi, Ina miki son so, Ina miki son kauna, Ina miki tacacciyar ‘kauna marar gauraye...”

Shiru yai yana goge hawayen fuskar sa, ahankali Islam tasa hannu ta ‘dago shi tana goge masa hawayen kafin tace,

“Ni ma Ina kaunar ka Zawj, I love you pass my mind beyond my soul, ni ban rike kaba dama a raina, Allah ya yafe mu baki d’aya...”

Dadi Saifullah yaji, ya kama hannun Islam suka zauna, Kazar ya dakko ya sa mata a baki yana cewa,

“Ki ci sosai Love, wannan itace kazar amarcin mu, ki dau yau tamkar itace ranar da aka kawo ki gidan ki, kuma a yau ne zan shayar da ke zumar da tafi kowacce zaki, Ina fatan zaki bani hadin kai?”

Islam tai gum da bakin ta, Saboda ta gano nufin sa, Ai kuwa ya saki murmushi yana cewa,

“Matsoraciya...”

“Eh dai...”

Caraf ya hade bakin su, dama tun dazu yake muradin haka, sun jima suna abu d’aya, kafin su cinye kajin tas su ka kora da yoghurt, bandaki suka shiga atare sukayo alwala da brush, bayan sun kurkure da mouthwash na mint, Su kai sallar isha’i, sun ‘dan tab’a kallo kafin su koma dakin sama, Saifullah yace da ita,

“Love tashi muyi sallar nafila mu godewa Allah, abisa azurtamu da yayi na samun junan mu..”

Daga kai kawai Islam tayi, suka yi sallar, Saifullah yaja ya zauna a gabanta yana mata tambayoyi akan addinin musulunci, ta amsa dai-dai gwargwadon sanin ta, gado suka haye gaban Islam sai fad’uwa yake yi, Saifullah na hankalce da ita, janyo ta yayi jikin sa yana karanto adduar bacci;

“: اَللَّهُـمَّ بِاسْمِكَ أَمُوتُ وَأَحْيَا,”
Can kuma ya ‘kara da adduar saduwa da iyali(du’a when having relation with wife):

“: بِسْمِ اللَّه ، اَللَّهُـمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا”

Benefit;
Ibn Abbas (R.A) the Messenger (Peace and Blessings of Allaah be upon him) said, "If anyone of you, when having sexual intercourse with his wife, says (This Du'a) and if it is destined that they should have a child, then Satan will never be able to harm him."

[Bukhari - Volume 7, Book 62, Number 94]...

Cikin firgici Islam ta nemi ‘kwace kanta, jin yadda Saifullah yake shafa ta

A hankali ya shiga shafa bayanta zuwa gashin ta, cikin rad’a rad’a yace da ita,

“Wane turare ki kai using a gashin ki, it smells nice..”

Cikin rawar jiki da baki tace,

“Strawberry conditioner ne na product din body shop..”

“Love... calm down.”

Cikin tab’o cikin rigar ta ya lura ba komai a jikin sai rigar baccin ta, ahankali yace da ita,

“Love...”

“ummm!!”

“I want you, let’s make this day romantic and most memorable pls..”

Mutuniyar ku da alama tsumin da Fatima ta bata yafara aiki, a hankali Islam tace

“I want you too”

Haba Saifullah sai ya dauki ragaman aiwatar dakomi lokaci guda yafara bata hot kisses a lebanta, ita kuma Islam sai take kokarin suma, bata ankaraba taji Saifullah yayi fatali da rigar ta, ranar Islam taga abin mamaki, Saifullah sai faman sumbatu yake unnecessary, jikin Islam ya fara rawa, Saifullah ya lura da hakan yace da ita,

“Love! do not be afraid, I'm not gonna hurt you insha Allah! I promised to be an excellent lover”

Islam dake rawar jiki tace,

“ I know you are not gonna hurt me... And I love yo...”

Bata karasaba Saifullah yafara aikamata hot kisses, tuni ya mai da Islam cikakkiyar mace aranar da lallami da komi, yana kuka tana kuka, shi kukan dad’i ita kukan jiga ta, Duk koda shi dinma ya jigata kwarai matuka.

Ni miss xoxo naja masu kofa dan nafara wuce hurumina, sannan naxauna abakin kofa inajira! Yau dau burin masoyan ya cika ko kuma nace burin ango Saifullah yacika aure yau kusan wata 3 amma sai yau hakarsa tacimma ruwa, kafin gari yawaye Islam ta gane kuranta, Don kusan kwana sukai ana abu daya saida yaji kiran sallan farko kafin ya kyaleta, sai da suka shiga bayi don tsaftace jikinsu nan Saifullah yalura ya galabaitar da Islam, sosai yatara ruwan xafi da Dettol yasa tashiga ta gasa jikinta,

Cikin shagwaba yace,

“nima barin shiga ruwan xafin, Dan yau Love tayi dis virgin dina nima”

Ita dai Islam shiru tai, ya shrya yatafi masallacin asubah! ita kuma Islam tayi tata agidah,bayan yadawo daga masallaci yadau waya yakira wajen ppa dinsa yace yau ba zai samu zuwa ba, , abashi absence leave na sati d’aya. Sannan yakalla IsLam datai kasa da idonta tanajin kunya, Saifullah yai daria kafin yace,

“ Kinga kafin nan mun fara renan unborn baby dinmu ko?!”

itade Islam shiru tai.,Saifullah ya lura kunyar sa take ji yanzu, tun da su kai auratayya, a hankali yace.

“Toh tunda ba zaki magana ba shikenan, amma Ina mika godia ta agare ki, nagode sosai gaskia kin cika yar halas da baki zubar da mutuncinki awaje ba, Don kin nuna lallai iyayenki sunyi maki kyakkyawar tarbiyya, Thank you so much fa, Don wallahi na samu Mrs Saifullah din dai-dai, Ni na bude kayana, kuma nima kin same ni sabo, gaskia I’m truly grateful zuma na, duk da na sha rakin kiran su Ammi and plenty of others, Thank you so much, Allah ya bamu zuri’a dhayyiba Ameen..”

“Ameen”

Islam ta fad’a, hade da runtse idanu saboda zafi da zugin da ‘kasan ta keyi,

Safiya nayi Saifullah yafita siyo masu abinci a eatery, Islam ita kadai akan kujera sai murmushi take tayi, tayi wankan ta cikin kananan kaya, wando 3quater, sai rigar yar karama da ita, Sosai tayi kyau abinta, Sai kamshi take. cikin xuciarta tace,

“Saifullah kenan, mai kima da hak’uri, ya Allah kabar ni da Saifullah dina, namiji daya tamkar da dubu”

Sai tayi murmushi takuma ce

“Lallai soyayya lokacin da xata shigi mutum bata shawara..”

Ko da Saifullah yadawo shima shigar tasa kaman ta matarsa short nickers yasa da riga yayi kyau abinsa, brown eyes dinsa sai shining suke, Yazo gabanta yadauketa yadora ta kan lap dinsa ahaka yai feeding dinta abincin daya siyo musu, ita dae sai kunyar shi takeji, yai murmushi,

“Wai Love meyasa kikejin kunyata yanxu bayan mun riga da munxama daya, babu kunya atsakaninmu”

Ya kafe kan lallai sai ta kalli cikin idonsa, Islam ta kasa, da cakulkuli da komai yasa Islam takalla cikin idonsa sai Saifullah yakashe mata Ido ,gaba daya takasa dauke idonta anasa,Dan wani kyau da kwarjini ta ga yamata, Idonshi yatafi da ita ga kuma wata so da shakuwa data gani ta karanto cikin idonsa...kawai tasa hannu tafara taba curly hair dinsa dasu kai yala yala kaman gashin jarirai da idonsa da lips dinsa, Nan suka shiga tab’e tabe junan su, romancing kawai nothing beside the romance.

Ko da dare yayi, Arabian shi ga su kai, suka nufi wani wajen cin abinci bayan sun dawo suna xaune a parlor, suna shan milkshake, kan Islam akan cinyar Saifullah tace,

“‘Dan kira mun waya ta, bangan ta ba..”

Daga kai Saifullah yayi, ya kira wayar tata, ashe suna zaune akan ta ma, Saifullah ya ‘dago wayar yana kallon screen din, ‘suffocating being’ shi ne sunan da yagani a rubuce, Ai kuwa ya cuno baki gaba kafin yace,

“Love ni ne suffocating being, why?”

Ta gimtse dariar ta, kafin tace,

“Ka nason fadan so suffocating shi yasa..”

“Oh ai that was then, lokacin everyday felts so uneasy, and around mutane ina feeling uncomfortable. Tun ina school word din ya zauna a baki na, and with time it became addictive more like obsession, Thats it kawai, amma ai na rage fad’a, beside zan ma dena fada. Saboda ke, you mean the world to me, I love you more than life it’ self...”

Islam tayi murmushi in awwwn mood, kafin ta hade bakin ta, dana shi, sun jima a haka, kafin tace,

“I love you most sugar...”

_A gurguje_

Haka rayuwar su ta kasance, kullum suna cikin bawa soyayya hakkin ta, duk da tsakanin harshe da hak’ori ma ana samun sab’ani,Toh suma sukan dan samu sab’anin, amma dake sun riga da sun fuskan ci juna, ba sa jima wa suke shiryawa abun su, kullum suna cikin soyayya, kamar cin ‘kwan makauniya, da haka har Aji Mommodu ya biya musu umrah su dasu Khaled suka je, Bayan sun dawo ne Islam ta fara laulayin ciki, daga k’arshe, Sai deferring semester tayi, ana scanning aka ga yan biyu mace da namiji, Both familyn sunyi farin ciki wanda alqalami ba zai iya rubuta shi ba, cikin ta na tsufa Haj Zuwairah ta dauke Islam, Ai kuwa Saifullah yace bai san xance ba, dole sai da ya bisu ya manne mata, ranar da zata haihu ne kawai baya nan, Ta haifo santala-santalan ‘ya’yanta, macen aka sanya mata sunan Haj Zuwairah zasu dinga kiran ta da ‘Arya’, namijin kuma sunan Alhaji Mommodu suka sanya masa, za’a dinga kiran sa da ‘Aryan’, Murna wajen Saifullah ba’a magana, domin lokacin sa da soyayyar sa kacokam ya ‘dauka ya ‘dora akan su,Wani lokacin har kishi take dasu, sai yayi lallami da toshiyar baki kafin ta hakura......

_*DAWOWAR LABARI_*
_*(K’arshen Page 1)_*

Haka bacci ‘barawo ya sace Islam, zuciyarta cike take da tuna bayan rayuwar ta, tana ta shek'a baccin ta saifullahi yayo mata reply,

_"Sugar pie.It does not matter how my day was, I always long for the night, to cuddle you all night as you quench my heart.It was a stressful night,aiki muke tayi yanxu ma muna construction site na ikeja... A shafa min kan Arya da Aryan...I love you more than life itself. Goodnight my love.."_

*Da* Asubah ta farka saboda kukan ‘yan biyu, Sallah ta fara yi, sannan ta basu Mama suka sha,suna gama sha kuwa suka koma bacci, ita kuma ta tashi ta sauka kasa, lokacin Hinde mai aiki har ta gama shara ta fara mopping, ta yata Islam tai da wasu abubuwan, sai takwas saura ta koma sama, tayi wanka, ta yiwa yan biyun nata wanka, da sauri ta kintsa su, Saboda asibiti zata kai su, akwai monthly shots (allura) da ake musu na kariya daga kamuwa da cututtuka. Sai a sannan ta janyo wayar ta, message din Saifullah ta karanta tana murmushi, reply ta masa kafin ta kira shi su gaysa, inda yake ce mata sai jibi zai dawo, kamar za tai kuka ta yi masa fatan alkhairi da Allah ya dawo dasu lapia...

Hinde na rike da Arya ita na rike da Aryan suka shiga mota, driver ya jasu, dake tunda tasamu ciki, Saifullah ya hanata driving gaba d’aya, sai driver ne ke kai ta duk inda zata, suna zuwa asibiti suka nufi wajen likita, yayi duk abunda zai musu, sannan suka je farmers market inda tayi y’ar siyayyar cefanan ta, sun jima kafin su dawo gidah, suna dawowa gidah tun daga parking space taji gabanta na fad’uwa haka dai ta danne, suka karasa cikin gidan, Ta haye sama da yaranta, Hinde kuma tai kitchen tana jere kayan da suka siyo a ma’adanan su.

Kamar daga sama ta jiyo muryar Saifullah, a razane ta juya tana duban sa, kashe mata ido d’aya yayi kafin yace,

“Surprise..”

Hawaye ne suka shiga reto a idanun ta, karasawa tai ta rungume shi tana dukan kirjin sa, murmushi yayi yana kara manneta a jikin sa, sun jima a haka kafin ta goge hawayen ta tace dashi,

“Me zaka ci? Na dafa maka yanzu Zawj”

“Love! A koshe nake wallahi, ni yanzu abunda nake so kawai ki kaiwa Hinde yan biyu, nayi missing dnki wallahi, a matse nake..”

Daria tayi, kafin ta sauka ‘kasa da yan biyun ta, ta bawa Hinde su, Sannan ta koma sama. Tun a parlor suka fara, zuba lobayya, daga baya ya dauketa cak sukai daki, anan suka gwangwaje suka rakashe yadda suke so, kafin su tashi suyi wankan tsarki, sukai sallar la’asar da aka kira, Saifullah ya dubeta yana murmushi kafin yace,

“Hakika kece rayuwa ta Love, you are my fantasy my only desire, ina son ki, So mai tsanani, Nagode wa Allah da su First Love, da suka hada aure na dake, hakika ZAB’IN IYAYE, Yafi SON RAI, ban taba soyayya ba sai a kanki, kuma akanki na fara sanin ‘ya mace, kin shayar dani zumar da ban tab’a ‘dan’dana ba, Allah ya bar min ke har abadan da’iman, kuma ina rokon Allah yasa zaman mu ya dore har aljannatul frdaus.

Please Login or Register in order to submit comment