Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, wallahi ya isheni wai sai na ba shi number dnki ya baki hak’uri, nace kinyi aure amma zan gaya miki on behalf of him. So kiyi hak’uri pls, Basher yayi lefi then, amma inaga shi dinne a live show din dan cousins dinsa singers ne.. That aside, ya gidah Lam-lam? Hope everything’s going on smoothly??”

“Alhamdulillah Riri, Yasu Mom?”

“Lapiar su lou, ki gayda mai gidan, ana kirana, later.”

“Alright bye, take care..”

Nan aka shjga kallon-kallo, Saifullah ya sunkuyar da kansa, kunya duk ta kama shi, deep down he’s feeling guilty, Fatma tai murmushin takaici, kafin ta dubi Islam tace da ita,

“Islam ki koma ‘daki, zan zo na same ki”

Islam tai nodding kanta, sai yanzu ta gano, bugun cikin ta akai ta fadi gaskia al’amari. Murmushi tayi daya nuna taji dad’in wanke kanta da tai awajen su, and finally Saifullah zai dena zargin daya ke mata, sai yanzu take recalling duk bakaken maganganun da yake gasa mata duk akan zargin ta da yake yi ne, wasu zafafan hawayen bak’n ciki ne suka shiga reto a kyakkyawar fuskart ta.

_A gurguje plls👏🏻_

Dare ya zama safiya, safiya ta zama yammaci, yammaci ta koma dare, Lalle Allah mubuwayi ne gagara misali, cikin haka kuwa akai sati biyu da wannan zancen, Saifullah kullum yana jelan gidan su Mami da Aunty Latifa, gashi daga baban nasa har uncle Aji Mommodu duk basa sauraren sa, Islam dinma bata bashi fuska, duniya dai tayiwa mutumin ku zafi, ya rame kad’an saboda rashin cin abinci da kwanciyar hankali, damuwa tayi masa yawa. Haka dai adaddafe yake tafiyar da aikin wurin ppa dinsa..

Ranar wata asabar da yammaci, ya je gidan su, ya tarar mahaifin sa na nan, yana kallon kwallo na La liga, tsakaninmu club din real Madrid’ da kuma Barcelona. Hankali kwance ya cigaba da kallon sa bayan ya amsa sallamar Saifullah, ‘karasawa Saifullah yayi yana gayda mahaifin nasa cikin girmamawa, nan mahaifiyar sa Haj Zuwairah ta shiga parlorn ta zauna, gaishe ta yayi, ta amsa kai a sama, domin batasan ma ta kalli kwayar idanun sa yabata tausayi.

Kai a ‘kasa Saifullah yace da mahaifin sa,

“Daddy wurin ka nazo..”

Juyawa mahaifin na sa yayi ya dube shi kafin yace,

“Ina jinka, meke tafe da kai?!”

Cikin rawar murya kai a ‘kasa yace,

“Daddy a... a... akk...akan maganar Islam ne, na ga kuna fushi dani, dan Allah kuyi hak’uri, in sha Allah bazan kara kamanceceniya haka ba”

Alhaji Faruk ya kurbi tea din dake hannun sa, kafin ya fara yi masa fad’a, ta inda yake shiga, ba ta nan yake fita ba, Sosai yake jan kunnen sa akan laifukan da yayi, ya ‘kark’are da,”

“Kasan meye matsalar ka?”

Saifullah ya girgiza kai alamun a’a. Alhaji Faruk ya murmushi kafin yace,

“Zargi, kana zaton abun da ba haka yake ba, Allah mad'auka kin sarki yana cewa,

[30:22] ومن آياته أن خلق لكم من أنفسكم أزواجا لتسكنوا إليها وجعل بينكم مودة ورحمة ۚ إن في ذلك لآيات لقوم يتفكرون

And (one) of His Signs (is this), that He has created wives for you from among yourselves that you may find peace of mind in them, and He has put love and tenderness between you. In that surely are Signs for a people who reflect.

“Kuma akwai daga ayoyin sa, ya halatta muku matan aure daga kan ku, domin ku samu nutsuwa a gare su,kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakanin ku, Lalle wannan alama ce ga mutane masu tuba/hankali.,

“Sannan akwai wata ayar cikin suratul hujrat aya ta 12, inda Allah mad’aukakin sarki yace, Ya ku wa’danda kuka yi imani, ku nisanci abu mai yawa na zato, Lalle sashen zato laifi ne,

“Lalle zato shine ake nufi da zargi a addinin musulunci, idan har miji yana zargin matar sa da yin wani shu’uminci, kuma bai dai na zargin ta ba, to anan ba’a ma bukatar sai miji ya furta kalmar saki, rabuwar aure ta tabbata a gare su, Imamu Abu Dawooda ya rawaito cewa; Manzon Allah SAW yace: haramtaccen abu wanda Allah yake qi shine saki (divorce), Don haka idan har zato ya shiga cikin aure, to rabuwa tafi amfani, domin zargi yanada illa sosai da sosai, Toh Allah yasa mu dace, ya kuma ‘debe mana munanan zato daga zukatanmu...”

Gyaran murya Alhaji Faruk yayi, ya ‘kara sipping tea 'dinsa kafin ya mai da duban sa ga Saifullah, cikin muryar umarni yace,

"Yanzu ba sai anjima ba, Ina so ka rubuta takardar sakin Islam, ka bani. Ga biro nan a kusa da kai, Ungo nan ga paper, rubuta ka bani.."


Dai-dai lokacin da Saifullah ya 'dago a razane yana kallon mahaifin sa, A dai-dai lokacin a 'bangaren Islam kuma, wayar tace tayi 'kara, a razane ta jiyo muryar Saifullahi cousin dinta yana sanar da ita...........

*****

XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽





_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_*
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 67_*

_nanahafsat.wordpress.com_

‘Difff...... Numfashin Saifullah ya ‘dauke, wata razananniyar ‘kara Islam ta saki tana ‘dora hannuwa akai, Alhaji Faruk ya kira Mami ta janye Islam. Su kuma shi da Aji Mommodu suka ‘dauki Saifullah kamar gawa aka ‘dora shi akan kujera, ruwa aka yayya fa masa amma ko motsi ba yayi, Haj Zuwairah sai kai da komowa take yi a parlorn, tana adduar Allah ya tashi kafad’un Saifullah, ahankali numfashin sa ya dawo amma iya ciki kawai, cikin gaggawa suka ‘dauke shi sai asibiti, dayar motar kuma Haj Zuwairah ce da Islam sai Fatima yayar Saifullah itama da tsohon ciki, haihuwa ko yau ko gobe. Ana shigar da shi asibiti likitoci sukai kansa, suna bashi temakon gaggawa, ai kuwa da taimakon Allah da oxygen da aka sanya masa yafara numfashi normal, amma jikin nasa is weak, Dr Jalaludden, shine likitan da ya duba Saifullah, a tsaye ya samu su Daddy sunyi cirko-cirko, Islam kuma na daga can baya ta kifa kanta tana kuka, Dr jalaludden ya nufe su yana murmushi, Aji Mommodu yai hanzarin cewa,

“Dr ya jikin Saifullah, ya farfad’o kuwa?”

Dr ya zare face mask din dake hancin sa kafin yace,

“Alhamdulillah ya farfad’o, sai kuyi wa Allah godia, dan gaskia condition dinsa bamu saka ran numfashin sa zai dawo normal ba, saboda sanda kuka kawo shi har ya shiga coma stage, Toh kuma dai Masha Allahu, numfashin sa yadawo normal, amma acikin ku waye mahaifin sa? Inaso muyi magana ne..”

Aji Mommodu yace,

“Nan duk iyayen sa ne, waccen yayar sa ce, ta ‘k’arshen can kuma matar sa ce.”

Ya ‘karasa fad’a yana nuni da su Fatma da Islam. Likita yace,

“Allah sarki, Toh idan ba damuwa inason muyi magana da ku biyu mazan.”

Kad’a kai su kai, suka bi bayan sa har ofishin sa, guri ya basu suka zauna, kafin shi ma ya zauna yana duban su da kyau, sannan ya fara magana da,

“Toh kamar yadda na fada muku Saifullah yana cikin critical condition gaskia, jinin sa ya hau da yawa, sannan akwai alamar dimbin damuwa atare dashi, ba ma wannan kad’ai ba, harda chronic ulcer. Garin yaya kuka bar matashi haka da wa’ennan tarin cututtuka dake barazanar ‘karar da rayuwar sa akoda yaushe?”

Aji Mommodu ya dubu Alhaji Faruk, sukai kallon kallo, kafin Alhaji Faruk yace,

“Hau hawar jini fa kace likita...?”

Dr Jalaludden ya jaddada kansa alamar tabbatar da zancen da ya fada hakan yake. Aji Mommodu yai ajiyar zucia kafin yace,

“Amma likita a iya sanin mu babu wani abu da yake damun Saifullah, da har zai sanya kansa cikin damuwa haka..”

Alhaji Faruk ya girgiza kansa yana kallon agogon hannun sa, kafin yace.

“Toh ko zancen Islam ne?”

Dr Jalaludden yai hanzarin cewa,

“Wacece ita Islam ‘din?”

“Matar sa ce, wadda muka nuna maka ita a waje...” cewar Aji Mommodu.

Dr Jalaludden ya jaddada kai kafin yace,

“Ko zan san meyasa matar sa ta zama wani ‘bangare a sashen shiga matsalar sa?”

Alhaji Faruk ya hangame baki zai magana, Aji Mommodu yai hanzarin cewa,

“Da akwai y’ar matsalar da aka samu ne, shine muke tunanin rabuwar su zai fi, akan suci gaba da zama a inuwa d’aya..”

Dr Jalaludden yai shiru, yana kallon su, ya cire biron dake bakin sa, Daga kai yayi sama, kafin ya sake mai da duban sa gare su yace,

“Shin matsalar babba ce da har kuke maraba da ita? Yaron ku ya kamu da rashin lapiar dake barazanar farautar rayuwar sa, why.. why?”

Daga Aji Mommodu har Alhaji Faruk shiru sukai, suna raba idanuwa, dr Jalaludden ya saki dan karamin tsaki, kafin ya sake cewa,

“Toh ni dai abun da yasa na kira ku kenan, idan da hali dai ku ba shi matar sa pls, idan lefi yayi ku ke neman hukunta shi haka kuyi hak’uri dan Allah, rayuwar yaron ku itace gaba da komai agare ku yanzu, kuyi tunani akai Alhaji..”

Yana gama fad’a ya mike yana duba agogon dake daure a wutsiyar hannun sa, kafin ya sake cewa,

“Bari na koma wajen sa, maybe ko ya farfad’o.. Excuse me pls”

Cewar dr Jalaludden ya fice, rataye da stethoscope. Aji Mommodu ya dubi Alhaji Faruk, su kai kallon kallon, ‘Ina mafita?’. Alhaji Faruk yai ajiyar zuciya kafin yace,

“Ya kake ganin za’ai, an ya idan muka tilasta yarinyar nan bamu cuceta ba?”

“Gaskia kam, sai ya d’au dangana, komai ‘dan hak’uri ne, dama ba komai da kake so kake samu ba, akwai hills and valleys a rayuwa.. Allah ya zabi ahunda yafi alkhairi..”

Cewar Aji Mommodu, ya fad’a yana jinjina kansa, Alhaji Faruk yace,

“Kwarai kuwa, zab’in Allah shine mafificin alkhairi.. Muje Modu..”

Mikewa sukai, suka fita.. Yadda suka bar su Haj Zuwairah haka suka gan su yanzun ma, Islam still kanta a ‘kasa, Dr Jalaludden ya fito yana zare safar hannun sa, kafin yace.

“Toh.. Alhamdulillah, Saifullah ya farfad’o and yana tambayan wata Islam, so please Islam taje kafin mu san matakin da zamu sa shi a kai..”

Haj Zuwairah ta dago Islam itada Fatmah, zasu shjga ‘dakin dr Jalaludden ya girgiza kansa, alamun a’a, kafin yace.

“Mama kuyi hak’uri, Islam first,before anything else..”

Jaddada kai su kai, suka ja baya, ita kuma Islam ta shiga dakin gabanta na tsananta fad’uwa, ido hudu sukai da Saifullah, ya miko mata hannun sa a hankali , dr Jalaludden dake kallon su yai wani shegen murmushi, kafin ya janyo musu ‘kofar ya kulle..

‘Karasawa tayi, taki kallon sa bare hannun daya ke miko mata, ta mai da kallon ta ga window, a hankali tace,

“Ya jiki?!”

“Da sauki..”

Ya furta can ‘kasan mokoshi, kallon sa tayi, idanuwan su suka sarqe dana juna, ta ‘dauke da sauri saboda kwarjinin da yai mata, shi kuma ya shagala da kallon ta, mikewa tai zata fice ya rik’o hannunta, murya ‘kasa kasa yace,

“Please stay...Please...Islam’”

Mutuniyar ku har cikin magudanar jininta taji dad’in yadda ya furta sunanta, ya ja laaam ‘din kamar wani balarabe, dan bata rai tayi kafin tace,

“Me zan maka ne?”

“When you leave, I swear I can't breathe, Do you really care Islam?”

Kwace hannun ta tayi, zata gudu yai saurin jan mayafinta, luu tafada akan sa, baiwar Allah ta shiga neman kiciniyar kwace kanta, mutumin ku ya hana, ya kara mannata a jikin sa, yana shakar kamshin jikin ta, tsoro ya kama Islam jin saifullah na ajiyar zucia, zata tashi ya sake damke ta ajikin sa, cikin kunnenta ya shiga rad’a mata,

“Please calm down, gimme just 3mins..”

Shiru Islam tai, tana lafe a kirjin sa, jin kamar za’a turo k’ofa ya sa ta, saurin kwace kanta, suka shiga kallon kallo, ya saki lallausan murmushi, ta yatsina fuska tana kallon gefe kafin tace,

“Kar ka sake yi wa matar wani haka”

“Matar wani kuma?”

Yafad’a yana ware idanuwa, jaddada kai tayi alamun da gaskiyar ta ta fadi haka, murmushi kawai yayi, kafin ya sa hannu ya dafe saitin zuciyar sa, cikin lumshe idanuwa yace,

“Kece maganin zuciata Islam, I love you more than life itself. Pls kakki bari a raba auren mu Islam, nasan ada nayi kuskure amma wallahi yanzu na gyara, fiye da tunanin ki. Dan Allah ki bani last chance...Kinji?”

Yatsina fuska tayi, duk da har cikin zuciar ta takejin dad’in kalaman sa amma afili kuwa kemad’agas tayi, tamkar bata sauraren sa, adai-dai lokacin akai knocking, Dr Jalaludden ne ya shiga shi da su Mami.....


________

XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽


DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 64-66_*

_GAISUWAR BAN GIRMA GARE KI *TAWAN (BILLYN ABDUL)*,LITTAFIN SAIFUL_ISLAM, GABA ‘DAYA TUKWICI NE AGARE KU KE DA (YA HAJJA CE), FATAN ALKHAIRI A GARE KU KE DA UNCLE ABDUL👏🏻, INA MIKI SON SO FISABILILLAHI, TUN WHATSAPP BA KALA😹ALLAH YA BARKI DA UNCLE ABDUL ABADAN DA’IMAN, KI DAD’E KIYI ‘KARKO UWARGIDAH/AMARYA🥰SHAFIN YAU NA KI NE TAWAN💙, KI SHALLARA SHI DUK INDA KIKE SO😹🤲🏻❤🥰_

_nanahafsat.wordpress.com_

*A* razane Islam ta jiyo muryar Saifullahi cousin ‘dinta yana cewa,

“Hello Islam, dan Allah number DOCTOR SAMEER AMEER( littafi na) malamin physiology ‘din ku zaki bani, Kinga an kai Nusrah ne zata haihu a asibitin sa, Kuma wai baya kusa suna meeting ne, ni kuma bana garin, yanzu haka ina kaduna naje duba nuraddeen ne, Wai duk nurses din tsoran kiran sa suke yi, ni kuma da inada number ‘din sa, amman babu yanzu. Dan Allah ki turo min please, tunda shine level coordinator d’inku..”

Cikin rawar murya, cike da tausayawa halin da Nusrah take ciki. Tace dashi,

“Eh shine, Bari na turo maka, Allah ya sauke ta lapia. Ameen!”

Cike da hanzari ta nemo number a contact’s log ‘dinta, ta tura masa, bakin ta ‘dauke da adduar Allah ya sauki yayar ta ta lapia.

‘Bangaren Saifullah kuwa a razane ya ‘daga idanun sa yana kallon mahaifin sa, cikin rawar murya yace,

“Saki? Daddy saki fa kace.”

Ya fada a ‘dan razane, jaddada kai Alhaji Faruk yayi alamun tabbacin da gaske yake, cikin rawar jiki Saifullah ya ‘kara matsawa kusa da mahaifin nasa, yasa hannuwan sa duka biyun yana rik’o ‘kafafuwan mahaifin nasa, sai kace mai neman gafara, gaba d’aya ko Ina ajikin sa rawa yake, tamkar mazari na kad’a shi..Cikin rawar baki yace,

“Dan Allah Daddy kuyi hak’uri, hukuncin ku yayi tsauri, wallahi wallahi Daddy bana zargin Islam, kafin muyi aure ne dai tunda na gan ta a bakin wani joint, shi... shine zucia ta take zaton ko bata jin magana ne, amma Allah bayan nan Daddy wallahi ban ‘kara zargin ta ba, ko dana ganta a school dinsu da wani thou nasan shi a wani wajen, Allah banyi mummunan zato akan haka ba, kawai dai bana sakar mata fuska ne, wai ko rashin sakin fuskar zai sa ta hankalta ta de na, k...”

Kafin ya ‘karasa Alhaji Faruk ya ‘daga mai hannu alamar ya dakata, cikin yatsina fuska yace dashi,

“Daga ganin sarkin fawa sai miya tai dad’i? Kenan daga ganin ta a bakin joint sai kai mata kallon mummunan zato? Wallahi kabani kunya Saifullah, da ilimin ka da komai kake jahiltar abu? Wannan wane irin duhun kai ne da kai? Meyasa da kake zaton hakan baka same ta ka tambayeta ba? Sai kabar abu acikin ranka kana muzguna mata, shashasha, sakarai, sullutu kawai, wanda ilimin sa bai ‘kare shi da komai ba sai bakar zucia da duhun kai. Sakar min kafa ni, kafin nasa d’aya na ham’bare ka.”

Saifullah yaja baya a hankali yana zare hannuwan sa daga kan ‘kafar Alhaji Faruk. Cikin muryar tausaya wa yace,

“Abba dan Allah kuyi hak’uri, wallahi wallahi Ina son Islam yanzu, da ‘dinma shed’a...”

“Kar kayiwa she’dan sharri Saifullah, wallahi wannan wata aqidar kace ta daban, andeji kunya wallahi, Allah ya kyauta”

Cewar Hajia Zuwairah, ta ‘karasa fada tana zabga masa harara. Shi dai Saifullah hak’uri kawai yake ta basu, gaba d’aya bashi da kuzari, ambaliyar hawaye ne ke reto a kyakkyawar fuskar sa na nadama da dana sani, cikin haka Islam ta fito daga ‘daki, batasan da zuwan Saifullah ba, kusa da Haj Zuwairah ta xauna daga ‘kasan ta, kafin tace da Alhaji Faruk kanta a ‘kasa,

“Daddy barka da rana..”

Murmushi kwance akan fuskar sa yace,

“Barkan mu Islam, kina Lapia?

Kanta a ‘kasa tace,

“Alhamdulillah Daddy..”

Saifullah ya zuba mata idanuwan sa yana kallon ta ‘kasa-k’asa, ta dauke kai kuwa hade da shan kunu, dan karma ta gaishe shi, Haj Zuwairah ta dubeta tana fadin,

“Auta, na zo ne?”

Cikin rad’a rad’a islam ke cewa da ita,

“Mami dama sis dina Nusrah aka kwantar a asibiti, yanzu naga anata maganar a family group ‘dinmu, condition din nata is critical, kuma dama kafin nan ma Ya Saifun gidan mu yakira ni neman number Dr Sameer malamin mu an kai ta asibitin nasa.”

“Ayyah.. Allah ya sauke ta lapia, itace matar Saifullahi ko?”

“Eh...”

Ta bata amsa kanta a ‘kasa, Mami ta mai da dubanta ga Saifullah da ya mai da Islam tamkar television, gaba d’aya hankalin sa da nutsuwar na kan ta, cikin tabe baki Mami tace dashi,

“Kai..”

Daga kai yayi yana dubanta, alokacin kuma Alhaji Faruk ya mike ya bar wajen yana waya, cike da muryar tausayawa Saifullah yace,

“Na’am first love.”

“Auta ta, zata je asibiti dubo yayar ta.”

Kansa a ‘kasa yace,

“Toh first love..”

Ganin Islam ta shiga ‘daki, ya sashi mikewa jiki ba ‘kwari yace,

“First love na tafi..”

“Allah ya raka taki gona..”

Kawai Mami tace, ta mai da duban ta ga tv dake nuna shirin ‘sons of the caliphate’. Fita yayi ya shiga mota ya tayar da ita, ya fita daga gidan yai parking daga nesa daga gidan, alokacin Islam kuma ta fito da tata motar, da sauri ya tsaida ita, kamar ba zata tsaya ba sai kuma ta tsaya, buda gaba yayi ya shiga, wani kallon wulakanci ta jefa mai, kafin tace,

“Malam ya haka?”

Bai amsa taba, sai wani botton daya danna kujerar sa tayi baya, ya kwanta yana lumshe idanu, tsaki ta saki, ya dago yana duban ta, a hankali kamar mai rad’a yai nuni da bakin ta yana cewa,

“Clean that shit..”

Kamar zatai kukai, haka tayi rau-rau da idanuwa, kafin tace,

“Vaseline ne fa nasa, lips dina naturally red ne.”

Tab’e baki ya yi, ya koma ya kwanta yana fad’in...

“Do you believe in love?!”

Shan kunu Islam tayi, ta cigaba da driving ‘dinta, har suka kai asibiti yana zuba mata magana amma bata tanka shi, ita mamaki yake bata ma, dama yana magana haka?! Tana shirin zare mukullin yai hanzarin rik’o hannun ta, cikin muryar na dama ya fara mata magana,

“Bilkisu... Dan Allah ba dan ni ba kiyi hak’uri, kinji?”

Ya shiga murza hannun ta, ta kwace tana dankara masa harara, kafin tace,

“Wanda ka keso shine idan ya maka laifi kake adana shi a kundun zuciya, Saboda haka zargi na da kakeyi ni wallahi ko a jiki na, zaman takarda ta nake yi, domin ashirye nake na au...“

Rufe mata baki yayi da hannun sa dake tashin ‘kamshin Black oud, lumshe ido tayi tana shak’ar ‘kamshin, cikin rok’o ya fara mata magana,

“Dan Allah Islam, ba dan ni ba, wallahi wallahi Allah ya jarabce ni da son ki, So mai tsanani, nasan nayi lefi a baya, amma inaso ki ‘dau hakan ki ajiye a matsayin sharrin shed’an, wallahi ba wai zargin ki nake da aikata fasiqanci ba, a’a wallahi, kawai kishi ne, idanuna sun rufe, Believe you me bilkisu, wallahi da gaskiyata nake miki magana.”

Ya karasa fada yana langabar da kansa, agogo ta kalla, kafin ta gyara ‘daurin ture kaga tsiyar dake kanta tace,

“Ka gama?”

Ya kad’a kai kamar kad’angare, ta kalle shi ta watsar kafin tace,

“Toh fita zan kulle mota ta..”

Kamar yaron ta haka yafito yana raba idanuwa, a hankali ya furta,

“Why do I feel so suffocated?”

“Kace me?”

Cikin hanzari ya kad’a kansa yana saurin cewa,

“Ban yi magana ba.”

“Fine..”

Tace kawai, tasa motar ta a key, tai shigewar ta cikin asibitin,

Saifullah ya tsaya ‘ki’kam kamar wanda ya had’iye muciya, tunawa yayi da mahaifin su bai sallame shi ba, da sauri ya tafi titi ya tsare cab/taxi. Yana shiga gidan su kuwa gaban sa ya cigaba da fad’uwa, ganin harda motar Aji Mommodu mahaifin Khaled, addua yake ta faman yi kar Daddy ya tambaye shi ina da ya tafi?

Bai rufe bakin sa ba kuwa, Alhaji Faruk yai gyaren murya kafin ya dubi Saifullah dake raba idanuwa, kamar daga sama Saifullah ya jiyo muryar mahaifin sa ta doki kunnen sa da,

“Ina kaje kuma? Daga tashi naje nai waya na dawo mahaifiyar ka tace kace mata ka tafi?”

Saifullah ya sa hannu ya sosa ‘keyar sa, kafin yace,

“Na.. Naje nan bayan layi ne, wurin wani aboki na..”

“Madalla, Ina abun da nace ka rubuta?mikomin sauri nake yi.”

Saifullah ya sunkuyar da kansa, ya sake matsawa can kusa da mahaifan nasa, kamar zai shiga cikin su, ya fara kwararo magiya gwanin tausayi ya ‘kar’kare da,

“Daddy wallahi tallahi ba wai ina zargin ta bane, ko sanda naganta a Lagos ai lokacin ba aure a tsakinmu Daddy, kawai...Kawai nayi kuskure Daddy, Baba ka sa baki please, wallahi Allah na cancanci kowanne lefi fyace na saki, ba .. baz..Bazan iya rayuwa ba ita aciki ba Baba..”

Aji Mommodu yaja majina, yana kara kwakula tissue a hancin sa, kafin yace,

“Wacece kuma ita...”

Cikin rawar baki Saifullah yace,

“Matata... Ita Islam ‘din, dan Allah Baba, wallahi Allah ina sonta yanzu, ko da dinma sharrin shedanne..”

Sai faman zance yake zubawa, kamar sabon tabin hauka, Aji Mommodu yai ajiyar zucia, kafin yace.

“Toh Masha Allahu! Bi sa ga shawarar da mukai, mun yanke hukuncin Is...”

Bai ‘karasa ba, Saifullah ya riko k’afar sa yana rokon sa da,

“Baba dan Allah kakka ce na rabu da islam, wallahi I truly love islam, with all my heart and soul.”

Tsaki Daddy ya saki yana mikewa, can dispenser yaje ya tatso ruwan sanyin sa, ya koma ya harde kafofi . Aji Mommodu yayi murmushi kawai yana sake maida duban sa ga Saifullah daya makalkale masa kafa, cikin muryar umarni yace,

“ba zamu yiwa yarinyar tilas ta koma gidan ka ba Saifullah, kaga auren had’i aka muku, ba wanda ke son ‘dan uwan sa, yanzu kazo da maganar kai kana sonta, ta iya yiwuwa ita har yanzu ba ‘digon son ka azuciar ta, Saboda haka babu tilashe a zancen komawarta ‘dakin ta, id...”

Be karasa ba Islam ta shigo parlorn bakin ta dauke da sallama.. dake parlorn idan zaka shjga ko fita dole seka bi tashi, tsugunnawa tayi tana gaishe su, Aji Mommodu yace ta zauna dama yanzu yake shirin aikawa a kira ta, murmushi fad’ad’e akan fuskar sa yace,

“Islam..”

Kanta a kasa tace,

“Na’am, barkan ku da yawwa”

“Barkan mu..”

Daga haka, Aji Mommodu ya shiga labarta mata komai kan yadda sukai da Islam, kuma zab’i suka bata, idan tanaso ta koma ruwan ta, idan bataso nanma ruwan ta, Saifullah sai jifanta yake da kallon ‘karki min haka’ , ta ‘kasan ido suka had’a ido ta zabga

Please Login or Register in order to submit comment