Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kishin su na ilimi suke yi, babu hayaniya sai dai ayi gogayya ta nuna fini da kaza na fiki da wannan, sai ‘dan abunda ba’a rasa ba na gutsiri tsomar yau da kullum, Yaya Bala ‘ya’yan sa goma sha biyu,hudu daga ciki mata ne wanda dukkan su sunyi aure Nadia cema bata jima dayi ba.

Wanda sauran takwas d'in duk maza ne, biyu daga ciki sunyi aure, hud'u daga ciki agidan Dr Kabeer suke da xama, biyu na aiki a company din baban su na canji wato mudasser da mu’utaseer, biyun kuma d’aya banker ne anan zenith bank wato kamaluddeen dake abujan sai saifullahi dake lecturing a baze university, lecturer ne na Mbbs wato medicine.

Sauran hud'un kuma d’aya na lagos mubassheer kenan mijin Safa 'yar gidan Haj Aysa, da Shamsudden sune a lagos, Nuradden kuma yana aiki a kaduna, sai engineer najibulla dake kasar Manchester yana aikin wani company wanda shine mijin Marwa 'yar gidan Haj Aysa..

Toh abun dai sai sam barka kawai, amma wasu daga cikin iyaye mata na mazajen su Safa basu so auren ba, Haj Halima da Haj Nafeesa, hak'ik'anin gaskia saboda wani kuduri nasu na daban,

Inna Bilkisu zaman ta ya koma hannun Yaya Bala, tun mutuwar mijin Hansa’u kanwar su Dr Khaleel. Ya rasu ya barta da yara biyar wanda uku daga ciki maza ne biyu kuma mata ne.

Akwai Shema’u, wadda ta canxa sunanta xuwa shamie baby, acewarta wancen sunan yan kauye ne, da tana da wayo akai rad'in sunan ma da babu abunda xai hanata canxawa, sai Aysha wadda akewa laqabi da sholey, sai mazan Kabeer Kb, da Khaleel wanda yaci sunan Dr Khaleel ake ce dashi Ibrahim sai autan su Yusuf.

Gaba d’aya sai Inna Bilkisu da Hansa’u zaman su ya koma lagos wajen Yaya Bala, tuni ya k'ara fad'ad'a gidan sa ya yanki fili anan unguwar Maryland aka yiwa mahaifiyar tasu gidah ,ciki harda sashen Hansa’u ita da ‘ya’yanta aciki.

Gaba d’aya ‘ya’ya mazan Hansa’u su ukun zaman su ya koma gidan Dr Khaleel, matan ne kawai ke zama anan lagos, amma duk hutun dunia agidan Dr Khaleel din suke yinsa, da sun kafa k'ahon zuk'ar sai sun koma can saboda kulaficin son maza ne dasu, amma Inna Bilkisu tace bata yarda ba, babu wanda xai koma, ai wahalar sai tai masa yawa, duba da yadda ‘ya’yan 'yan uwa kowa sai yai kaura ya koma can, suna dandalar arziki ganin hannun Dr Khaleel din a sake yake, komai zaiyiwa ‘ya’yan sa to fa harda sauran ‘ya’yan yan uwan yake sawa dukkoda yawan su haka yake yi, sam baya gajia, Shiysa Allah yake dad'a bud'a masa harda Yaya Balan da ya kara manyanta, yawanci 'ya’yan sane ke tafiyar da harkar canjin da saurin kamfanonin sa, toh abun dai sai sam barka kawai..


*B* *N* *A*

Shirye-shiryen jarabawar k'arshe ta ajin sakandire na d’aya suke yi, wanda xasu shiga babban aji na biyu, wato SS2, gaba d’aya kowa karatu yake yi sosai, sanin dokar makarantar ce duk wanda baiyi abun arziki ba a jarabawar to option biyu ne, kodai ka sake maimaita ajin baya, ko kuma ka rungumi k'addarar kowa ne rukuni suka maida ka daga cikin Art ko commercial studies.

Shiga d'akin k'awar su wato Fatima Bichi tayi, tana sallama sai kuma taja dogon tsaki bayan ta zauna kusa da Islam, dake d'auke da timemen text book na chemistry tana karantawa.

“Ke dawa kuma?!” Cewar Islam tana kara gyara zaman medicated glass d'inta,

Kara sakin wani tsakin tayi, tana murgud’a-murgud’an baki ita kad'ai, Hafsat Rano dake gefe tana karatun biology ta dawo kusa da Fatima da sauri saboda tsabar son jin wacce gulmar tazo musu da ita,

A karo na ba’adadi Fatima ta sake sakin wani tsakin, Lee dake gefe haushi yakusa kasheta kamar ta tashi ta shak’o Fatima haka takeji, ai kuwa a fusace ta taso tana dalla mata harara, duk kuwa da idan masiface da fad'a Fatima ta kere mata, amma dan karfin hali irin nata da neman fad'a na Lee cewa tai,

“Dalla zarah menene?! Haba kinata mana tsaki, mu ba dangin tsaka ba, Idan Kinsan babu abinda zaki fad'a gwamma kawai kiyi shiru, kilan dai ta kuce ta had’o ku da wannan saurayin naki.”

Harara Fatma ta makawa Lee kafin ta watsa masu wasu papers na test d'in Fishery da sukai da safe, cike da fad'a ta fara magana,

“Walahi uncle Bilal ya mugun raina min hankali, dan tsabar son kai shine ku duk yabu 10 marks amma ni 9 and half (½).

Tsaki Hafsat Rano ta saki tana mikewa tsaye, dungurewa Fatima kai tayi tana dariya,

“Kin rainawa kanki hankali, yadda kike hakikan cewa kina faman huci dama half Mark ne kawai?.”

“Ware dalla.” Cewar Fatma.

Duk shiru 'yan d'akin sukai kowa yana kallon paper d’insa, Islam sai murmushi takeyi tana bin paper d'inta da kallo kafin cikin harshen kanuri tace,

“Ala kambo, Álà àlààlánjú cəd̀ əń à”

“Zagi na kikai ko Lam lam?”

Kyalkyalewa Islam tayi da daria tana kallon Fatma,

“Haba Zarah, a’a walahi, Allah kawai na yiwa godia wallahi, meyasa xan miki daria? bayan kema kin cinye, half Mark ne kawai babu fa, kuma kinsan dama Uncle Bilal ya gano ki kuna musu da Ishaq, kuma kinsan yace duk wanda yai surutu minus half mark..”

“Ohh...! About that, shege mai kan kwakwa, anyways nima dai Miyetti Allah(Nagodewa Allah da yaren Fulani)”

Daria sauran suka kwashe da ita, kafin suyi dif kuma, sanin halin fatma yanzun saita sa mutum kuka, sake sabon zama na serious discussion suka yi, banda Hafsat kanwar Islam dake can wajen Hilal suna tab'e-tab’en da suka saba yi.

Abun ba’a cewa komai, sai dai muce Allah ka shirya mana zuri’armu,








_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_🧕🏼
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
*ASY KHALEEL💕*


*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*😻
*BILLYN ABDUL*🌹



*SHAFI NA GOMA SHA D’AYA(11)*


_Wannan shafin na kune sisters, sis FAREEDAH MUHAMMED ABBAS &, DR TEEMAH GABS, fatan alkhairi agare ku, ina jin dad’in yadda kuke bibiyar wannan littafin, jazakum Allah bil jannah💕_

nanahafsat.wordpress.com

Muguwar harara ya zabga mata, kafin ya d'auke kansa ya mayar kan littafin da yake karantawa, gaba d’aya yarinyar nan yak'i jinin ganin ta a rayuwar sa, da wani k'atin-‘katin' idanun ta kamar na haihuwa,

Itama saurin d'auke kanta tayi tana mai da shi gefe,

“Ashe shine yasa zuciya ta take ta bugawa?, no wonder” Islam ta fad'a a zuciyar ta saboda sam basa jituwa dashi ya fiye wulak'anci.

Delman na packing suka sakko dukkan su, gayshe da Saifullahi kowaccen su tayi ya amsa da fara’a amman banda gaisuwar Islam.

Har sun fara tafiya ya kira sunan ta, tana ji, taki juyawa saboda ba sunanta ya furta ba duk da sabonsa ne cewa ke.

“Ke!” Ya sake kiran ta, yana mik’ewa daga zaunen da yake ya tsaya dan ganin zata wuce ko zata tsaya.

Kamar ba zata juya ba sai kuma ta juya, Ganin haka yasanya Hafsat yin murmushin mugunta, shi yasa take k'ara mutunta saifullahi saboda shima ya tsani Islam. Duk wata bola idan ya kwaso a kanta yake zubawa, tai ta dafa musu indomie shi da abokanan sa idan suna gida, bayan ga masu aiki.

Cikin gidah Hafsat da Hidaya su kai wucewar su, kowacce janye da d'an akwatin ta, suka bar Islam da Saifullahi dake faman cin magani kamar tayi masa laifi.

“Wato ga tsaran ki na miki magana ko? Shine Ina kiran ki, ki kai mun kunnen uwar shegu ko? Ke wai ni sa’an ki ne..ne? Ko kuwa dan kinga kin fara girma shine ki ke neman raina ni?” ya k'arasa fad'a yana nuni da k’irjin ta.

“Dan iska..” Ta fad'a a hankali yadda baxai jita ba,

“Kika ce mene?”

“Ni ba fa da kai nake ba Ya Saifu”

“Ku dama yaran nan da kun fara nonuwa ko ina yana cika, sai kuma rashin kunya ya fara biyo baya, get lost, wawiya kawai!”

Tunda ya fara magana, kanta yake a k'asa, ta lura tun ba yau ba Ya saifu d'an iska ne, maganar sa kenan ta kirji da mazaunan mata, a baya kwaila yake kiran ta, yanzu kuma yaga ta zama 'yan mata shine yake faman tankata,

Da sauri tai wucewarta itama zuwa ciki, tana mamakin wannan tsanar da yake yi mata ta babu gaira babu wani dalili. Kaf mazan gidan shine ke takurawa rayuwar ta, su dama maxan family d'insu jin kai ne dasu da wani d'agawa, sai kace sune matan, Saifullahi shine mai d'an sauqin kai, dan yana magana dasu Hafsat, tsakanin sa kuwa da Islam sai hantara da bakar magana, duk rashin fad'an ta wani lokacin har mayar masa da martani takeyi saboda haushin wasu kalmomin da yake gaya mata,

Sashen daddyn su ta fara zuwa, tayi sa’a kuwa yana nan, amma shi dasu Hafsat ne, ganin ta yasa Hafsat ta fad'ad'a murmushin ta, tana daga mata hannu, tamkar irin mugun shirin nan suke yi da juna,

“Babe.. Woo mun rigaki zuwa wajen Daddy.” Cewar Hafsat, harda yi mata gwalon wasa.

Murmushi kawai Islam tayi, ita makircin su Hafsat da Hidaya mamaki yake bata, Idan sun dawo gidah hutu sai ka d'auka irin shirin nan suke yi, sam basa nunawa agaban kowa sai dai idan su kadai ne, ko kuma agaban iyayen su amma banda wajen Daddyn su.

“Mamana...” Daddy ya kira Islam kasan cewar haka yake ce mata ganinta ta shigo. Da sauri ta k'arasa ta rungume shi tana murmushi.

“Daddy..” Ta fad'a tana kara matse shi cikin shauki dajin tsantsar kaunar sa a ranta.

“Mamana..” Sakin sa tayi tana gyara xaman ta, cike da murna take cewa,

“Daddy..Barka da rana, mun same ku Lapia?”

“Lapia Alhamdulillah Mamana. Duk sannunku ya studies?” Yace dasu, yana binsu da kallo cike da kauna.

Amsa mishi dukkansu suka yi suna murmushi suma.

“Masha Allahu, to yanzu kuje ciki ku huta, zamu yi magana da safe Insha Allahu. Mrs Thomas tace first week of next month aje a karb'o report cards d'inku ko?”

“Eh Daddy” cewar Islam da Hidaya banda Hafsat da tayi d'if tana tunano rashin k'in mai da hankalin da tayi, ko zata wuce successfully kuwa? Anya?.

Yatsina fuska tayi had'e da tab'e baki alamun ko ajikin ta d'in nan.

Ficewa sukai zuwa sashen Inna Bilkisu, don Daddy ya sanar musu da zuwan ta gidan tare da matan ‘Uncle Bala’. nan ma Islam tayi mamakin makircin su Hafsat, sai dai bata jima ba tai mikewarta ta fice, ganin su shamie baby da su Hafsat sun had’e kai zasu fara zancen batsar da suka saba yi.

Sashen su ta nufa cike da d'oki, tayi murna kwarai ganin 'yan uwanta da 'yan uwan Ammi sun cika gidan, bayan sun gaggaisa da kowa, Islam har kukan farin ciki tayi don dad’in ganinsu, gashi ta mak’ale 'yan biyu a jikinta, sai nan-nan take yi dasu, Idan ta kalle su ji take wani farin ciki na dad’a ratsa ta.

A daren Yakolo ta tsefewa Islam kanta tai mata kitso miri-miri na ‘âccà ngùdìjí’. Wayar Ammi ta d'auka ana mata kitson tana chatting da Lee, wadda itama da numbern Maman ta take yi,

“‘Ha’a àlàmðəḱ kì àlàmðî Islam..”( gyara xaman ki mana Islam) Cewar Yakolo cikin harshen kanuri,

Muskutawa Islam tayi tana cigaba da chatting d'inta da Lee, tana jaddada mata lalle tazo suna da wuri gobe. d'as aka fito da ita har lalle duk suka yi harda su Yaya Marwa gwanin ban sha’awa.

*WASHE-GARI*

*A* farfajiyar gidan aketa decorating wajen sunan, yasha balloons da decoration na baby colors, komai blue. Buffet ne babu kallar abincin da babu. Mai jego tayi shar da ita cikin wani dandatsetsen ubansun lace,

Ga Dj yana ta saka wakoki kala-kala, su Arfat da jikokin gidan ne keta rawa a tsakiyar fili, Islam ce tafi to cikin shigar wani purple lace, tasha kyau harta gaji, domin makeup artist aka dakko musu ta yiwa kowa da yake so,

Fitted gown tasa wadda shape d'innan nata ya kara fita, amma ta bayan rigar sai aka yi shi kamar riga da skirt, ma’ana anyi bayan a hade da wani style ya sakko ya rufe bayanta, shape dai ya fito sosai, tasha d'aurin d'ankwali irin na ‘zarah buhari’.

Gefen gashin ta ma tafito dashi, tayi kyau, gold ta sa amma ba mai nauyi ba barimar hancin ma duk purple ne har frame din medicated glasses dinta.

Wage takalmi tasa, mayafin ta a hannu take nufar hanyar gate dan shigowa da k'awarta Lee, wacce ke zaune a bayan motar da aka kawo ta, ta zuro kafafuwanta waje, tayi kyau itama ba Karya, idanun mazan gidan nan akanta dake zaune a bakin gate, inda suka maida wajen majalisar su,

Fita Islam tayi, ganin su fal awajen ya sanya gaban ta fad'uwa, gashi sun zuba mata idanu kamar wasu mayu, da kyar takarasa ta taho da Lee dake jaddadawa driver lalle ya dawo ya d'auketa karfe 9.

“Mazan gidan ku yan sa’ido ne dasu” cewar Lee tana faman banka musu harara.

“Ignore them kema dai, Kinsan haka suke”

Dai-da xasu bud'e kofar shiga gate Islam taci tuntub’e, shi kuma Saifullahi dake a jikin k'ofa daga ciki ya jingina yana waya, yayi hanxarin taro ta zuwa jikin sa dan ba ta taimako,

Luuu ta fad'a a kan faffad'an k’irjin sa, turaren jikin sa na ‘black oud’ ya sanya ta rufe idanu tana shak'ar kamshin, haka shima khumran data saka ne ya jefashi cikin wani irin yanayi,

Lee dake gefe ta tsaya tana duban su, ganin tunda ya tare ta bata fad'i ba ya saketa mana, itama Islam din banda shegen son jikin ta, ta daga masa kirji mana tayi shiru.

Saurin riko kugun ta yayi yana manne ta ajikin sa, yasha mamaki kwarai jin yadda na shanun ta suka gigita shi,

'Tab! dama haka yarinyar nan take?' Ya fad'a a zuciyar sa, domin duk yadda yake haskalo k'irarta ashe ba hakan bane ta zarce tunanin sa.

Mutsu-mutsu ta shiga yi, Hakan yayi dai-dai da shigowar kiran wayar Lee, dagawa tayi tana barin wajen ganin Mamanta ce,

Saurin jan hannun Islam yai suka koma baya wajen shukoki inda ba idanun mutane shi kansa bai san dalilin da yasa shi yin haka ba, idanuwa a bud'e take kallon sa tana k’ok’arin kwatar hannunta da ya rike yake ja kamar ya kamo mai laifi.

Hannun sa yasa ya kai dai-dai kan......








_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER: MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...💕*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
*ASY KHALEEL💕*


*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*😻
*BILLYN ABDUL*🌹


*SHAFI NA 7-10*


_Wannan shafin na kine daughter ta, momma loves you, more than just to the moon, round and back.. BILLY S FARI,Ilysm❤_


*H*elwa ce zaune a parlorn, da ‘yan uwan Haj Aysa, sai hira ake ana shewa sosai da ita, tamkar ba kishiya ba, domin ita Helwan dukkan su matan dr Khaleel tana basu girman su a matsayin su na abokan zaman ta, don a haife kowaccen su ta haife ta, shiyasa sam bata nuna ita din wai tana d’aya daga cikin matan gidan.

Afrah d’aya daga cikin yan biyun Helwa ne keta tsalle-tsalle a parlorn, sai tsokanar su ake wai yanzu su ba autoci bane,

“Afrah bazaki nemi waje ki zauna bane?! Kina ganin Arfat tayi zaman ta?, Idan ba xaki zauna ba na gaya miki su Abeed da Areef, (yan biyun Haj Aysa) ba xasu dinga ce maki yaya ba,” cewar Helwan, tana sake zare mata idanu.

“Ahh..لن أفعل ذلك مرة أخرى يا أمي”

(Baxan kara ba Ummy) cewar Afrah cikin harshen larabci, sosai suna ji, saboda Helwan shi take yara musu.

Kusada Arfat, Afrah takoma ta zauna, sam Arfat batada hayaniya kamar Afrah, akwai saurin fushi ,amman batada rigima, ita kuma Afrah akwai hayaniya amman batada saurin fushi, ba sufi shekaru hudu ba, amman suna da girman jiki, haka yan dagwai dagwai dasu TubarkAllah,

Suna matukar kama da Islam, sai dai fuskar mahaifiyar su suka dakko, farare ne tas, gwanin sha’awa.

Cikin hakane, a yatsine Haj Karimatu da Haj Yafendo suka shiga sashen Haj Aysa. Wanda kallo d’aya xakai musu kasan dole ce tasa suka je, kowanne fuskar sa ba walwala suka shiga ko sallama ba suyi ba, kamar idan sun yi hakan ne zai nuna farin cikin xuwan nasu,

“Wa’alaikummus salamu”

cewar yakolo ta fadi hakan da biyu, sanin basuyi sallamar ba, itama can d’aya y’ar neman rigima, ko takan ta su Haj Karimatu basu bi ba. suka zauna,

A ciki-ciki suka gaysa da ‘yan uwan Haj Aysaa, amsawa sukai suma cike da basarwa,

Gaishe su Helwa tayi tana dan murmushi, Yafendo ce kawai ta amsa, Banda Haj Karimatu, data sake turo daurin ta gaba, wanda akewa laqabi da ‘ture kaga tsiya’.

‘K’as’ ta sake fasa ‘kwan cingom (chewing gum) tana kallon Helwan cikeda rainin hankali tace,

“Da ban wuni ba kya ganni ne yanzu maman Arfat?”

Ita dai Helwa bata tanka mata ba, jin hakan yasan ya Ya Falmata, gwaggon Haj Aysa cewa dasu,

“Ku shiga ciki, tana ‘daki mai jegon”

“Madalla..”Karimatu tafada, tana mikewa tsaye.

Yafendo na biye da ita suka shiga dakin, a zaune Haj Aysan take tana bawa Areef mama, Abeed kuma yana baccin sa, ganin su yasanya ta gyara xaman ta, tana ‘kara sama da rigar ta,

“Sannun ku da zuwa”

“Yawwa maman biyu..” cewar Karimatu.

Tana ‘kara bin ‘dakin da kallo, ganin irin dukiyar da aka narka a dakin, ashe gaskia Innatu mai aikinta tafada, data kawo mata tsegumi.

“Ga su ko” cewar Haj Aysa, tana k’ok’arin mikewa da Areef.

“Me fa?! Au wai yaran..A’a bar su fa, Muna hango su daga nan”

Bata ce komai ba takoma ta xauna, tana mamakin wannan k’iyayyar da suke nuna mata k’arara.

“Lallai kinyi aiki wai..” cewar Karimatu bayan ta mike tsaye tana leka yaran.

Yafendo ta jinjina kai,

“Gaskia kam, ga sunan narka-narka dasu wai,” cewar Yafendo tana faman karkad’a ‘kafa.

Itade Haj Aysa ba tace komai ba, murmushi kawai tayi, a zuciar ta tana TubarkAllah, hade da neman tsarin Allah daga sharrin su Karimatu.

“Ni watan Safa nawa ne yanzu da koma wa? Ko ta yaye ‘yar tata ma kuwa, zata zo ne ko baxa’ai suna ba?”

“Bansani ba gaskia”

Haj Aysa tafada tana k’ok’arin danne wani abu dataji ya tsaya mata a mak’ogaro, ‘kwarai ranta ya sosu da irin kwandan rashin mutuncin da suke shuka mata,

“To gashi nan dai, sai tazo ta ga ‘kannenta jarirai, bayan shekaru sun ja ancire tsammani ma” Yafendo ta fada tana kallon Haj Karimatu.

“Uhm wallahi fa, haka fa wadda nake baki labari dinnan y’ar uwar mu, gotai gotai da ita fa taje aka sanya mata cikin yan uku ta haife biyu, d’aya yara su”

“Kai haba ana sanya ciki dama?” Cewar Yafendo,

Shiru Haj Aysa ta musu, sarai tasan ita suke yadawa magana, ta tsufa da haihuwa, ciki harda zargin zuwa tai aka sanya mata su, Tsinkayo muryar Karimatu tayi.

“Anayi mana, yo ai yanzu abunda ake yayi kenan, kaje kawai asanya maka, anmanta haihuwa Allah ke bayarwa, amma wasu matan sam ba tsoron Allah a ransu, kallo d’aya xakai wa yaran kagano ba tsatson su bane”

Yakolo dake lab’e a bayan k’ofa tun shigar su ciki tafito da sauri, ta shiga ciki tana binsu da kallon kunyi ‘kadan wallahi, cikin isa da gadara tafara mayar musu da martani,

“Kwarai haihuwa Allah ke bada ita, kuma sharrin da kuke neman ‘kullawa wallahi sai dai ya ‘kare a kanku, haihuwa ce tayi wallahi, sai sam barka, Alhamdulillahi abunda mai gidan yake muradin so, Allah ya cika masa buri ciki harda kamannin sa sak suka zo dashi, kamar yayi kaki ya tofar,ita din dai ta ladan noman, uwar gidan sarautar matan, tushen soyayyar, auren saurayi da budurwa, ita din dai hasken idaniyar sa , sauran duk alakoro ne Walahi, gashi ita Allah yayi arzikin daga gare ta xa’a samu cikar burin, na gaba yayi gaba wallahi..” ta ‘karashe tana huci,

Sam Haj Aysa bataji dadin maganganun Yakolon ba, domin batason ‘yan uwanta suyi musayar yawu da abokanan zaman ta, batada hayaniya shiysa batason tashin hankali, gaba d’aya duk ta rude, kallon Yakolo tayi dake nuna alamun ‘kin kyauta kenan?’

Basu tanka taba, harta fice tabar su, domin Yakolo bata daukar raini ko kadan, sosai take zagewa ta kankarowa Haj Aysa mutuncin ta a gurin su.

Mikewa sukayi jiki a mace suka fice, ko sallama ba suyi da yan parlorn ba, kai tsaye sashen da idan Inna bilkisu tazo take sauka nan suka nufa, dan gaishe ta,

Dama kunsan sashe bakwai ne, d’aya nasa, hudun na matan sa, biyar kenan ko? To dayan na mahaifiyar sa da Hansa’u a tare, sai ragowar dayan inda bataliyar mazan da suke zaune a gidan shine sashen su,

Gaisheda Inna Bilkisu sukayi da Hansa’u, tareda matan Yaya Bala, zama sukai suna ta hira kamar gaske, ciki harda shirga karyar fadan irin kyawun yan biyun da ‘doriyar kullum can suke yini, Inna bilkisu dadi ya isheta jin yanzun suna xaman lapia, sam batasan ‘karairakin su bane,

Mikewa sukai bayan sun gama gaysawa, Nan Haj Haleema tayiwa Karimatu sign din ‘sai na shigo’ da ido, kad’a kai tayi tana murmushi, suka fice.

Da sati ya zagayo, aka sanar da sunayen su Abeed a masallacin gidan, yan’uwa da makota sun shaida hakan, sai dai bikin suna sai sati ya sake zagayo wa xa’ai, wanda hakan yayi dai-dai da dawowar su Islam da kwana d’aya za’ayi.

Da kyar Haj Aysa ta yarda xa tai bikin sunan, acewar ta, ta wuce shekarun da zatai wani shagalin suna gotai-gotai da ita, Sam dr Khaleel yace bai san zance ba, suna kamar anyi angama, ya tsara komai, kayan fitar sunan ma abun kallo ne, ita har tsoro abun ya soma bata.

Tamkar wata budurwa, haka Dr Khaleel yayo mata kayan fitar suna kala kala, designers masu tsada nagani na fada, haka ma yan biyun sa ya shirgo musu kaya, raguna da shanu, su aka yanka akai rad’in sunayen yaran.

‘Abubakhar da Muhammad Tasi’u shine sunayen yan biyun Haj Aysa da aka sanya musu, laqabin su kuma Areef da Abeed xa’a dinga kiran su, kamar yadda Islam ta nemi adinga ce musu.’

Safa tazo tun daga Lagos, hakama Marwa na nan tafe daga Manchester, tace da ita xa’ayi shagalin komai, satin da zai zo na suna xata zo. Tuggu da makirci ciki harda qulle-qullen magani, babu wanda su Karimatu basu tana da ba, jira kawai suke dama tazo, su aiwatar da mugun nufin su.

*B* *N* *A*

Sosai fa kowa kansa na kayuwa, suna zana jarabawar su, banda Hafsat da gaba d’aya gangar jikin ta taxama mallakin Hilaal, sha’anin su suke shanawa kawai, sam bata maida hankali wajen karatun exams din tasu,

A haka suka kammala, hutun wata uku cur aka basu, da jaddadawar kar wanda ya kara hutu, da zarar ya kare an dawo kowa yadawo, koya fuskanci hukunci mai tsanani.

Wata mai kamawa kuma, satin farko kowa iyayen sa yazo taron malamai da iyaye da akeyi wato ‘parent and teachers meeting’ a kuma ranar xa’a bawa iyayen yara takaradar sakamakon da suka samu ‘result sheet’ ko kuwa na maida kai ajin baya ‘repeating’ ko kuwa canxa bangaren abunda ake karanta ‘Field swap’.

Ranar Friday kowa akazo daukar sa daga gidah, su Lee da sauran kawayen Islam kowa suna bankwana da saurayin su, Banda Islam da Kamalu class rep kawai sukai sallama ya tafi,

Sai da Hafsat sukai sha’anin su da Hilal sannan tafito tana wani sussun ne kai, ganin Islam ta gansu lokacin da yake cire hannun sa daga rigar ta, yi tai kamar bata gansu ba, har Hafsat tashige cikin School Bus din da tazo daukar su, Hidaya sai basar da Hafsat takeyi, hade da cin alwashin idan sukai resuming babu abunda zai hanata kula Hilal, sai dai Hafsat ta hadiyi zucia.

Islam da Lee ne sukai hugging juna, da yake su duk a Abuja suke basu wani damu ba, Hafsat Rano da Fatma Bichi ne ‘yan kano. Sallama sukai wa junan su, kowanne ya nufi wajen motar da akazo daukar sa.

Hilal na daga gefen motar da akazo daukar sa yana bin Islam da kallo, a tsorace take duban sa, ya sakar mata wani killer smile yana lashe ‘kasan lips d’insa, Tamkar kamar tsohon maye. Da sauri ta wuce har tana cin tuntub’e.

Cikin luxurious School bus din da akazo daukar su tashiga, can baya takoma ta jingina da pillow abinta,
Harara Hafsat ta maka mata, tana karkada hannuwa alamun jaddada abu,

“Yawwa ke!..Sauran ki kuskura ki gayawa Daddy abubuwan da yake faruwa, wallahi idan naji makamancin haka sai kin gayawa aya zak’inta”

“Okay! ga y’ar iska tana magana da wofi ko?” Hafsat ta sake maimaitawa cike da isa,

Ko

Please Login or Register in order to submit comment