Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakeyi, Ai kuwa da karfi Islam ta ture shi, yaita maza ya hade rai, ya yagi tissue yana goge kan bakin sa, zatai magana ya rigata cikeda borin kunya yace,

“Tun ba yau ba, nake kama ki kina satar kallon lips dina, sai gashi daga gwadawa kuwa kin rike mun lips sai kace kin samu alawa, idan nace ban yafe ...”

Katse shi tayi, tana masa kallon yaushe nai haka? ! Cikin bacin rai tace,

“Ni ce na rike maka lips?”

Ko kallon ta beyi ba ya fice daga wajen corridor yana nanata kalmar,

“So suffocating”


(THE START OF SOMETHING NEW; SAIFUL_ISLAM#LOVE STORY BEGINS🚴🏼‍♀)



_Unedited... Pls do ignore all typos😻_



_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 54-56_*

_nanahafsat.wordpress.com_

Saifullah na tsaye a bakin ‘kofa, yanata ayyana yadda zai sauke wa Islam kwandon rashin mutunci, na barin sa da tayi a tsaye tamkar ‘dan aike. Islam dake baje akan gado tana danna waya ta ajiye ta a gefe, jin knocking din da yake ya isheta, cikin turo baki gaba ta nufi hanyar ‘kofa domin bude masa, gaba d’aya ta ‘dauki darasin Lee a kanta, chewing gum ne a bakin ta, tana taunawa. Sanye take cikin wata shegiyar rigar bacci armless. Gaba d’aya santala-santalan cinyoyin ta sun bayyana a waje, domin rigar shara-Shara ce, ‘kirjin ta kuwa tamkar zai fito ta gaban rigar tsabar kamata da tayi.

A yangance ta bude ‘kofar tana yatsina fuska, Saifullah dake shirin zubo mata kwandon masifa, ya bude baki kenan zai yi ya kasa, ganinsa da jinsa sai suka tsaya cak akan siffar Islam. Bin ta yake da kallo, kamar ‘dan ‘kauye yazo birni. Yana ‘kissina abubuwa da yawa a zuciar sa. Tabe baki Islam tayi, ta wuce abunta tana juya mazaunanta, wani kakkauran yawu Saifullah ya hadiye, irin na kwadayin abun da kakeso aka hanaka ‘dinnan. Har ta koma daki bai dena kallon taba, tundaga saman ta zuwa ‘kafarta. Jiki ba ‘kwari Saifullah ya kullo ‘kofar. Dakyar ya hau sama yana hawa kowanne matattakalar bene yana bin dakin Islam da kallo. Ji yake wani abu na ingiza shi, kan yaje gareta amma ya kasa.

Islam kuwa tana komawa ‘daki, ta shiga bawa Lee yadda sukai ta WhatsApp. Take bacci ya ‘dauketa bayan ta yi alwala ta sauya wani kayan baccin, Don dama wannan tasa ne don tsokano Saifullah, Saifullah dake sama kuwa ya nemi bacci a idanunsa ya rasa. Yayi sallolin nafilfili da addu’oi, amma sam bacci yak’i ‘daukar sa. Daya rufe idanu siffar Islam kawai yake gani, Wani sabon yanayi yaji yana shiga jikin sa, tunani sosai ya shiga yi, cikin haka kuwa bacci ‘barawo ya sace shi...

*WASHE-GARI*

Islam bata fito ba sai wajen 10, dake weekend ce, sanye tafi to cikin sequence lace blue, dinkin fitted gown, bata ‘daura ‘dankwali ba, tayi kalba guda biyu manya da suka zubo mata har gadon bayan ta. Tasha jambaki. Tana fitowa sukai kicibis da Saifullah dake zaune a kujera ya saita ‘kofar dakin da zata fito da kallo. Kallo d’aya zakai masa kasan bai samu bacci ishasshe ba. Ko kallon sa batai ba ta ‘dauke kanta, y’ar gaisuwar da yake tsammanin samu ma ranar batai masa ba. Kitchen tashi ga, cikin ‘kan’kanin lokaci ta soya chips and egg, ta kira mai gadi a waya ya karbi nasa. Kanta tsaye ta wuce ‘dakinta da nata plate din a hannu. Saifullah dake kan kujera ya zama kamar wani mutum-mutumi. Ganin ko takansa bata biba, yau ko tayin abinci batai masa ba. ‘Kwafa yai yana mikewa tsaye. Mukullin motar sa ya zira rai ‘bace ya nufi gidan su Khaled.

Lokacin kuma Humaira tagama bawa Haj Latifa labarin komai. Ita ma kuwa batai ‘kasa a gwiwa ba ta buga tafawa Haj Zuwairah. Haj Zuwairah kuwa lokacin sunata shirye-shryen dawowa Abuja a satin. Wayarta kare a kunnenta ta jiyo muryar Haj Zuwairah na ‘kark’are xancen da,

“Na baki wuk’a da nama auntyn su, ki dau duk matakin da kikaga ya dace, kafin mu dawo, Insha Allah ni nasan me zan yanke akan al’amarin..”

A lokacin kuma Haj Latifa sallama takewa Haj Zuwairah, Ai kuwa Saifullah ya shiga parlorn bakin sa ‘dauke da sallama. Haj Latifa tai murmushi kawai tana cewa da Haj Zuwairah ta cikin waya,

“Kin ganshi ma ‘dan halak yazo. Okay to shikenan, Duk dai yadda ake ciki zan sanar miki.”

Cewar Haj Latifa ta katse kiran bayan sunyi sallama, Saifullah ya zauna a gefan kujerar da Humaira take, mikewa Humaira tayi bayan ya zauna, fuskarta a had’e ta gaishe shi, Don sosai take jin haushin abubuwan da yake yiwa Islam, bai kawo komai ba ya amsa da,

“Lapia lou Humaira, ya studies?”

“Kalau..” kawai tace a takai ce, ta haura sama abinta.

Har ‘kasa ya tsugunna yana gayda Haj Latifa, fuska a sake ta amsa, sosa ‘keya ya shiga yi, hakan ya sanyata tambayar sa ko lapia? Ya amsa da,

“Lapia lou Aunty.. Porridge(abinci me ruwa-ruwa) nake so..”

“Toh bari na sa ayi maka kunu.. Ina ita Islam ‘din take, ko tana school?”

Sai duk kunya ta kama shi, ya zama guilty conscious, ya ma kasa magana, Hakan yasanya Haj Latifa kyautata zaton dagaske ne de maganar da Humaira ta fad’a mata. Murmushi kawai tayi. Bayan ta mike ne tace dashi,

“Bari a damo maka, a hada maka da cup cake?”

Daga kai yayi kawai alamun Eh, yana jin sa duk a takure. Fita Haj Latifa tayi, ta shiga kitchen da kanta ta hado masa kunun tsamiya da chocolate cup cake.

Islam kuwa bayan fitar sa, ta shiga study room, dake sama, cikin sauri ta debi books din da takeson dubawa ta koma kasa, Don tunda akai auren ita a dakin ‘kasa take, shi kuma yana sama. Dama sama ‘daki uku ne da parlor sai kitchen, ‘kasa kuma daki ‘daya ne da parlor biyu, sai dinning area da kitchen/ store, sai daki d’aya a waje da balcony.

A ranar ne da rana ahalin Prof. Khaleel suka yiwa Islam zuwan ba zata, Ai kuwa taji dad’in zuwan su, ta sake wata kwalliyar tana bude musu kofa, Ammi ce kawai bata zo ba, amman Yakolo ta wakilce ta, da abincin su suka zo, nan aka shiga ci ana shafta, Saifullah kuwa bayan ya bar gidan su Khaled majalisaar su ya tafi, har yaje zai yi parking yaji gangar jikin sa na ingiza shi da ya koma gidan sa, zuciar sa na kwad’aita shi da son ganin Islam, idanuwan sa na nuna masa kyakkyawan murmushin ta, da tastiest lips dinta masu rugurguza mai tunanin sa.

“So suffocating...”

Ya fada yana mai dukan sitiyarin motar sa, kan motar ya juya ya koma gida, tun a kwanar gidan sa ya hango motoci, lambar kano da na Abuja, mai gadi ya bude masa gate ya shiga ciki, tun daga gate yake jiyo hayaniyar su, anata zuba hira. Lado mai gadi ya kalla dake zuba masa kirari, cikin melodious muryar sa yace,

“Baki mukai ne Lado?”

“Eh oga.. ‘yan uwan hajia ne suka zo d’axu.”

Kad’a kai yayi, ya shiga cikin gidah da takunsa na ‘kasaita, bakin sa ‘dauke da sallama, idanuwan sa suka zumo masa Islam dake zaune a tsakiyar wasu mata sai hira take zubawa, mamaki yake na ganin dama tana hira haka? Kansa ya ‘kara daurewa ganin Saifullahi da yayi, hankali kwance yana kurbar lemon robar hannun sa, Sai a lokacin suka lura da shi, aka shiga gaggaisa wa, shima cike da kunya yake amsa musu, ya bawa Saifullahi hannu suka gaysa, duk abunnan idanuwan sa na kan Islam dake dankaramai harara idan sun had’a ido, Sama ya hau , yana yi yana kallon Islam. Ganin haka yasanya Yakolo murmushi ta dubi Islam dake basu labarin makarantar su tace da ita,

“Islam je ki kai masa abincin ko? Ya dawo ko sannu da zuwa baki masa ba, shashasha na ‘dauka da kikai auren kinyi hankali..”

Cikin zumburo baki gaba Islam ta mike, duk yan parlorn suka sa daria, a nata ‘bangaren kuwa damuwa ce fal, na ganin su basusan halin da take ciki ba, ba susan irin zaman cakwakiyar da suke da Saifullah ba, harda bubbuga ‘kafa tai a ‘kasa irin na shagwabar nan, Yakolo ta kai mata dukan wasa, Ita dai Islam ‘murmushin da yafi kuka ciwo kawai take musu tana yak’e, Don kar su gano kan abun. Tana hawa bene tana addua, gaba d’aya a tsora ce take batasan irin bakaken maganganun da zai sake gasa mata ba. Duk abun nan Saifullah na kwance akan gado, yana kallon su ta madedeciyar tv da aka hada domin dakko rahotan cctv dake parlorn da suke, da kuma sauran ko’ina na gidan, bai tab’a kunna taba sai yau, Don sosai zuciar sa take sake kwadai ta masa son ganin Islam. Yana ganin ta kusa ‘karasowa dakin da yake yai maza ya kashe tibin (TV/television). Islam kuwa cikin sand’a ta shiga parlorn sama, daki d’aya ta bude tana adduar Allah yasa baya ciki. Ai kuwa ba kowa ciki, ta shiga tana sauke nannauyar ajiyar zucia.

Saifullah dake maitar son ganin ta yaji ‘dif , ba Islam ba alamar ta, cikin rawar jiki ya mike yana gyara collar rigar sa, ya kara banka turaren alharamein yana kallon kan sa a mudubi. Cikin hanzari ya fita daga dakin, ta kamshin turaren ta ya gano tana dakin tsakiya. Ai kuwa yana murda handle din kofa ya hangota a zaune akan gado tana raba idanu, daria taso tabashi ya danne, yana wani hade rai tamkar yaga kashi, kamar bashi ne mai ‘kulaficin son ganin ta ba. Tana ganin sa ta ‘kara sunkuyar da kanta. ‘Kasa ‘kasa ya shiga kallon ta, ba kadan ba tayi mai kyau cikin wani material lallausa ja, dinkin bubu, tasha jan jambaki, dauri kawai tayi bata yafa mayafi ba, jelar kalba biyun da tai ta matukar karawa daurin kyau.

Kusa da ita ya matsa, ta ja baya da sauri, sai da suka kai ‘k’arshen gado a haka, ya samu kansa da rike hannun ta, Cikin murya ‘kasa kasa kamar rad’a yace da ita,

“Who’s that guy?!”

“Wa kenan?” Ta bashi amsa tana cuno baki gaba, amma fa a tsorace take.

Hade rai yayi kafin yace,

“Na downstairs mana.. Wanene shi?”

“Oh ya Saifu... Cousin dina ne”

Kamar almara yaji abunda ya tsaya masa kwana da kwana ki a wuya yau ya sauka ‘kasa ya fad’a.

“Cousin?” Ya maimata yana feeling guilty.

Daga kai tayi tana kallon gefe, samun kansa yayi da ‘kara tambayar ta da,

“Malamin ku ne a school ko kuma student ne shima?”

Wani kallo ta watsa mai kafin tace,

“Malamin mu ne, shine lecturer dinmu na community medicine.”

Idanuwan sa ne suka sauka a kan labbanta, wani feelings yake ji a game da su na daban, So yake ya samu ya rage xafi akan su miskilancin sa ya hana, dakyar ya ‘ka’karo maganar,

“Wane warning na miki akan jambaki?”

Ta gano shi, hakan yasanya ta saurin kwace kanta ta mike a dari zata buda kofa ya rigata, ita da kofar ya had’a ya rufe da mukulli, ya jinginata a jikin kofar, yana kallon idanuwanta dake sanye cikin kwalli baki me kyau. Cikin takaici tace,

“Dan Allah ka sake ni na koma wajen su Aunty.,, Dan Allah ka..”

Bata ‘karasa ba taji bakin Saifullah Faruk Muhammad a nata, yana kissing dinta da wani irin salo na soyayya, wani irin French and passionate kiss yake bata, gaba d’aya jikinta ya zama weak, sun ‘dau lokaci a haka kafin ya turata gefe, idanuwan sa sun kada sunyi jajir, nunata yayi da yatsa yana fadin,

“Kar ki ‘kara saka jambaki daga yau idan wani ‘da namiji Yana wajen, ni kadai na yadda ki sa jambaki a gabana, Banda sauran maza. Wallahi kinji Allah Idan na sake ganin kinsa jambaki da maza awajen kuma sai na mugun sab’a miki, ko school zaki je ban yadda ki saba, idan kuma kika shafa without my consent ban yafe ba.”

Baki sararo Islam ta saki tana duban Saifullah, na ganin duk akan jambaki yake wannan bala’in, cikin tunani ta jiyo muryar sa yana,

“Get lost.. don’t let me repeat my self”

Fecewa Islam tayi ta gudu, shi kuma ya zauna a bakin gadon dafe da kansa, hannun sa d’aya yasa a saitin zuciar sa yana dafe ta, jin yadda take bugawa da ‘karfi, ahankali yake furta.

“Ya Salam! Me ke faruwa dani? I’m feeling so uncomfortable”

Ya jima a zaune, nan Islam ta shiga, daga bakin kofa ta ce masa bakin zasu tafi, bandir din ‘yan 200 ya dauka ya sauka kasa, su Areef da sauran yaran ya daddan ‘kawa kudin a hannu, sunata tsalle suna murnar zasu sai alawa. Shi de cikeda kunya ya ‘karasa ya raka su har parking lot, sukai sallama da su, Sai bayan sunja motocin su sun tafi, Islam da Saifullah suka koma ciki, dakinta ta shiga ta datse da mukullii, shi kuma ya haura sama yana jin wani bak’on lamari yana ziyar tarsa. Dakyar bacci ‘barawo ya sace shi, ita kuwa Islam tuni ta bawa gado ‘hakkin sa don dama a gajiye take.

Gaba d’aya Islam ta fita harkar Saifullah, duk wasu abubuwa da zai hadasu tadena yi, tadena bari ko haduwa suyi bare ya karta mata rashin mutunci. A satin ne taje ganin gidah, Don tinda aka kai ta ba taje ba, Ammi batasan dawar garin ba, da Islam tatashi tafiya ta harhada mata kayan gyaran jiki dana mata, da sauran spices na girki, Ita dai Islam kawai ta amsa ne don karta ‘ki amsa, Ammi ta tambayi jin ba’asi. Sai bayan magrib takoma gidah don dama ta masa message zata gida, yace ok.

Tana shiga ta ganshi hakimce a parlor, ya kwantar da kansa akan pillow, idanuwan sa kamar mai bacci, ya rufesu. Sallama kawai tayi, ya amsa a ciki, tai shigewar ta daki tasa key, ajiyar zucia Saifullah ya sauke yana mikewa tsaye. Kashe komai na wuta yai a ‘kasan, sannan ya haura sama yana dafe kansa dake barazanar fad’o masa,...

*WASHE-GARI*

Wajajen 6 na yamma Haj Zuwairah mahaifiyar Saifullah ta dira a gidan su Saifullah, lokacin dawowar Islam kenan daga school, Sosai islam cikin rawar jiki ta cika gaban Haj Zuwairah da kayan ‘kwalam da makulashe, Ita dai Haj Zuwairah sai bin Islam take da kallo, yarinyar nada hankali ga nutsuwa, batasan meyasa Saifullah ya bad’awa idanuwan sa ‘kasa a ido ba yai fatali da wa’azin da tai masa na yasanya soyayyar Islam a ransa, aganinta yarinyar batada wata makusa da za’a ‘kita..

Jefi-jefi suke ‘dan taba hira, Sai bayan isha’i abadan Saifullah ya shigo gidan, hakan da yai ba karamin ‘kara ‘kona ran Haj Zuwairah yayi ba, wato sai dare yaja ma yake dawowa gidah kenan? Yabar y’ar mutane ita kadai sai mai gadi, yana shiga parlorn bakinsa dauke da sallama ya hangi mahaifiyar sa, cikin rawar jiki ya karasa gare ta yana wani shagwabancewa, Islam dake gefe ta zuba musu idanu tana kallon sarautar Allah..

Cike da shagwaba Saifullah yake gayda mahaifiyar sa, amsa masa tayi kamar ko yaushe. Ta danne abunda ke ranta sai nan gaba zata nuna masa fushinta idan ta yanke hukunci. Sai da suka dan taba hira ne ta mike tana gyara mayafinta, ta dubi Islam dake zaune a gefanta a ‘kasa tana wasa da gashin center carpet,

“Auta ta! Had’a kayan ki a akwati da duk abunda zaki buk’ata, zamu tafi gida na...”




****
_Wallahi kunci darajar wa’enda nake kunya, ba zan iya ja da su ba😊 sun nemi alfarmar na cigaba da yi DAN SU, Saboda haka zan cigaba da rubuta littafina kamar yadda na fara, amma dan Allah duk sanda aka ga banyi post ba to akwai dalili ne, ko na matsalan idona ko wani abu dai da yasha mun kai☺ Ashe haka masoyan littafin SAIFUL_ISLAM kuke da yawa 😅lord !😫 I’m impressed☺ amma fa gaskia yawan comments dinku shi zai bani ‘kwarin gwiwar rubuto shi da yawa, kuma akai akai, less comments, less posts gaskia_

_GA MAI BUKATAR SIYAN *KAI MIN HALACCI* dama sauran books dinmu na *ZAFAFA BIYAR*, zaku iya tuntubar details namu kamar haka;_

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*🤝🏽🤝🏽🤝🏽







_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO.💡_*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 50-53_*

_nanahafsat.wordpress.com_

Tun kafin ya kai ‘kofa yajiyo kukan Islam, tuni ta zube a ‘kasa tana zunduma ihu, hannuwan ta dafe da kanta, yadda ku kasan anyi mata aiken sak’on mutuwa. Rerashi tashiga yi ba ‘kak’kautawa, Saifullah dake bakin kofa ya juya ya koma wajen ta yana lashe ‘kasan lips dinsa, ta fuskar sa zaka gane he really enjoyed the kiss, hannuwan sa zube cikin wandon kakin sa. Tamkar bai tab’a daria ba ya tsaya akanta, cikin husky voice dinsa yace,

“Ke...”

Bata ‘dago ta dube shi ba, ta cigaba da kukanta, duba agogo yai minti biyar harta wuce, Lalle dagaske ne tarihin ta da aka bayar na mayyar kukace, tabe baki yayi kafin yace.

“Zaki ‘dago fuskar ki, ko sai na sharara maki mari tukun?”

Dakyar ta iya mikewa tsaye tana kallon ‘kasa, tana ‘dagowa ya zabga mata harara, cikin yatsina fuska yace,

“I ruined my first kiss akan ki, my very own first kiss, so precious and tantalizing! Daga dora shi akan lips naki kika cafke kamar kin samu alawa, gashi ke ba good kisser bace, beside wannan ba shine kiss dnki na farko ba kinyi da maza ba adadi, you better stop pretending, dama abunda kike so ne, you are desperately in need of a shoulder to lean on, kin samu miji da akai mai auren dole, kin nemi alfarma kin samu, kuma daga antemaka miki shine zaki wani tsiri kukan wofi... Stop crying abeg, grow up..”

Yana fada yai gaba yana nanata kalmar,

“So suffocating...”

Hawaye Islam ta goge na irin bakaken maganganun da Saifullah ya gasa mata, dakyar ta goge labbanta tana furta kalmar ‘Allah ya sakamin’. Ta gyara jikin ta ta zuri kayanta tai gate, ba motar sa, hakan yayi nuni da ya tafi kenan. Motar ta tashiga ta tasheta ta fita, ta dawo takulle gate din, ta wuce school...

Ko a school dakyar Islam take concentrating akan abunda ake koyar wa, bayan fitar malamin ‘dietetics’, ‘Dr Saifullahi Bala Muhammad’ ya shiga. Wato Saifullahi cousin din Islam. Sosai Islam tayi mamakin ganin sa, ashe dagaske Lee take, da tace xai fara koyar dasu, Ai kuwa yadda ta tsammata hakanne domin sun sha tambayo yi, yau Islam duk batai concentrating ba, shiysa daya basu open test batai wani abun arziki ba, Ai kuwa ana tashi daga lectures ta bi bayan sa cikin sauri, Don ko kadan batasan ta samu matsala a harkar karatun ta, tanason ta wuce komai successfully, Saboda withdrawing ake yi ko change of faculty’.

“Ya Saifu”

Cewar Islam, tana maganar ne, tana hadawa da sauri, domin kamo Saifullahi dake tafiya, hannun sa rike da waya yana karata a kunnensa, da alama waya zai yi. Ja tayi, ta tsaya daga bayan sa jiran yagama, Yana gama amsa wayar ya juya yana kallon ta, ‘dan rissina kai tayi, kafin tace.

“Ina yini Ya Saifu?!”

“Ah Amarya..Ya mai gidan naki?”

Ware idanuwa tayi, jin abunda Saifullahi ya ambata, lalle aure yana kankaro maka mutuncin ka, yana kuma ‘kara maka daraja da ‘kima a idanun mutanen da suka mai da ka ‘bawon albasa. Cikin kunya ta sunkuya tana murmushi kawai. ‘Dan darawa Saifullahi yayi, kafin yace,

“Menene matsalar ne? Nasan ba zata wuce open test dinnan ba ko?”

Cikin azama Islam ta ‘daga kanta alamun Eh, murmushi yayi yana gyara tsayuwar sa kafin yace.

“Kakki wani damu, attendance ce kawai zan mai da ita, nafison taking attendance sosai akan tests, saboda attendance kowane ‘dalibi zaifi zama serious baya missing sch. Tests kuwa har makeup anayi, and I don’t tolerate such shits kin sani ke ai.”

Daga kai Islam tayi tana murmushi, kyakkyawar wushiryar ta, ta bayyana, Shima Saifullahi dariar yake yi, a dai-dai lokacin Saifullah mijin Islam ya shigo school ‘din karbar mukullin gidan, Don ya manta bai dauki na gate ba, gashi tace xata jima a school yau, kalle-kallen inda zai hango Islam yakeyi, kamar ance ya ‘daga idanun sa, ya hangota itada Saifullahi ‘dan uwanta, gashi yasan fuskar sa gayen a wani waje, amma yakasa tunano a’ina ne.

Wani abu yaji ya tokare masa maqoshi, Lalle yarinyar nan batajin magana, juya kan mota yayi, ya figeta kawai, ganin kusan minti biyar da tsayawar sa, bai ga sun dena hirar ba, a lokacin kuma Saifullahi shi Islam ce ma take masa maganar Nusrah don takusa haihuwa yau ko gobe, cikin ta ya tsufa, tana sake karbar number Nusran saboda batada ita yanzu. Da wannan Saifullah yaja mota sai gidan su Khaled. Ran sa a matukar ‘bace, domin duk ‘daukar sa Islam bata dena kule-kulen mazan da yake zargin tayi a baya ba. Nan ya tarar da Khaled suna shirin tafiya Spain shida amaryar sa dr teemah, daga ‘k’arshe dai shiya kai su airport din, bisa umarnin Haj Latifa, dan tsabar iskancin Khaled kuwa a baya suka hakimce shida matar sa, suka kwantar da kujerun bayan. Duk abunda sukeyi Saifullah na jiyo su, minti kadan ya buga brake yana na-nata,

“So suffocating..”

Yana sauke su a airport aka fara yayyafi, Khaled dake janye da akwatunan su yace da Saifullah cikin murya ‘kasa ‘kasa,

“Aboki na yanayin nan yayi fa, shar da kai, ana ruwan nan, Allah yaso kanada mata, ta zama lapiyayyan bargon ka nake gaya ma, acan-acan da kai wallahi, dama gashi nan fuskar ka ta nuna alamar desi..”

Cikin sauri Saifullah ya katse shi yana matsar da fuskar Khaled daga kunnen sa,

“Abeg ja boxes dinka kuyi gaba pls, you are very annoying..”

Murmushi Khaled yayi yana jan hannun Nusrah, sai da sukai nisa kafin yace,

“Ka dai ajiye girman kan nan, kada kayi irin na mutumin ka NAUFAL(THE CHARMIN, littafi na), wallahi Allah yasa Islam ta gasa ka, kamar yadda Ayush ta gasa the charming, and kakka soma zuwa waje na neman favor.”

Tsaki Saifullah yayi, yana girgiza kai, ba karamin dadi yaji ba fa tafiyar Khaled. Domin ya takurawa rayuwar sa, shi matar Khaled din cema ke bashi tausayi, Sam Khaled din baya sarara mata, kullum yana ‘kwakwume da ita a ‘daki, Sam baya bari ta huta. Mota ya koma ya jata ya nufi gidah, domin yasan duk yadda akai yanzu Islam tadawo, akwai wasu zanen hostels daya keson ya ‘dauka, wani mutumi na neman contract a inda yake aikin PPA.

Islam kuwa tana shawo hanyar gidan ta, ta hango Saifullah akan mota yana danna wayar sa, gabanta yai mugun fad’uwa hango fuskar sa, kwarai matuka yanayin sa ya sa ta tsorata, hango motar ta yasanya shi dirowa daga kan motar sa, ya gyara parking yadda zata wuce, da kansa ya bude gate din ta shiga ya rufe, ta zura mukulli ta bude kofar parlorn suka shiga atare, bakin su dauke da sallama da adduar shiga gidah,

“Barka da dawowa”

Idan Saifullah ya amsa, bangon parlorn ya amsa, ko kallo bata isheshi ba, ya haura sama abinsa yana tsaki.

“Ikon Allah.. Yau kuma da wannan salon ka dawo kenan”

cewar Islam, hade da tab’e baki. Dakin ta tashiga, tayo wanka, ta zura riga marar nauyi. Ta kukkuna turaren wuta a ko’ina hade da karatun suratul baqrah’, a wata madedeciyar speaker dake gefan corridor. Kitchen ta shiga, rasa abunda zata dafa tayi, cikin sauri ta ‘dau ra’ayin dafa Italian spaghetti, cikin kankakin lokaci kuwa tagama, sunada cat fish tagasa shi, Tare da hadadden iced tamarind juice.(Yunwa nake ji😞) Ta debi iya nata, ta jere sauran a dinning. Har tagama zamanta Saifullah bai sakko ba. Daki takoma don yin assignment dinta, tana kuma labartawa Lee amarya yadda lectures din ranar ta kasance

Please Login or Register in order to submit comment