Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dm, Wordpress site, on and on and on. Wallahi I deeply appreciate itđŸ€—Da sauki sosai, Nagode for the warming prayers it means a lot to me wallahi. With out you guys I wud be fish food I knwđŸ˜č. Álà bárgà njoÌđŸ˜˜ love y'll fisabilillahi đŸ€—đŸ’•đŸ‘. Have a blessed weekend ahead._






_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXOđŸ§•đŸŒ_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


Âź *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CEđŸ˜»_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 30-31_*

_Shafin yau na ki ne FATMA_ZARAH (BICHI)Fatan alkhairi a gare ki, dangin agalawa😉Allah ya baki miji nagari, kyakkyawa mai kyawun hali💕_

_nanahafsat.wordpress.com_

Gidan sa na da dasu Karimatu suka tashi, Dr Khaleel ya k'ara gyara shi ya koma tamkar sabo, aka rushe wasu sashen aka mai dashi sashe biyar kawai, b'angaren sa, dana Haj Aysa da Helwa uku kenan. Sai na Inna Bilkisu da b'angaren baki. Tamkar wasu amare haka ya mai dawa kowacce apartment d'inta, Royal furnitures sababbi fil aka sanyawa kowane sashe, amma na b'angaren Inna Bilkisu yafi kowan ne tsada tun farko haka suka saba yi komai nata yafi na matansu tsada, ko atamfa ce tata super ce, su kuma Holland domin iyaye ba abin wasa bane musamman ita da ta tashi tsaye da addu’oi, dan ganin Allah ya cika musu burikan su tun suna k'anana.

Sosai su Islam suka fara lectures, gaba d’aya bata da lokacin komai, dan da asubah malam yake zuwa yayi mata tahfiz da safe kuma take tafia lectures sai yamma ta dawo da daddare kuma lesson teacher d'inta yake zuwa, sam bata da wani spare time kullum she’s busy, har time-table tayi na yadda xata dinga gudanar da ayyukan ta na yau da kullum. Cikin lokacin ne kuma aka sanya bikin Fatma Bichi dake kano, event d’aya Islam da Lee suka samu zuwa saboda school, gashi class d'insu d’aya kuma. Can Middle-East aka kai Fatima k'asar Qatar ko d'igon hawaye ba tayi ba domin tana matuk’ar son mijin nata, ko makaranta tace ita baxa cigaba ba ta yadda zata yi ABU mai labule.

****

Zaune suke a parlor Haj Aysa da Yakolo, wannan karan harda k'arin Yaburra(Zainab) ‘yar gidan Aunty d'in Haj Aysaa dake Bornu. Shirye-shiryen auren Yakolo suke yi sai kace auren budurwa, dawowar Islam kenan daga school a matukar gajiye take, gaishe su tayi ta haura sama abunta, mai aiki ta bita da abinci. Wanka tayi kawai tayi sallah ta kwanta bacci. Can k'asa kuwa suna list na kayan gidah. Yaburra da tun d’azu zancen ke cinta ta kasa ajiye shi a zuciarta sai dai ta daure tace,

“Ni wai Yayya Islam har yanzu shiru? Ba wani a k'asa ne?”

Haj Aysa dake gefe ta sauke nannauyar ajiyar zucia kawai bata ce komai ba. Yakolo ce ta dank'arawa Yaburra harara kafin tace.

“Sai akai yaya? Wai ke bakisan aure lokaci bane? Ko kuwa duk dangin mu da sun tasa aure suke yi? Haba mana, ni fa bana son k'ananan maganganu da gutsiri tsoma, sai inci...”

Hanzarin katseta Yaburra tayi da sauri tace.

“Kai! Wallahi ni ba da wani abu na fad’i haka ba, kawai dai naga ina ‘yar ya Fanna ta Askira? To itama kusan hakan ne issue d'in, sai da abu yai tsamari aka gane wai ashe jinnul-Ashiq ne.”

Dogon tsaki Yakolo taja tana maida d'ankwalinta kanta, kyakkyawar harara ta k'ara bankawa Yaburra kafin tace,

“Duk naji, Toh kina nufin kice Islam aljanine a jikin ta ko me?”

Girgiza kai Yaburra tayi, tana k’ok’arin wayarwa Yakolo kai, wadda sam tak’i yadda, ganin hayaniyar tasu na neman caza mata kai ya sanya Haj Aysa dakatar dasu cikin sanyi tace,

“Ku bar zancen dan Allah! Allah ne kad’ai masanin gaibu, ke kuma Yaburra tunda kin kawo suggestion ki kirawoshi ya mata tambayoyi idan sune Allah ya mata maganin su, idan kuma basu bane Allah ya gaggauta kawo mata mafita ita da duk masu matsala irin tata.”

“Ameeeen!”

Suka amsa gaba d’aya. Bugu biyu kuwa Ustaz Aliyu ya d'aga wayar, zaiyane masa komai Yaburra tayi cikin harshen kanuri, ya shaida mata gashi nan Insha Allah bada jimawa ba don dama basu dad’e da dawowa daga tafiya ba shida amaryar sa Jiddah. Ba’a d'au lokaci ba kuwa sai gashi duk sun gaggaysa dashi kafin a kira Islam dake sama tana bacci, sai data watsa ruwa kafin ta sakko sanye cikin hijabi. Gaishe shi tayi ya amsa cike da fara’a, ya d'anyi naxarin ta na d'an wasu lokuta kafin yayi addu’a yafara magana cikin sanyayyar muryar sa.

“Idan aka ce Jinnul Ashiq, ana nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji. Akwai kuma Ashiq dake bibiyar ‘yan mata ta hanyar ture (sihiri) ko kuma sun yi wasarere ya shiga jikin su. Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma k’ok’arin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga k’ok’arin kashe mata shi. Su na kuma k’ok’arin hana mace samun ciki ko kuma in ta samu cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa ya zamo tun daga haifar sa za a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau’in Aljani shi muke kira...JINNUL ASHIQ ïșŸï»Š ïșï»Ÿï»ŒïșŽïș·ï»–,

“Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne, alamomin shafar aljana mace ta b'angaren maza sune; rashin sha‘awar aure ko jima’i sam-sam, k'in mikewar gaba sanda kai nufin yin jima‘i alhali kuma haka kawai ma yana tashi, k'in fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana iya zama a cikin marainan mutum, saurin gajiya yayin jima‘i da rashin iya komawa, jin motsi kamar tafiyar wani abu a ga6o6in haihuwa yayin jima‘i, rashin cimma bukatar jima’i in ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya d'aukeka, da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo tun kafin ka fara, komawar gaba da maraina su shige ciki, yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili,

“fad'uwar gaba da dai sauran su, haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka, yawan mafarki kana saduwa da wata matat, yawan samun matsaloli a duk inda ka je neman aure sai maganar ta lalace, Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai, Matsananciyar sha’awa da tsoron mata da dai sauransu.,

_YADDA MACE ZATA GANE ALJANI YA AURETA_

“Yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi a cikin, a duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al’adarta bane, jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida, suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba ma ta ya dinga dawowa ba zai shiga mahaifar ta ba, matsanancin ciwon baya ko kwankwaso, kin yarda da jima‘i za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban, yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da taron suna, ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa a cikinki ya fizgo wani abu,

“Musamman idan kina da ciki, yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen dalili ba. yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke, jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yana dad'a girma amma in likitoci suka auna za su ce ba su ga komai ba, rashin son yin magana da kowa da jin haushin mutane haka kawai, tsanar mai gida haka kawai alhali za ki ji kina sha’awar wasu mazan,

“Jin wari mara dad'i yana fito miki ko kaykayin gaba da kurajen gaba Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba. Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi, In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suyi mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fad'ar cewa wance kwarjini take musu, za ta dinga yawan zama a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane, Idan yarinya tana zuwa makaranta za'a ga k'ok'arin ta yana raguwa kuma tana ramewa, yawan ciwon kai da yin jiri, fad'uwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa. Idan mace ta fara bacci sai ta ji an zungureta ta farka. Da dai alamomi da yawa. Ya k'ark'are da cewa,

“Mafita shi ne ka ziyarci mai Rukiyya don ya d'ora ki akan tsarin maganin da ya dace da ke. Kuma ki dinga zama da alwala da addu‘o‘in safiya da maraice. Idan kuma wannan matsala tayi karfi, to dole sai an yiwa mutum rukiyyah, an nemi Aljanin an kona shi ko kuma a had'a magungunan da za su kashe shi. Ko’a sami garin harmal, ad'ebi cikin karamin cokali d'aya azuba a cikin ruwa babban kofi d'aya, sai a tofa ayoyin ruqiya ciki a dinga sha sau uku ayini. sannan a had'a man zaitun, man habbatussauda, man hulba, man gelo, man tafarnuwa, man na’ana'a, man Khisdil Hindi, Turaren za’afaran,

“Turaren miski, turaren wardi, Garin khaltit. Sai a had'a su duk awaje d’aya, a tofa ayoyin ruqya aciki, ana shafawa sefe da kuma dab magriba. Insha Allah za’a dace”

Daganan ya shiga yiwa Islam tambayoyi ko zai gano alamun ko ta kamu da shafar jinnul Ashiq, amma kemad’agas ko alamu babu. Ta amsa komai tiryan-tiryan babu matsala, hamdala yayi, kafin yace ta samo biro ya babbata wasu addu’oi, Daganan yace ta koma sama abunta, ruwan da aka ajiye agabansa yasha kafin yace.

“Toh hajia Alhamdulillah domin gaskia ‘yarku bata da matsalar Ashiq, kawai jinkiri ne da zai zamto alkhairi Insha Allahu, tunda yadda na d'auka ma ashe ba hakan bane, domin yarinya ce har yanzun, Insha Allahu zata samu abunda ake buk'ata da yardar Allah, kawai dai shine ta rike addu’oi, azkhar na safiya da maraice dana kwanciya bacci. Kullum ta zamto cikin alwala, lalle ne kuma ya zama wajib idan zatai bacci ta kwanta da alwala, ta kuma dinga yin addu’o'in dana bata sannan ni zan mata wani tofi a ruwan zam-zam Allah yasa mu dace.”

“Ameen..” suka fad’a baki d’aya. Fuskar Haj Aysa fad’ad’e da murmushi.

Zungurar Yaburra Haj Aysa tayi da k'afa tana mata alamun nawa za’a bashi? Murmushi Yaburra tayi kafin tace,

“Malam Aliyu, Toh mahaifiyar Islam d'ince ke tambayar nawa za’a bayar na lada dana zam-zam d'in?”

Murmushi Aliyu yayi yana mikewa tsaye, hannunsa d'auke da ragowar ruwan sa, cikin muryar sa mai dad’in sauraro yace,

“Haba Yaburra. Ladan addu'a fa kikace? Haba Allah ya kiyaye, ni dan Allah nayi batun zam-zam kuma idan nagama yi zan aiko a kawo, fatanmu koma menenen ya warware cikin sauqi, ballantana ma k'alau take, kada kusa komai a ranku wallahi lokaci ne kawai bai yi ba, Allah yana sane da komai, ba kuma wai dan baya sonta ba, sam ba haka bane, wani lokacin ma jarabawa ce daga gareshi ya gani shin zata iya cinyewa ko kuwa? Toh Allah ya bata ikon cinye jarabawar ita da duk masu jinkiri irin nata”

“Ameen..” suka fad’a baki dayan su.

Har bakin k'ofa Yaburra ta rakashi kafin ta dawo ciki, Haj Aysa tai mata godia itada Yakolo. Nan suka sake zaman hirar Aliyun da irin kirkin sa, har maganar matan sa ta shiga ciki, Yaburra tace.

“Wallahi matan sa biyu, Maimuna itace uwargidan sai Jiddah ta biyun, amma naji ance yana neman ta uku a kano.”

“Haba?” Cewar Yakolo da Haj Aysa.

Jinjina kai Yaburra tayi cikin gasgata abun da take fada tace,

“Haka naji, kai dagaske nema domin yace min da kansa yana neman ta uku a kano, wai kinji sunan ta ‘Miss xoxo’ shine nickname d'inta, yace wai ta WhatsApp suka had’u a group d’insa na ilimi-haske ne. Ya ma sunan ta na gaskiyar..? Yawwa Nana-Hafsatu.â€đŸšŽđŸŒâ€â™€

“Allah sarki, Allah ya basu zaman lapia, ya sanya alkhairi.”

“Ameen” cewar Yaburra.

Basu tashi daga wajen ba sai da suka gama list d'in komai na biki, da sati ya zagayo kuma a ka raqashe bikin Yakolo, kamar wata ‘yar budurwa, rana d’aya akai wushe-wushe a farfajiyar gidan su Helwa ne akan komai. Aka kai amarya nan gidan ta dake unguwar Asokoro.

*LAGOS*

Tunda Saifullah ya dawo, ya fara shirye-shryen tafiya bautar k'asa (NYSC), ya gama komai. Jira kawai yake yaga inda za’a tura shi, ranar Monday da safe kuwa Mail ya shigo masa na anturashi 3weeks camp a Abuja. Sam bai so haka ba, domin yaso kudu aka kaishi, aganin sa wai zaifi samun life experience. Kwana biyu nayi ya d’aga zuwa Abuja bisa jagorancin Khaled, wanda vissa d'insa zata fito nan bada jimawa ba. Camp ya shiga, yanayin yadda ‘yan mata ke rushing d'insa ya sashi kasa zama, sannan shi mutum ne mai son tsafta, amma yanayin band'akin camp d'in sam bayi masa ba, beside gurin ma gaba d’aya is too noisy acewar sa. Nan yai ciku-cikun sa yai exeat from camp. Yakoma gidan su Khaled yana jiran fitowar ‘yan camp d'in don ganin shin za’a canza masa gari(relocation) ko kuwa?.

Sanyayyar safiyar asabar ce ya fito da damuna, garin yai luf-luf dashi, Sam ba hayaniya korayen bishiyu sunyi shar dasu ni’ima na busawa ta ko’ina. Da kyar ya fita daga gida domin daily exercise d'in daya saba. Yana tafe yana d'an had’awa da gudu ya rufe kansa da hular sanyi. Yanayin na matukar ratsashi sosai yake jin dad’in yadda yake motsa jikin nasa.

A lokacin ne kuma Islam tafito daga gida itama, don yin exercise, aganinta saboda yana da kyau yana gyare jiki musamman kuma don ta rage yanayin jikinta dan sam bata san yadda mutane ke bin jikinta da kallo, shi yasa a school kullum cikin hijabs/jilbabs ko Abaya take. Tafe take tana tafiya tana had’awa da gudu. Riga da wando ne a jikinta kasancewar da sassafe ne ba wanda ya fito tunda weekend ce, kuma d'ai-d'ai kune ke fita exercise din. Ba kowane zai ganeta ba, amma ta yane kanta da mayafin abaya, kunnuwanta saqale da earpiece tana sauraren karatun alqur’ani mai girma na k'ira’ar shureim. Medicated glasses d'inta kalar kayan jikin ta, ta bayan gidan su ta fara zuwa gaban layin su.

K’ok’arin rage volume take yi lokacin data shawo kwanar gidan su Humaira, kanta a akan wayar ta sam bata kallon gaban ta, hakama Saifullah dake tafiya da baya-baya, wai shi kwarewa cikin rashin sani ji kake garau, goshin su ya had’u dana juna. Tuni wayar hannun ta, ta sulale tafad’i a k'asa cikin azabar zafi Islam ta dafe goshin ta tana fad'in.

“Ouch! Ya Salam!”

Saifullah dake rik’e da nasa goshin yana mulmulawa ya sakar mata wata uwar harara, yana fad'in,

“What the fuck... hey watch it.”

Dago dara-daran idanuwanta tai tana duban mai fad’ar haka, ya bigetan sannan ya fad’a mata haka? Ba ko ban hak’uri. Dake blurred take ganin fuskar mai maganar sam batasan ya kalar sa take ba. Girgiza kai kawai tayi ta duk’a k’asa tana d'aukar wayar ta. Ko takansa bata biba tai wucewar ta gidah cike da haushin arrogant fellow d'in da suka had’u yanzu. Har ta wuce wa ganinsa yana bin bayanta da harara tamkar tana ganin sa. Cikin shagwababbiyar muryarsa yace,

“Annoying piece of shit...!”




_SAIFUL_ISLAM...!💕_
_perfect strangers_đŸ’«
_(Labarin tacacciyar soyayya marar gauraye...đŸ’«_)đŸšŽđŸŒâ€â™€










_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXOđŸ§•đŸŒ_

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


Âź *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CEđŸ˜»_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 32-33_*

_SHAFIN YAU NA KU NE GROUP ‘DIN sis UMMI AISHA, NA *DUNIYAR MAKARANTA GROUP*, FATAN ALKHAIRI AGARE KU, GODIA CIKIN KWANDO GA FIRDAUSI ABUBAKHAR, DAMA ‘DAUKACIN MAKARANTA SAIFUL_ISLAM💕_

_nanahafsat.wordpress.com_


D'an k'aramin tsaki yaja, tare da harar hanyar da yaga tabi sannan ya juya shima ya tafi, yana tafiya yana mulmula wajan da suka yi gwaran dan ba k'aramin zafi yaji ba shima. Kai tsaye bedroom d'insa ya nufa ya cire kayan jikin sa, ya zamana daga shi sai boxer da bak'ar vest ya nufi bathroom dan yin wanka, haka kawai yaji yana mamakin yarinyar, wato su mata idan suna so suyi wani abun da kai duk ta hanyar da suka san zasu samu abin sai sunyi, yana kyauta ta zaton wannan yarinya ta bigesa ne kawai dan ta tab'a jikinsa, kamar yadda yasan mata suna sha'awar yi masa hakan dan dai baya basu fuska ne kawai.

A ‘bangaren Islam, kuwa da gudu ta shiga gida duk a tunanin ta zai biyo ta gashi unguwar babu mutane kartaje ya danneta ya cuceta, tunda taga ita haka samari da magidanta suke yi mata, wani kallo na a huta da ita, ba wai kallo na kauna ko soyayya ba bare akai ga yin aure.

Numfashi taja mai tsawo tare da furzar da iskar da ta shak'o tana k'ok'arin warware tufk'ar da tayi ma gashinta, cilli tayi da ribbon d'in a kan gado sannan ta karasa ta d'akko towel ta d'aura ta nufi wajan madubi ta na kallan fuskarta zuwa sassan jikinta da inda sukayi gware da Saifullah, ta mulmula gurin yafi sau biyar kafin ta murgud'a baki tace a fili.

“Wallahi da ace inaji da rashin kunya babu abinda zai hanani yiwa mutumin can ita, dan iskanci kana ganin mace na tafiya baka sani ba matar aure ce, ko budurwa ko kuma bazawara kawai kazo ka bigeta dan salan iskanci, hmmm wallahi kaci sa'a da babu abinda zai hanani sharara maka mari a duka kumatunka sakarai kawai.'”

Tayi maganar tana yatsina fuska tamkar da wani take yi a wajan, ta d'auki comb ta shiga toilet ranta duk babu dad'i babban haushinta yadda boobs d'inta suka tab'a kirjinsa wannan abun yayi mugun b'ata mata rai sabida gani take kamar ya sake rage mata farashi. (Wa yaga sakarai).

Hutun mid semester suka samu, a lokacin kuma saifullah ya gama sati ukun sa na camp, ya tafi Lagos. Duk meyiwuwa yayi kan yakoma Lagos yayi one year service d’insa abu yakiyi, place of primary assignment d’insa still Abuja ne. Nan SMEDAN branch dinsu na wuse. Lagos Islam tayi tafiyar ta hutu, a lokacin Saifullah shima ya koma gida kafin ya dawo ya fara ppa d’insa. Unguwa d’aya suke gida biyar ne tsakanin gidan Ya Bala dana su Saifullah. Su saifullah idiroko 12b, su Ya Bala kuma 17b.

*LAGOS IDIROKO*


Haka suka ci gaba da fita motsa jiki anan lagos ‘din. kullum shi Saifullah yana ganinta ko zai tafi ko kuma ya dawo, yarasa wane irin naccacciya ce, acewar sa da ganin sa saboda shi tazo lagos ‘din. sab'anin ita da tun ranar da abin nan ya faru tsakaninsu a Abuja bata sake had'uwa dashi ba, sai wasu mazan daban wad'anda suke tare ta a hanya suna nuna mata wasu banzayen d'abi'u amman bata basu dama, Saboda yanzu itama tsoro takeji kar wani ya lalata mata rayuwa, daddyn su yayi mata aure da abokinsa kamar yadda aka yiwa su Hidayya da Hafsat 'yan uwanta.

Yau dai kam tare suka fito exercise d'in wato Saifullah da Khaled, jere suke suna d'an yin gudu kad'an-kad'an suna 'yar hira cikin tsantsar mamaki Khaled ya kalli can gefensa inda yake hango wata kamar Islam wadda suke tare da Riri ,sai ture-ture suke yi duk sun takurawa kansu wannan tana cewa ana tureta wannan na cewa Islam na takata dan kar su wuce junansu. Sake murza idanunsa yayi tare da kad'a kai ya kalli Saifullah tare da cewa.

'”Waccan yarinyar kamar Islam.'”

'”Wacece islam?”

'”Gata can nasan ta a abuja 'yar gidan makocin muce.'”

Mtscew Saifullah yaja tsaki, jin abinda Khaled ya fad'a, wai 'yar makocinsu a can abuja amman shine yake ta wannan fara'ar tamkar yaga wani abun daya shafesu. Kamar ance ya juya Saifullah ya kalli inda Khaled ya nufa kawai sai yaga wannan yarinyar ce da ta bigesa, wane tukukun bakin ciki ne ya tokare masa makogaro? Ya tab'e baki. tare da ci gaba da abinda ya fito dashi har ya nufi gida ba tare da ya tsaya Khaled d'in ba, kasan cewar besan lokacin da zai gama magana da 'yar makocin tashi ba.

A can kuwa Khaled ne yayi musu sallama duk suka d'ago suka kallesa, duk da cewar Islam taji dad'in ganinsa amman sai da taji kunya da nauyinsa, lokacin da ta tuno furta masa buk'atar ya aureta amman ya watsa mata k'asa a ido yayi rejecting d'in buk'atar ta.

Cikin dauriya da kawar da jin nauyinsa da take ji ta zaro ido tare da kama hab'arta tana cewa.

“Kai! Yaya Khaled kaine kuwa?'”

Murmushi yayi yana shafar d'an gemun sa,

'”Nine Islam ashe nan kika dawo shi yasa idan naje gida bana ganinki?''”

Farrr tayi da idanunta tare da d'agowa ta kallesa nan taga shima ita yake kallo irin kallon da yake mata har tayi tunanin ko sonta yake yi a baya shi yake mata yanzu tayi saurin sanya hannunta a kirji tana yatsina fuska tare da turo baki tana cewa.

''Eh wallahi yaya Khaled nazo nan ina hutu dai, sannan ina zaune a gidan uncle d'ina wato gidan su wannan kaifa?''

Murmushi yayi yana kallan Riri wacce ta kafesa da idanu kamar taga sabon abu, ya sosa d'an gemunsa daya fara tarawa tare da cewa.

“Nima nazo gidan uncle d'ina wato dai gidan su wancan..'”

Yayi maganar yana juyawa dan nunawa su Islam inda Saifullah yake tsaye yaga wayam babu kowa cikin jin kunya ya malk'aye hannunsa tare da cewa.

'”Ashe yabar gurin da yake jiran nawa, gaskiya naji dad'in ganinki Islam sosai.'”

“Nima naji dad'in ganinka yaya Khaled, bari mu tafi gida kar aga mun dad'e ayi mana fad'a ko a hana mu yi gaki d'aya, sai mun sake had'uwa Yaya.”

Murmushi tayi tana wasa da yatsun hannunta dan ita har lokacin ta kasa yadda da cewar shifa Khaled ba auranta zai yi ba, gani take kamar yana sonta amman shi sai waskewa yake yi, ganin yadda yake kare mata kallo me cike da ma'anoni masu tarin yasa ta kuma sanya hannu ta rungume kirjinta sabida yadda taga Khaled yana kallonsu tace dashi.

'”Yaya Khaled sai anjima.'”

'”Kai Islam sauri haka? Toh ki bani address d'in gidan da kike watak'ila na kawo miki ziyara wata rana.”

“Okay babu damuwa yaya Khaleed, Riri please ki bawa yaya na address d'in gidan ku yadda zaifi ganewa.'”

'”Okay toh ka bani phone number d'inki sai na turo maka yadda ba zaka manta ba.''”

Cewar Riri domin gabaki daya guy din ya tafi da ajinta babban abinda yake damun ta shine taga kamar akwai soyayya tsakanin Islam dashi duba da yadda taga suna yiwa juna wani irin kallo na kauna da soyayya, but zata san yadda tayi ta b'arar da gwamnatin Islam a wajansa ta shigar da kanta domin yayi mata sosai. Lambar wayarsa ya bawa Riri wadda take sake karairaya jikinta shi kuma duk hankalinsa yana can wajan Islam suna sallama kafin kowa ya wuce gida.

A d'aki Khaled ya tarar da Saifullah yana ta faman harhad'a takardu, Khaled ya fad'a kan gado tare da mirginawa yayi rigingine yana cewa.

“Gaskiya my friend baka da kirki shine ko kajirani mu taho tare.” Saifullah ba tare daya d'ago ba yace dashi.

“Da ban tsayaka ba yanzu waye ya dawo da kai? Ko wad'annan 'yan matan ne suka kawo ka gidan?”

Dariya Khaled yayi domin yasan haushi Saifullah yaji sabida yaga ya kula mata bai san cewar Islam 'yar uwar su bace domin makocinka duk talaucinsa duk kudinsa indai kun zauna tare toh ya zama d'an uwanka, cikin dariyar yake cewa.

“Basu suka kawo ni ba nine na dawo da kaina, sannan dan ka ganni naje wajan su sabida nasan ta ne shi yasa, wallahi yarinyar tana bani tausayi domin 'yan uwanta duk sunyi aure ita kadai ce bata yi ba kuma mahaifinsu yana bada lokaci ne idan matum bai fito da miji ba toh shine yake fito musu dashi a cikin abokansa, Allah yarinyar tana bani tausayi domin da kanta ta buk'aci na aureta ni kuma kaga inada wadda nake so.”

Mtwww Saifullah yaja tsaki wanda yasa Khaled d'agowa yana kallan sa yaga sam ba shi yake kallo ba dan haka yayi tunanin ko da zuciyarsa yake. Shi kuwa Saifullah abin ne ya daure masa kai jin cewar wai kamar yarinyar nan itace take zuwa gurin saurayi tace tana so ya aureta dan lalacewa da rashin kamun kai, shin wai me yake damun mata

Please Login or Register in order to submit comment