Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yinsa,an kammala fenti kawai yarage, abunda yasaka aka dakatar kuma kace kai ba anan zaku zauna ba sai Spain. Yanzu so kake ka ‘dauki yarinyar mutane kuje hotel? Ga manya a gidah, ka naso ka janyo abun da za’aita kananan maganganu ko?”

“Aunty .. Ni fa ko fuskarta an hana na gani, k..”

“Shikenan kawai, Bari zan turo maka ita yanzu sai ku gaysa.”

Dadi kashe Khaled, mikewa Haj Zuwairah tayi ta fita, mintina kad’an sai ga Fatma ta shiga tana sunkuyar da kai ‘kasa. Kasa hak’uri Khaled yayi, yayi hanzari janyota jikin sa yana wani shegen murmushi. Jikin sa sai rawa yakeyi, cikin kunya fatma tace,

“Ina yini..?”

“Ya rouh.! Wane yini kin gasa ni, har ramewa nayi na rashin ganin ki”

“Jiya ne fa kawai love..”

“Say no more! Dole ki karba hukunci.”

Ta shiga kiciniyar kwace jikin ta, ya riko hannun ta, yana sinsinar kamshin jikin ta, hannun sa d’aya kuma na karakaina cikin rigar ta....

*6:30pm*

Zaune Islam take, kanta a ‘kasa tana tsakiyar su Daddy (prof Khaleel) da Ya Bala, da Inna bilkisu, gefe kuma Hansa’u ce da Haj Aysa, can ‘k’arshen ‘kurya kuma bodara Yafendo ce, da alama dai mutuniyar taku ta nisan ta kanta don gudun abun kunya. Sosai aka shiga yiwa amarya Islam fad’an yi nayi bari na bari, kuka kawai take yi tana jan majina, Haj Aysa dake gefe lokaci zuwa lokaci itama take fakar idonsu ta goge nata hawayen. Haka ma Prof Khaleel shima idanuwansa cike suke taf da hawaye.

Haka dai kowannen su ya yiwa Islam fad’a, sosai take kuka, jikin ta har rawa yake yi. Ta rungume Daddy tana kuka yana kuka, sai da Yafendo ta raba su dakyar. Sannan aka komar da Islam sashen Haj Aysa, wanka ta ‘kara yi, ta sanya wata atamfa datasha stones blue, mahaifin Haj Aysa tun na aure shi aka yafawa Islam kamar yadda Aysan ta qudura, ba’ai mata makeup ba amma ba kadan ba tayi kyau cikin royal blue shigar ta, dai-dai stairs Haj Aysa ta hango Islam, da hanzari ta sulale zata gudu don kada su hadu Islam tayi saurin rikota tana kuka, duk mutanen dake wajen sai da suka koka, domin ba kadan ba xasu baka tausayi.

Dakyar dai aka ‘banbare Islam daga jikin Haj Aysa, sannan aka sanyata a mota, suka fara zuwa gidan su Haj zuwairah, gaisuwar surukai, tsabar sonta da Haj Zuwairah keyi rungumota tayi jikin ta, tana shafa bayan ta, kamar ta maida ta ciki haka take jinta, da alama dai soyayyar auta Saifullah ta fara shafar Islam. Sai gud’a ke tashi.

Motoci a convoy suka nufi unguwar Asokoro kai Islam gidan ta, Abbas ke tuka motar da Islam take, gaban motar Helwa ce, baya kuma tsakiya Islam ce, gefe da gefe kuma Hansau da Yafendo, sai sauran motoci dake ‘dauke da ‘kawayen amarya da ‘yan uwan amarya. Yan uwa na kaita suka mata sallama suka tafi bayan sun yaba akwatunan ra’aki da kususuram da aka jere su a drawer, gidan sai tashin ‘kamshin turarukhan wuta yake.

A ‘dakin ‘kasa aka zaunar da Islam, sai kuka takeyi, yan uwa duk sun dare, sai ‘kawaye dake jiran tawagar ango, Ai kuwa ba’a jima ba abokan ango suka shiga, aka tsadance kudin siyan baki suka biya, da yawa daga ciki sun karbi nambobin juna, Riri ma taci sa’a wani ya ‘kyasa ya karbi tata, sai 10 sannan suka watse, duk abun nan Saifullah na mota yana danna waya. Sai da ya mula yasha iska sannan ya fito, sanye cikin yadi kalar madarar ruwa, bai sa hula ba, kwantaccen gashin kansa ya kwanta luf, sai tashin ‘kamshi yakeyi, Abbas dake gefe ya ciro wasu ledoji a bayan boot ya mik’a masa yana jaddada masa da,

“Gashi Mami(Haj Zuwairah) tace lalle na baka, nasan kuma ta sanar maka, My G Allah ya baku zaman lapia ya kawo ‘kazantar ‘daki.”

‘Kwatar ledar Saifullah yayi sai kace fada, Abbas yai murmushi kawai yaja kan motar sa ya fice, Cikin takun ‘kasaita Saifullah ya shiga ciki bakin sa dauke da sallama, kamshin turarukhan wuta suka doki hancin sa, ya lumshe idanu cikeda Jin dadi. Sama ya hau, ya shiga wani ‘daki da ke dauke da furnitures blue and white, murmushi yayi ganin dagaske Mami ashe ta shrya masa dakin sa tamkar na Lagos. Bandaki ya fada yayo wanka da alwala, sallar nafila yayi ya karanta alqur’ani yayi addua ya shafa. Har ya mike akan gado ya tuna ledar da akace lalle yabawa Islam. Dauka yai ya bude tafarko kaji ne da gurasar larabawa da sauce, sai ta biyu kuma yoghurts ne da drinks. Tabe baki yayi ya fita.

Dakin dake kallon inda yake ya shiga batanan, ya bude dayan na kusada corridor nan ma ba ta ciki, ‘kasa ya sauka, kansa tsaye ya shiga ‘parlorn kasa ya murza dakin ciki, can yahangota a gefen gado tana karanta littafin addu’oin 40Rabbana. Ga wani sihirtaccen kamshi dake tashi a cikin ‘dakin. Dama fitilar dim ce saita ‘karawa dakin wani annurin haske, gyaran murya yai, hakan yasanya Islam daga kai ta dube shi, sai kuma tayi ‘kasa dashi tana cigaba da karatun ta.

Cikin takun sa, mai cike da samartaka da nuna isa ya ‘karasa wajen ta, dadda’dan turaren sa na Hugo boss ya daki kofofin hancin ta, shima fa ana sa ‘bangaren khumran jikin ta yasa shi lumshe idanuwa. Ja baya tayi, ya bita sai da suka kai ‘k’arshen bangon ‘dakin sannan ta tsaya tana kauda fuskarta gefe, siririn tsaki ya saki kafin ya dire ledar a gabanta yana mai nuni da ledar,

“Ga shi nan, Mami tace a baki.”

Yana gama fada ya sa kai ya fice, nannauyar ajiyar zucia Islam ta sauke, tana raba idanuwa.
****

_HASKE WRITERS ASSOCIATION_
_HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS_

_YAN UWA MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE, KU MATSO KUSA GA NAKU, HA’KI’KA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WASU DA’DA’DAN LITTATTAFAN MASU TAFIYA CIKE DA;_

_DARUSSA_
_WA’AZANTARWA_
_NISHADANTARWA UWA UBA_
_SOYAYYA...KADA KU BARI A BAKU_ _LABARI KU ZO A DAMA DA KU. _

_ZAFAFA BIYAR DAGA YAN BIYAR NA CIKIN TAURARUWAR ‘KUNGIYAR HASKE, (BATCH B)ZASU ZO MUKU NE DAGA GWANAYEN KU KAMAR HAKA,_

_DAGA TASKAR *MAMU GEE* MARUBUCIYAR TARAYYA A WANNAN KARON ZATA ZO MUKU DA LITTATTAFINTA DADDAD’A MAI SUNA *BURI D’AYA*._

_SAI TASKAR *SAFIYYA ABDULLAHI HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA ZATAZO MUKU DA ZAZZAFA MAI SUNA *DAURIN BOYE*_

_SAI TASKAR HAFSAT RANO, MARUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA ZATA ZO MUKU DA SABO MAI CIKE DA SOYAYYA MAI SUNA *SAUYIN ‘KADDARA*.. _

_SAI TASKAR BILLYN ABDUL MARUBUCIYAR RAINA KAM DA MUTUM DA DUNIYAR SA ZATA ZO MUKU DA WANI SABON SALON SO MAI SUNA *WUTSIYAR RAKUMI* ._

_SAI NI NANA HAFSAT WADDA KUKA FI SANI DA *MISS XOXO,* MARUBUCIYAR NAUFAAL (THE CHARMING) DA SAIFUL_ISLAM, A YANZU, ZAN ZO MUKU DA WANI SABON MAI CIKE DA ‘KAUNA MAI TAKEN, *KAI MIN HALACCI* _


_WANDA DUKA BIYAR DIN ZASU ZO MUKU A SABUWAR SHEKARA ME KAMAWA INSHA ALLAHU (2020). A WATAN JANAIRU, KADA KU BARI A BAKU LABARI. MAI SON DAYA ZAI BIYA 200 NE, MAI SON BIYU 350NE, MAI SON HUDU ZAI BIYA 450 SAI MAI SON BIYAR DIN ZAI BIYA 500._

_KADA A MANTA HAZIKAN MARUBUTAN SUNE:_
_MAMU GEE_
_SAFIYYAH ABDULLAHI HUGUMA_
_HAFSAT RANO_
__BILLYN ABDUL_
_MISS XOXO_

_LOVE YOU ALL FISABILILLAHI🥰❤💋_





_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😻_
_BILLYN ABDUL😘_


*_SHAFI NA 40-42_*

_WANNAN SHAFIN NA KI NE YAYYA NABEELAH 😻❤, MY BIGGEST SUPPORTER💫. ILYSM SIS,MAY YOU BE FOREVER BLESSED🤗_

_nanahafsat.wordpress.com_

Tunda Islam takoma Lagos gaba d’aya cikin k'uncin rayuwa tasa kanta, kullum addu'ar ta shine Allah yasa afasa auren nan nata da Saifullah. Ta matsu ma ayi resuming school don ta cigaba da harkokin ta, Kamar kullum yau ma tana zaune takaicin duniya ya taru ya tsaya mata a ma’kogaro. Riri dake k'asa tahau sama tana ‘yan wak’e-wak'en ta. Ja tayi ta zauna a kusa da Islam tana cewa,

“Wani guy nakeso a twitter, yaron nan yayi, komai yaji nake gaya miki, kyau da kud'i da background abun ba’a cewa komai. matsalar shegen ko following d'ina back yaki yayi, ku...”

“Dan Allah Riri ki kyale ni, can ta matse maku ke dashi, ni meye nawa aciki?”

Bud'e baki Riri tayi ganin har yanzu Islam taki sakkowa daga doron fushin data hau, masifar yau daban, ta gobe daban. Mikewa tsaye Riri tayi tana mik’a had'e da tab’e baki tace,

“Toh kizo dai inji Baba yana neman ki, yace na kira ki yanzu.”

''Daman aiko ki aka yi amman kika tsaya yi min zancen banzar nan.?'' Riri ta tafa hannu tana cewa.

''Islam kece kika d'auki wannan maganar ta banza saboda ke baki waye ba har yanzu.''

Tsaki Islam taja, tana gaba Islam na biye da ita suka tafi sashen Haj Nabeelah matar Ya Bala, wato marikiyar Riri. Shi kadai ne a parlorn yana kurbar kunun gyad'a. Ganin Islam yasanya shi fad’ad’a murmushin sa yace.

“Baba barka da rana..”

“Barkan mu Islam.. Kina lapia?”

“Lapia Alhamdulillah Baba.”

“Masha Allahu... Ammh! Ina wannan matar abokin nawa dana ce miki tana kawo kayan amare daga k'asar waje?”..

“Eh Baba na gane ta.” Cewar Islam kanta a ‘kasa.

“Yawwa toh, ya kirani jiya yake cewa tace kije shagon nata ki zabi abinda kikeso, nashi gudunmawar kenan.”

“Allah sarki! Nagode k’warai.”

“Fareeda ai ke kinsan shagon nata ko?!”

“Nasani Baba..”

“Yawwa ki rakata kuje tare please!”

Kad’a kai Riri tayi sannan suka koma d'akin su ita da Islam. Cikin fushi Islam ta sauya kaya zuwa doguwar rigar A shape ta atamfa mai zanen akwati ja da bak'i ta yafa mayafi akanta, da yake hannun dogone har gwiwar hannunta. Bata d'aura d'ankwali ba amma ta rufe kanta ruf da mayafin. Malam ubale direba shine yaja su zuwa can unguwar surulere dake lagos inda shagon matar yake. Kamar ta maida Islam ciki haka Haj Binta take ta nan-nan da ita, kwarai ta kwanta mata arai har takasa hak’uri sai da tace.

“Yanzu daman Alhaji nada sauran budurwar yarinya be gayamana ba sai yanxu da aka rigamu? Allah yayi rabon wani ce ke da na had’aki da d'ana Mus’ab..”

Murmushi kawai Islam tayi tana jin dama a fasa auren ta da saifullah ayi da Mus’ab d'in watakila shi zai darajata ya bata mutuncin ta na ‘ya mace. Cikin tunanin data fad’a Riri ta zungure ta, nan suka shiga duba kayan, kusan Riri ce ta d'aukar mata komai, ita Islam kasa zab’a tayi. Sun d'an jima suna hira da Haj Binta kafin su d'auki hanyar gidah. Dai-dai wani joint kafin a k'arasa unguwar su Riri tace su tsaya ta sauka, cikin fushi Islam ta dubeta,

“Haba Riri ai kya bari dai mu koma gidah idan yaso sai ki dawo ke, amma ya za’ai mun fito tare kice a saukeki..” Cikin rashin damuwa Riri tace,

“Toh sakko mu shiga tare.”

Harara Islam ta wurga mata, Riri tai murmushi tana d'aga kafad’a alamun kin yiwa kanki, Malam ubale zai ja mota kenan wani bayarabe ya d'an k'wank'wasa masa motar,

“Megida motanka na hayaki..”

“Subhanallahi ya Allah..”

Cewar Malam Ubale, da sauri suka fito daga motar shi da Islam, Riri dake tsaye a bakin k'ofar wajen ta k'araso tana tambayan Malam ubale,

“Meya faru Malam Ubale?”

“Hajia wallahi banduba ruwa ba, shine take hayaki, Kinga har wata roba tafara narkewa..”

Islam dake gefe ta ja ta tsaya a k'ofar joint d'in tana kamo addu’oi a baki. Riri ta kalli Islam ta gefen ido sosai a firgice take, gashi bata san ta b'ata mata Ap data had’a. Cikin dak’ilewar murya Riri ta cewa Malam Ubale,

“To ya xa’ai kenan yanzu?,Kai ma ka dinga dubawa saboda irin haka.”

“Insha Allahu Hajia..” ya cewa Riri kafin ya d'anje nesa da Islam yana rissinar da kai,

“Hajia bari naje na duba baya ko za’a samu bakanike yazo ya d'an duba mana, ayimin afuwa.”

“Tohm ba komi..”

Shine kawai abunda Islam tace, Riri ta k'arasa wajanta tana cewa,

“Mu shiga ciki to kafin a gama gyarawa.”

“Nanma ya isa..”

Kad’a kai kawai Riri tayi alamun shikenan toh, sannan tasa kai ta shiga cikin joint din, takaici duk ya kama Islam na rashin madafa. Ta juya nan ta juya can, haka taita yi, lokaci zuwa lokaci kuma takan saki tsaki. Cikin haka kuwa wani matashi ya fito daga cikin joint d'in cikin shigar ‘balman’ kayan duk a yayyage wai nan gayu ne, rabin wandon ya zazzago ta baya wanda akewa laqabi da ‘ass down’, gashin kansa kuwa a saisaye yake rabi da rabi sak kan zakara. Yana tafe yana wak’a, hango Islam dayai yasa shi sakin lallausan murmushi. Nufota yayi gadan-gadan tayi hanzarin mikewa tana ja da baya-baya dashi, saurin riko mayafinta yai taja da karfi da yake k'arfin ba ‘daya bane hakan ya sanya matashin mai suna 4gig k'wace mayafin Islam sai gashi a hannun sa, neman kare jikin ta tashiga yi, shi kuwa 4gig k'ara gigicewa yai ganin siffar Islam. Cikin sumbatu yace,

“Oh baby pls...”

Riri ganin 4gig bai dawo ba yasata fita waje da sauri, ganin yana neman cakumar Islam dake hawaye shab’e-shab’e duk sai Riri ta rud'e sosai ta shiga yiwa 4gig bayanin Islam fa ba ‘yar hannu bace, amman kememe yaki bada mayafin Islam d'in, yana ganin bakin ciki Riri ke yi masa dan taga zai shana. Dai-dai Lokacin kuma Saifullah da Abbas sunzo shiga wani gidan kallon ball dake kallon joint d'in dasu Islam suke, kamar ance ya juya idanuwan sa suka mai kyakkyawan tozali da Islam da Riri dama wani gardi a kusa dasu, gardin na k’ok’arin yafawa Islam d'in mayafi ajikin ta, alokacin kuma hak’uri 4gig ya shiga bata ganin dagaske ba ‘yar hannun bace bata saba ba, dai-dai lokacin Islam tai murmushin takaici tana kwatar mayafin tana yafawa akanta, Saifullah idanuwan sa suka sake d'akko masa hotan da Islam ke murmushin tana lullube jikin ta da mayafi.

Gaba d’aya sai tunanin sa ya nemi d'aukewa, ashe kallon sokuwa yakewa yarinyar ma gaba d’aya ta zarce tunanin sa. Da kyar yai kwafa yabi bayan Abbas suka shiga cikin gidan kallon ball d'in wanda gaba d’aya hankalin sa na kansu Islam, cikin murya ciki-ciki yace da Abbas,

“Aboki... Can joint din na meye ne?” Abbas dake sipping coke yace,

“Ina fa? Oh wai opposite nan wajen kake nufi? Wani joint ne naga su Dee na zuwa shi da Shambo, Kamar clubbing ne haka ina jin ana d'an shan shisha ne akwai kuma swimming pool awajen.”

Jinjina kai Saifullah yayi yana furzar da iskar bakin sa, hakan ya sanya Abbas dafa kafad'ar sa yana tambayar sa lapia, ganin damuwa kwance k'arara akan fuskar Saifullahin.

“Meyasa ka tambaye ni Aboki? Wani abun ka gani ne?”

Saurin kad’a kai Saifullah yayi alamun a’a, yana k'ak’aro murmushin da yafi kuka ciwo, cikin husky voice d’insa yace.

“Bakomi Aboki, kawai ina mamakin yawan irin guraren nan a Lagos ne, gaskiya sunyi yawa, barin ma dai area d'innan, so suffocating.”

Haka dai suka shiga wata hirar da Abbas, can waje kuwa 4gig sosai ya k'ara bawa Islam hak’uri kan abinda ya faru, Riri ma ta k'ara bata, da kyar Ubale ya samo mechanics suka gyara motar, sannan yaja su suka tafi ciki harda Riri da taji baxata iya zama ba acan. Saifullah daya koma gidah kuwa sakawa da warewa ya shiga yi, yarinyar nan dama haka take? ya ‘dauka son aure da nacin sai taxama matar sa shine burin ta, ashe ashe mizanin tunanin sa kad’an ya d’ebo akanta, harda harkar maza take bi kenan?

“Subhanallah ya Allah..”

Ya furta yana mai dafe da kansa sabida yadda yake sara masa yana barazanar fad'owa. A daren bai kwanta ba sai da ya yanke babban hukunci da zai aiwatar akan Islam inda sukai aure. Islam baiwar Allah kuka sosai ta shiga yi a sujjadarta, tana neman yafiyar ubangiji abisa abinda ya faru d'azu. Nan jikin Riri yayi sanyi lokaci d’aya itama ta mike ta shiga band'aki ta d'auro alwala ta shiga jera salloli..

Shirye-shiryen biki ake yi ganga-ganga daga duk b'angare biyun, nasu Islam dama na d’aya amarya wato Dr Teema, ango Khaled kuwa duk ya matsu so yake kawai a d'aura aure a damka masa matar sa su ware subar k'asar domin visa da yake jira ta fito, kai kace a gidan rik’o yake gaba d’aya tamkar wanda yake akan k'aya haka ya k’agu su bashi amaryar sa, shi kuwa miskilin sarkin fad’in rai wato auta saifullah kuwa, sai abinda aka tilasta shi yayi shi yake, domin abokan sa sun yi shirye-shirye sun shirya lafiyayyar liyafar barbecue yace babu inda xashi, k’arshe dai sai ‘kawayen Islam ne da abokanan nasa sukaje aka d'an gwangwaje duk da ba haka aka so ba.

Da misalin k'arfe sha biyu 12:00pm jirgin 'yan tafiya kano daga Abuja ya sauka a filin jirgin malam Aminu kano dake kano. Kowa kagani sai murna yake da wannan babban budiri da za'ai, 'yan d'aurin aure ne suka fara zuwa inda aka d'aura auren Fatima Muhammad wacce ake kira da Dr Teemah, da angonta Khaled Mommodu Mele, akan sadaki dubu d'ari biyu cif. Dubban mutane ne suka shaida hakan inda da rana mahaifiyar amaryar wato hajia Fareedah Muhammad Abbas ta shirya had'add'iyar liyafa wadda ake kira da mother's Eve. Taro yayi taro, anci an gyatse 'yan uwa duk sunxo kano,

B'angaren su amarya Islam kuwa k'awayen ta na BNA dama na Nile sune suka had’a mata d'an event d'insu na k'awaye na ‘bridal tea party’ , Amarya Islam tayi kyau ba k'arya inda Mamza Beauty ta tsantsare mata kwalliya, kayanta kuwa Hudayya Fadoul ce ta d'inka, gayawa mai karatu irin had'uwar da Islam tayi b'ata Lokaci ne, domin kunsan yadda prof Khaleel yake san Islam da ma Ya Bala, uwa uba autar mata ce, gata ta gaban goshin mahaifiyar Saifullah.

Washe garin safiyar Asabar da misalin k'arfe biyu na rana aka d'aura auren Saifullah Faruk Muhammad da amaryar sa Bilkisu Khaleel Muhammad (Islam) akan sadaki sisin gwal guda d'ari biyu cif, A masallacin central mosque dake Abujan. Domin mahaifin Saifullah yace tunda dai Islam ta had’a zuri’a da kanuri babu abunda zai hanashi yi mata irin al’adar su. Daganan aka yi reception d'an gaske domin anci ansha, ango yayi shiga cikin dakakkiyar getzna kalar sararin samaniya ya d'ora hula zanna bukar gashi yasha takalmin sa batozzi sau ciki dark blue, agogon hannun sa na azurfa da zobe da suka amsa sunan su, kallo d’aya xakai masa ka furta kalmar ‘TubarkAllah’. Duk inda yayi masu hoto na binsa, sai murmushi yake yi kai kace auren soyayya ne.

Cikin takun k'asaita yake tafiya, daga nan suka koma gidah shi da abokan sa yin wanka na biyu dan zuwa gidan su Islam, kafin anjima suje liyafar gidan su Islam d'in da aka shirya ta ‘wushe-wushe’. Domin hatta kayan da zai saka komai irin na al’adar ne, shi abun har mamaki Maman ke bashi ganin yadda take komai a tsare sai kace akansa ta fara aurarwa.

Islam kuwa na can tana kuka, tunda akace an d'aura auren take hawaye domin tasan babu wanda ya isa ya yanke wannan k'addararren auren dole da Allah yayi sai anyi shi. Da kyar tadaina kuka ta koma ajiyar zucia. Hafsat da Hidaya dake gefe kuwa murna suke mata ganin ita kam ta tsallake sirad’in auren sa’annin daddy, zata auri sabon jini uwa uba kuma yaro matashi mai jini a jika. Duk sun wani yamushe duk da yanzu ba laipi suna samun kulawa, amma ba kamar suna gidah ba, domin sai kace wanda sukai shekara goma a gidan aure. Hidaya duk ta yi laushi, Hafsat kuwa idan ba dole ba yanzu bata fiye magana ba, domin dunia ta koya mata hankali. Cikin taushasshiyar murya tace,

“Uhm! Islam ba kuka ya kamata kiyi ba, alwala zaki d'auro kiyi sallah ki godewa Allah ya azurtaki da wannan babbar kyautar..”

Hidaya dake gefe tai murmushi tana jinjina kai kafin tace.

“Wallahi kuwa Hafsat, yanzu da ace ba muyi wasa da rayuwar mu mun cuci kanmu ba, ai da muma samarin kila zamu aura, amma dubemu Islam, ko ba kya son mutumin nan karki tab’a nuna masa da sannu zaki so shi, ki kuma kyauta ta masa sai kiga Allah ya dube ki da idanun rahama yasa ya mato akan ki.”

Islam dake gefe ta dube su kawai tana d'auke kanta, kafin cikin sark’ewar murya tace.

“Ba zaku gane ba, baya so na shima yana min kallon wata k'ask'antacciya, fisabilillahi meye nawa aciki? Wallahi bansan anzo an nema masa aure na ba sai da Yayya Yakolo take fad’a min... ku..” Hafsat ta katseta tana mikewa tsaye, cikin fushi tace,

“Islam ya kamata ace ni da Hidaya mun isheki ishara, kalli yanzu ni wanda aka aura min mai mata biyu fa, daga shi har matan nasa sun haife ni. Kai ‘ya’yan sama sun mugun girme mini.” Hidaya dake gefe ta amshe da,

“Ba gwara ke ba Hafsat, ni fa matan sa uku ni ce ta hud'u, ko a mafarki ban tab’a zaton hakan zata kasance dani ba, sai gashi wanda ya girmewa mahaifi na shine ya zamto mijina, harda rabon d'ansa ko ‘yar sa gashi a k'unshe a marata. Amma Alhamdulillah kukan kurciya jawabi ne ga mai hankali, Tabbas abubuwan da mukai na laipi ada shine muke girbesu yanzu. Fatanmu Allah ya k'ara karb'ar tubanmu yasa hakan shine mafificin alkhairi”

“Ameen..”

Suka fad'a baki d’ayan su, zumbur Hafsat ta mike ta fita daga dakin da alama ta tuno mahaifiyar ta, maganganun da sukai ya taso mata da zaman mahaifiyarta Karimatu a baya. Nan Hidaya ta shiga baiwa Islam shawarwari na irin yadda zatai zamantakewar gidan aure da sauran su. Sun jima kafin Yakolo ta shiga d'akin ta tasa keyar Islam su koma sama.

Wani ruwa mai tashin k'amshi a babban baho Yakolo tasa Islam agaba ta cire kayanta ta shiga ciki, bayan ta fito daga ciki ta sake turarata da wani turaren wuta na jiki, kafin a d'akko mata wasu kaya da sukai kwana da kwanaki ana turararasu a kabbasa. Lungu da sak’o na jikin ta sai da aka shafeta da wasu irin turaruka.. (sirri ne tawan (billyn Abdul) tace karna soma fad'a muku).

Wani arnen komole lace royal blue ta saka mai kwalliyar golden, tasha adon gold hatta mayafinta da takalmin duk Golden ne, ba kad'an ba Islam tayi kyau ga wani sihirtacce kuma ni’imtaccen k'amshi da yake tashi daga jikin ta na shuwa-shuwa-yerwa fato-Chadians, kai duk ita d’aya dai akai mata wannan combo. Light makeup Lee tayi mata, sannan takama hannunta suka sauka k'asa wajen angwaye inda Saifullah ya wani hakimce a zaune yana danna waya.

Ta k'asa-k'asan ido yake duban su Islam dake sakkowa, baki da hanci harda idanuwa haka Saifullah ya baje yana kallon Islam.. ‘Fata barakAllahu ahasanul khaliqeen.’ Shine abinda ya furta ba tare da yasan yayi ba daman k'asa-k'asa ya fad'a yana neman sai-saita kansa, sai yanzu ya lura yarinyar bayan jiki mekyau tana da wani irin sihirtaccen kyau sosai. Ya dubi abokansa yaga yadda suka zuba mata idanu gaba d’aya sai yaji haushi ya kama shi kuma.

Cikin takun sa na isa ya k'arasa ya fincikota zuwa jikin sa, kirjinta ya manna a nasa, take yaji tsigar jikin sa na tashi yarrrr, itama mutuniyar taku anata b'angaran hakan ne ya faru. Cikin rad’a-rad’a kamar irin soyewar nan suke yi ya shiga yi mata magana a hankali kamar zai lashe mata kunnen, gaba d’aya kamshin jikin ta narkar dashi suka yi, k'ok'ari kawai yake yi ganin bai yi wani abun da zai sa a gane yanayin da ya shiga, gashi abokansa da kawayen ta sai tafa hannuwa suke a lamun ya burgesu domin yadda suka yi irin na masoyan nan ne,

“Sam baki yi kyau ba malama... Ga wani kaurin turare dake tashi a jikin ki so suffocating.” Shine abinda Saifullah yake gayawa Islam a cikin kunne gashi ya nanuke ta danma dai ta zama tasa yanzu. Mutsu-mutsun kwace kanta take yi ya sake rad’a mata cewar,

“Don’t you dare create a shameless scene here, abokai na masu class ne basu zubar da nasu ba kamar yadda kika zubar da naki a titi. So karki bawa kanki kunya a gabansu fatana Allah ya shiryeki.”

Yana fad'a ransa na k'ara jagulewa tunowa da yai da ranar da daya gansu da 4gig a joint, mayafinta a hannun gardi tana sakin murmushi. Saurin tunkud’eta gefe yayi yadda ba kowanne zai gane ba sai ita, murmushin takaici tayi ta shiga gaishe da abokan ango, sunata tsokanar ta aka

Please Login or Register in order to submit comment