Join Our WhatsApp Group

BABBAN KUSKURE Complete Hausa Novel Document by BABBAN KUSKURE


BABBAN KUSKURE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 42099



BABBAN KUSKURE

Reading Time: 3 Hours

Added On: 02, Sep 2023

Author: Rasheeda A Kardam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 222.43 kb

File Type: txt

Views: 591+

Download: 229+

Last download: 2 days ago

Description/Story: BABBAN KUSKUREN DANA TAFKA
Na Rasheeda A Kardam
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com





BABBAN
KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Bismillahi rahmanu raheem, dukkan godiya, da yabo,
tsarki da mulki sun tabbata ga Ubangijin sammai da
kassai. Na fara rubuta wannan littafin cikin iko Allah, ya
Allah ka bani ikon isar da sak’o mai amfani aciki, san nan
ka sanya, mutane zasu, nishad’an tu dashi, ta hanya mai
kyau ameen. Pg-1~5 Wani kyakyawan Matashi, mai jini
ajika, sanye yake cikin, kakin sa na Police, kalan blue da
bak’in wando. Kayan sunyi matuk’ar amsan jikinsa,
tamkar dashi aka tsara kayan, ko da na kali wannan guy
d’in. Dogon ne fari sol, yana da faffad’an k’irji, sannan ga
shi da dogon hanci tamkar pencil, yana da k’aramin baki,
ga kuma wasu sexy eyes, d’insa da suka rikitani,
shekarunsa bazai wuce 37 ba. A hankali yake tafiya, falo
ya nufo, dai-dai nan, naji muryan mata tana kiran Indo!
Indo! Indo!. Wacce a ke kira da indo ta fito da sauri, sam
bata lura da Yallab’oi ba, tana yankowa sai jin, garam
sunyi karo, take jikinta ya d’au rawa ta fara dan Allah
kayi… Bata k’arasa ba yasakar mata, wani lafiyayan mari
a fiska. Da gudu tayi ciki don tana matuk’ar tsoron
Haiydar. Shi ko gogan kar-kad’e inda ta tab’a ya fara,
cikin zuciyarshi kuwa, cewa yake”mtss na tsane ki bana
son ganinki, don ba yanda na iya ne. Indo tana shiga, sai
da ta share hawayenta,ta k’arasa cikin d’akin, taje ta
rusuna agaban wata mata, wanda da’alama itace matar
gidan, cikin sanyi muryanta mai dad’in sairaro tace”gani
Hajiya”. Wacce aka kira da Hajiya sai wani yatsina take,
tace”ga hulan Haiydar nan ki kaimasa, ya fita ni bazan iya
tashi ba, cikin tsoro Indo ta bud’i baki tace”Aunty wal….
“Kee yi min shiru umurni na baki, tashi ki kai masa, kina
yar aiki, har zanyi magana kema kiyi. Jikin Indo ba k’wari
ta k’arba ta fito falo, dai-dai koma ciki ya d’auko hulan,
wani kalo ya watsa mata, take yan hanjin cikinta suka
soma rawa, sam bata son had’uwar su, da Haiydar, don
ya matuk’ar tsanata, sam baya son ganinta, Indo kuwa ta
mak’ure ajikin garu kamar munafuka, duk tayi kalan
tausayi. cikin fushi yayi kanta. DEDICATED TO AISHA
MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV
[5/26/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-6~10. Cikin
fushi Haiydar yayi kanta, hularsa ya fin cike tare da tofa
mata yawu, ya wuce abunsa, cikin zuciyarsa na masa
suya, “mtss ace wai matar ka ta sunna, batasan kula da
hakkin miji ba. “Bata damu da duk wani abun da nake
bukata ba, wai sai yar aiki. “Yar aikin ma wanda bata min
ba, sam na tsani ganinta mtss. Yayi tsaki, dai-dai lokacin
ya shiga motar sa, mai gadi da sauri ya bud’e masa
yafita. Tafe yake cikin nutsuwa har ya isa area
Commander, yana shigowa aka fara sara masa, da han
zari ya nufi office d’insa dake sama. Yana shiga na biyo
sa, nima da sauri don na fara aikina, d’an madai- daicin
office ne, d’auke yake da tebur sai kujeran zama, gefe ga
k’araman fridge, da nesa na hango yar k’aramar TV
bango da ke mak’ale, office d’in yayi dai- dai misali. File
d’in da ke kan tebur ya duba, nan ya fara yan rubuce-
rubuce, nan ya d’aga waya yace”hello Sargent Nasir, kazo
ina nemanka a office d’ina yanzu. Wayar ya ajiye ya
cigaba da rubutu, ba’a d’au lokaciba wani d’an matashi,
ya turo qofar office d’in, yana shigowa ya kame kamar
katako tare da buga k’afansa a kasa, hannusa ya sanya
shi a gefen damansa tare da waresu. Cikin girmamawa
yace” Morning sir”. Naji an kira da sir, bai s’ago kansa ba,
yana rubutunsa yace” Morning how is your work?.
Sergent Nasir yace”fine too. Haiday ya ci gaba da cewa”
na duba file d’in case din mutanen nan, kun kaisu CID
ne?. “Eh Sir tun jiya ma aka kaisu. “Ok daman abun da
nake son ji kena. “Zaka ita tafiya. Sergent Nasir ya sake
sara masa tukunan ya juya ya tafi. Haiydar ko aikin da ke
gabansa yayi, bai fito ba sai lokacin Sallah, k’arfe uku da
rabi na yamma, ya kamala duk aikin da zaiyi ya fito ya
shiga motarsa ya nufo gida. Tun a hanya da yayi tunanin
abunda zaije ya tarar tsaki ya farayi, duk sai yaji baya
son komawa gidan. DEDICATED TO AISHA MUH’D
(MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016]Rash
Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-11~15. Indo ko tun
lokacin da Haiydar ya tofa mata miyau, da gudu tashiga
d’akinta, kan gado ta fad’a tasoma rusa kuka kamar ranta
zai fita, a fili take cewa”wannan wani irin rayuwa ne?.
“Mai na tsare masa ya tsaneni?. “Ina da iyayena suna nan
nasan duk rashinsu ba ran zauna cikin wanna k’uncin ba.
“Wayyo Ummi na! Allah ya jikanki, tabbas nayi rashi. “Ina
zansan inda dangina suke na nemesu, nasan su bazasu
tsaneni ba. A hankali ta tashi ta d’auko wasu fotuna, da
wani awarwaro masu kyau, sai d’aukar ido sukeyi,
rungumesu tayi tana kuka mai tsuma zuciya, a haka har
baci ya d’auketa. Kamar ama mafarki takejin ana kiran
sunanta, firgigit tanfarka, aiko taji an sake kiranta, da
sauri ta mike ta b’oye war-waronta da hotunanta, ta fito
cikin hanzari. Cikin isa Falmi tace”kee mai kikeyi da baki
min aiki na ba?. “Kin san Darling d’ina ya kusa dawowa.
“Ke harkina da wani saken da zakiyi bacci a gidan nan?.
“Ko kin manta matsayinki na baiwa ne?. “Mtss na baki
nan da 30 minutes ki gyara gidan nan, kuna in kin gama
kije ki gyara ma only d’akinsa. “Zakiga kayan daya ciresu
ki wanke su tass, kuma karkisasu a engine kinsan bai cika
son wankin…. Sallamansu Xahra da Meesha luv ne
yahanata k’arasa magana. “Oyoyo sis kune haka?. Cikin
sakin fuska sukace”eh mune da mayya. Falmi tace”ni
fushi nake daku ma rabon ku da gidan nan yau kunsan
wata 2 fa. Meesha tace”kawas tuba muke amana hak’uri.
“Sadeey tace” kyaleta kamar ita ta a zuwa mana a kai-
akai. Falmi tace”kudai ku k’araso tukun sannuku da
zuwa. Juyaa tayi ta kali Indo tace”keee mai kikeyi anan
har yanzu baki mik’e kinyi aikin gaban ki ba?. “Ko sai na
b’ata miki rai ne?. Sum-sum Indo ta wuce cikin gida.
Xahrah BB tace”Falmi wacece wannan?. Cikin ko in kula
Falmi tace”house girl d’ina ne. Meesha tace”kee baki da
hankali zaki d’auko wannan zankad’ed’iyar budurwa,
wanda duk na miji mai lafiya sai ya yaba da ita. Sadeey
tace”tayani gani fa, amma kinyi gan-ganci. Falmi tace”kai
banza haka zan barta, yanda nake da kishi ae ba zan so
wani ya rab’i Haiydar d’ina ba. “Muna tare daku bari ku
ga yanda zasu k’are in yadawo. “Kuma bana barinta tayi
kwaliya. “Kai gasalima ya tsaneta tsana mai muni. Xahrah
tace”kee baki san wani lokacin tsana yana dawo soyayya
ba. Falmi tace”kee zan bar Haiydar hakane, san a haka
ma baya son ganinta. DEDICATED TO AISHA MUH’D
(MAMAN ABDUL-SHAKUR) RASH LUV [2:30PM,
9/14/2016] Rash Kardam: [26/5/2016]Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA daga www.hausaebooks.com.ng NA ©RASHEEDAH .A.
KARDAM. Pg-16~20. Shewa sukayi, hiransu ta yaushe
gamo sukeyi. Indo ko kitchen tashiga, ta d’aura girki,
tukun tayi side d’in Falmi, sai da ta gyara ko ina, sannan
ta je bedroom d’in Haiydar ta gyara, ta d’ebo kayansa da
sukayi datti, ta wankesu, tana duba abinci. K’arfe uku da
ta gama komai, ta jera a dining. Falmi tace”ki kawo mana
abincin mu falo”. Sai da da d’an rusuna tukun tace”to
Aunty”. Taje ta zubu musu a cooler da plate takawo,
Falmi cikin isa tace”kee wazai kawo miki ruwan ko ni
zanje ba d’auko?. Indo ta rusuna tace”ayi hak’uri zanje
na sauke abune akan wuta. “Mtss wuce ki d’auko kafin
kiyi abunda zakiyi. Indo ta jera musu komai agun gar
zata tashi Falmi tace”ni zanyi serving d’in ko sai na fad’a
miki?. Indo ta tsuguna ta jera musu komai, tasaka ta
mik’a musu, tukun ta mike ta nufi kitchen, don k’arasa
sauran aikin da takeyi. Sadeey tace”Falmi baki da k’yau,
gaskiya kina juya yarinyan nan. “Irin tsawan da kike mata
ni har ta ban tausayi wallahi. Meesha tace”niko yarinya
k’yau ta min gata black beauty. Falmi ta b’ata rai
tace”mtss dad’ina da ke rashin ganewa, mai maza zasuyi
da bak’ar mace. “Bakijin yanzu cewa suke su Fara ko da
mayya ce, suna sonta. Xahrah tace”Falmi ae bazaki gane
ba, sirrin k’yau yana tattare da bak’ar mace, don fara
inda za’a kwashe farin ba komai zaki gani ba zai tsaban
muni. “Amma magaanan gaskiya Indo ta had’u ba k’arya.
“Sai dai rashin gyara da wayewa ne ya mata cikas. “Ki kali
tsarin jikinta mana, irin shape d’in da maza keso ne. Take
Falmi ta b’ata rai jin an kushe farare, don bak’aramin ji
take da haskenta ba, gani take tafi kowace mace kyau. A
haka har suka cinye abinci su, Indo ta fito ta tattara
kwanuka ta kai kitchen, tana ajiyewa ta k’oma d’aki, ko
zama batayi ba taji k’aran shigowar motar Haiydar. Sai
da gabanta ya fad’i, addu’a tafara yi, sabida duk lokacin
da suka had’u, bata kwashewa ta dad’i. Haiydar cikin
takun isa ya shigo ckin gidan da Sallamansa, su Sadeey
suka amsa, ganinsu yasa ya d’an saki fuska don yasan
k’awayen Falmi ne sosai. Gaisawa suka kafin ya wuce
d’akinsa, yana shiga wani sassayan, k’amshi ya bugi
hancinsa. Ajiyar zuciyzuciya ya sauke, kayansa ya cire ya
nufi toilet, yayi wanka ya fito, k’ananan kaya yasaka,
sabida ga bak’i, da na shan iska zai saka. A hankali ya tako
zuwa falo, Falmi tun da taga ya fito tasan in ba’a yi
serving d’insa ba, zata sha surutu, cikin muryan isa ta
fara kiran, Indo! Indo! Indo dake d’aki jiki sai b’ari yake
ta fito da sauri, ta rusuna a gaban Falmi. DEDICATED TO
AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV
[5/26/2016] RashKardam BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-21~25. Notice
Masu karatu, na cire Sadiya a k’awar Falmi, zan maidata
k’awar Indo, sabida wani dalili, ku kasance da YAR’GIDAN
JARAWA. Falmi tace”ke kwai bakinsan aikinki bane?.
“Bakiga Haiydar ya dawo bane?. “Kije ki zuba masa
abinci. Indo ta mik’e jikinta ba k’wari, sai bari yake, ta
nufi dinning area, Haiydar ko tun da ya hango ta, yayi
yar karamar tsaki, cikin zuciyarsa ko cea yake”wato
falmin bata ji, nace mata bana son aikina tana saka
wannan wariyan taki ji. “Dun taga ina qaunarta da yawa
bana son abunda zai bata min rai. Indo tana zuwa dining
ta fara serving d’insa, sai da ta zuba maza jelop d’in
shinkafa yaji Salad, sai k’amshi yake tash, gaskiya Indo ba
ya bace gurin girki, don ta taso cikin horon aiki, shiyasa
bata samun matsala game da iya girki, gyaran guri. Wani
lokacin in tayi decoration ta gyara ka d’auka, ba ita bace
tayi, wasu daban akayi hayansu sukayi. Sai da ta zuba
masa shinkafan ta tura masa gabansa, hannuta sai rawa
yakeyi, a haka ta d’auko kofin glass ta zuba masa zob’o
drink da tayi, ta d’auko zata ajiyea gabansa, hannuta sai
b’ari yakeyi, bisa tsautsayi ya sub’uce ya fad’i aiko sai
jikin, Haiydar, take rigansa tarine. Nan ganjin cikin Indo
suka soma shooky, hawaye ta fara yi. Haiydar cikin
b’acin rai yaga yanda ta b’ata masa jiki, ransa ya b’aci ya
rasa mai zai mata, mikewa yayi har yazo zai tafi, sai ya
fasa, d’auko juke d’in zobon yayi, ya shek’a mata a fuska.
Ae ko sai cikin idonta take tafara mutsu-mutsu, tana
niman hanyan saukowa, ganin abunda ya mata bai
sheshi ba, sai da ya bari tana lalub’en hanya, ya saka
k’afarsa ta fad’i timm! A k’asa, aiko ba shiri ta saki k’ara
shiko ya mik’e abincin da bai ciba ya kima d’akinsa. Duk
abunda ya faru a idon su Falmi, cikin jin dad’i tace”kun
gani ko ita kanta yariyan tsoronsa take, bare shi uban
gayya da baya son ganinta. Xahrah tace”to ki dai bi a
hankali, don in wahala yayi wahala karta gudu. Falmi
tace”ina zata je wa take dashi a Bauchi. “Ina ga ma la
Uwarta cikinta tayi tazo ta haife ta. “Don tun zuwanta sai
tana cemana ubanta Indo na raye, kulum maganan
d’ayq kenan. Meesha tace”Xahra ya kamata mu wuce fa
yamma tayi. Falmi tace”kai Messha wato ke kike zugawa
ku tafi ko?. Duka sukace yau ai mun dad’e, mu zamu
wuce sai gani na biyu. Falmi tarako su har gate kafin ta
koma ciki. Haiydar ya fito zai wuce Falmi tace”darling
bazaka ci abincin bane?. Ko kalonta baiyi ba yace”nagode
fita zanyi. Ya na fita motarsa ya shiga bai zarce ko ina ba,
sai k’aton katafaren gida, na alfarma, tun daga kan gate
d’in, gidan abun kalo ne, horn yayi mai gadi ya bud’e
masa, ya danna hancin motarsa, cikin gidan, gurin
da’aka tanada don ajiye motoci, nan ya nufa, sai da ya
ajiye motar ya fito. Gidan yana da girma sosai ko da na
kali harabar gidan, zagaye yake da fulawas ja da yelo,
sun matuk’ar k’awata gurin, a hankali yake takawa har
yashiga cikin gidan, falo ya fara tararwa, ko da na kali
falon, gaskiya ya tsaru komai na ciki Silver colour ne da
baki, abun gwanin burgewa. Daga nesa na hango wata
yarinya wacce bazata gaza 17yrs ba, tana danna waya,
farace sol kamar Haiydar, kuma suna d’an kama amma
shi yafita kyau sosai, da sallama ya k’arasa shiga ciki,
Hasna ta mik’e tace” Yaya Haiydar sannu da zuwa. Cikin
fara’a ya amsa mata, zama yayi a d’aya daga cikin
kujerun dasuke falon. Yace”Hasna kawo min abinci naci”.
Cikin tausaya ma Yayanta, mik’e wa tayi ta nufi kitchen,
abinci ta kawo masa, sai da tayi serving d’insa, tukun
koma gefe ta zauna. DEDICATED TO AISHA MUH’D
( MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV
[5/26/2016]RashKardam BABBAN KUSKEREN DANA
TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-26~30. Cikin
zuciyarta ko tana tausaya ma yayanta, wanan wani irin
aurene ace mutum sam bai isa da matarsa ba, ko yasata
abu batayi, ga rashin kunya, ga kin jama’a, Hmm Allah ya
kyauta. Sai da ya gama cin abinci, Hasna ta kale Yayanta
tace” Yaya Ya Indo?. “Ina son yarinyan tana da hankali, ga
kirki wallahi, Hajiya ma tana yawan tambayanta. Wani
harara ya sakar mata, wanda yasata jan bakinta tayi
shiru, a zuciyarta ko cewa take”wai me Indo tayi ma Yaya
ya tsaneta, ko sunata bai son a kira, kuma ni tafin
Falminsa sau dubu wallahi. “Mtss ina ma da itace matar
yayan. Maganan Haiydar ne ya dawo da ita daga duniyar
tunani, da ta luka. “Hasna ina Hajiya fa? “Tana d’akinta.
Mik’ewa yayi ya haura sama. Haiydar na fita Falmi ko
kafad’a ta d’aga, alar ko in kula ta d’aki ta koma,
WhatsApp ta hau taci gaba da chatting da friends d’inta.
TUSHEN LABARI Alhaji Hashim Marad’i, Haifafen d’an
Niger ne, ya kasance mutum ne mai neman na kansa,
Allah yana bud’a masa, a haka har ya auri matansa
Firdausi, bayan aurensu da kwanki ya tattara, yan
dukiyarsa ya baro gari, ya dawo Bauchi da zama, shago
ya bud’e, cikin ikon Allah, kasuwansa ta bun k’asa, Allah
ya sanya ma dukiyar Albarka, nan da nan ya shahara ta
ko ina a garin Bauchi. Ana haka Matarsa ta samu cikin
karkuso kuga kulawa da tattali, har cikinta ya kai wata
tara, ana haka nakuda ya tashi, baiyi wata-wata ba sukaje
Asibiti, nan aka karb’e su, sai d’akin haihuwa. Bata dad’e
sodai ba ta sankato, yarta fara sol, Nurse suka gyarata,
suka dawo gida, ranan suna Yarinya taci sunan Fatima,
Alhaji Hashim ya d’au son duniya ya d’aura ma fatima,
baya son abunda zai tab’ata, Firdausi ma duk d’ayane,
kula ta musamman suke bata, har yarinya tayi wayo ta
girma sosai. Fatima tana da shrkara biyar, tayi wayo ko
ina tana zuwa har sun sata a makaranta. Wani safiya
ranar asabar, anyi ruwa sosai wata mata tana d’auke da
k’aramin ciki, tazo qofar gidan Alhaji Hashim ta zauna,
sai b’ari takeyi, ana haka Alhaji ya fito, ko da ya ganta, sai
yaji ta bashi tausayi sosai. Mai gadi ya kira yace”kaje ka
shigo...


Read / Download BABBAN KUSKURE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album