Join Our WhatsApp Group

TAKARI Complete Hausa Novel Document by TAKARI


TAKARI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 198333



TAKARI

Reading Time: 16 Hours

Added On: 15, Mar 2024

Author: Zainab Idris Makawa ,

Ebook Compiler : Umar Dalhatu

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 703 602 1388‬

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 1.07 mb

File Type: txt

Views: 238+

Download: 815+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: Compiled by Umar Dalha.








✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣
1⃣
👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣
BY

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎 HUGUMA WRITERS🐎
Kir, kir kir kir kir,
fanfom bohle kakeji, Yara ne da matan aure keta diban ruwa a bakin bohol kamar yadda akasaba akowani kauye.
Yarinyace yar shekara goma sha daya ke saman karfen tana buga ruwan yan uwanta biyu sunata faman tarawa suna kwashewa gefe. Dahaka har suka gama ciki duk wani kaya da suka zo dashi gurin.
Wani dan gidan laka suke shiga da ruwan duk rigan jikin su yajike kunsan duk ruwan yana komawa cikin roban da suke daukan ruwan.
Randa ne irinta laka suke zuba ruwan aciki duk bakin randan ya fashe , harda faci akaimay da siminti . akwai shukan Iccen shuwaka a,tsaye gefen randan ruwan .
Inna yar kulu tafito daga cikin dakin lakan da saboda tsufa har ya dan duka kamar zai zube, amma haka yar kulu ke rayuwa acikin dakin tare da yan marayun diyan ta su hudu hafsat fatima mariya sai Abdul wanda suke ce ma datti saboda sunan mahaifin babansu ne akasa ma yaron.
Kai amma yau hafsi kunyi saurin samun ruwa akan lokaci, hmmm inna aikin san wanan aikin yar gidan kice , fadima . Wlh layin su kuburah taci, tace atabau mun riga su bada ashirin din mu dole aka kyale mu, muka diba aida layi ko kusa damu baizoba. Fadima ce ta fado cikin gidan dawani katon bahon ruwa akanta tana haki ataimaka asauke ta.
Inna yar kulu na fada tasauketa, ; haba fadima wanan bahon yafi karfin ki wlh , ai wanan sai ya buda maki gaba ,
bahon waki,ka dauko ne ? Wlh na Asiya ce na dauko ka kafin diba yazo garesu, Don Allah yar nan kibar daukan roba mai girma kada ciwo yakamaki banda kudin kaiki ko wurin mai agangama balle asibitin gari
Dagudu ta koma donta maida roban da ta dauko na ruwa.
Inna tagama kwasan tuwo taba kowa nashi uku kwanon su guda datti nashi daban sai inna ita kadai tsugunne abakin murhu bisa wani dan guntun kujeran katako , tanayi tana kara masu miya a tasu kwanon.
Duk talauci da maraicin su yar kulu da yaranta baisa tai masu sakaci da karatun addini ba dana zamani haka suke zuwa karatusu ,babu mai taimaka masu sai Allah sai yar sanar, saida kamun koko da inna takeyi haikan garin ansanta da wanan sanar basai yaranta sunje yawon talla,ba.
Yau ba akaratun boko sungama aikinsu tunda safe suna sauri sutafi makarantar islamiyar su don malam bugunsu yakeyi idan an makara.
Gefen hayar su ta islamiya su kaga wasu mata su uku a tsaye suna gaisawa , cikin ladabi su hafsat suka gaida matan , suka tafi.
Kai wanan matar akwai karfin hali ,wlh inji Ramatu daya daga cikin matan da ke tsaye agefen haya wakenan? inji ; Gajiye , yar kulu mana matan marigayi sani mai shago ai yaran tane nan suka wuce mu taki bari kowa yadaukar mata ko guda ne,Wai a cewar ta itace zata tarbiyar da diyanta don haka ko aure taki yi waisai yaran sun girma , sunyi aure da farko har andauki yar babban amma saboda nacin yar kulu kan wai sai yarinya tayi ilimi dole akadawo mata da yar ta , yanzu duk dangin ta sun kyaleta da abinta dama mijin ba,asan asalinshi ba, Itace uwa itace uba.

Yar kulu tana da tauhidi azuciyar ta yarda da Allah da kuma duk wani kaddaran da yasamay ta , hakan yasa batasa wa,ranta wani kwadayin duniya ba ita dai akullun taga Allah yabasu abinda zasu ci su sha basai ta tara wani abin duniya ba.
Kwadayinta su samu dan ilimin zaman duniya data lahira, koda sunyi aurene su iya karanta ko yar wasika ce
Saidai mutanen kauyen suna dauka wani girman kaine irin nata , ita wacece da zata hana yaranta talla.
GAJIYE takasa zama ta kasa tsaye yanzu yar kulun da tasani itace da wa"yan nan yaran haka jari gida ba,asan yadda za,a sarrafa suba tawani nacewa wai ita yara na karatu ba,talle wata sana,a kwarara.
Aiko gobe dole in koma kano wurin hajiya in ji yara yan shekara nawa take bukata idan naga da irin su acikin yaran yar kulu tau nikan abin yazo min da sauki wlh basai na shiga yawon bida ba ga abu a gida,,,,,, ,,,,,, ,,,,

🐎 ZEE MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA🐎 🐎WRITERS🐎
[10/3, 14:35] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWa🐎
🐎. HUGUMA WRITERS 🐎

KANO KANO,,,, KANO koda maikazo an fika,,, hmmm inji kanawa .
Gajiye ce zaune saman tabarma an aje mata kwalban coca cola mai sanyi ga shinkafa da miyar naman shanu tanaci, ,,,,,,,
Hajiya mai sharwali nazaune agefenta suna hira ,Gajiye kinsan wancan karon ba abin kware, kika kawo min ba shiyasa banison kara harka dake ,,,,,,,,,
Hmmm hajiya kenan aikinsan wanan karon akasi akasamu insha Allah wanan karon
,a samu matsalaba.
Hajiya mai Sharwali wata matace mai zaman kanta a garin kano , tana harko ki kalakala na bidan kudi,
Cikin irin hakane suka hadu da gajiye a,motar haya, tasamo yan mata guda biyu daga jahar katsina. Gajiye ce ke cewa hajiya wa"yanan yaranki ne kuwa sai take fada mata ai , aikatau tadauko su daga kano . Nan ta dinga ba Gajiye labarin yadda harka tasu take da irin kason da ake ba duk wata dillaliya, hajiya tace saidai wanan karon ita ba dillancin zatayi ba daukan kanta ne zatayi don ita ma zata fara nata harka ce.
Sun, kulla harka da gajiye har ta ke kawowa hajiya maisharwali yan mata daga sashe sokoto.
Tunda gajiye tadawo gida take tunanen hanyar da zata fara bullo ma al,amarin.
Saboda tasan idan har taci nasaran daukan wa,"yanan yaran na yar kulu lalai zata caba so sai
Don ita a,nata haukan duk yaran biyu masu wayo zata kwashe ma yar kulu, taje taci riban duniya dasu. Sam bata damu da halin da yar kulu zata iya shiga ba.

Yar kulu na,ta,tsan kamun kokon ta taji sallama ta ansa ,,,,, Saidai bata gane , kowace bakurwar ba , don yar birnice , "tashigo ba irin matar kauyen , su na majidadi
bane ; wanan "tawaye dayawa
Bayan sun gaisa Gajiye tace nasan diyar kulu bata gane ni ba ko?
Gaskiya ban gane kiba inji Inna ,,,,,, nice Gajiye diyar dada makwabtar ku na kusa da massalancin sarki, a,a,a,aikuwa nagane yanzu kice min abokiyar fada ta itace kuwa.
Nan aka shiga hiran yaushe rabo tsakani,,, inda Gajiye ta labta karyan ai aure takeyi a kano harda yaranta, biyar, tazo ganin gida, Ida takawo tsaraba taba inna , su sabulun waka dana wanki sai manshafawa da su turare da turmin zani guda,,,,,,, da kyat inna ta karbi kayan bayan Gajiye ta nuna bacin ranta . jiki a sanyaye Inna ta karbi kayan tare da godiya .

Sanu sanu shakuwa mai karfi yashiga tsakanin inna da Gajiye don tace ma inna yar kulu sati biyu zatayi ta koma .
Ko yaushe inna tai abinci zata ba hafsat ta kaiwa Gajiye nata , har sati biyu ,yacika ta koma ,Inda ta fito.
Tare da tunanen yadda zata shawo kan yar kulu nan gaba.
Inna yar kulu , nata kokarin kula da iyalenta tarbiyan su da duk wani kulawa da yadace uwa taiwa danta.
Su ko mutanen gari gani sukeyi girman kaine kawai yasa yar kulu sa "ya" yanta yin karatun boko ba talla, sai bakar wahala take yi a,kansu.
Hafsat ta dan girma don duk wani kiran diya mace ya bai,yana mata,
Hafsat bata da hayaniya sosai, ita farace irin farin yaran fulanin kauye na a,sali batada jiki sai gashin kai ja . Idan tana tafiya kamar ta kalle .
Fadima bata kai hafsat fari,ba amma tadan fi hafsat jiki kadan tanada round face , fadima bata magana amma akwai ta da zafin nama tafi hafsat kuzari sosai , ita,ko mariya da datti zubinsu guda.
Mahaifin su yarasu tun da aka haifi datti da wata biyu , yayi hatsarin mota a hanyar shita zuwa cikin garin sokoto sarin kayan tiredan shi.
Tun alokacin rayuwa ta canza ma iyalin marigayi malam Adamu mai tireda danshi, mutumin kirki wanda yasan darajan iyalin shi.
Yazo kauyen dogon daji daga yola ya biyo wani dan uwanshi da suke sanar fata tare daga karshe sai Allah yai zaman shi nan kauyen dogon daji ta cikin jahar sokoto .
Allah ya hadashi da inna sukayi aure shine dalilin zaman shi nan kauyen har Allah ya karbi ranshi.

🐎ZEE MAKAWA🐎
🐎 HUGUMA 🐎🐎WRITERS🐎
[10/3, 14:39] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈KANO TO JIDDA✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣
👣👣👣👣👣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎


Bayan sati uku Gajiye tadawo kauyen dogon daji da sunan tazo bukin wata diyar yar uwanta,
Gidan bukin yacika gwargwadon yadda ake buki a kauye ,
Tuwo ne na shinkafa sai miyar alaihu da kulili , shimata da yara keta kwasa suna ci. Su Gajiye sune kirjin buki manyan yan birni zaune take ta hakince a saman tabarman roba
Akawo mata wanan akawo mata wancan ,,,, Saidai ita duk hankalinta baya guri kofa take kallo taga shigowar yar kulu.
Sai bayan sallah la,asar inna yar kulu ta iso gidan bukin abisa gaiyatar da Gajiye tai mata jiya da dare bayan ta iso harda ankon taimasu , su uku nafitar buki.
Jamma,a da dama wurin bukin suna mamakin zuwan yar kulu wurin wanan buki saboda ita ko haihuwa kayi da dare take zuwa taimaka barka,. Idan kuma aurene za,tazo taima Allah sa albarka ta,tafi.
Yau, sai gashi tazo harda anko kayan da Gajiye taimasu. koda yake mutane sun san akwai zumunci da zaman makwabtaka atsakanin su tun asali.
Anci ansha a,wuri tuwo da zobo mai zafi ko sanyi babu amma haka a,ke ta wasoso
Inna na gefe guda saman tabarma duk a takure take saboda bata saba shiga jamma,a ba haka.
Uhmmmm wai inna "yan mata ne inji Gajiye, tana tambayar yar kulu ?
Aiko suna gida lafiya lau kina dai min rowan yaran nan, yar kulu
A,a,a habadai Gajiye in,banda abin,ki aike uwarsu ce ta yaya zan maki rowar su ,,,,,,
Haba ai,sai Gajiye ta, gyara zama saboda tarkon ta yafara kama wa,
Ainaga ko wurin bukin baki bari sunzo ba yar kulu, ai,kamata yayi a, ce suna nan tunda gani a gari. Cikin kunya da kamala inna ke magana aikinsan basu da lokaci irin haka tunda suka dawo diban ruwa suka wuce islamiya sai gab da magriba suke dawowa,,,,,
Kinga ko basu da lokacin zuwa nan gurin amma insha Allah kafin kitafi zanturo maki su, su gaisheki,,,,,,,,,
Hira sosai mata ke,tayi wurin kamar yadda Gajiye da inna da wasu mata ke gefe guda suna tasu hiran.
Acikin hiran ne Gajiye kece ma inna akwai diyar mijinta zata haihu insha Allah inta haihu zuwa sabon wata zata zo ta,tafi da su hafsat suje mata buki,,,,,,,,,
Dam,,,,,,, gaban yar kulu ya fadi aje birni da yaranta ina sam baizai sabu ba,,,, ko a mafarki ma balle ai in yaranta sunje birni to kafansu kafanta ,,,,,, saboda birni ai a can yara ke lalacewa ,,,,,,,
Gajiye nata magana amma sam inna bataji ba tana can tana tunane a zuciyan ta.
Hmmm komai wayyon ki sainaci kudin diyar ki inji Gajiye acikin zuciyar ta don ta kulla inna tai nisa da tunane kuma fuskan ta ya nuna bata amince ba,,,,,,
Bayan taro yawatse Gajiye taba inna kayan buki wadatacce wai takaima yaranta
Ramatu, Gajiye ta bida don ta taimaka mata da batun yaran agurin...


Read / Download TAKARI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

1 month ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album