Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Compiled by Umar Dalha.








✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣
1⃣
👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣
BY

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎 HUGUMA WRITERS🐎
Kir, kir kir kir kir,
fanfom bohle kakeji, Yara ne da matan aure keta diban ruwa a bakin bohol kamar yadda akasaba akowani kauye.
Yarinyace yar shekara goma sha daya ke saman karfen tana buga ruwan yan uwanta biyu sunata faman tarawa suna kwashewa gefe. Dahaka har suka gama ciki duk wani kaya da suka zo dashi gurin.
Wani dan gidan laka suke shiga da ruwan duk rigan jikin su yajike kunsan duk ruwan yana komawa cikin roban da suke daukan ruwan.
Randa ne irinta laka suke zuba ruwan aciki duk bakin randan ya fashe , harda faci akaimay da siminti . akwai shukan Iccen shuwaka a,tsaye gefen randan ruwan .
Inna yar kulu tafito daga cikin dakin lakan da saboda tsufa har ya dan duka kamar zai zube, amma haka yar kulu ke rayuwa acikin dakin tare da yan marayun diyan ta su hudu hafsat fatima mariya sai Abdul wanda suke ce ma datti saboda sunan mahaifin babansu ne akasa ma yaron.
Kai amma yau hafsi kunyi saurin samun ruwa akan lokaci, hmmm inna aikin san wanan aikin yar gidan kice , fadima . Wlh layin su kuburah taci, tace atabau mun riga su bada ashirin din mu dole aka kyale mu, muka diba aida layi ko kusa damu baizoba. Fadima ce ta fado cikin gidan dawani katon bahon ruwa akanta tana haki ataimaka asauke ta.
Inna yar kulu na fada tasauketa, ; haba fadima wanan bahon yafi karfin ki wlh , ai wanan sai ya buda maki gaba ,
bahon waki,ka dauko ne ? Wlh na Asiya ce na dauko ka kafin diba yazo garesu, Don Allah yar nan kibar daukan roba mai girma kada ciwo yakamaki banda kudin kaiki ko wurin mai agangama balle asibitin gari
Dagudu ta koma donta maida roban da ta dauko na ruwa.
Inna tagama kwasan tuwo taba kowa nashi uku kwanon su guda datti nashi daban sai inna ita kadai tsugunne abakin murhu bisa wani dan guntun kujeran katako , tanayi tana kara masu miya a tasu kwanon.
Duk talauci da maraicin su yar kulu da yaranta baisa tai masu sakaci da karatun addini ba dana zamani haka suke zuwa karatusu ,babu mai taimaka masu sai Allah sai yar sanar, saida kamun koko da inna takeyi haikan garin ansanta da wanan sanar basai yaranta sunje yawon talla,ba.
Yau ba akaratun boko sungama aikinsu tunda safe suna sauri sutafi makarantar islamiyar su don malam bugunsu yakeyi idan an makara.
Gefen hayar su ta islamiya su kaga wasu mata su uku a tsaye suna gaisawa , cikin ladabi su hafsat suka gaida matan , suka tafi.
Kai wanan matar akwai karfin hali ,wlh inji Ramatu daya daga cikin matan da ke tsaye agefen haya wakenan? inji ; Gajiye , yar kulu mana matan marigayi sani mai shago ai yaran tane nan suka wuce mu taki bari kowa yadaukar mata ko guda ne,Wai a cewar ta itace zata tarbiyar da diyanta don haka ko aure taki yi waisai yaran sun girma , sunyi aure da farko har andauki yar babban amma saboda nacin yar kulu kan wai sai yarinya tayi ilimi dole akadawo mata da yar ta , yanzu duk dangin ta sun kyaleta da abinta dama mijin ba,asan asalinshi ba, Itace uwa itace uba.

Yar kulu tana da tauhidi azuciyar ta yarda da Allah da kuma duk wani kaddaran da yasamay ta , hakan yasa batasa wa,ranta wani kwadayin duniya ba ita dai akullun taga Allah yabasu abinda zasu ci su sha basai ta tara wani abin duniya ba.
Kwadayinta su samu dan ilimin zaman duniya data lahira, koda sunyi aurene su iya karanta ko yar wasika ce
Saidai mutanen kauyen suna dauka wani girman kaine irin nata , ita wacece da zata hana yaranta talla.
GAJIYE takasa zama ta kasa tsaye yanzu yar kulun da tasani itace da wa"yan nan yaran haka jari gida ba,asan yadda za,a sarrafa suba tawani nacewa wai ita yara na karatu ba,talle wata sana,a kwarara.
Aiko gobe dole in koma kano wurin hajiya in ji yara yan shekara nawa take bukata idan naga da irin su acikin yaran yar kulu tau nikan abin yazo min da sauki wlh basai na shiga yawon bida ba ga abu a gida,,,,,, ,,,,,, ,,,,

🐎 ZEE MAKAWA 🐎
🐎HUGUMA🐎 🐎WRITERS🐎
[10/3, 14:35] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWa🐎
🐎. HUGUMA WRITERS 🐎

KANO KANO,,,, KANO koda maikazo an fika,,, hmmm inji kanawa .
Gajiye ce zaune saman tabarma an aje mata kwalban coca cola mai sanyi ga shinkafa da miyar naman shanu tanaci, ,,,,,,,
Hajiya mai sharwali nazaune agefenta suna hira ,Gajiye kinsan wancan karon ba abin kware, kika kawo min ba shiyasa banison kara harka dake ,,,,,,,,,
Hmmm hajiya kenan aikinsan wanan karon akasi akasamu insha Allah wanan karon
,a samu matsalaba.
Hajiya mai Sharwali wata matace mai zaman kanta a garin kano , tana harko ki kalakala na bidan kudi,
Cikin irin hakane suka hadu da gajiye a,motar haya, tasamo yan mata guda biyu daga jahar katsina. Gajiye ce ke cewa hajiya wa"yanan yaranki ne kuwa sai take fada mata ai , aikatau tadauko su daga kano . Nan ta dinga ba Gajiye labarin yadda harka tasu take da irin kason da ake ba duk wata dillaliya, hajiya tace saidai wanan karon ita ba dillancin zatayi ba daukan kanta ne zatayi don ita ma zata fara nata harka ce.
Sun, kulla harka da gajiye har ta ke kawowa hajiya maisharwali yan mata daga sashe sokoto.
Tunda gajiye tadawo gida take tunanen hanyar da zata fara bullo ma al,amarin.
Saboda tasan idan har taci nasaran daukan wa,"yanan yaran na yar kulu lalai zata caba so sai
Don ita a,nata haukan duk yaran biyu masu wayo zata kwashe ma yar kulu, taje taci riban duniya dasu. Sam bata damu da halin da yar kulu zata iya shiga ba.

Yar kulu na,ta,tsan kamun kokon ta taji sallama ta ansa ,,,,, Saidai bata gane , kowace bakurwar ba , don yar birnice , "tashigo ba irin matar kauyen , su na majidadi
bane ; wanan "tawaye dayawa
Bayan sun gaisa Gajiye tace nasan diyar kulu bata gane ni ba ko?
Gaskiya ban gane kiba inji Inna ,,,,,, nice Gajiye diyar dada makwabtar ku na kusa da massalancin sarki, a,a,a,aikuwa nagane yanzu kice min abokiyar fada ta itace kuwa.
Nan aka shiga hiran yaushe rabo tsakani,,, inda Gajiye ta labta karyan ai aure takeyi a kano harda yaranta, biyar, tazo ganin gida, Ida takawo tsaraba taba inna , su sabulun waka dana wanki sai manshafawa da su turare da turmin zani guda,,,,,,, da kyat inna ta karbi kayan bayan Gajiye ta nuna bacin ranta . jiki a sanyaye Inna ta karbi kayan tare da godiya .

Sanu sanu shakuwa mai karfi yashiga tsakanin inna da Gajiye don tace ma inna yar kulu sati biyu zatayi ta koma .
Ko yaushe inna tai abinci zata ba hafsat ta kaiwa Gajiye nata , har sati biyu ,yacika ta koma ,Inda ta fito.
Tare da tunanen yadda zata shawo kan yar kulu nan gaba.
Inna yar kulu , nata kokarin kula da iyalenta tarbiyan su da duk wani kulawa da yadace uwa taiwa danta.
Su ko mutanen gari gani sukeyi girman kaine kawai yasa yar kulu sa "ya" yanta yin karatun boko ba talla, sai bakar wahala take yi a,kansu.
Hafsat ta dan girma don duk wani kiran diya mace ya bai,yana mata,
Hafsat bata da hayaniya sosai, ita farace irin farin yaran fulanin kauye na a,sali batada jiki sai gashin kai ja . Idan tana tafiya kamar ta kalle .
Fadima bata kai hafsat fari,ba amma tadan fi hafsat jiki kadan tanada round face , fadima bata magana amma akwai ta da zafin nama tafi hafsat kuzari sosai , ita,ko mariya da datti zubinsu guda.
Mahaifin su yarasu tun da aka haifi datti da wata biyu , yayi hatsarin mota a hanyar shita zuwa cikin garin sokoto sarin kayan tiredan shi.
Tun alokacin rayuwa ta canza ma iyalin marigayi malam Adamu mai tireda danshi, mutumin kirki wanda yasan darajan iyalin shi.
Yazo kauyen dogon daji daga yola ya biyo wani dan uwanshi da suke sanar fata tare daga karshe sai Allah yai zaman shi nan kauyen dogon daji ta cikin jahar sokoto .
Allah ya hadashi da inna sukayi aure shine dalilin zaman shi nan kauyen har Allah ya karbi ranshi.

🐎ZEE MAKAWA🐎
🐎 HUGUMA 🐎🐎WRITERS🐎
[10/3, 14:39] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈KANO TO JIDDA✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣
👣👣👣👣👣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎


Bayan sati uku Gajiye tadawo kauyen dogon daji da sunan tazo bukin wata diyar yar uwanta,
Gidan bukin yacika gwargwadon yadda ake buki a kauye ,
Tuwo ne na shinkafa sai miyar alaihu da kulili , shimata da yara keta kwasa suna ci. Su Gajiye sune kirjin buki manyan yan birni zaune take ta hakince a saman tabarman roba
Akawo mata wanan akawo mata wancan ,,,, Saidai ita duk hankalinta baya guri kofa take kallo taga shigowar yar kulu.
Sai bayan sallah la,asar inna yar kulu ta iso gidan bukin abisa gaiyatar da Gajiye tai mata jiya da dare bayan ta iso harda ankon taimasu , su uku nafitar buki.
Jamma,a da dama wurin bukin suna mamakin zuwan yar kulu wurin wanan buki saboda ita ko haihuwa kayi da dare take zuwa taimaka barka,. Idan kuma aurene za,tazo taima Allah sa albarka ta,tafi.
Yau, sai gashi tazo harda anko kayan da Gajiye taimasu. koda yake mutane sun san akwai zumunci da zaman makwabtaka atsakanin su tun asali.
Anci ansha a,wuri tuwo da zobo mai zafi ko sanyi babu amma haka a,ke ta wasoso
Inna na gefe guda saman tabarma duk a takure take saboda bata saba shiga jamma,a ba haka.
Uhmmmm wai inna "yan mata ne inji Gajiye, tana tambayar yar kulu ?
Aiko suna gida lafiya lau kina dai min rowan yaran nan, yar kulu
A,a,a habadai Gajiye in,banda abin,ki aike uwarsu ce ta yaya zan maki rowar su ,,,,,,
Haba ai,sai Gajiye ta, gyara zama saboda tarkon ta yafara kama wa,
Ainaga ko wurin bukin baki bari sunzo ba yar kulu, ai,kamata yayi a, ce suna nan tunda gani a gari. Cikin kunya da kamala inna ke magana aikinsan basu da lokaci irin haka tunda suka dawo diban ruwa suka wuce islamiya sai gab da magriba suke dawowa,,,,,
Kinga ko basu da lokacin zuwa nan gurin amma insha Allah kafin kitafi zanturo maki su, su gaisheki,,,,,,,,,
Hira sosai mata ke,tayi wurin kamar yadda Gajiye da inna da wasu mata ke gefe guda suna tasu hiran.
Acikin hiran ne Gajiye kece ma inna akwai diyar mijinta zata haihu insha Allah inta haihu zuwa sabon wata zata zo ta,tafi da su hafsat suje mata buki,,,,,,,,,
Dam,,,,,,, gaban yar kulu ya fadi aje birni da yaranta ina sam baizai sabu ba,,,, ko a mafarki ma balle ai in yaranta sunje birni to kafansu kafanta ,,,,,, saboda birni ai a can yara ke lalacewa ,,,,,,,
Gajiye nata magana amma sam inna bataji ba tana can tana tunane a zuciyan ta.
Hmmm komai wayyon ki sainaci kudin diyar ki inji Gajiye acikin zuciyar ta don ta kulla inna tai nisa da tunane kuma fuskan ta ya nuna bata amince ba,,,,,,
Bayan taro yawatse Gajiye taba inna kayan buki wadatacce wai takaima yaranta
Ramatu, Gajiye ta bida don ta taimaka mata da batun yaran agurin innna.
Bayan buki da kwana daya Ramatu ta shigo gidan inna ,
kai kai kai maraba da Ramatu ke ce , yau agidan namu,
Nice yar kulu hanya ce tabiyo dani nace bari nashigo in maki yaya gajiyar buki .,,,,,,
Aiko nagode wlh
Bayan sun zauna andan yi hira ,Can Ramatu ta kawo zancen zuwa birnin yaran inna.
Aiko yar kulu kiji
dadi wlh, Gajiye yar birni zata dauki diyanki zuwa birni da ma ace nice aida yanzu nafara kuri agari ,,,,
Take innna ta canza fuska aiko Ramatu tashiga aiki zuga ,,,,,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎

[10/3, 16:22] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎


Zaune yar kulu take suna cin abinci da yaranta.,,,,, Yau ma kamar kullun nasiha take masu akan zaman duniya.
A duk yanayin da suka tsinci kansu su dinga hakkuri da duniya don duk abinda kai hakkuri zakaci riban agaba,,,, Fadima ta dago kai ta kalli mahaifiyar tasu tace inna koda an zallunce mu kina nupin kada mu rama sai muyi hakkuri,,,
Kware kuwa inji inna ko baki son Allah ya rama, maki, ne da zaki rama da kan ki ????.
A,hankali tadago ta,kalli inna tace,Inaso tafadi a sanyaye.
Murmushi inna tayi ta kauda kai so da kauna da tausayi yaran nata yakara shiga zuciyar ta, Tundai fadima wace tafaye zafin acikin su,,,,,
Daidai wanan lokacin itama Gajiye tana cikin mawuyacin halin da matsinancin tunane a kano,,,, tana tunane hanyar da zata bullo ma inna ,,,, Don tasha Alwashin wanan karon intazo dongon daji da yaran inna zata dawo kano.
Saboda lokacinda sukayi alkawari da hajiya mai sharwali ya kusa cika.
Muskudawa tayi tare da gyara zama dan taji dadin tunanen. Ahaka har barci ya kwasheta bata gama tunanen taba.
Kwana biyu tana shirye_shirye
Komawa, dogon daji, har barci take rasawa don tsantsar tunanen yadda zata riski yar kulu.

Dogon Daji

Karfe uku na rana tasauka garin, don ,haka gidan, Ramatu tanufa kafin taje gidan su, don jin yadda abubuwa ke tafiya ta fannin, Ramatu.
Saida safe Gajiye tai sallama gidan inna,,,,, inna nadaga cikin daki tana sallah walha tadanyi gyaran murya, alamun sallah a ke yi.
Cak taja ta tsaya kamar mara gaskiya a,tsakar gida,,,, tana dan waige ,waige har idonta yakai ga dan guntun kujerar innna dake gefen daki jingine... Tsab tabi gidan da ido tana kallo tana wani yatsune fuska azuciyar ta tana fadin ,,,, kai dadina da kauye kenan wlh,.
Komai nasu na tsafta ne ji randan ruwanta duk da sun tsufa amma an wani lulube shi da wani marfi mai fadi gidan gashi na lakane amma jiko ina tsab,,
In a gida nake aiko tashi banyi ba yanzu balle har inyi gyaran wuri.
Motsin dataji shi yasata dagowa da sauri takai diban ta akofar dakin .
Hakan yai daidai da fitowar inna a,daki a,a,a lalai marhabin mutanen birni ne yau a garin namu .
Cikin sakin fuska da murmushi suka gaisa cikin natsuwa.
Inna ta koma daki tashinfida tabarma mai haske tace bisimillahgag shigo daga ciki,,, batare da bata lokaci,ba Gajiye ta shiga suka kara gaisawa abisa al,ada irinta bahaushe idan kai bako gaisuwa kusan biyu akeyi,,,,,
Hira sosai sukeyi na yanayin lokaci,,,,,,, A cikin hiran tasa Gajiye ta sako zancan daukan yara.
Saida inna tanisa sanan tace, a gaskiya Gajiye bawai bani son yaran nan su, gusa, kusa dani bane,aa,Kinsan amana suke gare ni Allah yai ma mahaifin su rasuwa, batare da nasan asalin gidan su ba,. saidai zuciyata tana fada min cewa insha Allahu zasuga danginsu koda kuwa bani raye ne.
Saboda hakane yasa nake kokarin ganin nabasu ingattancen rayuwa,.
Saida gajiye ta gyara zama tace inbada abinki yar kulu ai zuwa kawai zamuyi sudanga inda nake kwana biyu indawo dasu.
Kinga aiko watan wata rana su zasu kai kansu inda nake don zumunci ko?
Shiru inna, ta karayi tana nazari maganar gajiye acikin ranta.
Gajiye kibari sainayi shawara da yaya na malam sale duk abinda yace zakiji kafin ki wuce. Nakuma gode da kulawar ki,,,,,,
Malam sale yayane ga inna, "Saboda haka kamar yadda inna tace haka tayi tasamu malam sale ta fada mai duk yadda sukayi da Gajiye shiru malam sale yayi yana nazarin maganar da yar kulu tazo masa dashi .
Can ya nisa yace tau yar kulu mutum yazu ba abin yarda bane , Saidai kuma ita Gajiye din ai ina ganin ta gida ce koma dai maiye aibazata wuce nan ba.
Cikin murya mai rauni Inna tace tau yaya duk abinda kace insha Allah haka za,ayi.
Malam sani ya lura inna batason tafiyan kokadan,,, Sai yace kiyi hakuri diyar kulu addu,a zamu Allah yakai su lfy yadawo muna dasu lfy tace ameen
Inna tace zata koma sukayi sallama ,Sai dai shi malam sani yasan cewa inna bata amince da wanan tafiyar ba,,,,, tausayi Gajiye da bata taba haihuwaba yakeyi kuma gashi har ta taya diyan " yar uwan shi idan har bai bada baki ba Gajiye bazataji dadi ba,,,
Dasanyi gwiwa inna ta dawo gida .


🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
[10/3, 16:28] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment