Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarage karan tv,
Yasa kai yafita zuwa masallacin unguwar inda Shek Abdullaraham bin, Inus,, keba da salla, wanda duk ke wanan uguwar yana jin dadin limancin wanan bawan Allah,,,

Barcin da baifi awa biyu ba da,dan wani kai,,,, nayi, nafarka,
Zubur na mike,daga barcin, inda naji marana yai min karfi kamar na hade dutse,,
Ko kari nayi natashi,Wanka nashiga nayi,
nafito bakin mirror naje nadan dubi kaina naga nawani ramay kamar wace tayi wani dogon jinya
Sallah na fara gabatar wa ina zaune ina addu,a abinda yafaru dani dazu yafado min a rai,
Cikin mamaki nadan motsa kadan lalai ba shakka sheriff udeen din, mune yabani magani na,
To a ina yasamay shi sai kuma natuna ai shine ma yakaini asibiti a birnin madina kuma yai min komai,a lokacin har naji saukin jikina
Oho,,, ,, hmmm watau wanan mutumin ,Don tsananin kulawar shi bai manta da lokacin yin period dina ba,ke nan yake nufi ko may
Wa,iyazu billah,, ashe duk wani motsi nawa yana kula dashi kenan,,
Da wanan tuna nen natashi zuwa cikin gida don in gabatar masu da dinner dinsu,
Saboda har yanzu ina dan jin jikina marana ban iya tafiya sosai,
Amma ya zan iya hada ido da sheriff din namu,,
Ko da naje falon kowa na falon zaune cikin dabara nake komai, na hada ma anty nafisa nata, nazo gefen da yake don in hada mai sai yace min yau bazai ci abinci ba in bashi juice kawai sai tea da zai sha anjima, kawai,,,
Tsayin da nadan yi don in saurari bayanin shi, yasa marana ya kara kullewa wuri guda sai wani irin azaba ciwo ke kokarin taso min,
Cikin hikima nadan yi dabaran barin wurin,
Muryan shi naji tun ban wuce ba yana cewa idan nasan cewa banda lafiyane inje inkwanta mana
kada in jawa kaina matsala tunda ba kullun ne mutun zaiyi lafiya ba,
Inkuma har ciwon ya matsa min ne inje inga likita ko za,a san may ke damuna,,,
Wayancewa nayi na,ce mai kainane kemin ciwo kawai, zai fada min zuwa anjima
Dadabara naja kafana zuwa cikin dakina,, yabini da kallon tausayi
Ina shiga dakin na haye gado na ,
Na dunkule wuri guda kamar yar mage duk kafana nashige dashi cikin jikin na nade wuri daya,
Saida nadan samu barci kadan a,hakan bandade ba na farka don ina son in dan fita, in karsa aikina
Ina zuwa Falon shiru yayi bakajin motsin komai sai karar naurorin dake aiki a falon,
Kayan tea da yace zai sha na hado mai acikin wani dan karamin ture,
Nakai bisa tebur din cin abincin su na aje,
Saida na kusa gama abinda nakeyi a bisa tebur din,
Na,hango shi zaune can wani dan corner da aka kebe afalon , bakowa ke zuwa wurin ba ,sai shi,
Don koda nazo gidan nafara aiki saida almustapha, yai warning dina kan zuwa wanan gurin,
Glass ne aka kewaye wurin dashi sai wasu kujerun masu taushi da tulin takardu, akwai alkur,ani mai girma da sauran litatafan addini ciki, sai computers iri iri,
Nikan shiga sau daya a sati don gyara wurin,
Ashe shi tun dazu ya gurin yana tura sako a computer wa mr William,
Koda zai fito saida suka kwashi artabu da nafisa kancewa, gaskiya ita bata yarda duk dare a ce mutun sai ya fita,,,,
Ba wani kulawa tsakann miji da mata hankade ta yayi gefe yafito abin shi yabarta tana mita,,,,,
Ita abinda bata sani ba shine bata cikin rayuwar shi sam don jinta yake yi kamar ba mace ba,
Shi duk da bai taba taraiyya da wata mace ba a,duniya sai ita,
Yansan labarin mata yakaranta komai a cikin wani, littafin
Mai suna, Surar ya mace na wani shahararen balarabe marubucin addini, musulunci, wanda ya, wallafa duk yanayin kowace irin mace,
Ita ko nafisa tadauka bai fahinci komai gamay da ita,ba
Tunda tanaganin tasha gyara wurin mamanta kafin tazo duk wani sadda baru da kayan mata an hada ta dashi,
Shiko anashi ban garen
Biyayya kawai yake wa tsohon shi kanta saboda ya fuskanci cewa baban nashi nason wanan hadin auren,,,,

Daga inda nake tsaye na hage shi, zaune yamaida hankali ga abinda yakeyi,kuma hankalin shi a kwance yake aikin
, bai,man san cewa, ina cikin falon ba alokacin,,,
Hankalin shi duk ya,naga computer shi,
sai yaji a,jikin kin shi cewa bashi kadai ke a falon ba
Da akwai alaman mutun a falon, baigama tune ba,
yaji motsi a bayan shi lokacin yasan cewa na shigo falon,
Daidai lokacin da nake aje cup din da zai sha tean cikin dan karamin tiren da na hada mai kayan tea din ciki,
Naje in juyo haka sainaga mutun gaba na tsaye,
saida nadan firgita, saboda tsoro, nadan waiga inda yake zaune naga tabas shi din ne a gaban nawa,
Kalo guda nai mai na,kauda ido na gare shi, saboda rigar barcin dayasa cotton ce tana nuna mai surar jikin shi waje,
Muryan shi naji yana fadin keda baki da lafiya may yasa kika fito yin aiki idan natashi shan tea din ai zan kira nafisa ta hada min,
Ki koma kawai ki,bar shi koni da kaina zan hada,,, , ba musu na juya don dama daurewa nake duk banjin dadi sam,
Nafara tafiya naji muryan shi yana cewa kin ko ci abinci
kai na kada mai alamar a,a
Batare da yakara magana ba naga yafara hada kayan tea din da na aje mai asaman tebur, din ,,,,,, tea mai kauri ya hada min ya miko min yace inje insha
Ya miko mi magani, yace Kuma in,tabbatar da nasha shi yanzu kafin in kwanta,nasamuace tare da godiya,,,
Nabar falon a duduke zuwa dakina,
Tausayina yakara kamashi, don harga Allah yana tausaya wa wanan yar yarinyar da aka sako ma,duniya ta yi rainon ta,,
Tunda nasha tea din da maganin da aka bani sai naji marana, da ya kulle min tam yadan sake sosai har nadan ji saukin ciwon
wani barci mai karfi ya kwashe ni, a hakan ,,
Bani na farka daga barcin, ba sai daidai lokacin da ake ta kokarin kiran sallah asuba,
Dama daidai wanan lokacin nake tashi, koda agida nake don fara ayukan mu, yau da kullun,,,,
Jina nayi cikin yanayin bako tare dani watau period yazo min, hakan yasani ni kara yin lankwas bisa gadon,
Da kyat nasamu natashi zaune na rarafa zuwa bayi don in,tsab tace jikina,
Bayan nafito sai na tuna cewa aiko nasiyo kadan pad ranan nan da mukafita da anty nafisa
Shinake ta nema cikin dakin tunda nasan cewa ban je dashi gidan hajiya ba,
Turo kofan akayi duk da ina cikin wata duguwar rigan da zura bayan fito wana wanakan,
Saida naji kunyan ganina hakan da yayi ba wani saya jiki,.
Yajikin yace min nace mai da sauki ledar dake hannun shi ya,miko min, yace min ina wanan ne kike bida,
Ledar pad dina dana sayo da muka fita nida NAFISA
Juyawa yayi yana ce min indinga kula da rayuwata tunda ni kadai nasan irin wahalar da nake sha,
Wayyo Allah kamar in shige cikin kasa don kunya kila yafi minti goma da fita ban iya daga ko kai ba balle in cire kafana,
Saida naji alamar bakona zai iya zubowa anytime nai saurin kai ma ledar kalo,
Tabas ledan kadan pad din da na siyo ne, ranan,
Haka nadaure na dan shiya jikina tsab cikin nasa wando da rigar jeans don gudun wahala,
Abokiyar aikina ce ta shigo dakina da ture a hannun ta ,
Kayan tea ne acikin shi sai sauran abin karin kumalo
Nai,mata godiya tace min sheriff ne yace akawo min nan kuma insha magani na,
Daga haka bata kara cewa komai ba ta wuce abinta,
Tundaga wanan ranan ban kara yarda mu hadu da sheriff ba ko a cikin gida
Saima muka fara wasan yar boya da shi yana sane da nufi sarai amma yakamar bai gane ba,,,
Yai tafiya zuwa Riyadh don dama yafi zama can din saboda aikin shi akusan can yafi yawa
Yanzu daine ma da su,ke kokarin bude wanan mai,ai,katar ta Abu Abdallah,
Shiyasa yake dan yawan zama cikin garin makka so sai,
Duk kwanakin da yayi bai gari cikin dadi da walwala nayi su, ban shakar komai,
Daga anty Nafisa kawai nake dan samun takura wani lokaci, don tana da yawan sa aiki,
Amma dai ba laifi ina ina jurewa da takurar ta,

Yau aiki yai muna yawa don saida muka gama abincin dinner sai anty nafisa tace muna wai bata son wanan saidai muyi mata wani mara nau,yi taci,
Don haka dole muka koma girka wani
duk da marance yayi muna, amma bai hana mu yin sauri ba,
Mun,gama komai muna jerawa a table ,ina dan wake ,wake na na larabci ,
Sai kawai hancina ya sanar min da akwai mutum abayana don fitinanen kamshin turaren sa, da ya gauraye falon,
Waigawa nayi kadan don in,tabbatar ko da shi din ne,
Don koda bai nan gidan namu baidaina kamshin sa ba tankar yana gari,
Ina waigowa naganshi tsaye yana kokarin karba waya hannu shi rike da briefcases din shi,
Wayan yake karbawa amma hannkalishi naga reni ,,,, ganin hakan danayi yasa nataka a hankali har zuwa inda yake nakarbi dan briefcase din nashi cikin ladabi ina mai sannu da zuwa,
Koda nabada baya ido yabini da shi yana mamakin yadda yaga nakara girma cikin dan lokaci guda,
Dai lokacin yakare wayan shi yana kokarin sa wayar a aljihu yadaga kai gefe anty Nafisa ce tsaye tana kallon shi,, cikin mamaki,,,,

[10/4, 14:31] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story


Koda suka hada ido da Nafisa sai ya wayan ce zance saboda gudun zargi,
Yace mata kidiba fa karamar yarinya tafiki hankalin ,
Ke ko gaisuwa baki iyawa mitun ,
Tace au to anan zan gaishe ka a gaban yan aiki,
Bai ce mata komai ba ya haura sama, abinshi,,
Yau kusan kwana biyu da dawowan Sheriff Ahmad daga Riyadh,
Babu zaman gida yanzu sam gare,sh,
Don tunda yadawo aiki sukeyi tukuru, don kusan komai na kamfanin su ya gama haduwa ko,
Yana zaune a office din shi,sai ga abokin shi Yusuf da suke zama tare a kasar saudiya tun zuwan shi kasar suka hade da yusuf din
Shima karatu yazo yi daga kasar ghana,
Halinsu yazo daya shine suka kulla abota,
Allah kadai yasan sirin su,
Shi ya aika ma Yusuf din yazo yaga sabon ma,aikatar da suka hada, wanda tallafin ABU Abdallah ya taimaka masu komai ya hadu,
Inda shi Ahmad din ne zai kula da duk wani aiyuka na kasa shen, biyu saudiya da Nigeria,,,
Yusuf yanu farin cikin shi sosai yayi mai addua da fatan alheri a rayuwan ,
Office din suka koma bayan sundan gama zagayawa cikin company.
Zaune yake saman kujera irin da ake samu a kowani kayataccen office,
Hannu yasa ya zuge nicktie din wuyar shi gadan,
Yadauki daya daga cikin lemon gwangwanin da aka aje, masu, agaban su,,
Saida ya dan zuki lemon yakai diban shi ga Yusuf wanda ke kokarin diban dabino a cikin wani dan plate,
Yusuf din ne ke fadin bamuzo dai munga madam ba har yanzu,
Ina fatan bakayi fushi ba damu,
Don dama mun yi magana da sauran Friend's cewa zamu hadu karshen wata mu kawo maku ziyara,
Saida yadan juya kujera tukun sanan yace ai ba wani matsala,,,
Kafin Yusuf yaci gaba da maganar shi, sai shi Ahmad din ya tare shi da wani zance,
Wai ya batun form din danayi ma gana ne,
Duk da Yusuf yagane abokin nashi bai son zan cen da sukeyi ne shiyasa ya basar da ita,,
Yace mai Af, kaga ko na manta dasu cikin mota, na fa
An samo form din har ma guda uku, don dama biyun da kai requesting suna bukata sai nayi sa a aka bani uku,
Idan mun fita sai inbaka su,
Sunda jima suna hira gamay da wuraren aikin su, dakuma kasa shen su,
Yusuf din yai haraman komawa don a madina yake zama shi,
Tun bayan gama karatun su nan yasamu nashi aikin a wani makaranta,, yana koyar wa,zaman shi sai yafi karfi a madinan,
Sun mike lokaci guda sun musabi,a Yusuf din ke ma Ahmad magana akan yayi kokari ya rike amana
Don sanin halin shi dayayi kan ko bai son abu zai iya hakuri yayi abin,
Don haka ma yasan cewa ko wanan auren na abokin nashi ba,ra,yin shi bane ,
Don tunda suke baitaba jin yai mai zancen wata mace ba saida zancen
Tsohuwa dana mahaifiyar shi,
Sai ko kwanaki da yai mai zancen yana son form din makarantar su don ya siyawa sister dinshi,,,
Kafin su rabu saida suka dan tatauna so sai kan zancen,,,,

Yau a gajiye yadawo gida, dom haka yana dan bukatar hutu kadan,
Wanka yayi kafin lokacin sallah yayi ya wuce masallaci bai dawo wa sai an idar da sallah isha,i,
Acikin shigar jalla biya fara kal, mai yar guntun hannu yake,
Zaune yake saman kujerar yadan kishin gida kadan kafanshi mike a saman wani dan stol dake gaban kujerar, ,,
Hannu shi guda ya sa ya dafe kan shi, kamar wanda kan shi ke mai ciwo,,,,
Nasan cewa idan yana cikin wanan irin yanayin bai son damuwa sam
Saboda nataba, yi mai katsaladan watara naganshi zaune irin,hakana nadinga buruntu da kayan da nake jerawa a dinning har cup ya fado ya fashe,
Aiko ya mike tsaye ba shiri, naji ya ce Ya, Subahanallah,,
Kofa yanu min da in fita falon ,
Nikuma ina kokarin nuna mai cewa zan kwashe glass din da yafashe, ne
Wani uban tsawa yadaka min ban san lokacin da bar falon ba, don tsoro,
Ina zan yarda wanan katon yamake ni,
Saida nabari yafita nadawo na kwashe glass din ina yi ina waigen hanyar shigowa,
Shiyasa yau dana ganshi a hakan nake taka tsantsan da aikina,
Hankalina na ga abinda nakeyi sai kawai , ban san cewa anty NAFISA ta shigo falon ba,
Jin muryan shi kawai nayi cikin wata irin tsawa yake magana Idon shi ya yi ja alokacin ,,,
Yace Nafisat nafada maki tun jiya Umurni na baki ba wai uzuri na ce ki kawo mini ba ina fatan kin gane,
Yadda yai maganar shi ya ba kowa dake falon a,lokacin, tabbacin ba alamar wasa acikin zancen nashi,
Da sauri ta juya rai bace ta shige dakin ta yabita da harara,
Muda ke tsaye a gefe wani irin mugun kallo ya watso muna,
Yamike yabar falon cikin bacin rai shima,
Nikan ko a jikina don nasan wanan fadan manya ne, kuma mata da miji,
Dakinta na shiga don in gabatar mata da abincin su na dare,
Waya nasamay ta tana yi cikin fada, take magana
Yanzu ummi kamana zaice wai tunda zai yi baki dole sai naje kitchen da kaina na shirya masu wani abincin alfarma, irin ta mu ta gargajiya, wai yan aikin shi basu iyaba
Yo ni ina zan iya girki ko na mutun biyu bale na mutun fiye da ashirin,,,
Gaskiya saidai yaji kunya amma na fada mai cewa bazan yi komai bani,
A bangare wace take cewa ummi hakuri naji tana bata , tana cewa abinda zaki samu lada kuma zai jidadi kila ya baki kudi masu yawa a sanadin hakan,,,
Duk hakkurin da ake bata bata yarda ba sam dom tace ita bata da matsala akan kudi dashi don ko ma may tace tana so zai siya mata, ne,,,

Niko tunda naji wanan hirar ta nafisa sai na dan shiga halin damuwa don nasan cewa koma su waye zasu zo suna da matukar mahin,manci a gareshi,
Don haka na kudiri aniyar zan fidda shi wanan kun yan isha Allah,
To saidai matsalar ban san wani rana bane bakin zasu zo muna,
Almustapha ne yafado min a rai,
Nasamay shi yana shirin fita,
Da dan saurin nakarasa inda yake, shiko yana gani na sai yadan dakata min,
Bayan nagaishe shi ne nake tambayar shi don Allah ko yasan ranan da bakin Sheriff zasu zo,
Yace min aibanda gobe ne zasu zo abokan sheriff ne da da matan su, da suke zaune nan kasar saudiya sune zasu zo ziyar shi don suga amaryan shi,,,,,,,
Naidai nasamu almustapha yai min bayanin komai a cikin hikima,
Najidadin jin wanan bayani sosai duk da bayanin yazo min a kuraren lokaci,
Banshiga cikin gida ba direct wurin su Rugaiyya na nufa,
Naimata bayanin komai acikin tsanaki ba mu bata lokaci ba maka kama shirye,shiyen kayan da za mu bukata wurin aiyukan,
Tun wanan, lokacin ban samun zama gida ina nan ,ina can, sai zirga zirgan nakeyi kawai,,,

Duk da ya lura da cewa ba wani shiri da nafisan kewa bakin nashi , hakan baisa yadauki wani mataki ba,
Ido kawai yasa mata don yaga gudun ta,
Azuciyan shi kuma,yasan abinda ya kulla zai matan nadaukan fansa,
A,na mu bangaren bayanin da mustapha yai min na taron abokin shi guda da sukaje wani dan kasar mali
Shi mukayi amfani da shi muka dan can za namu salon,,,,,
Washegari, tunda safe muka tashi masu gyaran gida nayi masu yin girki suna yi,
Nai decoration din wani fili dake cikin gidan da duk wani abu da ba hause ke gyara gida dashi,
Hjy laila ce ta taimaka muna da duk wani abinda zamu bukata,
A fanin abinci munyi masa, da miya tuwon shinkafa da miyar ganye, tuwon alkama da miyar kubewa,danye, danbun shinkafa yaji carvege, sai pepper soup nakifi da na kayan cikin rago,
Sai fura da nono mai kauri wanda yasha sanyin fridge,
Ga kunun tsamiya da sugari, har da shimkafa da wake da salad,
Komai an shirya gwanin sha,wa, Idan kagani sai ka dauka ko agida Nigeria ake wani buki ,,,,,,

Tunda ya iso haraban gidan yaga canji sosai har takai idon shi ya hango mai haraban da muka gyara inda za a ci abincin
Batare da ya nufi gurin da aikai decorating din, ba ya wuce cikin gida direct
Ya mai jin dadin hakan da yagani
Itako tana zaune falo tasa wani material, ja,dinkin shi yadan matse mata jiki,
Ta bayan ta yazo yadan rugumay ta kadan saboda farin cikin abinda yaga tayi don sai yau yadan fara cire shakkun ta da yake,
Godiya da taji yana mata yasa tatsaya sororo tana, kallon shi cikin mamaki,
Kafin yai wani magana itace tafara magana,
Tace ban fahince ka ba fa habibi,
Murshi yadan yi yajawo zuwa cikin jikin shi yana fadin wanan surprise din haka,
Tace na may ke nan fa, na taron bakin da kikai muna,
Tadan daga hannu ta alamar aa bata da masaniya ita,
Cikin mamaki ya ke kallon ta takara cewa wlh ban san may kake magana ba aikai
Ture ta yayi daga jikin shi rai bace,
Idan bake bace towa yayi wanan aikin ,cikin ikon Allah dai dai lokacin na shigo falon cikin shigar irin ta hausawa
Atamfa ce zani da riga koriya da dan ratsin flawer yello cikin jikin atamfar dinkinta yadan matse min jikina dan dagwas,,, sai gyale dana dan yafa yellow akai na
Da kagan ni, Duk alamar girma ya dan bayana min, dan kuguna yadan ciko cif cif ,kirjina yadan kunburo alamar dai nadan kosa komai na girma ya baiyana sosai ,ajikina,
Ban ko kula da su ba ina kokarin nuna wani dan center carpet da za,a dauka zuwa waje
Kallo duk suka bini dashi na mamaki,
Sai a lokacin nagan su tsatsaye,,,
Batare da wani damuwa ba nadan gaishe su cikin girmawa,
Nacigaba da abin da nake yi abina,
Da mamaki yabar wurin zuwa sama inda dakin shi yake,
Yau gezena,shadda yasa mai ruwan chuculate,, dinkin tazarce ne ,,,sai hula yar zanna bukar yar asali da yakafa akan shi ,,,,agogon company rolex yasa a hannu shi takalma bakake, suna wani irin kashe ido,
Yusuf ne yabugo mai waya cewa gasu nan sun iso ,
Cikin fara,a nake taron bakin zuwa cikin katafaren falon mu, daguda guda sukai ta iso wa gidan har suka gama zuwa,
Saura mutum guda ya rage baizo ba, wanda naji suna cewa Ali baba ,, wai ai baida iyali anytime zai iya iso, daga yamal,,,
Agaskiya duk wanda yazo wanan yar walimar taron amaryam Sheriff din mu ya yaba da irin tarbon da akai mai sosai,
Zirga zirga nake tayi cikin jama, don gabatar masu da abin tabawa ,,
Gefen mata daban na maza daban amma

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment