Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dayin wani mugun abinda ba daidai ba,,,,
Wanda ninasan cewa ina iya kokarina wajen kula da mutuncina da inna tace min inkula dashi lokacin da zanbar gida,,,,,
Acikin tunanen naje bayi nayi duk yadda tace min inyi nagama nadawo,,,
Muryan Rugaiyya naji tana cewa kici abinci fadima za,abaki maganin ki kisha,,
Dataga kuka nakeyi shine tashiga rarashina tana fada min cewa ai bakomai bane duk macen da takai lokacin yi batayi ba to tabbas wanan mace bata da lafiya ne,,,
Hakadai taita kwantar min da hankali har nadan sake jikina na dan ci abinci,,,,
Tundaga wanan lokacin banyarda mu hada ido da sheriff din mu Ahmad sam don wani irin nauyin shi da kunya nake ji,,saboda yasan lalurar da nake ciki,,,,
Abinda ban sani ba ashe ba wanda yasan ko may yasamay ni,agidan
Don yasan cewa wanan wani sirine mai nauyi ba,abinda kowa zai sani bane,,,,
Daya koma gida kuma ce masu yayi ai zaki nasha da yawa shiya ja min ciwon ciki,,
Hjy tsohuwa ta nuna mairo da ido tace wanan ja,irar yarinyar tasa su shan shi jiya saida nai masu magana akan kada su sha tarin alawal danaga sun sayo
Amma basu ji ba, saida suka sha abin su,,
Yanzu gashi kin jawa yarinya wahala,, saboda ke kin saba da sha tun a,gida
Mairo tashi , tashige daki tana magana ciki,ciki hjy tace ja,ira fito waje mana ki fada inkin isa,,,,
Hjy mama da takaici duk ya ci ta azuciyan ta,,,ko magana bata samu yi, ba don dama bataso azo da hjy tsohuwa ba wanan tafiyan
Ta,sone su zo su, kadai da ita da Alhaji da yan matan da take riko, kawai
Saiga hjy tsohuwa ta tubure masu akan sai tazo ta ga dan lelenta Ahmad,,,
Kuma duk ta gane nufin hjyn waidon kada suzo su cinye ma Ahmad kudin shi,,,
Tunda anki bari mamanshi tazo da yan uwan shi, shine kulun korafin hjy tsohuwa,,
,,,,,
Nasamu sauki sosai don inka ganni bazakace nice mai rashin kafiyan ba,,
Saboda duk yadda ake kula da mutum nasamu kula daga wayan nan mutanen kirkin masu arziki da sanin ya kamata,,,
Sun maidani tankar yar uwan su ta jini,,,,,,
Ashe bell din company da sherrifudeen din mu ke aiki su ne zasu biya duk kudin da aka caje ni a asibitin,,,,,,
Lokacin da za sallamana yayi ,
Aka sallamay ni nadawo gida,,,
Hatta Alhaji lawal zannah yayi farin ciki da dawowana, saboda ya nuna muna farin cikin shi fili da dawo na,,,,,
Hajiya tsohuwa taimin fadan cewa in kula da lafiyan jikina in,daina shan zaki tunda gashi saboda zakin da mukasha har saida nayi ciwon ciki kamar zan rasa raina,,
Acikin zuciyar mu nida Rugaiyya muka gane cewa sheriff din mu bai fada masu ko may yasamay ni ba har nai ciwo, watau ya boye min sirina,,,,,,
Gefen dayake na,kalla nakoyi sa,a muka hada ido dashi cikin kunya da alamar ko in kula anashi bangaren kowan mu ya,kauda idon shi ga,dan uwa,,,,
Washe gari da safe jinin ya tsaya min banga komai,tun da,daren har zuwa, da safe yau,,,,,
Nasamu Rugaiyya a kitchen tana aikin abin karyawan mu na,fada mata,
Tadan yi murmushi ta dafani tace kwana uku ke nan zaki dinga yi fadima,
Aiko kinyi sa,a,,,,
Taimin bayanin yadda zan tsarkake kaina bayan nagama jini,,



Mun shirya komai duk kayan mu anyi parking,
zamu koma makka zuwa marance yau insha Allah
Dama rashin lafiya na yasa suka kai har wanan lokacin,basu koma ba,,,,,
Hjy tsohuwa tace min sai na kaita tayi ziyarar ban kwana a Rauda,,
Cikin shirin mu nida ita muka fito don mu samu motar da zata kai mu massalacin,,,,,
Akofar gidan namu muka hadu da sheriff din mu Ahmad ,
Da baban shi Alhaji lawal da hjy mama,
Ido suka bimu dashi almar tanbaya ina zamu a fuskan su,,tunda sun san cewa yau za,a wuce,,
Hjy tafada masu zan kaita ziyara ne kafin mutafi tana son tayi ziyarar bankwana a Rauda,
Wani irin mugun kallo sheriff din mu yai min saida na tsargu da wanan kallon
Kayan dake hannushi yamiko min alamar in kai mai ciki,gida,,
Lokacin da nazo ansan kayan sai ya sausauta, muryan shi,,
Yake ce min cikin larabci nida banda tsarki shiga massalaci shine zan bi hjy zuwa massalaci,
Saida naji kamar in,dauke wuta saboda kunya,,,
Akunyace idona akasa nace mai nayi tsarki yau insha Allah don har nayi sallah asubah,,,
Cikin rashin yadda yasa yashiga ciki don ya tambayi Rugaiyya,,,,,
🐎 ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:14] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣7⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS
MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Cikakkiyar nutsuwa da wadatar Ruhi ya tabbata ga mutumin da tunanen laifukansa ya hana shi hangen laifin wani,,,,,


Masoya na asali ko yaushe Maman Nasiba, Mamam Ayman, Sahura Ismaeel ,Anty Batu,ul, sister ,Zainab Ibrahim ,Maman yahy musa ,Anty Hadiza, Ibrahim, maman Rufaida,Anty mariya sb da Anty hafsat yusuf
Fatan Alheri gare ku da karewa lfy da duniya,,, tare da duk sauran yan huguma group👏👏👏👏


Almost true life stor


Allah yadawo da mu makkah lafiya, sai dai tafiyan marance, mukaiyi sai,cikin dare muka iso garin lokacin duhu yayi sosai,
Saboda tafiyan na marance ne kuma ba gudu mu,kekayi,ba, tafiya ce ta hankali kwance,,,,
Saboda haka agidan sheriff din mu muka sauka da muka iso, dole, a nan zamu kwana da su,,,,
Sam ban so hakan ba na so a,ce muntafi gidan kodan inga hajiyan mu,, wace na bari ba lafiya,,,
Dakin hjy tsohuwa muka kwana kamar yadda ta bukata,
,tsohuwa mai albarka ga sanin darajan dan adam,,,

Mun samu gidan na sheriff din mu, ba laifi an gyara ko ina, tsab,
duk da munyi tafiyan kwana biyu,,,
amma wa yanda akabari gadin gidan sunyi kokarin ,sosai komai neat muka samay shi kamar akwai mutane,,,
Don haka bamu sha wani wahala ba gurin gyarawa gidan da muka iso,,,,,
Yau, Saura kwana uku bakin mu, su koma gida, Nigeria, shiri kawai suke tayi, kowa ana mai parking din kayan shi,,,
Tun da muka,iso na so mutafi gida a wanan lokaci, don ina ganin mun shigo garin makka sai naji ina son mutafi ,,
saboda hankalina yana wurin hajiyan mu,
Amma Hakan bai samu ba don shirin tafiyan da ake tayi,,na bakin mu ,
Wanda agaskiya banso rabuwa da su ba musan man hjy tsohuwa,,,,
Ga jamila da mairo sun sani gaba sai na kaisu shagon,, Top ten sun sawo kaya let's one,,
Dole a haka nadaure na raka su,shagon Top ten din ,,dake kan hanya sharmansoor,, naso ace natafi gida tunda safe wlh,,
Muna shiga shagon naga duk sun rude sun ma rasa wanda zasu zaba ,aciki,
Magana nayi da walk services na shagon nace yanuna muna inda zamu zabi kaya na kware ,
Sunyi sayayya so sai agurin
Kudin da tso huwa tabani in kara mata kaya itama na sawo mata abubuwa masu kyau da ma,ana,,,,
Saida kusan duk sayayyan ta na yan mata ne ita ma,,, sai kuma jallabiyan maza masu kyau da sayo mata,,,
Muka koso kayan mu niki niki muka dawo gida dashi,,,
Ko ,da muka dawo,gida, duk yadda naso nabar gidan kafin dare yayi hakan bai samu ba gareni
Don,hjy tsohuwa tace sai nakaita tayi dawafin ban kwana, a Ka,aba,,,,,
Sai dare muka dawo kuma cikin daren nan nabiyo hanya ni,kadai saboda Rugaiyya tace baza tabi hanya ba cikin dare don kada,,,yan, bagaladi su,kamata,
Mutane jefi, jina ne a unguwar tamu,,
Duk da mutane sun fara shigewa gida saboda dare daya dan soma yi,,
Hakan bai hana wasu makwabtan mu su gane ni ba,,,
Wata makwabciyar mu ne anace da ita,lamilami ta fara ganina, tace min fadima ce nace eh,,,
Yo ance muna kun gudu kunbar hajjiya mana,,
Ban,bata ansa ba nawuce cikin gidan mu kai,tsaye,,,,
Su ,Sukaina ne zaune suna dan ciye ciyen su sai Yumma da ke wanki a gefen famfo,
Ido suka bini dashi suna mamaki ina nafito cikin wanan daren , haka,
Don kusan sati kenan ana cigiyar mu agari,
Don, inda duk san,sanin takari yake, anbada cigiyar mu,,,,, saboda suna zaton mun gudune munbar hjy wanda yin haka yana jawo takari irin mu,kanana matsala,
Don da mutun ya gudu yabar uban gidan shi gara yan bagaladi su kama ka,,,
Ana cikin kururuwan mun gudu nida Rugaiyya
Sai gani nadawo gida hankali kwance abina, batare da alamar wani tashin hankali ba,,,
Ban tsaya ta kansu ba don nagane nufin su,
dakin hajiyan mu na fada kai tsaye,,
Kwance take cikin wani irin mugun yanayi wanda ko kai waye dole ta baka tausayi,,,,
bata iya dagawa daga kwance, da take,,
A,firgice nanufi inda take kwance, na rugumay ta, ina kuka
Ina,cewa hajiya may yasa may ki haka kika zama haka cikin lokaci guda,,,
Ina mai,daga muryana, Cikin kukan nake cewa duk a rasa wanda zai kaiki asibiti sai abarki haka,,,,
Yumma ce ta fado dakin tana cewa fadima ai na sayo mata yan kwayo yi na sha kuma ina bata abinci,
Ko yumma bata fadi ba,
Dama nasan cewa ita kadai ce zata iya dan kula da hajiya, cikin su,,,,
Dan sauran hajiya bata da wani daraja a idon su yanzu ,
Saboda sun girma kuma idon su ya bude,
Su anasu wautan suna ganin cewa hakan da sukeyi ma hajiyan shine daidai saboda ai itace tafara cutar mu tun a gida,, Nigeria,,,,,,,
Sun kasa yarda da kaddara cewa Allah yariga yanufi sai mun zo,, munyi wanan bautar koda da kafane sai munzo kasar saudiya munyi takari,tunda hakan na cikin destiny din mu,,,,,
Na juya wurin yumma nace taci abinci kuwa tace min tunda rana ba kuma ba sosai ba,,,,
Dama kudin da Alhaji lawal zannah yabamu a madina don muyi sayayya muma,,
yana ajikina don haka fita nayi zuwa,
wani shago can kasan mu inda ake saida kayan gasawa iri iri na ci da sha,,,
Naje nadan siyo mata dan abinda nasan zata iya ci,,
A cikin daren na gyarata tsab tare da taimakon yumma, ,don su sauran ko kallo ban ishe su ba,
nabata abinci taci tasha maganin da yumma ta sayo mata,,,,,
Tana kwance Gefen kafar ta nazo nadan zauna ,ina kokarin bude inda nasa kudi don in kidaya su.
kudin wanda,ke cikin jikina ko zasu i,she mu zuwa asibiti gobe,,,
Yumma kuma tana gefe tana, cin sauran abincin da hajiya ta rage,,
Muryan hajiya naji kasa kasa tana cewa ina muka je kwana biyu bamu gida ina Rugaiyya,
Ban boye mata ba nace mata madina mukaje ziyara tare da iyalin Sheriff din mu, da suka zo daga Nigeria,,,,,,
Shiru tayi tunda Maganar dama na dole ne
daga hakan bata kara cewa komai ba,
Saidai ajiyar zuciyan danaji tayi ,ahankali, ta gyara kwancinta
Dama tun da nake kirga kudin da ke ajikina dan zamu tafi asibiti da su da safe ,naga mari da sukaina suna min wani kallo, kasa kasa suna magana,,
Nasan cewa suna iya sace kudin in, nai barci,,
Aiko haka din ne, ina cikin barci, gefen hajiya kwance dama na faki idon su na canza ma kudin wuri,,
Cikin barci naji ana lalabata caraf na rike mata hannu nace lafiya,mari ce
Saicewa tayi wai tana bidan wani abune data aje daidai inda nake kwance,
Duk da nagane nufinta sai,kawai, na,gyara mata don ta diba abin,
nikuma daga haka barcin da ban koma ba ke nan,,,
Tashinayi na fara gyara muna gida da duk wani abu da yakamata muyi, amma suka yi don son kai,,,

Tunda safe muka ziyarci asibiti da ni da hajiyan ,mu
Allah ya taimake ni muka ga likita da wuri saboda mun fito da wuri daga gida,,,,
Bayan yan aune aunen da a,kayi wa hajiya aka gane cewa jininta ya hau sosai , kuma tana sakaci da shan maganin da likita ya dorata akai
Don haka tana bukatar aimata wasu allurori har da karin ruwa, aciki,,,
Tafiya nake yi, a,hankali,
Yan kudin da nazo dasu asibiti nake ta kirgawa saboda ina ganin cewa baza su ishe mu abinda ake bukatar yi ma hajiya, ba,,,
Jinayi nayi karo da mutun agabana har yan kudi nawa suka zube kasa,
Banko kalli wanda yasa nazubar da kudin kasa ba ,hankalina ya ga kudin magani,, kada iska yajamin su su rage yawa,,
Duka wa mai shi yayi yana tayani kwashe kudin ,,,,,,
Saida ya miko min kudin na karshe ne da,yataya ni kwasa,,
,Sainaji kamshin turaren Sheriff din mu Ahmad,
Da sauri kuma cikin mamaki hankalina, yadawo,nakai dibana gare shi,
Shidine kuwa ,shikuma daidai ,
Lokacin yana mikewa tsaye daga tsugun nin da yayi don kwashe min kudin,,,,,
Hjy tsohuwa tana a bayan shi tsaye da a,lamar bata jin dadin jikin ta,, ita ma,,
Batare da yakalleni ba ya ja hannu hjy don suwuce zuwa wurin likita,,
Sai alokacin hajiya ta ganni don dama batasan cewa nice ba,
Tanbayana takeyi cikin mamaki ko ya akayi na biyo su asibitin tunda safe, wa ya fada min suna asibiti,,
Shiko sheriff din mu azuciyar shi cewa yakeyi,
wanan yar wahalan kuma ko may yakawo ta nan tunda safe yarinya kamar aljanna duk inda kabi zaka ganta,
Can kuma yatuna kodai jinin nawa bai tsaya bane, shine nazo ganin likita,,,
Muryana dayaji cikin hausana da ba daidai ba Ina fadawa hjy tsohuwa cewa nakawo hjy ta asibiti ne,,, saboda nadawo na samayta bata da lafiya sosai,,,
Saboda girmamawa da nuna kulawa sai naji bazan iya wucewa inbar su shida hjy tsohuwa ba
Kodan irin so da kaunar da yar tsohuwar ke gwada min,,,
kawai sai na tsinci kaina da,bin,su abaya har zuwa office din likitan da zasu,,gani,
Bayan anyi ma hajiya booking din likitan da zata gani, ,,,
An,yi komai har a lokacin muna tare dasu sam na ma mance cewa da hajiyan mu muke, a,asibitin,,,
Takardan maganin dake hannu ya buka ta ,,,
Na bashi yakarba yadan diba kadan
Sai naga yawuce inda ake saida magani kai tsaye, batare da yai min magana ba,,,
Maganin yasiyo min harda ledar ruwan da za,akara ma hajiyan mu,,
Inda take ya buka nakai shi,
hajiya na zaune gefe ta wani, makure gefe, duk ta mokade kamar ba itace hajiya mai sharwali ba,,
Koda mukaje, Kallon banza naga yai mata,
Wanda saida na tsargu, sosai da irin kallon
duk da tana cikin ciwo baisa ya tausaya mata ba, saboda irin mugun halinta na cutar da kananin yara,da tayi batare da sanin iyayen su ba,,,
Sai kawai naji banji dadin yadda naga yana kallon hajiya ba,
Saboda aiko da nake tallaka kuma ,yar aiki shi ai, yakamata a mutunta min yan uwana nima,,, ,,,
Sam ni bansan cewa Rugaiyya ta fada mai abinda ke tsakanin mu da hajiya ba.
Tun,a madina
Ko yanzu yasan cewa nice zan walaha shiyasa ya taimaka mata,,,
Allah yataimake ni hajiyan mu tadan warwale sosai don duk ledojin ruwan da akasiya ta zuke su ajikinta
Sai bayan kwana biyu aka sallah may mu daga asibitin
Taji sauki sosai wlh,,,
Kusan kwana biyar nayi banje aiki ba, ina fama da hajiyan mu,,,
Yau danaga taji sauki sosai nace mata ta kula da jiknta zanje wurin aiki don kada in yi laifi da yawa,,
Gashi nadauki lokaci ban je ba ban kuma dauki permission ba,,,

Saida na tunkari gidan sanan natuna cewa hajiya tsohuws sun wuce kila,
Gashi bamu samu yin bankwana cikin dadi ba ,
Ina can asibiti da hajiyan mu

Ashe basu samu wucewa ba a lokacin don jikin hajiyan da likitan ta ya dan tsay da su,
Ina shiga nanufi inda Rugaiyya na take aiki ,saboda mun kwana biyu bamu haduwa , ko ,agida sau guda tasamu lokaci taje asibiti diba hajiya,,,
Abincin da tagama nataya ta dauka zuwa babban falo don mu jera,
a saman table,
Amma azuciya na ina mamakin yawan abincin da ta dafa,
Sam ban kawo cewa bakin mu suna nan ba,,
Ina shiga falo naga su, mairo da jamila suna game tunda safe haka,
Dakin hajiya tsofuwa na nufa don ina kewanta dama sosai
Dan shakuwar da mukayi kwana biyun nan yai yawa,,,
Sheriff din mu ne zaune dakin tare da ita sai,dai fuskan shi da alamar ba, sauki amaganar da sukeyi,, da hajiyan fuskokin su a daure yake,,,
Cikin sauri na juya zan koma waje,,,,,,,

🐎 ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:14] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
3⃣8⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Murna farin ciki da annashuwa, sun tabbata ga duk wani mutumin kirkin da tunanen, Hisabi ya hana shi tara dukiya ta hanyar haramu,,,,

Gaisuwa da jinjina gaduk wanda ya fahinci ma,anar wanan littafin

Almost true life story


Gefen hajiya tsohuwa nadan rusuna nagaishe ta cikin ladabi da biyayya,
Zandaga in wuce take tambayana jikin hajiyar mu, inda take ce min taso zuwa ta dibata ,
Saidai itama din likita yace tadan samu hutu wuri guda shiyasa bata zo ba,,,
Sheriff din mu dake zaune gefe ya mike a lokacin zai bar dakin
Barin zancen namu tayi taci gaba da magana dashi ,
Tace kadaiji abinda na fada maka,
Ka maida hankali kaje Nigeria ka diba ma haifiyar ka da yan uwan ka ,zama anan kashare kowa ba zai maka ba,
Kasan cewa itama uwar ka tana da hakki akanka don tana bukatar ganin ka ,
Saidai don bata magana ne amma nasan cewa azuciyar ta bata jin dadi
Sanan batun wa yan nan yan matan sam ban yarda da inkara hada zuri,a da yan uwan Amina ba
Yadda mahaifinka yake tauye haka akeso kaima a,tauye min ka ,
Shiyasa ina jin cewa za,a kawo su nan don kazabi guda daga cikin su nace dani za,ayi wanan tafiyan sai naga yadda za,ai wanan hadin auren in ina da rai,,,,,
Kanshi yadan sosa kadan ya jingina jikin shi da bangon dakin hannayen shi na zube a aljihu kamar yadda yake yi,
Yace haba hjy na fada maki ki kwantar da hankalin ki wanan abin ba zai yiyu ba sam nariga na fada ma ,Abba da kuma ita maman
Idan ma hadin zumunci suke so aiga su Suraj can da salis sun gimay ni kuma yan uwan su ne akai masu su su aura mana
Hajiya tsohuwa da alama zancen yadan yi mata dadin ji,
Don murmushi nagani a fuskanta,
Daidai zai fita yace ma hjy Dama ina son in zo Nigeria saboda ummina, da yan uwa ,
Sai kuma malam mijin ummi ina son ganinshi sosai,,,
To dadai yafi maka walhi
Inji hajiya tsohuwa ke fadin hakana
Har yasa kafa guda zai bude labulen kofar takara ce mai , akula da kyautawa duk wanda ke da bukata in har da halin kyautatawan,, Saboda kyautata zumunci wani abu muhinmin a wurin Allah,,,
Nasan kana yi ya kokarinka da yin aike, to ka kara ka dinga kai kafar ka don yafi lada,,
Kadinga ziyar da kula da lafiyan maihafiyar ka da yan uwan ta,,
Sai kuma maihaifin ka wanda a,halin yanzu na bukatar ku, kaga yan uwan ka ba wanda yasan alkiblan su kuma uwar su bata son sam ayi zancen su ko kadan,,,
Tana kara ce mai mahaifinka Amadu maihafinka
Saboda yana bukatar kulawa da komai nashi yanzu,
Wanan matar tashi sam ban yarda da ita ba,ko a,da, balle yanzu,,,,,

Bayan fitar shi dakin sai dan shiru yabiyo dakin nadan wani lokaci,
Fadima nace na,am hajiya tace nagode maki kware Allah yai maki albarka,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment