Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A hankali na dan ansa tea suka hada min saidai ba mai zafi ba kanar yadda likita yabada umurni,
A hankali yadan ta dani yabani kadan na kurba na koma na kwanta ,saboda barcin da ya rinjaye idona,
Kusan a zaune sheriff da su bashir suka kwana dan barci kadan sukayi,
Cikin ikon Allah sai naji sauki zuwa safe don da kaina natashi da niyar zuwa toilet,
Amma sai matar kawu ta kamani dan dan jirin da nake gani ,
Nai wanka nafito tsab dani nadan zauna a bakin gado nai tagumi sai a lokacin ido na yakai ga yaran da ke barcin su a hannun su Gwago matar kawu,
Kofar dakin aka turo a lokacin sheriff ne tare da su Doctor kamal wanda yai farin cikin ganin yadda nai saurin samun sauki,
Bayan yan aune aune sai doctor ke tambayar lafiyan yaran ida aka sheda mai cewa lafiya lau suke,
Waau magani yarubuta yace asiyo su ai min allura,
Annan ne yake mun sallamar cewa shi zaitafi, zai koma saudiya tunda na rike mai abikin tafiyar shi,
Dan murmushi nayi da ga kwancen da nake nace mai Allah ya kai ahi lafiya nagode,
Sai tumba ce take ce mai a,a diyan ku dai ne sukari ke shi,.
Sheriff na gefe yana jin mu sai wani dan murmushi yake yi,
Tare suka fita zuwa raka doctor zuwa airport don zuwa Abuja, tare da, Almustapha wanda zai koma shima dan cigaba da aiyukan su,

Washegari da rana aka sallame mu zuea gida,
Alhmdullahi don naji sauki sosai a wanan lokacin,
Matsala ta guda shine bawa yara nono,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎



,
[12/3, 9:43 PM] β€ͺ+234 706 078 6258‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
8⃣8⃣
BY
🐎 *ZAINAB*IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost True Life Story,,,


Muhawara so sai akeyi a tsakanin Shehi da kawu, akan cewa sai su wuce da ni da yara,
Inda kawu yace sam ba,zai yiyu ba sai dai kawai,
Su barni a nan har yara suyi kwari tukun, Sheriff a zuciyar shi ko haihuwar da nayi a dogon daji baiso ba sam,
Amma da yake mutum ne mai saurin tawakkali ga ubangiji sai yai tuna nen cewa aiko ni a garin aka haife ni har kuma na girma cikin koshin lafiya,
Wanan tunanen yasa shi ya kawai da duk wani damuwa da fargaba dake cin zuciyar shi tun farko,
Shiyasa ko yanzu da ake wanan muhawarar bai ce komai ba sai dan murmushin da yakeyi dan ganin manya na ta takkadama atsakanin su,
Ajiyan zuciya yasaukar a hankali tare da kara gyara zaman shi, yana mai murmusawa kawai,
Yadanyi gyarar murya yace cikin muryan tashi mai taushi,
Malam nima naso a ce natafi da su kodan in kai fadima asibiti dan akara diba min lafiyar su acan,
Amma tunda kawo ya nuna cewa yafi son abarsu a nan din ba matsala, sai mutafi kawai mubar su har zuwa lokacin da za,a bamu su mutafi,
Ya juya inda Bashir ke zaune yace sai kayi duk wani shiri da yakamata ai masu kafin mu wuce,
Musa da ke gefe guda zaune kara kwalalo idon shi yayi waje,
Yace a zuciyar shi watau dai wanan mutumin ba karamin mutum bane ,
Bama shine zai tsaya shirya komai ba wai sawa kawai zaiyi ai mai, hmm lalai,
Mikewa sheriff yayi daniyar shiga cikin gidan Inna dan yai sallama da mu,
Hakan yai daidai da zuwan maigari,
Cikin girmamawa yagaida maigari yadan samu wuri gefe guda ya zauna cikin ladabi,
Saboda duk irin wa yan nan abubuwa yau sun zama mai bakon al,amari saboda ba sabawa da shiga mutane haka yayi ba,
Maigari ne yai yar gyarar murya a lokaci guda
Yafara da sallama irin ta addinin musulunci,
Inda maigari ya ce wa kawu da shehi, duk suyi hakuri ga sabanin fahintar da basusyi wa juna ba,
Nan maigari yai makowan su bayanin cikin kyakyawan fahinta ta yadda kowa zai fahinci uzurin dan uwa,
Maigari yakare zance da bawa kawu salihu hakkuri akan ya bari kawai su wuce da italin su,
Saboda yanzu sun fi su iko akan su, sosai, ka ga cewa wai ta tsaya har yara suyi wayo duk bai taso ba,
Tunda can asibiti ne zasu kai su akara diba lafiyan su dakyau, kabari kawai su tafi da abin su,
Jin bayanin maigari yasa kowa dake gurin shiga cikin natsuwa a,lokacin,
Dole badon kawu yaso ba ya hakkure da zancen tafiya da mu,
Duk da bani isa,shen lokaci yake da shi ba hakan bai hana yace abari da safe tunda rana ta yi yanzu ,
Zuwa lokacin kuma yana ganin duk mun gama shirin da zamu yi,
A haka taron yawatse, alokacin a kan zamu tafi da safe,
Kawu salihu ya shigo cikin gida yana bawa inna labarin duk yadda zancen ya kasance a waje ,
Dakuma akarshe an yake cewa zasu tafi da ni da yara,
Inna tace ai ba matsala Allah yasa hakan shine alheri agare mu,
Allah kuma ya raya yara yasa masu albarka arayuwar su,
A gagauce aka fara shirin tafiyar mu, inda sheriff yace jirgi zamu bi zuwa Abuja ,
Jin cewa tare da ni za,a tafi yasa hankalina yadaga sosai saboda a gaskiya bazan son tafiya inbar mahaifiyata cikin wanan halin ba,
In koma cikin daular duniya ita ko tana cikin wanan kangin rayuwa a halce,
Jin bayanin da kawu yai min ne ta karshe da yace gobe zan koma gidan miji na kamar yadda suka bukata,
Jikina a mace nadan mike daga zaman gurfanan danayi ina mai kallon kawu salihu nace, agakiya kawu ni bazan tafi tare da su ba a yanzu
Kawu ya katse ni da fadin saboda may fadima ai an riga an gama zance ko ,bawai shawar ki nazo nema ba ina fada maki abinda aka zantar ne kawai,
A tsorace na karasa mikewa tsaye na ce cikin murya dishi,dishi,
Inna kiyi hakkuri wallahi,,,,
Ban karasa ba Inna tai sauri ce min fadima ai kinji abinda kawun ki yace maki ko umurni aka baki akan ki shirya kutafi da mijinki,
Jin kalamar Inna yasani tsayawa tsaye sororo sai kawai naji wani hawaye na zubo min
Duk hankali na yata shi sai tunane nakeyi taya zan koma dauke da yara har biyu haka ba kwari kuma ni kadai sai kace wata mara galihu,
Kawu ya tashi yafita zuwa gida dan ya dan lalubo abinda zai ba mu,
Anan ne kuma shehi yatare shi yana fada mai cewa suna son su san koda suwa zan tafi,
Indan kuma saidaga baya za su biyo ni to, kawu salihu yace bari ya koma cikin gida don sukara shawara tukun,
Ko da kawu ya shigo yasamau ni cikin tashin hankali ina ta kukan akan cewa bazan tafi ba,
Shawar da kawu ya kawo ne yasa nadan tsagaita kukan nawa dan ji koda suwa zamu tafi,
Inna da kawu suka yanke shawar a tafi da daya daga cikin matar maigari sai kuma gwago matar kawu,
Ina jin haka nacewa innar mu gadkiya da mariya zan tafi,
Sai inna tace anyi yawa kada suga rashin hankalin mu ,
Wani sabon kuka nasa alokacin, mariya ma wace ke zaune dauke dan jariri a hannu ta tasa kuka,
Sai kusan zuwa yamma sheriff ya shigo cikn gidan mu,
Kaina na,duke kasa a lokacin har suka gaisa da matat kawu mu,
Ta fita dakin ta barni nida shi sai mariya dake kokarin gyara min kayana,
Kallon mariya yayi sai ya lura daga ni har ita babu wanda ke cikin walwala,
Ya dan tako har inda nake zaune ga wani kwano ancika min shi da kunun kanwa sai kamshin kayan yaji ke tashi,
Ganin shi duke yana karewa kunun kallo yasa nadan daga kai na kalle shi,
Yai daidai da dagowar shi da ga tsugunin da yayi,yakarewa irin kunun da nake sha kallo,
Ido muka hada kawai sai nakawar danawa cikin sauri,
Cikin sanyin murya yace min bakya iya sha ko kai nagirgiza mai ,alamar zan iya mana,
Sai ya juya gurin mariya yace ma mariya idan mutafi can ashe kece zaki dinga yi mata wanan din ko,
Da sauri na kalleshi murya na min rawa na ce wai bada ita zamu, ba,
Cikin alamar tambaya yace saboda may baza,a da maman babies ba,
Ya ce haba no,no no yakamata inna tayi hakkuri a tafi da ke mana,
Yunkuwa yayi ya mike gaba daya yana fadi tare da ke zamu tafi gobe insha Allah ,
Sai a lokacin nadan yi murmushi tun zuwan sheriff dogon daji,
Ido ya zuba min yana nazarin irin son da muke wa juna nida mariya,
Dan ina jin cewa da mariya zamu tafi gashi har yaga murmushi a fuska,na,
Fuskan da tun da yazo garin yake daure kamar wace akaiwa mugun, sako,
Yana mikewa yace min zanbar wa inna da maigari kudi suyi bukin sunan su a nan duk yadda yakamata,
Sanan zuwa suna zan sa a shirya wasu suzo gurin mu dan ayi suna dasu,
Ya miko min wasu kudi yace in baiwa inna tayi nata taron sunan a nan yadda al,adar mu ya tanada,
Gaba daya sai jikina yai sanyi so sai dan ganin irin yadda sheriff ke kokarin ganin ya farautawa yan uwa na rai,
Musanman mahaifiyata wace ke cike da kewa ta da kuma zullumin rabuwa da ni ko wani lokaci,,
Dan murmushi yayi yaja baya yace ki karba ba wani abu yasa nabata ba sai dan kawai ta yi wanan hidimar dasu,
Har yafita dakin ina nan yadda yabarni, cikin zulumi da kuma jimamay yadda abubuwan zasu kaya muna,
Bakaramin kokari maigari yai muna ba a,wanan tafiyar namu gaskiya dan harda dan rakiya ya hada mu dashi namiji wanda zaije ya ga garin su Sheriff, da yan uwan shi,
Kawu ya kawo ma su sheriff tsaraba zuma don itace sana,ar shi pure one har gora biyu,,
Kilishi mai yawa da shi da maigari suka basu tsarabar shi,
Sai kuma dakuwar ayya da fura da nono tsaraba irin ya yan kauye shi akaiwa su sheriff,
Aisha ce ke wasa da wani tsohon photo a hannu ta a cikin akwatin karfe inna ta dauko shi lokacin da inna ke fitar min da,wasu yan zoben azurfa tace in sa wa a hannun su,
Har waje Aisha ta fita da photo a hannunta tana ta wasa dashi, gurin sheriff taje ta zauna a jikin shi,
Karban photo yayi kura mai ido, yana kallo har wani lokaci, kamar may son ya gane wani abu aciki,
Gefe yadan aje photon daniyar ya dan gyara Aisha da ta zauna mai,
Sai sheriff ya mika hannu ya dauki photo ai tun bai karasa kallo ba yadan mike dan mamaki,
Saboda shi dai yasan cewa iyasanin sa baizo da nashi photo nan garin ba, to ina wanan yafito,
Cikin mamaki yake kallon photo ya ce wanan ai photo dan uwa nane
Da mamaki sheriff ke kallon shi yana jin abinda shehi ke fadi kamar al,mara,
Sheriff ya nemi jin bayani gurin shehi nan yai mai bayanin cewa, Photo shine shida kanin shi, lokacin da suna yara amma dai dan uwar nashi yabar gida har yau basu da labarin shi,,
Wata sabuwa dan sai yanzu yake tuna zan cen inna a asibitin sokoto inda take mai godiyar jin da yaba fadima tace mai ai jin su yanada wuyar samu dan hakana mahaifin su yayi da yayi accident sai, akai bidan jinin da zaa kara mai ba,a samu ba har Allah ya karbi ran shi,
Zubur ya mike ya na mai fidda kwalla a idon shi yace,
Tabbas wanan dan uwan shi ganin shehi da gaske yakeyi yasa su duk zuwa gurin mai gari,
Bayanin tun zowar su mahaifin fadima garin zuwa sayen fata da suke har takai shi da zama garin,
Shehi yace watau Dangiwa mai fata shine ya wuto masu da dan uwa har nan, amma akayi ne man shi akarasa kuma bai fada masu cewa yana tare da shi suna sana,ar jima,ba alokacin,
Nan wani sabon kuka yazo wa yan family mu dan kukan murna da farin ciki a lokaci guda,
Yau gori ya karewa hafsi a gidan mijin ta dan duk inda fada ya hada ta da yan gidan sai suce ai ita ba,a san asalin su ba
Mahaifinta yawon duniya yazo yi har ya auri yar kulu a lokacin,
Kuma ai kwadai yasa inna ta auri bako dan tagan shi mai sana,a ne,bai noma,
Kafin ace haka labari yafara karade gari cewa dangin mahaifin su fadima yazo an gane shi,
Shehi yai kuka sosai don jin cewa dan uwanshi ya rasu ya fada masu irin gatan da mahaifin mu ke ciki amma rana guda aka nemay shi aka rasa,
Murna a cikin murna ke nan a gurin innar mu dan ba karamin dadin hakan yai mata,
Ba dan gori da hattara yaranta sun ji shi ga jama,ar gari so sai wallahi,
Hira akayi so sai tsakanin mu da malam.shehi ko in ce wan mahaifin mu ,
Inda ya jajanta mu na rasuwar mahaifin mu,
Yakuma ya ci gaba da muna nasihar rayuwa,
Yace ya jin jina ma irin rayuwar da inna tayi da mu shiyasa ake cewa amana tana hannu hagun mutum,
Gaskiya gaskiya tana nan a damarka da sune mutum zai tsalake siradi ranar lahira,
Haka nan idan baka da dasu koda kataba tsamanin zakaci ribar rayuwar duniyar da ta lahira,
Yakare da cewa ina mai jinjina maku tare da mahaifiyar ku wace ta iya rike gaskiya da amanar ku,
Duk munyi shiru mun natsu muna sauraren nasihar da Shehi ke muna,
Yace yau gaskiya da amana yasa duk kun kai ga samun nasarar rayuwar ku,
Haka akai wani lokaci cikin kulawa da kuma kara kaunar junan mu,,,
Tunda safe motocin da sheriff yazo dasu suka Parker kofar gidan inna akai masu loading tafiya inda mu da su gwago da matar maigari zamu bi jirgi zuwa Abuja,
Cikin irin shigar da nasaba yi a saudiya yau shine a jikina ,
Yan kauyen mu sun fito tab dan yi min fatar alheri da kuma kara taya mu farin ciki,
Tun cikin dare innar mu tai ta min nasiha ajan zaman duniya da kuma koyi da sunnan ma,aiki, S A S W,
Harda maigari wanda yake min kamar uba cikin masuyi mun rakiya zuwa airports,
Karfe sha biyun rana har angama muna checking din komai mun shiga motocin da za su kai mu Maitama gidan Sheriff,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘


✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£πŸ‘£
8⃣9⃣
BY
🐎 *ZAINAB**IDRIS**MAKAWA*🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost True Llife Story,,


Mota guda muka,shiga nida sheriff sai kuma wata doguwar mota mai kama da kifin ruwa, ita su gwago da matar maigari suka shiga
Mariya da yaran suna tare da,su,
Kusan tun ranan da sheriff yazo kasar mu ban mutaba kebewa ba sai yau,
Driver na tada mota alamar zamu bar airport din ke nan sai kawai naji sheriff yadan lalubo hannu na,
Ya danke cikin nasa gami da sauke wani irin ajiyar zuciya,
Yace min fadima kiyi hakkuri ki daina wahal da rayuwar mu hakana pls,
Sai naji jikina yai sanyi da kalaman shi, sai naji kawai ya bani tausayi,
Dan gaskiya sheriff bai can canci haka ba daga gareni,idan har nai la,akari da irin taimakon da sheriff yai min a,rayuwa ta,
Musan man wanan na karshen da yai min nataimako akan inna ta, wacce nafi damuwa da al,amarinta,
Ban san lokacin da na dan kwantar da kafada na saman nashi ba, ina mai a,jiyar zuciya,
Dan kokarin kallon fuskana yayi a lokacin, sai yaga hawaye nakeyi kawai,
Dan murmushi yayi yace min may kuma na kuka yanzu tunda ga ki gani ni nai maki alkawarin ba, Aziza ba kowani irin ma,sherancin abu bazai kara zuwa kusa da ke ba,
Kaina yana a kafadar shi still ina dan she,shekar kukana
Nadan dago kaina ina mai kallon shi cikin murya maiban tausayi na ce mai amma dai ba zaka kara barin mu zauna guri guda da ita badai ko,
Batare da ya juyo ya kalleni ba yace min kin riga dai kin tsorace da al,amarin Aziza ne kawai ba abinda da zata iya yi maki,
Kara narkewa nayi a jikin shi kamar zan shige mai, kaina na saman kafadar shi still nace ba tsoro bane,
Kawai dai ina tsoron ta rabani da mijina ne kawai, uban diya na,
Shiru yayi bai ce min komai ba a lokacin saidai yar sautin murmushi, shi dana ji,
Ashe har mun,kawo gidan nashi na maitama ban sani ba,
Jin muryan masu gadin gidan dake muna sannu da zuwa ne yasani gane cewa mun shigo gidan ko,
Badon naso ba nadaga da kafadar sheriff ina mai gyara Mayafin kaina da kyau, ta yadda ba za,a iya gane fuskata ba sosai,
Gidane na gani tsantsarare ginan zamani don tsaywa musalin shi zai bata min lokaci ,hawa guda ne,
Sama da kasa kawai, amma fadin gidan yakai wani tsayi mai tsawo gaskiya,
Yadan kalle ni bayan yasan cewa na zauna da kyau a sit din yace ina fatan ginar gidan zai maku,
Idan akwai abinda bai maki ba sai kiyi min bayani in sa a gyara maku,
Cikin mamaki na bude baki da zumar in mai godiya sai kawai yasa yar yatsar shi a bakin shi ya ce min shiiiiiiiiiii alamar inyi shiru,
Dole na rufe bakina ba shiri tunda an hana ni furta komai,
Kofar motar a ka bude muna, a lokaci guda, mukafito, daga ciki,
Yan officer din su ne na nan Abuja suka zo tariyar mu da kuma taya ogan su samun karuwa,
A hankali nake takawa kamar maijin tsoron kasa bakina fam da duk wani addu an da yakamata in yi a lokacin,
Sai kallo nakeyi yadda Naira ya sha kashi anan, a gaskiya na tsinke da al,amarin sosai sai naga kamar wanan ginan duk ya cuna ma gidajen Sheriff,
Wanan irin ginan na sheriff ya tamfsa abin abin kallo ne gaskiya,
Sai a yanzu na tuna cewa su gwago da yaran basu karaso ba, dan haka dan dakatawa nayi dan su iso mushiga gabadayan mu,
Isowar su naci gaba da tafiyana a hankali suna biye dani rungumay da yaran a jikin su,
Sheriff yadan tsaya nisa dani kadan yana muna wani irin kallo cikin so da kauna,
Don ji yake tamkar a lokacin ya rungumay ni don wani irin so da sha,awar mu dayake ji kamar ransa zai fita don so na da yaran,
Azuciyan shi mamaki yakeyi waiyau shine keda wanan baiwar na diya biyu a lokaci guda,
Ya lumshe idon shi yadan karasa takowa muka shige cikin gidan atare dashi lokaci guda,
Sai da nakarewa ko ina kallo da ido tunkun na sai nadan waigo nakalli inda sheriff yake tsaye ,
Alamar godiya nai mai da ido ta yadda bakowane zai fahinci may mukayi wa juna ba,
Duk a falo muka sauke yar gajiyar mu inda masu aiki suka gabatar muna da abinci,
Ganin su gwago a gajiye suke yasa shi yi min magana cikin harshen larabci, ya zai tafi yaga inda yakamata mu sauke bakin mu, kai kawai na gyada mai,
Sai a lokacin su gwago suka dan sake jikin su suka fara mamakin irin abincin da aga jib ga agaban mu, wai mu kadai,
Hassan nai yai dan motsi wanda ke ta faman barci tun a jirgi, gwago ta miko minshi wai in bashi nono yasha,
Saida gabana yafadi a lokacin,
Sai nace mata barin da kewaya kafin in zauna tare da mariya muka shiga daya daga cikkn dakunar da ke kasan ,nadan zagaya ban daki, dan inji dadin zama,
Dakin ba laifi dan haka muka zauna ciki dayani nida mariya,
Ganin nafito daga bayi yasa mariya fita dan ta dauko min hassan din kusan a kofar dakin suka hadu da gwagon mu,matar kawu dauke da hassan wanda ke ta faman mutsitsiri a cikin showell
Mikon min shi gwago tayi ,daniyar inba shi nonon
Baki na turo dan in akwai abinda banson ji yanzu shine ace yaran zasu sha nono,
Dan har ga Allah bana son jin wanan bada nono da gwago ke damuna dashi,
Muryan gwago naji tana cewa , oh ni Salamatu kun gamin yarinya
Nafa lura da take taken ki sarai bakya son jin zancan shan nono,
Indan baki badu nono suka koshi ba may kike son aba su
Bayan ga abincin su Allah ya hore masu wadataccen nono bawai babu ba,
Baki nakara turo idona yai ja kamar may shirin yin kuka,
Gwago ce ta gyara min yadda zan rike yaron da kyau dan yaji dadin shan nono,
Daidai na daga riga na kenan zan sawa yaron nono a baki sheriff ya shigo dakin da sallamar shi,
Cikin sauri na sake rigar ina mai gyarawa sa kyau dan kada yaganar min nono na,
Gwago dake tsaye sai abin yabata mamaki tace shin wai mi kika nuhi

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment