Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ido yabini da shi yana mamakin irin girman da ya hango nadan kara yanzu, kafin mu shigo,
Ashe tunda yaga hadari yakasa zaune ya kasa tsaye, hankali a tashe, don baisan halin da muke ciki ba,
Saidai yayi amanan cewa baza mu biyo wanan iskan ba,
Saman dakin shi ya tsaya, dai inda zai iya hango ta,waje yana yi yana dan leken hanya,
Aiko sai gamu cikin wanan uban iskan mun doso gida,,
Mamaki ne ya kamashi haikan ta yadda muka iya kasadan biyo hanyan hakana ba wani fargaba ko tashin hankali
Har fitowan mu yana kallon mu da yadda iska ke kwasan mu kafin mu shigo gidan
Cikin sauri yarigamu isowa falon bayan yariga ya kare muna kallon mamaki ko rashin hankali,
Itama wucewa tayi batare da tabashi hakkuri ba, don gani take gaskiya ya fara takura mata,,

Dakin da aka tanadar min na gidan nashiga , don indan gyara jikina,
Ina shiga batare da bata, lokaci ba, don dama duk nayi futub da kura gashi kuma na jika kaya na sama,
Cire bakan rigan da nasa sama na yi
Nakoma dagani sai dan wandon jens dark blue, na mata wata yar karaman riga pink mai guntun hannu ke jikina,,
Sai ribon mai kalar baki dana dan daure kaina dashi,
Nasamu wuri gefen gadon dake dakin na dan baza bakar rigan nawa don yadan bushe kafin in wuce,,
zaune nake ina kokarin cire takalman da ke kafa na, ahankali ya turo kofan hannu shi rike da tawul fari,
Ban san lokacin da na mike tsaye ba ina wage wage ko zan dan samu abinda na rufa ma jikina, alokacin ba komai adakin don ban barin kayana agidan kamar yadda sauran ma,aikata keyi,
Towel din ya jefo min tunda ya gane nufi na ,,
Shiko aganin shi baiga wani abin da har zan boye ajikina ba ,
Yar ficir dani kamar mage,
Juyawa yayi yabar dakin cikin sauri,
Shi dai tausayi wanan yariyar ke bashi a,rayuwan shi don koda baiji tarihina ba yakan tausaya min duk lokacin da muka hadu,
A dakin ta yasame ta tana kara gyara kwaliyar da akai mata a wurin akafar
Cikin dan dakikan lokaci ya kalle gyaran kan nata ya kauda idonshi tamkar baigani ba,,
Tasowa tayi tana wani rangwada ita adole tayi kwaliya ma miji,,
Tana batun rungumay shi yace cikin dakiyar fuska maynene haka pls,
Bana son irin wanan shashancin pls,
Sha shanci fa kace ,kana ,a matsayin mijina zakace min sha,shanci,
Nifa Ahmad bangane may kake nufi ba dani yau kusan satina uku kenan agidan nan
Amma ba wani nuna cewa ni matar kace, balle ,,,
Bata karasa maganar ta ba daidai lokacin nai sallama dakin dauke da cup din ruwan shayi mai tururi ,
Dai lokacin kuma wani sabon ruwa yakara gwaucewa kamar da bakin kwarya,,,
Shayin na gabatar mata ,wanda nasamu gundun mawar harara,
Bisa tebur din dake dakin na aje mata nafito abina,,,,
Dakina nakoma don naga yau abin ba dama,
Wajen window dakin na zuge glass din nadan tsaya, ina kallon ruwan
Wata zuciya kuma tana tuna min hajiyan mu dasu Aisha da umar ko yaya suke yau cikin wanan yanayin,sanyin
Danagaji da kallon ruwan baidauke ba sai kawai na kara cire rigana na fada bisa gadon mai wani katon bargo da laushi, nace barina dan huta kafin ruwan yadauke in,tafi gida,,,,
Har gari yai duhu ruwa ake ta tsulawa bakama hannun yaro,
Niko kwance nayi barci mai nauyi ne yai awon gaba dani,
inata barci abina don jin dadin wanan yanayin danayi,
Nadunkule wuri daya na,hada hannaye da kafana wuri daya na nadae, kamar wata yar mage,,,,
Kusan sau biyu ya shigowa dakin don ya ta dani daga barci,
Amma yana samuna dunkule ina ta sharar barci na, daganin yanayin da nake barcin yai min dadi,
Yasan cewa ko kadan bani da lokacin hutu balle har na barci don hakane ma koda yaga magrib ya kusa daidai lokacin da aka hana barcin marance yayi ,,
Sai yai niyar zuwa yata dani, saboda bai yarda wani ya shigo mai cikin gida har inda nake
Don ni dakina ya ta ciki ne inda kusan inda nasu yake,
Sabanin nasu rugaiyya dake can ta baya kadan inda hanyar kitchen yake,
Sanin da yayi cewa ina gidan yasa shi, zuwa kirana don in, tashi ,,,
Ganin ina ta barcin ne har yanzu yasa shi juyawa ya koma, yata tausaya min cikin zuciyar shi,
Shidai baisan dalili ba kawai yarinyar tana bashi tausayi so sai wlh,,,,,

Arazane na mike akan gadon gami da salati , nazaune atsakiyan gadon kafana lankwashe cikin na juna,,
Nadan lunshe idona kadan don barcin bai sakeni ba,,,,
Azatona magaruba bai mayi ba tukun, yanayin dai garin ne haka, nadan kara lumshe idona daga zaune,
Idona yana rufen naji kamshin turaren shariff din wanda yakara dawo wa daniyar yatasheni daga barcin,,,
Jinkamshi yasani saurin bude idona saidai banyi sa,a ba yariga ya wuce ko tunda ya leko tagan ni a zaune,,,,.
Kallo nakaiwa agogon bangon dakin zubar na sauko kasa don ina gizo,,, idona ke min ba wai takwas saura nadare,,,, agogon ya nuna,
Bayi, nafada nadauro alwala na gabatar da sallah a gagauce,,,,
Ina idar wa natashi na nufi hanyar cikin gida don indiba abinda gidan keciki ,,,,,,
Don koni dan karen yunwa nake ji don harda kugi cikina keyi,
Ina tafe duk su hajiya nake tunane ko yaya suke can ko may zasu ci tunda ba girki takeyi ba,,,
A dining nasamay sherriff din zaune yana cin abincin shi daya,,,
Haka kawai ganin shi yasa kirjina bugawa don na tuna da fadan da yai muna dazu,
Yanzu gashi don jin dadi da samun,wuri na zo nayi kwance inata sharar baci kamar wace Abadan bata da aikin yi,,
Cikin girmamawa na gaishe shi,,,,
Amma maimakon ya ansa min sai dago wanan yadaurarren idanun nashi ya watso min, wanda kulun yakale ni dasu ban iya gane komai acikin su,
Shima tambayana yayi kinci abinci kine,
Batare dana bashi ansa ba
nace madan bata fito bane, sai kawai na nufi hanyar zuwa dakin ta, nashiga da sallamata,
Zaune take cikin wata yar rigar barci wanda yake dan iya nuna surar ta waje,
Dan damtsen hannuta yadan wani murde kamar na matashi kato,,,
Kanta duk da an gyara shi wai yau yawani yi tsirma tsirma dashi dayake guntun gashi gareta,
Waya takeyi, har na juya kamar in wuce sai na hago cup din dana kawo mata shayi dazu saina nufi inda yake indauko,
Jin maganar da tajeyi awayan yasani faduwan gaba duk na,riki ,
Saida nayu kokarin saita kaina, don kada tasan cewa ina jin hausa,, don ita duk dauka takeyi, banjin hausa ko dan turanci sai larabci kawai
Abinda naji tana fadi shiya tayar min da hankali sosai hankali,sosai
Cikin rashin damuwa da inajinta tacigaba da fadin,
Wlh duk da auren dukiya nai mai salwa yanzu ina son Ahmad,
Kafin in fara yaudarshi sai na dan more rayuwata dashi,
Hmmm zancan kawai hjy ke yi, kina tsan manin cewa zai ta bani kudine a haukace,
Ganin da tayi nadauki cup din kamar zan fita taimin alama da hannu cewa wai in dakata har ta gama wayan,,,
Cigaba tayi da maganar ta, Salwa don dai baki ganshi bane shiyasa kike cewa hakan
Yo nima dana fara ganin shi ai,saida na manta da plans din mu,
Takare karshen zance da cewa ai dole inbi a,hankali don in Daddy yagane plan din hjy duk mun mutu Salwa,,,
To sai kin kirani din,,, takashe wayan tana kallon inda nake tsaye
Niko alokacin duk nagama rudewa kokarin saita kana kawai nayi,,,
Yadda naga ta dan zuba min ido yasa nadan tsargu,
Saidai kuma naji tayi dan tsaki tace, waima ko taya zan ma wanan mara hausan magana fahince ni,,,,,,
A,lamatai min kawo mata abin sha jiki ba kwari nabar daki nata,,,
Hankalina a,tashe anya kuwa ba munafuntar Sheriff wanan matar keyi ba, au har ma shakukeyi inji wata zuciya tace min hakana keda yanzu kikaji komai ,
agaban ki fa akai maganar komai kina ji ba labari aka baki ba ji kijayi,,,
To inko hakane gaskiya akwai aiki ja agabana
Wurin wasu kujeru dake tsakiyan coredon gidan na isa na zauna gami da buga tagumi, don dai inji dadin tunane, don gaskiya dole in taimaka ma Sheriff nima saboda shima yataimaka min a rayuwat, lokaci da dama,
Minti goma tsakani na tashi na shiga dakin
Wanan karon bisa gado take kwance tayi daidai da ita saman gado da alama akai abinda take tunane,
Dakatawa na danyi na kare mata kallon tsab sai naji wani tsanar ta ya shiga zuciyana,
A sanyaye na karasa gareta na aje mata dan tiren da na hado mata abin shan sama wani dan stol .
Juya nafito dakin nabar mata cike da tsanar ta,a raina,
Tausayin Sheriff din naji ya kaman,,,
a gaskiya dole ne indan taimaka mashi batare da sanin saba,
Ajiyan zuciya nasaukar daidai lokacin da nagama tunane mafita,,,

Dole wanan ranan agidan muka kwana, saboda dare yayi ba damar mu fita waje,,,
Tunda safe dana tashi bayan mun kanmala komai,
Naje gun mama mai abinci na fada mata cewa, zanje gida indiba yaran nan biyu,
Batare da nafada makowa ba na gidan n sulale naitafiya na,

Motar shi yadauka don zai je yadan zagayo wurin aikin su dake cikin gari ,,,,
Har yadan fara tafiya sai ya lura da wani leda a,gefen kujera, daukowa yayi yadiba sai ya mayar inda yaga ledar, aje,
Har Saida yaje yadawo inda zashi ne yadauko ledan ya shiga dashi cikin gida,
Dakin shi yashiga da ledar ya aje, batare da yayi cigiyar mai ledar ba,
Falo yadawo don yadan huta, saidai yana zama sai yaga ai kamar yadda yabar falon dazu da safe haka yakara samun shi,,,
Wayan intercom yadauka yana son kirana
Yayi kira kusan sau uku amma ban,dauka
A fusace ya fito falon yana kokarin yaga ankira ni, saidai an fada mai fita zuwa gida amma nace bazan da de ba zan dawo, yan zun nan,,
Ranshi bace yakira almustapha yai mai kaca kaca kan sakaci da aikin da nakeyi,..

Agidan mu kuwa gaskiya nasamu hajiya ta kula da yaran don ta basu abinci kuma tai masu wanka,
Suna gani na suka yo kaina da murna suna nuna farin cikin su na gani na da,sukayi,,,,,,,,,
Jawo su nayi a jikina ina farin ciki da ganin su,
Saida muka gama yar hiran mu naje gurin hajiya muja gaisa na fada mata cewa ruwan samane ya hanamu dawo jiya,
Tace min ai,gara da muka tsaya can don da munce zamu biyo hanya za,a iya kama mu a,lokacin,
Nadan kai wani lokaci a gidan tare da hajiya da yaran inda na dan kara gyara wuri,
San nan mukayi sallama na koma cikin sauri don sai yanzu nafarga d lokacin da muke ciki,
Tabas nasan cewa na bata lokaci sosai a gida tare dasu hajiya,

Ina shiga gida tun abakin get aka fara fada min cewa Sheriff yana bida na,
Babu fargaban komai atare dani nasa kai cikin gidan don ansa kiran Sheriff
Da salamana na shiga falon, zaune yake cikin shigar cort da wando irin ta maza, saidai ya cire cort din ya sagale ta gefen kujera,, daga shi sai wata farar riga yar ciki mai dogon hannu,
Tare yake da wani bakon mutun sun zuba tulin takardu suna diba,
Ganin yana aiki kuma ba shi kadai bane agurin yasa nai shirin juyawa don in,bar wurin,,,,
Ke yace min cikin daga murya saidana dan ja baya kadan
Ina kikaje lokacin aiki , kin ko san ka,idar aikin da kikeyi kuwa,
Kaina yana kasa bandaga ba balle in kalle shi,
Wakike son yabar aikin shi yakama maki naki aikin dibà nan ki gani yadan sa yatsan shi yagoga dan teburin glass din,
Tare da nuno min ya tsan wai indiba ingani ido nadan daga nakali abinda yake gwada min
Saidai ni,banga ko mai ba,
Amma shi cewa yayi wai aiga datti nan ko ina a falon ,
Falon nakara bida ido don indiba kozanga dattin da yake nuna min banga komai ba,
Shiru kawai nayi ina sauraron shi,har yakare, kuma daga yau in har zaki iya aiki da mu to dole komai naki yadawo nan gidan, har kwanan ki,,,
Saidai kalman shi ta karshe ce ta razana ni har na fidda idona waje,
Waje don kidima,
Idan har bazaki iya ba ga hanya nan ki tafi, sai in,dauki wata,
Kawai ya juya yaci gaba da abinda yakeyi batare da yakara kulani ba,
Nadan dan yi,jim nadan wani lokaci don mamaki kalaman shi da yai min cikin kakausar murya
Cikin yar muryana mara sauti nace mai,amma kasan cewa inada tsohuwar da bata da lafiya dakuma yara,,,,,
Zancigaba yadaga min hannu batare da ya juyo yakaleni ba idonshi naga aikin da yakeyi
Yace hakan naga dama kuma ban shirya jin ko wani irin korafi ba a yanzu
Idan zaki iya kije kiyi inko bazakiyi ba,
Yahada hannayen shi wuri guda alamar ma,assalam
Falin nabari cikin sanyin gwiwa don na ma rasa ta, ina zan fara,
Kitchen na nufa nakira antyna Rugaiyya na fada mata duk yadda mukayi yau da sheriff din,
Flower da zata kwaba tayi ambuss da shi don abincin dinner ta dauka a wani dan silver ,
Tana fadin fadima inbanda abinki aikema kinsan aikin ki aikine mai daraja ,ba aikine na wasa ba,
Don kinsan duk wani kulawa na mutanen gidan nan yana akanki ne
Wanda ko da acikin dare ne bukatar hakan yataso dole ne ki yi aikin ki,,,
To idan baki nan waye zai masu fadima,
Kinsan cewa wanan aikin da muke yi a gidan nan yafi duk aikin da mukayi a wanan gari sauki,ga kuma kudi masu albarka da ake bamu
Koda kin fadawa hajiya bazata yarda ki bar wanan aikin ba sam,
Don haka tun wuri ki wa kanki fada ki zauna gurin aikin ki
Zanyi magana ta daga min hannun da take kwaba flower dashi tace min ya isa,
Ina dai yaran da kika jajibo wa kanki wahala kike tuna ne ko,
Kaina kada mata alaman eh, tace min to ai mu ,muna gida zan dan dinga kula maki dasu gwargwado,

Hakan ne dalilin dawo wana ,da zama gidan aikinawa,
Don ko hajiya da naje gida na fada mata ansar guda ce in koma can kawai din,

Yau kusan satina guda agidan ban zuwa ko ina kulun ina cikin gida , bawani kwareren aiki amma wai aiki nakeyi a,hakan,
Yau da marance kamar kulun mun gama komai mun hada aikin mu na yau
Na shirya cikin wasu doga yen riga mai dan kalar rainbow,
Ina dakina ina kallo wani tashn da ake yin wani gasan talent na larabawa,
Sai naji kamar marana yadan murda min aikuwa sai gaba na ya fadi don in har ban manta ba yau nake expecting din period dina,
Gashi kuma banda magani anan yana gida na bari,
Kadanda nasawo ranan da muka fita da a,maryan sheriff ya fado min arai,
Ban gama tunanen da nakeyi ba naji wayan dakina nakirana,,,
Alamar ana bukatana acikin gida,
Zaune suke a haraban gidan shida wasu baki suna tataunawa,
Kayan jika makoshi suka bukata,
Lafiya lau nakawo masu, na juya nabar wurin nabasu baya kadan aiko sai na kasa cira kafana,
Dukawa nayi wurin nadafe cikina,
Marana kamar zai fashe nake ji na,
Bango na dan fara bi don insamu inkai dakina,
Aiko na kasa, idona ya kade yayi ja,
Cup da magani naga an miko min,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
[10/4, 14:30] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

Matan huguma group Allah ya kara daukaka,
Allah ya shirya muna zurian mu ,yasa mugama da duniya lfy,,,,,,

Almost true life story



Ban san lokacin da na karbi maganin natura baki ba duk da ban gane kalar magani ba kowane,irine nidai muradina insha magani,,,
Cikin rawar hannu na karbi cup din na,sha ruwan kadan,
Ina hade, Ruwan da magani Nakara dunkulewa wurin, saboda wani irin azaban ciwo da naji,,,,,
Duk da ina jin kamshin perfume din shi ya,na tashi yana shiga min cikin kai,,
yau ciwo ya hana ni yin re,acting din komai,
Kamar kar maganin da ruwa su shiga cikina aiko sai na kara dunkulewa saboda wani irin azaban ciwo dake damuna,
Cup din na sha ruwan yana rike hannun shi , ya wurgat da cup din gefe guda,
Dafa min kafada yayi yace min in dan tashi in shiga ta cikin gida,,,
Ai,kafin ince zan tashi wani irin amai ne ya zo min nai kokarin indan kauce da kaina,gefe, kadan don kada aman ya taba shi,,,,
Amma, ina kafin in haka aman yazubo ko,,,,,
Duk na,wanke mai jiki da shi,,,,
Sannu kawai yake ce min, cikin nuna rashin da muwa,
Ina samun yin aman sai nakama wani irin zufa, kamar nasha ruwan masu mugun zafi,
Idona yadan kama rufewa a hankali, ahankali har ya rufe lub,
Nai lu, zan fadi kasa yai kokarin yasa hannu shi guda ya tallaboni dashi,
Almustapha yakira da sauri ta cikin wayar shi,,, ya fada mai ya zo da sauri ga in da yake,
Almustaph yana zuwa yaga irin yanayin da nake ciki, shima sai hankalin shi ya tashi,,,
yace ma Almustapha ya dan rike ni su kaini daki, na,,,,,
Har mustapha yakai hannu zai rike ni ,
Komai Sheriff yatuna sai kuma
Yace mai dakata ,kada ya tabani,
Cak yadaga ni sama kamar wata baby yai cikin gida dani mustapha na ce mai ba asibiti zasu dani ba,
Bai saurare shi ba cikin gidan yayi dani,,,
Anty nafisa na zaune tana waya saman wasu fararen kujeru, ta hango shi dauke dani ga mustapha yana binshi a,baya cikin tashin hankali,,,,,,,
dakina suka kaini,direct
Ya shimfidar dani saman gado,
Ganin ina zufa yasa suka kuna min AC, a,dakin,
Barci ne mai karfi yadaukeni cikin dan kakanin lokaci ,kamar yadda dama maganin ke min aiki da nasha,
Indai har nasamu nai amai to zan yi dan barci indan na farka sai inji ciwon yadan lafa min,,,
Kofan dakin yajawo ahankali, yarufe min,,,
Sai a lokacin hankalin shi yakai ga rigar shi dana sharara mai,amai akai,
Cikn sauri batare da yace ma Almustapha komai ba,ya nufi hanyar shiga shiyan da dakunan su yake,,,
Almustapha da aka bari tsaye da mamaki yakalli kofan dakin da nake kwance yakuma kalli hanyar da sheriff yabi,,,
Zuciyan shi cike da wasiwasin akan rashin lafiyar nawa,cikin dan kan kanin lokaci haka,
Anty Nafisa ce tsaye a falo cikin mamaki da kuma son sanin may ke faruwa, ne haka, har mijin nata tadau koni, ajikin shi,
Jikin da take muradin tabawa koda yantsan shine bata samu ba yau ga common yar aiki, cikin shi dumu dumu,
Wuce ta, ya,yi fu,u yahaura sama abinshi, Inda dakin shi yake, batare da yako kali inda take ba,,,,,,
Bin,shi tayi da kallo har ya bace mata, daidai lokacin da mustapha ya fito shima daga inda nake,,,,
Mustaphane,, yagaishe ta cikin girma,mawa zaidan wuce ,,take tambayar shi may ke faruwa ne,
Yace mata banda lafiya ne shine suka taimaka min ,,zuwa daki,
Baki ta tabe nuna ko in kula,,,
Yana shiga dakin shi ya wurgat da rigan tun a kofa,
In akwai abinda yaki jini arayuwan shi ne yaga ,amai ,,,
Idan yaga amai bai iyan komai ko abinci bazai iya ci ba a ranan ,,,,,,
yau gashi , an mai amai a jiki, amma yadaure dashi a hakanan
Subbahanallah, rin,tse idon shi ,yayi tare da sake shower akanshi, ruwa nata zuba mai,,,
Yafi kusan minti goma a haka yadauki sabulu da soso duk ya goge jikin shi dashi, don ji yakeyi kamar aman ya mane mai a fatan jikin shi,,,
Yadauki lokaci da dama acikin bayin san nan yafito,
Ya dan gyara jikin shi jallabiya kawai yasa don lokacin sallah magrib ya kusa,,, saboda har in yana gari duk sallah da zaiyi cikin jan,i ne,,,,,
Koda yafito zuwa masallaci Nafisa tana zaune, falo ta kure karar tv tashan yan rawan kasar turawa, keta ,tashi,, kamar gidan yan rawan disco,,,,,,
Mamaki yakamashi fal a zuciyar shi,,,,,, don shi tunda yake gidan baitaba sanin ma akwai wanan tashan ba a,talabijin din,
Batare da yai mata magana ba yadauki remote din dake saman dan karamin tebur din

1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment