Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take min wai naki murmurewa in koma wurin bara.

Yanzu kan nadan ji sauki nida kaina na shirya fita yau,
A,hankali nake tafiya har na iso kofar masallaci dai dai kofar shiga Bin dawood nasamu gefe na zauna na hada kaina da gwaiwa na .
Yakamata ace nasaba da wanan kamshin turaren Al, madinal nuriya, .
Cikin sauri nadago kaina ,saboda nasan kamshin turaren wanan mutumin da ya taimakeni ne har kusan sau biyu.
Mukayi ido biyu dashi abinki da mara gaskiya, saina dukar da kaina kasa, Nadan gyara zama na kadan gefe na ya shimfida salayar shi,
Batare da ya fuskance ni ba yace min ya jikin na ansa da
Alhamdullah baikara ce min komai ba sai yaci gaba da lazimin shi baiko kara kallon inda nake ba,,,
An idar da sallah azahar ina son in je gurin barana .
Kamar yasan abinda nake sakawa a,zuciyata sai naga,ya mike tsaye ,, ya,miko min kudi masu yawa yace inkai gida basai nayi bara ba yau .
Hawaye kawai ke zuba min a idona ko godiya na kasa yi mai ,,,
Hakana na dan lalaba nakai ma hajiya kudin tana ta washe baki tana fadin koke fa, da kina nan kwance da wazai bamu wanan kudin masu yawa haka,
Nidai bansan komai gamay da wanan mutumin ba amma haka yadinga taimaka min da kudin bara har naji saukin jikina.
Itako hajiya bata taba tambayana ina nake samo eanan kudin sabbi fil dasu ba ka kamshin turaren shi dake man,ne makudin
Rugaiyya ce ta lura da hakan saboda idan na raba biyu zan bata wanda muke boyewa kulun ranan ina bata sai tace min Fadima ,,,,
Nace na, am wake baki wanan kudin masu yawa haka kulun,,,
Shiru nayi nadan wani lokaci,,,,ina wasa da yan yatsun hannu na,
Takara maimaita tambayar ta
Cikin tsanaki na warware mata tun lokacin da na fara ganin shi amasallaci har zuwa yau,,,,
Tanisa a, hankali tace kuma bai fada maki koshi waye ba, nace mata a,a
Shiru takarayi tana nazarin maganata,,,,,
Kidai bi a hankali kiji don mutum abin tsoro ,,,
Inda nadanji sanyin maganar taki dakikace yakaiki , asibiti kuma ya ce ki gwada mai gidan ku
Kada kiyarda wani yasan gidan ku fadima, saboda hajiya kin ji.

Tunda naga naji sauki sai ban kara barin mun hadu da wanan bawan Allah ba,,,
Na canza gurin yin harkokina,
Sai inje in saro kaya irin su jakkuna takalma da dai sauran kayan da nasan mata na bukata indinga bi masaukin Alhazai ina sayar wa ina samun riba masu yawa.
Hajiyan mu sai tana rena kudin da nake kawo mata wai sunyi kadan ita tafi gane ma indinga fita bara,,,
Yafi kawo mata kudi da yawa,
Da,taga naki zuwa baran ranan da nakawo mata kudin cikina sai ta watsa min su afuska ta dinga surfa min zagi wai ina mata bakin ciki yanzu,
Don karta sa,mu karuwa dani tun tana zagi har ta hau,fada da duka na
Saida na,jibgu sosai wurin hajiya san nan nasamu maceta aka, kwace,ni kacal a, hannuta.
Duk wanan dukan baisa na koma wurin da zanga bawan Allah nan mai taimako na ba.

Sannu sannu mahajjata suka watse kowa ya koma kasar shi akabar mu mu yan labe muna ta labe laben mu don kada akama mu.
Don da ankama kasai yadda hali tayi da mutum
Irin wanan lokacin ba komai muke samu ba so sai
Don haka mazan mu da matan mu yan takaru, sai mu dinga bin gidaje mu aikin , ana biyan mu kudi,

Muma dai irin hakan ne ta kasan ce damu,,,
Wani Alhaji aminin hajiyan mu ne ,ina, ganin,shi,yana yawan zuwa wurinta anytime,,,
Shi yataimaka mata yasamo muna guraren da zamu dan dinga neman kudi don kada a zauna hakana.
Duk da aikin da muke dan yi muna zuwa bara dan lokaci lokaci, saboda kasan cewar kasar makka kullun cikin yawan baki take baka gane dare da rana anytime akwai jama,a agarin.

Abinda bamu sani ba nid antyna Rugaiyya shine Sukaina ta gane inda muke boye kudin mu ,,,,, sai kawai muga kudi yana rage yawa .
Nidai tunda naga kudi na rage yawa nadauka antyna ce ke dauka tana wanu lalurar ta da shi
Ita kuma da taga haka sai ta dauka ai nice ke dibar kudin, saidai, da ta,ga da gaske ana zarar kudin so sai ,,,,,,
Tace min Fadima may kike saye da kudaine haka,
Cikin mamaki nace kudi wasu kudi kuma tace wanda muke tarawa mana,,
Ni tunda nake ban taba daukar ko kwandala ba acikin su,,,,
Yo nima may zan saye da kudi ,,,,, kaya dai tun wanda baban Nailabin sukayi min sunake ta sawa ajiki na har yanzu.

Nanda nan naga ta shiga cikin wani hali takai zaune tana fadin mun shiga uku ,,,,,,,,,
Akwai wace ce tagane inda muke aje kudin mu har take diba.
Nadauka ko kece ai saida naga abin yai yawa shiyasa natanbaye ki yau.
Nima nadauka kece ke anfani dasu ai,,,, yo wani amfani kudin da saura kadan mu hada kudin komawa gida mu huta da wanan bakar wahalan,,,,,

Cikin bacin rai tace aikuwa zangane ko wace take muna wanan sherin.
Tundaga ranan muka canza gurin boye kudin mu,,, amma muna dan aje saura a,gurin.
Antyna ta kula kulun zamu fita Sukaina ce ke zama ta bayan fitar mu,
Yau bayan duk mun fita sai akabarta abaya tana fadin wai sai ta dan gama abinda zatayi zata fito,
Har Yumma da mari suna mata ba,an wai tadai saba da zaman na baya yanzu,,,
Bayan fitar mu da yan mintoci sai kawai tanufi wurin da antyna take boye kudin can bayan fridge din mu kasan wani tsohon basket da muke tara tsofafin kayan mu ciki,,,,
Ta bude raggan da muke kule kudin ke nan Rugaiyya tashigo dakin sukayi arba da juna,,,
Ragan da sauran dan kunshin kudin ta karba a hannu ta ta juya tana fadin mun barki da Allah muguwa,,,,,,
Cikin daga murya tana borin kunya take fadin ,,, eh andauka din aike ma sata kike wa hajiya shiyasa nima nake dauka,,,,,
Ashe wai saurayi tayi dan bagaladi shi take bawa kudin so sai,,,,
Shikuma sai yaudar ta yake yi yana karban mata kudi yana lalata da ita,,,,,
Wai ba zai bari akamata ba,,,,,


🐎 ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP 🐎
[10/3, 20:51] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣4⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Allah ubangiji bai yo mu daidai ba, indan harka ga wanda yafika to kaima kafi wani,
Don haka yan, uwa, kai ma wanda yafika fatan alheri , karkayi masa hassada, kai kuma Allah zai maka sakaiyan na Alheri,,,,,,,

HUGUMA GROUP ina jin, jina maku tare da KAINUWA GROUP,,,, MAMAN FATI GROUP Allah yakara dauka nagode nagode,,,,,,,

Almost true life story,,,,


(NIGERIA)
DOGON DAJI

Ranan da malam jibo yadawo ranan ya kai sakona gidan mu da
kanshi,,,,,,,,,

Inna tana zaune bakin murhu tana hada miyar marance sai taji a,na kwada sallama kofar gida,,,,,,
Yaranta duk suntafi makarantan islamiya ,.
Takoma daki tajawo hijab din ta tayafa,,, zuwa ganin wanda ke mata sallama kofar gida,,,
Takusa kawai kofar yai daidai da yaran sun dawo daga makaranta,,,,
Su sukafara gaisawa da shi, suna fadin Alhaji ho Alhaji ho ,Yaushe ankadawo yace yau munka sauka,,,,
Sai ga inna ,,,,,, Alhaji jibo kaina tafe lalai da dawon ku,,,,
Banyan sundan gaisa inna tana gefe guda,tsugune tana sauraren abinda yakawo shi gidan ta ya,u,,,,
Ya tura mata sakon gabanta yace yar kulu tace na,am, Ya,sake cewa, Fadima ta tacce inkawo maki wanga sako ,,,,,,,,
Zubur inna ta mike don kaduwa jin sunan fadima da taji anyi,,,, yaciga ba da fadin awo, ita,taban wanan sakon tacce inkawo maki inda kike
Kuma tana gaishe ku,,,,
Aiko motsi bata iya yiba daga inda take,,,,
Hasfsat ta tace kaga fadima shin kaka,fadi ,,, yaca, A,woo da ijjiyan ga na,u, naganeta,
Aiko inna,sai kuka ita dayara tana fadin wayyo ita Allah fadimarta wayyo fadimata,,,,

Fadima don Allah kiyafan ni nakai ga haka,,,, malam jibo dake gefe rakube shima hawayen yake gogewa,,,,
Yai gyaran murya tun jama,a basu taru yace ke hafsi shiga da kayanga ciki tukub na,,,,
Shiganta keda wuya sai ga jama,a sun fara taru gidan jin kukan yar kulu da yaranta
Shin wai mi ka faruwa, na, nanga?
Fadimata yaggani makka ,, makkafa ? A,woo ita,ta kuwa naggani da ijjiyaga nau,
Nan yashiga basu lbr yadda suka hadu da fadima dakuma irin tai makon da tayi mai har da sayayan tsaraban da ta tayashi yasaye.
Abuguda ya boye bai fadi ba gudun datayi na kaishi masauki, ta,,,
Kowa yana ta al ajabin wanan maganar ta malam jibo watau fadima na nan da ranta a,makka zaune daram,,,
Kuma hannu mutanen kirki masu mutunci,,,
Yayi hakan ne don cire zargin yarinya kamila mai kirki fadima a,zukatan mutane ,,,
Saida komai ya lafa an watse kowa ya koma gidan shi yana fadin albarkacin bakin,shi

Cikin dare inna ta tada hafsat ta bude masu sakon da fadima ta aiko dashi,,, sugani.
Dogayen riguna ne da zanin gado cottoning masu kyau kala biyu sai kudi wanda ya kai kimani kudin Nigeria dubu dari,,,,
Aiko hankali inna yakara tsshi sam bata yarda da maganar malam jibo ba.
Tunda safe tadauki kayan taje gidan yayanta malam sale ta kai mai ,, shima yana gani yaji tsoro ,,,, Anya kuwa yarinya karama kamar fadima zata bada wanan sakon akawo mata gida,,,
Sana,ar may takeyi can da har ta samun wanan kaya haka masu kyau da tsada,,
Ya tashi yaje gurin
malam jibo dakan, shi ,nan malam jibo yakara yi mai bayani daladala har ya fahinta,,
Malam jibo yakara yiwa kawu godiyan irin dawainiyar da nayi masa acan,,,

Duk da malam sale yakwantar wa inna da hankali yaba kowa sakon shi,yan uwana sunata murna da sakon da na aiko masu dashi,,,,
Amma ita inna ji takeyi kamar tayi ihu taganta makka,,,,
Magana ya kama yawo agari malam jibo yaga Fadima a,makka tare da matar da Gajiye ta sayar mawa ita,,,
Har zuwa akeyi ganin sakon da fadima ta aiko da shi anata mamaki,,,,
Bayan kwana biyu inna tadauki kudin takai wa malam sale tace yayi abinda yadace da kudin
Shiko, sai yace tacire masu yawa asai kiwo da su saura ta sai abinci suci ita da yarant,,,
Har inna taso taki wanan shawaran malam ya dan lalabata ,har yashawo kanta tayarda ,,, yace kowa da hanyar da Allah yai mai na arzikin shi killa arzikn fadima da, su yana can ne shiyasa yakai fadima har can inda kowa nata bai taba zuwa ba gashi kuma malam jibo yace tana zaune da mutanen kirki.

Da haka inna tadan sake jikinta taba kowani yaro kayanshi tace yasa
Zanin gado kuma za,a ,aje ma Hafsat na aure ,,dama aurenta ya kusa,

Tun lokacin inna yar kulu ta kara maida hankali ga addu,a tana neman Allah yakara kare mata tar diyar ta Fadima,,,,,,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA NOVEL🐎
[10/3, 21:02] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣5⃣
B Y
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Daure ka/ki biyayya ga iyayenka domin watarana ,kaima mahaifine/mahaifiya


Godiya nake,wa,antyna Hafsata yusuf da anty mariya sb, Anty safiya mai huguma, da babban marubuciyar littafin Dan maliki ,,,,,,,,

Almost true life story,,,,,





AHAMED

Wanene Ahamed wai,,,,,

"hmmm ,,,,,,

Ahamed wani bawan Allah ne dan shekara talatin da haihuwu, fari ne irin farin da bazaka iya gane cewa ba,aciki , jinsin larabawa bakake yake ba, Saboda sajewan da jikin shi yayi danasu.
Dan Nigeria ne,da ke zaune a babban birnin Riyadh ta kasar makka,,,

Karatu mahaifin shi yakaishi yi can ,,Daga nan wani kamfani tatar mai ta kasar saudiya ta dauke shi aki saboda kwazon shi da zama gwani, afanin, gyara gyaran. Kayan nauran mai wanan fannin.
Engineering ne a maikatar da yake aiki,kwanzon ,shi, da zama gwani, yasa suka ki barin ya bar kasan,,, anturashi sauran kasashen duniya, yaje yakaro ilimi sosai,,,,,
Sauran referners na kasan saudiya masu zaman kansu suna hayanyan shi ,, Don gyara masu na,urar su, idan sun samu matsala aiki,,,
Don ,haka kudi,na shigo mai ta kowace hanya time to time, kamar ruwa,
Ahamad mutum ne shiru ,shiru wanda bai son magana kuma shi baison hayaniy akusa dashi
Mutum ne,wanda bai wasa da ibadan shi ko kadan, duk abinda yakeyi lokacin sallah bai wuce shi,,, ,,, hakan yasa ko da yaushe zaka samay shi a masallaci yana ibada,,,,,
Saikuma, ranakun aiki ba kullun ne zaka ganshi ba .
Yanada sha,awan business sosai don hakane ma yabude wasu sha guna masu kyau da kaya masu ma,ana acikin garin Riyadh da kuma garin makka,,, shagunonin suna tashe sosai saboda kayane irin nazamani zaka gani acikin su,,,,,,,
Idan lokacin aikin hajji yayi hutu yake dauka ta musam man danyin ibada .
Baya kaunar irin da bi,ar da yaga matan Nigeria suna yi acan don haka shi ko sadaka baya ba irin su,,, don yasan kwadai ne kawai yakaisu bawai rashi ba.

Ahamed haifafen garin maduguri ne,,,, mahaifi sh,i shine, Zannah garin maduguri,,,

Tun yana jariri maihafan shi suka rabu,,, hakan yasamo, a,saline, tunda daga komawa gida shan ruwan zafi da mahafiyar shi tayi,,
Yan uwanta suka rike ta, a gida suka ce bazata dawo ba ,
Dama ba wani dadi auren yayi,ba, aure ne,na,gidan ,aure na danki yan uwa suka hada ,, tare da sa hannu mahafiyar mahafin shi watau Zannah lawal,,,,,,,,,
Mahaifin shi a Landon yazauna inda ya auro hajiya mama, a,can suka hadu da ita kaunar wani abokin shine da sukai karatu Can,
Ganin kirkin dakega zannah lawal yasa yasa yayan Amina ya hadusu aure dayake shi mutum ne mai hakuri saiko ya amince da tayin abokin nashi,,
A,kano aka daura aure aka kai mashi ita can inda yake aiki london,,,
Saida hjy mama ta haifi diya uku duk maza sanan ,,,, suka dawo Nigeria da zama,,,,,, irin dabi,un ta yasa mahafiyar ,Alhaji lawal Zannah tace dole ne ya bidi yar gida ya aura.
Saboda gashi da abin hannushi amma badama yan uwan shi suzo gidan shi,,, sai ace aibasu fadi cewa zasu zo aranan ba,
Dole mutum ya hakkura ya koma inda yafito, ko kuma yuwa takar mutum.
Ire iren wanan halin yasa maifiyar shi ta je can kauye cikin dangi tasamo mai mata yar asali da mutunci.
Tunda aka kawo,ya ghana gidan zanna ta koma kamar boyi boyinsu itace mai masu aikin komai agidan.
Wani fitina ma wai,sai dare yayi karfe tara zatayi masu pepper soup na kifi, ko kaji ,ko kayan ciki,,,
Ahaka ,yaghana tai ta bauta agidan bawani jindadin aure da tasani.


Da rabon cikin Ahamed yazo, lokacin hjy mama ta tafi garin kano ganin gida ,shi ne, rabon Ahamed,, yaratsa tsakanin su,,,

Aiko tunda mama tadawo taga alamar ciki ga yaghana ,,,,,,, aiko ina wuta tasakata,,,
Fitinar ma sai ya,kara karuwa fiyeda na da,,, ga lalurar ciki ga wahalar aikin gida
Taramay taiwani fayau, da ita,
Da haihuwar yazo mata tsohuwar dakemasu aike da,sharar gida itace ta kama mata ta haihu ta haifi danta mai kama da uban shi sak,,,
Saidai shi yaron yafi uban haske da kuma hanci,,, na uwar yadebo,,,
Har kwana biyu ba,a fada ma maigidan,Yaghana ta haifu ba , bakula kuma ba abinci mai dadi irin da yakamata aba mai haihuwa, da ita da dan jaririn ta duk suna cikin wahala,,,,,
Saida tsohuwar nan mai shara, taga diyar mutane na shirin mutuwa , sai ta saci jiki tafita taje tafada ma wasu dangin su, a,cikin gari,,,,,,
Sukuma suka aika ma mahafiyar zannah lawal dontazo ta ceci diyar mutane
Tsohuwar batayi sanyi da gwaiba ba,,, tai masu dirar safiya agidan,,,,,
Yayi mamakin ganin su da safe haka,, har mama ta fara fadin,,,
Tau mu bamu san zaku zo ba gashi bamuyi abinci karin kumalo da kuba,
Tsohuwar tadaga mata hannu tace aje abincin ki ,, ina yariyar mu,da ta haihu,
A,lokacin zannah yafito da ido waje yace yaghana ta haihu ne ,,, takama wani inda inda tana cewa dama naso in surprise dinkane ,,,,
Ranan yadan yi ta maza yadaka mata tsawa yace Amina ashe baki da imani ne haka ban sani ba
Yi min shiru inji mahaifiyar shi ai,duk abinda takeyi da saninka don kai ka daure mata ,,,
Fito min da yarinya na gida ne gashinan mubar maki ki jika kisha babu dan uwan lawal da zai kara zuwa nan muddin ina raye,,,,
Wani daki da akayi acan bayan dakunan ,su aciki yaghana ke jego, acewar mama wai kada tabata cikin gida da karni.


Tunda tsohuwa tazo ta,tafi da yaghana garin su bai samu zuwa gida diban su ba,,,, da ranan suna ya zagayo yan uwan lawal,su,kasa ma yaron sunan mahafin lawal,,,,, watau Ahamad

Saida suka kai kusan sati uku agida, lawal mahaifin Ahamad,yazo masu da kaya niki niki dana uwa dana yaro,,,
Tsohuwa taita masifa tace yatafi da kayan shi ita kudin shi baida may su ba ,,,,
Dama ta yi wanan hadin ne don kada zumuncin shi dana,"yan,uwan shi ya lalace,, nan gaba yasa ta aura mai diyar kaunar ta,,,,
Saboda idan akawai yar uwanshi agidan, aidole dangi suzo gidan ganin ta koda mama bata so,,,,,,
Sai gashi ashe shi mijin hajiyace sosai bata sani ba,
Sani Allah sani Annabi ya tara ma tsohuwa jama,a aka bata hakkuri tayarda zata karbi kayan da yazo masu dashi,,,, amma batun komawa sai yaghana ta huta tukun ita da yaronta,,,,

Yau zaizo gobe zai zo shiru, kake ji,, koda yazo kuma har ya koma baiyi maganar komawan su ba,,,, ganin haka wani yayan yaghana yabishi har can birni yakarbo mata takardan saki
Ya fada mai cewa da ma don zumunci su da tsohuwa suka bashi yagana don tsohuwa da uwar su aba,guda suke,,,
Kuma koda uwar su tarasu tsohuwa ce ta koma tankar uwar su itace ke masu komai da yakamata uwa tayi wadanta
Yace to kagani babu yadda za ayi taso abu wurin mu mu hana mata .
Mungode ma Allah tunda munyi mata biyyaya munbaka kaunar mu ,
Amma kai, ka kasa mata biyayya ka rike muna kauna amana,,,,,,,,
Tunda dan uwanshi ke magana yasada kan,shi akasa baidago ba har yakai karshen maganan shi.Tabbas yasan gaskiya ne yakasa yi ma mahafiyar shi biyayya akan wanan auren ,, wai kuma badon baison yaghana bane ,aa yana son ta amma yarasa dalilin rashin kulatan da baiyi.

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


[10/4, 07:53] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
2⃣6⃣
BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎


Dan uw/ "Yar uwa , Daure ka/ki rike sallah akan lokaci domin zata sama, hasken a,fuska sanan , Watara zata taya ka kwanciyar kabari ,,,,,,,,,,,,,

Anty safiya mai huguma Anty hafsat yusuf da anty mariya sb kulun fatan alheri na gare ku bai karewa , Allah yasa mu dace da rahamar sa,,,,,,,👏👏👏👏👏👏


Almost true life story,,,,,,.



Tun lokacin da aka yaye Ahamed sai rikon shi ya koma hannu tsohuwa watau kakan shi,,,
Ita kuma mahaifiyar shi yaghana tai wani aure nan kauyen su ta auri wani malamin arabiya mai karantar da yaran garin,,, hankalinta kwance,,,
Tunda hajiya mama ta lura da cewa Alhaji lawal yana yawan zuwa kauye kai ziyara,wurin " yan uwan shi,,,,, hakan yasa,ta yin tunane,yan zu saboda Dan shi, yake yawan zuwa kauyen,,,, kuma yana kai mai abin arziki har yan uwa suna samu suna amfana da Alhaji lawal din,, jifa,,,,,, Ta mance cewa uwar shi ma tana kauyen zaune
Aiko sai ta tadda fitina wai ai ita,ce ya,dace, tarike Ahamed a hannunta ba wai akashi kauye ba,,,, kulun cikin cewa takeyi yanzu , shi wanan yaron a kauye zai tashi ga yan uwan,shi a birni kada yazo sufishi wayewa,,, tana wani tausa murya,,,,,,
Da, irin wanan dadin bakin har taciyo kan Alhaji lawal,,,
Watarana bayan yaje kauyen sai ya fito da zancen tafiya da Ahamad birni,,,,
Nanda nan tsohuwa ta haushi da fada tace babu mairabata da Ahamad ,,,tunda gurin macuciyar matar sa,ce zai kai shi,


1 Comments On TAKARI
avatar
fatima-8-7-9-6

10 months ago

Reply

I love it

Please Login or Register in order to submit comment